You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauqi irin haka?" Hajja ta yiwa
maamah tambayar da taketa cin ranta.

Wani murmushi maamah ta ajiye tana goye hannuwanta a qirji,daidai sanda
sabreen ke shigowa wajen tana takowa cikin nutsuwar nan tata me fusgar hankali,sai
maamah din ta dauke idanunta daga kanta ta maida ga hajja ba tare data bawa ganin
data yi matan muhimmanci ba,amma abu daya taji ya darsar mata a rai

"Da mata masu kyau irin haka ya kamata ta yiwa fu'ad din fatsa.....domin su din
suna da saurin kama zukatan mazaje".
"Komai lalacewar uwa uwa ce.......hakanan komai lalacewar d'a yasan me ake nufi da
uwa.....ballantana fu'ad da nasan me na haifa?,nasan iya matakin kaifinsa da
kafiyarsa......wannan ba wani abun damuwa bane".

Ba tare da jira ko neman izini ba taja spare kujerar dake gefansa ta
zauna. Shimfidadden kyan nan dake fusgar zuciyarsa tunda can baya wanda ya jashi
zuwa ga wanzuwar alaqa tsakanin su a yanzun sai yakega ya ninka yadda yake a baya.
Fuskarnan a rubuce da dabi'ar miskilanci baro baro samanta.

"Zuwa da kai ai yafi saqo ko?......ka nema qanwar ga yayar tazo da kanta.....zaifi
kyau a sauka ta inda aka hau". Tayi maganar a jejjere da wani irin aji da kintsi
daya qara kwarjantata a idanunsa.

Zuciya da ruhinsa suna masa d'ari d'ari gami da gargadinsa a kanta,to
amma kuma wani sashen na zuciyarsa na bashi tabbacin tabbas yaci wasan
ne......lallai ta fuskanci cewa shike da nasara wannan dalilin ya sanya tsananin
wayonta ya bata shawarar tayi gaggawar bada kai.

Wata irin dariya ya kece da ita yana kallonta gami da gyara zamansa sosai

"Haba 'yammata?,irin wannan karaya haka da sauri?"

"Karaya kuma?......sabreen bata taba karaya ba.....hakanan ba zata karaya akan
wulaqantaccen mutum maras daraja irinka ba". Mamaki ne ya lullube farincikinsa,a
hankali yanayin fuskarsa ta sauya.

"Daga yanzu zuwa sanda zaka isa gidan birsin ka fara qididdige yawan adadin
haramtattun kudadenka da zasu salwanta bayan cafke jirgin da aka boye cocaine me
nauyi,wadannan kudaden an samesu ne ta hanyar maida mutane zuwa dabbobi wajen basu
gurbatattun magungunan bugarwa da sanya maye.....kaga kuwa garin banza a farau
farau din banza yake qarewa".

Wani irin shock ya shiga saboda kiran sunan jirgin da ayau yake sanya
ran isowarsa. Ya lissafa yau a ranar sa'a a gareshi.....zai aike mata da sakamakon
abinda tayi masa ta jikin 'yar uwarta......hakanan kuma zai maida gurbin hasarar da
yayita jiran cikewar gurbinta.

Bai qara koda motsi daya ba sautin takun ma'aikatan cikin sassarfa da
hanzari ya karade gurin. Hankalin kowa dake wajen ya tashi yayin da aka soma kallon
kallo a tsakanin juna.

"Kada wanda ya motsa.....munxo kama me laifi ne.....kowa yana cikin aminci.....amma
kada ku motsa har sai mun gama mun bada umarni" Daya daga cikin ma'aikatan da ba'a
iya ganin fuskarsa yayi maganar a gaggauce.

Ance mara gaskiya ko a ruwa gumi yakeyi......wannan ya sakashi miqewa da
zummar samun hanyar fecewa,saidai kuma tuni suka ankara suka masa qofar rago gami
da fadin

"U are under arrest!". Wadannan din ba irin ma'aikatan daya saba gani bane,rana
dubu ta barawo,ya tabbatar idan har ya saba kubce musu to a wannan karon babu
wannan damar,don haka ya tsaya kyam jikinsa yana kyarma har suka gama.

"Koda ka sake samun rayuwa a nan gaba.....kayi komai da lura" Ta furta tana nuni da
gefen kanta,sannan ta juya a nutse ta fara takawa

"Thanks for the information" Daya daga cikin ma'aikatan ya furtawa sabreen din da
ta fara barin wajen. Murmushi ta saki kadan
"Wannan aikin kowanne dan qasa na gari ne"

"Gaskiya ne" Ya furta yana saluting nata,yayin da suka waiwaya zuwa ga Naseer suka
riqeshi sosai suka sanyashi a tsakiya suna fita dashi ta daya qofar cikin hararrami
da tsaurara masa tsaro.

"Keep calm......you're safe guys.....kowa yaci gaba da sabgarsa". Mutumin da yayi
musu jawabin farko a yanzu ma ya fadi sanda yake bin bayan abokan aikinsa da
sassarfa.

"Tabbas akwai wata boyayyar fuskar a bayan wannan" Muryar hajja ta daki kunnen
maamah wadda idanunta ke kan hanyar da sabreen ke wucewa.

Dauke kallonta maamah tayi zuwa kan hajja

"Kada dai ace tunaninmu yazo daya?"

"Me kenan?" Hajjan ta cewa maamah tana dubanta

"Na samota.....inaji a jikina zata iya.....inaji a jikina ba iya fuskar da muka
gani yanzu ce kadai a tattare da ita ba.....zo muje" Maamah ta fada tana jan hannun
hajja zuwa hanyar da sabreen tabi.

"Inason insan wacece.....inaji munzo nan ne a yau domin cikar burina" Maamah ta
fada tana jin wani irin nutsuwa da fuskar data gani din.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 91


Agogon fatar dake daure a hannunsa ya duba bayan yadan gyara shirt din
jikinsa. Lokacin da yake hutu na mintuna ashirin zuwa talatinne a yanzu.

Iska ya furzar daga bakinsa yana duba adadin mutane da jerin sunayen
wadanda keson ganinsa ta qaramar computer gabansa wanda mutumin da yake kula da
sashin da zaka soma tsaiwa kafin ka samu damar ganinsa ya tura masa wato mr
abdulhaleem.

Mikail shine mutum na farko cikin jerin sunayen,to amma baya buqatar
ya fara da ganinsa,don hakan zai iya hasala fushinsa ya gaza ganin sauran mutanen
dake da muhimmanci su ganshi din.

Me sunan malam ya kira,ya bashi apple da strawberry sai ruwan dumi.
Mintuna goma kacal ya bawa kansa sannan ya fara bada umarnin shigowar baqin.

Duk wani mutum me muhimmanci sai daya kammala da ganinsa kafin ya bada
umarnin shigowar mikail,wanda zuwa sannan yayi imanin inda za'a auna jininsa yakai
dari biyi qila harda talatin ma.

Sanda yake shigowar fu'ad din yana tsaye daga bakin book shelve din
da aka yiwa wani kyakkyawan tsari cikin office din. Dukkan documents din da suka
shafi case din yake cirowa a nutse yana qoqarin danne yadda ranshi yakeyi yana
baci.
Ba kaman kwanakin baya kadan da suka shude ba.... Lokacin da yake da
daraja da martaba ta gaba gaba cikin kamfanin......a lokacin da zaiyi sallama cikin
girma da mutunci cikin office din,ya tako kaman kowanne ma'aikaci da Allah ya
tarfawa garinsa nono yake iya idanu biyu da muhammad jadda din kai tsaye ba tare da
shamaki ba. Akwai dubban ma'aikatan dake kamfanin wanda basu taba idanu biyu dashi
ba......amma shi yana cikin wadanda zasuyi tattaki har zuwa cikin office din su
zauna saman kujerar da ake bawa kowa don ya tattauna da CEO din.....a yau din sai
gashi a matsayin qasqantacce,me tarin laifukan da baisan ta inda zai fara kare
kanshi ba. Ya fadi gaskiya?,wadda ya tabbatar fadar nata wata faduwa qasa ce
wanwar......yayi qarya?,ita kuma ta zame masa alaqaqai da babbar matsala a duk
sanda me jadda din ya gano ainihin matsalar.

A nutse ya juyo abinsa ba tare daya kalli sassan da mikail ke gurfane
saman gwiwoyinsa ba. Baice komai dashi ba sai daya koma saman kujerarsa sannan ya
motsa bakinsa a nutse

"Tsugunna kazo kayimin ko bayyana min gaskiya?....idan kuma duka ba wannan ba ka
shirya amsa tambayoyin muhammad fu'ad?" Ya qarashe qarshen maganar yana dauke
idanunsa daga kan file din yana zube masa su.

Kallonsa kadai ka sanya razani a zuciyar mutum,ballantana ma mutum
irinsa maras gaskiya ko qanqani?.

"Na shirya sir.....don Allah kayimin rai"

"Gaskiyarka kadai ita zata fiddaka.....am listening" Ya furta yana dora qafarsa
daya kan daya,sannan yayi relaxing bayansa sosai da fuskar kujerar tana juyata a
hankali,wanda banda motsa kujerar da yakeyi idan ka kalli kyakkyawan fuskarsar nan
me shimfidadden kwarjini zakayi zaton bacci yakeyi.

Bai boye masa komai ba......ya gaya masa komai yadda ya
wakana......saidai statement dinsa na qarshe da harshensa yaso sarqafewa

"Saidai.....daga b.....dag.....ga baya na gano da ita da wan....."

"Da wancan tsohon dan cacan UBA NE DA 'YARSA BA ka gayyatosu suka taba dukiyar da
gumin halal ya tarata?!" Ta furta da wata irin tsawar da hatta mutumin dake qofar
farko bama reception na office dinsa ba zai iya jiyo tartsatsinta,bayan dukan table
din da yayi da hannunsa abinda ya sanya wasu files din da takardun misplacing daga
inda suke.

Har cikin tsokarsa yake jin fushin yana masa tasiri.....bai taba ganin
an raina masa wayo kaf rayuwarshi irin wannan lokacin ba. Sanda yake kammala
binciken da sakamakon daya karba daga hannun wadanda yasa suyi nasu binciken ya
duba yaga conclusion nasu yayi daidai da nasa.....saidai duk da haka zuciyarsa tana
masa kokwanto.

Ta yaya 'ya zata zama KARUWA?.....yar fashin YANAR
GIZO.....MAYAUDARIYA ME SACE XUKATAN MAZA DON KAWAI TAYI AMFANI DASU?. Sannan kuma
ace uba ya zama DAN CACA?,WANDA ZAI IYA ZUBA KOMAI A CACAR NAN DON NASARA TA ZAMA
TASA CIKI HARDA TAKARDUN GIDAN DA MARAYU KE ZAUNE A CIKI?.

Dukka jikin mikail bari yake kai kace wanda aka watsawa ruwan qanqara ne
cikin hunturun matsanancin sanyi.

"Kayi haquri yallabi.....tuba nake.....kayimin gafara kayimin aikin rai....wallahi
banci komai a ciki ba sir.....ko sisi sai nawa kudaden ma da suka narke!"

"Will you shut your mouth or not?!" Ya sake fadi da wata gigitacciyar tsawar data
sanya fitsari balle ma mikail din,ya kuma koma yayi zaman dabas a qasa don ya gama
sarewa.....ya kuma yi imani bashi da sauran mafita.

"Ni zaku mayar dan iska?,dukiya ta halalina a gidan caca?,a wajen karuwai?,a wajen
sabon Allah?.....ko an gaya maka ni ban san dadin rayuwa ba?,sai kai?......to daga
kai har su wannan shine zai zame muku aikin ashsha na qarshe da zaku
aikata.....daga kaina ba zaku sake marmarin sake aiki irin wannan ba......ka tashi
ka fita ka bani guri.....zan nemeka.....idan kaso ka gudu duk inda kakeso" Ya fadi
yana huci idanunsa da suka sauya launi akan fuskar mikail da yayi jalaf da gumi da
fitsarinsa.

"Na roqeka sir......kayimin duk kalar hukuncin da zakamin a yau basai wani lokaci
ba......amma ka yiwa Allah kada ka koreni daga bakin aiki koda zaka sauyan
matsayi".

"Naci gaba da biyanka albashi kaci gaba da shan barasa da neman mata.....ka bacemin
a wajen tun ban gama tunzura ba!' Ya amsa masa yana sake jin zuciyarsa tana hasala.

Ajiyar zuciya gami da iska zazzafa ya dinga fesarwa bayan fitar
Mikhail din. Ya sake komawa yayi relaxing sosai yana jin wani irin huci yana fita
daga fuskarsa. Ya tsani dukkan wasu ayyukan ashsha......mikail yayi masa abu mafi
muni....abu mafi munin koda dashi kadai ya kamashi cikin company dinsa zai iya zama
silar korarsa ko rasa aikinsa....NEMAN MATA.....zina itace abinda yafi qyamata
cikin rayuwarsa bayan shaye shaye,dukka rayuwar mikail ta dagula ta kuma gurbata
cikin wadannan ayyukan. Wata qyama ta mikail dama yarinyar gaba daya suka sake
kamashi,ya waiwaya fannin caca......abar data tabbata da nassi cewa haramun ce
itama qarara.....

"Wadanne irin ahali ne wannan?" Ya furta a fili qasa qasa zuciyarsa na masa wani
irin ciwo. Baisan girman tsanar da ya yi musu ba....ko don ya taso ya samu
nagartaccen mahaifinsa ko yaushe yana jaddada musu su guji su kuma nisanci wadannan
abubuwa iya gudunsu?.

Wanne hukunci ya dace yan yankewa mikail?,tsohon dan cacar da kuma 'yar
kwaltar Yarinyar?. Wannan tambayar ce har ya gama zamansa a company na wunin ranar
bai samo amsarta ba.

Yau koda ya koma gida sai yaqi zaman sassansa.....ya zauna sosai
sunyi dinner dukkansu kaman yadda suka saba a duk sanda dama ta basu irin haka
dukansu su shidan. Sun jima suna hira tsakaninsa da abba,wanda anni na gefe tana
jin gwarazan 'ya'yan nata. Qauna da kuma wani alfahari dasu yana ratsata.

Sha daya saura ya sanya qafafunsa a sassansa,wanda kamar tunanin yana
tsaye daga bakin qofa yana jiransa ya mamayeshi. Yaja dogon tsaki kamar zai tsinke
harshensa......ya taka a hankali yana zarcewa toilet bayan ya sanya me sunan malam
ya sallami kowa,masu kwanciya sun kwanta,masu kwana bakin aikinsu sun kama wajen
tsaiwarsu.

Shafa'i da wuturi yayi a kebantaccen wajen daya ware saboda ganawarsa
da ubangijinsa. Koda ya idar sai yayi zaune saman abun sallar. Yana jan
hasbunallahu da duk dare bata wuceshi qafa dubu da la'ilaha illa anta subhanaka
inni kuntu minazzalimin. Iya wadannan abubuwa guda biyu ya tabbatar suna taka rawa
me yawa cikin rayuwarsa,sun kuma zame masa mabudin sirrin nasararsa.

Har ya kammala ya kasa tsaida hukuncin da zaiwa kowannensu,har sai daya
hau saman lalallausan gadonsa,ya dauki qaramin remote yana sauke rumfar gadon da ke
tattare ba lallai ka lura ma da ita,kyakkyawan net din ya sauko ya lullube gadon
ruf yana bada wani dim light da ke bawa bacci nutsuwa.
Numfashi me zurfi ya sake ja yana jingina bayansa da pillow hadi da
lumshe idanunsa kana ya budesu. Kamar wannan kawai ake jira yayi qwaqwalwarsa ta
fara aiki.

"Mikail ya dade da zama korarre daga dukkan wani aiki da yake da nasaba da jadda
diamondchore resources company......kamfanin dake kano ko lagos.....koda kuwa aikin
shara ne cikin kamfanin........mutumin da ake kira da samaila fa?,idan yace ya dawo
masa da dukkan abinda yaci nasu horo ne me sauqi.....dole ya hada masa da wani
abun....YARINYAR KUMA FA? .

Jan duvet dinsa yayi yana lullube fuskarsa har zuwa kanshi. Koda a qasan
zuciyarsa bayason tunata. KARUWA wani suna ne daya samu gurbi cikin kunnuwansa tun
yana da shekara goma sha uku a duniya.

_"mariya......bansan me yasa idanunki suke makancewa ba da barin daidai.......kina
matsayin matar aure.....wadda ke auren sunna da yara har guda biyu,me zai hadaki
alaqa da qawance da karuwai?"

"Karuwai?,hmmmm.....bakasan a yanzu babu wanda yakai karuwa mutunci ba?,saboda
zaunannun kudi gareta da zata yiwa duk wanda taso ihsani.....kyautar ban girma da
ban mamakin da ke da kike qarqashin inuwar aure baki isa ki sameta ba.....kaga kuwa
karuwanci ai ya biya su".

Muryoyin dukansu su biyun da irin zancan da sukayi a sannan ya dawo
masa tarwai cikin kwanyarsa abinda ya sake qarawa zuciyarsa wani irin zafi da
radadi. Abbansa dake kwance a qarqashin qasa yanzu......da kuma maamah din da take
rayuwa dasu a yanzun hakan itama. Wani yanayi ne da bayason tunashi......wasu
abubuwa da binnesu yafi zama alkhairi a gareshi duk da yadda kullum suke qona masa
zuciya da mafi zafin ciwo da suka.

"Dole ta fuskanci hukunci me girma....." Ya fada yana bude idanunsa,ya dauki
wayarsa ya aika gajeran saqo sannan ya koma ya kwanta yana qoqarin tilastawa kansa
yayi bacci.

Kwanaki ukun da ya dauka yana dakon jiran kira daga wajen Muhammed
jadda sai suka zame masa tamkar me jiran ranar mutuwarsa ne. Komai ya tsaye masa
cak.....wata iriyar nadamar sanin sabreen dake a mazaunin fateema a wajensa tana
mamayarsa irin nadamar dashi kansa baisan yawanta ba.

Ranar da saqo daga kamfanin jadda din kwana yayi yana zawo. A gobe
jumaa....juma'ar da baisan yaya zata kasance masa ba.

****takardun gabanta ta jawo ta rufe a nutse tana maida dubanta kan
fuskar hajja dake shan lafiyayyen nonon da aka zubawa madara aka kuma niqeshi cikin
'ya'yan itace masu dadi.

"Na gode sosai qawata.....na gode qwarai da gaske......tabbas banda ke koda komai
zai tafi zai kasance me wahala a wajena..... Banda abinda zan iya biyanki
dashi,kedai Allah ya bawa autarki miji na gari". Wani qasaitaccen murmushi hajja ta
saki tana Ajiiye mug din dake cike da furar idanunta akan fuskar maamah. Ita daya
tasan me take tsarawa cikin zuciyarta,ita kadai kuma tasan me ke kai kawo a ciki

"Ameen mariya......banda abinki mene ne amfanin amincin?,mene ranar
amincin?......yanzu kawai abinda ya rage shine.....muyi tattaki har zuwa cikin
gidansu don mu sake tabbatar da komai a kanta.....daga nan sai mu saka rana ta
daban da zamu tunkari yarinyar.....komai ina ganin bazai mana wahala ba......ina ji
a jikina zata karbi komai cikin sauqi da hanzari,tunda kudi ta fito nema......mu
kuma biyan buqata kawai mukeso". Kai maamah ta jinjina farinciki yana lullubeta.
Hasken nasararta da dukkan wata lamba ta nasara tana walqawa cikin idanunta.
"A shirye nake na rasa komai don wannan abu ya tabbata" Maamah ta furta

"Ba zaki ma rasa komai din ba.....don komai zai fito ne daga jikin wanda ake abun
don shi" Hajja ta fadi tana sake sakin murmushi.

"Ina jin me zai hana yau mu shiga gidan nasu?,tunda ga adress nan da komai jikin
takardar?" Maamah dake sake duba takardun ta fadi

"Da zafi zai haka?......"

"Bakiji abinda bahaushe ya fada ba?,da zafi zafi ake dukan qarfe?" Maamah ta katse
maganar hajja,sai kuma suka saki dariya dukkaninsu.



*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 92


Cikin wani dan banzan lace peach colour da torches na purple maamah din
ta shirya,sannan tayi amfani da wani irin luxury veil me wani irin lafiyayyen jiki
ta lullube jikinta dashi. Tun daga takalmi da jakar hannunta zaka sallamawa
shigartata,ballantana azo ga sarqa da awarwaraye zuwa zobunan gold data sanyawa
yatsunta guda hudu kowanne hannu bibbiyu.

Cikin motocinta ta sanya driver ya fidda wadda bata fiya shiga ba,aka
gogeta tas ainihin kyawunta da qyallinta ya sake bayyana.

"Gaskiya kin fini gaggawa mariya" Hajja dake shiga cikin motar ta furta tana 'yar
dariya.

Ajiyar zuciya maamah ta saki tama girgiza kai

"Mariya kenan,ba zaki gane yanayin da nake ji ba,saboda ke komai ya miki daidai
cikin rayuwarki,yara biyu?,amma ba guda daya wanda zaka juya yadda
kakeso?......zaiyi wahala idan har yarinyar tana cikin gidan ma ban nemeta
ba......gwara mu yita ta qare hajja.....idan na samu yadda nakeso ma zuwa qarshen
watan nan a gama komai ta tare na fara aiwatar da aikina.....don na samu labarin
dab yake da kammala ginin wannan gidan da nake burin kasancewa a ciki ni da duk
wanda naso naga dama". Kai hajja ta jinjina tana sauke boyayyar ajiyar zuciya. Tafi
kowa buri da kwadayin wannan gidan,saboda bahaushe yace gani ya kori ji.

Tayi yawo da qafafunta tsakanin katangun gidan,ta kuma samu ganin iya
abinda Allah yayi tana da rabon gani,don hatta ginin da akeyi qarqashin kulawar
security ne,so shiga ko fita din yana qarqashin kulawa.

"Karki damu.....komai zaizo yadda muka tsara qawata"

"Haka nake fata" Dukkaninsu sukayi maganar cikin ransu suna gamsar da kansu tasirin
tasarrufinsu ba tare da sun tsarma kalmar IN SHA ALLAH a ciki ba.

Idanunsu kaf cikin layin lokacin da motarsu ke gangarawa,suna lissafe
da kowanne gida da suke giftawa har suka qaraso babban qofar gidan

"Yauwa......tsaya a nan,shine wannan da alama" Hajja ta fadi tana baiwa driver din
umarni.

Tare suka fito kowa ta qofa daban daban,maamah ta soma gyara lullubin
kanta tana duban gidan. Gida ne da kana masa kallon farko zaka fahimci a wani
zamani da can mamallakin gidan yana cikin sahun masu arziqin wancan lokacin,to amma
duk da hakan data fuskanta sai tadan tabe baki

"Banda lalura da neman biyan buqata babu abinda zai sanya na nemawa fuad aure a
irin wannan gidan........bari amma ba komai.....ranar biyan buqata rai ba'a bakin
komai yake ba,muddin komai ya kammala,xan sanya binciken qwaqqwafi sai na nema masa
auren yarinyar da tafi kowacce 'ya gata a al'ummarmu.....sannan kuma wadda zata
dace da tsarina". Murmushi hajja ta saki tana jin maamah tana motsa mata wani abu
cikin ranta.

"Qwarai kuwa qawata......dan gata ai sai 'yar gata,amma naji dadi da kika fahimci
nema masa wannan ba matsala bace.....tunda AUREN WUCIN GADI NE AUREN BIYAN BUQATA".

Ranta a sake tana murmushi suka fara kutsawa gidan suna magana da juna
qasa qasa.

Har suka dangane da babban tsakar gidan gidan basu hadu da kowa ba.
A irin wannan lokacin lokaci ne da yara da sauran wadanda suka tasa cikin gidan
suka jima a makaranta har wasu ma suna dab da tasowa,don haka ba kowa din sai
tsakar gidan dake a tsaftace kamar kullum.

"Salama alaikum.....gafaranku dai mutanen gida" Hajja ta ware muryarta ta kwarara
sallamar idanunsu yana yawo bisa tsaftataccen tsakar gidan.

A hankali ta bude idanunta dake a lumshe,kimanin awa guda tana
kwance a haka saman doguwar kujerar falon tun bayan kiranta da JIB yayi ya shaida
mata an rarraba wasu cikin kudaden a account din mutum dubu d'ari tsaffin 'yan
pension da suka rasu da bashin banki,wanda hakan ya sanya ake cirewa daga cikin
abinda gwamnati ke bawa iyalansu duk wata. Hakan ya tagayyara iyalai da dama,domin
basu da qarfin biyan kudin bare su tsira daga zari d'ai d'ai da banki yake musu.
Cikin ranta da jikinta takejin wani irin sanyi kamar ta aiwatar da wani wajibi da
yake kanta. Ta zame ta kwanta cikin mutuwar jiki tana tuna yadda bashin bankin ya
zamo silar shigarsu halin ni 'yasu bayan rasuwar abbansu,duk da cewar bashi yaci
bashin ba ci masa akayi babu saninsa babu kuma yardarsa,rayuwar ta dinga qwallo
dasu har zuwa sanda tasu mahaifiyar ta sake tafiya ta barsu da tsanani da uqubar
rayuwar. A yau tasan iyalai da yawa zasu kwana cikin farincikin da take fata ya
zama sanyi da haske cikin qaburburan mamatansu ciki harda iyayenta.

Ta jima a kwancen tana tunanin me gobe zata haifar mata?,a wanne gurbi
zata dora rayuwarta wadda daga rana irin ta yau takeso ta koma aminatu dinta ba
sabreen fateema minal da sauran tarkacen sunayen data yita rabawa maza ba. Ta zauna
taci gaba da kula da rayuwar qannenta dake da matuqar tsada da muhimmanci a gareta.

Tanaso subar gidan,tanaso su bar kano ma gaba daya idan
zaiyuwu,saidai kuma tana hasaso irin qalubalen da zata iya fuskanta a sanda ta koma
rayuwa cikin wata al'ummar da basusan ainihin wacece ita ba. Wanne kallo zasuyi
mata sanda take zaune cikin gidan da daga ita sai qannenta mata?,wannan ne kadai
abinda yake sake taka mata burki,sai kuma ga sallamar ta ratso har dakinta.

Sallama ta uku taji an sakeyi,dole ta miqe daga kwanciyar ta sauko
da qafafunta qasa ta miqe tana takawa a hankali don amsa sallamar da kuma duba
waye. Don tasan lokaci irin wannan da yawa cikin matan gidan suna bacci.

Har ta sanya hannu zata yaye labulen muryar daada ta dakatar da ita,sai
ta koma a hankali ta zauna a inda ta tashi tana jawo wayarta ta bude.
"Wa'alaikumussalam" Ta amsa tana binsu da kallon rashin sani. Saidai kafin ita ko
su su sake cewa komai bibo ta bankada nata labulen ta fito da buta a hannu.

Itama sakin bakin tayi tana kallonsu,saidai ita tana musu duban farko
ta karanto zallar wadatar da suke ciki da kuma arziqi. Atamfar jikin maamah ta
kalla,saitaga tana mata kama da atamfar da sabreen ta saka rannan har musu ya barke
tsakaninta da hadiyya,inda daga qarshe hadiyyan ta tabbatarwa da bibo kudinta ya
kusan kaiwa dubu sittin da biyar idan ma baifi haka ba.

Wannan abun data tuna ya sanyata saurin ajiye butar hannun nata sannan
ta kawo fara'a da murmushi ta aza saman fuskar tata. Idanma arziqi ne kamata yayi
ace kai ka fara tararsa a dakinka ya fara sauka

"Marabanku sannunku da zuwa lale" Ta fadi cikin haba haba da tsananin kulawa.

Hausawa sukace shimfidar

Please Login or Register in order to submit comment