You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

̶2
ⱧɄ₲Ʉ₥₳

𝙋𝘼𝙂𝙀 104


104


Kalmar 'ya'yana din kuwa ta daki zuciyar maamah da wani matsanancin
kishi. Wato har fu'ad dinma ya tashi daga sunan dan riqo ya koma danta?.

"Aah anni....inata dai qoqari" Ya amsa mata yana fahimtar inda saqonta yasa gaba.
Kai ta jijjjiga

"Zan sabawa fu'ad kuwa muddin qafafunsa yasa ya tafi bai sanarwa iyayensa
ba.....idan kuma wani keda hannu kan hakan....na rantse da Allah ko waye bazan
barshi ba.....tashi kaje,tsakanin yau da gobe nakeso ka lalubomin shi" Kai kawai
kada mata yana tashi,maimakon ya koma daki sai ya juya yana sake ficewa a gidan.

Yau din Jordan ya nema kai tsaye,shima ya gaya masa tun randa suka
fita tare bai sake ganinsa ba. Ci gaba yayi da bibiyarsa ta waya amma a banza,sai
ya koma ya lalubi system dinsa da yakan ajiye schedule nasa da komai. Yasan
password nasa da komai don haka kai tsaye ya bude ya shiga. Zallar aminci ne da
yarda da kuma dawwamammiyar qauna,shima iya abinda yaje nema ya shiga ya duba kawai
ya fito. Bai samu bayanin komai ba,hasalima bai ajiye inda zashi ba banda ranar da
sukayi zasu fita din satin baya daya wuce ranar daya bace kenan.

Awa daya ya bawa ransa zai sake kiransa,idan bai sameshi ba kuwa aikin
safa da marwa ya sameshi cikin tsibirin Maldives,wala'alla sai yayi hayar boat ko
skis ya gewaye tsibirin Maldives ya nemowa anni 'ya'yanta.

"Oops.....wannan soyayya taku nima ta jefani kwale kwale.....where are
you?.....anni ke kika jawo,da kin damqa masa matarsa salin alin dani kaina ban
tsinciki kaina a halin da nake ciki ba" Ya fada yana furzar da iska daga bakinsa
gami da yin relaxing jikin kujera yana lumshe ido. Murmushi ne kuma ya qwace masa
saboda hango fuskar maamah da yayi,tayi wani laushi da yaushi ba tare data fahimci
hakan ba

"Wato anni kema kinsan takan tsiya?" Ya fada qasan ransa yana komawa ya kwanta
sosai saman sofa din.


★Gaba daya ya wani narke saman sofa din bayan ya miqe qafafunsa saman table
din gabansa daya dora system dinsa. Tun dazun ya kunna system din amma ya gaza saka
mata password ya budeta. Sai yau yakejin ya kamata ko farouq yasan inda yake,don
yayi imanin ko kowa bai nemesa ba anni zata nemesa,zata kuma damu da rashin
ganinsu.

Gilmawarta kadai a gabansa yana debe hankali daga gangar jikinsa,a
kwanakin nan shi kansa yasan mahaukacin so yake mata wanda baisan adadinsa ba. Idan
ya kebe yana salla,yana yawan tuhumar kansa wanne irin so yake mata wannana?,abu
daya ke sanya masa relief addu'o'in daya debe tsahon rayuwarsa yana yi akan.

"Ya Allah,idan ka tashi dasamin soyayyar wata 'ya mace.....ka jarabceni da soyayyar
da zan iya.....ka dasamin soyayyar macen data dace dani ta dace da rayuwar
'ya'yana,macen da zata soni itama sama da yadda nakeson kaina....macen da ni karan
kaina takeso ba abinda na mallaka ba.....macen da zata fifitani sama da kowa da
komai....tsaftatacciyar mace.....kamila aaqila....aabida,ya Allah,kada ka jarabceni
yadda ka jarrabi mahaifina......ubangiji ka azurtani nida dan uwana da matayen da
zasu rufe ciwukan da suke cikin zukatanmu kaman yadda kayi mana baiwa da samun
anni". Idan ya tuna wannan addu'ar sai yaji son da yakewa sabreen din ba komai
bane.....yayi imanin Allah bazai wofantar da addu'ar da aka dauki tsahon lokaci ana
qwanqwasa qofarsa saboda ita ba.

Duk wasu kaya nata tunda sukazo wajen tayi bankwana dasu,daga kayan
safiya zuwa na dare duka tana shigarta ne a bisa zabinsa. Tun tana dojewa har ta
fara ragewa,don idanma tace zata musa shi zai tubeta ya kuma sanya matan. Yayi
amfani sosai da damarsa......yayi amfani da tsoronta da gurin ya mata wani irin
sabo da kwana a jikinsa,ya sanya wata shaquwa me qarfi a zuciyarta da wannan. Ranar
farko da hakan ta fara kasancewa.....
Tayi wani irin bacci da idan zata iya tunawa irin baccin qarshe da tayi saman
cinyar ummenta ranar da asthma dinta ya tashi. But bacci cikin jikinsa yana da wasu
qa'idoji da ta kasa kiyayesu har yanzu. Wani sabon abune kwanciya hakanan ba tare
data rabawa jikinta komai ba....shi kuma kullum sai ya maimaita mata bayan ya
maidata yadda yake

"That's my rules". Daga qarshe wayo yake mats,wayon da yake sanyawa washegari ta
tashi da matsananciyar kunyarsa da bata iya hada idanu dashi.

Duk yadda taso ta gano yadda yake iya cimmata ya firgitata ya fiddata
daga saitinta ta kaucewa wannan abun amma ta gagara......wani lokaci har jira
takeyi yayi wani motsi don tayi masa tawaye.....to amma da an iso gurin sai ya
sanyata ta manta wacece a ina kuma take?,sai bayan qura ta lafa ta isheshi da kukan
banza da qorafi. Wani lokaci ya biye mata ya lalace wajen rarrashi.....wani lokaci
kuma yaja hancinta

"Har yanzu baki fara koyan maida martani ba......am dreaming about it,saikin gama
kwashe alkhairan kuma ayitamin kukan abunga...." Gulma tason yakeson cewa,fadi ne
kawai bazaiyi ba.

"Sabrrrr" Ya kirata jikinsa yana sake macewa. Wani irin Palazzo ne a jikinta da
wata 'yar top data zauna mata sosai a jikinta,ta kuma bayyana masa albarkatun
qirjinta yadda yakeso. Kanta yasha hair pins wanda shi ya zauna ya shiryata,ya kuma
gyara mata kan yadda yakeson gani.

Yasha wahala sosai wajen nesanta kanshi da mata,ya kame kansa,ya runtse
ganinsa ya kuma kiyaye al'aurarsa.....wannan ya sanya yaci alwashin ko meye dake
burgeshi game da mace sai yayi qara'insa a jikin matarsa......sai ya kalla yadda
ranshi keso. Yana ankare da ita a takure taka,yasan zaayi hakan,don shima ko sau
daya bai bari idanunsa sun huta da kallonta ba.

Duk sanda yaga dari darinta akan sakin jiki ga d'a namijin da ya
kasance mijinta sai yaji wani qunan rai da bacin rai ga wadanda suka dinga sadakar
mutuncinta,suka kuma dangantata da sunan KARUWA.

"Zo kiji" Ya fada a galabaice yana miqa mata hannunsa sanda tazo gilmashi. Baima
bata lokacin tunani ba ya sanya hannunsa ya jawota saman cinyarsa yadda ya saba
mata. Sam bata masa nauyi wajen dauka ko jawowa,kaman wata leda yake daukanta.

Matseta yayi a jikinsa yana rungumeta sosai,ya kuma dauko system din
ya aza saman cinyarta yana saka password dinsa.

"Massages nakeson dubawa amma gaba daya kin hanani sukuni.....sai rarrabamin
hankali kike,gwara ki zauna mu duba tare,wataqila nafi samun nutsuwar dubawar"

"Me nayi kuma?" Ta tambaya a shagwabe. Hancinta yaja yana kashe mata idanu
"Aah hajiyata....komai mafa kinyi.....satar da kikayi a gangar jikin muhammad
fu'ad.....zuciyarsa dinnan ta tafi kenan,bana jin zata dawo masa har abada" Ya fada
yana sakinta gami da fara buda saqon farko wanda ya sakashi sakin murmushi ganin
saqonnin farouq a jejjere a jejjere. Na qarshen ya fara budawa wanda bai wuce
mintuna talatin da turowa ba.

_"You're rocking the boat,you're fanning the flames.......dude.....ka shiga
hankalinka ka dawo gida.....yaqi zai barke tsakanin ummominka.....am serious dude"_
shine saqon qarshe daya gani mintuna talatin baya. Dan murmushi ya saki yana tabe
baki,yasan abinda farouq zai masa qarya.....ya kuma san wanda bazai masa qarya
ba,wannan statement din nashi yasan real ne ba wasa yake masa ba,sai ya danna
replies ya soma bashi amsa

_"Step back BB.....leave them.....nasan anni ba zata biye abun yayi worst
ba.....ina nan ina neman hadin kan DUNIYATA.....zamu hadu a airport ranar Tuesday
to makka in sha Allah"_ yana tura masa ya koma duba ragowar saqonni masu muhimmanci
yana ragewa,saidai kusan bayan kowanne minti daya sai ya tura kansa cikin rigar ta.
Tureshi tayi har sau biyu,ana ukun yayi warning nata

"Idan kika sake ban yafe ba" Idanunta dukka ta fidda idanunta waje tana dubansa a
mamakance,rai ya hada

"Yes....aikin karanta walau alattanur ko wajen rumaisa?" Qasa tayi da kanta tana
tunawa da hadisin,ya kuma aza mata wata irin kunyarsa sosai. Yadda yaga tayi ya
masa dadi.......da gaske karatun yana kama zuciyarta har haka,tsaf fa zai iya
komawa wajen malam ci gaba da daukan karatuttukan da zasu sanyashi sake sanyata ta
sake zama sassanya.....buqatar maje haji sallah. Yadda tayin ya bashi daman dauke
hannuwansa daga can system din ya maida inda yafi muradi da wani tattausan yanayi
yana sake shigewa jikinta.

"So kike na zama dan is......" Batasan ta saka tafin hannunta saman bakinsa
ba.....batasan sadda hakan ta kasance ba sai data tsinciki narkakkun idanunsa cikin
nata,hakan sai ya zama kaman wani lasisi ta bashi kenan daya sakashi yunqurawa
dauke da ita,daidai sanda saqon farouq da mamakin fu'ad din ya kasheshi ya shigo
system din,ta baya ya saka qafa ya tureta ba tare daya damu da idan ta fadi zata
iya fashewa ba

"Just leave me have this moment,don't dampen the mood" Yayi maganan kaman wanda
yasha giya ya maku,saidai duk da hakan abun mamakin shine,sanda ya mata masauki
saman tattausan gadon da harshensa dake hardewa yace da ita.

"Let me relish this moment,and then I'll tell you more about fu'ad. Ya kamata kisan
waye fu'ad......am ready to make you DUNIYATA da gasken gaske.......inason kisan
komai nawa da gaske......".




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

̶B̶O̶O̶K ̶2

ⱧɄ₲Ʉ₥₳
𝙋𝘼𝙂𝙀 105


105


_Barkanmu da dawowa,fatan munyi sallah lpy,ubangiji ya maimaita mana cikin lafiya
aminci da kwanciyar hankali_




Batasan me yake tsarga mata ba duk sanda ya kirata ta DUNIYATA ba,wani
irin feeling takeji yana motsa zuciyarta,wanda tun tana qaryatawa har ta soma yarda
tana jin wani abu a ran nata duk sanda ya ambaci sunan. Yafi mata dadi ya kirata
DUNIYATA akan ya kirata my world.

Susutacciya ya maidata yadda ta fahimci ya soma maidata a wadannan
kwanakin,lallai so yake sai ya matso komai a kansa dake cikin zuciyarta. Ta sani
tabbas muddin zaici gaba da wannan salon......muddin zaici gaba da tafiyar da ita
da wannan tsumammen yanayin to ba shakka zata gaza boye duk wani abu dake
zuciyartata kuwa.......yana kuma dab da maidata mahaukaciya da gasken gaske,zata
rasa duk wannan dauriyar tata da basarwa da takeyi.

D'aya bayan daya ya dinga zare hair pins din da dama shi ya zauna ya
jera mata su,duk daya idan ya zare yana ware gashinta me tsaho baqi da santsi,wanda
zuwa yanzun hair mist dinsu shi da ita ya zama guda daya,kaman yadda mayataccen
mouth fresh dinsu ya zama products daya. Kusan komai nata cikin kwanakinnan ya
canza mata zuwa kalar wanda yakeso,qamshinta,creams lip gloss da komai
ma......komai kuma me tsada ne fiye da tunaninta,ranar data duba kudin perfume din
daya sauya mata zaune kawai tayi tana binsa da kallo ba tare da yasan ma me ake ba.
Su huda na wata duniyar duk da tayi imanin suna cikin kulawa......amma ita tana nan
tana rayuwar da take ganin tafi qarfin matsayinta?.

Sai daya zare mata duk pins din,sannan ya kutsa yatsunsa cikin sumarta
yana barbazata yadda yakeso,ta fahimci tana daya daga cikin abubuwan da suke
matuqar burgeshi ga diya mace. Kaman yasan abinda yake saqawa muryarsa me kama data
mashaya ta sauka a kunnenta

"I love it duniyata......kina da komai da nakeso..... Please ki sake bani dama na
gina miki wasu dabi'u.......na dade ina kame kaina daga kallon Haram da kuma
zina.......i only want my pure halal.......please ki qarasa mallakamin kanki da
rayuwarki gaba daya I want the best from you,i want the best relationship with you"
Ya qarashe maganar yana mata wata kyakkyawar runguma kafin ya fara maidata
birkitacciya yana cireta daga ainihin tunani nutsuwa da saitinta. Batasan wanne abu
daban yake buqata daga gareta ba.....batasan wanne best yake nema ba bayan duka
fitar da ita daga tsarinta da yakeyi. Yana sakata jin wani irin nauyi da kunya da
bata taba tsintar kanta a ciki ba.

Ko yanxun da qura ta lafa tana gaban madubi yana tsaye a bayanta yana
bata dan kunnenta tana maidawa daya bayan daya,ya kafeta da idanu murmushi na fita
daga kan fuskarsa qasa qasa. Idan yana kallon fuskarta a irin wannan yanayin sai
komai ya dinga dawo masa. Idonsa ya lumshe yana jin zuciyarsa kaman zai fashe don
tsananin cika da qaunarta da sukayi,yadda yakeji a duk sanda suka kasance da
juna.....yasha imagination abun idan tana participating itama,yana kwadayin yaga
wannan lokacin.

Taku uku ya qara ya hade tazarar dake tsakaninsu,ya dora fuskarsa
saman kafadarta yana dubansu a tare shi da ita ta fuskar madubin.

"Idan Allah ya bamu 'ya'ya......wanne irin kyau xasuyi my world?". Wani kunya ya
saukar mata,tayi qasa da kanta qaramin murmushi yana subuce mata. Shima murmushin
ya saki,a duk sanda kunya haka ta bayyana saman fuskarta tana mata wani irin
kebantaccen kyau na musamman.

"DUNIYATA.......Why aren't you responding?" Idanu ta daga alamun tambaya ba tare
data yarda ta kalli tsakiyar idonsa ba. Ya fahimci haka,sai yasa yatsunsa yayi gefe
da gashinta yana cusa bakinsa ta kunnenta abinda ya sanya tsigar jikinta tashi.

"On bed dear......" Ta fahimci inda ya dosa,don haka bata bari ya qarasa bama ta
soma neman inda zata boye fuskarta. Ire iren rashin kunyarsa suna sakata jin wani
irin nauyi ba kadan ba.

"Ko sai randa aka yanke shawarar ana sona ko ba'a sona?" Ya sassauta muryarsa yana
fadi qasa qasa gami da riqe hannayenta da kyau qaramin murmushi yana subuce masa.

"I hope wannan ranan zata zo soon.......na matsu,ko akwai wani abu da ake buqatar
nayi da za'a gayan I LOVE YOU MUHAMMAD FU'AD JADDA?....." Ya tambayeta da gasken
gaske,har qasan zuciyarsa yana sha'awan jin ta fadi hakan. Kai ta girgiza tana
basarwa,neman tserewa takeyi ya kuma fuskanceta,don haka ya sunkuceta kawai yana
nufan stairs din da sukayi dakin qasa.

Idanu ta fitar waje,har ha Allah tsoron dakin qasan nan takeyi,yatsa
ya saka ya lakuce mata hanci yana girgiza kai.

"Relax.....you're safe my world.....bazan taba yin wasa da DUNIYATA ba fa". Kasa ce
masa komai tayi sai idanu data lumshe tana shaqar daddadan qamshinsa daya cika mata
hanci,ta kwantar da kanta a qirjinsa tana jin bugun zuciyarsa. Batasan me yasa ko
yaushe bugun zuciyarsa daban yake ba,wani bugu ne me sauri sauri wanda tasan
qa'idan bugun baikai haka sauri ba. Idanunta saman dakin duke kallo,yadda ruwa yake
gudu saman kansu tare da kifaye kala kala ba tare da ko damshin ruwa ko qwaya daya
ya tabasu ba,ta dauke idanu tana tasbihi ga ubangijinta.

Saman lafiyayyen gadon dakin ya ajiyeta,ya dawo gabanta ya tsugunna yana
zagaye hannuwansa da qugunta.

"Muhammad fuad jadda.......d'an alhj Muhammad ne,haifaffen bafulatanin
mambila......,ta gefan mahaifiya kuma...." Sai ya danyi shuru yana hadiyar
numfashi.

"Mariya da akafi sani da maamah itace mahaifiyata.....bafulatanar mayo belwa ganye
local government" Hannuwanta ya riqe a tausashe cikin nasa zuciyarsa na karyewa.

"Lokaci na farko da zan bude bakina na fasawa wani dan adam daban rayuwata.....waye
ni?....me naji me na fuskanta?.....sabrrrrrr.....abbana......abbana yana cikin
jerin sahun mutumin da nafiso nafi qauna kaf cikin rayuwata.......saidai mun
rasashi a sanda mukafi qaunarsa......mun rasashi a sanda mukafi buqatarsa......mun
rasashi saboda wa'adinsa ya cika.....amma da taimakon maamah". Kai ta daga tana
dubansa,tana ji yana tayar mata da wani mikin ciwo dake zuciyarta.

Kai ya gyada mata idanunsa suna sauya launi.

"Ta shayar dashi guba......ta dura masa miyagun maganganu da suka qarasa illata
gangar jikinsa da zuciyarsa,suka Haifa masa da ciwon zuciya......kalmomin bakin
maamah su suka jefa abba na a matsanancin ciwo......ciwon da haquri ya gadar dashi
dashi,ya kuma ci gaba da tara masa guba na maganganun da suka zama silar fashewar
zuciyarsa daga qarshe. Tun a gaban idanunsa muje ganin qasqanci da wulaqanci,ba
wanda yake samun tausasawa ko kulawa daga gareta,daga shi mijinta harmu
'ya'yanta......bazan boye miki komai ba......bamusan dadin uwa ba,bamusan wani abu
da ake kira dadi tsakanin mahaifiya da 'ya'yanta ba,mun rayu tamkar irin rayuwar da
bawa zaiyi a hannun ubangidansa,walwala 'yanci da farinciki dukka yayi mana
qaura,mun rayu tamkar agololi kuma 'ya'yan riqo......abbanmu kuma ya zama tamkar
wani yaro gida bame gida ba......ba abinda tafi bawa mutunci da kima sama da KUDI
sama da tayi KUDI sama da abbanmu dole ya zama me KUDI ya nemo KUDIn da zatayi
kalar rayuwar da takeso,yayi lafiya ko kada yayi......ya rayu ko kada ya rayu,muyi
lafiya tarbiyya ilimi mu tsaftatu mu qoshi duk basa cikin lissafinta,abinda ya
dameta shine KUDI.....sabrrrrr..... Mun rayu cikin qasqantacciyar rayuwar da
al'umma suka gaza janmu a jiki a garin da bamu da kowa,kowa yana ganin tunda wadda
tayi silar zuwanmu duniya ta gaza tallafawa da tausayawa rayuwarmu,lallai mudin
akwai wani abun aibu ne a tattare damu. Taji a rant ba zata iya rayuwa damu ba,ba
zata iya zama damu bs,ta watsar damu da abba dake buqatarta saboda matsanancin
ciwon zuciya dake sake kwantar dashi....duk inda abba bai qwallafa rai a soyayyarta
ba,tayi nesa dashi shi yafi alkhairi,kunnuwansa xasu daina kwana su wayi gari da
jin munanan kalmominta a kansa wanda hakan shizai bashi lafiya da wuri.....saidai
kuma sonta ya zame masa jarrabin rayuwa,ya kasa haqura da nesanta kanta damu da
tayi,ya sake zame masa silar hauhawar ciwonsa. Nayi kwasar kashi......nayi aikin
bola da hannuwana duk don na kula da musaddiq da abbana......nayi sharar kasuwa
nayi ta kwata har bansan iyakarsu ba kawai don na samo abinda xan kula da abbana da
musaddiq.......munci abincin bola saboda gudun yunwa kada ta halakamu.......na
kwana da GAWAr abbana.......na kwana da gawar mahaifiyar abbana JADDA saman cinyata
dukkansu ba tare da nasan mutuwa sukayi ba ko bacci?,naci gaba da gadin gawarsu ba
tare da nasan ya akewa gawa ba?,a shekarun da duka duka baifi a koreka daga bakin
gawa ba idan kana da gata don kada kaga abinda shekarunka basukai ba. Jadda tazo
mana da wani irin gata da muka dinga tunanin wahalarmj ta yanke......ta saida duk
komai nata don tazo ta kula damu......ta bamu wani jin dadi wanda ko maamah da tayi
silar zuwanmu duniyata tsahon shekarun da mukayi tare da ita bata taba bamu irinsa
ba. Saidai sanda muke tsaka d wannan tunanin ashe ragowar kwanakinta na rayuwa yazo
qararwa tare damu ajalinta yazo mata a kusa.....ta sake kwanciya ta barmu a wani
irin yanayi. Daga sannan muka sake gane meye ma'anar rayuwa?,muna ta tunanin maamah
zataji labarin komai......zataji tausayinmu ta dawo garemu amma inaaa......wanda
yayi nisa bayajin kira........wata kalma da maqocinmu ya fada a kanta sanda ya dawo
daga kudu yace mana ya ganta a can.......taqi barin raina da zuciyata.......har
yanzu da ita nake kallonta.......bansan ranar da zata bar zuciyata
ba.........maamah dinnan dai da daga qarshe naji duk duniya ba wani abu da nake
qyamatar ya kusanci inda muke......itace silar mutuwar abba......ke daya kikasan
wannan a duniya......na kamata har sau uku tana ciyar dashi da abubuwan da likita
ya hanashi ci saboda suna tunzira ciwonsa.......suna kuma iya sanyawa komai ya faru
dashi ciki harda rasa rayuwanshi......a dukk ukun nan dana kamata tayi alqawarin ba
zata qara ba.....mantawa takeyi ne......na fahimci abinda ya sanyata take aikata
haka ta hirarta da qawarta da har yanxun nake tunanin kamar matar nan harira da
suke tare ne......so take ta kashe auren,so take abbanmu ya saketa shi kuma
yaqi......tace tana buqatar tayi arziqo,tana buqatar freedom amma yaqi
sallamarta....wannan shine dalilinta......shine kuma silar tunzurar ciwonsa har ya
kaishi ga kushewarsa......ba ita ta kasheshi ba kenan sabrrrrr?" Yayi mata tambayar
da wani irin yanayi daya tsorata sabreen qwarai da gaske.......yanayin da yake
tabbatar mata wani abu ne guda daya da yake masa ciwo har yau har gobe a
zuciyarsa......salon tambayar data tabbatar ya jima yana so ya yiwa wani dan adam
ita......amma rashin jin kowa a matsayin na kusa da zuciyarsa sosai ya sanya ya
gaza furtawa kowa,yadda yayi tambayar kaman hankalinsa na neman gushewa daga
jikinsa sai ta kama kafadarsa da kyau tana riqewa kuka yana shirin qwace
mata......tana jin ashe suna da yawa irinsu wadanda suka rayu cikin wulaqantacciyar
rayuwa?......amma dashi dake da sauran uwa a raye........dasu da ba ko daya ga
dangi masu tsananin jifa da zumunci waye yafi rashin sa'a.

"Sabrrrr" Ya rigata sakeyin magana duk da tana buqatar magana dashi.
"Idan kika gwada yimin abinda maamah ta yiwa abbana......nima mutuwa zanyi kaman
abba.......saboda na fahimci zuciyata irin tashi ce......bamu iya soyayyar qarya
ba,bamu iya soyayya da wasa ba,bamu iya yiwa masoyi qaramin riqo ba.......a
halittarmu yake.......wannan ya sanya na tsani soyayya na kuma tsani kowacce 'ya
Mace......anni ce mace qwaya daya data fara samun qauna irin ta uwa daga gareni
bayan faruwar komai......amma hatta da amna bata samu komai daga gareni ba sai
sanda naga tana shirin mutuwa ta barmu........bazan jure ba sabrrrrr idan kikace
zaki gujeni......bazan iya dauka ba idan kika ce zaki barni sabrrrrr,da gaske nake
nima mutuwa zanyi" Ya qarasa fada muryarsa da dukkanin jikinsa suna wani irin
rawa,tabbacin ya tabo mikin da baida kamarsa a rayuwarsa.

Gaba daya sai ta rude,ta rasa yadda zatayi dashi,ga wani irin ciwo
daya tayar mata wanda baida magani illa itama tabar hawayen idanunta su sauka ko
xata rage abinda takeji tsakanin qirjinta zuwa zuciyarta.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

̶B̶O̶O̶K ̶2

ⱧɄ₲Ʉ₥₳

𝙋𝘼𝙂𝙀 106


106


"Kasan wace sabreen din da kake muradin ta tabbata a matsayin taka?". Ta
fada muryarta na yayyankewa. Wani kyakkyawan riqo yayi mata yana sakata cikin
jikinsa.

"Na sani......na sani,iya abinda kuma na sani a kanta ya isheni yanxu
haka......abinda ya ragemin ME YASA WANNAN TSAYAYYAR SABREEN DIN sauri bada kai ta
yarda da wannan muhammad jadda din?,shima bana fatan kiban labari,da kaina zan
lalubo......duk wanda keda hannu wajen maida sunanki wancan mummunan sunan baxai
shaba.....sai na hukuntashi" Ya fada jikinsa na daukar rawa gaba daya.

Luf sukayi a jikin junansu,kowa yana qoqarin controlling
yanayinsa,sannu a hankali yanayinsu ya fara daidaita,saidai kuma a hankali taji
jikinsa yana daukan wani irin dumi......kafin kace meye wannan zazzafan zazzabi ya
rufeshi me tsananin zafin da har cikin fatarta da tsokarta takejin zafinsa.

Rudewa tayi sosai,ta fara qoqarin zamewa daga jikinsa tana fadin.

"Zafin yayi yawa......yayi yawa ka bari a samo magani".

"Banaso ki kira mana kowa a gida.......inason kwanakin nan biyu da suka rage nayisu
dake.......banason kowa ya shigo tsakani" Ya fadi dumin numfashinsa yana saukar
mata saman goshinta. Kai ta girgixa hankalinta yana tashi.

"Jikinka yayi zafi da yawa...akwai buqatar temperature din yayi qasa". Sake sanyata
yayi a jikinsa ya lullubeta da kyau
"It's not......haka fever na yake......zai sauka" Ya fada yana lumshe idanunsa duk
kuwa da cewa yau zazzabin na daban yake jinsa,don har kusan cikin qasusuwansa
yakeji kaman ana karyasu,saidai kwanciyarta a jikinsa yafi masa komai a yanzu haka.

★Shi kadai ya dinga dariya sanda saqon fu'ad ya tarar dashi. Hannu yasa yana
shafa kwantaccen sajensa yana duban saqon yana sake karantawa. Wato ko yaya kusanci
yakai tsakaninka da iyaye akwai sanda soyayya da matar aure ke diban nasu kason
idan kusanci yakai kusanci. Bai taba tunanin akwai sanda fu'ad zai nemi kebewa shi
daya ya barsu tsahon kwanaki ba tare da ya buqaci kowa yasan inda yake ba....ko ya
rabi kowa ba. A nutse ya maida masa amsa sannan ya juya akalar motar yana komawa
gida don bawa anni saqon d'anta. Fitarsa dama kenan daga gidan yana tsammanin zai
iya samunsa a wani gurin,amma yanayin amsarsa kawai ya tabbatar masa ba zai ganshi
ba koda ya shiga neman nasa.

Suna dab da kammala kalbar da amna kewa annin ya shiga parlor
din,yadda ya barsu a daxun haka ya samesu,kowa zaune yana sabgar gabanshi.

"Anni.......sai kisa haquri,ba zaki samu ganin yaronki ba sai Thursday a
airport,haka yacemin" Ya fada yana daga kafadunsa. Maganan farouq taja hankalin
maamah duk da bata waiwaya sashensu ba bata kuma nuna taji abinda suke tattaunawa
ba,ta riqe waya kawai a hannunta kaman tana daddannawa amma maganganunsu take
saurara.

Qaramin murmushi anni ta saki,iya bada saqon da yayi a gaban maamah
dinma ya wadatar mata,tabbas zai isar mata da wani muhimmin saqo,duk da ta san
farouq din ya fadi ne kawai ba tare da wani nufi ko wata manufa ba,ya fada ne
kanshi tsaye.

"Indai suna lafiya alhamdulillah,lafiyarsu tafimin komai" Sosai maganar ta soki
maamah,ta tattaro wani yawu me tauri ta hadiye da qyar tana qoqarin daidaita
numfashinta.

"Na rantse da Allah yadda kika dasa baqinciki cikin rayuwata.....saina dasa miki
fiye dashi a taki rayuwar......indai har ban aikata haka ba lallai ba shakka ni
mariya 'yar zina nake" Ta fada cikin zuciyarta wata wutar daukan fansa tana ruruwa
cikin zuciyarta. A yanzun inda za'a bata bindiga.....aka ce ta kashe maqiyinta
qwaya daya da tafi tsana a duniya.....to xata nemo harsasai guda biyu ne,ta kashe
Alhaji hamza da ameenatu.....harsashinta na ukun kuwa muddin ya samu to sabreen ce
ta gaba. Tayi imanin bariki ce zallah......zallar barikice ta sanyata janye mata
yaro,wannan dukka plans din yarinyar ne,ita ta shirya ta tsara ta kuma gabatar,amma
indai da numfashi a gangar jikinta saita gaya fahimtar da ita tazarar shekaru

Please Login or Register in order to submit comment