You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tausayi sabreen din take bawa Dr mubeena,tako wacce fuska ta kalleta
tausayi take bata. Hannu ta miqa ta dauki abun gwajin BP din data gama gwada mata
ta riqe a hannunta,tadan sakar mata murmushi wanda sabreen qarfin hali kawai tayi
ta maida mata.

"Kiyi bacci sosai Mrs jadda......fi amanillah.....in sha Allah boss yana cikin
aminci,Allah baya bari bayinsa na gari su wulaqanta kosu tozarta ko su wofanta" DR
mubeena ta fada cikin kwantar mata da hankali. Murmushi ta tattaro da qyar ta samu
ta maida mata martani,Dr mubeena ta kalli anni dake zaune gaban gadon kaman ko
wanne dare tana riqe da tasbaharta.

"Yau ba checking din dare,BP dinta ya kusa dawowa daidai da yadda nake buqata,kuyi
baccinku,idan Allah ya kaimu qarfe shida ko biyar da rabi zan shigo". Ta fada cikin
girmamawa itama tana jin alhini har cikin qasusuwanta na rashin labarin komai akan
fu'ad din. Murmushi kadan anni tayi tana sauke qafafunta daga saman kujerar,yau
momma ta dage lallai a bawa anni 'yar tayin kwana ko huda ko ma'u. Ta karbi ma'u
saboda ta matsanta dole gobe su wuce mali huda taje tayi ton print dinta duk da a
goben zasu rufe.

"Sannunku da qoqari kuma,Allah yayi muku albarka"

"Ameen,Allah ya qara lafiya saida safe" Tayi musu sallama tana fita daga dakin.
Idanunta a lumshe suke kawai,ita kadai tasan me yake yawo tsakanin
qirjinta da zuciyarta,a duk sanda kwanyarta zata harba da lafazin.

"Sun harbeshi.....ba'asan inda suke ba!" Sai taji kaman zata mutu......sai taji
kaman ba wata tazara tsakaninta da tashin alqiyamarta. Takanji faruwar komai kamar
a mafarki.....daddadan farinciki da wata iriyar tsaftatacciyar kulawa tana shirin
rikida zuwa tashin hankali da firgici.....wannan kusancin tashin farko ya juye ya
koma kewa da tsananin buqatar makusanci izuwa zuciyarta.

Duk dare kafin alluranta su dauketa zuwa duniyar bacci.....duniyar
dasu Dr mubeena suka matsanta mata zuwanta badon son ranta ba.....sai rayuwarsu
tsakanin Maldives da madeena tayita dawo mata tamkar a faifan CD,takanji inda ana
maida hannun agogo baya tabbas data maida.......tabbas data hanasu dawowa nigeri da
tana da masaniyar ibtila'in da zai fada musu kenan.

Tun tana iya jin muryar anni da ma'u sama sama har ta daina ji,ganinta
da ruhinta suka koma zuwa ga wanda ya yisu nadan wucin gadi.

Shuru da anni taji ma'u tayi shi ya bata tabbacin bacci yayi awon
gaba da ita,saita gyara zamanta saman kujerar tana ci gaba da jan
tasbaharta,tunanuka kala daban daban suna hana idanunta tafiya duniyar barawo wato
bacci da itadinma duk dare satarta yakeyi,bata kuma fiya dogon zango ba yake
sakinta,takan farka da mafarki ki razani duk dare,saidai ko sau daya bata taba
farkawa ba ba tare da ambaton hasbunallanu wani'imal wakeel a bakinta ba.

Batasan baccin yayi awan gaba da ita ba,har tasbhar hannunta ta
sulale ta fadi da hasbunallanu wani'imal wakeel data kasance ta qarshe a harshenta.

Dukkanin daukacin asibitin harda dakin ya dauki shuru,dare ya fara
nutsawa awanni suna gudu......a irin lokacin da bayinsa nagartattu ke neman kusanci
dashi saman darduma,ashararan mutane kuma suma ke nasu aikin saboda neman duniya da
abinda yake cikinta.

Daya daga cikinsu ta samu nasarar kunnowa dakin,ta murda handle din a
hankali cikin sanda. Sanye da suturarta ta dazu,suturar qarshe data shigo dakin
dasu babu abinda ya canza,daidai da takalminta da kuma dan qaramin hijabin
kanta,saidai a yanzu akwai baqin face mask saman fuskarta koma bayan dazu.

Kai tsaye ta wuce parlor din ta kuma tunkari dakin da sabreen ke
kwance,ta saka hannu ta bude qofar dakin tana shiga. Daga bakin qofa ta tsaya,ta
qarewa kowa kallo,ta kuma tabbatar dukkansu sunyi nisa a baccinsu. Ajiyar zuciya ta
saki hakan yana bata nutsuwa da kuma qwarin gwiwar aiwatar da abinda ya shigo da
ita,taci gaba da matsawa zuwa gadon da sabreen ke a kwance.

Daidai inda ruwan dake saqale a hannunta ta isa,ta tsaya ta zuba
masa idanu. Bisa qa'ida ruwan yake diga kaman yadda ya dace,aiki biyu zatayi a
ciki,ta gaurayashi da sinadarin dake aljihun rigarta,ta kuma qara gudun ruwan dake
shiga sassan jikinta,wannan shi zai saurin hautsina tsarin jikinta,ya kuma
taimakawa sinadarin wajen yin aiki a jikinta da gaggawa.

To amma ta wani bangaren tafison ta fara tabbatar da inda wayar
take......wayar itace babban burinta na farko,wanda iya ita kawai idan ta mallaka
kaman yadda akayi mata alqawari ya isheta kudin aikinta koda ba'a qara mata komai
ba.

Ta tsakanin annin da sabreen ta wuce tana miqa hannunta locker gefen
gadon,durqusawa tayi ta soma binciketa a hankali. Sai data hautsine komai bata
ganta ba,wannan ya qara gudun jinin jikinta energy dinta ya qaru fiye da yadda ya
kamata ya kasance. Tana bala'in son wayar,don itace cikar burinta. Miqewa tsam tayi
ta sake wucewa ta tsakaninsu,hannunta gefe da gefen sabreen din ta soma lalubawa ko
a nan ta ajiyeta.

Kaman wadda aka tasa ta dinga jin wani sauyin yanayi tattare da ita
tamkar wadda aka canzawa muhalli daga wanda take ciki,jin hannu ta gefan kafadarta
ya sanyata murmurewa daga yanayin bacci zuwa rayuwar zahiri. Baqon turaren da
takeji a hancinta ya sanyata budewa idanunta qanqanuwar qofa da zata iya ganin
wanda waye haka keda kusanci sosai a kusa da ita?.

Dr mubeena kamar take gani,amma kuma qamshin da yanayin nutsuwar sam
ba ita bace......saidai a idanu a kallon dake a fusge tabbas Dr mubeena ce.

Tabo wayar da hannunta yayi ya sakata sakin ajiyar zuciya,ta saka
hannu ta jawota ta jefata aljihun lab coat din jikinta,sannan ta fiddo hannun da
syringe da wani irin ruwa a wata mitsitsiyar roba.

Tas ta soma zuqe ruwan a syringe din,wanda tana dab da kammalawa
anni ta motsa bakinta dauke da HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKIL Tana shafa fuskarta da
tafin hannunta.

Fitar hasbunallahu din ya daki qirjinta,ya kuma sabbaba mata faduwar
allurar dama robar ruwan,abinda ya sake sakawa sabreen matuqar ankara da ita,ta
sunkuya da sauri ta dauki syringe din qirjinta yana dokawa.

Idanu anni ta zuba mata a mamakance,duk da ta juya mata baya bata iya
ganin fuskarta. Mamakin yadda suka canza tsari ne na Shigowar likita dakin mara
lafiya haka kai tsaye?.

Kaman Dr mubeena take gani......amma kuma abun da mamaki,Dr mubeena da
ta musu sallama sai bayan sallar asuba?,me ya dawo da ita?,kuma ta shigo dakin ba
tare da sanin kowa ba?.

"Dr akwai allurar data rage ne?" Kai ta gyada mata kawai tana qoqarin qarasa zuqe
ruwan a syringe din a gaggauce don ta qarasa cika aikinta.

Hakan bata samu ba kuwa,don hannu sabreen takai mata cikin shammata ta
daki hannunta,da syringe din da ruwan sukayi gefe suka watse,abinda ya darsa wani
abu da gaggawa a zuciyar anni,ta miqe sa wani irin zafin nama ta damqo kafadarta
tana juyo da ita.

Kallon kallo suka yiwa junansu,tana shirin kubcewa anni,annin ta saka
hannu ta yage face mask din fuskarta ta.

Baquwar fuska ce da bata santa ba.....kaman yadda ya bayyana fuskar bata
Dr mubeena bace.

"Wacece ke?!" Tambayar da anni ta mata cikin madaukakim sautin tsawa daya qarasa
farkar da ma'u ta miqe ta zauna sosai ta yunqura ta tashi.

Kai matar ta girgiza,ta juya da gaggawa tana nufar qofa,saidai tuni
ma'u ta rigata isa qofar ta danneta ta kulle ta zare key din.

Raba dubanta take kan fuskar anni tana zaro ido waje,hankalinta ya
soma tashi tana tunanin girman hadarin da zata shiga muddin ta bari taje hannu.

"Kiban hanya na fita ko kuma na illataku!" Ta fada da wata gurbatacciyar hausa da
zata baka tabbacin wani yaren ce daban ba cikakkiyar bahaushiya ba.

Daga annin har matar ba wanda ya zaci haka,saukar kakkauran plastic
plate din da sukaci abinc dashi dazu ma'u ta sauke mata a tsakiyar kai,sai gata ta
zube qasa warwas zubewar data sanya wayar sabreen silalowa daga aljihunta.

A hankali sabreen data sauko daga gadon ta dauki wayar tana
juyata,iya daukar wayar kawai ta bata kowacce irin amsa da take buqata koda matar
batace komai ba.

Matsawa anni tayi da hanzari tana kiran security emergency line cikin
qasa da minti daya sai gasu sun bayyana a dakin.

Kiran security din ya tayar da kusan duk wani security alert na
asibitin,kasancewar dakin babban daki ne,yana cikin VIP rooms da asibitin yake
dasu.

Cikin qanqanin lokaci qofar dakin ya cika da security da wadanda ihun
security alert din ya tashesu. Kusan kowa yasan wacece a dakin a cikinsu,suna da
masaniyar mahaifiyar wace a dakin,don haka fitar security alert daga dakin ya
zamana kaman tashin hankali a wajen kowa.

Sanda chief of security service na asibitin ya shigo dakin yana neman
ba'asin abinda ya faru ya girgiza. Cikin matuqar tsoro da kuma kaduwa ya shiga bawa
anni haquri.

"Am sorry maaa.....muna dukkan iyawarmu wajen bawa madam tsaro,bamusan ya haka ta
faru ba.....amma ni da kaina banyi minti talatin da shiga office ba bayan ba gama
zagaye na tabbatar kowa yana kan aikinsa,hatta shige da fice na asibitin nan tun
bayan faruwan abun muka sake saka ido akai....amma zamu duba in sha Allah,zamu kuma
binciketa har sai mun tabbatar daga ina take?,meye kuma ya shigo da ita
dakin......muna masu bada haquri". Kai kawai anni ke jinjinawa tana duban matar
wadda tuni ta jiqe da fitsari,ainihin mummunar suffarta dukka ta fito saboda yadda
tayi wurjanjan da kuka da tsananin tashin hankali. Haquri kawai take bayarwa
hannuwanta a sama kaman me addu'a. A haka suka jata suka fice da ita,sabreen ta
koma gefan gadonta ta zauna kawai rungume da hannayenta kanta yana cakudewa.

Dr mubeena ta qaraso inda allurar da robar suka fadi ta sanya hand
gloves ta daukesu,har yanxu ita kanta a tsorace take jikinta kuma rawa yake. Mamaki
ne yake qara kasheta na yadda akayi amfani da kamanninta da komai nata aka shigo
dakin za'a cutar da iyalin jadda.

"Zanje dashi lab mu gwada muga meye ma taso zuba mata cikin drip din". Dr mubeena
ta fada tana duban securities din guda biyu da suka rage a dakin. Juyawa tayi ta
kalli anni da sabreen.

"Ku kwantar da hankalinku,babu abinda zai faru in sha Allah,zasu dan xauna kadan
daku kafin daga waje kafin security dinku na gida su iso....don anyi alerting nasu
abinda yake faruwa".

"Sannu Dr" Kawai anni ta iya fadi Dr mubeena ta juya ta fice da sauri Dr kamal da
yake on duty yabi bayanta abun shima yana girgizashi. Case ne da makamancinsa bai
taba faruwa cikin asibitin ba,sai gashi yau yana shirin faruwa akan matar mutum
mafi girma da kima cikin idanunsu banda Allah ya kiyaye.

Ajiyar zuciya me nauyi sabreen ta sauke tana dora hannunta saman
cikinta a hankali. Wat qqqarfar soyayyar abinda take dauke dashi ya ratsa mata
zuciya irin wadda bata taba ji ba,wato tako ta ina farautar rayuwarsu akeyi?,so ake
a salwantar dasu gaba daya?,kowa rayuwarsu ta tsone masa idanu ta kowacce fuska?.

"Nayi alqawarin baku kulawa da dukkanin qarfina da kuma iyawata.....nayi alqawarin
kula daku har zuwa sanda zaku taka doron qasa......da ran mahaifinku ko babu.....da
kulawarsa ko babu......zamu zame masa madubi kuma ababen alfahari in sha Allah"
Tayi maganar ita daya tana sakejin kaman wata sabuwar alaqa na qulluwa tsakaninta
da abinda ke cikinta da batasan meyeshi ba.

Batasan hawaye takeyi ba saida muryar anni ta ratsata.

"Ki rage damuwa da gaske sabreen ko don diyoyin cikin ki.....karki cutar
dasu....Allah shike riqe da kowanne bawa yake bashi kariya....musamman idan ka
sallama masa ka kuma miqa masa al'amarinka". Tayi maganar a tausashe tana goge mata
damshin fuskarta.

Ba wanda ya iy komawa bacci,abinda ya sanyata yanke shawarar yin
alwala,ta daura alwalar ma'u ta shimfida mata abun sallah. Ta jima tana kaiwa Allah
kokenta wanda tayi Imani shine sarki guda daya da baya maida hannun bawansa ba tare
da ya amsa addu'arsa ba. Sanda ta idar tana zaune kanta a qasa,tana jin tattaunawar
guards din fuad daga parlor din dakin. Kusan kowannensu zuciyarsa a kusa
take,muryar abdulgafar ce ta qarshe.

"Daga yau koda wasa ba wanda zai sake gigin zuwa kusa da inda take ma......daga
gobe zuwa jibi ko da numfashinmu da jinin jikinmu zai qare sai mun lalubo duk inda
oga yake,a cikin qasar nan ko africa ko a wacce nahiya ta duniya ma".

Numfashi ta sauke a hankali,ta jawo wayarta tana lalubo number
musaddiq. Dole ta fara taba mata nutsuwa kaman yadda tayi musu,dole ta taba
kwanciyar hankalinta ko yaya ne,saboda itama tasan kifi na ganinka me jar koma.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 123


123


Cikin qasa da awa daya ta gama turawa saddiq komai da komai da take
buqata,sannan ta sauka tana lalubo rubutaccen qur'ani dake kan wayarta.

Ko yaya ne tanaso ta karanta ko zata samu sassaucin zugi da radadin da
zuciyarta take mata,don ta dade da fahimtar babu wani abu dake bawa jiki da zuciya
nutsuwa irin karatun alqur'anin.


β˜…Zuwa sanda gari ya qarasa haske abba ya iso,already su musaddiq dama tun
cikin daren suka qaraso,saidai da safen musaddiq yadan fita sannan ya dawo.

Dr mubeena ta shigo da sakamakon gwajin,a sannan sabreen din tana
zaune ana gyara mata cannula dinta data goce. Idanunta a runtse tana jin radadin
yadda ake luguiguta qarfen allurar cikin Jikinta.
"Guba tayi attempting zuba mata.....wadda take bin jiki a hankali ta lalata kowanne
organ na jikin dan adam......alhmdlh da ubangiji bai bata nasara ba......inda hakan
ya faru to fa da saidai addu'a kawai....poison ne da bashi da magani a nan qasar ko
makari kwata kwata". Kai kawai sabreen ke gyadawa tana sake girmama rashin imani da
rashin tausayi irin na wanda ya dauki nauyin abun. Zuciyarta tayi wani mugun
karyewa fu'ad jadda yana fado mata. Allah ne kadai yasan a wanne yanayi yake a
yanzu?,a wanne irin hali yake?.

Da sassarfa take saukowa daga saman nata kaman zata hada matakala
bibbiyu. Duk sanda taga kiransa tasan tabbas lamari ya baci,ba kasafai take
sanyashi ayyuka ba.....ba kuma kowanne lokaci bane take bashi aiki na sai aikin
daya kasance babba.

Yana tsaye tsakiyar falon,hannunsa goye a bayansa yayin da idanunsa ke
lullube da baqin gilashi.

"Me ya faru?,ya ake ciki?". Baqin hannunsa ya saka yana cire glass din nasa,bakinsa
da yake baqiqqirin ya motsa.

"Aiki ya baci,kuma komai na iya faruwa saboda ta fado hannu a sanda kowa yake abun
zargi ne". Hannuwa bibbiyu ta sanya yana dafe qirjinta dake wani irin buga
mata,duka idanunta a warwaje tana jin tashin hankali yana zagayata.

Wannan shine aiki na qarshe da take sanya ran samun nasara a kanshi,aiki
na qarshe da take da kyakkyawan fata da hasashen indai ya tafi daidai ta gama da
matsala daya cikin matsalolin rayuwarta guda uku,aikin data kwana jiya batayi bacci
ba tana jiran jin kyakkyawan sakamako a kansa.

"Waye ka bawa aikin?,ina fatan sunana bazai fito ba?" Ta tambayeshi zufa tana yanko
mata tana jin kan an mata wanka da ruwan zafi. Kai ya girgiza yana dubanta.

"Ko sunan wanda na bawa aikin bazai fita ba bare sunanki bare nawa,don da kika bada
aikin na bawa wani shima ya bawa wani shima wancan wani ya bawa sannan aka bawa
yarinyar......nasan yarinyar amma ban bata aiki kai tsaye ba saboda gudun qwacewar
rana irin wannan......amma.abinda yafi bani mamaki,itadin expert ce,bata taba
missing target ba tunda ta fara aiwatar da irin wadannan ayyukan sai yau ta
silarki" Yayi maganar abun yana tsananin bashi mamaki na yadda ta fadi warwas a
qaramin aiki irin wannan.

Ajiyar zuciya ta sauke,ita komai ba damuwarta bane......kama
yarinyar ko tsallakewarta,nata damuwar shine samun tabbacin nata kubutar da kuma
tsiran.

Kujera ta samu ta zauna tana juya tambayarsa. Me yasa rashin nasarar
yarinyar da faduwarta bai tashi afka mata ba sai da aiki yazo kansu?. Tambayar data
kasa samun amsarta kenan,saidai kawai ta sakawa ranta akwai wani boyayyen abu na
daban da sabreen din ke amfani dashi.

"Labari na gaba" Ya fada yana fiddo jaridar dake hannunsa. Kamfanin jaridar yafi
kowanne kamfani fidda adadin jaridu siyar dasu da cinikinsu,saboda yafi kowanne
gidan jarida fidda labarai latest masu daukan hankali,labarai na gaske da suke
daukan hankali tsakanin kwanaki da makonni.

Hannu ta saka ta karba tana dan mita,saboda a yanzun ba abinda tafi
buqata irin ya barta ta zauna tayi nazarin hasarar data sake fada mata. Kudade masu
ciwo ta biya don wanzuwar aikin,sai data siyar da bangles dinta na gold sannan ta
biyashi kudin aikin.
Wareta tayi tana mita a ranta,saidai bata samu sukunin sauke mitar
ba tafkeken hoton farko daya mamaye jaridar ya dauki hankalinta.

Hoto ne da alamu suke nuna daga cikin video aka ciroshi,fuskar hajja
sosai ya fita,yayin da ita dake gefen hajjan kwata kwata fuskarta bata fita ba bata
kuma nuna ba.

Bata sani ba.......ta gurin bugun jaridar aka samu akasi tayi damage?
ko kuma ana sane aka lalata gurin?.

Kayan dake jikinta a jikin hoton tabi da kallo,sune dai......sune dai
wadannan kayan data sanyasu a ranar da zasuje gidansu sabreen zuwa na
farko......gabanta yayi wani mahaukacin faduwa sanda wani abu ya darsu a ranta.

"Na shiga uku?!,me zan gani wannan?" Ta tambayi kanta da kanta hannuwanta suka
dauki rawa,da wani irin sauri ta maida dubanta saman manyan rubutun da suke saman
newspaper din da aka yisu in bold style yadda zai dauki hankalin harda na nesa.

_CIKIN WADANDA AKE ZARGI KENAN DA SACE SHARARREN ATTAJIRIN KASUWAR GOLD DA DIAMOND
KENAN MUHAMMAD JADDA_

Dukka hannunta suka dauki rawa,wata kidima ta saukar mata,ta dubeshi
gumi yana sake tsatstsafo mata,yau itace buge cikin calendar da sunan wadda ake
tuhuma da satar d'anta?,ba wanda zai aikata wannan sai yarinyar.....don kuwa ita
daya take videos din ta tabbatar. Kamar wadda kuka zai qwacewa cikin rawar murya da
qwacewa dukkan wani hanzari daga gareta tace.

"Yaushe aka buga wannan labarin?,har ina kuma labarin yakai?". Gyara tsaiwarsa yayi
da fuskarsa da bata nuna wanzuwar imani a zuciyarsa ko kadan yace.

"Tun da sassafe....nima a teburin me shayi naga wani yana karantawa,sai naga kaman
nasan fuskar,koda na duba sai naga fuskar hajja harira ce.....wannan ta kusa da ita
dince dai ba'a gane fuskartata". Wata gauruwa ajiyar zuciya ta sake,tabbas zai
wahala a gane fuskartata,amma ga wanda yayi mata farin sani hakan bazai bashi
wahala ba sam.

Qarar wayarta ya sanyata zabura tana dubanta,don sam bata tsammanin
kiran wayar kowa a irin wannan lokacin. Hannu ta sanya ta dauka tana duba me
kiran,hajja harira ce,tayi kaman ba zata daga kiran ba amma sai taji tana buqatar
sanin waye.

Karata tayi a kunnenta,tana shirin yin sallama sai sallamar tata ta
maqale. Muryar hajja harira ce wadda ta fara da sauke mata zazzafan ashar.

"Ni zaki wulaqanta a duniya?,ni xaki toxarta mariya?,meye ban miki ba a
rayuwa?,saboda kin asircemin yarinya na miki shuru?,an gaya miki shuruna yana nufin
tsoro ne?,bakisan ja da baya ga rago ba tsoro bane shirin fada ne?,ni xaki buga a
jarida akan abinda bani da masaniya?,ke bakisan kuskure bane tarar fada da wanda
yasan sirrinka ba?,ganganci ne tarar rigima da wanda yasan waye kai ba?......to kin
tara kin samu....mu zuba,dani dake shege ka fasa,hoto na gaba idan kika tashi
tsirara zaki sakani......hukuma kuma ina nan ina dakon isowarta gidana,qarqari idan
sun kamani su kulleni......idan kuma ya tabbata bani ke da hannu ba dole su
sakeni". Daga haka hajja harira ta katse kiran.

Wani tashin hankalin na daban maamah taji yana sauko mata,har
numfashinta taji kaman yanason riqewa. Sam ba wani motsi data sakeyi akan hajja
harira saboda dalilai.guda biyu. Dalilim farko ita daya ce mutum guda daya data
mallaki sirrikanta ciki da bai,birnannun sirrikan da babu wanda ya sansu,babu wanda
yasan da zamansu sai ita din tak!. Dalili na biyu laila dake hannunta,tasan wannan
kadai ya isa ya zame mata daukan fansa game da cin amanar da hajja taso tayi
mata,to amma ko a yanzu ikirari da kurarin da hajja tayi mata bazaiyiwu ta barta
ba,don haka ta share gumin fuskarta ta soma tura mata gajeran saqo.

_"kiyi komai harira,bazan hanaki ba,amma kada ki manta a hannu kike,laila tana
gaidaki da kyau da kyau,tace kuma na gaya miki ki kula,ki kuma kula da kanki"_

Kamar jira shigar saqon yakeyi wani kiran ya sake shigo mata. Baquwar
number ce da haka kawai ta sanya gabanta faduwa,ta dinga bin number da kallo tana
raba daya biyu. Special number ce,simple da bata cika tarkacen lambobi da yawa
ba,ta jima tana kallonta kafin daga bisani dab da xata tsinke ta daga.

Karo na farko da muryarta kawai ta saukar mata da wani mummunan
faduwar gaba da bata taba jin irinsa ba.

"Ina fatan saqona ya riskeki zuwa yanzu?,idan ma bai iskeki ba to na tabbatar yana
dab da iskeki......somin tabi ne kenan wannan din.....iname sake aike miki da
gargadi.....ki nemo min mijina kuma uban 'ya'yana a duk inda kika kaishi.....ba
sassauci ba daga qafa.....idan nar yakai awa saba'in da hudu.......abinda zai faru
na gaba yafi qarfin wannan......yanzun ba irin wancan lokacin bane.....lokacin da
zaki zubdasu ki watsar dasu a duk inda kikaga dama,yanzun rayuwarsu gewaye take da
masoyansu......rayuwarsu gewaye take da rayukan dake buqatar su,suke da muhimmanci
a wajensu.....suke muradi da mararin ci gaba da wanzuwa tare dasu,da dadi ko ba
dadi.....da dukiya ko babu,da lafiya ko babu,saboda su din akeso.......zallar su
din ba abinda ke tattare dasu na ni'ima ba".

Har sai da maamah taji numfashinta ya sarqe guri daya da zafafan
maganganun data soka mata,to amma zuwa yanzun ko taqi ko taso tana ji a jikinta
itace a hannu,duk da tana ji nadan lokaci ne hakan zata kasance,sai maganan harira
da suka gama yanzu ta dawo mata.

_"Kuskure ne tarar fada da wanda yasan sirrinka.....yasan waye kai ciki da bai"_
tabbas a dazun kawai.harira ta bata wani darasi daua kamata ace kanta ya kawo
mata,amma ko banza a yanzun ma ta zamu wani ajiyayyen darasi da zai zame mata
makamin yaqi tsakanin ita hariran

Please Login or Register in order to submit comment