You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kadan sannan tace

"Haka naji labari!"

"Amma kina da yaqinin ni na daukoki ko kawoki cikin gidan na maidaki sunan
matarsa?.......idan naso qasa da awa biyu rak! Zaki rasa wannan damar?" . Qaramar
dariya ta saki ma maamah din,ta gyara zamanta sosai tana kallon kanta a madubi. A
yau hirar nishadi take bata a maimakon razani da take samu a kwanakin baya da suka
shude.

"Kina zaton kina da wani makami da zaki iya fiddani daga gidan yaron
naki?........kiyi haquri da abinda zance......amma ko shaidan a yanzu bai isa ya
fiddani daga gidan yaron naki da kike tutiya ba........bana son danki ko kadan
bazan kuma taba sonshi ba......amma yadda kika sakoni cikin rayuwarku......kika
maidani matarsa da qarfin qwanji dana kudi.......to haka fitata daga gidansa da
rayuwarku zata kasande bisa zabin kaina a kuma duk sanda nayi niyya......so kibi a
hankali,bawai sonshi nake ba.....infact ma baiyimin ba.......amma bazan fita daga
rayuwarku ba har sai sanda nayi niyya"

"Qarya kike....baki isa ba!"

"Dama bance na isa ba......amma zan gwada saiki tayani tabbatarwa...."

"Kina kirawa kanki ruwa!,zaki iya rasa rayuwarki ta dalilin haka fa!"

"Bari na fara raba naki d'an da rayuwarsa tukunna ki fara ganin kalar wannan baqin
cikin kafin ki aiwatar a kaina......zan shayar dashi ruwan guba a ruwan shayinsa na
yanzu a maimakon tsubbace tsubbacenki....." Tana kaiwa nan ta kashe kiran tana ma
kashe wayar gaba daya.

Murmushi ta dinga yiwa kanta a madubi,hirar ta sanya mata nishadi
sosai,ko ba komai ta dasa mata tsoro da fargici tabbas na mintunan data ambata.

Da gasken haka shine ya faru. Wani irin gumi ya fara tsatstsafowa
maamah da wani irin kalar tashin hankali. Zuwa yanzu bata da tabbas akan
yarinyar.......tana ji a jikinta zata iya aikata komai da tace din. Kasa zama
tayi,jikinta yana rawa ta soma lalubar layin fu'ad tanason gargadarsa akan ya
kaucewa komai da zai fito a yanzu daga hannun yarinyar.

Kira kusan goma tayi masa a jere saidai ba wanda ya daga,abinda ya
sake tsananta tashin hankalinta kenan,ta dinga duban agogo tana qirga mitunan da
yarinyar ta kwasa mata.

Daidai lokacin ma shi ya jima a office. Ayyukane da yawa a gabansa
da suka hade masa saboda jiya bai samu yin komai ba a office din yayi baqi da suka
tsaidashi har zuwa dare.

Daga jiyan zuwa yau komai zaiyi yana yinsa ne cikin wani irin fushi da
zafin ran da hatta saddiq ya fahimci akwai abinda ke damunsa,kuma tabbas ranshi a
bace yake.


Ture file din gabansa yayi yana jan wani mugun tsaki. A duk sanda ya
tuna ko abun ya fado masa a rai sai yaji wani mugun bacin rai yana lullubeshi.
Tashi yayi daga kan ainihin kujerarsa yana takawa a nutse,yasa hannunsa yana
sassauta tie din dake wuyansa cikin wani irin yanayi da yakejin kamar numfashin da
yake shaqa yana masa kadan.

"Why i cares so much?" Ya motsa labbansa yana furtawa da wani irin zafi. Ba kasafai
yake sanya kulawarsa ko damuwarsa akan komai ba sai abinda yake da muhimmanci a
rayuwarsa. Ya tabbatar a karan kansa she's nothing to him amma me yasa abun yake
masa zafi

"Igiyar aurena" Abinda yake da tabbacin shine dalilin tsaiwar abun a ransa. Sai
daya sassauta tie din hade da belt din suspenders din jikinsa,sannan ya jsa ga
dispenser dinsa ya tsiyayi ruwan sanyi ya rage sanyinsa ta hanyar zuba ruwan zafi
kadan akai,sannan ya koma saman recliner chair din dake gefe wadda aka ajeta don
gajeran hutu irin wannan ya zauna akai.

Kadan ya samu sassauci sanda yasha ruwan,ya dire cup din idanunsa suna
sauka kan wayarsa dake haske. Da farko ya share yana tsammanin fareeda ce data zama
kaman wata mahaukaciya. Kusan kullum cikin canza layin da zata kirashi dashi gudun
kada yaqi dauka. Layinsa nada wani tsari na hana baqin numbers shigo masa amma nata
kiran ya tsallake wannan shingen bai kuma san dalili ba. Sabanin mamakinsa sai yaga
maamah.

Baya iya qin daga wayarta komai runtsi,duk da daga ita har anni zai
wahala su kirashi a irin wannan lokacin,sai ya jawo wayar ya daga yana sanyata a
kunnensa.

"Kana ina?" Abinda ta fara tambaya kenan tana qoqarin daidaita muryarta

"Ina office.....wani abu ya faru?" Ya tambayeta a mamakance

"Daga yau wannan yarinyar......." Sai kuma ta dakata saboda wani qaqqarfan gargadi
da aka watso mata daga can qasan zuciyarta. Dan jim tayi shima sai yaci gaba da
sauraronta baice komai ba
"Shikenan,ka kula dai da kyau" Ta yanke tunaninsu su duka biyun da fadin haka.

Wani haushi ya cikata bayan ta aje wayar,ita yarinyar zatayi wa wasa da
tunani irin wannan?,tabbas idan har ta bari yarinyar ta qara kwanaki uku a
gidanma.......bata amsa sunan mariya ba.

*_to masu karatu......me maamah zatayi da zai saka auren sabreen qarewa cikin
kwanaki uku?.....wanne qwarin gwiwa ko tabbaci sabreen ke dashi wanda yasa taci
alwashi ko shaidan bai isa ya kashe mata aure ba?.....muje zuwa jama'a,WANNAN
ALQALAMIN NA HUGUMA ZAZZAFA NE_*



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
51


_Daga sumrah dan jundub RA,yace manzon Allah S A W ya kasance yana nemawa mumunai
maza da mata gafara a kowacce juma'a_

_harda ni dake da kikazo a wannan zamanin kin shiga ciki,LALLAI HASARA DA TABEWA TA
TABBATA GA DUK RUHIN DA BAISON ANNABI,ALLAH KA DAUKI RUYUKANMU RUHINMU YANA CIKE DA
MATSANANCIN SONSA S A W_




Sai data fara lalubar number da take da muradin yin magana da ita sannan zuciyarta
taci gaba da kwabar data fara mata.

"Da kinason gayawa fu'ad me?,ya saki yarinyar?,kada ya amince da ita?,kada yaci
abun hannunta?,bayan ke kika aura masa ita?,ke kika bashi tabbaci akan ingancinta
da kuma cancantar aurensa da ita?,bayan ko sati biyu ba'ayi ba ke dindai ke kika
kafa masa sharadin ya bata kulawarsa?,ya sota?,ya jata a jikinsa?,kinason dabawa
kanki wuqa?,kinason sanya wani zargin saman zargin dake kansa naki?".


Wannan tunanin ya sakata sakin ajiyar zuciyar tana kiran number da
tazo kai,a gefe guda tana mamakin abinda ya hana hajja nemanta ko zuwa gurinta ko
tuntubarta akan matsalar da ta shaida mata jiya,TABBACIN DUKKAMIN MAGANGANUN LAILA
BA QARYA KO SHAKKA AKAI KENAN. Sai taja qwafa tana gyada kai

"Duk wanda yaci tuwo dani miya yasha" Ta furta a bayyane,daidai sanda taji an murda
qofar dakin an shigo laila ta bayyana.


Da kallo tabi lailan har zuwa sanda ta qaraso gabanta. Ta durqusa saman
gwiwoyinta wani abu da bata taba yiwa maamah shi ba duk da matsayinta na qawar
mahaifiyarta shekara da shekaru.

"Ina kwana maamah" Ta furta cikin tsantsar ladabi har bata iya hada idanunta da
nata.

Kai ta daga ta kalleta,dukka wani bayanin plan nasu da lailan tayi mata
jiya sai ya shiga dawo mata kanta tar tamkar a lokacin take labarta mata. Wani
bacin rai da radadin da wanda akaci amana keji ya taso mata,sai ta maida kanta ga
waya kawai tana tura masa saqo. Sai data tabbatar saqon ya shiga sannan ta kalli
laila,wadda kafin lokacin duk wani kalar tashin hankali laila ta shigeshi. Tana jin
kamar ta dora hannunta aka ta yita zunduma ihu,iya yadda maamah taqi amsa mata
gaisuwa ya sanyata cikin firgicin kodai wani laifi tayi mata?. A yanzu a rayuwa
bata jin akwai wani abu da zai daga mata hankali sama da taga fushin maamah.....ko
kuma tayi wani abu da zai saba umarninta.

"Lafiya qalau....." Amsa matan kawai da tayi ya sanyata sakin wata sassanyar ajiyar
zuciya,tana godewa Allah da ba wani abu tayi daya bata mata rai ba.

"Na shiga dakinki naga basu shareba.....na gyara miki,saiki duba idan akwai abinda
baiyi ba ki gayan a sake gyara mikin". A nutse take qarewa laila kallo,ji take a
ranta inama ace fu'ad ne haka a gabanta yake wannan bayanin bawai laila ba?,inama
ace aikinta ya fada daidai?,i yanzu da batasan wanne irin farinciki take ciki
ba.....lallai da zata kasance wata halitta mafi farinciki a fadin duniya,ta qarasa
wannan tunanin tana runtse idanunta gami da budesu.

"Basai na duba ba,saidai anjima kafin na kwanta ki sake"

"To ba matsala.....waida so nake naje wajen hajja.....jiya muna magana bamu gama ba
kika kirani" Kai ta girgiza,duk da tanason sake samun information,don tayi imanin
duk abinda zasu tattauna tamkar a gabanta za'a yishi,to amma kuma tana buqatar ta
kammala da aikin sabreen tukunna......tabbas komai da zai biyo baya me sauqi ne.

"Ki kirata ki gaya mata nace ba yau ba,zan duba gobe na gani idan ya dace kije
goben" Ta fada kanta tsaye tana ci gaba da riqon wayarta cikin jiran tsammanin
shigowar kiran hanzari nan da kowanne lokaci.

Sanda laila ke gayawa hajja saqon maamah kai tsaye murmushi ta saki
bayan sun gama wayar tana jinjina kai

"Mariya!.....Mariya,zan miki babban karatun da gogewarsa sai a cikin kabarinki,a
sanda qasusuwan mowacce halitta ta jikinki ta gauraye da qasa,kin bani qofofi masu
yawan gaske ba tare da kin sani ba.....zan shiga ta kowacce qofa......na fita ta
kowacce qofa.....na shiga kuma cikin rigarki na dimauta duniyarki......sannan na
hana muradinki da mafarkinki su zama gaskiya" Abinda ta fada kenan tana qurawa
wayarta idanu dake aje tana ta burarin nemon taimakon a daga kiran daya shigo.

Tun safen har azahar zuwa la'asar da tayi dukka cikin dakon shigowar
kiransa take. Sai bayan la'asar din liqis cikin ba zata daya daga cikin masu
aikinta suka shaida mata tana da baqo me suna hanzari.

"Ki rakoshi can cikin setting room,kada a barshi a waje" Ta fada cikin doki da
zumudi,ta miqe tana daukan dankwalinta ta maida kanta,har ranta tana jin mafita
tana tunkaro ta.

Fitowarta ya sanya hanzari sauke qafafunsa da suke dore daya saman
daya. Sanye cikin baqar shiga,wandon jeans da shirt dukka baqaqe,sai baqar hular
Ascot cap daya jawota tadan rufe fuskarsa kadan.

"Barka da fitowa" Yayi maganar yana miqa mata nannadaddun takardun dake
hannunsa,sai ta fasa zama ta sanya hannu ta karba sannan ta zauna dasu ta soma
budewa tana cewa

"Aiki dakai akwai jan kudi.....amma kuma akwai hanzari kamar yadda sunanka yake" Ta
fadi a nutse tana bin list na sunayen da kallo da kuma hotunan.

Sai data gama qare musu kallo tas sannan ta kaudasu daga fuskarta tana
kallonsa
"Kin gansu hajjaju?" Ya rigata fada,sai ta gyada kai ranta yana yin fari.

"Kayi qoqari sosai hanzari.....amma waye kake ganin ya dace mu dauka?" Ta fadi
maganar tana sake kallon list din. Matsowa gaba yayi kadan ya miqa mata hannunsa
yana cewa

"Kawo nan ki gani" Ba musu ta miqa masa,ya aza takardar saman teburin dake
tsakaninsu yana binsu da yatsa daya bayan daya,kafin daga bisani hannunsa ya tsaya
daidai fuskar mashkur,sai ya daga kai yana kallonta.

Duk da baiyi magana ba bai kuma ce komai ba amma maamah ta fuskanci
abinda yasa gaba da abinda yake nufi. Sai ta zuba masa idanu tana sauraron qarin
bayaninsa.

"Wannan shine mashkur......dan tsuntsu me wayo kenan..." Yayi maganar yana sake
xuba yatsunsa saman fuskar mashkur. Sake jan hoton gabanta tayi,tunda ya aje din
dama kusan fuskarsa tafi jan hankalinta. Yana da kyau daidai misali,wanda zaiyi
daidai da plan dinsu,ta jinjina kai tana duban hanzari

"Yayi......a tsara komai.....amma karka manta,secretly" Ta fada tana nuna hanzari
da yatsa.

"An gama" Ya furta yana murmushi.


*FAREEDA*

Ci gaba tayi da duba bayanan,murmushi yana sake wanzuwa saman fuskarta.
Murmushin da takejin yana gauraya da farinciki da take da yaqinin zai zame mata
tabbatacce ta hanyar samarwa da zuciya da ruhi abinda sukesu ta sassauqar hanya.

Sake bude shafin qarshe na takardun tayi,take hotonta ya mamaye screen
din tab din nata gaba daya,shafin qarshen daya zama shine na qarshe data bude cikin
dukka bayanan data samu. Ta barshi a qarshe ne saboda dukka sauran shafukan na
dauke da full details da bayanan da suka faranta mata rai sosai,sukayi kuma daidai
da muradinta.

Hoton sabreen din daya cika allon tab din ta zubawa idanu. Wani abu yana
tsarga mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafukan qafafunta. Wani mahaukacin
wutar kishi ke ruruwa cikin zuciyarta. Ta kusa kwashe sakanni talatin a haka,kafin
ta dafe dukka hannuwanta saman kujerar da take kai tayi zullo zuwa gaba har a
sannan ta gaza dauke idanun nata. Labbanta suka motsa kadan rana son kiran ainihin
sunan nata,saidai ya tsaya ne can qasan maqoshinta ba tare da sautin harafin ya
fita ba. Adan hanzarce ta maida hannunta saman tab din tana komawa shafin da yake
da alaqa da komai daya shafi sabreen din,ta sake karantawa sosai kamar me shirin
haddace komai daya shafeta

"How comes?" Ta tambayi kanta tana yamutse fuska lokacin da takai qarshen bayanan

"Karuwa?......How did he get married to her?" Ta sake tambayar kanta da kanta

"She's karuwa officially fa?" Ta kuma nanatawa cikin zallar mamaki. Ba wata amsa
data samu daga kowanne sashe na kwanyarta,saita dage kafadunta duka biyun sama tana
sakin murmushi,lallai komai zai tafi da alama daidai

"Fu'ad isn't your type madam.....its over between you too" Tayi maganar tana nuna
hoton sabreen da dan yatsa,saidai ba abinda ya canza zuciyarta daga mahaukacin
kishinta da takeji.
Ta kowacce fuska,ta kowanne bangare sabreen din ta yaga mata indai ana
batun kyau ne da sassanyan zubi da ta tabbatar yana daya daga cikin abinda ya fusgi
hankalin fu'ad din,banda hakan.....yadda ta samu full details dinsa zai wahala ya
nuna interest akan karuwa har ya aureta.

"It's my turn......my time to shine has come" Ta fada da qwarin gwiwa,ta miqe tana
nufar closet dinta ta sauke luxury luggage dinta guda daya ta fara selecting kaya
tana shiryawa a ciki ba tare da jiran kowa cikin masu aikinta ba.

Cikin qasa da mituna sha biyar ta gama packing komai da komai
nata,sannan ta dawo ta dauki wayarta ta kira number abbanta.

"Hello dad....." Ta fada a shagwabe. Ita din 'yar gaban goshinsa ce da dukka
yaransa babu wanda ya kamo matsayinta a zuciyarsa. A kullum tana maida kanta tamkar
'yar shekara goma a gabansa,haka shima yake biye mata,saidai hatsabibancinta da
girman izzarta ta dara tashi shi da yake da muqamin ambassador din gaba daya.

"Dad.....ayimin booking flight please......gobe nakeso if possible,it's an urgent
dad..." Ta furta a shagwabe kamar yarinyar dake tsakanin shekara shida zuwa bakwai

"Thank you dad" Ta fada da murnarta jin ya bata tabbacin zaisa a mata booking
private jet.

Da murmushi sosai a fuskarta ta soma turawa zababbun qawayenta da za'ayi
tafiyar tare dasu request. Cikin qasa da minti goma ta gama komai,sai ta sauke
wayar ta matsa gaban dan wani madaidaicin table dake dauke da tukunyar shi sha ta
fara qoqarin hadata. Tanajin a yanayin da take ciki na farinciki ita daya zata
tayata sarrafa murnarta,

Kyakkyawar zuqa tayi mata tana bulbular da iskar daga dukka qofofin
hanci da bakinta,ta lumshe idonta fuskar sabreen na mata shawagi tsakanin tunaninta
da qwayar idanunta

"Blast it!" Ta fada da qunan zuciya tana kaiwa iska naushi,tana jin kaman tayi
using acid ta dauke wannan kyan da ya hanawa zuciyarta sukuni.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
0818725586252

_Daga dariq dan shihab RA,manzon Allah S A W yace "juma'a haqqi ce kuma wajibi akan
kowanne musulmi yayita cikin jam'i,sai akan mutum hudu kawai(ta
sauka),MACE,BAWA,YARO DA MARA LAFIYA"_

_Abu dawud ne ya rawaito_



★Shuru ne ya biyo baya duk da wayar tana riqe a kunnenta. Dukka bayanan
zuwaira ta gama saurara wadanda suka gama bata tabbacin lallai da gaske yaran sunyi
nisan da ba wanda zaice ga inda suke......uwa uba kuma yarinyar tana ci gaba da
harkokin gabanta hankali kwance kamar ba wani qalubale a gabanta.

"Ni kaina yanzu komai na taba ko nace zanyi mata dakatar dani takeyi,waccar
munafukar me aikin da ameena ta kawo mata yanzu da ita takeyi,munafuka me shegen
iyayi da bariki,idan kikaga yadda takeyi mata zaki rantse da Allah sabreena ce
babba ba ita ba". Wani tattauran yawu maamah ta hadiye,tsananin bacin rai yana sake
cikata
"Ki saurara,ki sanya dukka kunnuwanki da hankalinki dama idanunki kan
gidan......kada kice komai,kuma kada kiyi komai,akwai gagarumin al'amari da zai
faru cikin gidan.....abu daya nakeso kiyimin,ki kasance me bibiyar diddiqi bayan
faruwar lamarin" Abinda maamah ta gaya mata kenam ta kuma yanke kiran. Bin wayar
tayi da kallo......har a sannan tanaji a ranta muddin tabar sabreen din taci
galabar ci gaba da rayuwa tana shan inuwa da arziqin danta lalallai ba shakka bata
cika mariya. Shekaru da gwagwarmar rayuwa da gogayya da tayi da kalar mata daban
daban bai amfaneta da komai ba.....shekarun data kwashe ma a duniya basuyi mata
amfanin komai ba,dole ta fiddota daga gidan......wannan shine zai bata damar yin
walagigi da rayuwarta da kuma d'aid'aita rayuwarta kamar yadda ta d'ai d'aita mata
burinta.

Qarfe daya da rabi na rana driver din hajja ya faka motarsu qarqashin
muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci. Koda ya tsaida motar ya kuma kasheta
amma hakan bai sanya hajja fitowa daga cikin motar ba. Da idanu take bin kowanne
sashe na ginin gidan da kallo tamkar yanzu ta fara ganinsa. Saidai sam a badini ba
wannan bane damuwarta ba......ba kuma shi take kallo ba.

Tana nazarin yadda ALKHAIRI ya juye izuwa SHARRI,ta gama tura mota
tsaf tana shirin buleta da balbalin hayaqi maras dadin shaqa?,hayaqi mafi cutarwa
cikin qofofin hanci da kwanyarta?..

Wata gauruwar ajiyar zuciya ta sauke,sannan ta balle murfin motar yau
da kanta tana fitowa,sabanin a baya da sai driver ya fito da kansa ya bude mata
sannan ta fito. Gyara yafen mayafinta tayi,kanta tsaye kuma take takawa zuwa hanyar
da zata sadar da ita da ainihin cikin gidan.

Duk taku daya idan tayi la'anar maamah take cikin ranta,tana ji a jiki
ta jefeta a wata kalar musiba da batasan ranar fitarsu ba. Zuciyarta tana mata wani
qunci da ita kanta batasan iya adadinsa ba......amma wani sashen na zuciyartata
yana sake jaddada mata

"Fushi ba naki bane.....nasara bata masu gaggawa ko saurin fushi bace!" Wannan
shine abinda yaketa mata burki take hadiyewa da qyar. A jiya da qyar bacci barawo
ya dauketa,cikin fargaba da tsoron fitar dukkanin sirrinsu daga bakin laila.....
Yanayin aikin bokansu dabanne,a aikin da aka tanadarwa fu'ad harda na rariyar
baki,wanda baida wani sirri na kansa sai abinda maamah ta buqaci ya sirranta,muddin
maganin yayi tasiri a jikin laila kamar yadda aka tsara.....hakan yana nufin duk
wani sirri nata yanzu a tafin hannun mariya yake?.

Wannan tunanin ya hana mata cikakken bacci da safe,ta dinga qididdiga
da lissafin wucewar sa'o'i don ta samu ta fito zuwa gidan mariyan. Tanaso taga
yanayin fuskarta,abinda zai nuna shine zai zame mata amsa na abinda take zato da
zargi. Duk da cewa na tsuburi ya mata alqawarin ba abinda laila zata iya gayawa
maamah.....to amma tasan aikin bokansu daban yake dana kowanne boka.

Sau daya tak! Yake maka aiki.....idan har yayi maka na biyu to tabbas ka
taki sa'a,uwa uba yawan yawan ayyukansa basu da makari.....shi yasa ta jima tana
murza zaren rayuwarta ta kowanne fanni.....a yanzu kuma bata fatan wata matsala
tazo mata ta wannan fuskar.

Idanunta akan parlor din maamah.....falon da kullum maamah din ke
kusheshi da ganin tsadar kayan adon ciki bai kama qafar na gidan alhaji hamza
ba.....Parlor din da ita kuma hajja harira kullum kwanan duniya ta daga kai ta
kalleshi sai kishin zamowarsa mallakar mariya ya baibaye zuciyarta da wata irin
hassada me tsananin qarfi. Iya bariki da qwarewa wajen boyewa koma waye yanayin da
kake ciki ya sanya maamah din bata taba fahimtar komai ba.

Takun da taji ana fitowa daga kitchen ya sanyata waiwayawa cikin
tsammanin daya daga cikin masu aikin gidanne wadanda su zasu yiwa maamah maganar ta
iso tana son ganawa da ita. Amma kuma sabanin hakan,laila ta gani a gaba,dauke da
kwando cike da warmers kala kala,saman rigar jikinta kuma apron ce a daure.

"Laila?!" Ta kira sunanta cikin qaraji da wani kalar madaukakin mamaki tana takawa
da hanzari don isa gabanta.

"Sannu da zuwa hajja" Lailan ta furta fuskarta shimfide da murmushi dake nuna ba
wani abu da takejin ba daidai bane

"Bari na ajewa maamah abincinta nazo mu gaisa" Ta furta tana wucewa dining din. A
nutse ta shirya komai.....kamar ba lailanta diyar gata ba,lailan da idan taci
abinci ko kwanon da taci abincin batasan ta janyeshi ba......lailan da saidai tana
mimmiqe saman sofa ko gado ta zabi abinda take da sha'awar ci.....wannan lailan
itace yau a kitchen da rigar 'yan aiki?.

Sanda ta kammala shiryawar saita dago tana murmushi,suka hada idanu
da hajjan tace

"Ina wuni?,na kira miki maamah din?,Allah yasa bata kwanta bacci ba don tace ko
waye yazo kada a tasheta"

"Gani nan laila baccin baizo ba....kun gama ne?" Maamah dake saukowa daga stairs
din ta fada.

Tare suka daga kai suna dubanta,sanye take da applique lace purple
color da ya dan ciza kadan,dinkin doguwar riga da aka qawatata da wani irin dinki
me daukan hankali. Shigar tabi jikinta....wadda ke bayyanar da zallar izzarta da
isarta.

"Kun gama laila?" Kai ta shiga gyadawa kaman mara hankali da sauri

"Mun gama maamah ko akwai wani abun?". Ta fada a rusune. Murmushi maamah ta saki
tana dafa kafadarta

"Amma dai yau kin koyi yadda ake dambun gargajiya da kuma liver salad ko?".
Murmushi ta saki kaman wata shashasha

"Sosai ma maamah.....ai kin taimaken na gode sosai". Ta fada tana rusunawa a wajen.

"Shikenan,yanzun zaki iya yin wanka,idan kin gama kiyi zamanki a daki kada ka fito
yanzu"

"To maamah" Ta amsa mata a ladabce tana juyawa ba tare data dubi ko bangaren da
hajja take tsaye ba. Idanu suka hada da hajjan,wata tayi wata irin mutuwar tsaye.
Gefe guda kuma taci gaba daya tamkar qwaqwalwarta ta daina aiki ne gaba daya. Wani
qaramin shu'umin murmushi maamah ta saki,ta juya da hanzari bangare da laila ke
tafiya

"Au.....nikam nace kin gaida mamanki kuwa?" Kai ta girgiza tana fadin

"Bakice ba ai". Fuska kadan maamah ta bata

"Haba ke kuwa auta.....yarinyar kirki,zo ku gaisa mana....wataqila sanda zata tafi
ai baki fito ba". Dawowa tayi ta rusuna har qasa tana gaida hajjan abinda bai taba
faruwa ba kenan tsahon rayuwarta. Da fari idanuwa kawai hajjan ta saki tana kallon
lailan,har sai da taji lailan ta maimaita gaisuwar sannan ta duqa tana dagota daga
tsugunnon da tayi
"Ki dauko mayafinki kizo mu tafi gida" Ta fada muryarta na rawa amma tana qoqarin
danne rauninta don bata fatan maamah din ta gani.

Kai ta girgiza tana duban maamah wadda tayi kaman batasan abinda ke
faruwa ba,tana laluben wajen zama hankalinta akan fuskar wayarta

"Nafison nan hajja.....ni ki barni a nan" Ta fada tana zamewa daga jikin maamah din
ta wuce abinta hankalinta kwance zuwa hanyar dakin da aka bata.

"Bismillah.......zauna mana surukata" Maamah ta fada fuskarta a sake. Kalmar suruka
din da maamah ta fadi shine ya sanya hajja jin wani abu tamkar wutar lantarki ta
fusgeta. Cikin qasa da minti guda gumi ya fara tsatsatsafo mata ta kowacce kafar
gashi ta jikinta.

"Atika!" Maamah ta qwalawa me aikinta kira,wanda cikin qasa da minti daya ta
bayyana,sanin da sukayi mata batason ta kiraka ka samu jinkirin zuwa.

"Dauki remote ki kunnawa surukata A.c,karki saka da yawa kada kuma ta saukar mata
da zazzabi"

"To hajiya" Atika ta fada da rawar jiki tana me aiwatar da abinda maamah ta
umarceta.

Zagayawa kawai kalmar takeyi cikin kunnuwan hajja.....indai har
kalmar surukuta zata fita daga bakin maamah a wannan yanayin,lallai ne ba abinda
bata sani ba kenan.

"Ki maida hankalinki jikinki hajja......har mariya ce zata firgitaki har haka?".
Wani sashe na zuciyarta ya bata qwarin gwiwa har ta samu qarfin halin tattara 'yar
nutsuwar jikinta tana neman wajen zama gami da fuskantar maamah.

"Mariya......zuwa nayi na duba lafiyar laila.....ya kuka tashi?". Murmushin nan dai
ta kuma saki,sannan ta ajiye wayarta a gefe tana bada hankalinta gaba daya a

Please Login or Register in order to submit comment