You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce da sai da suka shafe aqalla awa biyu ba kadan suna
tattaunawa da alhaj hamza din,daga qarshe abban yayi shuru kafin ya sake magana.

"Na fahimceka muhammadu.......kuma na gamsu da bayananka da hujjojinka........amma
me zai hana ka jira na qaraso nan din ko ku ku dawo gida?". Kai ya girgiza


" Kayi haquri abba.....bawai inason inyita musu dakai bane.... Amma karka manta
annabi ya fada mana,ba'a jinkirta aikin alkhairi gaggauta yinsa ake"

"Na sani muhammadu banaso ka kirawa kanka matsala ne gaka kai daya" Murmushi
ya sake saki yana yin gefe da kansa.

"Abba...ka manta muhammadu nake?....ka manta wannan me babban sunan?" Qaramin
murmushi ya qwacewa Alhaji hamzan

"Ban manta ba kam.....jarumin gold daga qasar yarbawa da inyamurai" Wannan karon
shi kansa fu'ad saida murmushinsa ya fadada

"Ka samu alhaj muhyidden,yana alranuna unguwar da gidanka yake......Allah yasa haka
shi yafi alkhairi......amma kabi komai a hankali,idan akazo batun iyaye bin komai
ake a sannu"

"In sha Allah abba.....na gode" Ya amsa masa yana jin wani farinciki yana ratsashi
sukayi sallama.

Zaune kawai abban yayi da waya a hannunsa. Wanne irin yaro ne wannan
Allah ya baiwa mariya amma har yanxu batasan baiwar da Allah yayi mata ba?,tabbas
ahmadu ya dace da kalar yaron da yake zamewa mutum sadaqatul jariya bayan
ranshi.....Allah ya gama masa komai......baisan wanne irin qauna yaron yake gwada
musu ba. Ajiyar zuciya ya sauke yana tashi

"Ubangiji yasa albarka albarkacin wajen......yasa kuma silar zuwan komai qarshe
kenan a tsakaninsu".

Kansa tsaye ya wuce nashi dakin,so samu ace tana tare dashi a
wannan lokacin.....to amma kuma yasan yanzu dole ne ya mata uzuri ya daga mata
qafa,ya kuma bata dama sosai na ganawa da 'yan uwanta,don haka sai kawai ya rage
kayan jikinsa ya shiga wanka. Tsaf ya shirya cikin jallabiyya,sai gashi ya juye sak
balaraben madina. Wayarsa ya dauka ya kira saddiq bai sameshi ba,don haka ya kira
musaddiq. Bugu daya ya dauka cikin girmamawa.

"Ka fadiwa saddiq ya shirya nan da thirty minutes mu wuce masjid.....banason wannan
ragoncin naku"

"In sha Allah hamma......amma maamah tacemin idan ka shigo ka shiga tana son magana
da kai". Agogo ya kalla,indai zai bata minti ashirin sauran lokacin zai ishesu
tafiya,ya amsa masa da okay yana katse wayar.

Ya sani babu wani lokaci da kiranta ya zama na alkhairi,babu wani
lokaci da kiranta ya zama me dadi,shi yasa ya yanke koma meye gwara yaje yanzu ya
jishi ya tattara damuwarsa ya tafi masallacin ma'aiki da ita ya juyeta a can. Kafin
ya fita ya duba number da abba ya tura masa,yayi kiran alhj muhyidden ya nema inda
zasu hadu.

A girmame yace zai sameshi a masaukinsa,hakan ya yuwa fu'ad nauyi,don
babba ubane a wajensa,don haka duk wanda ya jibanceshi yana masa kallon uba shima.

"Ka zabar mana guri,zan iskeka in sha Allah ko a ina ne". Nutsuwar fu'ad da
hankalinsa ba wani baqon abu bane a wajensa,don haka cikin masallacin yace su hadu
bayan sallah isha'i,ya duba lokaci sai ya yanke daga sallar la'asar din yayi
zamansa har isha'i acan yayi jiransa,don yana da tarin addu'o'i daman da zaiyi.

"In sha Allah zan zauna ta babus salam". Ya fadawa alhj muhyidden.

A nutse ya dauki casbaharsa,ya sake feshi jikinsa da lallausan
turarensa sannan ya saka wasu loafers masu taushi marasa nauyi ya fice a dakin.

Ita daya cikin dakin tunani kaman zai fasa kwanyarta,tana zaune daga
gefan gadon,madarar almara'i ce a gabanta tana tsiyaya da kadan da kadan tana
sha,don batajin abinci xai wuce ta cikinta. Kwata kwata jinta take kaman akan
qaya,lissafin kwanakin da zasuyi a qasar takejin sun mata yawa sun mata kuma nisan
da kamar ba zata iya jira ba.

Ganin yaran ya sake gigita tunaninta,tun sanda ta samu ta sabule yaran
daga hannunta dama tana tare dasu?,ko wani gurin ta kaisu?,ya akayi suka kasance a
nan gurin?.

Tunaninta ya katse sanda akayi knocking qofar dakin,idanunta ta daga
ta kalli qofar,tasan ba kowa bane sai fu'ad din,murya a cunkushe tace

"Shigo" Qofar ya murda ya tura ya shigo,don bayan fitar musaddiq tace yabar masa
qofar a bude.

Kallo daya yayi mata yasan dai kaman kullum ne,kaman yadda aka saba
wani abu da ya shafi buqatar qashin kanta ya sanya ta kirashi,saman dressing mirror
ya qaraso,ya dosana kadan ya zauna samansa yana dubanta.

"Gani" Ya fada a nutse yana shirya jin komai da zai fita a bakinta.

"Muhammadu......wai nikam duniya na haifawa kai ne?,wanne irin wauta da hauka
kakewa rayuwarka?,sam ba ruwanka da tattala rayuwarka?,ba ruwanka da sanin ya
kamata?,ka zama baitul mali ka maida kanka bayin wasu?". Dukka maganganunta tana
yinsu ne cikin fada zafi da kuma daga murya. A nutse ya lumshe idanunsa sannan ya
budesu.

"Yanzun me akayi?,me ya faru?" Ya tambayeta a nutse yana qare mata kallo. Bayason
ranshi ya baci ko kadan,yanayin abubuwan maamah suna neman fara ta'azzara,shi daya
yasan me ya adana a zuciyarsa daya shafeta,sirrika masu nauyi da tsanani wanda ita
kanta batasan da hakan ba.

Ido itama ta zuba masa,saidai nauyin nasa idanun yafi nata,dole ta
janye idanun nata. Tanajin zallar rainin hankali da wayo a al'amarinsa......tanajin
wani irin ciwo da yadda ya gagara zuwa hannunta tamkar ba ita ta haifeshi ba.

"Tuni na dade da sanin ni din marainiyar wayonka ne........wadannan yaran daka debo
meye alaqarka dasu da har ka fara barnatar da dukiyarka a kansu?" Ta tambayeshi a
zafafe. Idonsa ya dauke yana qoqarin jawo sabuwar iska zuwa hunhunsa,al'amarin
maamah yana daure masa kai maqura......tana yin abubuwa da zummar ba wanda yasan
kalarta ta badini a nata hangen?.

"Maamah......nayi tunanin kece me bawa wani labarin alaqar dake tsakanina dasu
ko?,a wajenki na fara sanin dacewar kulawa da qannen matarka,na dauka idan nayi
hakan nima wani abune me kyau nayi?" Yadda ya amsa matan ya mata wata bulala data
ratsata matuqa,shuru ya gifta tsakaninsu na wani lokaci,wani sashe na zuciyarta
yana gargadarta

"Ki kula da dukka amsar da zaki bashi.....akwai.magana cikin maganganunsa". Abinda
wani sashen yake nanata mata kenan.

" Muhammadu.....ka saurara da kyau ka jini,qannen matarka ko wani abu makamancin
haka ba damuwata bane......ba ruwana da alaqarka dasu,bana buqatar wata hidima
tsakaninka dasu,wannan maganar da gaske nake gaya maka ita,tunda kai ka zama abinda
ka zama,bazan sanya ido mata su sakamin yaro a tsakiya sai yadda sukaga damar yi
dashi ba......bazan lamunta ba,tun wuri ka saki dui wata hidima tasu,banaso na sake
ji ko na sake gani muddin kana neman albarka daga wajena". Wata qaramar dariya ta
taso masa amma.ya kwantar da ita ta hanyar lumshe idanunsa,ya jinjina kanshi da
kyau mamaki yana sake cikashi.

"Kana jina?" Ta fada da mugun zafin da takeji a ranta.

"Maamah.....cikin arziqin da Allah yayimin......ina iya daukan dawainiyarsu data
danginsuma gaba daya ba tare da komai dana mallaka ya samu matsala ba......dukka
mutumin da ka kawoshi nan wajen yayi ibada kana da lada na musamman,duk aikin
alkhairin da kayi asalinsa kana da lada daidai da wanda yayi aikin ba tare da an
tauye ladan kowa ba.......maamah......tabbas inda albarkar uwa ita ke sawa yaro ya
rayu.....ba shakka da tuni mun jima da amsa sunan GAWA,so inaga ba matsala bane ka
zama silar sanya farinciki a rayuwar wani......dukiyarmu da kason wasune dole a
ciki da ubangiji ya sanyata cikin tamu.....ya zama dole ka raba ka bawa kowa don
fita haqqinsu da ubangiji ya dora maka.....ina fatan ba wani magana a ciki daya
bata miki" Ya qarasa fada yana miqewa.

Mutuwar zaune tayi kalamansa suna bata mamaki me tsanani,kasa ce masa
komai tayi har ya fara takawa zuwa qofa.

"Muna kusa da masjid nabawi,dukka sallolinku zaku iya qarasawa kuyi a ciki.....ni
na wuce sai zuwa dare" Ya qarasa fadi yana ficewa cike da fatan kada ta sake cewa
komai din bare ya tsaidashi.

A bakin elevator ya samu su musaddiq,sai kawai suka wuce zuwa
masallacin. Suna tattaki a qafa yana sauraren hirarrakinsu,yayin da nashi Hankalin
yayi nisa zuwa wani guri na daban.


β˜…Sau uku tana juyawa tana qare musu kallo cikin daren,idanunta duka suna
tsakanin huda nadra da haneefa da kuma momma bahijja dake kwance saman nata gadon.

Tashi tayi ta zauna sosai,zazzabi takeji yana sake qaruwar mata,ko amai
din sai data sakeyi dazu amma bata bari kowa a cikinsu ya gani ba,saboda wannan
farincikin da wannan walwalar take so taci gaba da gani saman fuskarsu,batason
ganin komai da zai bata wannan yanayin.

Hadewa jikinta tayi waje daya tana jin sanyi,yayin da can qasan ranta
ya cika da ambatonsa. Tana ji ya gama yi mata komai na rayuwa.......tanaji ya gama
mallakar komai nata.....gangar jiki da kuma zuciya,tana jin ya sayi wani babban
gurbi a rayuwarta da rufe babinsa ba abu bane me yuwuwa. A yanzun daya qarasa cika
mata burinta.....

Sun gaya mata abubuwa masu yawa da ya yiwa rayuwar su wanda bata taba
kawowa mafarkinta hakan zai kasance ba. Wani irin gini da ya yiwa rayuwarsu har ya
zarta nata mafarkin a kansu.....ko yanzu ta fadi ta mutu ta godewa Allah......tana
da dukkan tabbas da yaqini akan rayuwarsu.

Haka kawai takejin kaman yayi tsaho ace ta jirayi gobe kafin tayi
masa godiya.....sai takeji ya cancanci ta abokanceshi a wannan daren. Tafi kowa
sanin yadda waje yake masa qunci idan ta matsa......tafi kowa sanin yadda yake
qulafucinta da son kasancewarsu tare. Tun saukarsu bai nemeta ba ko a waya,tasan
kara kawai yayi mata bawai don hakan yakeso ya kasance ba.

Zazzabinta da komai da takeji ta hadiye,ta shiga bandaki ta sake
wanka,ta dawo cikin dabara tana tunanin inda zataga luggage dinta. Ba luggage amma
akwai wani bag daban data shigo dashi,kusan duka sabbin kaya ne a ciki,saita samu
kanta da neman rigar da tasan zata dace da yanayin. Tsaf ta gyara sumarta cikin
hair mist dinta,ta kuma tajeta ta saketa a gadon bayanta. Yadda farar tattausar
rigar maras tsaho ta zauna mata a jikinta ita kanta ya burgeta,komai ya fito das
das a jikinta da wani irin salo me daukan hankali,saita nema dogon hijabin daya
rufe mata jikinta ruf ta aza saman rigar,ta dauki wayarta ta taka a hankali tana
fita a dakin.




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 113


113


Waiwaye ta dinga yi don ta tabbatar da kowa bai ganta ba,ta qarasa qofar
dakin a nutse tana fatan samunta a bude. Taci sa'a kuwa,don tana murdata ta bude
din,sai ta tura ta shige a hankali. Abinda bata sani ba tayi shuka idanun
makwarwa,daidai sanda maamah ke fitowa daga dakinta da zummar sauka floor din qasa
ta rage zaman kadaici koda cikin reception ne.

Dif wuta ta dauke mata,wata qaqqarfar guduma ta saukar mata. Lalubawa
tayi ta nema kujerun da suke ajewa jifa jifa ta cikin hallways din ta zauna ganin
duhu yana nemam giftawa idanunta tana maida numfashi,maganar da sukayi da ita ta
qarshe ta dawo mata.

"BANA SONSHI....BAZAN KUMA TABA SONSHI BA.....BANMA SHIRYA ZAMA DASHI BA.....AKWAI
LOKACIN DA XAN TAFI.....AMMA ZAN TAFI NE KAWAI SANDA NI NA TSARA NA TAFIN,BAWAI
SANDA KE KIKA SHIRYA FARUWAR HAKAN BA". kai ta jijjiga tana sake dilmiyewa cikin
mamaki. Wato ita yarinyar take rainawa hankali kenan?,ita takewa wasa da
hankali?,wai ya akayi kaman ita mariya yarinya 'yar cikinta wadda inda fuad mace ne
yaci ace jikarta ce amma take wasan kura da hankalinta haka?. Dukan kujerar tayi ta
miqe tana komawa cikin dakin,zata kasa ta tsare taga iya awannin da zata dauka
kafin ta fito a dakin.

Matsakaicin haske ne a dakin,da alama ya kashe kowanne qwai banda side
lamp din dake gefen Kujerar data hangoshi kwance samanta.

Yana kwance sosai ya miqe dukka wannan tsahon nasa,hasken fitilar ya
haske fuskarsa sosai. Qur'ani ne a bude kife a qirjinsa,da alama yana tsaka da
karantawa bacci ya daukeshi. Baqar sumar nan dake habarsa da qasan hancinsa girarsa
da zara zaran eyelashes dinsa sun sake qawata fuskarsa da wani irin annuri. Ita
kanta saita samu kanta da qare masa kallo,har zuwa sanda ta isa gabansa cikin
sanda.

A hankali ta tsugunna a gabansa tana sake matsawa dab dashi,qamshinsa
ya taso ya daki hancinta,abinda ya sakata lumshe idanunta ba tare data shirya ba
saboda dadi da nutsuwa da qamshin ya saukar mata.

Cikin takatsantsan ta miqa hannunta tana zare alqur'anin da yake
rungume dashi,ta daga tana duba wacce surar yake.

Alama ce saman ayar muhammadur rasulullah bisa dukkan alamu nan yake
karantawa,ta motsa bakinta a hankali ta furta.

"Sallalahu alaihi wa sallam" Ta sanya bakinta kan ayar a nutse tayi kissing nata
sannan ta rufe qur'anin ta adanashi.

Sake dawowa tayi ta tsugunna saitin fuskarsa tana qare masa kallo.
Karon farko data karanci ainihin sassanyan kyau da Allah ya masa baiwa dashi. Ba
banza ba yake da wani irin kwarjini da ba kowa ke iya saka idanunsa kan fuskarsa
zuwa cikin idanunsa haka kai tsaye ba,labbansa sukayi mata kyau sosai,ta miqa hannu
tana taba dogayen eyelashes dinsa sannan ta sauko zuwa labbansa masu kalan red
tadan taba. Motsawar da taga yayi sai ta janye hannunta da sauri zuciyarta tana
bugawa,dan gyara kwanciyarsa yayi kadan zuwa hannun damansa,abinda ya bashi daman
fuskantarta sosai itama ya bata daman ganin fuskarsa sosai.

Hannunta ta sake miqawa ta kama yatsunsa,a hankali ta motsa labbanta.

"Ka dage sai da ka farauci wannan sabuwar zuciyar......ka dage da qarfin zuciya
dana damtse sai daka fanshi wannan ruhin da baisan soyayyar kowa ba saita 'yan
uwansa......ka nuna sadaukantaka da jarumta har sai daka yaudari zuciyar marainiya
ameenatu......wallahi na sallama......sabreen ta sallama maka,ta mallaka
maka......ta kuma miqa wuya.........na baka dukkanin soyayyata dari bisa
dari......ka cinye yaqin.....kayi nasara......na karbi faduwar ta wannan bangaren
muddin wannan shine faduwar......ka mamaye DUNIYATA ka sabuntata da irin DUNIYAR
kowanne mutum.....nima kaine DUNIYA TA" ta qarasa fada tana kallon zara zaran
yatsunsa masu farare qal din farce kaman baya taba komai dasu.

Motsin da ya dan sakeyi ya sanya gabanta faduwa

"Idan yana jin duk abinda kika fada fa?" Wata zuciyar ta gaya Mata,saita fidda
idanunta dukka waje tana miqewa da hanzari a ranta tana cewa.

"Da na gama jin kunya".

"Ina zaki tafi kibar zuciyar da kika gama lugiguitawa?" Muryarsa ta daki kunnenta
me dauke da alamun bacci yatsunta na cikin wanda yaci nasarar cafkesu sanda take
juyawa zata fice.

Zare idanunta dukka tayi gabanta na harbawa,kada dai ace yana jinta?.

"Zan iya cewa kunnuwana sun manta dajin wata kalma me dadi a rayuwarsu irin na
yau......karki tafi ki barni cikin wayen wadannan kalaman" Yayi maganar yana
saukowa daga kujerar sannan ya sakar mata hannum yana takowa bayanta.

Kane kane yayi a bayanta yana rungumota ta baya ta hanyar aza
hannuwansa saman ruwan cikin ta. Ya cusa hancinsa ta wuyanta yana zuqo daddadan
qamshinta daya soma aike saqo sassan jikinsa da wani irin hanzari
(Karki raina turare,kada ki rabu da turare amatsayinki na matar aure,duk yadda zan
gaya miki rawa da muhimmancinsa a wajen matar aure ba zaki gane ba......amma hatta
da sha'awa turare yana tayar da ita,musamman irin masu sanyi da laushin qamshin
nan,amma ki lura,akwai inda za'ace ki kama kalar qamshi guda da mijinki xai ganeki
dashi,tom wani.namijin ba haka yake ba,wani yafison kullum da kalar da zaiji a
jikinki,bayason kala dayar nan,saiki fahimci mijinki wanne iri ne).

"Sabrrrrr" Ya kirata a rikice yana jin wannam feeling din da yakeji a kanta yana
taso masa.

"Hamma" Ta amsa masa itama idanunta a lumshe tana jin yadda saukar hannunsa a
jikinta yake haifar mata da wani irin yanayi me wahalar fassara.

Magana yakeson sakeyi mata amma ya kasa,sai kawai ya fara tattara
hijabin zai rabata dashi. Hannunsa ta riqe sannan a hankali taja baya,ta tattare
hijabin da kanta ta zameshi daga jikinta ta wurgar dashi gefe daya.

"Ya subhanallah" Ya furta bakinsa yana rawa. Zai iya cewa bai taba ganin sanda tayi
masa kyau irin yau ba,tayi ado sosai da gashinta irin yadda yakeso ya gani. Kowacce
boyayyar sura ta jikinta ta bayyana yadda yake da muradin ya gani,kafin ya qara
kowanne motsi ta qara sanda bashi mamaki ta hanyar balle hannuwan rigarta suka zame
ta saka hannunta da kanta ta zare rigar zuwa qasa sannan ta fara takowa har inda
yake ta iskeshi.

Wani irin mahaukacin tarba yayi mata cikin tsananin yunwarta,yana jin
kamar yau ne rana ta farko daya fara sanyata cikin idanunsa,martanin data soma
maida masa ya sanya yaji bashi da wata jarumta sam,yana gudun suci gaba da tsaiwa
tsaf zasu iya zubewa,sai ya sauqaqa musu ya dauke abarsa ya qarasa da ita inda
sukafi wayo.

Kirif ya rufe musu fuskokinsu da mayalwacin gashinta dake fesar da
qamshin hair mist dinta. Gaba daya ya shiga wani rudani da bai taba shiga irinsa ba
tsahon kasancewarsu tare. Komai yayi mata saita maida masa martani,duk inda ya nufa
kafin ya qarasa tayi masa jagora,sai yaji kaman ya kurma ihu ko xai samu sassaucin
dimuwar dame yawo cikin kwanyarsa.

Yanaso ya gaya mata ta sassauta saboda kada ta jashi yayi mata babban
aiki,don yana iya jin dumin dake jikinta,amma inaaa ta qarasa dimauta kowanne
tunani nasa,ba abinda bakinsa ke iyayi banda furta sunanta a jejjere da bada
zazzafan kiss da karbar martani daga gareta.

"Ki soni sabbrrrrr......na rantse da Allah ni kadai nasan me nakeji a kanki......ki
soni,zan miki komai....zan zame miki komai.....zan mallaka miki komai". Fuskarsa ta
riqe sosai cikin hannuwanta tana dubansa,gaba daya kamanninsa sun sauya ya birkice
sosai.

"Muhammad" Ta kirashi

"Fu'ad" Ta maimaita

"Muhammad jadda......ameenatu ta yarda ta soka......ameenatu ta yarda ta mallaka
maka kanta da rayuwar ta,ameenatu ta zama taka har gaban abada....dakai da ameenatu
yanxu duka abu daya ne.......ka gayawa kowa wannan cikin alfahari taqama isa da
samun tabbaci"

Ya riga ya sallama,gaba daya ta gama susuta qwaqwalwarshi......yasan
a yau kam duk wanda yayi kusa da yawa da dakinsa zai iya jin motsin da xai saka
zargi a ransa,baisan me yake yi ba kaman yadda ya manta wayeshi. A lokaci ji ya
dinga yi inama akwai wata duniyar ta daban da zai iya maidasu shi da ita?,duniyar
da babu kowa saisu kadai?,wannan albishir daya samu daga bakinta......daga gari me
tsarki yafi komai masa dadi da zame masa tarihi cikin rayuwarsa.

Wani irin dare suka raya,daren data sakar masa dukka ragamarta,ta
cika masa mafarkinsa ta hanyar bashi kowacce gudunmawa da cikakken hadin kai,saiga
muhammad fu'ad din yana mata kuka sosai kaman qaramin yaro. Kukan daya sake
susutata itama,banda abune da ubangiji ya sanyashi ya zama sirri tsakanin
ma'aurata......tabbas duniya data cika da mamaki idan akaga matashin zaki gwarzo
irin muhammad jadda yau a gaban mace yana mata kuka har haka.

Ita kanta a rikice take,ta kuma aikatu sosai a hannunsa duk da
controlling din kansa daya dinga qoqarin yi,kafin wani lokaci zazzafan zazzabi ya
sake rafketa bayan amai data yi a jere har sau uku.

Abinda ya daga hankalinsa kenan,ya tsaftacesu shi da ita,ya kuma
shiryata cikin abayarta me sulbi shima ya sanya jallabiiyyarsa,ya duba asibiti mafi
kusa ya kirasu donsu dauketa aje a duba masa ita,don bayajin zai iya jure wannan
zazzabin yaci gaba da taba masa ita.

Cikin mintuna qalilan motar al_ansar hospital ta iso suka wuce da
ita. Baiko samu tsaiwa gaya musu ba,don kiran sallar farko kawai akayi,sai ya
rubuta saqo kawai ya turawa Farooq.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862




𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 114


114



Ko na second daya bai barta ta matsa daga jikinsa ba,tana kwance cikin
jikinsa da wani irin yanayi. Cikin kowanne numfashi da zai sauke ko zai fitar jinsa
takeyi da wani irin maqalallen yanayi a cikin zuciyarta,duk bayan minti kadan sai
ya tambayeta

"Ina ne kuma yake miki ciwo?,menene yake damunki?,me kikeso?" Ido kawai take
lumshewa,don ita kadai tasan me takeji cikin qasusuwanta,saidai tana qoqarin nuna
masa all is well saboda ta fahimci a gigice yake,amma duk da haka bataga nutsuwa a
tattare dashi ba,kaman me gani har hanji,ya fahimci duk wani motsinta.

Yanayin zazzabin ya sanya suka fara bata taimakon gaggawa a daki na
musamman,kafin daga bisani su fara gudanar mata da test har kusan kala biyar suka
tafi kan zasu dawo da result din.

Sanda tayi farkawa na biyu bayan tayi sallar asuba gari ya waye
sosai,kusan goma saura na safe. Shine mutum na farko data fara gani,fuskarsa ta
fito fes yana zaune daga gaban gadonta yana jan tasbaharsa,lokaci lokaci yana duba
saqonni a wayarsa.

"Sabahal khair muffin" Cikin ba zata muryarta ta sauka a kunnensa. A nutse ya daga
kansa ya sauke mata idanunsa. Itama shi take take kallo da fararen idanunta
murmushi na fita daga fuskarta.

"Muffin?......thanks ny world" Ya fadi sunan data bashin yana masa wani mugun dadi.

"Sabahannur......khaifa asbahti?" Ya fada da tataccen larabcin da kana ji zakasan
yasan qa'idar kowanne harafi a cikinsa yana nutsa tafin hannunsa cikin nata.

"Asbahatu bikhair walhamdulillah" Ta maida masa da murmushin nan nata data
tsinceshi saman fuskarta.

Kansa ya langabe gefe guda kaman wani qaramin yaro,fuskarsa a narke
yace mata.

"I'm scared that am going to loose you,i know it's stupid,but i just can't stop
thinking about it" Murmushi ta saki tana danjin nauyinsa kadan

"Ka wahalar dani ne kawai......you won't lose me,am not going anywhere in sha
Allah". Riqe hannunta yayi sosai cikin nasa.

"That's my wish in sha Allah,you're the most important thing in my life" Sosai
maganganunsa suke sake samun mazauni a zuciyarta,maganar amna data taba fada mata
ta dawo mata fes akai.

"You're the luckiest woman da kika samu hamma na" A yanzun take sake tabbatar da
maganganun amnan,duk da a baya ta qaryata hakan.

"Have your breakfast and then brush your teeth" Idanu tadan bude kadan tana
kallonshi kafin ta sauke dubanta kan jerin kayan breakfast din daya jawo gabanta
saman dan wani gado.

"Ehnnnn" Ya fada yana dage mata girarsa,ya fahimci akwai abinda takeson fadi.

"Brush din xai zama first ko?" Kai ya girgiza

"No.....Brushing teeth after breakfast helps remove food particles and maintain
oral hygiene" Shuru tayi murmushi na qwace mata,ba a banza ba takejin su musaddiq
na gulmarsa. Komai nasa yasha banban dana kowa,tsare tsarensa ba irin na mutane
bane.

A jikinsa ya ajiyeta,ya dinga qoqarin bata breakfast din amma ta kasa
cin komai a ciki. Iya black tea kawai ta dinga kurba,tana sha yana kallon fuskarta
yana qarfafa mata gwiwa,a haka tasha rabi da qyar. Saidai tana kammalawa ya dawo
duka,ta wankesu tsaf da aman shi da ita.

Hankalinsa tashe ya danna wani guri,qasa da second sha biyar wata
nurse ta iso. Zata karbi gyaran wajen ya dakatar da ita da harshen turanci.

"Barmin zan gyara,aman nan da takeyi ne banaso,inaso shima ya tsaya ko ya tafi,ya
kamata abinci ya tsaya a cikinta hakanan".

"Likita yana dab da shigowa da dukka result na gwajin da

Please Login or Register in order to submit comment