You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma,tabbas kina buqatar tarbiyya,Your attitude
needs a serious adjustment.....and im not going to put up with anymore nonsense,I
won't tolerate any more of your nonsense,its time to get in line" Yayi furucin
harshly muryarsa cike da seriousness. Din din din da taji wayar nayi shi ya
tabbatar ya yanke kiran. Ta sauke wayar daga kunnenta tana jin wani irin daci yana
taso masa tun daga cikin maqogoranta har zuwa saman harshenta. Tabi wayar da kallo
ranta yana mugun baci,tana jin maganganun daya gasa mata suna yawo cikin
kunnuwanta.
Tana jin kamar tayi cilli da wayar ko zata samu sauqin radadin dake
cisgar zuciyarta......to amma saita tuna idan tayi hakan bata kyautawa ainihin me
wayar ba,wanda shima da alama komai nasa yana yine bisa tsoro da kyakkyawan bin
umarni ba tare da sabawa ba.

"Kai mishi wayarsa" Tace da nadra tana miqa mata wayar,sannan ta miqe tana gyara
jakarta tabi bayan nadra zuwa qofar gidan,tana jin yau saita nuna masa iyakarsa ta
hanyar fita,idan yaso ya tashi duniyar a yau kowa ya huta.

Nadra ta rigata isa,ta bashi wayar dake ringing,yana duba me kiran yayi
hanzarin dagawa tare da matuqar rusunawa yana fadin

"Hello sir" Idanunshi suna sauka kan sabreen,sai ya miqe yana sauraron umarni daga
wayar yana kuma kallon sabreen wadda ke tafiya cikin tsananin fushi,har kuma ta
samu nasarar sanya qafafunta a qofar gidan.

"......idan naga sabanin haka ka kuka da kanka" Qarshen maganarsa kenan data jawo
hankalinsa zuwa ga sabreen wadda ta dauki hanyar barin layin sosai bata tsaya koda
waiwayarsa ba ballantana wayarsa da yakeyi,tana jin bata da lokacinsu gaba dayansu.

Da sassarfa abdulgafar ya jefa wayar a aljihunsa ya juya da sassarfa
yabi bayanta. Daga yadda yau boss din ya masa magana ya tabbatar akwai magana a
qasa. He's speaking seriously,yasan abinda ya fada da gaske yake.

"Madam.....ah.....am,madam sorry......listen please" Ya furta bayan ya cimma
bayanta. Nuna ma tasan yana biye da ita a wajenta bata lokaci ne,bata da lokacin
batawa ta saurareshi daga shi har boss din nasa

"Madam please ki tsaya ki saurareni,am going to loose my job.....please listen to
me". Maganar ya taba mata zuciya........yanzun nar rashin imaninsa yakai ace ya
kori mutum bakin aikinsa saboda wani abu daban ya faru?. Daga yadda yake maganan
kawai ya gaya mata da gaske yake fadi,don haka tadan sassauta tafiyar ba tare data
kalleshi ba tace

"Ina jinka"

"Please madam ki koma gida.....kiyi haquri ba yadda muka iya.....haka boss ya
tsara......"

"Wannan kuma bazai yiwu ba,idan baka da abun fada ka koma yafi maka sauqi" Daga
hakan taci gaba da tafiyanta. A nutse take ratsa layin,yayin da idanun 'yan sanya
ido ya soma yin caa a kanta. Ba yadda zaka kalleta ita da abdulgaffar din kace ba
body guard dinta bane,saboda yake take mata baya yana maida takunsa duk inda ta
dauke ba tare da sunsan abinda ya sanya ya biyota ba,take tsegungumi suka fara
tashi,masu rade radi akan irin mijin da zata aura a yau suka samu tabbacin hakan

Da alama zazzafa ce itama tamkar boss din nasu,ya hanga ya hango babu
wani sauran abinda ya rage masa illa ya kira oga farouq,don haka yana biye da itan
yayi kiransa,yayi kuma bayani a taqaice.

"Turawa hood location ta watsapp...zaizo da mota ya kaita.....idan yazo din give me
a call.....zanyi magana da ita" Yayi maganar haushin fu'ad yana kamashi.

A ganinsa tunda batu ake na aure koma meye ya kamata ya ajiyeshi a
gefe,batun aure ya wuce wasa.....ya kuma wuce tunanin mutum.

Wani irin aiki ne da ake yinsa da umarni da kuma doka. Iya tsaiwar da
tayi tana jiran ababen hawan da batasan dalilin da yasa duk wanda ta tsaida sai ya
wuce ba.....wanda qwarewar aiki irin na abdulgaffar ya sanya yake musu alama me
nuna gargadi kan tsaiwar tasu,take suke wucewa abinsu.

A hankali motar ta rage gudu tana qarasowa gabansu,wanda tun kafin
takai ga qarasowar abdulgaffar ya ganeta. Motocin da dukka suka jibanci familyn
muhammad jadda da kuma gidan alhj hamza kibiya ba boyayyu bane,don hatta da plate
number dinsu na dabanne da wani irin kebantaccen tsari na daban.

Bai bari motar ta qaraso gabansu ba ya kirayi farouq din,sai komai yazo a
daidai,isowar motar gabansu da kuma matsawa da yayi daura da ita ya saka wayar a
handfree yadda idanunta zasu iya ganin wayar

"Ranki ya dade......Allah ya taimakeki,tuba muke,kunyi magana da boss yana cikin
fushi ne.......ayi mana alfarma kiyi haquri,ga driver da mota nan ya iso,ki shiga
ya kaiki duk inda kikeso,tuba muke,tuba muke" Ya maimaita har sau biyu yana hade
tafukan hannayensa guri daya.

Batasan me ysaa ba,amma sai taji tasss ta sauka daga fushin da takeji.
Yanayin maganarsu dama komai nasu ba daya bane,batasan kuma waye ba......sannan
batasan nasabarsa dashi ba.....amma da iya lafuzan bakinsa kadai ta tabbatarwa
kanta yasha banban dashi tako ina.

Batace komai ba ta soma takawa tana nufar motar da tuntuni suka wagale
mata qofar suna tsaye suna jiran isowarta,tadan dubi security din kadan ta kauda
kai tana tabe baki. Su kuma a haka rayuwarsu zata qare?,basa da aiki sai ta'ammali
da murda murdan garadan da babu rahama akan fuskarsu?,idan kuma suna tsaye sai kace
gumaka?,wacce irin rayuwa zata shiga ne?. Da wannan tambayar ta shiga cikin motar
suka maida murfin suka rufe.

Duk da yadda ranta yake a bade,zuciyar kuma bata tare da komai amma
hakan bai hanata fahimtar banbancin inda ta shigo ba. A hankali ta kalli wani sashe
na motar,cikin ranta tana jin zallar tsagwaron banbanci. Batayi kuskure ba idan
tace tsahon rayuwarta bata taba tsammanin da gaske akwai mota irin wannan a
nigeriar mu ba,cikin motar bai mata kama da komai ba saida wani qawataccen
madaidaicin falo na alfarma,idan ba yaye labulen window din kayi ba zata ko dan
jirin motsin motar kadan ba saika tsammaci cikin wani killataccen falon kake. Taja
numfashi a boye tana saukeshi,duk da ita kadaice a nan amma saita killace ganinta.
Bangare daya zuciyarta tana bugawa da samun tabbacin lallai da gasken da kawun ke
fada su din ba qananun mutane bane......amma ta yaya suke bibiyan rayuwarta?,me
yasa sai ita?,me suke tunanin tana dashi wanda zata iya basu?. Amsar dai kamar
kowane lokaci.....hasashen kaman na kowanne lokaci shine AKWAI WANI ABU A QASA.

Da wani irin makirin narkakken murmushi ta maida murfin qawataccen
akwatin ta rufe bayan ta gama ganin suturar alfarmar da aka tsumata da wasu
tsatsube tsatsube na musamman da suke a mazaunin matakin farko na fara tunkarar
shirin data yiwa rayuwar mutum biyun.......sanadin wato sabreen.....da kuma
maqasudin wato muhammad fu'ad.

"Komai yayi hajja........suturar million biyu kam baa kashe kudinsu a banza
ba.......yanzu zuwaira za'a aika?.....inajin kamar nayi tattaki naje nakai Mata da
kaina,don inaso ta fahimci muhimmancin sanya suturar nan" Tayi zancan da wani irin
muhimmanci cikin sautinta,tana tuna bayanan bokan da bata dana biyunsa a yanzu haka

_".......tana sata a jikinta ta fara zuwa hannu fa hajja......hakanan shi Kansa
fu'ad kallon farko da zaiyi mata da suturar zai jarabtu da sonta,abinda zai bada
damar gudanar da aikinmu cikin sauqi,zai karbi komai daga hannunta yaci ya kuma sha
ba tare da wani matsala ko tangarda ba"_

Murmushi hajja ta saki tana dora qafarta daya saman daya
"Tafiyar zuwaira ita daya yana nuna aiken bame daraja bane,hakanan zuwanki da kanki
zai jefa shakku a idanun mutanen da hankulansu ke kanmu irin aminatu hamza
kibiya......wannan saqon babbar aminiya kuma amintacciya ya kamata ta isar dashi"
Murmushi me sauti ya qwacewa maamah,ta bawa hajja hannu suka tafa tana fadin

"Allah yabar mutum da nasa.......bari na yiwa usama magana" Ta fadi tana dauko
wayarta dake ajiye gefe ta fara lalubar number wayar usaman.

Zuwanta wajen aysha da dawowarta....farincikin data samu na ganin
yarinyar ta dawo cikin cikakken hayyacinta da wata lafiya data sanya kumatunta
cikowa shine ya haifar da sakewar fuskarta,ya kuma saka mata farincikin da ta kusa
mantawa da abinda ke tunkararta a gobe.

Kallon masu kallo da idanun masu sanya idanu tun daga qofar gidansu da
lafiyayyar motar ta ajiyeta bai dadata da qasa ba,har zuwa sanda ta isa tsakar
gidan,ta kama matakala tana haurawa zuwa saman nasu.

Tana sanya qafarta sukayi kacibus da momma dauke da tray da lemuka da
ruwa akai.

"Yauwa yanzu nake shirin kiranki......kina da baqi suna qasa,ki hanzarta ki samesu"
Ta gaya mata tana rabata zata wuce

"Baqu momma?,su waye?,daga ina kuma?"

"Kinga duka wadannan tambayoyin ki adanasu idan kinje kyayi musu.....me lalle ma ke
take jira tunda kika fita". Ambaton sunan me lalle saiya fara dagula mata
lisssafi,bayan dirje fatar da aka dameta dashi na kwanaki kusan goma yanzu kuma
wani me lalle ne na daban zata zauna yi?,salon a bata mata hannu da qafar da bata
shirya diga musu komai ba?.

Ganin momma tayi gaba har tana gangarawa qasan stairs din ya sakata
itama ta laqume dukka tambayoyinta tana wucewa ciki. Zuciyarta fal da saqe saqe ta
sauya abayar jikinta zuwa wata sassauqar doguwar Riga cotton me gajeran hannu data
zauna daidai jikinta,ta dauki qaramin hijab daya tsaya mata iya kafadu ta maqala ta
juyo tana saukowa.

Dukkansu su biyun suka amsa mata sallamar idanunsu a kanta

"Tubarkalla ma sha Allah" Zuwaira da tayo rakiya ta qarfi da yaji don ba haka Hajja
taso ba ta furta kyan sabreen yana bugar da ita. Duk yadda take jin hira da yadda
aka tsara komai bata taba kawowa kyan yarinyar yakai haka ba,ta dauka maamah din
nada tsananin wayo......zata dauko yarinyar da bata da cikakken siffa gudun juyewar
reshe da mujiya. A iya sanin data yiwa halittar 'ya'ya maza masu jarabtuwa da
kyakkyawar mace komai kamewarsu kuwa. Sanda suka iso gidan batayi tunanin gidan
masu matsakaicin qarfi da gata irin wannan yana qunshe da kyakkyawar sura har haka
ba,taci gaba da qare mata kallo yadda shape me qirar Coca-Cola ya fita sosai ta
cikin rigar ta wajen qugunta.

Duk kallon da zuwaira ke qare mata hankalinta baikai ba,saboda
hankalinta daya tafi akan hajja da suka fara hada idanu. Ta yaya zata manta fuskar
matar?,bayan tana a wajen sanda sukazo da tallar qazamtacciyar hajarsu?,kuma kusan
itace tafinta a wajen matar dake iqirarin mahaifiya take a wajensa.

Yadda sabreen din ta tsareta da idanu tana zama a dosane a hannun
kujera irin yadda takeyi idan zuwan mutum magana ko mu'amala dashi baiyi mata ba

"Sannu ko?" Hajja ta fada tana qaqaro murmushin dole. Wani irin kishi me girma ya
sauko mata akan Sabreen din. A haduwarsu da suka taba yi qwaya biyu hankalinta bai
taba kaiwa kan sassanyan kyan da yarinyar ke dashi ba. Wani irin halakakken kyau
dake boye a kowanne sashe da kuma halittarta. Anya wannan ba kuskure bane?,idan har
tayi saken daya fadawa sonta rabasu kuwa zai zama abu me sauqi kuwa?.

Tabbas bata taba kula da wannan kyan ba,wanda inda tasan dashi tana da
dukkan makaman da zata rusa tafiyar........a yanzu bayan komai yayi nisa ta yaya
zata katse wannan wasan da bata taba ganin abinda maamah ta ciwa buri a kansa har
haka ba.

"Yauwa sannu" Sabreen ta maida mata da salon yadda tace da ita. Haka kawai taji ba
zata iya gaida matar ba,tun a waccar ranar duk wata kima martaba da kuma mutunci da
ake ganin dan adam me girma da shekaru nasu duka su biyun suka kwaranye mata.

"Ya gida ya shirye shirye?" Hajjan ta sake dauriyar fada yadda sabreen din ke shan
qamshi yana qara qona mata rai,amma duka wannan ba komai bane......tasan s nan kusa
zata fahimci wace ita?kuma su waye su.

"Alhamdulillah" Ta sake amsa musu. Kai tsaye hajja ta gabatar da abinda ya
kawosun,da dukkan alamu sun nuna ba'a maraba dasu ata nan din

"Saqone daga mamarki" Hajja ta fadi tana turawa zuwaira akwatin,ita kuma tana
sadar dashi xuwa ga sabreen dake binsu da idanu.

𝐃𝐔𝐍𝐈𝐘𝐀𝐓𝐀 𝘭𝘊ð˜ĩð˜ĩð˜Ē𝘧𝘊ð˜Ŋ 𝘎ð˜ķð˜Ĩ𝘊 ð˜Ŋð˜Ķ

08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀

ĖķBĖķOĖķOĖķK Ėķ2

ⱧɄâ‚ēɄâ‚Ĩâ‚ģ

𝙋𝘞𝙂𝙀 8


Page 8

Duniya ta

Sai data qarewa akwatin me ruwan gold kallo,sannan a nutse ta aza kallonta akan
hajja,don tayi yaqinin itace jagorar tafiyar kamar wancan karon.

Kallon kallo ne dake nufin ina buqatar qarin bayani. Da yake hajja din
'yar gari ce har ta fahimci ma'anar kallon,ta saki wani qaramin murmushi sannan
tace

"Kusan duk inda akace ana arziqi tsiya guduwa takeyi.....lallai ba shakka kina
cikin matan da sukazo duniya a sa'a da har tarihi zai baki daman kasancewa matar
muhammad jadda.......wannan suturan ta lashe miliyoyin kudi.....kuma an tanadeta ne
kawai saboda ki sanayata a ranar da za'a miqa ki zuwa gidan fuad,wannan shine burin
uwar mijinki da kuma umarni na farko da takeso ki fara dauka cikin tafiyar
ku......lallai ne muddin kika kasance me biyayya ina miki busharar keda sunan
talauci kinyi adabo.... Aiki ne na qididdgaggun watanni,amma ribarsa zaki ci gaba
da cin gajiyarta har qarshen rayuwarki data zuri'arki". Idanu ta lumshe a nutse
sannan ta budesu. Tana jin wani murmushi yana taso mata daga qasan zuciyarta amma
kuma batason bayyanarwa hajja dashi. Shin sun dauka ita din wawiya ce da har zata
aminta da komai daya fito daga garesu?,sunyi tsammanin shirunta galaba ce a tare
dasu?,ko sauraro da dakonta a kansu suna tsammanin alkhairi ne?.

Zamowa tayi a nutse daga saman kujerar ta zauna a gabansu gaba daya tana
langwashe qafarta. Idanunta tsakiyar na hajja ta soma magana da nutsuwar nan tata
dake qarawa maganarta kwarjini da fahimta a muryar me sauraro

"Ina zaton aikin data nema daga gareni zaya tsaya ne kawai iya kan danta.......aiki
kawai tace zanyi mata na wata uku ko hudu......bata da hurumin komai cikin
rayuwata.....kama daga cima ko sutura......" Ta tsaya iya haka tana maida numfashin
bacin rai. Ranta ya fara dugunxuma na ganin yadda suke qoqarin maida rayuwarta
tamkar gare gare tsakanin uwa da d'anta da suka zamo tsatso daya......abinda sam ba
zata lamunta ba kenan,ita tayi mata......danta ma yayi mata?,shin ummeeenta su ta
haifawa su?.

A mamakance hajja ke binta da kallo,bata taba zaton haka daga gareta
ba,kallon hajjan ya isheta hakanan,dom haka ta miqe cikin rashin damuwa tana gyara
lullubin kanta tace da ita

"Ki gaya mata damuwarta ta tsaya iya kan aikinta kawai......indai tace zata hada da
shigar da rayuwar sabreen......komai bazai tafi yadda take tunani ba.....ni din
tamkar wahainiya nake a wasu lokutan.....sawun keke da gane gabansa yake da wahala
koda a wajen gwanaye".

*MAAMAH*

Idanunta ta runtse bayan hajja ta jera mata dukkan wadannan bayanan da
sabreen ta aiko mata dasu ba tare data rage komai a ciki ba.....koda ta manta wani
abun zuwaira dake gefe tana taso mata dashi. Ta bude idanunta cikin bacin rai tana
duban akwatin da iya shi daya kawai kudi ta zuba masu yawa,banda kayan banda kuma
aikin da akayi akan kayan.

"Yarinya ce qarama tabbas.....amma na yarda da gaske tana da hadari........tana
kuma da wasu boyayyun abubuwan da bamusan dasu ba......iya kalmominta na yau sun
sake zaburar dani akan dole na ninka shirina a kanta......amma ba wannan
ba.......asarar data sani nayi tun a matakin farko yafi damu na....."

"Kada ki damu.......akwai mataki na biyu da nayi imanin ba zata tsallakeshi
ba......saidai shi na biyun bangare daya ya qunsa.......bangaren cusa soyayyarta a
zuciyar fuad ya saraya,saidai a samo masa wata hanyar ta daban". Ajiyar zuciya
maamah ta saki tana jin sassaucin tashin hankalin dake sauko mata

"Wannan dinma wahalar da nayi a kansa bazai tafi a banza ba.....koda bataso sai
tayi amfani dasu,ta hanyar da takeso ko ta hanyar da bataso bata kuma shirya mata
ba". Daga haka ta jawo akwatin ta cusashi qasan lafiyayyen gadonta.


𝙈𝘞𝙁𝘞𝙍𝙄𝙉 𝙏𝘞𝙁𝙄𝙔𝘞𝙍......

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀


Tamkar jira akeyi su kammala sauka daga jirgin,wayarsa dake riqe hannun
daya daga cikin guard dinsa da tun tafiyar zuwa yanzu shike da alhakin riqe masa
ire iren wadannan kayan nasa.

"Sir.....oga farouq" Ya sake matsowa kadan bayan fuad yana fadi cikin rusunawa.
Baice komai ba ya miqa masa hannun shi kuma ya dora masa wayar,ya dawo da wayar
fuskarsa yana duban kiran farouq din yana ci gaba da takawa yana fita a wajen.
Boyayyen murmushi ya saki,tun jiya ya kashe wayarsa dama duk wani hanya
da farouq din zai sameshi,yasan tabbas idan ba haka ya masa ba bazai shafa masa
lafiya ba,zai birkita masa lissafi ne kawai.

"Idan baka da niyyar dawowa ne malam ka yiwa mutane magana.......awa uku kadai suka
rage awannin daurin aurenka su cika......amma still ace baka iso ba?".

"Who told you dude?.....mu hade a Bristol,banason hayaniya" Daga haka ya kashe
wayar ya miqa masa yana magana dashi ya tura masa number dakin da yayi booking
already. Yana da gidajen da zai iya sauka a cikin su,saidai sam sam baya shaawar ya
sauka a can din gudun kada a cimmasa a dameshi da damuwa.

Abinda bai sani ba yayi gudun gara ne,don kusan mafi yawan abokansu da
sunzo ne don farouq a Bristol din sukayi masauki.

Sanda saqon yakai wayar farouq shafa kansa kawai.yayi,yaci alwashin sai
ya rama wasa da hankalin da fuad din yayita yi masa. Ya ajiye wayar yana kiran
musaddiq kan ya fiddo mota yanason kai yakai ga fitowa su ruskeshi a can.

Yayi mamakin ganin motocin jadda har guda biyar a wajen suna jiran
isowarsa. Bai gama wannan mamakin ba farouq ya fito cikin daya daga cikinsu yana
qoqarin rufe wayarsa ya jefata a aljihu.

Wani kallo me kama da harara ya watsama fuad din wanda ya jingina kawai
jikin daya daga cikin motocin yana kallon qarewar fushin farou a kanshi. Ya sani
shi ko farouq din babu me iya fushi da dan uwansa.....duk wani abu da daya daga
cikinsu zai fadi burga ce kawai da cika baki,da zarar sunyi face to face yake
wucewa tamkar bai faru ba.

Koda ya iso duka yakai masa ya goce yana wannan tsadajjen murmushin nasa

"Haka kawai ka nakasani bayan banyi komai ba?" Ya furta murmushin yana shimfide a
fuskarsa

"Sa'arka daya wallahi......yau babbar rana ce" Farouq ya fadi yana buda masa murfin
motar da kansa. Sai daya shiga sannan yabi bayansa,yana zama wayarsa kuma ta dauki
tsuwwa ya ciro yana amsata.

Tunda suka taho a hanya farouq ke amsa wayoyin mutane iri iri. Yana
ankare dashi amma baice komai ba,ko a iya haka ya samu alama da shaidar lallai
gayyar jama'a farouq din yayo.

"Kada kacemin tsayawa kayi ka batawa kanka lokaci kayita kiran mutane?" Yayi
maganar yana tabe baki cikin rashin bawa abun muhimmanci. Wani kallo ya watsa masa

"An gaya maka kowa irinka me wai?,kai abinda ka dauka daban.....yadda mu muka
dauka......aure komai lalacewarsa sunansa aure.....barema ba lalataccen koda na
bariki ne".

"K'nnnnn" Kawai ya fada yana zamewa gami da yin relaxing sosai jikin motar

"Nidai muyi mu qarasa,bacci ne a ido na,kwanakin duk da nayi acan ba wani bacci na
samu ba".

" Mutuwa zakayi ba bacci ba" Farouq ya fada cikin harzuqa. Kallo daya ya yiwa
farouq din ya lumshe idonsa yana cewa

"Allah ya baka haquri" Daga haka bai sake cewa komai ba kaman yadda bai kuma bude
idonsa ba har sukaje.
Da lallausan farin towel ya fito daga toilet din dakin daya zame masa
masauki daure a qugunsa. Ya qarasa gaban madubin dakin yana duban yadda farouq ya
zube masa duk wani kayan shafawarsa. Duddubasu yayi kawai ya ajiye yana mamakin
yadda farouq ya dauki auren nan serious. Sai ya jawo stool ya zauna akai yana
kallon kyakkyawar fuskarsa ta cikin madubi gami da sanya qaramin towel yana tsane
ruwan kansa. Koda ya gama sai ya aje towel din,ya soma lalubar wayoyinsa. Sunyi da
larab zai kirashi don ya tabbatar an gama design na hall din dake cikin kamfanin
inda za'a gabatar da taron budeshi a jibi kaman yadda ya tsara.

Gajiya yayi da dube dubensa,sai ranshi ya bashi farouq ya kwashesu.
Qaramin murmushi ya saki,yasan zai aikata,kuma duk zaiyi hakanne don ya tilastashi
shiryawa. Duk da abun ba wani muhimmanci gareshi ba a wajensa.....amma farouq ya
tattara duka lokacinsa akan komai dason ganin komai ya tafi daidai din,ya qarasa
gaban madubin ya sake zama yana bude lotion dinsa na dindindin ya fara shafawa.
Yana tsaka da taje sumarsa me tsananin daukan hankali aka murda handle din aka
turo,bai motsa ba don yasan mutum daya ne zai masa haka.

Ta cikin madubi ya hangoshi ya shigo. Sai ya samu kansa da dan qare
masa kallo. Yayi kyau cikin wata irin danyar shadda dake nuna nauyin kudaden da aka
narkar domin siyenta,aka kuma keta alfarmar nera tare da nuna mata iyakarta wajen
tsara mata dinkin jikinta.

Farar hula ce saman kanta da aka yiwa nadin farin rawani,wanda aka
saki jelar rawanin ya zubo ta qirjinsa daga gefan kafadarsa ta dama. Iya abinda ya
iya gani kenan,amma fadin yadda shigar ta qarawa farouq din kwarjini ma ba'a
magana.

"Kayi kyau ango" Ya fada da sigar zolaya yana maida idanunsa saman mirror table din
yana aje comb din hannunsa tare da lalubar hair spray.

"Kaima yanzu zakayi naka kyan.....don komai namu iri daya zai kasance". Da sauri ya
daga kai ya kuma juyo gaba daya yana dubansa hadi da fiddo sexy eyes dinsa sosai
zuwa waje,abinda ba kasafai ya fiya yi ba

"Wanne irin rigima ne wannan farouq?,kafi kowa sanin banason manyan kaya basu
dameni ba......for god sake zakace babban riga zan saka harda wani qarin rawani
kamar nine zan jagoranci sallar juma'a na yau din?".

Watsa hannuwansa farouq yayi

"Kai ka sani" Ya fada a gajarce yana nufar inda kayan suke ya soma ware masa.


𝐃ðŪ𝐧ðĒðē𝐚𝐭𝐚 𝐧𝐚 ðĪðŪ𝐝ðĒ 𝐧𝐞
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
ð˜Ąð˜Ē𝘧ð˜Ē𝘧ð˜Ēð˜Ģ𝘊𝘚ð˜Ēð˜ģ

ĖķBĖķOĖķOĖķK Ėķ2

ⱧɄâ‚ēɄâ‚Ĩâ‚ģ

𝙋𝘞𝙂𝙀 9


Page 9
Duniya ta


Tsaye yayi ganin da gaske farouq din yake,daga qarshe baida wani zabi
illar amsar kayan daya dinga yi da daya da daya yana sanyawa.

Komai nashi fari ne qal yayi amfani dasu,tun daga undies har zuwa
complete suturar jikinsa. Qerarren handmade half shoe din me ainihin tsada da kyau
gami da daukan idanu dan asalin qasar italy,da agogon rolex me asalin daraja da ya
samu ado daga wani yanki na gold din da kamfaninsa ke sarrafawa.

Gurin saka rawanin akaso asha daru,amma shigowar ahsan cousin din farouq
ya raba gardaman. Shi ya karba ya nada masa shi tsaf saman kansa

"Ya subhanallah......ya Allah,na taba ganin wanda rawani ya yima kyau kaf tsayin
rayuwata kuwa irinka?.....amma ban taba ganinsa dashi ba farouq" Ya maida tambayar
kan farouq sanda fuad ke tsaye gaban madubin yana kallon yadda fuskarsa ta fita fes
kamar an sauya masa ita. Wani annuri shi kansa yaga tana futarwa wanda bai taba
gani ba,da gaske manyan sutura suna qarawa mutum kwarjini,karon farko yaji manyan
kaya suna sake burgeshi.

"Lokaci yayi" Yaji farouq yana fada ba tare da yaji amsar da ya bawa ahsan ba.

"Ya salam" Ya fada sanda suke yo tattaki shi da farouq da ahsan zuwa
ma'ajiyar motoci na Bristol din. Yawan matasan masu jini a jika daya gani kowa
cikin shigar fararen kaya da babbar riga ya bashi mamaki. Abokan da da yawa ya
manta dasu,wasu kuma haduwa tayi wahala,saidai kowa a cikin su yana cikin jerin
sahun matasan da suke wasa da kudi som ransu saboda samun cikakken

Please Login or Register in order to submit comment