You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yiwa shi

"Ba zata zubewa duniya su ba....." Baisan zubewa ta nawa ya rage tayi musi
ba,kalamanta a kullum sake haska masa ita yake,yayi imani yana kuma sake samun
gamsuwa da dalilai masu tarin yawa dake bayyana masa lallai AKWAI DALILIN dawowarta
cikin rayuwarsu......lallai ta dawo ne bawai da sunan nadama ba ko gyaran
kuskure......AKWAI DALILI AKWAI KUMA HUJJA.

Wasu yana kallonsu shimfide a zanen tafin hannun qaddararsa,wasu kuma
baisan daga inda zasu soma bullo musu ba.

"Ba'a canzawa tuwo suna Muhammad,kuma ko ma meye ka zama sai dana haifeka sannan ka
zama din......mahaifiya daya ce kuma ni dince dai". Idanunsa ya lumshe na wasu
sakanni kafin ya samu budesu. Ba abinda maganganunsa ke haddasa masa sai sake
jagula duk wata qanqanuwar nutsuwa tasa da yake qoqarin samarwa kansa.

"Kiyi haquri" Ya sake maimaita mata kalaman da ta dade da haddacesu daga bakinsa.

"Yaushe zaku dawo?,idan ba nan kusa bane dawowar taka ka sanarmin......don nasan
sai yadda akayi dakai,sai kuma abinda aka shimfida maka".

Yaji saukar kalamanta sosai har saman zuciyarsa. BATA SON AHALIN ALHAJI
HAMZA KIBIYA ya dade dayin wannan karatun a qanqanin lokacin data duro cikin
rayuwarsu......ya kuma san halinta tun daga sanda ya fara rarrabe abubuwa har zuwa
sanda ta fice daga rayuwarsu. Idan batason abu bata sonshi kenan......dadi ko
wahala basa sauyata akan abun. Idan taqi taqi kenan.....hakanan idan taso taso
kenan......bata ja da baya akan duk abinda ta sanya a gaba......bata rasa ABUN
HARINTA komai dadewar lokaci.

Wadannan abubuwan ya sanya ya sanya dukkan wata nutsuwa da karatu nasa
a kanta......ya sanya duk wani nazari da dogon hange da tsinkayensa a kanta,yasan
wacece......sanin da ita kanta batasan bata kuma yi zaton yakai zurfin haka ba.

"Ba zamu wuce satin nan ba in sha Allah" Ya amsa mata kamar yadda ya amsawa anni a
dazun.

"Har sai ankai sati?" Ta masa tambayar a zaqe,har abun yadan so bashi mamaki,don
sam salon tambayar nata baiyi kama da ta zaqu ko tsahon kwanakin sun mata yawa da
zasu bayu ga ganinsa ba,tabbas yasan akwai dalilin tambayar a qasa.
"In sha Allah" Ya bata tabbaci yana jiran dalili na gaba

"Kudi nake buqata ka turamin ta account dina akwai amfanin da zanyi dasu......kada
suyi qasa da million daya" Tayi maganar kanta tsaye cike da karsashi da qwarin
gwiwa kaman yadda hajja ta kwatanta mata.

Mamaki kadan ya kamashi.....saidai ya ajeshi a gefe

"Akwai abinda baki dashi?,cikin gidan ko sutura ko wani abu makamancin haka?,ko
akwai wanda kike da buqatar ayi masa wani abun?"

"Duka babu ko daya.......shin waima sai ina da wannan buqatun zan buqaci kudi daga
wajenka?,yarinya ce ni qarama ko kuwa?,ko banyi isar da zaa dauki tsabar kudi a
bani ba har sai akwai dalili ko hujja?"

"A'ah......"

"To dakata......ba sharhi nakeso ba......kayi abinda nace daga yau zuwa gobe". Sai
yaji alamun yanke kiran,abinda ya tilasta masa sauke wayar daga Kunnensa yana binta
da kallo.

Yatsunsa kawai ya dora saman goshinsa yana murzasu a hankali,kadan
kadan yake furzar da iska me zafi daga bakinsa. Tabbas yasan da akwai wani
abu......akwai wata a qasa......

Wanzuwar kudi a hannunta kwata kwata ba alkhairi bane,kuma ko yanzun
bayajin alkhairi ne ya sanya ta nema.

Cikin lokaci qanqani yaji jijiyoyin kansa sun qara adadin gudunsu da
kuma harbawarsu,abinda ya haifar masa da fara jin alamun ciwon kai. Bayason
hayaniya......bayason matsala kwata kwata,wannan ya sanya yake nesa da mutane da
al'amuransu,banda kasuwanci daya daukoshi tsundum ya jefa cikin mu'amalantar mutane
qarfi da yaji.

Ba wani karsashi ko qwarin gwiwa ya dauki dukan abinda yasan yana da
buqata,a maimakon tattare takardun nasa gaba daya da yayi niyyar yi ya kuma
shiryasu kamar yadda ya saba. Yana da wani irin tsafta da duk abinda yayi amfani
dashi zai wahala ka sameshi ba'a killace ba.

Kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka ya tura qofar dakinsa
idanunsa akan dakunan abba da saddiq daya tabbatar zuwa lokacin sun jima da yin
bacci,wani lokacin sai ya dinga ji kamar su kadai ne basuyi sa'ar rayuwa ba.....sai
ya dinga ganin kamar kowa ya dace da rayuwa me kyau amma banda su. Duk sanda irin
wannan tunanin ya fado masa yakanyi qoqarin korar shaidanne daga ransa.

A gefan gadon ya zauna,ya miqa hannu ya kunna bedside lamp,dan siririn
hasken da baida takura da yawa ya bayyana. Hannunsa ya zura qasan drawer din da
fitilan take kai,ya ciro wani mini wallet dinsa,ya bude ya sake zaro wani qaramin
hoton dake ciki.

Duk da hoton baida cikakkiyar kala amma fuskar mutumin ta fita
sosai,kamannin nan nasa da murmushinsan nan da idan ya kalla sai yaji kaman idan ya
kirashi zai amsa.

Wani abu ya tsaya masa a wuya,yayin da idanunsa suka sauya launi,gefe
daya wani qaqarfan abu da ya jima yana kokawa dashi akan maamah din ya fara taso
masa,sai ya fara hadiyar zuciya kadan kadan yana qoqarin hadiye bacin ranshi,tamkar
me hadiyar lomar abinci,don daga inda inda kake kana iya hangen Adams Apple dinsa
daya zamewa wuyansa dama fuskarsa ado yana kaikawo daga sama zuwa qasa.

A duk sanda ya kalli fuskarsa cikin hoton sai yaji duk duniya ba wanda
ya kaisu maraici......a duk sa'ilin da zai kalli wannan jarumar fuskar sai yaji
zuciyarsa ta cika da qiyayyar kowacce d'iya mace a duniya idan ka debe anni da
manal......wata irin wuta ce take ruruwa a zuciyarsa a kanta......har yakanji kamar
bazai iya sake kusantar muhallin da take bama ballantana yaci gaba da accepting
nata ko kyautata mata a matsayin uwa.

Fuskar abban wata fuska ce da a kullum take tunasar dashi gwagwarmaya da
ainihin ma'anarta.....fuskar tasa fuska ce dake karanta masa tare dayi masa bitar
cusgunawa....uzzurawa da azabtarwa irin ta diya mace. Kowanne hoto nasa da abinda
yake karanta masa.....hakanan da abinda yake tunasar dashi. Ko kusa ko alama....ko
sau daya.....hakanan koda wasa bai taba sha'awar aure ba ballantana wata diya mace.
Yana kallonsu a wasu halittu ne na daban da babu imani ko tausayawa cikin
lamuransu.

Sanadin ciwon abban....da silar data sanya ya dinga ci gaba abune da
bayason tunawa,abune dake dake tilasta zuciyarsa juyawa MAAMAH baya da dukkan
abinda ya danganceta. Koda ya tuna da abin a sanda take daura dashi yakanji baya
buqatar kallon fuskarta ko kuma sauraren muryarta,yanaji cewa ba abinda zai bashi
sukuni face yayi nesa da ita.

*_AKWAI WANI SIRRI.....AKWAI WANI BOYAYYEN SIRRI CIKIN DUNIYARSA_*


*******Sannu a hankali take tafiya cikin daya daga cikin layukan da suke zame musu
turba kuma hanya ta isarsu gida a duk sanda suka rasa samun abun hawa ko kuma kawai
jin rikici irin na dalibin dakan qirqirarwa kansa tafiyar qafa haka siddan.

Ita daya a hanya amma tanata mamakin yadda yau aka raba musu lokacin
tashi daga makarantar alhalin tunda suka fara tsahon shekarun tare ake tashinsu. Ta
cika tayi fam akan yadda nadra din da haneefa sukayi gaban kansu suka taho gida
abinsu ba kamar yadda suka saba ba abinda basu taba yi ba.

Gefe daya kuma na zuciyarta ya cika da saqe saqe tare da tunanin yadda
zata qarqare haddace ayoyin qarshe na shafin da a yau zata bada haddarsa a
islamiyya. Kaman daga sama,babu zato kuma ba tsammani taji an finciki qaramar jakar
da take dan cillata a hannunta wadda ke dauke da muhimman abubuwa da dama. Sanda ta
daga kai kuwa a firgice barawon ya soma nisa da ita yana gaya mata

"Idan kina da gata,ko kina da me qwatoshi ki turo shi" Sai ya juya cilla sassarfa
ya fada wani lokon dake daura dasu.

Ko wanne sashe na jikinta rawa yake,tayi wata irin tsorata da bata
taba yin irinta ba.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 51


Abune da bai taba faruwa da ita ba koda wasa,ta waiga gabas da yamma kudu
da arewa,ba kowa a layin,babu gicci ko wulqawar kowa,ko cutas da ita zayayi zaiyi
ne hankali kwance,abinda ya sake kada mata hankali kenan,ta soma yunqurin tattara
dukkan qoqarinta wajen ganin tabar layin.
Taku uku tayi ya shawo kwana. Hannunsa riqe da jakartata da yanzu yanzu
aka wafceta. Birki taja ta tsaya,gudun zuciyarta yana sake qaruwa kaman zuciyarta
zata fito ta bakinta. Ta qura masa idanu tana kallonsa kaman yadda shima ita yake
kallon. Guduwa takeson tayi amma ta kasa kaman an kafeta a wajen.

Duk taku daya da zaiyi yana sake ganin kamanni na jini da kuma
yanayinta da SABREEN din. Yana mamakin yadda ta iya boye komai nata,yadda ta iya
bad da bami,ta iya nutsewa da narkewa cikin sararin duniya ba tare da ka iya gano
daga ina take fitowa ba ina kuma take komawa?.

"Karkiji tsoro......ni ba cutar dake zanyi ba.....jakarki na karbo miki,nazo wucewa
naga abinda ya faru,karbi jakarki" Baya taja kadan,bata jin aminta dashi sam sam a
zuciyarta. Wani irin raino da horo sabreen ta yiwa kowannensu na rashin yarda da
baquwar FUSKA muddin sunanka NAMIJI.

"Da gaske nake miki.....ba cutar dake zanyi ba,idan kuma baki yarda ba ga jakarki
nan" Ya fada yana ajiyeta a tsakaninsu sannna ya juya ya fara takawa yana barin
wajen fuskarsa shimfide da murmushi,qasan zuciyarsa kuma fes cike da murnar samun
CIKAKKIYAR NASARA da kuma tabbacin DAUKAN FASA mafi ciwo a gareta.

Sai data tabbatar ya bada tazarar da koda ya juyo zuwa gareta zaiyi
wahala ya cimmata sannan ta taka ta isa ga jakar,ta tsugunna ta dauka,ba tare data
damu da datti da qurar data debo daga qasa ba ta rataya tana maida idanunta kansa.

Tafiyarshi yakeyi baiko waiwayota ba,ta kalli jakar ta kuma
kalleshi,sai ta buda bakinta a hankali tana furta

"Na gode". Cak ya tsaya tamkar dama yana dakon martaninta ne,sai ya waiwayo yana
sake fadada fara'ar fuskarsa

"Nima na gode.....sunana....." Dakatawa yayi kadan saboda tuna wani abu da yayi

_"Tana da wayo,tana da hadari.....da alama kuma akwai abinda ta taka_ kalaman suka
dawo masa kai fes

"Sunana BASSAM....kefa?" Ya furta yana murmushi tare da samun gamsuwar lallai sunan
zaifi saurin isar da saqo a maimakon ainihin sunansa na NASEER. Bashi da buri baya
kuma fatanbta fahimci komai har sai zuwa sanda komai din ya kammala......har sai
zuwa sanda shi da kansa zai mata bayanin komai. A lokacin da yake buri da kwadayin
jin sheshsheqar kukanta......a yanayin qunci baqinciki da kuma tarin damuwa da yake
fatan ta hallakata......koda bata hallakata ba yana fatan tayi mata mummunar illar
da koda gaba ba zata qara gigi kasada ko gangancin shiga shingen mutane irinsa ba.

"Kefa 'yammata?" Ya tambayeta cikin lanqwasa murya da tausasa harshe gami da sanya
wani amo me sanya nutsuwa ga duk me saurare.

Lokaci daya ta danji ta samu nutsuwa kadan,sai ta sauke boyayyar
ajiyar zuciya sannan ta bashi amsa

"Huda" Ta furta a nutse tana jin wani iri da kiranta da sunan 'YAMMATA da yayi,karo
na farko cikin rayuwarta da wani ya taba kiranta da wannan sunan.

Murmushi ya sakar mata yana gyada kanshi gami da lumshe ido yakuma
budesu a lokaci guda

"Nice name.....duk wanda ya baki wannan sunan ya iya zaben suna". Maganar tasa ta
sanya fitar murmushin dole a saman fuskarta. Tadan murmusa kadan,abinda ya sake
sanyashi ganin kamanninta muraran da sabreen. Wutar daukan fansanshi ta sake ruruwa
cikin ransa.

Kai ta jinjina a nutse tana dan sadda kanta qasa kadan

"Autyna ce" Ta samu kanta da bashi amsa

"Antynkin nan tana ja da yawa.....ta iya zaben sunaye" Ta fada da ma'ana biyu,a
zahirance kuma da harshen da ba kowane zai fahimci boyayyen sirrin dake qasan
zuciya ba.

Dagowa tayi a karo na biyu ta sake kallonsa,sai taji wani dadi
zuciyarta tana saki kadan. Duk wanda zaya so sabreen a wajensu basu da
kamarshi......kaman yadda suke nisantar wanda zai kawo suka a kanta ko wanene.

"Nadan rakaki kadan ko?,ki fita daga layin nan,don har yanzu ban gamsu da
sahihancinsa" Ya fadi yana duban gefe da gefansa bayan ya zube dukka hannayensa
cikin aljihu.

Tayashi duban itama tayi gabanta yana dan faduwa,ta yaya zata iya
jerawa dashi wai?. Amma ko kafin tace komai ya fara takowa zuwa inda take tsayen
yana jifanta da murmushi,tadan ja baya kadan dole ta fara takawa ya rufa mata baya

"Kada ki damu,bawai zamu jera bane,ba wanda zaisan tare muke......kawai dai zanyi
gadinki har ki aminta" Kalmar aminci daga bakinsa ta sanya taji ta sake,sai taci
gaba da tafiya,shi kuma yana biye da ita da 'yar nisan tazara a tsakaninsu.

Duk wani taku nata guda daya yana lasafta yadda komai zai
wakana......a yanzu bayan wutar daukan fansa dake ransa,wata wutar daban ta soma
rura kanta da kanta a zuciyarsa.......bayajin koda ba komai tsakaninsa da sabreen
zai iya qyale wannan danyar 'yar shilar ta wuceshi. Duk da bata qarasa 'yar uwarta
ba a komai.......amma zata sama masa nutsuwa yayi yaqinin hakan ko yaya take kaman
yadda ya dade yana tsara zai samu daga yayartata.

Bai tsaya ba har sai da qafafunta suka isa babban qofar gidan nasu,sai
ya samu waje nesa kadan saboda gudun bacin rana da bacin aiki,ya tsaya kawai yana
jifanta da wani mayataccen kallo tamkar mayunwacin zaki.

Har ta sanya qafafunta sai ta dakata ta waiwayo,suka hada idanu abinda
ya bashi damat jifanta da wani shu'umin murmushi. Itama murmushin ne ya subuce daga
bakinta tana jin cewa ya kyautata mata matuqa,abinda ba kasafai suke samunsa daga
wajen al'ummar da suke kewaye dasu ba,don haka wannan din ya qawatar da ita.
Bakinta ta bude a hankali ta furta kalmar

"Na gode sosai". Duk da tasan ba lallai ya iyajinta ba,amma zai karanci bakinta. Ya
kuma karanta din,sai ya daga mata kai don haka ta juya tana shigewa cikin gidan.

Haka kawai murmushi ke fita a fuskarta tana tuna yadda komai ya
kasance. Badan shi ba Allah ne kadai yasan abinda zai faru da ita a wannan qonannen
layin da babu kowa. Ba yadda kuma zatayi,nan dinne dai hanyar wucewarsu tilo guda
daya,inda da wata hanyar tabbas ba abinda zai sanyata ta sake bi ta nan wajen.

"Ke dawa kike murmushi ke daya?" Sabreen dake tsaye gaban fridge dinsu tana duba
adadin pure water da lemon daya rage musu a ciki ta fada hannunta dafe da murfin
fridge din. Cikin sauri ta gyara yanayin fuskarta tana qoqarin adana takalmanta
data shigo dasu

"Ba kowa adda...." Idanunta ta zube mata sosai tana son karanto wani abu amma bata
samu nasarar gano komai ba,saidai duk da hakan haka kawai takejin bata nutsu da
irin amsar huda din ba. Emotions ke sauya yanayin fuskar mutum,walau na farinciki
ko baqinciki,dole idan ya nuna saman fuska to akwai wani labarin a qasan zuciya.

Sakin fridge din tayi bayan ta rufeshi tana takowa tsakiyar dakin

"Wacce irin tafiya kukayi ne yau ke dasu nadra?,kinsan dai banason kuna raba tafiya
ko?" Ta fadi tana zama idanunta still akan fuskar huda din.

Fuska ta bata ba kaman dazu ba tana duban sabreen

"Wallahi dama nace zamu hadu dasu.....kawai adda ina fitowa na samu wai sun wuce
gida?,yau bansan me yasa aka rarraba mana lokacin tashi ba" Ta qarasa maganar
fuskarta a bace da gaske. Idanunta tadan dauke daga kanta tana sauke numfashi

"Banason irin wannan tafiyar,kome raba lokacin su dinga jiranki" Cikin ranta tana
jin abun kwata kwata baiyi mata ba.

Qaramar dariya ya sakarwa kansa bayan ta shige gidan. Fara takawa yayi
hankali kwance yana barin layin. Tabbas shima zai buga nasa wasan yadda ya
dace,zaiyi wasa da rayuwarta da kuma hankalinta yadda ya kamata......zai gigita
mata rayuwa ya dagula dukkan wani lissafi nata......zai guntule dukkan wani
farinciki nata kaman yadda ta gurgunta ta kuma dagula rayuwa da nutsuwarsa. Yanaji
a ransa abun zai bashi nishadi qwarai,zai kuma qarasa goge baqinciki qunci da
takaicin data qunsa masa.

********Cikin nutsuwar nan tasa yake saukowa daga matakalar jirgin riqe da kyawawan
briefcase guda biyu. Tasa data Alhaji hamza kibiya.

Biye yake da dattijon,yana aje tasa qafar a duk muhallin da ya cire.
Kamilallen dattijon da adadin furfurar dake baibaye a fuskarsa da kuma gashin kansa
suka sake tabbatar da dacewar sunan dashi. Cikin kamala yake komai nashi,sanye da
shadda dinkin babbar riga da maroon hula dara sak ainihin shigar marigayi malam
aminu kano.

Muhammad fu'ad jadda,mamallakin kamfanin jadda diamond chores resources
wanda ke biye dashi a baya. Sanye cikin dinkin kaftan da yayi matuqar qara masa
kwarjini da wani irin haiba me cika idanun me kallonsa. Idan ka kallesu shida
Alhaji hamza kibiya din zakayi tsammanin shine ainihin mahaifi gareshi saboda yadda
tsahonsu yake kusan daya da kuma murjewar jikin. Bayansa kuma sadiq ne janye da
luggage dinsu. Shikam t.shirt ne jikinsa da trouser,ya lullube qafafunsa da
lafiyayyen boots ba kaman fu'ad ba dake sanye da wani lafiyayyen halfcover ba dan
qasar itali da aka samar dashi da dinkin hannu(sau da dama mu a nigeri muna raina
takalman hannu,amma a qasashen qetare babu takalma masu daraja da tsada irin
handmade shoes,wani ma kana ce masa handmade ne ka bata show dinπŸ˜‚,nija my nation
πŸ˜‚
).

Tare suka jero kafada da kafada shi da Alhaji hamza din zuwa
muhallin da farouq yafi tsaiwa a duk sanda yazo daukosu daga tafiya irin wannan. Ko
a yanzun da suke nufar mota don isa gida ma duk hirar akan kasuwanci ce. Abun yana
bawa Alhaji hamza mamaki. Duk qwarewarsa da qaunarsa da kasuwanci fu'ad din ya
shallakeshi. Kowacce rana kowacce safiya,kowanne dare da wuni plan din rayuwarsa da
komai nasa yana kan kasuwanci. Me za'a bunqasa?,me za'a qirqira?,me kuma za'a
gyara?,ina ne nasara take a bunqasata?,ta ina faduwa take ayi hanzarin bawa gurin
kulawa da kariya?.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*
PAGE 52


Yana jingine da motar yana kallonsu,idanunsa fes a kansu. Yana masa dadi yana kuma
sanyawa ya manta cewa fu'ad ba dan uwansa bane na jini a duk sanda ya ganshi kamar
haka da Alhaji hamza din. Yana alfahari yana kuma qara ninka alfaharinsa akan
muhammad fu'ad din. Shi kansa ya sallama......jajirtaccen mutum ne da jajircewa
take a cikin jinin jikinsa.

Ya maida idanu a hankali akan yanayin takunsa. Tafiya ce me cike da
ginshira gami da cikakken kuzari da karsashin da zai bayyana maka adadin cikakkiyar
lafiyar da yake da ita.

Daga abban har fu'ad din hankalinsu baya wajen,yana duba wani qaramin
takardu da suke dauke da bayani da taswirar burinsa na gaba wato ginin katafaren
kamfanin samar da kayan ado na sarqoqin mata da zai dinga amfani da wani sashe na
ma'adanan da yake haqowa.

Tun daga fitowarsu gaba daya security guards dinsa da ya bari a gida
kowanne ya koma kan aikinsa. Dukan inda ya ajiye qafarsa nan suke maida tasu.

Murmushi ya subucewa farouq,ya dawo kenan,kuma yanzun za'a fara.
Bayaso abba ne ya tilastashi daukan guardsmen duba da yanayin qarancin tsaron da
ake fama dashi. Uwa uba ma zaiyi wahala a nasibin rayuwa daya samu......da irin
mu'amalarsa ace ya zauna haka gayansa yana yawo babu masu tsaron lafiya tattare
dashi.

Wani lokacin idan yaso yana kubce musu ne yayi fitarsa shi kadai a
mota yasha iska ya dawo. Ba kasafai ya fiya son fita qasashen waje sai idan harka
haka ta taso takai kayan da sunyi yawan yayi wakilci......amma yanzun ya koyi fita
din lokaci bayan lokaci haka siddan ma don ya samu ya sarara yayi rayuwarsa shi
kadai. Mutum ne da bayason matsi,bayason takura,zai iya rayuwa me dogon zango shi
kadai a wani muhalli na daban,shi yasa ko a yanzun a sassansu gini ne me zaman
kansa dake dauke da bedroom and parlor da toilets kowa shi kadai. Saddiq da
musaddiq sun hade dakunansu saboda kowa nashi apartment din ya masa girma. Amma oga
fu'ad shi daya ne a nashi,hakama farouq,sai shi farouq din da lokaci bayan lokaci
yakan dawo sassan fu'ad din yayi kwanaki yana kwana a nan sannan ya koma wajensa.

Kullum ya hangi fu'ad din daga nesa ba abinda yake tunawa sai wannan
matashin dan bautar qasar,mara tsoro kuma mara shakka,cikakken jarumin daya shiga
yankin daba nasa ba,yayi abinda koda haifaffen yankinne ya aikata bazai sha
ba.....ya kubuta da tarin nasara. Farouq yadan sake murmusawa yana tuna yadda yaci
wahala bayan uban gudun da sukayi,ya tuna yadda fu'ad din yayi jinyarsa tamkar ba
dashi akayi gudun ba

"Ba abinda nakeji man.....ni dakai ba daya bane,sau nawa ana gaya maka ka dinga gym
saboda yuwuwar samuwar irin wadannan lokutan na qwatar kai?,sai kuyita zama kaman
mata,baku da wani banbanci dasu?" Ya tambayi farouq din a wancan lokaci yana dage
masa dukka girarsa bayan ya bashi maganin ciwon jiki yasha.

"Yanzu wannan pain killer din da kake fana dashi......da warm water da fenugreek
kake sha da yafi maka amfani". Harara ya balla ma fu'ad din yana dubansa

"Ba zaka qarasa kasheni ba da wadannan home remedies din naka ba" Sai ya juya ma
fu'ad din baya yana sauke numfashin wahala yabar fu'ad din da sakin siririn
murmushin nan nasa me tsada. Miqewa yayi yana dauke cup din

"Idan home remedies bai kasheka ba......son jiki da rashin exercise....aci a kwanta
duka ya kasheka......naga wanda zai aureka da qaton tumbi" Ya qarasa maganar yana
jefa kwalin lemo a dutsbin. Duk da farouq na cikin yanayi a sannan saida murmushi
ya qwace masa.....fu'ad mahadin rayuwarsa ne kuma mahadin zuciyarsa ne kaman yadda
ya tabbatar a wajen fu'ad dinma haka yake.

Kafadarsa y
Ta dama yaji an daka

"Murmushin me kake kai kuma?" Sassanyar muryar nan tasa sake cakude da wani
deepness ta shiga kunnen farouq. Kallonsa ya dora saman fuskar fu'ad din yana jin
yawan kewarsa da yayi

"Ina nan ina kallon gujajjen dan bautar qasar nan da bai kammala service dinsa ba
sai a garin kano". Murmurshin nan da shi daya ke iya fidda masa shi daga kan fuska
ya saki kadan yana sake kaiwa kafadarsa duka. Dariya kadan ya saki shima farouq din

"Ina hasaso yadda zasu cinye namanka danye duk sanda suka fahimci daga ma'adanin
qasarsu ne aka samar da attajirin nan mamallakin jadda diamondchore
company........" Murmurshin ya sake sanyashi saki,sai ya saka tafin hannunsa saman
wuyansa yana dan karyar da wuyan kadan

"Naman muhammad jikan jadda yafi qarfin cinsu umaru...." Ya bashi amsa da anihin
sunansa,abinda ya sanya farouq din sakin dariya sosai. Kafadar fu'ad din yadan
bubbuga

"Na sani.....nafi kowa sanin wannan dan uwan nawa wanne iri ne......tun daga ranar
da mukayi temple run dinnan na sake yadda da hakan..."

"A nan zaku gama hirar ne?,idan ku baku gaji ba ku tallafa ku kaini naga aminatu
na" Muryar abba ta sauka kunnuwansu.

Fu'ad ne ya waiwaya don farouq yana fuskantar abban ne. Dan murmusawa
kadan fu'ad yayi ya matsa yana yunqurin budewa abban qofa,amma farouq ya rigashi

"Dukkanku kai da abban yau

Please Login or Register in order to submit comment