You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wayar tahau kadawa,ta zubawa sunan da
zuwaira tayi saving dashi wato hajjaju. Tattaro dukka wata dauriya tata tayi,ta
hadiye wani yawu me kauri sannan ta daga kiran ta sakashi a hands free hana ajiye
wayar saman cinyoyinta.

"Ka kula da ita.....huda kuje ya baki magani kisha kafin ki kwanta.....sannu
qawata". Abinda kunnuwanta suka fara jiye mata kenan wanda ya sanya tsigogin
jikinta tashi. Ta runtse idanunta tanajin kamar an daukk guduma an kwada mata saman
kanta.

"Huda kuma?" Ta motsa labbanta tana furtawa a wahalce. Murmushin maama ne ya soma
riskarta kafin tace

"Eh,huda.....ko bazatayi lalura ba?......kowanne sakaci da zakiyi akwai sakamakonsa
kan halittar da kika fi so fiye da komai da kuma kowa......"

"Bani huda din" Ta fada kanta tsaye da wani irin yanayi me kaushi. Wata qaramar
murmushi me kama da dariya ta saki

"Da wuri haka?,zabin cetonsu ai yana hannunki tunda na gabatar miki da dukka kayan
aiki.......bansan me yasa kika yanke sadarwar dake tsakaninmu ba.....saidai koma
meye wannan ba damuwa ta bace......kowanne ganganci kuskure ko sakaci sakamakonsa
rubutacce ne a nan......"

"Idan kikayi kuskuren cutar da ko farcen daya daga cikinsu ne......to lallai ba
shakka ba mallaka miki danki zanyi ba......zan sadar dashi da kabarinsa ne,zan
mallakaws barzahu shi a madadin ki" Sabreen ta fada cikin tsawa da wani irin
birkitaccen sauti daya ratsa maamah,taji kuma har cikin jikinta da gaske ta fadi
maganar. Ta danyi jim kadan tana jin wata shakka tana ratsa ta,sai kuma ta saki
wata dariya

"Bismillah mana......indai har kina ganin hallaka mutum kamar muhammad jadda abune
me sauqi....."

"Akwai abinda yafimin wannan sauqi?.....aikinki ya ninka shi wahala sau dubunnan da
bazasu qirgu ba.......idan naso a safiyar gobe za'a wayi gari da sanarwar
jana'izarsa hajiya maamah.......saboda haka ki kula......akwai kadarata a
hannunki......a nan kuma akwai ruhinki dama kadararki gaba daya a tare dani" Daga
wannan ta yanke wayar.

Zare wayar daga kunnenta maamah tayi tana kallo. Wani irin mamaki da
tsoro yana kamata,wacce irin yarinya ce wanannan?,wadda bata tsoro ko shakkar duk
wani abu girman tsoron dake tattare dashi?.

Gabanta yayi mummunar faduwa sanda ta tuna zancan idan taso za'a sanar
da jana'izar fu'ad din a gobe. Ta motsa da wani irin hanzari ta miqe sai kuma ta
koma ta zauna. Waye zata gayawa?,shi fu'ad din?,tace yakula da za'a iya
kasheshi?,to waye zai kasheshin?,ya kuma zatayi masa bayani akan yadda akayi ta
sani?,ya daina cin abinci?,wannan kuma shine burinta babba a yanzu ya karbi abinci
daga hannunta don samun cikar burinta,ta yaya zata sanya idanu akan wani abu daban
da zata shirya wanda zai sauka daga kan tsari da kuma muradinta?. Zuwaira ce ta
fado mata rai,sai taji tana samun sassaucin tsoron da kuma firgicin da take ciki.

Hannunta dukka biyun ta sanya ta dafe kanta.

"Huda,ya kula da ita ya bata magani tasha?,who's she?" Abinda ta dinga maimaitawa
kenan. Hudan da har yanzu take ganin tana buqatar therapy tana buqatar counselling
akan mikin da nasir yayi mata.......yanzun kuma tana shirin sake fadawa wani abun
na daban?,kanta da zuciyarta kuwa zasu iya dauka?,ya kamata ta ciyar da d'anta ta
kowacce siga muradinta.....idan yaso in taga dama bayan ta mallakeshi ta
yayyankashi ta cinye.

Abu daya ta kasa jurewa ya kuma gaza barin zuciyarta huda,ta yaya
zata ji muryarta?. Bata taba jin dauke wayoyin ya dameta ba irin yau,ta dinga jin
kamar tayi hauka idan ta tuna ba wata sauran hanya da zata iya samun damar magana
da huda.

Sosai tayi qoqarin ganin amna bata gane komai akan fuskarta ba. Ta
kama mata aikin sukaci gaba dayi,tana ci gaba da mata hira tana bata labarin fu'ad.
Kwata kwata bata jinta ma ballantana ta fahimci abinda amna din ke fada,a haka suka
kammala amna ta fito tabar mata kitchen din. Sosai ta zazzaga dukkan abinda ya
kamata ta sake juya abinci ya koma ainihin launinsa. Ta tsaya kaman ko yaushe ta
zubawa abincin idanu zuciyarta na wani yamutsawa,mafi rinjaye na zuciyarta tana jin
kamar wani yanayi mara dadi,wani yanayi da yafi kama da rashin jin dadi?,rashin
kyautatawa?,ko aikata abinda ba daidai ba?. Itama bata sani ba,bata taba zaton da
hannunta zata iya ciyar da kowanne dan adam abinda bai kamata yacishi
ba......saidai abu daya ta sani shine....itadin guba ce ga duk wanda yace zai
kawowa innocent rayukan nan guda uku farmaki.

Takun da taji dake alamta mata an shigo kitchen din shine abinda yayi
bala'in razanata. Da sauri a kuma birkice ta daga kanta tana duban me shigowar.
Zuwaira ce fuskarta da murmushi ta qaraso cikin girmamawa.

"Afuwa,dama cewa nayi bari nazo naji ko akwai aikin da za'a kama miki?" Tayi
maganar tana duban warmers din da a gaban idanunta tana labe sabreen din ta cika
aikinta tsaf. Idanunta ta lumshe tana jin yadda zuciyarta ke bugawa,sannan ta
tattaro dukka qarfinta ta bude idonta akan zuwairan

"Wannan shine kuskurenku na farko,bana buqatar ki sake shiga wani guri a cikin
gidan nan ba tare da kin tsaya kin nemi izini ba an kuma baki" Kai ta rusunar

"Ayi haquri bazai sake faruwa ba in sha Allahu" Bata iya amsa mata ba,sai kawai
warmers din data mata nuni dasu

"Ki kaisu kan dining" Tayi maganar tana dosar qofar fita a kitchen din,don sam bata
da qwarin tsaiwa ci gaba da magana.

Tana sanya qafafunta da zummar fita tana sako tata qafar abinda ya
sanya suka kusa karo da juna,yatsun qafarta suna caki na sabreen haka gwiwarta
saita tsaya cak bata ja baya ba bata kuma koma ba. Tsaiwa cak itama sabreen din
tayi tana danjin qafarta na dan radadin kadan saboda qafafunta akwai alamun tana
ajiye farce.

Shirun da sabreen din taji ya sanyata daga kanta ta sauke dubanta
akan laila. Tana tsaye cak ba alamun zata kauce mata ta bata hanya. Bisa dukkan
alamunta tana jiran sabreen ne ta kauce mata,kota koma sai ita ta wuce. Cikin qasa
da second biyu sabreen din taji wani abu ya saukar mata,wani abu me kama da izza da
jin mallaka ya mamayeta. Ta lumshe idanunta sannan ta zubesu fes akan laila tana
duban tsakiyar qwayar idanunta da wani irin kallo dake qure qarfin halin mutum. Da
farko itama laila din ta zuba mata idanu,saidai a hankali wani kakkaifan abu ke
ranqwafar da nata idanun. A hankali taji ta gaza jurewa,saita dauke dubanta daga
kan sabreen din tana ja da baya,ba tare data sake dubanta ba ta rabata ta wuce a
tsanake ba tare data sake duban sashen da take a tsaye ba.

Da idanu tabi sabreen din har ta wuce,ta maido dubanta cikin kitchen
din tana jin kamar yau karon farko ta tozarta......a karon farko taji wata 'ya mace
tayi mata kwarjini,har kuma ta juyata ba tare data furta kowacce kalma daga bakinta
ba. Hada ido sukayi da zuwaira,sai zuwairan ta tabe baki tana dauke kai. Cike take
dama da lailan,cike kuma take da yadda maamah ta dinga jaddada mata ta girmama
lailan,don gidan fu'ad a wajen lailan tamkar gidan mahaifinta yake,tammar kuma
gidan yayanta da suke uwa daya uba daya yake.

"Idan me guri yazo dai me tabarma nadeta yakeyi,nan din dai akwai macen data amsa
sunan matar gidan,komai ayishi bisa takatsantsan". Sarai ta fahimci abinda zuwairan
ke nufi,amma sai taga sam bata da lokacinta,don abinda sabreen tayi yafi tsaye mata
a rai,yadda zaiyi handling nata. Da gaske komai na gidan yayi mata,da gaske zuwa
yanzu tanaso ace itace mamallakiyar gidan. Ta cika gidan da izzarta da mulkinta da
kuma ikonta kwatankwacin hajja,tako ina ta zama ME MULKIN gidan.

Samun amna tayi tana shirin tafiya.

"Har me?" Ta fada cikin nuna kulawa. Murmushi ta saki

"Driverna na aje adda tun dazun fa,daga cewa anni zanzo na miki sannu da zuwa".
Fararen idanunta da a yau take jinsu wani iri ta kada,bata da energy din dogon
magana.

Closet dinta ta bude kawai tayita fiddo abinda take ganin ya kamata
ta bawa amna. Ta hada abubuwa cikin qaramar jaka me kyau da daukan hankali.

Ido amna ta fiddo tana nuna tsananin murna da mamaki

"Duka adda?" Ta fada da murmushi. Abun ya burge sabreen sosai,yadda amna din ta
nuna,duk kuwa da cewa tasan tafi qarfin duka abinda zata bata din.

Fitowar zuwaira da laila daga kitchen din ya danja hankalin amna dake
qoqarin ficewa,ta bisu da kallo kawai kafin ta juya a hankali ta fara takawa tana
fita daga falon.

"Sai haquri ranki ya dade....laila kenan..... D'iyar hajja harira.....hajja harira
'yar majalissar zartarwa hajiya mariya maamah". A badini kyakkyawan masauki maganar
zuwaira ta samu,hajja hariran da sukayi tattaki har cikin gidansu suka kai qudurin
aurota don su cimma buqatarsu?,ta yaya zata manta wadannan fuskokin,ranar,dama
abinda ya faru a ranar....har maamah din tana da qarfin halin ajiye budurwa irin
wannan a gidan d'an data haifa?,wanne irin kwado ne wannan?,budurwar da babu wata
alaqa tsakaninsu face ta zallar qawancen dake tsakaninsu?,a tsarin abota da
mu'amala da zata fishshi dan adam tasu bata kan ko guda daya. Kai ta
jinjina,information din ya mata kyau da ma'ana,amma kuma batajin zata sakewa
zuwaira ko ta nuna jin dadin hakan.

"Ya kamata ki dinga tsaiwa a iyakokinki kawai" Abinda tace da ita kenan tana takawa
zuwa hallway dinta don komawa dakinta,duk da har yanzu ba wani cikakkiyar nutsuwa
ko sukunin data samu daga uban tunanin dake addabarta,gefe guda kuma tana cike da
fata da fargabar sanya abincin a bakinsa ya zarce zuwa cikinsa.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_ZAFAFABIYAR_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 33

_Daga nana Aisha R.A tace:manzon Allah S A W yace:Duk matar da tayi aure ba tare da
izinin waliyyinta ba,to aurenta batacce ne,idan mijin ya tare da ita taci sadakinta
saboda halastar farjinta a gareshi_




33


β˜…"ma sha Allah,sannunta da qoqari" Anni ta fada sanda ta gama ganin
kayan da amna ta kawo wanda sabreen ta bata.

"Tana da kirki anni......amma sai nake ganin hamma me irin halinsa ya dauko,she's
so quite,batason hayaniya da yawa,bata fiya bada amsa ba ko magana,tafi yawan
murmushi kawai". Murmushi anni ta sauke,har zuciyarta tana sake jin yarinyar tayi
mata,a duk wani lokaci da maganarta zata tashi tana sake jin sabreen ta kwanta mata
ne.

"Ai dama sai hali yazo daya ake iya zama ko?,Allah ya qara hada
hankulansu......yauwa farouq yayi nemanki kuwa sanda kika fita......naji kaman yana
maganar zaku abuja passport dinki yayi expired,za'a sake miki wani". Idanu amna ta
fiddo sannan ta qanqame anni

"Anni hala Lokacin tafiya ya kusa?". Dan tureta kadan tayi daga jikinta

"Gashi kuwa kin gani keda tafiye tafiye basa isarki" Dariyar jin dadi ta qyalqyale
dashi.

"Amna wannan tafiyan daban yake a rayuwata Allah,ba wani trip da yakaimin wannan
dadi....whole family fa anni.....wannan karan kuma abun zaifimin dadi saboda nima
na samu partner addana,adda sabreen,na daina maqalewa su ya saddiq suna
wulaqantani,wannan karon tafiyar zai zama na musamman" Tayi.maganar with full
excitement. Da kallo kawai amna ta bita kafin ta saki murmushi,ita kanta tasan
tafiyar zata qara dadi musamman da idanunta zasu dinga gane mata fuad dinta da
iyalinsa a gefe,cikon mafarkinta kenan

"Anni bari naje na sameshi" Ta fada tana daga yatsunta gami da lissafa watan da
tafiyar tasu zata kama

"Yes" Ta furta tana jin farinciki yana lullubeta,saita cilla da sauri zata fita
tana cewa

"Dis time har abba fa sai na karbi kudin tsaraba a hannunshi,komai bibbiyu zan
dinga siya nida addana"

"Kunfi kusa ai" Anni ta bata amsa. Dakatawa daga fitar da anni taga amna tayi shi
ya sanyata daga kai tana dubanta zuciyarta cike da tambaya. A sanyaye taga amna din
ta dawo tana zama gefanta

"Lafiyarki ke kuma?" Ta tambayeta tana nazartarta da kyau

"Wani abu na gani anni a gidan hamma". Jin an ambaci fu'ad din ya sanyata tattara
hankalinta akanta

"Me kenan?" Ta amsawa amnan cikin zuciyarta tana fatan ba wata matsala bace a
tsakaninsu.

"Anni.....me aikin gidan maamah na gani,ita da wata budurwa......bansan budurwar ba
amma tana kama da wannan qawar maamah din aminiyarta dinnan....."

".....hajja harira" Anni ta samu kanta da fada ba tare data shirya ba

"Eh ita" Ajiyar zuciya anni ta fesar

"To shine me amna?" Ta furta cikin hikima. Tun asalin tarbiyya anni irin matannan
ne da basa bari yaro yana kawo musu hira ko maganar wani guri. Qasa amna tayi da
idonta

"Ba komai,kawai anni ji nayi jikina bai aminta dasu ba,daga yanayinsu fa anni kamar
a gidan zasu kwana fa,qilan ma komawa gidan sukayi Allah anni". Ta fada tana bata
rai. Da kallo tabi amnan,amna din ba yarinya ce qanqanuwa har can can ba,kome ake
ciki ko yake faruwa tabbas dole tana gani tana kuma fahimta.

"Hammanku majibancin lamura da jama'a ne,bazai zama abun mamaki ba idan anga sabbi
ko baqin fuska a gidansa ba,kedai kici gaba da taya dukka 'yan uwanki da addu'a".
Kai kawai amna ta gyada ba tare data samu cikakkiyar gamsuwa da bayanin anni ba,ta
miqe tana fita daga dakin kamar yadda tayi niyya da farko.

Fitar amna dukka sai hankalinta ya dawo jikinta,sam sam taji bata gamsu
da wanzuwar zuwaira da waccar yarinyar a gidan ba. Tasan wacece maamah,tasan kuma
dukkanin wanda ya rabu da ita yaya dabi'arsa zata iya kasancewa. Indai da wata
manufa ko wani qullin daban aran maamah din,muddin tana raye ba zata taba bari
haqarta ta cimma ruwa ba. Koda ta dauke idanu akan abubuwa da yawa,koda tayi
kawaici akan abubuwa masu yawa....amma a nan ba zata bari ba,ba zata bari tabi
fu'ad har rayuwa cikin gidansa ta ruguzata ba. Saita jawo wayarta tana qoqarin
danna kiran.


*SABREEN*

Batasan adadin sau nawa ta leqa dining din ba da zummar ganin ko ta
samu nasara ya taba kayan abincin?. Saidai a duk gewayen da zatayi bataga wani
alamun taba komai ba cikin kayan dake danqare a table din ba.

Ba iya yaci abincin bane kawai damuwarta ba aah......tanaso tayi amfani
da wannan damar ta karbi wayarta a hannunsa,tanaso duk yadda za'a yi ta samu
cikakken bayanin yadda su hudan suka koma qarqashin kulawa da mulkin maamah. Abun
yana tsananin daure mata kai......ta yarda da momma bahijja....ta kumayi imanin
haka siddan ba zata bari haka ta faru ba,duk dadai ma batasan ainihin wacece maamah
din ba. Sam bata sako kawu rufai a ciki,shikam tasan ko ya fita sanin wacece mariya
to zai aikata fiye da hakan ma.

Zuwa sha daya na dare haqurinta ya gaza,ta miqe da wani irin kaiwa
maqurar haquri tana yafa mayafinta saman doguwar rigar jikinta ba tare data buqaci
dankwali ba ta sanya slippers dinta tana bude qofar dakin ta fice.
Kamar magen dake kwanton farautar kamun bera haka ta dinga tafiya a
hankali tana durfafar stair case din dake facing dinta. Duk taku daya sai bugun
zuciyarta ya qaru,amma kuma tuna huda nadra da haneefa kadai ke qara mata qwarin
gwiwa.

Tana jin a kansu zata iya komai,zata kuma fuskanta da tunkarar komai
da kowa.

Cak ta tsaya a stairs din farko tana jin kaman wanda ke kusa sosai da
ita idan ya qurawa qirjinta idanu zai iya ganin yadda zuciyarta ke bugawa ma.

"Shi waye?,mutum ne kamar kowa,mutum ne kamar ni,bashi da wuta bashi da aljanna,bai
isa kuma ya yankani ya cinye namana ba" Ta gayawa kanta da kanta murya can qasa
qasa dukka tana zaton BUGUN ZUCIYARTA zai daidaita. Aqalla ta tsaya jiran mintuna
kusan goma amma still ba abinda ya canza,sai kawai ta runtse idanunta ta kama
makarin stairs din ta fara haurawa saman da wani irin confidence da batasan daga
inda ta aro shi ba.

Idan ba jikinta da hancinta ne ya mata qarya ba,to tabbas atmosphere da
weather na wajen daban yake dana kowanne bangare na gidan. Wani irin lullumsan
yanayi da wani irin kebantaccen qamshi da bata taba jin makamancinsa ba. Bata taba
lura da cewa shimfidadden carpet bane kan stairs din sai a yanzun da qafafunta ke
barazanar nutsewa a cikinsa. Bayan qafafunta sun nutse din kuma wani irin sassanyan
yanayi tafukan qafarta ke riska a can cikin carpet din. Duk yadda taso jure
qauyancinta amma abun yafi qarfinta,dole ta dinga bin carpet din da kallo har zuwa
sanda ta riski wata pivot door wadda gefe da gefanta duka glass ne da bazaka iya
hango ainihin parlor din ba,yayin da daga tsakiya ta kasance ta gogagen katako da
aka yima design na zamani wanda ya maidata smart door. Tun daga zubin qofar tasan
wajene na musamman kuma kebantacce,ta bangare guda kuma taji dadin samun qofar a
bude,banda haka da sai tayi tsaiwar da qofar zata gama tantance wace kafin ta bata
daman shiga parlor din.

Mutum ne shi me wani irin jiki wanda baya qaunar zafi tun asali,saidai
duk da hakan tsananin kare lafiyarsa ya sanya bai fiya kwararawa kansa A.c ba. Duk
wanda ya sanshi ya sanshi da wannan dabi'ar na kaucewa abubuwa masu sanyi ciki kuwa
harda ac din.

Zaune yake saman wata qawatacciyar minotti sofa qwaya biyu dake bayan
qwatattun Belgium sofas din da aka yiwa yalwataccen parlor din ado masu wani irin
design me daukan hankali. Daga bayan Belgium sofas din aka yi wani muhalli na daban
da aka zuba minotti sofas guda biyu wanda suke bashi daman kashingida ko miqe
qafafunsa a duk sanda yaso.

Dogayen qafafunsa na miqe saman sofa din,yayin da night shirt dinsa
ke ajiye a gefe,daga shi sai gajeran wandon rigar wanda iyakacinsa cinyoyinsa.
Hakan ya bayyana zallar halittar fararen cinyoyinsa dake lullube da baqa sidik din
gargasa. Madaidaiciyar Ac ke kadawa cikin dakin,wadda ba lallai yanayin sanyin ya
sanya ka fahimci itace ba saboda glass door din dake hannun hagu na falon da yake a
bude,tatacciya iska me kyau dake tasowa daga jikin tsirran da aka qawata wajen dasu
tana busowa zuwa cikin falon. Tattacciyar iskar data sanya masa kasala da mutuwar
jiki,duk karsashin aikin da yakeyi ya soma raguwa.

Turo qofar da akayi shi ya sanyashi dauke idanunsa daga karanta saqon
da William ya tura masa ta email da suke buqatar ya duba da kyau ya karanta ya kuma
sanya hannu.

Fes yake ganin fuskarta wadda ke tsaye daga bakin qofar,fuskar data
bayyana tsakanin lullubin mayafinta wanda yadan zame baya kadan ya bawa
kwantacciyar sumar dake gaban goshinta daman bayyana sosai. Fararen idanunta da
suke da wani irin haske ta zube a kansa wani abu na dukan zuciyarta saboda yadda ta
sameshi.

Ba wani abu da gajeran wandon jikinsa ya suturta sai qasan cibiyarsa
zuwa cinyarsa,don bai samu daman qarasawa gwiwarsa bama sam. Ginannen jikin nasa
daya samu kulawa ta kowanne fanni,motsa jiki,tsananin tsafta da kuma cima me kyau.
Kwantaccen gashin dake cike da qirjinsa shi ya zamewa faffadan qirijinsa tamkar
adon baqin abu bisa farin yanki ko farar takarda. Wani irin kwantaccen gashi daya
shirya kansa da wani irin siririn layi har zuwa cibiyarsa ya zarce har qasa.

Har cikin jikinta taji rudewa sosai,don wani abune da tsahon
rayuwarta bata taba gani ba,hakazalika bata taba hasashen zata shigo ta sameshi a
haka ba. Cikin zafin nama ta juya da niyyar komawa inda ta fito,don batajin zata
iya ci gaba da daurewa kallon wannan halittar tasa. Da nasa salon hanzarin da kuma
son qurewa rashin kunyarta tare da qoqarin fuskantar wani abu daga gareta ya dauki
remote na qofan ya dannan close,take ta rufe kanta da wata irin gaggawa kamar
qiftawar ido. Cak ta tsaya zuciyarta na bugawa sosai,tsoro yanaso ya kamata Amma
kuma wannan dakakkiyar zuciyar ta taso mata,taji a ranta cewa idanma ta juya ta
fita ta nuna masa ta damu dashi kenan ta kuma damu da wanzuwarsa a haka.

Nasa idanun ya janye daga kanta yana hade ransa tsam waje daya. Duk
da kallon data masa bai wuce na second biyar ba amma ya fahimci lallai ta qarewa
jikinsa kallo.

Hannu ya miqa gefansa ya jawo night shirt dinsa ya zura,sai ya koma ya
jingina da fuskar minotti sofa din yana ci gaba scrolling saqon yana dubawa.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 34

_Daga hassan dan sumra R A yace,daga manzan Allah S A W yace:Duk macen da waliyyai
biyu suka aurar da ita ga maza mabanbanta a lokaci guda,to ita din mallakin na
farkon ce(wanda aka fara daura mata aure dashi)_


34


Minti daya biyu uku har zuwa biyar bataji motsin komai ba,wannan ya sanya
tayi tsammanin yabar falon ne,don haka ta juyo a hankali tana sake zube idanunta a
wajen da yake. Haushi takaici da bacin rai suka hadu suka lullubeta ganin aikinsa
yake hankali kwance,sai ta gyara tsaiwarta sosai tana fuskantarsa ganin ya lullube
wannan faffadan qirjin nasa,wannan ya dan rage mata kaifin abinda takeji,duk da
cewa cinyoyinsa dake a waje nason sakata a razani da tsoro.

Rasa ta yadda zatayi calling attention dinsa tayi,sai ta danyi
gyaran murya kadan cikin qufula da fusata. Minti guda kaman baisan tana wajen ba
kafin ya motsa,ya daga kansa da idanunsa daga kan hasken system din yana zubesu a
kanta da wani irin kallo na qurilla. Karo na farko yadda ya tsareta da ido taji
kaman yanaso yayi mata nauyi,jajayen lips dinsa hasken fararen qwayar idanunsa wani
abu ne da bata taba gani wajen wani d'a namiji ba sai a kansa,akan nasa ma a yau
data masa kallo itama nakai tsaye.

"Wayoyina nazo karba saboda ina da buqatarsu....... Akwai mutane masu muhimmanci a
rayuwata da nake da buqatar na dinga magana dasu" Ta fada tana tsuke girarta da
kyau tana kuma tura dan qaramin bakinta gaba wanda sam batasan ma tanayi ba,saboda
zuciyarta cike take da haushi. A hankali ya sauke idanunsa zuwa saman qaramin bakin
nata data tattara lips dinta duka ta turasu gaba. Wasu irin siraran lips da sai
kayi tsammanin jambaki ta shafa musu. Tsigar jikinsa ta zuba kadan saboda bayyanar
daya daga cikin abinda ke burgeshi a jikin mace yake kuma lissafin ya sameshi
kenan,wato cute lips masu nau'in light pink ko red me haske irin nasa.

"A hakar kamar cikakkiyar mace" Ya fada qasan ransa yana jan tsakin da baisan ma ya
fito sarari ba. A duk lokacin da zai kalleta sake raina shekarunta yakeyi,hakanan a
duk sanda zaya kalletan sai mamaki ya sake cikashi game da yadda ta samu cikakkiyar
shaida da certificate din zama KARUWA. shi kam gaba daya ma baisan me yahau kan
mazajen dake mu'amala da ita ba,a bisa qa'ida da yanayin halittarsa ta masa yarinta
da yawa. Yanason macen daya tabbatar zata iya dauke lalurarsa komai girmanta,ire
iren sabreen din guda goma yana ganin yafi qarfinsu nesa ba kusa ba,baima san
abinda mazajen da ta dinga tatsewa me suke tsammanin samu haka daga gareta ba da
har ta samu tasirin gusar musu da hankali.

"Labari kike bani?.....ko tambaya kike?,ko daukan excuse?" Yayi maganar a nutse
yana dage mata dukka girarsa guda biyun bayan ya dora qafarsa daya saman daya,ya
kuma yi relaxing jikin makarin sofa din.

Duk sai ta ji ya muzantata,akanme zai dinga mata tambaya akan abinda
ya gama fahimtar inda ta dosa?. Tsaiwarta tadan gyara tanason hana kanta jin nauyin
idanuwanta.

"Amma dai cikin zamanmu ba sharadin tabamin waya.....wayata sirrina ne,bana tunanin
akwai abinda ya shafeka a ciki" Ido ya zuba mata kamar bazaiyi magana ba,yanaso
yaci gaba da karantar bayan karatun da yayi mata na binciken da yayi a kanta. Ya
fuskanci akwai burbishi da tasirin rashin kunya tattare da ita. Yarinyar da ko
saddiq ba sa'anta bane ballanta musaddiq ko farouq.....amma tana da zarrar tsaiwa
ta fadi mishi magana yadda takeso. Wannan wani abune da ba wata diya mace data iya
fuskantarsa dashi....kai koda dan uwansa namiji yana matuqar shakkar hakan.

Please Login or Register in order to submit comment