You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ba fahimta take cancan ba,saita yanke kiran fannah kawai suyi hira.

A qalla sun kusa awa daya da fannah din,har sai da taji farouq ya iso
kusa sosai,tana jinsa yana saka fannah din dariyar da bata shirya ba,dole ta yanke
kiran. A gogo ta kalla,taji kewar nata mijin yana saukar mata,banda wannan matsalar
data faru a tsakaninsu da tuni zuwa yanzun shima yana tare da ita,ta sauke idanunta
tare da ajiyar zuciya zuwa saman Tv din,daidai sannan ya murxa handle din qofar
parlor din ya shigo da sallama muryarsa can qasa,yanajin kowacce gaba ta jikinsa a
mugun jigace.

Idanunsa da sukayi laushi qwarai su ya fara zube mata,tayi masa wani
irin fitinannen kyau,ya sauke dubansa kan gashinta da yasa kwalliya da wani irin
salo,salon da hatta yanayin zamanta saman kujera yau din na musamman ne.....

Cikin wani irin hanzari ya dauke kanshi daga dubanta sanda ta daga
risunannun idanunta zuwa kanshi. Yadda ya dauke kan baima ko nuna ya ganta ba ya
mata wani irin ciwo,duk da haka ta daure tace masa.

"Sannu da zuwa".

"Yauwa " Ya amsa still ba tare daya kalli sashenta yana takawa zuwa hallway din.

Idanunsa ya lumshe,yana jin wani abu yana harbawa zuwa kowanne sashe na
jikinsa. Ta masa kyau iyaka,ta fusgi hankalinsa qwarai,saidai har yanzu yana jin
tasirin fushinnan da yakeyi da ita. Ta dauka masa yara sun fita daga gidan daya
killacesu ba tare da yasan adadin nisan da zatayi ba,ta dauka masa yara ba wasu
cikakkun masu tsaronsu......uwa uba ta taba masa martabar igiyar aurensa......tayi
nisan da bai kamata ace ta yishi ba tare da muharraminta ba.....ba kuma tare da
izininshi ba.

Idan har ya sake mata haka da yawa gaba yana da guarantee din me zaya
faru?. Iyali suke tarawa shida ita,fata yake kuma su gina iyalin da kowa zasu zame
masa abun alfahari. Babban abun dake mintsinar zuciyarsa shine......tsoronsa daya
karanta cikin idanunta tun wancan ranar,to meye yake mata a shimfidarsu da zai
sanyata gudunsa har irin haka?.

Ya sani......duk duniya ita zata fadi wayeshi a wannan
fannin.......tafi kowa alfahari dashi........wani irin yanayine da take ji dashi
cikin rayuwar aurensu,amma dare daya saita nema sauya hali?.

Alqawari ne ya yiwa kansa tun first night nasu......bazai sake
kasancewa da ita ba ta wani yanayi na daban har sai da shauqinta da cikakkiyar
amincewarta,koda kuwa son kusancinsa da ita zai masa mene ne.......bare a yanzun da
yake cikin fushi da ita.......banda wannan kallon daya mata na yanzu da yake shirin
wargaza masa lissafin da baiyi niyyar wareshi a nan kusa ba.

Dakinta ya wuce kai tsaye,kaman yadda ya saba shiga ya gansu suna bacci
batasan ma shigar tasa ba bare fitowarsa. Ya qarasa gaban gadon,ya riqe yatsun
yaran idanunsa a kansu. Wani sanyi yaji zuciyarsa tana yi.......da gaske da ake
cewa yara sanyin idaniyar iyayensu ne.

Yana iya jinta sanda ta tura qofar dakin ta shigo yana tsaka da musu
addu'a,bai waiwayo ba,bai kuma tsaya da abinda yake ba har ya gama tofesu da
addu'ar sannan ya juya a hankali da zummar fita a dakin.

Dab da zai isa bakin qofar tasha gabansa,ta shiga ta tsakanin
hannayensa ta tsaya a tsakiyarsa tana lalubar qwayar idanunsa ta saka nata a ciki.

Narkakkun idanun nan nata da suke kasheshi......narkakkaun idanun nan
nata da suke zare masa dukka wata laka tasa,su kuma kashe wutar fushi dake ruruwa a
zuciyarsa,idanun da har yau wani haske da qyalli suke kasa kaman ranar farko daya
fara ganinsu.

"Zan wuce a gajiye nake.....bacci nakeji". Ya fada da wata maqalalliyar murya daga
can qasan maqoshinsa,muryar da takeso lallai saita tona asirin dake danqare a
zuciyarsa da gangar jikinsa.

Qwalla sosai ta cika fararen idanunta,ta koma masa kaman wata yar shekara
goma saboda yadda ta maqale.kafada.

"Zakaje ka kwanta kayi bacci ko?,sabreen ita kuma ta mutu?". Sai kawai ta fashe
masa da kuka.

Cije labbansa yayi,yana jin yadda kukanta ke huda masa sassan jiki
yanason kassarashi da kassara qarfin qwanjinsa dana zuciyarsa. Ya dake sasai yana
fadin.

"Nifa ba kuka na tambaya ba,hanya nakeso a bani......zancan sabreen ta mutu kuma ai
bai taso ba.....ki bani hanya please" Ya fada a dake yana basarwa,yana fata ta
matsa ta bashi hanyar kafin ya qarasa karyewa daga hawayen dake fita a fuskarta.

_Wato dai da gaske kai ragon namiji ne indai akan sabreen ne?,zamu gani,zaka iya
daurewa?😂😂_167



"Hamma" Ta sake kiransa muryarta a karye da sautin kuka.

"Am really sorry hamma......Allah bazan sake ba" Tun daga tsakiyar kansa har tafin
qafarsa yaji kiran sunanshi da tayi,zuciyarsa tayi sanyi amma tana gaya masa ba
yanzun ba......da sauran karatun.

"Naji na haqura.....matsa na wuce" Ya sake fadi yana kuma tsare gida. Fararen
idanunta da suka dan surka kadan saboda kuka ta daga ta kalleshi,shima idanunsa
suna kanta,amma koda ta kalleshin sai ya dauke kansa,saboda tsigar jikinsa ya da
yaji gaba daya ta tashi.

"Hamma baka haqura ba....."

"Goyaki kikeso nayi?,shi zai tabbatar miki na haqura ko kuwa yaya?". Yadda yayi
maganar da wani basarwa sai ya karya mata gwiwa,gaba daya sai taji kaman ya
tozartata da yadda yake qoqarin tankwabe rarrashin da take masa.

"Bani hanya please" Ya sake fada yana kuma hade gira.

A hankali ta janye jikinta ta bashi waje,ya taka hankali kwance kaman
wani abu be tsikareshi ba ya fice a dakin.

Sulalewa tayi a wajen,sai wani sabon kukan ya tsinke mata. Tsoro
taji yana shigarta,tsoron kada ya zamana fu'ad ya fara juyawa daga muhammad din
data sani......zuwan mazajen yau da mata ke complain a kansu. Idan haka ta kasance
a kanta bata jin zatakai labari.....don ta ta'allaqa dukka burinta da fatanta a
kansa,ta karkatar da akalar rayuwarta a kansa,ta saka buri me yawa kuma akan nasa.

Tas taci kukanta ta godewa Allah,sannan ta miqe tana qarfafawa kanta
gwiwa. Ta shirya abincin duka cikin wani kwando na daban ta haura masa sama dashi.
Ba kowa a parlor din,tafi sanya ran wanka ya shiga,don haka ta jera komai tsaf
saman dining ta wuce bedroom dinsa.

Kai tsaye ta murza handle na toilet din ta shige abinta gaba gadi.
Cikin Jacuzzi ta hangoshi,ya sakarwa kansa ruwa wanda yake wanka duk kumfar daya
sabawa jikinsa. Idanunta ta Maida ga bathtub din data cika masa d ruwa da kuma
sassanyan turaren wanka,ba alamar ya taba ruwan ma bare akai maganar yayi wanka
dashi,saita hadiye abinda ya taso mata ta nufi jazucci din kai tsaye.

Zuge qofar tayi,ta taka a nutse tana shigewa ciki. Ya ganta sarai
amma bai waiwaya ba,yaso ace sanda bai shiga azumin fushi da ita ba ta kawo kanta a
irin wannan lokacin,lallai da ya samu ganima.

Yana jinta ta gama tsokane tsokanenta bai nuna yasan tana ciki ba,ya
gama ya nannade jikinsa da towel ya fito. Tana tsaye a nan kamar wata hoto har
yabar toilet din,ranta taji ya soma baci,to amma ya zatayi?,duk ita ta jawo,ta
tabbatar fushinsa lallai ba abu bane me dadi,tunda ya gwada mata ta gani.

Ko data zuba masa abinci ma cewa yayi ya qoshi baya buqata,ta san
halinsa koda yana buqatar abincin ma ba lallai yaci,zaice bazaici abinci bane
late,don haka ta shiga kitchen ta hada masa fruit salad me kyau da nau'un fruit din
da basu da matsala ga lafiya da dare,a cisu kuma a kwanta.

"Ajiye a nan xanci" Ya fada kawai yana duba wasu file. Ajiye masan tayi,ta kuma
sauka qasa tayi shirin bacci.
Still cikin wasu red night gown ta shirya,ta saki gashinta kafadunta
yanzun bayan ta tajeshi daga curling nashi da tayi a dazu.

Sanda take kawo yaran zuwa gadonsa dake gefan dakin,yana kwance cikin
duvet a qudundune amma tun shigowar farko sassanyan qamshinta ya ruskeshi har inda
yake din.

Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke yana runtse idonsa,bai taba
kawowa zai iya jure wadannan kwanakin ba.......bai taba zaton yana da haquri a
kanta har haka ba sai yanxu.

A nutse ta gama komai,ta sake musu addu'a,ta shiga toilet nashi tayi
brush sannan ta hauro gadon tana rage hasken qwayayen dakin.

Ya jita kusa dashi sosai,amma bai taba kawo zatayi abinda tayin ba a
yanzun. Wata kyakkyawar runguma tayi masa ta baya,cikakken dukiyar fulaninta da
shayarwa tasa y qara cika ya tokare a bayansa.

Saura kadan numfashinsa yayi qaura daga gangar jikinsa,wasu irin
kaifafan kibiyoyi ta sakar masa wanda suka ratsa sassan jikinsa d wani irin matuqar
sauri suka aike masa da wani nannauyan yanayi daya sakashi takure jikinsa ba tare
daya shirya hakan ba.

Matseshi tsam tayi ta baya,tana bashi wata kyakkyawar runguma. Har
cikin jininsa sai da yaji yadda dumin jikinta da tudun dukiyar fulaninta ya zauna
sosai saman fatar bayansa.

Sosai ya riqe numfashinsa don hana kansa jin abinda yakeji yana masa
yawo a jiki,amma yadda zuciyarsa ke bugawa da sauti ya sanya ta kasa aiwatar da
hakan,ya kamo numfashin da qyar sannan ya tattaro juriyarsa yana dan zamewa.

"Stay away please" Ya fada da wata irin kasalalliyar murya.

Maganan tashi tazo mata a bazata,tsam tayi da ranta tana dakatawa da
komai,tana jjn yadda zuciyarta ke bugawa da sauri,tana kuma jin yadda itama a yau
din take jin ta dokanta dashi.

"Hamma" Ta furta a sanyaye. Qarasa janye jikinsa yayi,sannan ya miqe ya zauna sosai
saman gadon yana dubanta

"I'm not in the mode,im feeling off" Ya furta muryarsa tana qara yin can qasan
maqoshinsa. Idanunta da suka fara lumsheea ta ware tana kallonsa. Yau ita jadda
yake cewa he's off?,off for what?.

Tana tsaka da wannan tunanin ta ganshi ya dauki babban blanket nasu da
pillow ya aza saman sofa ya kwanta abinsa ya lulluba har saman kansa.

Baki ta sake kawai tana kallonsa,abun gaba daya ya bata mamaki,yau ita
abben su fauzan din ke yakicewa?,ita din yake dodging?. Wani matsewa zuciyarta dake
qirjinta tayi,sannan a hankali wani hawaye me dumi taji kawai ya sauko mata saman
fuskarta.

Da hanzari ta sauko daga saman gadon kai tsaye,ko bedroom slippers
dinta batayi ta kai ba ta soma fita a dakin da sassarfa.

Komai da takeyi yana jinta,bai kuma motsa ba har sai da yaji
fitarta,kunne ya kasa sosai,kusan mintuna biyar sannan ya yaye duvet din ya sauka a
hankali yana fita a dakin.
Bata duka bedrooms din hakanan bata parlor din,abinda ya bashi tabbacin
sauka tayi gaba daya daga sassan nasa.

Wani qaramin murmushi ya saki,qasan ranshi yana fadin ashe babu dadi.
Maida qofar parlor din yayi ya kulle abinsa ya koma bedroom din duk da yadda
zuciyarsa ke jin matsananciyar kewarta.

Yaran gaba daya ya sauke daga nasu gadon,ya maidosu kan gadon nashi,ya
bajesu ya shige cikinsu abinsa ya kwanta sosai yana sakin ajiyar zuciya,yana kuma
jin kusancin dake tsakaninsa da yaran.

Kwata kwata bacci qaurace mata yayi,batajin zata iya jurar wannan
abun. Yayi mata komai zata jure amma banda nesanta kanshi da ita,ita kanta cikin
tsananin buqatarsa take,don ya riga ya horata ta wannan fannin ya kuma maidata
irinsa. Abu daya ne ya sanyata ta guje masa stitches nata na CS dinta da take ganin
kamar zai farke.

A haka bacci barawo ya lallabo ya saceta,cike da fata da sanya ran
zai shigo har dakin ya nemeta,ko don saboda yaran ma. Sam baccin baiyi wani tsaho
ba ta farka firgigit,ta shiga buda idanunta sosai tana sanya ran ganinsa ko yaran
ko alamun ya shigo ya fita,amma bataga komai a ciki ba.

Ranta taji ya bacu,zuciyarta ta quntata,sai ta shiga toilet tayi
fitsari ta daura alwala,ta dawo tayi nafila raka'a shida. Tana saman abun sallan
tana addu'o'inta wani baccin ya sake waftarta,wanda shine bacci mafi tsaho da
tayi,don bata tashi farkawa ba sai da akayi kiran farko.

Yanzunma bataga alamun ya shigo ba,kawai sai wata qwalla ta cika mata
idanunta. Dama yake da ciwo kayi abandoning mutum?. Yaran sun tsaye mata a
rai,tasan zai wahala ace duka tsahon daren ba wanda ya nemi nono,kawai saita sauka
daga kan abun sallar ta soma takawa a hankali ta fice a dakin.

A Hankali ta bude qofar bedroom din,mamaki da haushi ya cikata fam
kaman zata fashe. Wato shi ya sanya yaranshi a gaba abinsa suna sheqa baccinsu ko a
jikinsu?,ita gata nan wahalalliya ta hana kanta da kanta sukuni duka saboda yaran
da nasa tunanin,kawai saita saki kuka me sauti,kukan daya tasheshi ya kuma saka
yaran motsawa,daya bayan daya suka farkawa tarwai abinsu,sai kuma a sannan suka
fara neman abincinsu ta hanyar fara cilla qafafu suna son fara sakin kuka.

"Alhamdulillahil lazi ahyana ba'ada ma amatana wa ilaihinnushur" Ya fada sannan ya
miqe ya zauna sosai saman gadon yana dubanta inda ta zauna gaban gadon tana musu
kuka.

"Me akayi miki?" Ya tambayeta hankali kwance,tambayar data sakata sake masa hararar
da batasan tayi ba,sai ya dauke kansa kawai yana sauka daga gadon a hankali ya wuce
toilet don daura alwala yayi raka'atanil fajr kada ta subuce masa. Rigima ce fal
idanunta yake hanga,shi kuma indai wannan rigimar ce a shirye yake da ita,ya fita
jinta ma.

Ko kafin ya gama alwala ya fito dakin duka ya karade da kukansu su
ukun,ga mamar tasu zaune a gabansu itama tana hawaye sosai.

Tausayi da dariya abun ya bashi duka lokaci daya,ya dake yana zura
jallabiyyar jikinsa da sauri bayan ya tsane ruwan gargasarsa.

"Baki gani kuka suke kika zauna kika sakasu a gaba kina kallonsu?". Kaman jira take
yayi maganar ta miqe tana nufar qofar,kuka takeyi sosai,sai ya qarasa yasha gabanta
yana duban idanunta.
"Hamma raino kawai na iya dama?".

"Ni me nace miki ne Sabreen?,me kikeso kuma ehmmm?" Yayi maganar da alama shima
ranshi ya fara baci. Ta kalleshi sosai ta kuma fahimci kukan yaranshi ke dagula
lissafinsa,kenan yafi jin kukansu a ransa sama da nata?,wannan ya sanya ta soma
neman hanyan fita kawai.

Hannu daya ya sanya ya jawota baya kafin ya saka hannuwansa duka biyun
ya dauketa cak yana lullubeta a qirjinsa yana jin yadda sassanyan qamshinta ke
bulale masa hanci,bai kuma direta ko ina ba sai tsakiyar gadon. Haurawa saman gadon
yayi ya dauko farouq da nasa kukan yafi na kowa ya aza mata saman cinya,ya kuma
tsare ta da idanun nasa. Zuwa yanzu qwayar idanun nan sun kuma na muhammadun
sosai,me babban suna kuma shugaban kamfanonin jadda.168




"Feed him" Ya bata umarni nakai tsaye da husky voice dinsa. Duk wani
annurin fuskarsa yana daukewa,kukan yaran yana jinsa kamar d'igar ruwan dalma saman
tsokar zuciyarsa.

Umarnin ya zarce har cikin kwanyarta,saita soma nuqu nuqun fidda
maman. Gani yake bata masa lokaci takeyi shida yaran gaba daya,don haka ya buda
hannayenta kawai ya balle duka button din rigar tata ya zameta daga kafadunta.

Cikakkun dukiyar fulaninta da suke a tsaye,sun cika sosai irin na masu
shayarwa ya bayyana,abinda yayi nasarar karya alwalar da yaketa faman tattalawa
kenan.

Hannunsa ya miqa cikin dakiya ya dagoma fauzan abincinsa,nan da nan
ya kama,sannan ya saki ya koma wajen su fawwaz da kukan nasu ya sassauta.

Bai nuna yaga hawayen da take zubarwa ba sam,yaci gaba da bata yaran
suna sha,har sai kowannensu ya qoshi sannan ya janyeshi. Suna sha yana karbarsu
daya bayan daya yana sauka dasu. Batasan inda yake kaisu ba,amma haka yake dawowa
hannunsa babu su.v

Almustapha ne qarshe,don kusan ya fisu haquri,sai daya tabbatar
shima ya kama sannan ya tashi yayi raka'atanil fajr din. Sanda ya idar ya gama sha
shima,ya miqa mata hannuwansa yana kallon fuskarta da tayi ja saboda kukan da tayi.
Miqa masa shi tayi shima,sai ya karbeshi ya kuma ajiyeshi a gefe. Hannunsa yasa
yana maida mata rigarta yadda take duk da qoqarin maidawa da takeyi da kanta.

"Ka barmin abata zan mayar" Ta fadi cikin rawar murya. Wani kallo ya jefeta dashi.

"Ina ruwanki?,wannan din ba jikinki bane.....jikin muhammad jadda ne.....naki jikin
gashinan" Ya fadi yana nuna kansa da kansa da yatsa.

Wani abu me sanyi taji ya sauka a zuciyarta,har sai data lumshe idonta
kadan,ya kammala maida mata ita tsaf,ya saka hannu ya dauki almustapha fawad yana
tafiya qofa.

"Kiyi alwala kiyi sallah.....zanje sallah na dawo" Ya qarasa maganar yana qarasa
fita. Tsaiwa yayi yayi locking qofar da new password ta yadda ba zata iya fita
ba,sannan ya gangara ya miqawa salwa fawad yace a gyarashi shima kaman sauran 'yan
uwansa sannan ya wuce masallacin.

A sanyaye tayi alwalar tayi sallar,tayi addu'o'inta kaman yadda ta
saba. Idanunta sun mata nauyi sosai,kuma da alama rashin bacci ne isashe na
kwanakin,don haka sai kawai ta koma toilet ta hada ruwa me dumi sosai tayi wanka,ta
kuma nade kanta da jikinta da towels dinsa wadanda qamshin jikinsa ya kamasu sosai.
Idanu kawai take lumshewa,wanxuwar towel din me manne da qamshinsa sai ya xame mata
kamar shine nannade a jikinta. Wani irin azababben shauqinsa takeji ta kowacce
fuska,tana jin kaman takai kanta gareshi ta roqeshi.

"Wanne irin abune wannan?" Ta tambayi kanta da kanta sanda tayi zaune saman stool a
gaban madubi. Hirarta da fannah ta dawo mata fes a kanta.

"Wata macen sai ta fara haihuwa take zama cikakkiyar mace me cikakkiyar buqatar
namiji..sai a sannan komai nata yake qosawa yake kuma bunqasa" Dauke hawayenta tayi
da yatsanta,tana raya cewa wataqila ita din tana cikin irin wadannan matanne.

"Kamar ke kadai keda idanun kuka?,bakisan ni ya kamata na zauna nayita sheqa kuka
ba?" Taji maganar sa daga gefanta wanda harga Allah batasan da shigowarsa ba.

"Taso kizo nan" Ya bata umarni kansa tsaye yana nuna mata daura dashi.

Da kallo yake binta sanda take takowa inda yake. Duk da yake shi ba
ma'abocin kallon mata bane amma yayi imanin samun takun isa a wajen diya mace irin
na sabreen dinsa zaiyi wahala,kaman yadda qirar jikinta tasha banban data dubban
mata,don ko a yanzun da take tafiyar saika rantse ba wani yaro daya zauna a cikin
ta tsahon wata tara,sai cika da komai nata ya sakeyi. Duk da yanayin halitta ma ya
lura macace me gyara sosai(idan kina da kyau ki qara da wanka,karki yadda ki zauna
a wargaje waike jego kike ko kin tara yara sun miki yawa,xaki banu zaki lalace fes
wallahi).

"Sabrrrr.......don ni bani da gata?,don ni bani da wanda zan gayawa
damuwata......don ni namiji ne bani da idon kuka?" Yafada da wata raunanniyar
muryar data tilasta mata daga idanu ta dubeshi. Wani irin tausayinsa daya tsarga
mata ya sanya hawaye taruwa a idanunta. Miqewa yayi,da alama baiso maganar ma tayi
tsayi can.

"Alqawari nayi,tun a wancan daren bazan taba koda yatsarki ba muddin zamanmu sai
kina cikin yanayin".

" Ina ciki wallahi" Ta furta da wani irin sauri bayan ta yiwa kanta kyakkyawar
masauki a qirjinsa tana cukuikuyeshi. Dariya ta kusa kubce masa duk da yadda sanyin
hawayenta daya sauka budadden qirjinsa da wuyan rigan ya zama V shape ya taba
zuciyasa sosai.

"I can't live without you.....You're my everything,without you,I'm lost,i need you
now and forever,you're irreplaceable hamma........ka yafemin hamma.....bazan sake
ba hamma......na tuba" Ta qarasa fadi tana sakin masa wani kukan kisisina me
tsayawa a zuciya.

Hannunsa har rawa yake sanda ya riqeta,ya sake mata wani tsatstsauran
riqo yana sanyata tsakiyar qirjinsa yayi mata kyakkyawar runguma. Kasa magana
yayi,kasa cewa komai yayi,kaman yadda shirunsa ya isheta amsa ta hanyar bugun da
zuciyarsa takeyi.

Ta yarda ta kuma amince tabbas taso ta zalunceshi,jikinta ya sake sanyi
da kalar soyayyar da yakeyi mata.

"Dukka wannan bugawar da Xuciyar nan takeyi tana yine saboda ke.....ke kadai
sabreen,ban taba koda sha'awar daga kai na kalli wata macen ba bare har naji ta
fusgi hankalina na ko ta dace da rayuwata ba bayanke".
"Nayi maka alqawarin xame maka aljannar duniya koda shine xai kawo qarshen bugun
zuciya dana numfashina" Lafaxinta na qarshe kenan daya iya tantancewa,ya dauketa
cak ya ajiyeta inda yafi wayo sannan ya fara rabata da towel din jikinta.

Wata irin sassanyan safiya ta bashi.....wata irin safiya me tsayawa a
Xuciyar masoya.....

"Can i have you for breakfast today?" Ya fada da wata narkakkiyar murya dake wani
irin rawa.

Yana dire tambayar ta tabbatar masa da abinda yake buri,abinda yake
fata yake kuma tsananin buqata. Shi da ita kowannensu da zafinsa yazo,shi da itan
gaba daya ba wanda bai gigita dan uwansa ba da wani irin zazzafan salo daya sake
tabbatar masa itace DUNIYARSA shima shine DUNIYARTA. Gaba daya ta canza masa,ta
kuma caza masa kwanya,yana jin tamkar yaune ranar farko a rayuwarsa daya fara
kasancewa da ita. Ta gigita duk wani tunani nasa......ya sake fahimtar cewa lallai
macen datasan kanta haihuwa ko shekaru basa saka kimarta zagwanyewa,a yanzunne ya
sake gamsuwa da lallai sabreen dinshi ta zama cikakkiyar mace.

Tana kwance luf saman qirjinsa sanda komai ya kammala,kalar
alqawuran da yake zayyano mata ya sanyata sakin wani sassanyan kuka,nan ya sake
lalacewa wajen lallashin kayarshi.

Sanda taga lokaci bayan ta kalli agogo batasan sanda ta wantsalo
daga gado ba ta nufi bandaki tana fadin

"Su fawad" Miqewa yayi ya bita toilet din da towels dinsu.

"Ina da nufina dana daukarwa su fawad nannies,kwanan nan kuma zan qara guda daya
kowacce taji da guda daya,lokaci na lokaci na ne.....banaso nayi sharing nasa da
kowa" Yaso ya bata dariya,saboda yadda yayi maganar da gaske.

"Ayi musu afuwa naje na dubasu,don zuwa yanzun ya kamata ace an dubasun" Bai amsa
mata ba ya turata cikin bathtub din kawai yana sake maqale mata.

Tsaf ta shirya cikin atamfa riga da zani,shigar data jima bata yita
ba. Shi kansa yau din saita masa kyau sosai,ta maqala wasu sabbin design na
earrings na gold marasa nauyi a kunnenta da

Please Login or Register in order to submit comment