You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hayewa kan
gadon,burinta kawai taji jikinta saman gadon.

"Meye wannan?" Tambayarsa ta ratsa kunnuwanta gami da saukar wani abu a jikinta
sanda take shirin kwanciya.

Birkitacciyar fuskarsa ta kalla,yadda taga ya hautsine ya sanyata bin
abinda ya jeho din da kallo da sauri.

Tablet ne na family planning wanda har ansha rabinsa. Saita saka hannu
ta dauka gabanta yana wani irin bugawa,ta miqe da sauri da maganin a hannunta a
rude ta sauka daga saman gadon.

"Magani ne hamma......"

"Na tsarin iyali ko?!" Ya fada da wata gigitacciyar murya dake nuna tsananin fushin
dake sauka saman zuciyarsa.

"Eh hamma.....amma ka tsaya......"
"Na tsaya sabreen?,na tsaya kiyimin me?" Ya tambayeta qofofin hancinsa da jijiyoyin
kansa suna budewa.

"Na tsaya ki gayamin ke kika tsaida haihuwa hakanan tun daga kan iffa?,na tsaya ki
bani labarin yadda kika fara shan maganin planning?,ko na tsaya ki gayan kin gaji
da haihuwa?"

"Duka ba haka bane hamma!" Ta fada itama da muryar data dagu fiye da dazu.
Kalamansa gaba daya sun firgitata da wani irin tsoro,lafaxinsa gaba daya ya gama
rudata.....ya zaiyi hukunci irin haka?.

"Duka ba haka bane to yaya ne?,kin taba samun tazarar haihuwa irinta iffa?,ko kin
taba kaiwa haka?,shi yasa nayita tambaya ba bayani gamsashe?,ko shi yasa naketa
magana ke sam ba damuwa a lamarinki!!!" Ya qarasa fada da wata tsawa data sanyata
danne kunnuwanta tana fadin.

"Ya isa hamma!!" Ta fada da murya me qarfin gaske saboda tsoratar da tayi.

"Tsawa kikeso kiyimin?" Ya tambayeta yana nuna qirjinsa da yatsansa.

"Kiyi kome kikeso sabreen.......sonki da nakeyi ne ya jawomin......ki jani da duk
kalar abinda kikaga dama.....kiyi duk yadda kikeso!" Ya fada yana wurgar da daya
kwalin dake hannunsa a qasa.

"Karka qarayimin tsawa hamma" Ta fada tana jin fushi ya fara taso mata.

"Karka qara zargina akan abinda ba haka yake ba......idan ba haka ba..."

"Ba zaki yafe ba?".

"Basai na fada da bakina bama......na gaji hamma na gaji,wanne irin 'ya'yane ban
haifa maka ba?,wanne irin baiwa ce Allah bai mana ba na 'ya'ya,samun tazara
tsakanin haihuwa da wata haihuwar lallai sai ace sai ya zama daidai dana
baya!......ana yiwa Allah dole ne?,idan kuma yace gaba daya ka gama haihuwa fa?!"
Ta qarasa fada kuka yana qwace mata.

Wani malulun bacin rai ya taso ya saukar masa,donme zatace idan ya gama
haihuwa fa?.

"Ban gama haihuwa ba sabreen.......saidai idan kece zakiyi silar faruwar hakan"

"Eh nice din.....nice hamma" Ta fada itama a fusace cikin gajiya da jin bayanansa.

"Okay.....okay.......yanzu kika fitomin a mutum.....kin tabbatar min da abinda nake
zargi kenan".

" Ba zargi dama kakeyi ba.....kana cusamin laifin da bansan dashi ba......ko meye
kake tunanin na aikata na aikata hamma!" Ta fada da wani irin kuka.

"Don kin aikata sai me?,saboda kinga na damu dake?,saboda ina sonki.......saboda
kina ganin bazan iya rayuwa ba tare da ke ba?........idan na daina sonki shikenan?"
Ya fada da salon tambaya yana dage mata girarsa dukka biyun gami da bude idanunsa
da suka sauya launi.

Wani irin abu taji kaman an jibga mata a saman kanta.

"Kana zaton nima bazan iya rayuwa babu kai ba?,bazan iya rayuwa ba soyayyarka
ba?......ka daina sona din fine......sai me?" Ta fada da qarajin kuka. A gaggauce
ta juya ta fusgu hijabin data cire dazu ta maida,ta juya ko wayarta dake kuwwa bata
dauka ba illa jakarta data ajiye ta fice a dakin a gaggauce.

"Kiyita tafiya.....zan iya rayuwa nima ko babu ke" Ya fada a birkice kaman wanda
zai zauce.

Komawa yayi ya fada saman gadon yana jin wani irin bacin rai yana
saukar masa. Tayi masa laifi kuma sannan ta fishi fushi?,ya samu yara alhamdulillah
amma arziqin da Allah ya bashi yana jin yana buqatar qarin wasu......yanason ya
gina family din da aka jima ba'aga irinsa ba......yanaso ya gogewa maamah gorin
yawan haihuwar da tace asali dangin babanshi na dashi,haifarsu su biyu da tayi daga
jikin ubansu ne.

Wani irin duhu da qunci dakin yaji yayi masa,tsahon awa guda da wani
abu yana zaune guri daya batare daya ko motsa ba. Sake maida dubansa yayi ga sachet
din maganin,ya saka hannu ya daga yana sake karantawa sai yayi jifa dashi wanda kai
tsaye ya sauka a bakin qofa. Hannu bibbiyu ya saka ya dafe kansa yana jin yana wani
sara masa,yaushe sabreen ta fara sha?,wanne lokaci ta dauka tana sha?,kada ya
zamana ta illata mahaifarta fa?.

Juyi kawai ya dingayi tsahon awa uku,sai daga bisani a hankali
hankalinsa ya dawo gangar jikinsa,ya miqe ya shiga bandaki ya daura alwala. Saman
abun sallah ya zauna yana karanta wasu addu'o'i hadi da sunayen Allah,A hankali sai
yaji zuciyarsa tana saukowa tunaninsa yana daidaita.

Sannu sannu sai komai daya faru tsakaninsu ya dawo masa fes cikin
kanshi,wani sashe na zuciyarsa ya dinga masa zafi.

Kwanciya yayi niyyar yi kafin ayi kiran sallar asuba,amma sanda ya
isa gadon da zummar kwanciya sai maganarta ta fado masa.

"Hamma na gaji.....bacci nakeso nayi". A nutse ya sauka daga saman gadon,ya koma
saman kujera da nufin kwanciya,nan ma sai yaji ya kasa.

Da daya da daya ya dinga sauya guraren kwanciya amma ko ina ya sanya
kai sai yaji ya kasa,sannu a hankali ya fahimci zuciyarsa na neman 'yar uwarta
ne.....zuciyarsa na neman mahadinta. Duk yadda yaso ga kafewa wajen fita nemanta
amma sai zuciyar taqi bashi hadin kai,daga qarshe dai ya fahimci ba wata mafita da
yake da ita illa ya fita ya nemo duniyarsa.

Yana miqewa ana kiran sallar farko,don haka sai kawai yayi alwala,ya
zura riga ya sanya flipp flops dinsa ya murza qofar zai fita a dakin.

Farouq ya samu daga bakin qofar dakin

"Yauwa dude......dan yiwa adda magana please ta miqo maganin fannah,jiya ta manta
maganinta a jakarta duka biyun.....kasan ba'ason fashin shansa" Farouq yayi maganar
hankalinsa yana wani gurin bai bada hankali ga fuskar fu'ad ba.

Wani irin sanyi jikinsa yayi kaman an watsa masa ruwan qanqara,ya
juya gwiwarsa a sabule ya koma dakin ya hada kan magungunan ya bawa farouq. Sanda
farouq din ya wuce sai yaji kaman bazai iya sake taku ko guda daya ba,sai a sannan
tunaninsa ya dawo,fannah tana shan maganin planning saboda matsala da take da ita a
mahaifarta,dole take shan maganin sabida akwai buqatar ta huta sosai tsakanin
kowanne ciki.

Sam bai kawo hakan a ransa ba,ta yaya ma zaiyi tunanin maganin fannah
zai shigo jakar sabreen?.
Yana rangaji haka ya dinga takawa har yakai masallacin harami,daidai
lokacin da ake dab da tada sallar,yayi raka'atanil fajr yabi jam'i aka tayar da
sallar.

Koda aka idar zama yayi yayi addu'o'i sosai,yayi istigfari akan zato da
kuma yanke hukunci ba tare da bincike ba. Ya jima sannan ya miqe ya fara zagayawa
guraren da yasan tafi zama ko zai ganta,amma har ya gama zagayensa ya koma duba
guraren da ba wajen zamanta ba baiga koda me kama da ita ba.

Zuwa sanda rana ta fito ya gaji sosai,dole ta sanya ya koma masauki. Ya
samu yaran duka sun gama shiryawa,kowannensu kuma ummeensa yake da buqatar
gani,musamman su fauzan dake jiran fitowarta su duba gifts da suka samu kafin su
wuce harami.

Baisan amsar da zai basu ba,saidai kawai ya zauna cikinsu ya sadaukar
musu da wannan lokacin,amma dai duk da haka hankalinsu yana kan uwarsu.

Har azahar shuru bata ba dalilinta,ga anni na nemanta,maamah ma da bata
iya magana sosai sau uku tana tambayarsa.

Zuwa la'asar hankalinsa ya tashi,don masu neman nata suna qara yawa
ne,iffa ma dake da shekaru biyar neman ummenta takeyi bare sauran da suke da
hankali.

Ya kasa gayawa kowa abinda ya faru,yadai ce musu tana masallacine
kawai. Sannu a hankali hankalin anni yakai kai,saboda yaran da suka matsa da
qorafin taje ta dade a masallacin.

Zaman jiransa sukayi har yaran sukayi bacci bai shigo ba,yana can
yana dubata a ciki da wajen masallacin. Bai shigo ba sai daya baza masu duba masa
ita,wai ko madeena ta koma daya daga cikin gidajensa?,saidai acan dinma duka daya
ne bata koma ba ba wanda yaga gilmawarta.

Nigeria ya karkata kiran nasa,tsakanin abuja lagos da kano,can dimma
duka daya,don bata je musu ba.

"Innalillahi wa inna ilahi raji'un" Kawai shine abinda ya dinga maimaitawa,a
rayuwarsa wannan shine ainihin color din tashin hankali tsurarsa daya taba gani ido
bibbiyu.

Yana kallon wayarsa na ruri da numbers na anni da maamah,kowacce
kiranta yana katsewa na 'yar uwarta yake fadowa,amma ya gaza daga koda yatsansa ne
bare ya amsa musu.

A jikinsa yake jin bazai iya komawa masauki ba,idan ya koma da anni
da maamah da dukka yaran me zaice musu?,sai kawai ya wuce bandaki ya sake alwalarsa
ya dawo gaban ka'aba yayi salla raka'a biyu ya sake istigfari sannan ya zauna ya
durqushe yana roqon Allah cikin qanqan da kai da neman afuwarsa da agajinsa.



*_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽

*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*

*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*

*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_*
*_Da yardar Allah saikin godemin_*

*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*πŸ˜‚πŸ˜‚

Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray

*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*

*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*

*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI*

*SUNA NAN A*

*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_*

*BA'A KANO KIKE BA?*

*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin
aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*

*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*πŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎ
wa.me/+2348103155915

KO KI KIRATA TA NAN

08103155915𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 177



*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
_________________________
*_PLEASE FOLLOW MY TIKTOK PAGE_*

https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1
177


Baisan adadin lokutan daya kwashe a wajen ba,baisan mutun dari
nawa ne suka zauna suka kuma tashi ba a wajen. Har zuwa sanda ya soma jin wani
siririn sautin kuka daga gabansa.

Guri ne da mutane masu damuwa da buqatu kala kala ke zuwa,don haka
baiko dago ba yaci gaba da abinda yakeyi,saidai kukan dayaci gaba da tashi ya fusgi
hankalinsa don sautin Sabreen yake ji sosai.

A hankali ya matsa zuwa gaba,ya kuma daidaita zamansa daidai da inda
ta zauna. Jin mutum kusa da ita sosai ya sakata daga kanta,idanunsu suka gauraya
dana juna,take kowannensu wani qaqqarfan abu dake riqe da zuciyarsa akan dan uwansa
ya motsa.

Fatali tayi da abun,ta kuma yi zumbur ta miqe kamar wadda cinnaka ya
cijeta,saidai ko gama daidaita batayi saman qafafunta ba shima ya miqe,hakan ya
sanyata ta fara hanzarin barin wajen,don tabbas inda tasan zai fito da tsakiyar
dare irin haka ita ba zata fito ba.

"Sabreen" Ya dinga kiranta da tausashiyar murya sanda suka fita a haramin gudun
kada ya janyo hankalin jama'a kansu.

Kaman ba zata amsa masa ba........amma wata raunanniyar zuciyar ta
gaza jure jin yadda yake jera kiran sunanta da wata irin sassarfa wadda tafi qarfin
tata tafiyar,saboda qoqarin tsere masa da takeyi sai data hada da gudu gudu.

"Ki dakata sabreen".

" Bana buqatarka" Maganar data cake masa a tsakiyar qirjinsa kenan. Bazai iya jure
jin sake fitar wata magana haka daga bakinta ba,don haka yayi taku uku qwarara sai
gashi a gabanta,baiyi wata wata ba kuma ya dagata cak kaman yadda ya saba yi mata.
Ya raina jawota da hannu daya ko dagata kaman yarinya qarama,saita fara wuntsila
qafafunta tana magana cikin kuka.

"Ka saukeni......bana buqatarka,kace ka daina sona fa.....kai kacemin na
tafi.....na tafi kenan bazan dawo ba,kuma nima na daina son......." Ai bai iya bari
ta qarasa ba ya manne bakinsa da nata,wanda cikin second kadan qafafunsa suka soma
qoqarin kayar dasu saboda wasu irin taurari da suka soma kewaya jininsa.

Sauketa yayi ya hadeta da bangon wani gini dake kusa dasu,ya sake
lalubar bakinta ya shigar dashi gaba cikin nasa yana aike mata da wani irin
zuzzurfan kiss.

Hawaye kawai takeyi,ta kasa hanashi,ta kuma kasa tsaidashi,kaman yadda
zafin maganganunsa suka kasa cirewa daga kanta.

Sai daya galabaitar da ita gaba daya,ya kuma zare duk wani tasirin
fushi da yake iya hanga sannan ya zare kansa daga gareta. Hannunta yaja ya zaunar
saman wata concrete chair dake wajen shi da ita duka suna sauke numfashi kaman
wadanda sukayi tsere.

A madadin ya zauna,sai ya zame yana tsaiwa saman gwiwoyinsa. Hannunta
ya kamo ya sanya tsakiyar nasa hannun.

"Sabrrr" Ya kirata da wani irin taushi daya sanya taji wani sanyi ya sauka tun daga
tsakiyar kanta har tafin qafarta.
"Sabrrr" Ya sake kiranta wannan karon saita lumshe masa kyawawan idanunta kawai da
suka sanyashi yaji kaman ya hadiyeta ya huta

"Ki amsamin don Allah.......kice na'am hamma idan baso kike na zauce miki ba".

" Hamma" Ta furta tana ware idanunta da suka wani zuge saman fuskarsa. Sosai yaji
abun ya sokeshi,me ya shigeshi ne haka jiya?.


"Please forgive me my world......forgive me.....am mad duniyata.......i hurt your
feelings......ki yafemin......bazai sake faruwa ba,ke na batawa amma ni na karbi
hukuncin,'ya'yanki da iyayenki da qannenki dukka sun zuba mini ido ja fiddo musu
madame dinsu......in fact ni kaina zuciyata da kanta fushi take dani,don na haramta
mata ganinki.....na haramta mata kasancewa dake". Yayi dukka maganar yana dora
hannuwanta saitin zuciyarsa dake fama gudu.

Hannunsa guda daya ya zame a nata,ya danganashi da saitin ka'aba
sannan ya fara magana.

"Ni muhammad fu'ad......daga rana irin ta yau nayi alqawarin bazai sake bari
hawayen bacin raina ya zuba a idanun ameenatu na ba.....idan har kuma
hakan.......".

Da wani irin sauri ta zame daga inda take zaune tana riqe dukka
hannayensa biyun tana girgiza masa da sauri.

"Kada kayi haka......kowanne zaman aure dauke yake da qalubale.....komai dadi kuma
wataran sai an bata ran juna......nima ina bata maka rai fa hamma......sau nawa
ma......amma saika dinga yi kaman ma ban bata maka ba......kawai abu daya ne banaso
ka sake fada don Allah". Ta fadi hawaye yana silmiyo mata,da alama maganan ita daya
tayi mata ciwo fiye da sauran komai. Kafin ma yaji abinda zata ce din ya dora kanta
saman qirjinsa yana lallashinta

"Mene ne?,me na fada sabrrrr?".

" Kada ka sake cewa zaka iya rayuwa babu ni......don wallahi ni bazan iya rayuwar
da babu kai a cikinta ba". Wani abu me nauyi yaji ya sake sauka saman zuciyarsa
game da ita,ya runtse idonsa sannan ya budesu.

"Sabrrr" Ya sake kiranta a tausashe.

"Na'amm hamma"

"Adda na" Ya sake kiranta yana jin kaman ya maida agogo baya ya shafe abinda yayi
mata.

"Muffin" Ta motsa labbansa tana kiransa da sunan da yafison ji a bakinta sama da
kowanne suna

"Wallahi Allah mugun maqaryacine ni indai akan wannan ne......zan iya rayuwa babu
ke?,ko na daina sonki?,babbar qarya ce wallahi wallahi da babu ta biyunta a
duniya".

Sam sam ta mance da mode dinta sai wata irin dariya data kwashe da
ita. Yayi matuqar bata dariya yadda ya taqarqare yake siffanta kansa da siffar da
tasan yafi tsana guda uku a rayuwarsa. QARYA YAUDARA DA HA'INCI.

"Mijina ba maqaryaci bane......ban taba ganin mutum me gaskiya irinsa ba........a
shekara goma sha shida ban taba tuna wata tana daya batamin rai ba koda sau daya
kuwa.....don me bazan masa shaida ta cikakken adali ba?,tabbas dana zama cikakkiyar
butulu kuwa idan na tuhumeshi akan wannan laifin qwaya daya". Dagata yayi cikin jin
alfahari da ita,ya kalli fuskarta sosai ya sumbaci goshinta.

"Allah yasa ke matatace har a aljannah".

"Haka nake fata ka zama mijina har aljanna.......amma akwai albishi daya" Ta fada
tana murmushi.

"Wanne kenan?" Ya fada yana dubanta cikin zaquwa.

"Allah karimi ne me karamcin da babu irinsa kaf a halittun duniya.......Allah me
boye baiwarsa ne ga bayinsa duk yadda yaso yayi hakanne zai faru.......bayan na
fito sanda gari ya waye jiri ya daukeni,daga haram suka kaini asibiti don na
huta,sunyimin gwaji abun mamaki sun tarar da cikin da ake rigima a kansa a
jikina......kasan watansa nawa hamma?" Ta qarasa fada a mugun sanyaye tana aza
hannunsa saman cikinta. Kai ya girgiza yana jinsa kaman a duniyar mafarki.

"Wata uku hamma amma dukanmu bamu sani ba.....dama haka yana faruwa?" Wani irin
rauni ya kamashi,ya daga tafin hannunta ya sanya saman bakinta wai yana qoqarin
controlling farincikinsa kada murna tasa ya furta abinda bai dace ya fada ba.

Sai bayan wasu wasu sakanni ya iya magana da muryarsa me rawa.

"Yana iya faruwa saboda haka Allah yaso ya kasance.......astgafirullah......Allah
ka yafemin bisa gaggawa da shishshigin da na yiwa lamarinka......tashi na maidaki
cikin ahalinki don basu da wata madadinki" Ya fada yana dagata zuwa jikinsa gaba
daya.

"Da alama su suka sanya sabrrrr dina me ma'anar sunan haquri ta zama mafadaciyar
qarfi da yaji?" Kunya ta kamata,ta shige jikinsa sosai yana boye fuskarta,ga kunyar
albishir din da takeson yi masa.

"Hamma two embrayos........ina fata su zama dukka baby girls,abinda na zauna na
yita roqa maka kenan......sunan waye da waye zaka saka?".

" Sunan maamah.......da kuma nagartacciyar surukar data haifamin wannan DUNIYAR
TAWA" Ya qarasa fada yana matse hancinta me kyau. Dariya ta saki har fararen
haqoranta suna bayyana,tana wassafa kuma irin soyayyar da yarinyar me sunan umminta
zata samu daga gareta.

"Godiya ga Allah daya bani DUNIYATA na haqiqa......ya fiddani daga wancan DUNIYAR
me cike da rudani" Tayi maganar ne a zuci batasan ta fito ba har sai da suka hada
idanu ya kashe mata ido daya,kunya ta sakata cusa kanta cikin qirjinsa tana boye
fuskarta gami da shaqo tattausan qamshin nan nasa daya mata wani irin dadi kaman
bata taba jin qamshin ba sai ranar,da alama za'a fafata kenan,da alama kuma wannan
cikin meson zuminci da babansa ne,don dama tanata mamakin yadda cikin watannin ta
sake zama very addicted da lamarin.


*_Tammat bi hamdillah_*


*_Alhamdulillah alhamdulillah,Allahumma lakal hamdu fil ula wal Aakhira_*

*_lallai a rayuwa komai yayi farko yana da qarshe,doguwar tafiya me cike da tarin
qalubale masu dadi da sauqi dalilin SUPPORT NA MASOYA_*
*_sau tari wata rayuwa na zame maka mabudin alkhairan da bakayi zato baπŸ₯°_*

*_sau tari wasu dalilan ma zame maka falala me tarin yawa cikin hikimar gwani na
gwanaye wajen iya tsara rayuwa da dukkan hukuncinsa da iyawarsa_*


*_wata DOGUWAR TAFIYA da inajin bamu taba irinta baπŸ˜„,wadda a zahiri bazai yuwi
nayi shuru ban yaba muku ba ku kanku_*

*_kunyi yawan da bansan wasu bama a cikinku......masoyan da suka dora dambar
bibiyar SAFIYYA HUGUMA badon tafi kowa ba.....ba kuma don tafi kowa iyawa ba,sai
don saboda soyayya da qauna data zama SILA_*


*_INA MUKU FATAN ALKHAIRI DA DUKKA FURUCIN BAKINA......INA FATAN ALLAH YA SAKE
SADAMU A TAFIYA ME DADI IRIN WANNAN CIKIN QOSHIN LAFIYA AMINCI QAUNAR JUNA DA
SUPPORTING JUNA_*

*_ALKHAIRIN ALLAH YAKAI MUKU A DUK INDA KUKE AREWABOOKS FOLLOWERS_*

*_ALKHAIRIN ALLAH YAKAI MUKU 'YAN WHATSAPP.....INA FATAN ALLAH YA AMINTAR DA
KOWANNENKU YA YALWATA ARZIQINSA DON ALFARMAR SHUGANA S A W_*

*_NAJI DADIN WANNAN TAFIYA MATUQA,NA SAMU SUPPORT DA SHINE QASHIN BAYAN NASARATA A
WANNAN TAFIYA DAGA GURIN MABANBANTAN MUTANE,UBANGIJIN AL'ARSHI YA DAFA MANA GABA
DAYA_*

*_AMANA/GASKIYA/ADALCI/DATTAKO/KAWAICI SUNE TUSHEN KOWACCE NASARA_*

*Darasin DUNIYATA*

*_KOWACCE RAYUWA AKWAI NATA KALAR QALUBALEN,BA KOWANNE MUTUM BANE ZAKA GANI CIKIN
INUWAR DUKIYA KA DAUKA SHIKAM BAIDA MATSALA BA,BA KOWANNE MUTUM ZAKA HANGA KA DAUKA
YA SAMU DUKKAN WATA WATA NI'IMA TA RAYUWA BA_*

*_KAYI RAYUWA IYA MATSAYINKA......KADA KAYI MIQAR DA ZATA WUCE TSAHONKA,DUK
GAGGAWARKA RABONKA SHINE NAKA,BA ZAKA TABA CIN RABON WANI BA_*

*_BAWA BAI ISA YA YIWA KANSA ARZIQI BA,SAI ABINDA BUWAYI GAGARA MISALI YA HUKUNTA
MAKA_*

*_KE UWA!.....BAKI DA KAMAR 'YA'YANKI.....SUNE RAYUWARKI.....KIYI AURE AMMA KARKI
YADDA KI FIFITA KOMAI NAKI SAMA DA TARBIYYARSU DA KUMA RAYUWARSU_*

*_AIKATA ALKHAIRI KA WUCE ABINKA KA BARSHI AGUN,ZAI CIMMAKA WATAN
WATARANA.....KAMAN YADDA IN KAYI SHARRI HAKA WATARAN ZAI DAWO MAKA_*


_Kusakurai da aka samu a ciki da abinda bai kammalu ba ayimin haquri,na rubutu
matuqa har naji rubutu ya ginsheniπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚_

_wanda na batawa ya yafen,na yafi kowa,kuskuren ciki ubangiji yayi afuwa,ya
tattaramu a ladan,ya bamu ikon daukan me kyau a labarin mu watsar da shirme_


Every conclusion sparks a new inception
Nothing lasts forever
Every dawn has a dusk
Ending are part of beginnings in sha Allah
_subhanakallahumma wabi hamdika ashahadu an la'ilaha illa anta,astagfiruka wa'a
tubu ilaika_

_Allahumma salli wa sallim ana nabiyyurrahmati_ S A W

08187255862

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment