You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba.

"Kin shirya?" Ya tambayeta da wani irin sauti,kasa ce masa komai tayi sai ya dora
audugar saman yatsan nata.

"Wash" Ta fada tana qoqarin janye yatsanta gami da runtse idonta.

Hanata daman hakan yayi,sai ya zubawa fuskarta idanu yana ganin yau
d'aya wannan tsiwar ta tafi sai alamun rauni da radadi.

"Am sorry" Ya fada can qasan maqoshinsa da wani kalan sauti daban ba irin na dazu
ba,abun daya tilasta mata bude idonta ta zubesu cikin nasa. Abinda yakeso dama
kenan,sosai yayi qoqarin riqe qwayar idanunta cikin nasa,ya matso da yatsar saitin
bakinsa yana busa mata a hankali,abinda ya hadu da sanyin spirit din dana bakinsa
ya bada wani abu daya sanya tsigar jikinta zubawa,tanaso ta janye hannun ya
hanata,hakanan dole tabar masa hannun tana jin yadda jikinta duka ya mutu.

"Ya daina zafin?" Ya tambayana yana dorawa kansa alhakin yankewartata. Kai ta gyada
masa a hankali,burinta kawai ya gama yabar mata hannunta ya matsa daga kusa da ita
din.

Tsaf ya gyara,saida jinin ya tsaya da fita sannan ya kammale
komai,ya qwalawa amna kira ta qaraso.

"Ki dauke kayan.....ki kula da ita zanje na dawo,zamu taho tare da anni" Kai ta
gyada tana tsugunna tana hade kadan gami da yiwa sabreen sannu. Kai kawai ta
daga,ita bataga wani ciwo da taji wanda yakai girman sannun da take mata ba.

Hannayensa ya zube a aljihun wandonsa yana kallonta,har sai da amna ta
gaya hada komai suka wuce dakin annin.

Ajiyar zuciya ta subuce masa,yana saqa abubuwa da yawa a kanta,sai
sannan ya duba inda yabar farouq a zaune,baya nan,yasan kuma ya fita qilan yana
jiransa cikin mota,don haka sai ya fara takawa a nutse yana barin parlor din ba
tare da musaddiq daya basu space ya isar da saqon maamah ba.

A mota ya samu farouq yayi d'ai d'ai suna shan hira da fanna dinsa.
Kusan duka hirarsu yanzu tafi rinjaye ne akan shirye shiryen bikinsu. Baice masa
komai ba ya miqa masa hannu ya karbi key din motar ya shiga ya tayar da kansa suka
fara fita daga gidan gaba daya.

Basuyi nisa sosai ba farouq ya kammala wayarsa,ya ajiyeta gefe yana
cewa.

"Sai yanzu hankalinka ya dawo kenan?" Ya fada yana kanne ido daya da sigar tsokana.
Waiwayawa yayi ya balla masa harara sannan ya dauke kansa,kaman bazai tanka ba sai
daga baya yace.

"Ina baka shawara kaqi ji ko?.....ina gaya maka ka dauke idanunka daga kan lamarina
ni da iyali na amma kaqi ji ko?". Sosai dariya ta zowa farouq,ya kuma soma yin
abarsa yana cewa.

"Allahu akhbar......dadin abun ma muma mun kusa aje iyalin nan muji abunda
akeji......muji ya giyar soyayyar nan take bugar da mutum" Qaramun murmushi ya saki
daya sake fidda kyan fuskarsa yana duban hanya.

"Kota tashi bugar dakai farouq ba zaka ji abinda nakeji a kan sabrrr ba.....nata
son daban yake a zuciyata......ban taba jin soyayyar abu a raina har haka
ba.....bansan daga ina wannan qaqqarfar alaqar ke sake gina kanta ba duk wayewar
gari zuwa faduwar rana" Yakai qarshen maganar yana furzar da numfashi a bakinsa.

Ido farouq ya zuba masa.......tabbas zuwa yanzu ya tabbatar da gaske
MAHAUKACIN SO fu'ad din yakewa sabreen,irin soyayyar da bai zaci zata kamashi ba
har ibada. Miskilancinsa da komai nasa na dabanne.......amma zuwa yanzu soyayya
tana sauyashi zuwa wani mutum na daban,idan ya zauna yana masa magana akan yadda
yakejin sabreen din cikin ranshi abun yana bashi mamaki sosai......yana jin kaman
ba me babban sunansa ba,wanda komai da kowa basu dameshi ba idan ka cire su da
anni.

"Inaji a raina da zuciyata......akwai wani abu cikin rayuwarta......akwai boyayyen
abu.......i need to know farouq".

"Kabi a sannu........da sannu zakasan komai din". Kai ya gyada masa.

"Na sani......but am eager to know about everything about her......inaji kaman
akwai sauran mutane daya kamata na hukunta bayan wadanda suke hannuna yanzu" Yayi
maganar yana jin kalmar karuwa da kowannensu ya taba fada a kanta tana masa zafi
har can qasan ransa.

"But naji maamah tana nemanka ma...." Farouq ya fadi yana tsoron kada fu'ad din
yaji amma yaqi zuwa.

"Maamah kuma.......ba wanda ya fadamin" Ya furta haka kawai yaji gabansa yana
faduwa. Ba kasafai kiranta ke zama alkhairi ba.....kai zaima iya generalizing cewa
kiranta ba wani alkhairi ko abu me muhimmanci da d'a zai iya tsinta a cikinsa.

"Musaddiq ta fadiwa.....bansan me yasa bai gaya maka ba"

"Yabar parlor din ne......anyway koma meye zamu koma gidan.....saina qarasa" Ya
fadi zuciyarta tana son lalubo dalilin kiran amma ya gaza.

Kai kawo ta dinga yi cikin dakin nata tana tattare kowanne tashin
hankali da take ganin zata sauke masa har zuwa sanda zata tursasashi guntule igiyar
jarababben auren data hada. Bata taba dana sanin aikata wani abu ba irin hada
aurensa da sabreen......tabbas yarinyar tana neman zame mata qadangaren bakin
tulu......itace cikakken ma'anar karin maganar nan da ake cewa DAN HAKKIN DAKA
RAINA SHIKE TSONE MAKA IDANU. Inda qannenta suna hannunta kawo yanzu tayi imani da
yaqinin da batasan ma wanne hukunci zata sakasu su karba ba a madadin 'yar uwarsu
ba.

Minti daya zuwa goma sha biyar ta lissafa amma bataji shigowarsa
ba,wannan ya sakata daukan wayarta ta kira musaddiq.

Ba'a daga ba amma taji an turo qofar dakin nata an shigo. Koda ta
waiwaya musaddiq dinne,ajiye wayar tayi tana dubansa.

"Ina yayan naka?".

"Na shiga daki kafin ya kammala,ina fitowa na tarar sun fita shi da BB farouq".
Wani irin kallo ta watsa masa cikin fushi tana qanqance idanu.

"Kasan me kayi musaddiq?!,kasan muhimmancin wannan kiran kuwa?....har yakai na baka
saqo ka kasa zama ka jirayeshi ka isar masa?,kana hauka ne musaddiq!" Ta fada da
wani yanayi daya bashi mamaki me kama da zata kai masa duka. A mamakance ya shanye
mamakin yana yin qasa da kansa kafin yasake dubanta.

"Kiyi haquri,idan ya dawo saina sanar masa,ko ina sukaje nasan ba nisa sukayi ba".

" Baka da hankali.....bani da wannan lokacin,bani da Lokacin bata lokaci......wuce
ka kiramin sabreen" Ta sake fada cikin daga murya tana nuna masa qofa.

Mamaki ya sake kamashi ganin yadda ta birkice,yaga dai koma meye duk
inda sukaje a gidan zasu dawo su kwana.....amma duka me ya kawo wannan yanayin mara
dadi?. Yankewa kansa wahalar tunanin yayi ya juya a salube yana fita a dakin.

Tana zaune daga gefan gadon tana duba hotunan da amna tace ta dauka a
wayarta sanda saqon ya isketa. Ta daga kai tana duban musaddiq a mamakance.

"Taje inji maamah" Ta sake maimaita saqon tana zubewa musaddiq dubanta. Tana juya
dalilin kiranne da kuma abinda zai iya biyo baya a kiran. Bawai tana tsoron zuwa
bane.....babu shakkarta ko dis cikin ranta.....bata wani tsoro ko shayin
fuskantarta......kawai tana duba girman musaddiq ne da tabbas zata ce masa yaje
yace mata bata zuwa.

"Gani nan zuwa" Ta amsa masa tana aje wayar a gefanta sannan ta miqe tana zura
qaramin Malaysian hijab dinta ta taka a hankali tana dosar qofar fita a dakin.
Zuciyarta fal saqe saqe,cikin jikinta takejin koma meye ya sanya ta kira BA
ALKHAIRI BANE.....koma meye kuma ta shirya fuskantarta.

Tana tsaye ta zubawa qofar idanu tana dakon shigowarta,tana jin
kaman tayi nawar isowar.....a haka ta murza qofar ta shigo kai tsaye ba tare data
maida qofar ta kulle ba. Kallon kallo suka yiwa junansu me wani irin zurfi kafin
maamah ta soma magana.

"Bakisan adadin kuskure da wasan da kikayi da rayuwarki ba sabreen......bakisan
gona da adadin iyakokin da kika sanya qafa kika tattaka ba......amma koma meye a
yau zan yanke wannan alaqar da kike taqama dashi......yau dinnan.....kuma a nan
wajen zan tabbatar miki da tsinkewar igiyoyin aurenki". Manyan idanunta ta maida ta
lumshesu a nutse sannan ta budesu.

"In har don wannan ne ni banga dalilin kirana da kikayi ba......wani abune da ke
daya ya shafa maamah.....don Allah saboda daraja da mutuncin musaddiq da nake gani
na roqeki kibarni na huta..... Allow me to rest.......tsakanina dake ba kare bin
damo. Contract ne nace bazanyi ba dama ba tun yau ba,yana da wahalar gaske na yiwa
rayuwata hukunci ayi challenge dina a sakani warwareshi......na bar miki contact
dinki......na karbi rayuwar qannena kuma akwai abinda yayi saura?" Ta qarasa
maganar tana zube mata idanunta wadanda suka fara tunasar da maamah wace ainihin
sabreeen din......ta fara juyewa kuma zuwa tsohuwar sabreeen da ake dab da
jana'izar halayenta.

Wani irin mamaki maganganunta suka bawa maamah din,ranta ya sake
dugunzuma.

"Kina tunanin kinci bulus?,rayuwar yarona zaki gwadawa bariki?,a gaban idanuna zaki
gwada aiki a kansa?"

"Wanne yaron naki?" Ta fada cikin calmness.

"Indai wannan ruhin dakike burin mallaka ne kike tunanin nayi wani abu a kai to ki
hutar da kanki......banason wata hayaniya akan hakan don bani da sauran buqatarsa a
rayuwata".

"Yanzu kuwa zan tsinke duk wasu igiyoyi da suke tsakaninku" Ta fada a zafafe tana
sungumar wayarta. Tana jin ya mata tsaho ta jirayi dawowarsa......ya mata tsaho har
sai sanda ya dawo gidan ta gwada mata koda magani ko babu akwai sauran power na uwa
da zata iya sakashi ya mata dukkan abinda tayi niyya.

Mamakin maamah din ya sake cika sabreeen din. Tanaso ta gogewa matar
haddar kanta tsaf.......tanaso ta gwada mata wani abu kansa amma inda akaci sa'a
har yanzun da take tsaye bata jin jituwar halayensu shi da ita.....tabbas don a
tsukin kafin ta hada karonta tabar rayuwarsu saita aje mata zazzafan darasi.

Mummunan faduwa gabansa yayi sanda kiran ya shigo wayarsa,abinda zai
iya cewa ya manta rabon da ya jishi.

"Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis......aslih li sha'ani kullahu fala
takilni ila nafsi darfata ainin" Ya motsa bakinsa a nutse ya karantata kafin ya
daga wayar ya hadata da earpiece din da ya jawo ya saka a kunnensa,don ba kasafai
yake magana da ita a hands free ba.




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 97


97

_An rawaito daga manzan Allah S A W yana cewa"babu wanda zai shiga aljanna alhali
akwai qwayar zarra na haqqin dan'uwansa a kansa_

_Bukhari da muslim_


"Muhammadu kana jina?" Tayi lafazin da wani irin kaushi.

"Ina jinki maamah"

"Indai ni uwarka ce dana haifeka.....na shayar dakai nono na har ka zama
mutum.....ina umartarka a duk inda kake ka dawo gida yanzu yanzu......a sanda kake
shigowar kuwa ina buqatar shaidar sakin matarka sabreeen......ma'ana ka datse dukka
igiyoyin aurenka dake wuyanta.....muddin baka dawo ka aikata hakan ba daga yau ka
dauka sunanka tsina......". Da wani azama ya latse kiran don bazai iya saurara ba.
Sauti mafi muni da zai iya cewa kunnuwansa sun sake saurara kenan bayan tsahon
shekaru.....sauti na biyi da ya kusa sanyashi kaman zai zare bayan sautin ALLAH
YAYI MASA RASUWA ME BABBAN SUNA.....KUYI HAQURI...a ranar da ake gaya masa rasuwar
mahaifinsa.

Subuce masa steering motar yayi abinda ya ankarar da farouq kenan,ya
sanya hannu da wani irin zafin nama ya kamoshi yana furta.

"Subhanallah" Da wani irin qarfi. Karbar steering yayi yana qoqarin maida
hankalinsa jikinsa amma sai yaji hakan ya gagareshi,wannan ya sakashi gangarawa
gefan titi ya tsaida motar yana fita daga ciki.

Numfashi yake ja sosai zuwa hunhunsa yana jin iskar da yake shaqa ta
masa kadan,ko tambaya daya ya kasa amsawa farouq dake gefansa,sai daga baya ya
fusgi kalmar

"Mu koma gida farouq.....now" Bai musa ba ya bude masa murfin motar,ya taka da wani
irin yanayi yana shiga,shima ya shiga mazaunin driver ya kunna motar yana juya
kanta zuwa hanyar da suka baro.

Ga mamakinta sanda ta sauke wayar a fusace saita samu idanun sabreeen
a kanta da wani irin nutsuwa tana dubanta.

"In don wannan abunne.....ai da basai kin tasoni ba,zaki iya aiwatarwa koda bana
wajen" Ta fada tana zama saman stool din dakin tana kallonta.

"Sabreeen tana zaman zamanta aka gayyatota kan abinda bai cikin
tsarinta......sabreeen tace bataso.....ba zatayi ba akayi amfani da rayuka uku masu
matuqar muhimmanci fiye da nata ruhin aka sakata yin abinda bata taba yiwa wani
ba......ta yaya a yanzun saboda ita din ba kowan kowa bace za'a cisgeta daga inda
aka dasata?" Kai ta girgiza.

"Yadda aka gayyatoni ba shiri......bazan fita a sanda ban shirya ba,saboda gaba a
guji taba rayuka irin na ameenatu din.....da kin kwantar da hankalinki ma zan
fita.....amma fa a sanda nayi niyya,a sanda koshi wanda kika hada alaqarmu dashi
din bai shirya ba......amma tunda kin zabi na fita a sanda kikeso kaman yadda kika
shigo dani a sanda kikeso......inajin ya kamata shi wanda akayi komai dominshi
yasan yadda aka qulla abun aka kuma warwareshi.....don nagaya yanamin wani gani
gani yana kuma kallona a matsayin makwadaiciyar dukiyarsa......bayan kuma ata nan
gefansa akwai uwarmu gaba daya" Tayi maganar fuskarta da murmushi kaman me fadin
wasu kalmomi masu dadi. Abinda kenan yake sake qule maamah......yadda qaramar
alhakin ke zama tana yaba mata zance duk yadda taga dama. Iya wannan kadai ya
isheta hujjar qwace suna da license na zama surukarta. Suruka take nema irin wadda
zata juyata kaman d'iyar data haifa,wadda zata bita kaman yadda raqumi yake biyar
akalarsa ba saba hanya.

"Kina tunanin ke dinnan qaramar alhaki kina da wani hujja dalilo ko qwarin gwiwar
fadan magana akaina d'ana ya yarda?".

"Aah" Ta fada idonta akan wayarta tana dannawa wadda ke sake tsokane idanun maamah.

"Ni bance dole ya yarda ba....amma dai qila wannan zai taimaka" Ta qarasa maganar
tana kunna wani sauti wanda sai data waiwayo dashi maamah ta fahimci video ne.

Tayi matuqar kaduwa,ta kuma yi mummunar razana da yadda ta gansu tarwai
ita da Hajj harira......rana ta farko da suka fara takawa gidansu dakinsu suna
gabatar mata da contract din aurenta da fu'ad. Komai ya fita kaman yanzu ake
dauka,da sautin muryarsu da komai.

Boyayyen murmushi ta saki ganin yadda abun ya daki.maamah da
wani.irin razanannen yanayi. Boyayyar CCTV camera din data saka a parlor din kenan
ba tare da sanin kowa ba. Zama da JIB ya qareta abubuwa da yawa,tun sanda tayi
noticing canzawar huda awancan lokacin da Naseer yaso bata ta,ta yanke ta
sakata,wanda ita ta taimaka mata taga duk wani motsi na huda.....ya kuma sake
qarfafa mata zargin da shi yayi sila ta gano komai.

"Wannan kawai zan nuna masa don yasan cewa bani na kawo kaina rayuwarsa.......ba
sonshi nake ba.......ban taba kuma sonsa ba.....banajin kuma zan soshi
din.......rabuwa da zaiyi dani kaman ragemin aiki yayi......" Maganarta ta tsaya a
nan sanda lallausan qamshinsa ya marabci hancinta.....kaman giftawar walqiya kuma
sai gashi a wanze cikin dakin a wani birkitaccen yanayi.

Wani irin kallo da yake saukar mata shi ya sanyata zare idanunta daga
kanshi. Wani irin birkitaccen kallo yake mata zuciyarsa na wani mahaukacin bugawa
da kalamanta na qarshe da kunnuwansa sukayi katarin ji

"Ba sonshi nake ba......ban taba kuma sonsa ba,bana jin kuma zan soshi
din......rabuwa da zaiyi dani kaman ragemin aiki yayi......". Inda tasan girma da
nauyin da kalaman sukayiwa qirjinsa tabbas ba zata fadesu ba.

Janye nasa idanun shima yayi daga kanta da suke sake sauya launi saboda
bacin ran da yakeji cikin ransa. Yayin da idanun maamah suke zube a kansa ita
kuma.....zuciyarta na quna tare da jaddada mata baqar mallaka sabreen din tayi masa
da yake kasa sukuni a duk sanda take waje......yake kasa aza idanunsa akan kowacce
halitta idan ba ita ba.

Da confidence dinsa ya shiga cikin dakin,yana jin cewa idanma tazo ta
gayawa maamah ne bata sonshi don ta sanya su rabu.....ba shakka ta dauko aikin da
bazata iya qareshi ba.....a yanxu a kuma yadda yake jinta a kusa da kowacce jijiya
ta jikinsa.....ko mutuwa bayajin xaya lamuncewa ta rabashi da ita.

"Gani" Ya fada yana dosana gefan sofa din dakin.

Idanu maamah ta zuba masa tana jin wani irin abu yana birkitata. Ga
qoshi ga kwanan yunwa,gashi a gabanta cikin qasa da mintunan data nema ya
isketa......gashi a gabanta cikin neman umarninta ya kuma cikashi.....rijiya ta
bada ruwa guga ya hana. Ko sau daya koda a cikin mafarkanta na zahiri da na
badini.......bata taba tunanin sabreen din nada kaifin basirar ajiye kowacce hujja
data shafi rayuwarta ba.....tunanin hana faruwar hakan ya sanyata bata waya ta
musamman da zasu dinga communicating......wadda bata nadar komai....komai din kuma
idan ya nadu ma zai goge kanshi da kanshi ne automatically.

"Tashi kaje kawai.......zan sake nemanka a lokacin da ya dace" Ta fada tana zubewa
sabreen wani kallo dake nuna zallar gargadi da yiwuwar afkuwar komai a karonsu na
gaba.

Sam sam sai yaji hankalinsa ya gaza kama maganar maamah din.......kamar
ba ita bace ta kirashi ga waya mintuna kadan da suka shude ba cikin wani irin
zazzafan yanayi?,to meye ya sauyata da sauri haka?.

Waiwayawa yayi kai tsaye yana duban sabreen,saidai idanunta kaf baya
kansu yana kan wayar hannunta. Sake maido dubansa yayi ga maamah,har yanzu shi take
kallo......saidai kuma da alama kalaman bakinta na sallamarsa ba sune a qasan
zuciyarta ba.

"Kaje nace" Ta sake maimaita masa tana fargabar kada yaci gaba da zama ta kunna
video din a gabansa. Kaman bazai miqe ba sai kuma ya miqe din,ya sake duban sabreen
da still tayi kaman bata wajen kaman kuma ba kowa cikin dakin. Maganganunta suka
dinga tsikarar zuciyarsa da wani irin ciwo. Girman qin da take masa har yakai ta
zauna ta fayyacewa duniya?,ta fayyacewa kowa?,shi kam idan bai dasawa sabreen
jarababben sonshi ba rako maza yayi duniya kenan,da wannan zafin da fushin ya fice
a dakin.

Miqewa tayi sanda ta tabbatar ya fita,tadan kalli maamah din
kadan,kaman zatayi magana sai kuma ta shanyeta tana tuna cewa ba sa'arta bace.

"Karki saki jiki kiyi farinciki da tsammanin kin kubuta ko kinci nasara akan
mariya.....a'ah....wasa farin girki wannan,hausawa sukace somin tabi ne wannan
hatsin gara a buta". Dan waiwayowa tayi,sai ta sake mata murmushi kawai tana sanya
qafarta waje.

Bawai kaman jiran fitowarta yake ba......dama jiran fitowartata
yake......ba zato ba tsammani taji ya cafke hannunta,bai kuma tsaya sauraren komai
ba ya soma tafiya da ita zuwa bakin qofa.

"Ina zaka kaini?.....ina zamuje?.....ka sakarmin hannuna......wannan bai kamata
ba,ni ba inda zanje......ka sakeni......wai ina zamuje?" Ta sake tambayarsa da
qarfi wanda ko sau daya bai waiwayo ya kalleta ba sai daya tabbatar ya sanyata
cikin motar ya kwashe qafafunta ya maida ciki ya rufe ya kuma zagayo ya zauna
gefanta.

Wani irin zama da ya bata daman jin irin hucin dake fita daga can cikin
zuciyarsa har saman fuskarsa. Ya tsareta da kallo da idanunsa da sukayi kaman
kwanciyar jini daga qasansu saboda zallar bacin rai.....farar fatar fuskarsa itama
ta canza launi zuwa reddish kaman wanda aka dinga yamutsa fuskar da maruka.

"Zan kaiki na killace......a muhallin da ba wanda ya isa ya ganki......zan kaiki
inda zamu rayu daga ni sai ke.....zan kaiki inda ba zaki sake ganin kowa ba sai
muhammad fu'ad.....zan kaiki wajen da soyayyar fu'ad ce kadai 'yancinki da zaki
samu" Yayi maganar yana sauke don rage radadin da zuciyarsa ke masa. Kafin tace
wani abu ta fahimci motar tasu ta fara motsawa tana fita daga gidan.

Hankalinta ya dan tashi,saboda sanin halinsa da tayi,to amma sai
tabi shawarar zuciyarta ta hanyar dakewa kaman abinda ya fada din bazai tabbata ba
ko bai dameta ba.

Tana iya jin wata irin birkitacciyar ajiyar zuciya da yake saukewa,har
tsakiyar kwanyarta takejin fitar ajiyar zuciyar wanda ba zata ce ga dalili ba. Ya
maida bayansa yayi relaxing sosai jikin kujerar yana sauke numfashi kaman wanda
yaci kuka. A hankali taji ya laluba tafin hannunta ya sanya nashi. Mannewa sukayi
guri guda abinda ya sanya tsigar jikinta tashi,tana iya jin yadda dumin tafin
hannunsa yake bin kowacce jijiya ta jikinta dake aika saqo,tayi yunqurin zame
hannun amma ya hanata,saima ya sanya hannunsa guda daya ya tayar da motar,cikin
qwarewa yake sarrafa steering din da hannu daya suna ficewa daga gidan.

Batace masa komai ba.....amma jikinta ya soma sanyi da ganin hanyar da
suka dauka. Basu taba bin hanyar ba duk a fice ficensu.

Wani irin guri ne da zata iya cewa tsahon rayuwarta bata taba ganin
gurin makamancinsa ba.....wani tsuburi na musamman dake kewaye da ruwa wanda kafin
su qarasa dab da wajen ya ajiye motarsa,tun bai fito ba ma'aikatan gurin suka
qaraso. Idanunta ta daga tana duban sunan dake maqale a signboard CONRAD RANGALI
ISLAND RESORT. Sanda take dawo da idanunta ya kammala kashe motar ya zare belt din
jikinsa,tattausan tafin hannunsa ya miqa mata yana tsareta da fararen idanunsa,a
hankali ta kalli hannun sannan ta kalli fararen qwayar idanunsa da suka fara komawa
daidai a lokacin.

Yayi wani irin laushi gaba dayansa,tun daga qwayar idanunsa zuwa
gangar jikinsa zaka karanci hakan.

"Banaso.....karkimin musu.....na gaji.....na gaji da jin musu,taurin kai,saba
maganata.....i beg you koda na awanni kadanne kawai kibi umarnina,koda na iya yau
ne" Ya fada da wani sauti me matuqar laushi. Haka kawai taji wani abu me kama da
tausayi yanason saukar mata.......duk wani izza da qasaita nashi duka ya zuge
tsakanin tafiyarsu zuwa yanzu. Gefe guda halaye da dabi'un matar da take kiran
kanta a matsayin mahaifiyarsa yana dawo mata. Wanne irin barazana wannan uwa keyi
da rayuwar d'anta?, ta tambayi kanta. Tunawa take da rayuwar da tayi a
gidansu,tsakanin kawunta da kishiyoyin mahaifiyarta,dabi'unsu da mu'amalarsu a
kanta gaba daya wasu iri ne da basu da dadin ji ballantana gani.....ta fuskanci
rashin nutsuwa da barazana me tarin yawa......yau inaga ace mahaifiya da kanta keyi
maka haka?.

Tana tsaka da wannan tunanin ta tsinceshi saman kanta,har ya zagayo
ya bude mata qofar side dinta,bai gaji ba ya sake saka hannunsa ya kama tafin
hannunta yana tayata fita a motar.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³
π™‹π˜Όπ™‚π™€ 98



98


_Manzan Allah S A W yace: Bawa zaizo ranar qiyama da tarin ayyuka da kuma tarin
lada,yana murna zai shiga aljanna sai Allah ya dakatar dashi,ga tarin mutane da
baisan daga ina suke ba.....dukansu masu neman haqqinsu ne a kansu a wajen
Allah,yaci dukiyar wancan.....ya zagi wancan.....ya zalunci wannan,ana biyansu da
haka da haka sai ya wayi gari bashi da komai cikin ayyukan ladansa,bayan ayyukansa
sun qare za'a koma ana diban zunubin mutanen a maimakon biyansu da ladansa ana
lafta masa,daga qarshe sai ya tashi baida komai sai tarin zunubai,sai Allah yayi
umarni wa mala'iku su jefashi a wuta( Allah ka tsaremuπŸ™πŸ½)_

_bukhair da muslim_



Sosai ya riqeta yana zagayo da hannunsa zuwa qugunta,sai ta
kasa janyewa kaman yadda ta saba saboda idanun mutane,zagaye da ma'aikatan suka
taka har zuwa inda wani boat ke ajiye. Kadan kadan zuciyarta ke bugawa saboda
shimfidadden ruwan dake zagaye da wajen fari qal da yake bada wani color me kama da
sky blue.

"Ina zamuje saman ruwa kuma?" Ta tambayi kanta tana jin tsoro yana shigarta. Tunda
take a rayuwarta wanna shine karo na farko da zata taba shiga jirgin ruwa,duk da
wannan din wani irin jirgi ne da zai nuna maka tsadar da yake dashi,tsarinsa daban
yake da sauran jiragen da take gani,yana da wata fargajiya da kujerun zama masu
daukan hankali.

Bata fahimci maganar da suke ba don cikin harshen Dhivehi suke magana
yaren 'yan qasar. Can qasan ranta tana mamakin yadda ya iya

Please Login or Register in order to submit comment