You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qare......ba abinda
bakiyi mana ba,banda ke da Allah ya jefo mana da yanzu bansan a wanne bigire
rayuwarmu take kai ba......zan kula miki dasu fiye da yadda kike muradi"

"Na gode titi......kina da tsohuwar waya da bakya amfani da ita?"

"Banga abun godiya a nan ba,hasalima kamar wajibi na na aikata.....akwai wayata da
kika canzamin sanda zamuyi tafiyar nan......bari na dauko miki ita"

"Idan zan samu da wata wayar daban zanyi kira" Ta fadi tana qoqarin hada numbers
din momma a kanta.

Banda tana da kaifin basira da saurin riqe abu ba yadda zata iya hada
number wayar momma din,saidai cikin ikon Allah ta hadasu tsaf ta kuma kira
zuciyarta na bugawa da fatan ta kira daidai.

Bugu uku aka daga,muryar momma ta mamaye speaker din tana amsawa da
sautin da yake kama sak dana ummensu,sautin da har tata mutuwar ta risketa ba zata
manta dashi ba.

"Mom......momma" Sabreen din ta kirata bakinta yana rawa idanunta suna cika fal da
hawaye.

"Sabreena?.......kun dawo?,yaushe kika dawo?"

"Daga ina?" Ta tambayi momma din a mamakance qwallar idonta suna tsagaitawa.

"Tafiyar da kukayi mana ke da me gidan.......ko sanda zan koma ai naso haduwa dake
dole sai hannun surukarki nabar qannenki.......saboda dole sai passport dinsu ya
zama ready.....duk dama dai munyi magana tana ta iya bakin qoqarin ta,kuma kusan
kullum sai munyi waya da yaran". Mamaki ya sandarar da sabreen,sai ta bude bakinta
a hankali

"Momma me ya faru?,ban fahimta ba,ita ta nema ki bata su?"46


"Eh kusan hakanne,don naso ganinki ban samu ganin naki ba......tafiyar tawa bata
shiri bace......abbansu ne rashin lafiya ta taso masa,dole kuma ana buqatata a
kusa,a yadda na tsara zan jira passport din nasu da komai ya kammala,amna dole na
tafi saboda jinyarsa,saidai ba inda zan barsu don ban aminta da hannun kowa ba.
Randa nake wannan tunanin saiga surukarki Allah ya jeho ta. Ita ta roqeni na bata
yaran zata sanya mai gidanki yayi magana don a kammala basu komai da wuri,tace kuma
zata turosu ko ta kawominsu da kanta,to amma lokacin da nayi tsammani ma sai gashi
har ya gota. Kawai abinda yake kwantarmin da hankali duk sanda mukayi waya da yaran
alamu suna nunamin basu da matsala ko damuwar komai". Kai kawai sabreen ke
jinjinawa tana sake girmama kaidin maamah din. Ta tabbatar ita zata kawo tsaiko a
samun fasfunansu,wataqila ma kuwa an samu ta riqe ne taqi gayawa momma din. Tanason
ta yiwa momma bayanin da zata fahimceta,amma kuma bataso ta daga mata hankali. Tana
ji a jikinta zata iya komai,kuma wannan lokacin kamar wata dama ce da Allah ya ara
mata akan maamah din

"Momma"

"Na'am sabreen"

"Komai da kike kallonsa a haka yanzu a zahiri ba'a haka yake ba........abinda zance
rayuwarsu tana cikin hadari babba........basa hannunta yanzun suna wani hannun na
daban,saidai bana son ki gayawa kowa,don Allah mommma......koda ta kiraki kiyi
kaman bakisan abinda yake faruwa ba.......in sha Allah nan da kwanaki kadan zan
turosu su biyoki". Shuru momma din tayi tanaji a jikinta ba lafiya

"Amma sabreen me yake faruwa?".

"Ba wani mummunan abu bane momma,kada ki tashi hankalinki.....kawai dai komai
kiyishi kamar bakisan anayi ba" Kai ta jinjina bawai don hankalinta ya kwanta ba
sukayi sallama.

Tana ajiye wayar ta sabule zobunan hannunta guda biyu na gold,ta kama
hannun titi ta zubasu tana kallon idanunta.

"Yanzu bani da contact na kowa.....inaso ki saida wannan,ki nema mutumin da ya muku
visa na fita india ya yiwa su huda duka su ukun komai,inaso kada su wuce sati biyu
a nan don Allah titi". Zobunan ta kalla sannan ta maida dubanta ga sabreen

"In sha Allah.....zanyi duk yadda zanyi na miki abinda kikeso". Kai ta jinjina tana
jin wata nutsuwa tana saukar mata. Murya ta daga ta kira huda,ta shigo ita
daya,abinda ya sanya titi miqewa don basu guri.

"Ina wayar hannunki?" Ba musu ta dauki wayar daga kan cinyarta ta miqawa sabreen
din. Saita karbeta tana juyata a hannunta. Waya ce me asalin tsada da kyau wanda
kusan sai wane da wane. Idanunta ta maida fuskarta tana kallonta

"Huda baki dago komai ba?,bakiji komai ba game da matar da aka kira da sunan uwar
mijina?" Tayi mata tambayar kai tsaye tanason samun wani abu daya danganci maamah.
Shuru hudan tayi,tana qoqarin recalling komai,tun daga ranar farkonsu cikin gidan
kawo yau.

Siririyar ajiyar zuciya ta sauke,a hankali ta maida dubanta ga
sabreen

"Inajin kawai batamin ba.....duk kirkin da take gwadana mana sai nakeji jini na da
nata kaman bai hadu ba.......sannan yadda take mana kirki kaman ba haka dabi'arta
take ga masu aiki qarqashinta ba" Hudan ta fadi abinda da gaske haka takeji a
zuciyarta take kuma hasashe.

Wani siririn murmushi sabreen ta saki tana saukar da kanta qasa gami da
juya wayar hannunta. Anzo daidai gabar da tafiso.....anzo daidai wajen da zata
gwadawa maamah shege......anzo daidai gurin da zatayi wasa da hankali da kuma
tunaninta kamar yadda mage kanyi da qadangare ko bera a duk sa'ilin da yayi gigi ko
kakambar shiga hannunta.

Daukewa murmushin fuskarta yayi lokaci guda,ta maida kallonta kan hudan

"Ina fata ba wani abu na cutarwa data taba muku......idan kuma akwaishi ko da da
mugun kallo ne ina saurarenki". Kai ta girgiza tana kallon addar tata,tanason kuma
fahimtar dalilin da yasa taketa mata tambayoyi haka

"Babu kwata kwata adda......saidai kawai nidai hankalina ya kasa nutsuwa da ita...
Musamman da ya zamana kusan ko yaushe tana mana alqwarin zata kawomu wajenki sai
kuma ta gaza cikawa.....har sai da mijinki yazo.....shi yace ta barmu muje".
Jinjina kai take tana duban huda dake bayani,fuad ne kenan.......me yasa yace suzo
din?,shima akwai yiwuwar yana da nashi boyayyen manufar?.

"Kinsan garkuwa tayi daku?,kidnapping a fakaice?" Tambayar ta zowa huda a bazata,ta
zaro idanunta waje tana dafe hannunta saman qirjinta.

"Kidnapping fa adda?" Kai ya gyada mata gami da lumshe idanunta,sai kuma tace

"You are free in sha Allah.....zaku bi momma mali soon......abu daya nakeson na
gaya miki ko bayan kun tafi......be smart as much as you can.......ki dinga amfani
da kwanyarki da basirarki.....ki kula da nadra da Haneefa,ki zame musu garkuwa
kamar yadda na zame muku.....sannan......ki zama mara saurin yarda da mutune,walau
maza ko mata,a family yake ko a wajen family......saurin yarda tushen kowacce
rushewa ce" Ta qarasa maganar tana nunata da yatsa.

Iska ta zuqa sosai sanda take cikin napep din sannan ta furzar da ita
waje,tana jinta kamar mutumin daya dauki dutsen dala da gauron dutse yau Allah ya
'yan tashi ya samu saukeshi daga saman kansa. Sakayau take jinta,wani farinciki
yana ratsata gami da iskar abun hawa wadda ta manta rabon data ratsata. Ta ware
idanu sosai tana kallon titi.....Don yaushe rabonta data fito?,ko fitarta ta qarshe
cikin rufaffar mota ne qarqashin kulawar jami'an tsaro.

"Sabreena Ahmad AKA MUHSEENA" Sunan da taji an ambata kenan saitin kunnenta. Ko
daga bacci ta tashi tasan waye?......wannan wata shaidace kuma stamp ne daya
kasance nasa shi kadai. Mashkur....ta gayawa kanta da kanta,don haka ta tattara
dukka nutsuwarta da qarfin halinta ta maida sashen da sautin ya fito.

Shi dinne,zaune a seat din driver,ya dafe dukka hannuwansa saman
steering din motar yana jifanta da wani zazzafan kallo. Duk da yadda haushinta da
wutar son daukar fansa ke ruruwa a ruhinsa.......amma hakan bai hana shaidan
harbawa zuciyarsa wutar matsananciyar sha'awarta ba. A yadda yake hangen wani
lafiyayyen kyau a tattare da skin dinta......wani irin kyau da abaya fatarta bata
sameshi ba,sai yakejin burinsa ya ninku zuwa gida biyu,YA DAUKI FANSA sannan kuma
YA KASHE QISHIRWAR SHA'AWARTA A RANSA. Dadaddiyar qishirwar data maidashi sakarai
kuma shashasha a kanta duk da tarin tsananin wayonsa.

"Damn it!" Ya furta da qarfi yana dukan steering din motar tasa gami da cije lips
dinsa gami da kashe mata idanu guda daya. Salin alin ta dauke dubanta daga
kansa,tana jin wani matsanancin faduwar gaba yana saukar mata. Faduwar gaban da
bata taba ji ba a kansa ko akan wani d'a namiji ba idan ka dauke fu'ad din

"To ko wannan shine haqqin aure da kowacce mace kejin nauyinsa a kanta?" Ta tambayi
kanta da kanta tana jinjina girman abun. Kafin ya sake cewa komai traffic light ya
sakesu,motarsu ta riga tasa yin gaba. Cikin mamaki sai ta samu kanta da addu'ar
kada ubangiji ya bashi ikon ganinsu har ya biyosu yaga gidan da take,duk da ta
sani......gidan su zai wahala ya zama wani boyayyen gida da zai wahalar da za'a iya
ganoshi.


*MUHAMMAD FU'AD*

Basuyi nisa can can ba ya tuna yabar file dinsa a gida,wanda file ne
dake da muhimmanci ya dubashi a yau ya tura da bayanan cikinsa ga company din da
suka nema sanya hannun jarinsu a kamfanin. Ba kasafai ya fiya son yin alqawari ba
tare daya cikashi ba,idan har hakan ta kasance ta tabbas baida yadda zaiyi ne,don
haka ya sanya su saddiq sukayi gaba,shi kuma suka juya da wasu motocin suna dawowa
gidan.

Wuri wuri zuwaira tayi ta shiga raba idanu sanda taji dirin shigowar
motocin nasa harabar gidan. Raba idanu ta shiga yi sannan ta furta kalmar

"Na shiga uku!" Bayan ta tuna gargadin da yayi mata a ranar daya fara ganinta.
Yadda tasan halinsa ta kuma haddaceshi bata haddace fuskarsa haka ba,ta tabbatar
yazo ya sameta a sassan kamar yadda ya gargadeta shan ruwanta a gidan ya qare. Wani
abu guda daya da bata qaunar ya faru......zaman gidan yafi mata zaman ko
ina......zaman gidan cike kuma yake da 'yanci,ba kyara ba tsangwama,hakanan ba
nauyayen aikace aikace a cikinsa,sabanin gidan maamah din da yake cike da tsarabe
tsarabe kala kala.

Wuf tayi ta miqe tana dosar qofar da zata sadata da sassansu kamar zata
ci da baka,cikin ranta cike fal da Allah ya qarawa laila tare da fatan ubangiji ya
hadata dashi yaci zarafinta har fiye da tunaninta taga yadda abun zai kaya.

Da nutsuwar nan tasa ya shigo cikin falon,idanunsa suna kan inda ta
tsaya a dazun sannan ta waiwaya tana komawa ciki. Ya janye lumsassun idanunsa yana
wucewa parlor na biyu,daga nan ya doshi qofar da zata sadashi da hallway da kuma
stairs dinsa.

Saurin ja yayi da baya kaman yadda itama taja da baya da sauri. Ya
zuba mata idanu yayin da ita kuma kwarjininsa yaso bugar da ita. Bata shirya ba
amma sai gata tana rusunawa gami da gaidashi

"Barka da safiya hamma.....ya aiki?"

"Kece laila?" Ya tambayeta yana dinke girarsa tsaf saboda yadda yaga abun ya masa
wani iri. Ta yaya zata ratsa privacy dinsu ta shigo har nan wajen?,wani irin rashin
hankali ne da ita matar gidan zata bari haka ya faru?. Shi din wani irin mutum ne
me tsananin son privacy,kamar yadda yake da iyakoki akan komai daya shafi
rayuwarsa.....kuma kowanne mutum da nashi iyakar.

Murmushi ta saki tana wani karyar da wuya gami da rolling idanunta a
kansa

"Eh hamma.....nice.....baka gane ni ba?,nazo ne duba.....ammm.....ammm
sabreen,maamah nason magana da ita da gaggawa,so kuma unfortunately sai na duba ko
ina na gidan amma babu ita.....infact ma ta fita.....".

Banbarakwai yaji maganar kamar da wani yare daban take magana. Ta
fita?,zuwa ina kenan?,sannan da izinin waye ta fita?. Ajiye duka maganganun yayi
gefe guda yana dubanta

"What I have told you tun ranar farko?.....so ki hada kayanki kibar gidan nan" Yayi
maganar da murya me kaushi dake cike da zallar umarni.

Hukuncin ya daketa so sai hakanan ya mata tsanani,iya ganinsa data
sakeyi yanzu ya sake tada tsimin soyayyarsa a zuciyarta,saita dubeshi a rikice

"Amma hamma....maamah ce....."

"Arguing won't help the situation" Ya fada da wani irin yanayi maras hargagi saidai
kuma me ban tsoro ne a idanuwanta. Sum sum da wani irin sagaggiyar gwiwa tsoro da
bacin rai ta miqe tana fita daga wajen. Ya bita da wani irin matsiyacin
kallo,sannan yaja tsaki kamar zai tsinke harshensa.

Har ya taka stair case din sai kuma ya dakata. Ta fita bata
gidan?,maganar ta dawo masa fes cikin kansa. Juyawa yayi don tabbatar da abinda
lailan ta fada,ya fara bincike gidan guri guri.

Kaf ya gama duba ko ina a gidan,ya kuma tabbatar bata nan din. Wani
wutar fushi yaji tana ruruwa cikin ransa,yana so yaje ya saukewa duka Securities na
gidan,amna kuma wata zuciyar na gaya masa MARTABAR AURE koda sunanta MATARKA KADAI
A FATAR BAKI.

Samun kansa yayi da bin lafiyar daya daga cikin kujerun parlor din
farko,yayi relaxing kawai a ciki yana jin yadda jijiyoyin kansa suke harbawa,ba
abinda zuciya bata raya masa ba,ina ta tafi?,wajen su waye taje?.

"Da igiyar aure na?" Ya tambayi kansa da kansa yana jin yadda zuciyarsa yadda take
tafasa. Bai taba tunanin akwai wata diya mace da zai bari tayi masa wasa da
igiyoyin aurensa da ya biya sadakin daya nemo da guminsa ya bayar ba,kai koda
sadakarta aka bashi muddin da sunan muhammadu fu'ad jikan jadda aka daura bazai
taba bari wani abu ya gilmawa mutuncin igiyarsa ba......idan shi ya warwareta tofa
wannan daya.

Ba kasafai ake barin napep shiga unguwar ba,wannan ya sanyata dole ta
sauka daga baya ta sallameshi,sannan ta fara takawa cikin nutsatsen takunta zuwa
street din nasu.

Duk gidan dake da security a wajen suna ganinta sai taga suna miqo
gaisuwa da wani irin respect,abun sai ya shiga bata mamaki ita kanta. Wai har girma
da matsayinsa yakai wannan?,sannu sannu sai taga alamun mamaki bisa fuskar duk
wanda ya ganta tana takowa da qafafunta.

A hankali taji alamun tafiyar tayar mota daga bayanta. Bata waiwaya
ba,don tun can dama ita bame damuwa da abinda bai shafeta bane47

_Daga abdullahi dan abbas R.A yace,Lokacin da aliyyu R.A ya auri nana fadima,sai
manzon Allah S A W yace"ka bata wani abu(a matsayin sadakinta),sai sayyadina Aliyyu
yace "ba komai a wajena" Sai manzan Allah S A W yace "ina sulkenka?"_




"Ameenatu" Taji muryar nan dai ta dazu tayi kiranta. Sai da taja numfashi sosai
tana son danne bugun da zuciyarta keyi sannan ta waiwaya inda ya daidaita motarsa
saitinta,yana zaune kusa da window yana murxa steering hankali kwance fuskarsa
shimfide da wani shu'umin murmushi.

"Na rantse wannan karon ba zaki sha ba......na miki wannan alqawarin muddin na
haifu cikin uwata da ubana......lallai saina maida sha'awata a kanki......sai kuma
na bankadawa duniya wacece ke bayan na maido kudadena cikin dukiyata......ki rubuta
ki ajiye" Daga haka yayi saluting nata,sannan ya taka motar da gudu yana wuceta.

Bata fasa takawa tana nufar gida ba,kamar yadda bata fasa bin bayan
motarsa da kallo ba har ya qurewa street din nasu. Wata mahaukaciyar fargaba tana
ratsa zuciyarta,sunan mashkur tare da cikakken sanin wayeshi yana gewa tunaninta,a
haka ta isa qofar gidan,ta kuma yi tsaye tana duban dogayen katangun gidan kamar me
karantar ilimin zanen gidaje.

Tana wassafa yadda zai iya tsallake wadannan dogayen katangun mansion
House din......tana qiyasta ta yaya zai iya wuce wadannan securities din da
samudawan dake tsaron kowacce kusurwa ta gidan?. Tsaron gidan kadai ya dan sanyawa
zuciyarta nutsuwa.....saidai kuma bai kore fargaba ko kuma ya mantar da ita wanene
ASALIN MASHKUR BA.

Gangar hankalinta bata dawo jikinta ba sai data sanya qafafunta cikin
gidan,idanuwanta kuma sukayi mata arba luxury cars dinsa dinnan dake ajiye a
parking lot na gidan.

Sai yanzu ta tuna bata nema izinin kowa ba sanda zata fita,don sam ta
manta hakan yana cikin wata doka dake kan kowacce macen aure.....baya ga haka.....a
lokacin ba abinda take iya tunawa illa hanyoyin da zata nesanta rayuwarsu da maamah
din.

Da confidence din ba lallai su hadu ba har ta wuce daki.....ba lallai
ma yasan bata a cikin gidan ba ta tura glass door din parlor din tana sanya
qafafunta.

Da bude qofar da haduwar idanuwansu lokaci guda ya faru. Iya kallon
data gani cikin rusunannun idanuwansa sun bata wata fargaba da bata taba jinta akan
kowa da komai ba.

Dakiya ta aro ta azawa ranta,tana jin a ranta a yanzu daidai take da
kowa a cikinsu.....ko shi ko mamarsa. Tana jin lokaci bijirewa dukka wani sharuda
nasu yazo,tana jin abinda ya rage mata biyu ne......ta samu tabbacin fitarsu zuwa
mali a sannan takejin zaman wannan qallagaggen gidan dama me gidan gaba daya ya
qare mata.

Cikin dakiya da basarwa taci gaba da takowa kaman bataga kowa zaune a
parlor din. Tsaf ya gama karanta da kuma fahimtar abinda take shirin aikatawa. Ba
za'a fishi sanin miskilanci take taken miskili da kowacce dabi'a tasa ba,sai ya
dauke kai kaman bai damu da takunta ba,zuciyarsa na sake matsewa,ransa kuma yana
qara baci har zuwa sanda ta raba tsakiyar falon.

Ba zato ba tsammani ta tsinceshi a gabanta. Tsaiwarsa yayi mugun dab
da ita,hucin fitar numfashinsa da wani irin dumi da yake bayyanar da bacin rai da
zuciyarsa ke ciki yana sauka saman goshinta. Motsawa tayi da nufin ja baya don bata
tazara a tsakaninsu qirjinta na wani irin bugawa,saidai da tsananin zafin naman nan
nasa ya cafki hannunta yana matsawa da kyau

"Daga ina kike?!,ina kika fita?,gurin waye kika je?" Ya tambaya a jere cikin tsawar
data ratsa dodon kunnenta har sai data runtse idanunta.

Tattara dukka qarfinta tayi ta sabule hannunta daga nasa,wanda ta
samu sauqin hakanne saboda banguls din hannunta ya riqe saita zame ta barshi
dasu,saidai ko taku biyu batayi ba ya rufo mata baya,sai ya zamana tana tafiya da
baya da baya,shi kuma yana maida qafarsa kowanne gurbi data cira qafartata.

Kowanne taku guda daya sai qwayar idanunta sun gauraya da nashi.
Abinda take gani cikin idonsa batasan wanne iri bane......wani yanayi ne da bazata
iya fasaltashi ba. Yana sake kunsatota yana sake maimaita mata tambayoyin da suke
sake razanata,bata ankara ba taji ta bugi bango,tabbacin kowanne space ya qare mata
kenan,sai tayi cak sanda ya iso dab da ita,cikken motsi idan tayi yana iya sata ta
kasance cikin jikinsa.

"Gurin wa kika je?,me kuma kikaje yi nace!"

"Ban sani ba" Ta fada da rawar murya tana qoqarin daidata mode dinta. Ko kusa ko
alama bata tanadi amsar da zata bashi ba.....shi kuma ya matsa mata da
tambaya.....tambayar da ba abinda take mata sai qara fusatata......GURIN WA KIKA
JE?,ME KIKAYI?,idan ya fada din sai taji kamar ha debo garwashin wuta ya watsawa
sassan jikinta ne. Ba abinda yake tuna mata sai mummunar kalmar yawan mutane
musamman na cikin gidansu suke jifanta da ita.....kalmar da koda ta nuna ta
shanyeta tana iya hana idanunta bacci da wani matsanancin fushi da bacin
rai.....shima irinta yakeso ya ara ya yafa yayi aiki da ita a kanta?,batajin
kunnuwanta zasu iya jurar ci gaba da jin ana jifanta da kalmar da bata da masaniyar
komai a kanta.

Hannuwansa ya dunqule waje guda yanason hana kansa marinta da
zuciyarsa keda muradin yi. Bayaso yakai hannunsa jikinta......baya so ta zama mace
ta farko daya fara mari duk kuwa da yanajin ta cancanci haka.


"Karki bari nayita maimaita maganata......ina kika fita ba tare da izinina
ba?....wajen wa kika je?!!!!" Yayi zancan da wani irin qaraji daya sanyata curewa
waje guda,kowanne sashe na jikinta ya dauki rawa

"Banje wajen kowa ba.....ni ba wajen wanda naje"

"....You're going to regret messing with me,for the last time....ina kikaje?" Ya
sake tambayar yana sanya hannuwansa duka biyun dake a dunqule ya daki bangon da
take maqale a jiki ta saitin kunnuwanta. Abinda ya sake gigitata kenan ta saka
hannuwanta duka biyun tana toshe kunnuwanta gami da rruntse idanunta. Zuwa sannan
kowacce jarumta dake jikinta tabi ruwa.....ba abinda ya rage mata sai rauni daya
narke zuwa kuka.

Cikin qasa da second biyu ta tsinci hannuwan nata jikin nata hannun
dake toshe da kunnenta yana saukesu,da wani irin taushi da sanyin murya taji yana
fadin

"Is okay......wanne irin matsoraciya ce ke?.enough,stop crying please" Bata qara
tuna komai ba ta tsinci kanta saman faffadan qirjinsa,ya sanya hannunsa daya ya
lullube bayanta,daya hannun kuma yana shafa gadon bayan nata da irin salon da uwa
kanyi don lallashin jaririnta.

Wani sassanyan qamshi dake ratsowa daga qirjinsa da kuma kowanne sashe
na jikinsa ya cika hancinta da wani irin sanyi daya soma qoqarin daidaita
yanayinta. Saidai hakan ya gaza samuwa,don qarasa rudata yayi,daga yadda kunnuwanta
ke iya jin yadda zuciyarsa take bugawa kadai ya tabbatar mata fusatarsa ta gaske
ce......amma me ya sanyashi sauya yanayi haka cikin qanqanin lokaci tamkar
wahainiya?. To kodai yana da boyayyun aljanu da suke sauyashi haka da sauri?.

Bata gama wannan tunanin ba muryar ma'u ta zame mata amsa

"Ina neman afuwa ranka ya dade.....ayimin afuwa" Ta furta da tsananin kunya tana
sadda kanta qasa. Bata taba tunanin zatazo ta samesu haka dab da juna ba,kwata
kwata ma batayi tunanin suna nan ba,tasan me gidan dai ya fita......dawowar da tayi
kuma tazo dubawa amna ko ta dawo?,don sun hadu ta daya qofar sai kawai ta shiga
sassanta da taji sabreen din bata nan.

Kai kawai ya gyada yana ci gaba da shafa bayanta kadan kadan

"Hajiya amna ce tace nazo na duba kota dawo......"

"......ta dawo.....amma batajin dadi,kice ta qaraso" Da sauri ma'u ta amsa ta juya
tana ficewa a gaggauce.

Kaman yana jira ne ma'u din ta fita ya saka hannunsa ya tureta daga
jikinsa. Banda yana kusa da bangon daya bata kariya ba abinda zai hanata zubewa
qasa. Da wani fusataccen kallo yake dubanta.

"Kada ki dauka na yarda ne da abinda kika gayamin......muddin na bincika na samu
wani abu na daban saina miki mafi munin hukuncin da baki taba tunani
ba......hakanan duk ranar da kika qara gangancin fita koda qofar gidan nan ne ba
tare da izinina ba......saikinyi dana sanin sani na........nan din gida ne da aka
gina da tsaftatacciyar dukiya ta halas.....ba bariki bane ba ba kuma hotel ko gidan
karuwai ba" Daga haka ya juya yana daukan file dinsa dake ajiye saman daya daga
cikin kujerun falon yana ficewa da sassarfa.

Wani irin kuka ne yakeson qwace mata amma tana hana kanta,don idan har
kunnuwanta sun jiye mata daidai amna na gidan,kuma zata iya iskota koda wanne
lokaci,dole ta tattaro dukka wani bacin rai tana hadiyeshi,saidai kuma abinda
takeji yafi qarfin abinda zuciyarta zata iya dauka,sai bacin ranta ya zabi fita ta
hanyar fitar hawaye daga idanunta zuwa saman fuskarta,ta lallaba tana neman kujera
daya ta zauna a kai tana dafe da kanta.

"Oh god........ damn it....." Abinda ya dinga maimaitawa kenan cikin mota yana saka
yatsunsa cikin sumar kansa.

Ya manta yaushe ne lokaci na qarshe daya fusata irin haka.....yaushe
rabon da yaji zallar bacin rai irin wannan dake ratsa kowanne sassa na jikinsa. Ya
alaqanta hakan da tozarta igiyar aure da yake shirin faruwa. Sai ya samu kansa da
blaming kansa,me yasa zai daga hankalinsa har haka?,ai duk wanda ya siya rariya
yasan zata zubda ruwa. Ransa yaji yana qara baci,sai ya yiwa driver magana ya qara
speed na motor din.48


_An karbo daga abu hurairah Allah ya qara yarda dashi yace,manzon Allah S A W
yace,idan miji ya kira matarsa zuwa shimfida taqi zuwa,mala'iku zasuyita la'antarta
har gari ya waye_

*_qarqashin wannan hadisin akwai qarin haske,idan a wannan qin da tayi kuma ta samu
ciki koda ta rasu wajen haihuwa wasu malamai suna ganin bata samu wannan shahadar
da mace me naquda ke samu ba idan ta rasu_*




*MAAMAH*

Tunda ta cewa zuwaira taje ta duba mata su taci gaba da kiran wayarta ba
qaqqautawa don ta

Please Login or Register in order to submit comment