You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallon ruwan dake
gabanta din. Maida idonta tayi ta lumshe,da alama dai taci alwashin ba zata
kalleshi din ba. Kai ya jinjina,shi kadai yasan me yake saqawa a zuciyarsa......da
sannu zai saita komai kan tsarin da yakeso,a nutse yabi kowanne curtain ya
zugeshi,sannan ya dauki bath set dinsa ya soma dosan toilet.

Kadan ta bude idanunta taga yana tafiya bandakin,tasan kuma indai ya
shiga ita daya zai bari sai ruwan nan dake kada hankalinta. Zumbur ta miqe da gudu
gudu ta rufa masa baya,sai ya tsaya ya waiwayo yana kallonta sanda ya sanya qafarsa
a qofar toilet din.

Yadda ya zuba mata idanu ya sanyata yin qasa da kanta,tasan yana
neman ba'asin biyoshin da tayin,tana wasa da farcenta tace.
"Tsoro nakeji" A shagwabe har batasan sanda sautin tattausar muryarta ya koma haka
ba. Wani numfashi ya zuqa me zurfi yana dubanta,yana bala'in son shagwaba fiye da
yadda kowa zai fahimta.......saidai ba wanda yasan da wannan dabi'ar tasa saishi
kadai,don ya sanya a ransa ba shagwabar da zata burgeshi saita matarsa. Yana cikin
jinsin mazan da shagwaba ke tafiya dasu,yasa hannunsa yana shafan qirjinsa dake
cike da gargasa muryarsa a maqoshi yace.

"Ba wani abu fa.....kina cikin aminci,na miki alqawari daga yanzu har qarshen
numfashinmu.....ba iya nan kawai ba.....a dukka fadin rayuwarki ba wani abu daya
isa ya sake cutar dake muddin fu'ad yana raye". Idanu ta ware tana kallon qasan
curtain din,ruwan yadan kada alamun wucewar kifi. Tanason kallonsa ta tabbatar masa
da tsoronta amma kuma batason kallon muscles dinnan nasa.

"Still tsoron dai?" Ya tambayeta yana dage mata gira,saita daga masa kanta.

"Okay.....yanzu to ya zamuyi?" Ya tambayeta yana zube mata idanunsa. Satar kallonsa
tayi kadan sannan ta dauke kanta,itama bata sani ba......batasan ya zasuyi ba,kawai
dai abinda ta sani ba zata yarda ta zauna ita kadai ba. Kaman yasan abinda take
saqawa yace mata.

"Zaki shigo ciki ki jirani na gama wankan?" Ya mata tayi yana da tabbacin ba zatayi
accepting ba. Waro idanu tayi tana kallonsa kai tsaye tana mantawa da batason ganin
qirar jikinsa ma.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 100


100



_Allah S W T yana cewa "lallai sallah tana hana alfasha da munkari_

_Duk wanda salla bata hanashi qarya ba,zina sabawa iyaye,zuwan gidan boka shirka
kenan,cutar da maqota da sauransu,to tabbas ya tuntubi sahihancin sallarsa_




"Ki zauna to ki jirani......bazan iya kwanciya banyi wanka ba.....if not
ki shigo sai muyi wankan tare" Ya fada yana matsa mata hanya. Ai da sauri sauri
taja baya,ya saki murmushi ya matsa kusa da stool ya dauko mata ya ajiye mata qofan
toilet din

"Oya.....zauna a nan". A sanyaye ta zauna din kaman me gadinsa,yayin da shi kuma ya
wuce ciki. Sai daya shiga ya kunna shower sannan dariyarsa ta subuce....
Bai taba kawowa a ransa muraaka zai kawo masa wannan kusancin da yaketa fata
tsakanin shi da ita ba sai yanzu......tabbas inda yasan da hakan da tuni ya jima da
daukota wannan duniyar.

Idanu ta yita rarrabawa,tana sanyawa a ranta muddin taji wani abun da
baiyi mata ba zata afka bandakin ne,komai ta fanjama fanjam,saidai har ya gama din
ba taji komai ba. Daure da towel ya fito a tsukakken qugunsa,ya fito mata sak kaman
wani dan wasan dambe na duniya. Kanta ta dauke ta miqe tana basarwa gami da barin
wajen zata koma saman sofa.

"Kiyi wanka ki sake kaya kizo muje muci abinci" Ita da yayi zancan abinci ma saita
rasa cikin wannan rayuwar ruwan ina za'a samu wani abincin kirki.

Bata musa masa ba don itama ya zame mata al'ada yin wankan kafin ta
kwanta,saita dinga dube duben wanne sponge xatayi amfani dashi?,in fact ma tafiya
ce ta dole dole ko kayan da zata sauya bata taho dasu ba.

Miqa mata bath set dinsa yayi yana kafeta da ido,salin alin ta karba don
wannan kallon nasa bata qaunarsa,wani iri yake sata tana ji gaba daya.

A tsorace ta kammala wankan,duk minti guda sai taji kaman kifayen zasu
shigo su sameta,data gama ma hakanan ta maida kayan data cire ta fito dasu.

Sanda take shigowa ya kammala shirinsa tsaf,cikin polo shirt fara
qal me ratsin black,sai black trouser shima daya zauna a jikinsa sosai yana nuna
zallar hasken fatarsa. Duk yadda taso ta qaryata kanta sanda zuciyarta ke fadin
yayi kyau amma ta kasa haka,wani irin kyau kayan sukayi masa kaman saboda shi aka
qerasu.

Kallo daya ya mata ya dauke kansa,ya dauki wayarsa yana cewa.

"Ga kaya nan ki canza.....ki sameni a sitting room" Yana fadin haka yayi gaba. Taku
biyu tayi da zummar biyoshi ya dakata yana waiwayowa. Wata siririyar dariya ta
qwace masa.

"Dama matsoraciya ce ke har haka?,bazan tafi na barki ba.....zan baki space ne ki
shirya,in kuma kinaso zan zauna na tayaki shiryawar.....nima zanzo hakan" Fuska ta
bata tana dakatawa daga binsa din. Kai ta girgiza yana sauke murmushi ya juya yana
barin dakin.

Jikinta ta qanqame waje daya kafin daga bisani ta nufi luggage din
daya nuna mata,ta kwantar da ita ta zugeta tana duba kayan ciki.

"Turqashi" Ta fada bayan ta ajiye rigar qarshe data daga a kayan. Kusan an sake
maimaita abinda amna ta mata,kaf kayan bataga wata riga da zata suturce mata jiki
ba,wasu irin kaya ne masu kama da qannen dasu gwara babu su,sai kawai ta zauna a
qasa tana saka kayan a gaba gami da buga tagumi da hannu daya.

Lokaci yake dubawa,sai yaga ya wuce qa'idar lokacin wanka da
shiryawarta,wanda tuni ya fara riqewa a kansa,aje wayarsa yayi ya miqe yana komawa
dakin.

Kanta ta dago suka hada ido,sai ya maida dubansa ga akwatin,tayashi
tayi itama,ta kalli akwatin ta kuma kalleshi,idanunta kadai sun gaya masa abinda
take nufi,ya saki qofan ya qaraso ciki.

A gaban akwatin ya tsugunna ya fara daga kayan shima,tun baiyi nisa
ba ya cire wata gown yana ajeta gefe. Da ido tabi rigar,saboda ta dagata taga yadda
take,kusan gaba daya bayan rigar a kwakwashe yake sai zararruka da ake zargawa ta
bayan rigar a daure. Ta gaban kuma ajiyayyen breast cup ne da koda me zubabbun
qirji ta tabbatar sai sun tashesu tsaye ballantana irin nata.

Da idanu yayi mata nuni kan ta dauka ta sanya,tsoro ya bayyana
qarara a fuskarta,tadan ware idanu kadan tana jifansa da alamar tambaya. Idanu ya
lumshe mata gami da kada kai,ya tsugunna ya dauki rigar sannan ya soma takawa a
nutse yana rage tazarar dake a tsakaninsu. Dab da zai isa ta fahimceshi,saita
yunqura da zummar janyewa amma ya fita zafin nama don tuni yayi ram da hannunta
cikin nasa.

"Kowanne musu da taurin kai akwai cost dinsa a wajen nan" Ya rada mata a kunne
sanda yake rungumeta cikin jikinsa yana lalubar zip din rigar tata.

Kai ta soma kada masa,don indai zai rabata ne da wannan rigar tamkar ya
rabata da komai ne,saboda ba komai din a jikinta,don bata iya maimaicen pant da
brazier ba don haka ta zura rigan kawai ba tare data sanyasu ba,da nufin ta nema
wasu idan ta fito.

"Ka bari......zan saka Allah" Ta fada a tsorace muryarta tana rawa.

"Is too late" Ya furta can qasan maqoshinsa yana shaqar daddadan qamshinta duk kuwa
da cewa wanka tayi. Bai bata damar fadin kalma ta biyu ba ta zuge rigar tsaf da jan
zip qwaya daya tak.

"Don't move.......saka miki kawai zanyi muje muci abinci......musu ne
banaso.....kinqi ki gane kuma.....leave me mana na gama miki a nutse mu wuce?,idan
da rigima kuka kikeso to na iyata kwando kwando" Ya sanya labbansa saman kunnenta
ya karanta mata. Idanunta a runtse tsigar jikinta na zubawa,daga yadda yayi maganar
tabbas da gaske yake......wata zuciyar ya shawarceta tayi haquri na sakanni ya saka
matan kaman yadda yace.....dole ya barta idan ya saka mata din ai. Wani abu ta
hadiye a maqogoronta cikin matuqar tsoro tana kulle idanunta,tana jin wani iri na
yadda zai sake samun damar kallon surarta da taba jikinta a karo na biyu bayan
alqawari da tayiwa kanta makamancin hakan bazai sake faruwa ba......tana jin sanda
iska ta hura fatar jikinta,tana jin sanda yadan rabata da jikinsa ya salube rigar
ta sulale qasa. Dukka jikinta ya dauki rawa da bari ganinta cikin yanayin da ko
mahaifiyarta bata taba ganinta ba.......duk da ba haske bane tarwai a dakin amma ba
abinda zai hanaka ganin mutum sosai da sosai,tsoronta ya ninku,ta dinga jin kaman
qasa ta tsage ta hadiyeta a ciki.

Da qyar ya kamo numfashinsa dakeson kubce masa saboda sauka da
idanunsa sukayi a wajen. Ya miqa hannunsa yana me burin isa gurin,sai kuma ya tsaya
cak yana janyesu a hankali,wata qatuwar ajiyar zuciya ta kubce masa kaman yaron da
aka yiwa dukan tsiya yaci kuka ya qoshi,da wani irin zafin nama ya juyata fuskarta
ta daina facing dinsa,saidai can dinma ba sauqi,hips dinta ke tsokane masa
idanu,sai kawai ya rabata da jikinsa waiko hakan zai sanya ya rage ganin abubuwan
da yake gani din.

Baisan shima nasa hannuwan rawa sukeyi ba sai bayan ya zura mata
rigar ya dagata daga jikinsa yana zazzarga mata igiyoyin dake riqe da bayan rigar.
Sosai hannuwansa suka kama rawa,daure igiyoyin suka gagareshi. Ya runtse idanunsa
da matuqar qarfi yana fatan daidaituwar mode dinsa,saidai ko daya bude ba abinda ya
canza saima numfashinsa daya fara fuzga kaman me ciwon asthma.

Hannuwansa ya dora saman kafadunta gaba daya ya juyo da ita da wani
irin hanzari,yadda red din gown din ta sake haskata sai yaso.tafiya da ragowar
numfashinsa da yake kokawa dashi. Gaba daya labbansa rawa suke kaman me rawar sanyi
ya soma lalubo kalmominsa......
"DUNIYA TA.... please,kiyimin alfarma na sake kasancewa dake karo na
biyu......please na roqeki karkice zaki hanani" Firgicin data shiga ya kusa fin
nasa,take itama jikinta ya kama rawa,ta zare idanunta duka a kansa tana jin kaman
zasu zazzago tsabar tsoro. Ta motsa labbanta zatayi masa magana a tsorace amma ya
rigata

"Am so sorry.....naso na barki har sai sanda kika fara sona.....naso na barki har
sai sanda kika gamsu da kanki kikayi accepting muhammad fu'ad......but.....kece
DUNIYATA bani da wani gurin zuwa sai wajenki din dai" Sake rudata kalamansa
sukeyi,batasan yadda zata masa bayani bama,neman gurin tsira kawai takeyi,saita
saka hannunta tana neman zame hannuwansa daga kafadarta. Sarai ta fahimci a rude
yake kaman yadda take a rude,idanma tace zata tsaya masa bayani bazai fahimta ba.
Damqe kafadun nata yayi idanunsa suna sake juyewa hadi da canza launi.

"Please mana.....na miki alqawari wannan karon......I'll be gentle with you.....i
will never harm you again" Ya fada yana jin kaman ana qara izashi zuwa
gareta.....kaman yana qara loosing tunaninsa gaba daya. Sake buda baki tayi still
bata sare ba,duk da tsoron dake sake dabaibayeta da nufin masa bayani ko
kadanne,amma sai.ya kama hannuwanta duka ya sanya tsakiyar tafin hannunsa kaman me
begging dinta

"Please....please.......na yadda da kowacce kalan tuhuma zakiyimin......na yadda da
kowanne zarginki a kaina......kome kikace nayi ina neman gafara akai......kinqi
bani dama tun a baya nayi bayanin kaina......I'm pleading with you.......grant me
this favor" Ya qarasa maganar yana zubewa a gabanta......

Ji yake ya shirya rasa komai.....ya shirya kuma sadaukar mata da
komai,yayi qasa da kansa yana jiran cewarta jikinsa naci gaba da rawa.

Wani abu ya tsarga mata jin digar wani abu me dumi saman tafin
qafafunta,wata irin faduwar gaba ta ziyarceta saboda abinda zuciyarta ta raya mata.

"Muhammad fu'ad jadda ne kuka a gabanta?,muhammad fu'ad fa?,wanda gidan jaridu da
mujallu kowacce fitowar rana zuwa faduwarta suke rububin buga labari akan
kamfaninsa......suke rububin fidda labari akan kalan jarumtarsa tun kan ya balaga
har zuwa girmansa......jaddan da qasashen duniya keyi dashi?,jaddan da maganarsa
manyan kamfanonin qasashen qetare dake sarrafa diamond sukeji?,yau shine under her
feet?.

Daidai inda zaren tunaninta ya tsaya kenan,sai dauko mata sunkutarta
da fu'ad din yayi zuwa lafiyayyar shimfidar da muraaka suit suka zubeta musamman
saboda masoya masu yawon watan zuma wato honeymoon irinsu fu'ad din.

"Am sorry DUNIYATA.....am sorry my world" Shine abinda ke fita daga bakinsa cikin
wani irin gigitaccen yanayi. Tsoro ne fal qirjinta da zuciyarta,tuni ta fara sakin
nata kukan tana hango kanta gaban Dr fadwa ana sake dinketa. Tana sake rewinding
azabar da tasha wancan ranar.....ta kasa mantawa da yanayin daren da kuma lokaci.
Hatta da wucewar kowacce daqiqa a lissafe take a wajenta....abune da ya kasa barin
kanta da mafarkanta.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 101


101


_An rawaito daga manzan Allah S A W yace: Daga cikin mutane ukun da baxasu shiga
aljanna ba,kuma Allah bazai musu duban rahama sune 1_ _"WANDA YAKE ZINA TUN YANA
YARO HAR YA TSUFA YA MUTU BAI TUBA BA_

_2 _TALAKA ME GIRMAN KAI_

_Bukhari da muslim_




"Kar ka cutar dani" Ta fada a galabaice tana jin yanayinta yana canzawa.

"Bazan iya cutar dake ba.......sonki ne yayimin yawa.....ki taimakamin na koyi
controlling nasa" Ya fada ba tare daya saurara mata ba.

"In ka cutar dani ko ka zalunceni......"

"Ki daga hannu ki roqi Allah ya hukunta miki ni.....ki roqi Allah yayi miki
sakayya......ya jarabceni da wani son da yafi wannan yawa da fadi" Ya fadi yana
tallafo kanta gami da sanya jirkitattun qwayar idanunsa cikin nata dake cike fal da
hawaye......dukka hannayensa suna rawa kaman wanda aka tsamo daga ruwan sanyi.
Idanunsa kawai firgitata suke,ta saka hannu zata riqeshi saidai ko kadan bayason
sakejin wata magiya tata,don haka ya rufe bakinta ruf da nasa.

A hankali ya shiga aike mata wasu irin zafafan saqonni.......wasu irin
abubuwa da tun tana turewa har suka fara kama mata kwanya.....suka jefa ta a
duniyar tunani.....suka dauki duk wani tsoro nata da fargabarta sukayi cilli dasu
can bayan gadon.....suka gusar da duk wani hankalinta tunaninta taurin kanta tsiwa
dama tsoronta. A hankali saiga me jadda yana komawa fagen,fagen da bai taba zaton
zai sake ziyarta ba karo na biyu cikin rayuwarsa.......yayi musu ragama da jagora
zuwa wata sabuwar duniyar da shi da ita basusan akwaita daban bace.....tasha banban
da duniyarsu ta wancan karon nasu.

β˜…Tun yana dakon jiran fu'ad har ya soma lalubarsa cikin gidan,don dakinsu ya
shiga zaman jiransa. Ko ina ya duba bai ganshi ba,bai wani zurafafa tunani ba ya
dauki wata motar ya fita ya zauna da baqin nasu,suka kammala meeting din ya
sallamesu,ya kuma hada duka documents din a take ya aika masa ta email. Kaman yadda
suka tsara daga wajen sai ya wuce dauko anni data tafi wani herbal center a
traditional market dinsu. Suna mota take tambayarsa fu'ad din

"Mun fito tare so uzuri ya maidamu,sai nace bari nazo na daukeki" Daga haka suka
rufr chapter din suka dauko wata har suka isa gida.

Komai anni ta gama har tayi shirin kanwaciya amma bataga sabreen ba.
Tana saman abun sallah tana shafa addu'ar shafai da wutirinta tace da amna.

"Ina ameenatu ta shiga ne?" Kai ta girgiza,itama tun dazu take nazari
"Ban sani ba wallahi anni,maamah dai tayi kiranta,tunda ta fita kuma bata dawo ba".
Shuru anni tayi haka kawai taji gabanta yana faduwa.

" Maamah ce ta kirata?,tunda ta fita kuma bata dawo ba?" Ta sake maimaita statement
din tana duban idanun amna. Kai ta gyada mata.

"Turqashi" Anni ta fada tana miqewa hankalinta yana tashi,zuciya ta fara fasalta
mata abubuwa kala daban daban da zasu iya faruwa.

"Indai wani abune ya faru kaman yadda zuciyata ke gayamin......indai wani abu
mariya ta aikata na cutarwa ga ameenatu.......tabbas saita gane bata da wayo......a
wannan karon saina nuna mata ainihin kalata" Anni tayi maganar a zuciyarta tana
zare hijabin jikinta,ta dauki dankwali ta daura tana duban amna

"Ki zauna ina zuwa" Abinda kawai tace da ita kenan ta murda qofar tana ficewa.


_tofa.....πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚,me anni zatayi?,masu karatu ku tarota,ku gaya mata ba ruwan maamah
a nan......dan annin ne yayi kidnapping takwararta da kansa_ πŸ˜†πŸ˜‚πŸ˜‚


Daidai lokacin da maamah ke dakinta,abun duniya yana sake ta'azzarar
mata da wani irin zafi qunci da tashin hankali. Kaf tunaninta ya karkata akan yadda
zata raba sabreen da wannan copy din video din da yake hannunta.....rabata dashi
din shine tamkar mabudin iya wurgar da ita daga rayuwarsu cikin qasqanci da
tozarcin data tanadar mata.

Ta duba agogo ta duba agogo har sau babu adadi......ta duba agogo duk
bayan kowanne wucewar daqiqa.....cikin saka ran fuad zai dawo ya
lallasheta......fu'ad zai dawo yaji meye damuwarta kaman kowanne d'a yakewa
iyayensa,saidai tun tana dubawa tana kuma lissafawa har ta bacewa lissafin.

Kowacce alama da shaida ta nuna mata bazai dawo ba.....ya fita abinsa
ne,bashi kuma da niyyar bata wannan lallashi da kulawar da take yunwarsa. Ranta
yakai qarshen baci,da gaske dai bai dauketa uwa ba mahaifiya.....kunnuwanta na tuna
mata wata hira da taji musaddiq da saddiq nayi,suna gulmar fu'ad din. Ya fita aiki
ranar sai gashi ya dawo da Rana,suka dinga dariya suna gulmarsa,wai da zai fita ne
yaga ran anni kaman a bace....da yaje office ya kasa sukuni,dawowar da yayi yazo
zagayata ne ya tabbatar ta warware,ba kuma wani a cikinsu bane ya bata mata rai ba.

Tuna wannan kawai ya sake hura wutar zuciyarta,sai kuma ta tsinci
knocking da fushi yasa ta kasa tambayar waye,ta miqe kawai ta bude qofar a fusace.

Anni ta gani a tsaye tana duban ta,wani irin kallon kallo dake dauke da
ma'anoni da yawa a zukatan kowannensu.

"Zuwa nayi duba sabreen.....ta shiga dakinki kuma har yanzu bata dawo ba?,ina kika
kaita?". Me neman kuka ne wanda aka jefa da kashin awaki,wanda yake jiran kadan ya
fashe,saita fito daga dakin gaba daya tana duban anni tana huci.

"Dama dab nake da zuwa wajenki na tambayeki wanne irin baqin sihiri kika yiwa
'ya'yana?,wacce irin shirka kika ta'ammali da ita ameena?,da yake bani da haqqinki
sai gashi kin kawo kanki da kanki kina tambaya akan abinda ni yafi cancanta na
tambayeshi". Mamakin maamah din ya kasheta,ta zuba mata idanu sosai tana ganin
yadda take haqilo kaman zata fidda maqogoronta.

"Mariya......tambaya daya ce nayi ina kika kai sabreen?,don bata dawo dakinta ba".
Wani banzan kallo ta watsawa anni tana dubanta.
" Au.....bacewar karuwa dama abun mamaki ne?,har akwai mamaki don an wayi gari an
tarar karuwa ta gudu daga dakinta?"

"Subhanallah" Anni ta fada tana ware idanunta akan maamah mamaki yana ratsata.
Surukarta?,matar d'anta take kira karuwa saboda wani son zuciya nata?.

"Ameena.....ina me baki shawarar warware duk wani qulli da kikasan kin yiwa yarana
tun daga zamanin quruciya zuwa yanzu.....idan kuma kinqi wallahi wallahi ni mariya
bazan qyale ba......na dauki cikin yaran wata tara na haifesu.....naci kashinsu da
fitsarinsu amma rana daya azomin da bariki da salon mallaka?,ubanme kike basu wanda
ni bazan iya basu ba?,uban me kike musu?". Sosai zagin ya sosa zuciyar anni,sai ta
koma ta zauna tana qare mata kallo hannayenta harde a qirjinta.

Duk wasu sarari da filaye na yiwa maamah kara zuwa yanzu sun fara
cika,bata kuma da saura wanda zata bude mata taci gaba da zuba jujinta. Kai tsaye
kuma hankalinta kwance ta kirata

"Mariya......abinda na basu baki dashi.......kin kuma rasashi har abada......yadda
kika kasa rungumarsu kiji qansu a sanda suke da rauni......to kema kin rasa wannan
cikakken tausasawar sai wadda zasuyi miki donsu fita haqqinki da haqqin
addininsu......shima wannan din xasuyi miki shine saboda sun mori iyayen goyo da
sukasan hagunsu da damansu.....daidansu daba daidai ba......banda haka ke dasu dama
dukkan abinda suka mallaka sai gani sai hange daga nesa. Inda ce hankalinki a
daidai yake......inda ace hankalinki cikin jikinki yake.....ba cikin dimuwa kike ta
neman duniya idanu rufe ita da abinda yake cikin ta ba......da baki buqatar bayani
kan me yasa kika rasa kike kuma rasa kowacce dama,take kuma kufce miki.......bari
na gaya miki wani abu.....ni ameenatu na tsere miki.....ni ameenatu ba zaki taba
kamoni a zukatan naki 'ya'yan ba bare nawa 'ya'yan.....sauran dukkanin abinda zaki
zata ko ki tuhuma wannan ke kika sani.....kuma keda zuciyarki......zuciyar bawa
birninsa,abu daya zance miki shine......kada ki yarda kada kuma ki kuskura wani abu
ya samu sabreen,idan kikayi wannan gangancin to tabbas zan saka a binneki a cikin
qasar Maldives me tarin farin rairayi" Ta qarashe maganar tana nuna maamah da
yatsa,sannan ta miqe tsaye sosai.

"Daga yau gobe zuwa jibi naga dawowar diyata cikin gidan nan.....ko da fu'ad ne
yace zaiyi ganganci da rayuwarta shi dake aurenta saina hukuntashi.....ballantana
ke da nake kyautata zaton kwangilarta kika dauko". Anni na kaiwa nan ta juya tana
barin wajen,tanata qoqarin controlling fushinta kada maamah din ta ganshi.

"Aikin banza kenan qafafa da mallakin wani.....ke me ya hanaki haifar
kamarsa?,kinga sai kiji dadin yin mulkin mallakar da kyau ba tare da kowa yaga
wallenki ko ya qalubalanceki ba" Tayi maganar da nufin fusata zuciyar anni.

Da wani lafiyayyen murmushi ta waiwayo tana kallonta.

"Banda abinki tunda kin haifomin ai kin hutasshe dani......don yadda nake hutawa ko
asalin wadda ta kotseshi bata rabauta da wannan ba....idan kinajin tsuntsu daga
sama gasashe to fu'ad ne a hannun ameenatu" Ta qarashe maganar tana bude mata
tafukan hannayenta sannan ta juya taci gaba da tafiya abinta.

Kamar hauka zai kamata haka taji maganganun anni saman kanta. Kasa
shuru tayi ta soma zuba ruwan masifa da zagi.

"Ameenatu.....nafi qarfinki....nafi qarfinki wallahi,bakisan wacece mariya
ba....kibar ganin zamani ya cimmata......to ki giwa ta fadi tafi qarfin wawa,tafi
qarfin kiyashi ya jata.....zan nuna miki asalin wasan indai na haifu cikin uwata da
ubana".

Bataji komai cikin abinda take fada ba,don already ta wuce daki ta kuma
maida qofar ta kulle.

"Bari yazo shima zai sameni.....bazan sake kwana gida daya da wannan annamimiyar
makirar ba.....dole yazo ya zaba,koni ko ita" Ta fada kaman zararriya tana jawo
luggage dinta tana watsa kayanta ciki,sai kuma ta tsaya cak.

"Ina yarinyar ta shiga?" Ta tambayi kanta gargadin anni da fuskar daba wasa tana
dawo mata,saita saki kayan hannunta ta koma gefen gadon ta zauna.

Wani gumi ne ya tsargo mata tana jin hankalinta ya fara kadawa. Anni
tana da power din da bata da ita.....tabbas ne wannan,don idan akace ana buqatar
ganin fuskar maman muhammad jadda ta anni ce za'a fara nunowa.....daukakar fu'ad ta
sanyashi alaqa da manyan mutane da hankali baya zato,da yawansu kuma suna alaqa da
anni a matsayin itace mahaifiyarsa......KENAN UMARNI DAYA ZATAYI A KANTA AYI MATA
YADDA TAKESO?.

Tambayar data sanya 'ya'yan hanjinta curewa waje daya kenan,saita jawo
wayarta da sauri tana nemam number fu'ad.

Kiran duniya wayarsa a kashe,ta kira tun tana irgawa harta bacewa
lissafi,sai ta aje wayar kawai gefe tana tunanin meye abunyi?.

_πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚,maganin dan banza karen maguzawa ko inji hausawa.....shin a wannan lokacin
hajiya maamah xata shiga hannu ko kuwa?_

_meye hasashenku?_



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 102



102


Tsaye take gaban qawataccen madubin bandakin me tsananin haske da hasken rana
daya soma mamaye sararin samaniya ta bullo ta wasu sassan glasses na bandakin ya
kutso ciki.

Daure take da bathrobe me tsananin taushi,fara qal data zauna a
jikinta bisa taimakon igiyoyin dake maqale a jikinta,saman kanta daure da towel
data nade gashinta me tsaho da santsi,wanda ruwan da ya jiqashi ya sanyashi
kwanciya ta gaban goshinta dama wasu sassa na wuyanta. Brush ne

Please Login or Register in order to submit comment