You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waiwaya kadan don tabbatarwa da
idanunta. Muhammad jadda ne,tsaye daga baki qofar dakin yana riqe da handle
din,daure da lallausan farin towel wanda ke dauke da tambarin VERSACE baro baro a
jiki. Gaba daya towel din ya daurashi ne daga iya qugunsa,ya kuma sauka sosai zuwa
mararsa,abinda ya bata damar ganin full ginannen jikin nan dake cike da lallausar
gargasa data kwanta tayi luf luf.

Fadin kafadunsa ya sanya bata ko iya hangen qofa,sai yau ta sake
fahimtar GIANT ne na gaske,da murjajjen jiki da kuma ginannun tsokokin damtse dana
qirjin wato(muscles).

Wani mahaukacin faduwa gabanta yayi,a yau taga abinda bata gani ba a
wancan ranar data sameshi a parlor dinsa.....ko don yau din a tsaye yake da dukka
tsahonsa da kuma wadataccen haske a dakin nata?.

Duk yadda take da kafiya da taurin rai sai data gaza ci gaba da
kallonsa,wani irin tsoro ya kamata wanda ya tilasta mata maida kanta ta kwantar
saman pillow tana baiwa qofar dakin baya,wato qeyarta ke kallon qofar kenan.

Gabanta ya sake yankewa ya fadi sanda taji ya maida qofar ya rufe
gami da murxa key,ta fidda idanunta dukka biyun waje tanason yin hasahen abinda zai
iya faruwa da ita,saidai bata gama wannan ba taji an sanya hannu an birkitota gaba
daya,sai gata ta koma rigingine a maimakon rub da ciki da take a dazu.

Gaba daya ya zame mata rumfa saman kanta,tamkar me barazanar hanata
ganin komai na dakin sai wannan mudadden jikin nasa.

Da hanzari ta sanya tafukan hannayenta guda biyu da zummar tureshi
saboda yadda yake neman hade space din dake tsakaninsu,amma ko gezau kamar ma ba
wani hannu daya sauka a jikinsa. Bai bata second chance ba ya kama hannuwan nata ya
matse cikin hannunsa guda daya.

Qoqarin qwatar kanta sosai ta farayi tana tureshi,amma baiko motsa
ba,yana riqe da hannuwanta gaba daya yana kuma ci gaba da zube mata idanunsan nan

"Ka sakeni......ka cikamin hannu" Ta fada sanda ta fahimci ko kusa ko alama bata da
qarfin da zata iya amsar kanta a hannunsa. Ta cikin idanunta ya fahimci laushi
tayi,hakanan qarfinta ne ya fara qarewa. Bayajin zai qyaleta haka sai ya bata
mummunar barazanar da ba zata qara kai qararshi wani guri ba. Duk dabaya tunanin
wani tsoro me yawa a tattare da itan duba da ita din WACECE?. Ba wani sabon abu
bane a wajenta cudanya da maza,duk da maza suna suka tara kamar yadda mata suma
suka tara suna.

"Inajin a matse kike a sauke miki jarabar da take damunki ko?,wannan ya sanya ba
kunya cikin idanunki kika je kina kai qara a inda kike tunanin za'a sanyani sexual
affairs dake ko?". Duf wuta ta dauke mata,daga iya kalmar sex data shigo maganar ta
tabbatar lallai babbar magana aka baro. Yaushe takai qararsa?,kuma gurin waye?,me
tace tana da buqata?,duka wadannan tambayoyin sune suka soma mata yawo saman
kai,kuma inda tana da hali tana da buqatar amsarsu,saidai a yadda komai yake a
hautsine bata jin tana da tattararriyar nutsuwar nemansa da wadannan amsoshin.

Tana aje wannan tunanin yana sakin hannun nata,ya miqa hannu da wani
irin zafin nama zuwa Coller din rigarta,wadda tsaurin riqon da yayi mata ya bawa
bottom daya damar tsinkewa fit. Fitarsa sai ya zamana kamar ya hada da fitar
nutsuwa daga gangar jikinta,wani tashin hankali ya rufto mata har kala biyu. Na
farko yadda yayi kusa da ita da towel din da kadan ya rage marabarsa da tsirara,don
babu abunda ya lullube illa mararsa zuwa gwiwarsa,na biyu kuma fitar maballin
rigarta sai ya tuna mata waccan ranar a kitchen. Ranar da har yau idan ta dauki
rigar data sanya a ranar sai taji qamshin wannan mayataccen turaren nasa,abinda ya
sanyata kenan tayi adabo da rigar duk kuwa yadda take sonta. Saboda duk sanda ta
sakata haka yadda abin ya faru zai yita dawowa kanta,hakanan kuma zatayita tuna
yadda ya azabtar mata da lips haushinsa yayita kai komo kenan a ranta har sai ta
raba kanta da ita.

Matse hannunta yayi yana saukar dashi daga gaban rigar don so yake ya
tsinke maballi na biyu,kafin ta iya komai har ya samu nasarar yin hakan,ya kuma
wuce zuwa maballi na gaba,abinda ya sakata saka hannuwanta dukka biyun ta cukuikuye
gaban rigar,cikin fushi kuma taci gaba da magana

"Don't touch me.......ka daina tabani mana.... Wai mene haka?!". Ta qarasa fadi
sanda ya tattara hannuwanta da zummar turesu,cikin rashin sa'a hannuwan nasa suka
samu nasarar sauka daidai saman tudun qirjinta wanda ke tsaye car babu bra. Sabonta
ne idan zata kwanta dukka saita ciresu,don tana jin kamar suna hanata cikakken
bacci.

Daga shi har ita ba wanda baiji kaman an yarfa masa wuta a jikinsa
ba,yayin dashi ya hada wani azababben shock daya ratsa jininsa da wani irin
mahaukacin gudu ya aike saqo qwaqwalwarsa ya kuma dawo da saqon yana rabawa zuwa
sassan jikinsa gaba daya.
Taji komai har cikin jinin jikinta,sai taji kamar an zare mata dukka
wata laka tata da wani irin firgici da tsoro bakinta ya furta

"Please......don Allah ka bari" Kalaman nata na qarshe ya fito da zirarowar hawaye
zuwa saman kuncinta.

Duk yadda yaso ya zarce da tsoratata gami da gigitata cikin mugunta
sai yaji ya kasa,haka ya sake mata rigar yana dauke idanunsa daga kanta ba tare
daya bari sun sauka a inda take boyewar ba tamkar sulalewar ruwan kalkashi a
tafukan hannun mutum. Zuciyarsa ta cika da wani irin mahaukacin mamaki......daga
ina wannan weakness din ya taho?,ya tambayi kansa da kansa can qasar zuciyarsa. Bai
taba niyyatar zai dauki mataki akan wani abu ba tare daya qarasa aiwatar da
qudurinsa ba,bai taba jin rauni akan duk wani abu daya sanya a gaba ba sai akan
wannan dan qaramin aikin.

Tattare jikinta tayi waje daya tana neman hanyar sauka daga saman
gadon,amma sai ya sanya gwiwarsa ya take gefan rigar,ya waiwayo a nutse ya zube
mata idanunsan nan masu dauke da wani kakkaifan maganadisu,wanda duk yadda sukakai
ga haske sun surka launi a yau din.

"Kina zaton zan hada jiki dake ko?,over my dead body......duk randa zan hada jiki
dake ki sanya a ranki ranar mutuwarki ne kawai yazo,don zan niqaki da kyau kaman
yadda engine ke niqa tsaba ya koma gari....." Yatsunsa ya murza saman fuskarta
sannan yace

"Sharadi guda biyu ne zan baki idan kin kiyaye shikenan.....na farko....kada ki
kuskura ki sake kaiwa maamah qarata koda akan meye kuwa....ban hanaki kaiwa anni ba
idan kinga zaki iya fine.....sharadi.na biyu duk randa na sake miki umarnin yin
wani abu kika watsar kina daukan kanki wata tsiya.....zakiga abinda zai biyo
baya,sai na sanya an sako Michael yayi dambu da namanki,ki tashi kizo ki gyaran
sassa.....ki kuma samu note pad ki rubuta day one don lissafinmu yafi tafiya
daidai" Yana kaiwa nan yaja jikinsa yana sauka daga gadon,ya kuma fara takawa
hankali kwance yana fita daga dakin.

Da sassarfa yake haurawa saman cikin tuhumar kansa da kansa. Baisan
kanshi da kasawa ko gazawa ba,ya akayi ya kasa bata mummunan punishment yadda ya
kamata?. Koda ya tsaya gaban mirror na toilet din,sai ya dinga jin haushin kansa da
kansa. Baisan wani weakness nasa ko kadan ba......amma sai ya samu kansa yana
tsoron kada fa wannan ya zama shine weakness dinsa?.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 40


_Daga sumrah dan jundub RA,yace manzon Allah S A W ya kasance yana nemawa mumunai
maza da mata gafara a kowacce juma'a_

_harda ni dake da kikazo a wannan zamanin kin shiga ciki,LALLAI HASARA DA TABEWA TA
TABBATA GA DUK RUHIN DA BAISON ANNABI,ALLAH KA DAUKI RUYUKANMU RUHINMU YANA CIKE DA
MATSANANCIN SONSA S A W_
________________________________



Moroccon cotton jallab ya saka ta maza maroon color me gajeran hannu,wadda aka yiwa
ado da gold din zarurruka masu kauri. Har hantar cikinta sai data kada sanda taji
fitowarsa zuwa falon,amma ta dake bata nuna ba,tana duqe tana goge stand tv lokaci
lokaci tana goge 'yan hawayen daketa qoqarin lallai sai sun sake karya mata zuciya.

Kai tsaye ya wuce saman minotti sofa dinsa yana lumshe idanunsa,wata
azababbiyar kasala nason saukar masa. Dole yana buqatar wani abu da zaiyi awakening
dinsa for some hours don yana da aiki.

"Ke..." Ya kirata idanunsa suna lumshewa kadan. Kiran ya mata ciwo,amma kuma dole
ta nuna tasan da ita yake maganar.

"Bring me some coffee" Ya furta yana dauke idonshi a kanta ya lumshesu don kaucewa
kallonta.

Ajiye duster din hannunta tayi qirjinta na mata wata suya,ta fara
takawa don isa qofar da zata saukar da ita daga saman

"Hey.....ina zaki?" Ya furta da rashin qwarin murya. Sai kuma ya mata nuni da nasa
kitchen din da idanunsa,kai tsaye ta gane me yake nufi,ta kuma canza akalar tafiyar
tata zuwa can din.

Tayita dube dube da tsoron kada ta tabo wani abun duba da yanayin
machine da utensils din dake kitchen din daya sake shan bamban dana qasa nesa ba
kusa ba. Da qyar ta samu ta kammala,duk da bata da guarantee din yayi ko baiyi
ba,don itadai ba damunta yayi ba,koda ya dameta ma ba irin wannan bane.....nasun
irin nasun ne wato daidai matsayinsu yaku bayi.

Saman tea tray ta hado da cups. Ta qasan idanu cikin lumsassun
idanunsa yake kallonta sanda take nufoshi da wani irin kallon da zaka rantse da
Allah bacci yakeyi. Yana qoqarin binciken kansa me yasa yaketa tunawa da abinda ya
faru?,amma ya rasa dalili,haushin kansa sosai yakeji a yanzun,yana ganin kamar
wannan hanyar ta sanya tsoro a zuciyarta bazatayi aiki ba.....zata iya dasa masa
matsalar da zata gagari gangar jikinsa watan watarana.

Yadda jikinta yayi laushi sosai yake karanta,yana mamakin macen data
saba mu'amalantar maza kala daban daban me ya sanyata jikinta yayi laushi don ya
mata wani qaramin riqo da bai taka kara ya karya ba?.

"Kana murzata ne ta hanyar da ba haka su suke mata ba,da ta irin tasu hanyar ce
qila ba abinda zai sanya jikinta laushi" Wani sashe na zuciyarsa ya bashi amsa.

A gabansa ta ajiye tana jin inama zata samu wata dama ta zuba masa
wannan abun cikin tea dinsa?,qila cikin kwanaki uku ta samu nasarar da zata cika
aikinta,ta tattara tabar wannan DUNIYAR tasu ta koma tata ainihin duniyar.

"Serve me" Ya fada da murya can qasa. Sake baci ranta yayi,gaba daya a hankali yana
son canzata ta koma 'yar aikinsa kenan kome?. Tsugunnawa tayi a nutse ta soma zuba
masan tana qoqarin danne zuciyarta amma ta kasa jin relief. A sanda parlor din ya
dauki shuru,wayarsa da tafi kusa da ita ta soma kuka alamun shigowar kira. Kallo
daya ta yiwa wayar ta dauke kanta,yarinyar kullum ce dai wato fareeda khaleed
mustapha. Qaramar tsuka taja,ita ta sani zaa rina,mutum kamar muhammad jadda ace
yana zaune lafiya bisa kyawawan dabi'u?,ai ta qalubalanci wannan. Banda akwai wata
gurbatacciyar alaqa me zai dinga shigo da kiranta cikin wayarsa a kowanne dare?,a
daidai lokaci irin wannan da mafi yawan lokuta yake kebancewa shi kadai?.

Tana miqa masa coffee din yana daukan wayar yana kallon screen din
ransa yana baci,ya dauke dubansa daga kan fuskar wayar da yakeji kamar ya bugata da
bango saboda yadda tsananin nacin fareeda ya soma shallake hankalinsa,ya aje
dubansa akan fuskarta dake a dinke sosai.

"Fara sha kafin ki bani" Yace da ita a taqaice. Duban rashin fahimta tayi masa,sai
ya kafeta da idanu kafin yace

"Do you think am a fool?,kina zaton zan karba nasha any how?....." Ya qarasa
maganar yana daidaita zamanshi sannan ya tura mata teatray din

"Take a sip first" Sai data ja numfashi sosai ta aikawa hunhunta sannan ta samu
zuciyarta taci gaba da aiki yadda ya dace,me yake nufi data fara sha?,ta tambayi
kanta.

"Kada ki barwa kanki qofar zargi" Wata zuciyar ta shawarceta. A nutse ta dauka mug
din ta kurba kadan sannan ta ajiye masa,zata motsa yace

"Hang on for a bit" Ya fadi cikin halin shariya yana maida hankalinsa kuma kan
fareeda tare da tunanin ta inda zai bullo mata.

Ambassador yana da kima da mutunci a idanunsa,musamman daya kasance
babba harda furfura a fuskarshi,saidai fareeda tana crossing line da yawa da baya
bari a crossing masa shi.

"What's bothering you?" Ya fadi adan fusace,yayin data narke marya Kamar qanqanuwar
yarinya

"Kaineee" Labbansa duka ya cusa cikin bakinsa yana qoqarin hadiye takaicin data
bashi. Sai ya sauke idonsa akan sabreen wadda baisan ta soma barin wajen ba sai a
sannan.

"Where to?" Ya jefa mata tambayar data tabbata yanason jin inda zata ne. Ita ba
zata tsaya tana jinsa yana hirarshi da matan banzanshi ba,ba damuwarta bane ya
yanke dukan abinda yake ganin ya dace da rayuwarsa.....amma ita kuma ba wanda zai
tilastata yin abinda batayi niyya ba......wannan din dabi'arta ne da ba canzawa.
Sai data yi qaramin yaqi da zuciyarta sannan ta iya lanqwasa harshenta ta
sarrafashi tana fadin

"Dare yayi inaso na kwanta"

"Idan kin gama you can go" Ya fada cikin halin ko in kula yana katse kiran fareeda
itama gami da sanyata a DND mode sannan yaja coffee dinsa ya soma kurba.

Sassa ne na alfarma dake da yalwa wadatar kayan alatu dana qarau wadanda
ke buqatar a gogesu,wannan shi ya sake bata mata lokaci ya kuma dauketa har kusan
sha biyu na dare abinda ya bata mamaki samunsa sa tayi dungurgur ya sanya system a
gaba ya zuba mata idanunsa yana sarrafata,wanda motsin takunta ya sanyashi rage
mata haske sosai har baka ganin abinda ke allon.

Baki ta tabe ta qarasa,zuciyarta na ayyana nata waye ma yasan abinda
yakeyi tsakiyar darennan.

"You are free" Ya amsa mata ba tare daya waiwayota ba,sai ta fara nufar qofar a ran
ta tana fadin

"Shi mugun mutum ba kasafai bacci dama ya fiya damunsa ba".
Gyaran yayi masa sosai,don yafi qawatar dashi fiye da coffee din,don
sam bai masa dadi ba irin yadda yakeso ya kasance ba. Jallab din jikinsa ya zare ya
wuce toilet da zummar daura alwalar kwanciya bacci.


β˜…Duk a kasalance take kowanne aiki a yau,tun daga safiya zuwa daren da take kammala
girkin daren. Sai takejin wani irin qosawa,gaba daya ta fara gajiya da komai. Tunda
take wannan shine karon farko data aboci kitchen safe da dare da zummar dora sanwar
girki.

Kamar ko yaushe bayan ta kammala abincin,ta taka a hankali tana nufar
inda ta boye akwatin. Ta jawo ta miqa hannu ta fito dashi sannan ta bude. Kayan
cikin ta fara fitowa dasu kaman yadda ta saba,daya bayan daya kuma ta soma zubasu
saman abincin ta cakude dasu. Yau daya sai ta tsaya kawai tana kallon abincin,wani
irin rashin dadi takejin zuciyarta tana mata a yau din,a kasalance ta maida kayan
ta kuma rufe ta maidasu ma'ajiyarsu sannan ta dawo ta soma daukansu zuwa dining don
yau kwata kwata ma bata bari zuwaira ta shigo mata ba. Batason doguwar
magana,hakanan batason sanya idanu da wannan shegen binbinin kallon da take binta
dashi a kowanne daqiqa.

Dab da zata isa dining din saita dinga ji kamar qamshinsa. Batasan ya
akayi ba.....amma tun daga waccan ranar ta haddace wannan nataccen qamshin turaren
nasa da har yanzu yake maqale jikin rigunanta guda biyu. Sosai takejin qamshin,to
amma ta raba idanunta ko ina cikin parlor din bata ga wani alamun shigowarsa ko
shigowar wani ba. Agogo ta sake kalla sanda take ajiye warmer din,mintuna kadan ya
rage ayi sallar magariba.....wannan lokacin kuwa ba lokacin dawowarsa gida bane,don
qarfi da yaji ta haddace lokacin dawowar tasa saboda yadda ta aza dukka damuwarta
akan cikar burinta na yaci abincin.

Watsar da tunanin tayi,taci gaba da shirya komai ta kammala,ta tsaya
kawai tana kallon yadda komai yake jere saman dining din.

"Inama ace yau daya burina ya samu ya cika?" Ta furta qasan ranta duk da tana jin
wani sashe na zuciyarta kaman yana qyamatar hakan ya faru,sai kuma ta juya tana
nufar hallway din da zai sadata da dakin. Dab da zata shige laila ta murda pivot
door din tana shigowa falon tayi kwalliya sosai cikin wani silk material da aka
tsarawa dinkin daya dace da shape din jikinta sosai. Red ne colour dinsa wannan ya
sanya farar fatarta data samu gyara da pills na qara fari da allurai na qara hips
da sauransu ya sake qawata shigar tata. Kome takeyi tana da cikakken goyon bayan
hajja wadda a kullum burinta ta fita daban,ta kuma zama daban din ta kowacce hanya
cikin mata.

Idanu suka hada,sai sabreen din ta dauke idonta kamar kullum,ta kuma
taka a nutsenta tana wuceta,tana jin bata da wani lokaci nata sam sam.

Da idanu ta raka sabreen da wani irin kallo na qurilla,allurar kishi
tana tsikararta,tana tambayar kanta da wanne irin products haka take amfani masu
tsananin qarfi?. Tana ji ana cewa kowanne dan adam tara yake bai cika goma
ba.....to amma ita sai take ganin tamkar a halittar sabreen goma take cif cif!.

Tsaki taja tana maida dubanta kan dining din. A yunwace ta shigo,ta
samu zuwaira kuma bata nan,tabbacin a yau kenan saita shigo da kanta neman abinda
zataci.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 41


_Daga nana aisha RA tace,manzan Allah S A W yace: "anayin wanka akan abubuwa guda
biyar,janaba....da wankan juma'a...da idan anyi qaho,da wankan mamaci(mutum ya yiwa
gawa wanka)_
__________________________



Matsawa taci gaba dayi zuwa wajen dining din,tana cike da haushin yadda a
kullum ake jigilar qawata wajen da warmers na alfarma wadanda suke bata tabbacin
abinci ne lafiyayye.....to amma kullum idan ta tuna maganar da hajja ta gaya mata
akan abincin sai ta maida qwalamarta bisa tilas. Asali ita din mutum ce da ba
kasafai ta fiya bawa irin wadannan abubuwan muhimmanci ba. Hasalima tana ganin idan
ba dominka aka shirya abu ba bazai taba tasiri a kanka ba.

A nutse ta isa wajen,ta kuma jawo warmer din farko ta soma
budeta,budewar da ya qara adadin yunwar da takeji taji kuma bata da wata hanya illa
ta toshe yunwar dake sakadar mata hanji kamar bata taba cin komai ba.

Yau gajiya takeji sosai a jikinta,wannan ya sanya data idar da sallah
isha'i wanda duka zama tayi a wajen bayan magariba sai data yi isha din sannan ta
tashi. Wannan Dabi'arta ce qwaya daya da har yanzu bata rabu da gangar jikinta
ba,burbushin raino da tarbiyyar ummensu,bata wasa da sallah sam koda bayan gushewar
ummen,kuma ita kanta ta hori 'yan uwanta sosai akai
(Ko hori yaranku da sallah.....tana da matuqar tasiri wajen hana bawa sabon Allah
da kuma gyara halinsa,kamar yadda Allah ya fada cikin qur'aninsa me girma,tabbas
sallah tana hana alfasha da munkari,Allah ya bamu dacewa ameen summa ameen). Tana
shirin shiga wankan saita samu kanta da maimaita addu'o'in data karanta a littafin
da anni ta bata wanda shi ya qara sanyata jin dadin zaman. Tana nanata addu'o'in
suna tuna mata da zamanin da suke qananu......lokacin da ummee ke korasu makarantar
allo ranakun weekend,ita hadiyya da sameeha. Qaramin murmushi ya kubce mata,tadan
girgiza kai tana jin kewar lokacin quruciyar tata,tana jin inama tana da ikon dawo
da wancan lokacin,ashe ba abinda yakai zamanin quruciya dadi.

Pyjamas ta saka baqaqe gaba daya da suka sake haska mata fatarta,sai
ta dora qaramin farin Malaysian hijab saman kanta bayan ta nannade gashinta a
tsakiyar kanta cikin ponytail holder,hakan ya sanya kan yadan tashi kadan kamar
tayi acuci maza na.

Fararen flip flops ta zurawa fara tas din qafarta,wadda duk wani lalle
ya fita a jiki,sai tsantsar haske daga qara da gogewa kamar jini zaiyi tsartuwa.

Hankalinsa na rarrabe akan wayarsa sanda yake qarasowa cikin falon.
Daidai lokacin da laila ke saukowa daga dining din sai ya zamana mutum na farko da
idanunta suka fada a kai. Cak ta tsaya ana zare duk wani noti na jikinta,wannan
shine karon farko data taba gaba da gaba da muhammad jadda,kusan duka a baki ko
cikin magazines da news paper take ganinsa.

Duk yadda tasha fasaltashi a zahirinsa ya wuce nan,wani irin ingarman
namiji da a iya tafiyarsa kadai ta hangi izzarsa da kuma cikar isarsa.
Kaman a jikinsa yaji ana kallonsa,wannan dalilin ya sanya daga
idanunsa yana duban sashen da yaji jikinsa yafi rinjaye. Suna hada idanu gaba daya
kwarjininsa ya mata wani irin mamaya data gaza riqe kanta,duk wata zarra da jin kai
da takeji tana dashi a matsayinta na diya mace ya sulale yayi nasa waje. Yadda ya
kafeta da idanunsan nan masu qunshe da wani sirri sai taji komai yana kwance mata

"Barka da dare" Tayi namijin qoqarin furtawa bakinta yana son hardewa

"Yauwa" Kawai ya amsa mata dashi.

"Nice laila....'yar gidan hajja.....hajja harira ta maamah" Tayi bayanin a nata
zaton hakan zai burgeshi ko kuma ya sake bata matsayi na musamman a matsayinta na
'yar aminiyar mahaifiyarsa.

Fuska yadan yamutsa kadan yana fahimtar inda ta dosa.

"Yayi kyau.....ban fadi muku banson kowa around us ba idan ina gida?" Yayi maganar
fuskarsa na wadace da wani irin daurewa kamar baisan sunan wani abu waishi dariya
ba,don dama da bacin rai ya sauko.

Kasaqe tayi tana mamaki,tabbas zuwaira ta shaida mata,amma ko a sannan
kallon banza ta watsa mata ta wuce dakinta,don tana ganin ita ta wuce wannan dokar
tayi aiki a kanta. Tana jin kanta tamkar ita din halastacciyar 'yar gidan ce,don
haka bata ma wani tsaya amfani da dokar ba bare ta kiyayeta. Tana shigowa a duk
sanda taso tayi abinda takeso ta fita,saidai da yake dukkaninsu ba ma'abocin zaman
falon bane kowa sabgar gabansa yake shi yasa ba wanda ta taba karo dashi a cikinsu.

"Get out of my sight......and kada ki sake bari mu hadu" Ya fada cike da zallar
umarni ba tare kuma daya kalli sashen da take ba yaci gaba da tafiya kansa tsaye
zuwa dining din.

Ajiye wayoyinsa yayi bayan ya gama abinda yake,ya maida hankalinsa ga
abincin yana dubansa. Yau zai kawo qarshen duka wannan drama din ya ayyana hakan a
ransa,daidai sanda take fitowa daga parlor din zuwa ainihin falon da yake ciki.

Kai tsaye dama idanunta kan dining din suka fada,don ya zame mata wani
aiki na daban kiyaye waye a wajen da kuma duba waiko ya zauna cin abincin?. Bataso
yadda tashin farko suka hada idanu ba don zaya dauka ne kawai kallonshi takeyi,take
tata izzar itama ta motsa,ta dauke kai sosai tana takawa zuwa qofar kitchen.

"Hey.....com here" Ya fada da matsakaiciyar murya. Tanason gwada masa tsiwar amma
tana tsoron abinda zai biyo baya,dole ta dawo din fuskarta shimfide da kalar nata
miskilancin.

"Serve me" Ya fada cikin basarwa yana bude wayarsa. Cak ta tsaya,tana jin kamar
kunnuwanta ne suke jiye mata ba daidai ba. Ta zuba masa abincin fa ya buqata?,ta
tambayi kanta tana neman qarin haske.

"Zuba abincin nace" Ya sake maimaita mata ba tare daya dubeta ba. Wani irin abu
taji ya tsargawa sassan jikinta. Ta

Please Login or Register in order to submit comment