You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka qarasa warkewa....."

"Noooooo......dole farouq dina ya shiga qwaryar manya as soon as possible.....ta
iya yiwuwa ya rage zargina.....ta iya yuwuwa kuma ya daina katsemin muhimman lokuta
na da DUNIYATA". fuskewa farouq din yayi yana sosa kanshi

"Eh to.....kaman tafiyanma zaifi mana Alkhairi gaba daya.....don bana tunanin idan
ka zauna a nan dinma warkewar arziqi zakayi,gadon ya muku kadan gwara a koma gadon
gida". Toshe bakinta sabreen tayi,salin alin ta debi kayan kunyarta taja jikinta
tana barin gurin tun wani a cikinsu bai ganta ba.

β˜…Salati drivern ya saki,hannuwansa bisa saman kansa yana sake sakin salatin gami
da cewa.

"Ku kawo dauki bayin Allah......hajiya ta zube". Dukka hankalin ma'aikatan gidan ya
tattaru a kanta,saidai har matan ciki tsoro da shayin dagata suke,basusan haqiqanin
abinda zai biyo baya ba idan suka dagata bayan ta farka.

"Dole haka za'a ceci ranta,kome zai biyo baya ai ba za'a barta ta mutu ba ko?".
Malam sa'adu me gadi ya fada.

"Matso ke raliya ki kama musu ita" Ya fadi yana matsawa baya.

"Gashi ba kowa gidan Alhaji hamza ballantana muji ina ake kaita" Malam sa'ad ya
fada yana duban driver din.

"Kowanne asibiti ma kaita za'a yi tunda abune na gaggawa.....ki shigo mu tafi" Yace
da raliya yana shigewa cikin motar.

Tuqi yake a gaggauce yana tsoron kada ta mace a hannunsa,babar babban
mutum irin me jadda ta mutu a hannunsa tabbas ba qaramin tashin hankali bane.

Tafiyar minti shabiyar suka samu wani private suka tsaya a nan,aka
dauko wheelchair aka dauketa akai,har a sannan bata dawo daidai ba.

Sai da suka kashe minti kusan sha biyar a kanta sannna ta farfado,suka
cire mata oxygen suka daura mata ruwa da suke saka ran minti talatin ya qare sannan
likitan yace zaije ya dawo kafin ruwan ya qare.

Kanta kawai take mirginawa tana jin qirjinta yana mata wani ciwo,duk
inda ta juya fuskar raliya data drivernta kadai take gani,har bacci ya saceta.

Still data farka din ba wasu sabbin fuskokin saisu din dai. Wani abu ya
tsaye mata a wuya,wasa wasa tana shirin kamanceceniya da tsintacciyar magen da bata
da wani gata. A hankali ta sauke dubanta kan wata mata dake kusa da gadonta,wanda
su biyu ne kacal dama a dakin. Yara hudu ne tsaye a kanta,tana zaune saman
gadon,daya a hannun damanta.....daya a hagunta,dayan yana tsaye saman kanta yana
bare mata ayaba yana bata tana ci,dayar tana saman kujera gaban gadon nata riqe da
robar yoghurt tana jira ya gama bata ta miqa mata.
Hira suke a tsakaninsu,kowanne fuskarsa dauke da walwala duk da cewa
jinyar mahaifiyarsu sukeyi. Tana gama ci ya karbi bawon ya jefa a Dutsbin,zai karba
yogurt din daga hannun ta zaunen ta hanashi.

"Saika kwashe ladan duk kai kadai,nima inaso" Ta fada tana kai roban bakin
mahaifiyartasu.

Idanu maamah ta dauke tana runtse idonta,wani irin bacin rai yana
ratsata. Tasan koda kwatar kwatar kwatar kudin fu'ad duka yaran matar basu kai
ba.....amma yadda suke tattalinta da nuna mata qauna da kulawa kadai abun kallo
ne.....ita gata ta qare da zama 'yar kallo,cikin rayuwar kadaici da rashin wani
sashe da zai tallafeka.

"Allah ya isa ameenatu.....Allah ya isa" Ta fada a sarari tana ji har zuciyarta
anni ta mata cutar da bazata taba iya wankuwa daga ranta ba.....hakanan kowacce
kalar fansa data shirya dauka ba zata iya ramawa daidai da abinda tayi mata ba.

Daga raliya har driver din da kallo suka bita,saidai babu bakin
magana,daidai nan likitan ya shigo.

"Ta farka ko?" Ya fada cikin kulawa yana dauko file din gami da sake duba abinda ya
rubuta,ya qara wasu rubuce rubucen sannan ya ajiyeshi yana dubanta.

"Hajiya ki rage saka bacin rai a zuciyarki.....ki rage saka damuwa a ranki,kina da
hawan jini bai kamata ki dinga zama cikin damuwa ba.......irin wannan gaskiya yana
iya haifar da matsala kala kala,ba'ason abinda zai dinga sanyawa jinin yana hawa
haka ta farat daya....kuyi qoqarin ganin ta kiyaye" Ya qarasa maganar yana dubansu
raliya ganin maamah din taja idanunta abinta ta kulle.

"Tom.....in sha Allah" Raliya ta fada a sanyaye a ranta tana cewa mu asuwa?,indai
taji da kunnenta ai shikenan mun kubuta.

"Kuna iya tafiya gida.....amma da zarar taji wani abu daban ayi hanzarin
dawowa,saboda yanzun takai matakin da dole a dinga yawa checking up nata".

"Mun gode likita" Driver ya fada bayan ya karbi takardar magungunan daya rubuta
mata.

Yana shirin tada motar ya dan waiwayo

"Ya za'a yi da magungunan nan hajjaju?,zamu siya ne a hanya ko za'a kawo?".

"Kai sagiru" Maamah dake a qufule da yadda suke jaddada mata cutar hawan jini ta
kira sunansa.

"Naam hajiya".

"Ka fita daga ido na......hawan jinin banza hawan jinin wofi?,maqaryatan banza
wanda mutum baya ciwon Allah da annabi?,shekarata nawa a duniya hawan jinin bai
sameni ba sai yanxu ina fafutukar cika burikana?,Allah ya tsinewa wanda ya fasa
cewa ina da hawan jini.......hawan ruwa ne dani.....bani takardar nan nan" Ta fada
cikin fada tana miqa masa hannunta.

"Hajiya......ki tsaya ki duba maganarnan,don bakiga yadda kike bane dazu.....bai
kamata ki wasa da magani ba....." Kai ta jijjiga.

"Lallai sagiru wuyanka ya isa yanka.....ashe kana dab da rasa aikinka" Ta fada
cikin mamakin tsaiwa.musu da yayi da ita.
"Ka bata mana sagiru" Raliya tayi saurin tunasar dashi,salin alin ya miqa mata yana
cewa.

"Tuba nake,Allah ya baki haquri".

" Idanma hada baki kukayi dasu saboda ku manna min ciwo ku kasheni to ta Allah ba
taku ba.......rayuwa a duniya yanzu na farata,maqi gani ya kauda idonsa" Ta fadi
tana yayyaga takardar ta watsar ta window tana cewa

"Muje gida" Tana jin lallai tana buqatar tayi magana da fu'ad da gaske.

Ya gama shirin kwanciya tsaf sanye da pyjamas masu taushi farare
qal,yana zaune saman yalwatacciyar sofa yana binta da kallo sanda take qoqarin
gyara masa gadon don yaji dadin kwanciya.


"Sabrrrr" Ya kirata da sautin da ya sanya taji tsigar jikinta ta zuba. A nutse ta
waiwayo tana kallon lumsassun idanunsa.

"Yau bazan kwanta kan gadon nan ba". Da dan mamaki take kallonsa,kafin takai ga
tambayarsa dalili sai musaddiq yayi knocking. Sabreen ta sauka a nutse tana nufan
qofan da dan mamaki,don yanzun sukayi sallama dasu zasu wuce gida. Kanshi yadan
rusunar yanajin nauyinta da tsoron kada hamman ya fatattakoshi.

"Maamah keson magana da hamma" Ya fada yana miqa mata wayarsa. Bin wayar tayi da
kallo kafin ta matsa tana baiwa musaddiq hanya. Dubanta yayi saita daga masa kai
alamun ya shige,a sanyaye yake takawa ciki itama tabi bayansa da nufin gama gyara
gadon ta fita ta bashi waje don ya samu amsa wayar sosai.

Wani yawu musaddiq ya hadiye yana duban hamman nasa daya tsareshi da
ido.

"Maamah ce tace lallai na kawo......" Hannu ya daga masa yana amsar wayar,sai ya
miqa masa yana fita daga dakin a gaggauce yana jin bazai iya jiran ma ya gama amsa
wayar ba ya karba sa hadu gobe,don haka kai tsaye ya wuce inda cab ke jiransa.

Handsfree ya sanya wayar,ya kuma ajiyeta a gabansa kawai yana zuba mata
idanu,irin yadda yakeyi idan ranshi yana bace kuma baya da buqatar amsa wani kiran
amma tilas ta sakashi amsawa.

"Ina kyautata zaton kana jina?,ko yanzun ma 'yar mulkin taka ce ta daga kiran?"
Tayi maganar da wata irin hasala da fusata.

"Muhammad fu'ad jadda ne" Ya amsa mata da wani irin nutsuwa yana zubawa sabreen ido
wadda ka ta ke duqe tana gyara bedsheet din gadon da pillow case din.

"Naji dadin jin hakan......umarni ne daga uwa zuwa shashan danta wanda baisan inda
yake masa ciwo ba.........ka kama dukiyar mahaifin yarinyar dake mutuwar sonka ka
garqame.....ka masa sanadin aikinsa duka saboda kana hannuwan mutanen da suke riqe
da ragamar rayuwarka......sai abinda suka ce.....ni mariya dana dauki cikinka daga
gudan jini har zuwa tsoka.....harka zama mutum.....saboda lalurar rayuwa ta
nesantani daku shikenan yanzun nice wulaqantatta a wajenka......to indai nice
mahaifiyarka ina baka umarni cikin qasa da awa daya komai na ambassador khaled ya
koma kan aiki daidai".

"Tom" Kawai yace da ita yana sanya dukkanin wani qarfi na qwanjinsa dana ruhinsa
yana danne zuciyarsa. Wasu irin abubuwa ke taso masa......yana rantsuwa da
ubangijin ka'aba......banda da gaske ya ratsa jikin maamah ya bullo zuwa cikin
duniyar da yake rayuwa a yanzu a cikinta......babu wani halitta kaf duniya daya isa
yayi masa quarter quarter abinda tayi masa a yanzun. Hannunsa yake mutstsukawa
yatsunsa suna wani irin qara,yana jin wadannan mutanen guda biyu sun fara kai masa
ko ina a rayuwarsa.

Kunnuwanta ne taji ba zasu iya dauke maganan maamah din ba,saita saki
gyaran gadon ta soma nufar qofa tana takawa a gaggauce.

"Sabreen.....dawo" Ya fadi kansa tsaye ba tare daya damu maamah zata iya ji ba.

"Ina magana da kai kana kiramin sunan wannan yarinyar?,annamimiyar karu....." Ya
riga ya shanshano abinda take da muradin fada,sai kawai ya sanya hannunsa da wani
irin zafi ya datse kiran yana kashe wayar gaba daya.

Da gaske wani irin abu sabreen keji,wani yanayi taji yana tsarga
mata,ba zata iya zama ba da gaske,ba zata iya jura ba.....don haka ta sake takawa
zata fita,sai kawai ya sanya hannunsa me ciwon dake nade ya fusgota sai gata ta
fado zuwa jikinsa yasa hannuwansa duka biyun ya lullubeta cikin qirjinsa kaman ya
manta ko baisan ciwon dake hannunsa ba ko kuma wani sassauqan rauni ne da bashi da
radadi ko zafi ko kadan.

A zafafe yake kiran wata number,tsoronsa a karon farko ya kamata ganin
yadda numfashinsa yake fita da sauri,zuciyarsa na wani irin bugawa.

"Haka fushinsa yake?" Ta tambayi kanta da kanta,daidai sanda kiran ya shiga aka
daga. Ko muryar dake wancan bangaren bata jiba ya soma sauke musu umarni.

"Inaso a daren yau basai gobe ba.....fareeda khaleed mustapha ta kwana a a
cell......ba ita kadai ba,da duk wanda ya kawo wargi ko yunqurin hana fita da ita"
Abinda yace kawai kenan yayi wurgi da wayar.

Matseta yayi so sai a jikinsa,yana daga idanunsa da suka kada suka
sauya launi yana zubesu cikin nata......


_tofa.....ran 'yan maza ya baci.....an manta da ciwon da ake jinya......ko sabreen
zatayi aikinta?🫣,zamu gani_



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 133


*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA
KUKESO_*
*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA
IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE
SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA
A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*



133


Sasai taji wani abu yana ratsa jinin jikinta game dashi......wani
narkakken tausayinsa yana taso mata yana kuma mamaye ilahirin jikinta. Ta yarda
dari har bisa dari cewa......da uwa irin maamah gwara ka rayu cikin maraici......da
uwa irin maamah gwara ka zamana cikin layin yaran nan da ko dumin iyayensu basuji
ba ubangiji ya karbi rayukansu......ta sake yarda da cewa.....komai ubangiji ya
tsarawa bawa tabbas akwai manufa da alkhairi a ciki.

"Ya zakayi haka?" Ta fada tana sake saka idonta cikin nasa sosai tana kuma riqe da
fuskarsa cikin tafukan hannayenta. Kaman wanda yasha wani abu ya maku yake magana

"Ya bazanyi haka ba.....ta yaya zanyi wasa da duniyata?.....ta yaya zan bari a taba
duniyata?" Numfashi taja me zurfi wanda ya shige jikinta da wani irin mahaukacin
sonsa da kowacce safiya yake qaruwa cikin ruhinta,ta sake bude idonta a kansa tana
kallonsa.

Taga abubuwa da yawa cikin idanunsa......giyar soyayya da qauna.....da
kuma wani irin fushi. Ji tayi kaman bata da wani sauran aiki daya rage mata a
duniya a yanzun banda ta kwaranyar da wannan fushin da kuma damuwar daga wannan
ruhin daya gama macewa a soyayyarta. Ba zato ba kuma tsammani yaji ta hade
bakunansu guri guda.

Wani irin zazzafan kiss ta soma ajiye masa kafin ta tura harshensa cikin
bakinsa ta soma sarrafashi kaman yadda yake mata. Cikin qasa da second biyu kowacce
wuta dake jikinsa ta dauke,ya soma kokawar qwato numfashinsa,wanda bata daga masa
qafa ba ta fara aike masa da qarin wasu saqonnin da suka birkitashi......suka
sakashi ya soma mance wayeshi?,a wacce DUNIYAR yake?,meye matsalarsa a rayuwama
gaba daya?.

Tayi masa ba zata ta qarshen qarshe......ta kuma tashi kansa da wasu
irin zafafan salon da suka saka har ya manta meye ma yakeyi?. Wani irin saqo take
aike masa me cike da jan rai......sai taji ya gaza jurewa ya juyeta ya maidata
qasa.

Nutsuwarta taso maidawa jikinta,ta dafe qirjinsa a sanda yayi mata rumfa
tana kallon narkakun idanunsa da suka sauya launi. Dubanta yayi shima yana neman
qarin bayani,saita masa nuni da hannusa me ciwo da ya dafesu ya aza masa nauyi
kaman ya manta yana da rauni.

"Kina tsoron jini ne?" Ya tambayeta ha tare daya kalli inda take nuna masa din ba.
Fuska tadan bata daban,ta sani ba'a fiya son yayi wani aiki sosai da hannun
ba,saboda a samu ya warke da wuri.....kuma wannan fitinar da yakeso yayin tabbas
zata iya maida ciwon danye.

"Alright" Ya fadi da hanzari cikin qasa da second daya yana hautsinata ya koma
qasan ita kuma ta koma sama ta maye gurbinsa.

"You're in charge now" Ya fadi yana dage mata girarsa. Wani kunya ya kamata,ta cusa
fuskarta cikin ni'imtaccen qirjinsa da bata gajiya da wanzuwa akai.

"I give my self to you....i surrender to your will....play your role well" Ya fada
muryarsa can qasan maqoshi.

Duk yadda yake buri hakane ya kasance,duk yadda yake da buqata haka tayi
masa. Abun ya gigitashi ya sanyashi fita a hayyacinsa,wasu maganganun daya dinga yi
sai sukayi mata mugun nauyi,har ta dinga jin daga wannan ranar kaman ba zata iya
sake hada ido dashi ba.

Wani sabon amarcin aka balle a asibitin tsakanin fu'ad da sabreen
din,ba tare da kowa ya kula da lalurar da yake tare da shi ba.

Hankalinta ya tashi bayan komai ya lafa da taga bandages din hannunshi
sunyi staining da jini.

"Ka gani ko?,dama bana gaya maka ba?" Ta fada a narke muryarta tana rawa tana
shirin sakin kuka. Hannun nasa ya kalla ya saki murmushi yana jawota jikinsa
sosai,duk qoqarin sauka da takeyi daga jikin nasa amma ya hanata.

"Please stay with me.....i could use some relaxation time......sai muyi wanka"

"Ciwonka fa?" Ta tambaya a mamakance tana kallon fuskarsa da tuni ya maida idanunsa
ya lumshe yana fidda wani sassanyan murmushi.

"Forget about.....zasu gyara zuwa safe" Ta sake motsawa zatayi magana ya dora
yatsansa akan labbansa.
"Shshshsh" Yace da ita,dole ta maida kanta ta kwantar,saidai hankalinta gaba daya
yana kan ciwon.

Bayan sun idar da sallar asuba,tana kammala azkar dinta ta koma toilet
don yin fitsari saiga jini. Ta razana sosai ta ware dukka idanunta tana duban
jinin. Jikinta ta dauki rawa gaba daya,bata da wani qwarin daga murya ta
kirashi,tana ma ganin kaman bata lokaci ne,sai kawai ta fito a toilet din da wani
irin sauri.

Kansa ya daga yana kallonta sanda ta fito din,sai shima ya ware
idonsa yana dubanta kafin ya miqe da sauri ganin yanayinta. Sosai ya riqeta yana
tambayarta

"What's happening?.....relax.....gayamin" Pant dinta kawai ta daga masa,sai ya zare
idanunsa waje kaman zasu fado.

"Oh shit......subhanallah" Ya fadi yana jin gaba daya ya gama firgicewa. Cikin kula
da takatsantsan ya maidata gadonsa ya kwantar da ita.

"Lemme call a doctor" Ya fada yana fita a dakin da sauri don yana ganin tsaiwa
kiransa ta landline ma bata lokaci ne.

Su biyu suka shigo,shi da wata likitan mace daban,yanata masa magana
akan hannunsa amma bata wannan yake ba.

"Scan zamu fara yi mata don tabbatar da lafiyar babies din" Likitan ta fada tana
qarasawa gaban gadon sabreen din.

Maida dubansa likitan yayi a kansa.

"Hannunka ya akayi yayi staining haka?" Ya tambayi fu'ad din wanda hankalinsa duka
yake kan sabreen wadda dr din ta fara jawo na'urar scan wanda take a dakin
permanently.

Kafin yace komai anyi knocking qofar an turo an kuma shigo. Farouq ne
shida musaddiq dauke da breakfast da anni ke dafa musu.

Likitanne ya amsa sallaman,farouq ya qaraso dakin fuskarsa dauke da
alamun tambayar abinda yake faruwa.

"Lafiya dude?" Farouq ya tambayi fu'ad yana qarasawa kusa dashi. Bai amsa masa
ba,ya taka ya matsa gaban inda su sabreen suke ya jawo curtain divider ya rufesu
daidai sanda yaji tana tambayar sabreen din

"Kinyi wani aiki me nauyi ne sosai?" Amsa mata tayi da a'ah....still ta sake
tambaya.

"Ko kunyi mu'amala?". Shuru tayi tana jin kunya na dawainiya da ita,fu'ad da
hankalinsa ke wajen ya sauke hannayensa daya goya a qirjinsa yana fadin.

"Kiyi checking baby din kawai madam"

"Okay sir" Ta amsa masa a ladabce.

Daidai lokacin wani ma'aikacin jinya ya qaraso yana tura medication
cart dake dauke da bandages da sauran kayan dressing.

"Your hand sir" Dr din ya sake fadi yana duban fu'ad tare da masa nuni da abun
zama.
Sai daya waiwaya zai zauna din suka hada idanu da farouq,kai ya dauke yana
hade rai,sai shima farouq din ya basar yana girgiza kai.

Ana mata scan din likitan yana ware wancan bandage din a
hankali,farouq yana daga zaune a gabanshi yana danne dariyarsa. Ya wani maze sai
cin magani yakeyi?,karon farko da ya fuskanci fu'ad din baya son kallonshi. Koda
ba'ayi bayanin komai ba farouq din ya fahimci aika aika akayi a dakin a daren
jiya,saidai fatarsa daya babies dinsu ya zaman lafiya suke.

"Wow......unbelievable" Muryar likitan ta fita da wani irin sound da yaja
hankalinsu su duka. Kasa jurewa fu'ad din yayi,ya dagawa likitan hannu.

"Wait..." Sai kawai ya miqe yana danne sauran bandage din da ba'a gama cirewa ba.

Kai tsaye ya kutsa tsakanin curtains din ya shiga.

"Triplets ne sir" Likitan ta sake fada da wani kwantaccen murmushi saman fuskarta.
Idanu kawai ya zurawa na'aurar qirjinsa na harbawa,wani bahagon farinciki yana son
bugar dashi. Zooming na scan din tayi,sai gashi ya nuna wasu gurabe guda uku.

"Gasu a nan sir......congratulations" Ta fada tana sakin dariya cikin nishadi.

"Alhamdulillah.......alhamdulillah" Farouq da yakeji kaman yayi tsuntsuwa ya shigo
a nuna masa shima ya fada yana murza hannayensa bakinsa ya gaza rufuwa.

Idanunsa ya lumshe sannna ya budesu,yana so yaji mafarki yakeyi ko kuma
idanunsa biyu.

"Subhanallahi wabu hamdih.....subhanallahilazeem,Alhamdulillah......alhamdulillah
hamdan kaseeran dayyiban mubarakan fihi....." Ya fada yana yin qasa da kansa yana
jin wani abu yana taso masa. Wanne abu zaiyiwa Allah ubangiji da zai da dadawa
Allah?,wanne abu zai yiwa Allah mafi soyuwa a wajen ubangiji.....duk da ya ambaci
wadancan kalmomin,masu sauqi a harshe.....masu nauyi a mizani.......masoya a wajen
Allah(subhanallahi wa bi hamdih,subhanallahil azeem,kada ki wasa da yawan
maimaitasu,kalmomi ne masoya a wajen Allah,wato wadanda Allah yake sonsu qwarai,ga
nauyi a mizani,zasu qarawa ayyukanki nauyi ranar qiyama,ranar da ake auna ayyuka
akan ma'auni).

"Thanks.....thank you so much" Ya fada yana isa inda sabreen din take. Hannunsa ya
dora saman kanta yana ranqwafawa a samanta,sai a sannan ya dauke idonsa daga kan
screen din yan jin kamar zaiga yaran be baro baro a ciki. Idanunsu suka hadu waje
daya,saita fara sakar masa murmushi. Kai yake jijjigawa kawai ya kasa magana,sai ta
miqa masa hannunta shima kai tsaye ya bata nashi,ya sunkuya yana sumbatar mararta.

"You're my world sabbrrrr.......da nace ke DUNIYATA ce da gaske ke din duniyata
ce.......ya rabbb......ka tsaremin wannan baiwar taka da irin tsaronka ita da duk
abinda take dauke dashi......yadda mahaifanta suka haifamin alkhairin
rayuwata......ubangiji ka shimfida musu aljannarka cikin qaburburansu........"

"Allah ya hada da abba daya zama nagartaccen uban daya nunawa yaransa muhimmancin
mace" Ta tari numfashinsa tana jin zuciyarta na karyewa da irin addu'arsa akan
mahaifanta wanda bata taba jin irinta ba. Wata kyakkyawar runguma yayi mata wadda
ta sanya likitan ficewa daga cikin labulen ta basu guri. Wannan karon ba fu'ad
kadai ba.....hatta da sabreen saida fuskarta ta jiqe da hawayen farinciki. Ya fita
jarumta a wannan karon,don shi ya soma janye jikinsa yana goge mata fuskar.

"Kada ki tashi hankalin babies dinmu......ya isa.....is okay ko?" Ya fada bayan ya
gama goge mata fuskar ya sunkunya ya sumbaceta a goshi.
"Sir......zaa qarasa duba ciwon?" Likitan yace dashi,sai ya miqawa sabreen daya
hannun nasa ya dagata ta zauna ya yaye labulen bayan ya tabbatar ko ina a jikinta a
rufe yake.

Hugging nasa farouq yayi wanda ya kasa zama saboda farinciki,fu'ad ya
dan bubbuga bayansa yana murmushi

"Congratulations dude....." Kai tsaye ya taya farouq din murna,don ya sani suna
raye ko basa raye,zai amsa sunan mahaifinsu ne kawai wanda yayi cikinsu,amma sunan
uba farouq keda wannan matsayin.

"Thank you dude.....na gode" Farouq ya fadi murmushi yana qin barin fuskarsa.

Likitan yana duba ciwon daya doctor din tana sake yiwa sabreen
bayani.

"Duka fetuses din suna lafiya qalau,ki zauna sosai ki huta yau gaba daya,zai tsaya
nan bada jimawa ba....sai prenatal medication dinki da zaki ci gaba da sha da kula
dasu.....ina miki fatan haihuwa sassauqa da lafiyayyun Yara".

"Na gode" Sabreen din ta fada tana murmushi. A yau din jinta take wata ta
daban,jinta take ta musamman,yau ita sabreen itace a mazaunin uwa?,wadda zata kawo
wasu rayukan cikin duniya?,wasu halittun da suka kasance jininta?,jinin muhammad
fuad dukka a cakude a jikinsu?.

Duk bayan minti daya sai ya daga kai ya kalleta,daga qarshe parlor suka
koma don Dr din ya qarasa dubashi,sai yake jinsa ba tsaro,gani yake kaman yana
kalle masa ita.

"Amazing....haka kake da quick healing?" Likitan ya tambaya da mamaki yana murmushi
sannan ya dora.

"Nayi mamakin ganin saurin warkewar ciwon,kadanne ya rage banda an bashi pressure
me yawa ba da bazai fidda jini ba.....za'a maida sabon bandage amma dan
kadan.....please next time kada a matseshi da yawa hakan zai bashi daman warkewa da
wuri".

" Ai basai ka fada bama likita,ni nan zanwa tufkar hanci" Farouq ya fada yana
bubbuda hanci. Harara fu'ad ya watsa masa,sannan ya maida harshensa zuwa hausa.

"Kada kiyi gigin cewa zaka kai qarata wajen anni....muddin ka rabani da duniyata
saina maida maka naka hannun agogon baya" Ya fada sounding seriously.

Dariya farouq ya tuntsure da ita,baisan ya akayi ya dagoshi haka da
wuri ba

"Ko bankai qararka wajen anni ba nasan nayi dakai ai" Ya amsa masa yana miqe
qafafunsa nishadance yana duba saqon fannarshi daya shigo masa.

Sai da likitan ya kammala komai ya fice sannan ya kalli farouq.

"Bani abinci malam.....haka ake jinyar?" Ya fada yana hararasa.

"Zan baka mana....kai banda ka fanshi kanki jiya zaka sake ganin face din angon
fanna ne?" Yadda yayi maganar ya sanya murmushi subucewa fuskar fu'ad,yakau da
kansa kawai yana murmushi.

Ya zuba masa komai amma sai yaga yayi gefe da wani babban mug.
"Wancan meye a ciki". Da hannu farouq ya nuna masa.

"Wannan?,maca and ginseng tea ne".

"Zubashi a nan" Ya fada yana nuna masa wani glass mug. Nesa farouq ya qarayi dashi.

"Kai ina......kaida wannan ai ba yanzu ba wallahi......kana wannan barnar xan barka
kaci gaba da shan wannan?,kayi haquri ku haifemin yarana lafiya....to daga nan har
china kuje saikun dawo". Idanunsa ya janye kawai bai

Please Login or Register in order to submit comment