You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a tsananin firgice kaman
wanda akace masa ta hallaka. Murmushin qasaita ta aje

"To ai yanzu ma gashi na kasa dawowa din da kaina duk kasala ta rufeni...."

"Bari na kira driver din ya dawo ya maidaki" Ya furta da hanzari

"Kaga dakata.....wanne irin driver?" Ta fada tana bata rai

"Yi haquri hajja,me kk so?" Ya sake fada a rikirkice

"Matarka nakeso ka turomin ita zata maidani......kace ta kirani na bata kwatancen
inda nake yanzu haka ina jiranta......kada kuma ta batamin lokaci" Ta fada tana
bata rai

"An gama" Ya fada zuciyarsa na rawa.

Ta rigashi ajiye wayar ta waiwaya tana kallon maamah cikin murmushi

"Kinsan matar da nace a kiramin?" Kai maamah ta girgiza tana shakkar yiwuwar
wanzuwar umarmin da hajjan ta bada yanzu yanzu
"Matarsa ce......itace taso dagamin yatsa taso tayi fito na fito dani,a zatonta
tana da malaman da xasuyi mata aiki fiye da nawa......tanaso ta mallaki yahaya ta
mallakeni.....har na sanya ya saketa na sakashi ya dawo da ita don tazo taga
iyakarta......taga iya mizanin nawa aikin.....don tazo ta banbance tsakanin aya da
tsakuwa,ta sake kuma fahimtar da gaske fa shi ruwa ba sa'an kwando bane......ita
kanta a yanzun sai yadda nace mata,duk dana fahimci kanta yana fusga wani lokaci
kaman wasu abubuwan idan nayi mata tana jin ciwonsu,shi yasa nakeson na qarasa
horata da kyau" Kai kawai maamah take jinjinawa,abun yayi mata da kyau.....salon
kuma ya burgeta yahau mizani da gwargwado na abinda take hasashen shimfidawa kanta.
DA FUAD DA MUSADDIQ DAMA MATAYEN DA ZASU AURA SU ZAMA QARQASHIN IKONTA. wannan
shine cikakken iko da isar UWA. Ta fada a ranta

"Wannan shine cikakken iko da isa.....ki katange komai kaman yadda sanda kk sha
wahalar komai din ke daya kk sha" Hajja ta fada tana jinjina kai

"Indai ni na haifi fuad ya zama tilas ya fidda kudaden nan ya bani.....zan motsa
masa qwanjina.....zan kuma banbance masa uwa da mahaifiya a wannan lokaci karo na
farko" Maamah ta sake fada a ranta.

Ya jima riqe da wayar bayan gama waya da mahaifiyar tasa yana juya wayar
a hannunsa. Sassa biyu na zuciyarsa kowanne na qalubalantar dan uwansa.

"Tayi daidai,ko mutuwa hajja tace muyi daidai ne......ai ta isa....girmanta yana da
yawa,to laifin me ma tayi?,koni ta kira zuwa zanyi bare matata,komai tayi a kowanne
lokaci ko yanayi daidai yake" Daya sashen yake fadi,yayin da daya sashen zuciyarsa
yake cewa

"Ta yaya tana tsaka da hidimar gida,ya tabbatar yanzu haka tana can tana yiwa
hajjan girkin rana daya zama wajibi aka kowacce matar danta tayi mata shi kulli
yaumin rana da dare ba fashi......(tsarin girkin abincin gidan tsarin girki ne na
bai daya,duk da irin girma da wadatar gidan tukunya daya ake dafa abincin safe rana
dana dare,raba girki ne a tsakanin faccaloli tamkar kishiyoyi,kowacce zatayi kwana
biyu 'yar uwarta ta karba,hakanan a tattare a babban dining room dake dauke da
family dining table akecin dukka abincin. A nata fadin don a tattala mata dukiyar
'ya'ya,kuma dukkansu zasu samu sauqin kashe kudi a gidajensu,tunda kome zaa siyo
hadin gwiwa zaayi a kawo......amma kuma ta gefe daya.....tsabar nuna isa izza da
mulki ne,da kuma dabarar karantar motsin kowa cikin gidan ba tare data shiga sashen
kowa ba don ta tattaro kowa din waje daya.

A yanzun ya tabbatar tana can tana wannan hada hada.....bama wannan
ba......fita haka katsam a lokaci guda ba shiri?. Wannan sashen dake hango masa
rashin dacewar shine sashe mafi rauni a zuciyarsa,don haka wancan bangaren ya
rinjayeshi ya danna mata kira kanshi tsaye.

Sanda maamah ta bude baki da zummar sake magana kira ya shigo wayar
hajja. Ta daga wayar tana kalla,sai ta sake wani murmushi me sauti

"Naja'atu ce" Ta fada cikin nishadi,saita daga wayar tana sanyata a hands free

"Salamu Alaikum hajja......daddynsu arfat yace kina buqatar nazo daukarki......kina
daidai ina?" Fuska ta tsuke tamkar ba itace ta gama dariya yanzu ba

"Ke banason hauka......haka akeyi daga kiran waya ba gaisuwa ba komai?,duk kinzo
kin gaidani dazu da safe amma yanzu mecece?,la'asar fa muke dosa?" Shuru yadan biyo
baya kafin muryarta ta sake bayyana a karye

"Kiyi haquri,ina wuni?.....kin yini lafiya?"

"Lafiya lau" Ta furta a dake
"Ina 'yan kaba,kizo daidai bakin kasuwar turawa ki jirani" Daga haka ta katse
wayar.

Dubanta maamah tayi tana mamaki

"Hajja me kuma zai kaimu 'yan kaba?,ai sam ba hanyarmu bace" Zamanta ta gyara tana
sake sakin shu'umin murmushi

"Eh mana.....ai so nake ta sake gane girman izzar tawa......sai bayan mun isa gidan
ki zaki fahimci sauran aikin". Sosai maamah ke duban hajja din,lallai dole tasha
kan kowa da komai,dole ta murxa kambunta yadda takeso. Sai yanxu take tambayar
kanta ya akayi tayi sanyi haka ta sake?,hajjan da a baya a wajenta take daukan
courses na abubuwa amma yanzu nema take ta zama malamarta qarfi da yaji?.

"Kina mamaki ne mariya?" Ta tambayeta tana kallon hanya

"Ai duk wanda yayi bacci a wannan zamanin zaiga bacci.....ba yara na ba ba
surukaina ba.....hatta da jikokina.....yara da manya dukka sai abinda hajja ta
shimfida"........

Ji yayi tamkar an daka masa tsawa tsakiyar baccinsa ana kuma masa
umarni da ya farka. A nutse ya farka saidai kuma yanajin wani irin sauti mara dadi
yana amsa kuwwa cikin kunnuwansa tamkar dai a mafarki akayi masa tsawar. Idanunsa
ya lumshe a hankali yana son tuna abinda ya faru din,amma kansa blank bai iya
hasaso komai ba

"Hasbiyallahu la'ilaha illa huwhuw,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem"
Ya furta a hankali bakinsa yana motsawa.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 55



Tsam yayi da ransa yana jin yanayin jikinsa yana sauyawa daga ainihin
yadda ya kwanta din a dazun. Numfashi ya aje a hankali ya yaye blanket din ya
miqe,ya zauna sosai saman gadon. Duk da knocking din da akeyi din hakan bai hanashi
hada hannuwansa guri guda yayi addua ba,ya shafa saman fuskarsa a nutse sannan ya
zuro qafafunsa qasa ya miqe.

A nutse yake takowa zuwa ainihin falon nasa dake cike da nutsuwa,shuru
tamkar ba cikin gidan yake ba,komai komai cikin matsananciyar tsafta a killace
kamar yadd yakeso koda yaushe ya dinga ganin komai a hakan.

Yana ci gaba da jin jikinsa da wata 'yar maqalalliyar kasala har ya
isa qofar falon,ya murza key ya bude qofar amma bai murza handle ba,ya barta a haka
yana komawa da baya hadi da bada umarnin a shigo.

Tun bai zauna ba ta sako qafafunta falon,dauke da wani kyakkyawan
kwando me qananun tayoyi,yana da mariqi tamkar na luggage ko trolley da zaka iya
rageshi ko ka qarashi sannan ka jashi yadda kakeso.

Da sallama a bakinta da qanqanuwar nutsuwar nan da take samar da ita a
gabansa.
"Wa'alaikumussalam" Ya amsa yana zama saman daya daga cikin qawatattun sofas din da
suka yiwa falon qawanya masu tsananin taushi da kyau na gaske,yasa hannunsa yana
lalubem remote na A.c din falon don ya rageta. Shi din ba kasafai ya fiya son ac ba
ko ya qureta har haka ba,wannan din sai oga farouq,a nan ma zaka iya jin kansa
dashi.

"Hamma barka da warhaka". Ta fada cikin shagwabarta da marairaitar nan tata data
zama a halittarta. Labbansa ya motsa kadan da wani yanayi da yafi kama da murmushi

"Habibtyn hamma" Ya furta a nutse kaman yadda tsoron qarewar haruffan bakinsa.
Sunan daya kiratan dashi ya sanyata ta sake rakwarkwabewa. Ta tabe fuska tana
kallonsa

"....hamma na dauka ka daina yayi na......BB farouq yacemin ka samo wadda ta sace
zuciyarka.....tunda ta sace zuciyarka wai kuma tayi snatching naka a wajen
kowa....she owns you ita kadai". Qaramin murmushi ya sake subuce masa wanda yafi na
baya. Rigimar amna yawa ne da ita,har yau bata girma baisan kuma sanda zata girma
din ba,yafi tunanin aure ne kawai zai kawo mata wannan hankalin da girman. Gefe
daya farouq,shikam a duniya yanaso yaga ya tubura amna din,wani lokacin yana yi ne
kaman hankalinsu daya,abinda kuma bazai taba zama hakan ba

"Zo nan" Ya fada yana yafitota da hannu gami da nuna mata gefansa. Sai ta tako din
a hankali ita da kwandon nata har ta iso gabansa ta zame ta zauna sosai

"Baki gaya masa tare zaku zabi mata da hamma ba?,baki gaya masa sai wadda kikace
tayi kinaso sannan hamma ya aura ba?" Yayi mata tambayar yana kallon qwayoyin
idanunta abinda ya qara mata karsashi da qwarin gwiwa. Murmushi ya subuce mata data
tuna da wannan

"Na gaya masa hamma sai ya tabe baki,kasan me yace?" Kai ya girgiza yana qara
girmama quruciyar amna din,tabbas auta ba wasa ba,ko yaya sai wannan quruciyar ta
tabashi

"Wai ita soyayya ba ruwanta da jiran lokaci ko dacewa,sace zuciya takeyi ko an
shirya ko ba'a shirya ba....." Ta qarasa maganar daidai sanda farouq din yayi
knocking hadi da turo qofar yashigo gaba daya,don yaji muryarta alamun suna zaune
daga falonne.

Tsaf kalaman nata da suka fito daga bakin farouq din duka zauna masa
akai,sai ya daga kai yana dubansa sanda yake takowa falon. Ya bude baki zai fara
mata tsiyan nashi fu'ad din ya tari numfashinsa

"Kai kakeso ka lalatamin kunnuwan qanwa?.....kai kake karanta mata yadda soyayya
take ko?".

Wani dariya ya saki yana saka hannu ya dauki green apple guda daya
cikin apple din dake ajiye cikin wani dan kwando nan saman fridge din dake kusa
dashi yana takowa falon

"Har yanzu kallon jaririya kuke mata ba?.....zakusha mamaki sanda ta kawo wani tace
itace shi takeso,aure takeso kuyi mata".

"Hamma....." Ta fada idanunta suna yin rau rau tana duban fu'ad. Hannu ya daga mata
alamun tayi shuru kada tace komai,sai ya maida dubansa ga farouq din

"To sai me?,idan ta fada dinma ai daidai ne". Yana zama a gefansa yace

"Ni zanfi kowa murna da hakan ai......tashi ki bamu waje" Farouq din ya fada yana
komawa serious dinsa. Duk sanda yayi irin hakan ta tabbatar Lokacin wasa ya fita
kenan,don haka bata musa ba ta tsugunna tana rage plates da bowls din da tasan
fu'ad ya gama amfani dasu saboda ta sanshi bai fiya son tarkace a waje ba,yanzun
saisu sanyashi fasa cin abincin gaba daya.

Spoon ya dauka kawai ya saka a plate din fu'ad din bayan fitar
amna,wannan din ba wata sabuwar dabi'a bace,kusan sun saba cin abinci kwano
daya,tun daga wancan lokacin da suke fafutukar rayuwa da samarwa kawunansu
'yanci,har zuwa yanzun da suka zama cikakkun mutane kuma 'yantattun 'ya'ya.

A nutse suke cin abincin kuma ci gaba da tattaunawa akan tafiyar tasa.
Har suka kammala basu tashi a gun ba,sai da kiran anni ya shigo masa waya.

"Ka shiga wajen maamah kuwa?" Tambayar data fara yi masa kenan

"Zan shiga dai anni....."

"Kome kake ka barshi,ka shiga ka gaidata tasan da dawowarka"

"In sha Allah anni" Ya fada a nutse,sai ta katse wayar shima ya sanya hannu yana
sauka daga bangaren kiran gami da fidda siririyar iska daga hancinsa.

Miqewa farouq yayi abinda ya sanya fu'ad din daga kai daga zaune ya
kalleshi. Kafin yakai ga tambayar shi ya rigashi magana

"Na jima ban shiga abuja ba,ina jin gobe ko jibi zan shiga din......."

"Safe journey" Fu'ad din ya fada a taqaice yana miqewa shima. Siririyar dariya
farouq din ya saki yana tsare fu'ad din da ido wanda alamu ke nuna yana Neman
hanyan wucewa ne daga wajen

"Kar muyi haka dakai.....karka canza kuma daga yadda na sanka......ko da da sau
daya baka taba yimin kara ka rakani wajen fannah ba.....kayimin alqawari next time
idan na tashi zuwa tare zamuje......."

"Yanzun daga daukomin dogon sharhin nan farouq.....cewa nayi bazani ba?.....kawai
dai kasan ba abu bane me sauqi gajimare ya gama yawo dani na sake komawa wani
tsakanin kwana daya ko biyu kawai......infact ma kasan yanzun shirye shiryen dake
gabanmu ai.......ba cikakken lokacin batawa a irin wadannan abubuwan.....but duk da
haka bazan karya alqawari ba.....if zaka iya jirana na kammala sai muje din".
Dariya ce taso qwacewa farouq din amma ya maze,ya san dama zaa rina,kuma wannan
dogon bayanin da yakeyi duka yana neman hanyar guduwa yaqi zuwa ne.

Bai taba ganin mutumin da soyayya bata taba burgeshi ko d'ad'ashi da
qasa ba ko yaya takai ga bawa jama'a sha'awa ba irin fu'ad din. Bawai ya tsani mata
bane......aah......amma yadda yake nesa qwarai da al'amuransu kai tsaye idan kace
bai jituwa da shirginsu bakayi laifi ba.

"Kanka tsaye kacemin yanzun ma ba zakaje ba.....kacemin ka shirya nunawa fannah
iyakata....ni din ba kowan kowa bane a wajenka" Ya fadi yana hade rai sosai idonsa
akan fuskarsa. Kallon idanun farouq din yayi,bai wani damu ba yasan halin kayansa
sarai,yasan ya fada ne don ya motsashi,don haka ya daga kafadunsa

"Ka fada soyayya ne at wrong time......har yanzun kana da sauran lokaci da ya
kamata ace kana gina kanka ne bawai soyayya ba......ita soyayya idan lokacinta yayi
zata kawo kanta da kanta"

"Kaiii.....inaaa......a wannan lokacin da mutum ke bacci da qyar?,am against you fa
har abada indai ta nan wajen ne.....kaidai da waccan aljanar tayi maka shigar sauri
zamu ci gaba da nema maka magani......" Bai qarasa ba yaji saukar spoon a
kafadarsa,ya goce spoon din ya fadi qasan marbles,sai ya soma sauka daga dining
area din yana dariya abinsa gami da cewa

"Tafiya abuja dole ce......zan siya ticket harda kai......alfarma daya zan maka zan
daga zuwa next week cikin weekends din" Yana kaiwa nan ya fice abinsa daga parlor
din.

Kai kawai ya girgiza yana murmushi qasan zuciyarsa. Bazaice ko sau daya
ga sanda suka taba samun sabani da farouq ba ko wani ya bata ran dan uwansa. Wani
hadi ne daga buwayi gagara misali,idan kaga musaddiq da Sadiq zakayi tunanin sune
uwayensu daya,kaman yadda da yawa ake tunanin shi da farouq din twins brothers ne
da suke da kamanni daban daban.

Baiyi mamakin jin ba ruwan zafi a toilet kaman yadda ya saba samu koda
yaushe ba,don dukka ma'aikatansa da sauran masu masa hidiman sassansa ya basu hutu
na satittikan tafiyarsa south Korea,don haka ya kunna heater ya dawo cikin bedroom
din sannan ya wuce kai tsaye yana fita daga ciki.

Qofa ce qwaya daya tak wadda batakai duka sauran doors din falon fadi
ba,ya budeta ta hanyar key din dake maqale a jiki ya turata a hankali ya shiga.

Dakin yana da dan duhu don haka ya laluba makunni ya kunna fitila take
haske ya gauraye dakin


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 56

A yadda qofar dakin take daga waje,ba zakayi tsammanin taras da
yalwataccen daki me wani irin tsari da kyau ba kaman haka. Ci gaba yayi da kunna
kowacce fitila ta cikin dakin,kama daga ta bango zuwa kyawawan table lamps masu
wani irin kyau me daukan hankali. Wani irin guri aka tsaga daga sashen nasa da yayi
Linkin da ainihin farfajiyar gidan bangaren da duk yawan taro ko hayaniyar jama'a
da gidan zaya tara zaiyi wuya ka iya jinta muddin kana wajen. An qawatashi da wasu
irin shelves da drawers masu mugun kyau da daukan hankali da aka tsara takardu
documents zuwa litattafai nau'i daban daban daga yarukan duniya daban daban da yake
iya fahimta yake kuma iya magana da wasunsu.

Ragowar bangunan kuma manyan frames ne masu asalin kyau da tsada na
qasar turkey da dubai da aka kashewa kudade masu ciwo aka tsara sunayen Allah da
ayoyin qur'ani masu girma da wani irin ruwan gold daya sake baiwa frame din kima
kyau da daraja. Akwai kyakkyawan table din daya zama cikon ado wa home office din
nashi da yake hade da kujerarsa,sai kuma wasu cushions da aka zuba gajajjeru da ba
zasu bata tsarin wajen ba,daura dasu kadan kuma wani board ne dake dauke da rubuce
rubuce barkatai da baya rasa alaqa da tsare tsare na abubuwan da ya sanya a gaba
zaiyi.

Komai na room din neutral color ne kaman yadda dayan bedroom dinshi
yake,abinda zai bayyana maka kenan normally bayason kaloli masu hayaniya can can
can.

Da gaske a yanzun target dinsa shine bude kamfanin......babban burin
da a yanzun bashi da wani sauran abu daya rage masa kamar shi,saidai abune daya
tabbatar yana buqatar qarin jajircewarsa da kuma aiwatar da komai cikin sirri har
sai an kai gabar da ya kamata komai din ya bayyana.
Ba alaman qura ko datti ko qwalli daya,don duk wanda ke aiki dashi
yasan tsarinsa da kuma dokarsa. Waje ne da ba wanda yake bari ya shigar masa sai
family dinsa,anni farouq amna saddiq sai musaddiq......sai kuma amintaccensa mutum
guda daya me sunan malam.

Ya bude lockers da yawa,ya kuma jona abubuwa da yawa kafin ya
daidaita komai ya juya yana fita a dakin da zummar zuwa sanda zai dawo komai ya
zama normal,don yau din aiki yakeson yi sosai kafin ranar Monday ya isa kamfani ya
duba yadda ya barsu.

Fes ya fito a shirye,sanye da lallausan yadin filtex fari qal mai
qarancin nauyin da har kana iya hangen farar vest din jikinsa data lafe takuma saje
da yadin sosai saboda tsananin haskenta. Sassanyan qamshin nan nasa dake da daukan
hankali yake fitarwa sannu a hankali,fuskarsa tayi fresh cikin yanayin da zai nuna
maka cikakkiyar nutsuwar zuciya da ruhi da yake da ita. Sabanin wasu lokutan,yanzun
kanshi saye yake da hular data dace da yadin jikin nasa,sai half covers din daya
sakaye doguwan qafansa a ciki.

Komai rashin nisan waje bazai taba iya taka qafarsa ba tare da ya
sanar da anni ba,yanzunma sassanta ya bulla,yana tafe yana amsa waya har ya cimma
sassan nata.

Bai iya ci gaba da amsa wayar ba sanda qafafunsa suka shiga ainihin
falon,sai ya zare wayar daga kunnensa sakamakon sautin karatun qur'ani dake fita
daga speakers din dake daura da qatuwar plasma din dake girke saman mulmulallen tv
stand din.

Karatu ne cikin muryar babban malaminsa sheik abdurrahman
assudais,qira'ar dake balain kashe masa jiki tare da saukar masa da nutsuwa koda
yana cikin bacin rai. Falon anni na dabanne,badai ka shigo ka samu ana kallace
kallace marasa ma'ana ba bare akai ga batun jin kida ko waqa,kusan duka haka ta
azasu akai,suma kuma haka suka taso.

Lokaci irin wannan magariba ke kan hanyar qarasowa,zaka sameta zaune
cikin kamala tana wani abun da zaya amfani lahirarta,imma girkin abba ita da
amna,ko ka sameta da carbi,ko tana sauraren wani karatun addinin.

Yanzunma suna tare da amna din,wanda daga gefan amnan kadan wata
baquwar matashiyar ce da zata girmewa amna din da aqalla shekaru biyu ko uku.

Yana shigowa ta sanya remote tayi qasa da karatun sosai tana
murmushi. Ya qaraso a nutse ya zauna daga gefanta yana tanqwashe qafafunsa tamkar
ba wanda yayi shirin fita ba,sai kuwa ta tareshi

"A'ah miqe....ai sai ayi magariba kana zaune a nan.....kaje ka dawo.....don abincin
dare ma yau banda kai a gidan nan" Girarsa duka biyun ya daga alamun mamaki,yanayin
daya qarawa fuskarsa wani irin kyau,ya kuma fusgi hankalin matashiyar qwarai da
gaske

"Anni yau din nayi wani laifi ne....?" Ya fada calmly idonsa akan annin. Kai ta
girgiza

"Ko kadan......kawai nasan idan kayi dinner a daya gidan naku hakan zai farantawa
maamah sosai,zai kuma sake bada fahimtar juna da shaquwa a tsakaninku". Tayi
maganar cikin kwantar dakai itama tare da fatan kaishi zuwa ga abinda takeso din.

Kansa yadan motsa kadan,har yanxu anni kaman bata fahimci daga ina
ainihin tushen matsalarsu ya fara ba?,har yanzu kuma kamar annin bata fahimci
menene yake riqe da matsalar tare da sake wanzar da ita ba?,wanne fahimtar juna da
shaquwa a yanzun ake nema tsakaninsu ne?.

"Saika dawo......kace ina gaidata" Ta fada tana daukan remote zata qara
volume,abinda ke alamta masa ta gama fadin bayaninta kuma batason yayi sharhin
komai akai

"Hamma....." Amna ta kirayi sunansa tana murmushi idonta a kansa.

"Lovy dovy" Ya fada yana xuba hannunsa a aljihun rigarsa yana jin karsashinsa da
duk wani walwalarsa yana ja baya tamkar wanda aka tura gidan kaso.

Murmushi tayi,tsokanarsa takeso tayi amma kwarjinin nan nasa ya taso ya
danneta

"In fada hamma?" Tayi masa tambayar tana dubansa

"Say it amna....." Ya maida mata cikin caring din daya kusa sanya matashiyar
narkewa. Bata taba zato koda a mafarki yana da wannan siffar ta kulawa haka
ba......bata taba hasashen akwai dabi'a ta sauqin kai a tattare dashi har haka ba

"Muhammadu.......yi tafiyarka......ku wuce ciki keda unaisa ku wankemin bottles
dinnan,suna kitchen basu da yawa".

Duk da yaso ya wuce din kamar yadda anni tace amma dole sai daya dan
tsaya a farfajiyar gidan suka gaisa da ma'aikatan gidan,sannan kuma me sunan malam
yayi masa tattaki suka fice daga gidan bayan ya shaidawa security dinsa ba nisa
zaiyi ba baya buqatarsu.

Yana takawa a nutse yana sake fuskantar gidan wani yanayi yana
riskarsa,abubuwa masu tarin yawa da suka saba dawo masa a duk lokacin da zai gifta
ko ya shiga gidan.....al'amura masu nauyin dake iya motsa zukata qwarai da gaske.
Wannan yana daya daga cikin abubuwan da suka sanya yake janye jiki da rayuwarsa
sosai daga gidan. Duk da komai na fasalin gidan ya canza,ba wani abu da yayi saura
dangane da ainihin ginin gidan na baya,to amma dai wannan filin....wannan gurbin da
wannan muhallin da aka aza tubalin ginin gidan har yanzu dai shine a wajen. Har yau
har kwanan gobe idanunsa basa mantawa da tsarin gininsu na asali,wannan ya sanya
idan ya kalli wasu guraren sai ya tuna da JADDA sai kuma ya tuna da ABBANSA,duk da
guraren a yanzun sun sauya sun koma wasu abubuwan na daban,amma tambarinsu yana nan
kafe qasan ransa da zuciyarsa.

Cike da girmamawa,martabawa tare da kallon Cikakkiyar kima da darjtawa
malam sa'idu yake miqewa sanda ya fuskanci dosowarshi gidan.

"Barka da zuwa yallabai.....sannu da zuwa" Malam sa'idu yake fadi cikin mutuntawa.

"Barkanmu da warhaka baba.....mun sameku lafiya?" Fuad din ya furta shima cikin
tsananin bada girma. Malam sa'idu bawai me gadi bane kadai a gareshi,yana da wani
role da yake takawa da kuma wani ajiyayyen matsayi da fuad din ya bashi ba tare da
sanin kowa ba.

Malam sa'idun da asalinsa me saida kayan marmari ne a bakin titin tsohon
layinsu,wanda a yanzun layin ya koma tacan katangun gidansu yake,qofofin sun dawo
bayan gidansu na asali,inda kusan gaba daya fuad din ya siye layin sai tsirarun
gidajen da suke mazauna ciki suna da buqatar zama a ciki. Tun asali bayan layin
nasu suna kiransa ne dama da layin 'yan gayu,don kusan manyan gidaje ne ata
wajen,kamar yadda kusan mafi rinjayen unguwar tasu layinsu ne kadai keda qananun
gidaje jifa jifa. To a yanzun layin duka ya zama qarqashin kulawar fuad da wani
irin kwalta da aka zuba,gate a farkonsa da qarshensa da manyan fitilu jere
reras.....cctv cameras da masu gadin layin saboda tsaron dukiyar mazauna layin da
rayukansu.

Bayajin malam sa'idu zai iya ficewa daga tarihin rayuwarsa ko
zuciyarsa. Yadda mahaifinsa baya iya cin komai haka malam sa'idu zai hada fruit ya
bashi daidai qarfinsa lokaci bayan lokaci duk sanda Allah yakai wucewar fuad ta
wajen,ana tsaka da haka malam sa'idu yaje ganin gida,bai kuma dawo ba har sai bayan
wasu shekaru. Bai manta da yadda malam sa'idu ya nuna jin ciwon rasuwar abbansa
ba,wannan ya sanya ko

Please Login or Register in order to submit comment