You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har saman fuskarsa. Idanu abban yadan zuba masa,har a ransa yana
cike da zallar mamaki na yadda me babban suna ke damuwa da anni da rayuwarta fiye
da dukkansu su ukun. Annin da abban yake ganin ba itace halitta ta farko data
cancanci samun wannan qauna da kulawa daga gareshi shi din ba......annin da yake
ganin kulawar da yake bata baifi ya bata kaso hamsin cikin dari ba.......ita kanta
wasu lokuta tana sanya damuwa a ranta game da inda yafi karkatar da kulawar tasa
sama da daya bigiren da shine dolensa,.....kuma akafi buqatar hakan daga gareshi.

"Yanzun haka ma nan da awa daya zan fita,zamu gana da ceo na Labrilliante
company,zan miqa musu iya abinda zasu samu.....don abba wannan karon tunanina ya
fara sauyawa" Maganar fu'ad cikin tatacciyar nutsuwar nan tasa da wani irin jan aji
kamar mace ya dawo da Alhaji hamza daga tunaninsa

"Wanne tunani ne fu'ad?" Zamansa ya gyara sosai yana bawa abba dukkan kallo da
hankalinsa

"Abba......a yadda mutanen nan daga kowacce qasa suke rububin siyan resources namu
da muke fiddowa daga qarqashin qasar da Allah ya shimfida mana kadai ya isa ka
fahimci suna amfani damu ne suna kuma amfani da damarsu......yanzu haka a daren
jiya kafin na kwanta sai dana karba kira daga wani company dake japan bayan ainihin
kamfanin da muke kaiwa kaya......suna taya kayanmu akan farashin da wancan kamfanin
basa bamu......wannan shi yasa nayi wani nazari......abba ya kamata qasarmu ta
amfana da wadannan ma'adanai masu tsada da daraja,wanda mu Allah ya mallakawa
su.....abba inda a qasarsu wadannan ma'adanai suke,babu wani baqar fata daya isa ya
sameshi.....it's hardly ka iya isa wajen......nayi tunanin bude babban company da
zai dinga sarrafa wadannan ababen zuwa kayan qyale qyale na mata.....don dama
company daya muke da na alhaji rayyan(dangantakar zuciya),shi kuma duwatsu masu
daraja suke sarrafawa ba gold ko diamond ba".

Shuru abba yayi yana girgiza kai. Tabbas fu'ad din yazo da tunani me
kyau daya kamata ace tuntuni sun yishi

"Na yarda da wannan tunanin naka.....to amma fu'ad qarqashin haka akwai tarin
matsaloli da qalubale......"

"Na sani abba......insecurity na qasarmu ma kawai qalubale ne......amma a
hakan.....ya zama dole mu raya qasarmu da kowanne qaramin chance da muka samu a
rayuwarmu......tsoro da tunanin asara ko faduwa shine abinda zaici gaba da kasheta
kowacce rana......bayan tsoron dauko shi akayi aka dasa mana shi a
zukatanmu......kuma ake da buri da fatan ganin ci gaba da wanzuwarsa har zuwa
rayuwar na bayanmu"

"Best son ever" Abban ya furta yana sakin wani irin murmushi tare da jin qarin
alfahari da fu'ad din,gefe guda kuma yana taya ainihin mahaifinsa murnar samun
nagartaccen yaro mara tsoro irin muhammad fu'ad din.

Qas yayi da kansa cikin girmama abban

"A tayamu da addu'a abba"

"Kullum cikinta muke"

"Allah yaja kwana,ya qara lafiya me amfani" Ya masa addu'ar da yake jinta har cikin
zuciyarsa.

Agogon dake manne a bango ya kalla,sai ya miqe a nutse yana cewa

"Zan qarasa ciki abba na shirya kada na sabawa lokaci"

"Hakan yayi kyau" Abba ya fada fu'ad din yana sake burgeshi saboda yadda ya dauki
alqawari da matuqar muhimmanci kaman yadda yake girmama lokaci.

A nutse ya tura qofar dakin da sallama a bakinsa,duk kuwa da yasan ba
wanda zai taras a ciki. Dakine da duka duka basufi sati guda a cikinsa ba......amma
har ya kama ya kuma rine da sassanyan qamshin nan nasa dake iya bawa zuciya nutsuwa
da kwanciyar hankali koda cikin radadi da qunci take.

Towel din hannunsa ya rataye,ya kuma matsa gaba kadan ya ajjiye
takalmin motsa jikinsa wanda daga ranar da suka tasamma barin Korea sunansa shara.
Baya yawo da kaya,kowacce qasa zaije,koda kwana nawa zaiyi single yake tafiya
abinsa,saidai yana sauka a qasar komai da zai buqata na amfani zai sanya a tanadar
masa,yana gama amfani dashi kuma a nan zai barshi ya qara gaba.

Matsawa gaba kadan yayi gaban wata mini dispenser da tafi kama da
tulun zamani wadda ke zaune saman wani kyakkyawan table kusa da mirror,ya dauki
disposable cup ya matsi ruwan dake da madaidaicin yanayi ya fara sha a hankali
bayan yayi tsaye gaban madubin idanunshi a kai kamar me karantar yadda yake zuqar
ruwan zuwa cikinsa.

Ya gama ya ajiye saman madubin yana fidda siririyar iska yana ci gaba
da kallon fuskarsa a madubin. Kyakkyawar sumar kansa data wadatu da tsafta ya taba
sannan ya gangaro zuwa madaidaiciyar qasumbarsa data hade da gemunsa wadda ta
zamawa fuskarsa wani lafiyayyen ado daya qara fidda zahirin kyawun fuskarsa,ta kuma
qara masa wani mahaukacin kwarjini. Gemun da qasumbar daya zama topic of discussion
a wajen 'yammatan da suka marmace a kansa. Kusan kowacce tana gayawa kanta namiji
babu gashi a fuska ai mace ne,bata taba ganin qasumba da gemu da yakai kyan nasa
ba......tsabar macewa a soyayya ne.....ko kuma zallar tsagwaron gaskiya suka fadi?.

Rigar jikinsa ya yaye zuwa sama sannan ya zareta ya ajjiyeta saman
gadon,wannan ya bawa Ginannun muscles din jikinsa bayyana muraran. Muradden jikin
da zai gaya maka adadin lokutan da aka bata ana bashi kulawa ta fannin lafiya da
cin lafiyayyen abinci me gina jiki. Yayi taku daya don dauko bath set nashi zai
wuce toilet sai ya fasa,ya dawo da baya ya dauki wata farar samsung dake ajjiye
saman mirror din.

Yaga miscal amma sai ya fara maida hankalinsa ga dalilin daukar
wayar,ya latsa ya fara lalubar magaji. Umarni ya bashi na abincin da zai hada masa
kafin ya fito,saiya maida wayar yana shirin ajeta kira ya shigo wayar.

Cak ya tsaya yana kallon sunan dake tsalle saman wayar. MOM kaman
yadda farouq ya dauka da hannunsa yayi masa saving. Kafe sunan yayi da
idanuwa,wayar tana kadawa hade da zuciyarsa. Sunan yake tuna ma'anarsa da kyau
cikin kwanyarsa.....wadda aka maqalawa sunan ta cancanci wannan sunan kuwa
anya?......ta dace data karbi sunan?,nata ne sunan da gaske?.

Kamar bashi da idea akan yadda ake daga waya,haka yaci gaba da
kallon wayar har ta qaraci ringing ta katse. Ya sake daga qafarsa zai wucs kiran ya
sake shigowa. Kamar dai dazu a yanzunma haka ta gama kadawa ta katse,kira na uku
kuma ya sake shigowa immediately,saidai akasin dazu,yanzu sunan daya fito akai ya
banbanta dana dazu.

Lovy dovy shine sunan daya bayyana,sai ya saki qaramin murmushi yana
dawowa baya kadan. Kafin ya daga sai daya kalli lokaci,tabbas ya tsaya saurarenta
ya tabbatar saita kwakwashe masa duka mintunan daya tsara zaiyi a gidan ya fice
zuwa Labrilliante amma hakan bai sanya ya fasa dagawa ba,ya sanya wayar a kunnensa.

Da siririyar baby voice dinnan nata tayi masa sallama. A nutse fuskarsa
a sake ya amsa

"I will call you back habibty.....nan da one hour haka?"

"Yes habibee.....byeee" Ta fada cikin rashin damuwa da kuma fahimtarsa a duk sanda
ya sako mata uzurinsa. Wayar ya mayar ya ajjiye yana murmushi,daidai sanda a daya
BANGAREN.........


Ta daga kai ta kalleta sanda take zaune a gabanta

"Waya yake amsawa hajiya" Ta fadi tana sauke wayar daga kunnenta bayan computer ta
gaya masa ana amfani da layin ta hanyar amsa wani kiran

*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*
*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA
TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰


*D U N I Y A T A*
*_H U G U M A_*

*Arewabooks:@Huguma*

https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997


PAGE 32
___________________________

Waya kuma ake amsawa?” Ta tambaya cikin wata irin isa sa ginshiri tana qanqance
idanunta,qwayar idanun nata suna kan wadda tayi maganar. Kai ta jinjina mata cikin
bata tabbaci

“Eh haka ne”. Juyawa tayi ta zauna sosai tana fesar da iska me zafi daga bakinta.
Ta qanqance idanu sosai tare da zubawa guri daya idanu,abinda zai baka tabbacin
akwai wani radadi me yawa da take ji daga cikin zuciyartata

“Alamu kenan suna nuna yaga kiran,nice dai…….nice dai da bazai amsa wayata ba,nice
dai da bazai saurareni ba sai a sanda yaga dama ko kuma aka bashi umarni?” Ta
qarashe maganar ta hanyar yiwa kanta da kanta tambayar. Tambayar da bata haifar
mata da komai ba sai qarin qunci da bacin ran da ya sanyata miqewa tsaye.

Hannunta ta dunqule ciki juna,ta fara kai kawo tana naushin
tafin hannunta da daya hannun data dunqule waje guda. Ba shakka tayi sake ba dan
qarami ba,ba shakka kuma hajiya mariya tana son jefa kanta tsakiyar shingen da ba
nata ba. A baya tayi tarin ayyuka game da hakan,amma idan har tace taga nasara
tattare da hakan to tayi qarya me yawa ma,zata iya kiran ayyukanta na baya da JIYA
I YAU,tana tsaye a waje daya babu sauyi ko qanqani,zata zuba idanu ne abubuwa
mafiya daraja da kima a rayuwarta…..kuma mallakinta amma ace suna ci gaba da subuce
mata?,suna ci gaba da zama haramiya a gareta?,shin zata yarda da zamowa ‘YAR RAKIYA
ko kuma taci gaba da wanzuwa a mazaunin ‘yar kallo?.

“Ba zata sabu ba!” Ta furta a zabure sannan ta juya da sassarfa tana daukan
mayafinta dake yashe saman kujera

“Tashi samira muje” ta bawa hadimar tata umarni,wadda ke zaune tun dazu guri daya
tana duban kai komo da maganganun da takeyi ita daya

“Ina hajiya?” Ta tambayeta murya a lanqwashe. Tayi imanin tunda har ta buqaci fita
irin wannan afujajan ba shakka ba alkhairi a cikinta sam

“Gidan alhaji hamza!” Ta bata amsa a tsawace da salon abun nan da ake cewa haushin
kaza huce kan dami. Tsam ta miqe tana gyara daurin zaninta sannan ta wuce da
sassarfa zuwa shiyyar dakunansu don dauko hijabi.

Cikin jerin amintattu kuma lafiyayyun dakunan da mansion house
din na alhaji hamza kibiya ya mallaka. Zaune take tsakiyar wani lallausan rug dake
a gefe daya na dakin wanda aka masa rukuni da lausasan sofas qwaya uku da suka
zamewa wajen tamkar wani dan qwarya qwaryar falo ne na cikin bedroom. Wani irin
lafiyayyen daki ne da ba zai barka kasan safiya ko dare ba,zafi ko sanyi,damuna
ballanta rani ba muddin ka kasance wanzajje a dakin.

Daga saman rug din take zaune saman abun salla da zai baka
tabbacin bata jima da kammala sallar walaha ba. Salla ceda bata taba wuceta a
rayuwa muddin ba wani qaqqarfan dalili ya gifta ba,tun zamanin quruciyarta har kawo
yanzu da girma da shekaru suka hau kanta. Shine kuma ya same mata sila da tsani na
dawowa rayuwa hamza a shekarun baya,a sanda ta yanke zato da tsammani daga sake
rayuwa dashi da kuma yaranta da suka zame mata sanyin idaniyarta.

Wataqila nutsuwa da kamalar da fuskarta ta wadatu dashi yana da
alaqa da wannan din,yawan ibada,yawan bautar Allah,yawan azumin tadawwu’i da babu
wanda yayo gadonta a wannan fannin qafa da qafa irin muhammad fu’ad.

Akwai haske sosai saman fuskarta,tana saye da atamfar chiganvy gold
mekauri kyau da asalin tsada. Jikinta lullube da mayafi me kauri,yayin da yatsarta
ke maqale da qaramin carbi irin na ma tsawa.

Daga gefanta saitin kafadarta shine a kashingide,kana kallonsu
zakasan magana sukeyi,magana kuma irin ta da da uwa,hira cikin nutsuwa qauna da
kuma kulawa

“Nikam saddiq……sake kiramin wayata mana,jakata tun ranar da akayi asibiti dani ban
sake ganin gilmawarta ba,akwai muhimman abubuwa a ciki,harda kudaden Amna data bani
ajiya” idanu ya zaro sannan ya miqe yana zama sosai

“What?,anni?,dollars fa?”

“Wallahi sadiq” ta fada a nutse.

“To Allah ya tsananta rabo,don auta ta saka buri akan wannan ajiyar,naji tana
lissafin abinda zatayi dasu idan ta dawo” ya fada yana cusa hannunsa a aljihu yana
laluben wayarsa. Fuskarta anni ta shafa tana fadin

“Idan har ba’a gansu haka zata haqura ai,tsautsayi da qaddara tana wuyan kowane
bawa”.

Shuru sukayi dukkansu suna saurareb sautin din…..din,sautin
dake gaya musu lallai kiran ya isa ga wayar anni dake tare da documents dinta da
kuma sauran kudade masu kauri cikin jakar.

Kamar cikin mafarkinta ta dinga jin wani sauti mara qarfi yana ratsa
kunnuwa zuwa kwanyarta.

Shuru tayi ba tare data motsa ba,daddan ring tone din mara hayaniya yana
tasowa can qasa qasa,da alama akwai abinda ya sake rage kaifin sautin.

Sai data fahimci ba cikin bacci bane sannan ta qarasa bude fararen
idanunta da suka qara girma saboda bacci. A hankali ta yamutsa fuskar tata sannan
ta sanya hannunta ta maida lallausar sumarta me tsaho data rufe rabin fuskarta
baya,ta juya daga rub da cikin da tayi zuwa rigingine sannan ta miqe ta zauna sosai
tana wuwwurga idanunta zuwa kowanne sashe na dakin don gano ainihin ta inda sautin
yake fita.

Ba kowa a dakin,don tuntuni su huda sun gama shiryawa sunyi abincin
safe kaman yadda suka saba sun wuce makaranta,don ko idanunta bata iya budewa tace
dai kawai su buda jakarta su dauki kudin makaranta su kuma ja mata qofan idan sun
fita.

Fes dakin yake kamar kullum kamar kuma ko yaushe,sai ta saka hannunta
ta tattare gashinta ta qulleshi tsakiyar kanta idanunta ta tsaiwa kan medium
luggage din dake cike da tsarabar da aka kawo mata,wadda ko samun damar budeta
batayi ba.

Tayi matuqar gajiya a jiyan,tana fita kusan kowacce rana.....amma
bata yin awanni masu yawa kaman haka a wajen. Komai nata yana da lokaci tsari da
kuma iyaka. Ta zube fararen qafafunta saman qaramin carfet data sanya musu daga
gaban gadajen nasu saboda sanyin tile,ta jawo dankwali me santsi ta daura sannan ta
miqe tana isa gaban luggage din.

Sai a sannan ta kuma gasgatawa daga cikin qaramar handbag dinta
sautin ke fita,jakar ma da gaba daya ta mance da ita tun ranar data je musu siyayya
ta dawo,ko tarkacen ciki bata kwashe ba. Hannu ta zura tana laluben meye yaketa
qara din haka cikin jakar,sai kawai ta wuce gaban gadon ta zazzage jakar gaba daya
saman gadon.

Kyakkyawar purse baquwa ta gani cikin jerin tarkacen dake cikin jakar
wanda ta tabbatar duka nata ne. Onion color me ratsin maroon a jiki. Hannu ta miqa
ta jawota,ta dagata a hannunta tana jujjuyata cikin mamakin a ina ta samo ta?,kuma
ta waye?,tun yaushe take cikin kayan nata?. Kamar anason sanar mata da amsar duka
tambayoyinta ne sai wannan siririn sautin da ya tasheta a bacci ya sake kadawa daga
cikin jakar.

Kai tsaye ta zuge jakar,ba wani ba wata ta sani waya ce. Wayace qila
da take da alaqa da mamallaki ko mamallakiyar jakar.

Wata siririyar Samsung ta gani,ta sanya hannu don cirota da gaggawa
gudun kada kiran yanke,take sabbin dollar din dake maqale a zip na daban na jakar
suka biyota suka fada saman cinyarta hade da qananun hotunan passport. Ba wannan
bane a gabanta,don haka batabi ta kai ba ta fara duba sunan dake yawo saman screen
din wayar

MUSADDIQU NA....shine full name din dake jikin number. Tadan tsaya tana sake duba
sunan da kyau tare da bitar karantashi,sai kuma tadan tabe baki kadan sannan ta
daga kiran ta Kara wayar a kunnenta

"Alhamdulillah.....an daga anni" Musaddiq ya fada yana sanya wayar a kunnensa.

Shuru tayi tana sauraren motsin dake fita daga daya bangaren,kafin
daga bisani sallamarsa ta maye gurbin shurun. Muryarsa a nutse dake dauke da kamala
yayi cikakkiyar sallama data sanyata motsa bakinta da tata siriryar muryar tana
amsa sallamar.

"Barka da warhaka" Ya fada a nutse.

"Yauwa.....barka" Itama ta amsa masa a taqaice

"Don Allah idan ba zaki damu ba zan iya tambayarki wayar nan ta waye?" Banbarakwai
taji tambayar tazo mata,har sai data sake duba sunan dake jikin wayar,amma yanayin
yadda muryarsa ke nuna kamalarsa da nutsuwarsa ya sanya tayi gyaran murya daban

"Kaman sunan me kiran dana gani akan wayar yana da alaqa me qarfi ko kuma mafi
kusanci dame wayar ko?". Murmushi ya saki,yadda tayi maganar cikin fasahar harshe
da tsari sai yaji ya burgeshi,hakanan kuma a karon farko ya gano muryar,yakuma dago
ko wacece

"Hakane ranki ya dade.....idan na canka dai dai.....kamar mutuniyar kirkin nan kuma
baiwar Allahn nan data ceci rayuwar mahaifiyarmu ko?" Dan jim tayi tana son gano
ma'anar zancansa,don tuni rayuwarta taci gaba daga inda ta tsaya,tuni ta shiga wani
babin kuma na daban,ta manta abinda ya faru dazu jiya bare shekaran jiya.

Haka policy na rayuwarta yake. Ba kasafai take bawa komai gurbi
cikin rayuwarta ba bare ta hadu da traffic akan dukka plans nata da kuma tunaninta
ba.

"Dattijuwa me asthma a masallacin HGMS store?"
"Oops....." Ta furta a hankali,yanayin daya sanya musaddiq sakin murmushi don ya
fahimci abun ya kwanta mata

"Kayi haquri don Allah,ka kuma nawa mama haquri,na hada da purse dinta ne a cikin
kayana bisa rashin sani,bansan ma da ita din ba sai yau da aka kira"

"No....karki damu......mune ma muke fata Allah yasa bamu takuraki ba....."

"Zaku iya karbanta a jambulo third gate.....link 5" Abinda ta furta kenan ta yanke
wayar,daidai sanda anni ta miqa hannu da zummar karbar wayar su gaisa.

"Ya ka katse wayarwayar inaso mu gaisa nayi mata godiya da ban gajiya"

"Daga canne anni ta yanke......" Ya bawa anni amsa yana duban wayar tare da mamakin
yadda take magana da bada amsa haka cikin taqaice komai

"Babu matsala.....amma zanso sake ganinta ko magana da ita......zanso nayi mata
godiya sosai,dukan wanda yayi saving rayuwarka ai baka da sama dashi.....mutum ne
me matuqar kima da martaba cikin rayuwarka.....har yanzu ina iya jin sanda ta
rungumeni sosai a jikinta kamar ta sanni......sai na dinga jin kamar amna ke riqr
dani......ta damu sosai kamar mahaifiyarta ce a cikin halin" Ta qarasa maganar tana
duban fuskar musaddiq,fuskarta kuma na nuna abubuwa da dama da zuciyartata taji.
Zamanshi sosai ya gyara yana murmushi.



*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA
TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*
*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

*Arewabooks:@Huguma*


PAGE 33


"Ni kaina anni ina iya hango sanda taketa masifa da fada da gaske wai
mun banzatar da rayuwarki,bamusan illa da kaifin ciwon ba......amma fa anni kaman
ina zaton.....anya bata da ciwon itama ko wani nata?" Yayi tambayar yana duban anni
kamar annin tasan zahirin maganar.

Cikin isa izza da jin cewa takai kowanne qololuwar mataki na rayuwa
ta ratsa babban falo kuma na farko na gidan,ta ratse dukkan wasu hadimai da kuma
masu aiki na farkon gidan,falon farko har ta dangane da falo na biyu.

Kowanne taku idan tayi idanunta suna sauke zazzafan kallo ne akan
kowanne alatu da kuma jayan jin dadi na rayuwa dake kowanne muhalli na falon.
Kowanne abu da idanunta zaya sauka akai tana debe kallonta ne daga kanshi cikin jin
wani irin zafi da quna gami da radadi idan ta tuna cewa MUHAMMAD FU'AD ne ya yishi
tare da gumin dan uwansa MUSADDIQ.

Da wannan tunanin ta tsaya tsakiyar falo na biyu hannayenta riqe da
qugunta tamkar qaramar yarinyar da take ganiyar fitsara da kuma jin cewa tana
daidai da kowa.
Ko ita dinma a yanzun kusan hakan take. Tsaiwarta a falon qiris ya
rage dukkan wani ganuwar haquri nata kawaici da yakana da takeyi su qare,haquri da
kawaicin da take ganin tunda tazo duniya bata taba yiwa wata halitta irinta ba

"Amina nakeson nayi magana da ita" Ta fadi kanta tsaye sanda daya daga cikin
hadiman dake da alhakin kula da wannan sashen ta qaraso.

"Eyeee?" Me aikin ta tambaya cike da mamakin yadda ta kirayi sunan dattijuwar data
zame musu baya goya marayi haka gatsal,babu sayawa ko qanqani,duk kuwa da cewa
zasuyi sa'annin juna,amma a garesu kiran ainihin sunanta wani baqon abune da yake
jimawa bai faru ba

"Nace AMINA nake buqatar gani.....uwar farouqu da saddiqu" Ta maimaita a wannan
karon da madaukakiyar muryar data sanya hadimar maida hankalinta ta hanyar dubanta
da kyau,sai kuma taja baya kadan tana cewa

"Inji wa zaa ce mata?" Ta tambayeta tana sake kallonta sosai

"Kice mata uwar Muhammadu da musaddiqu" Sunayen data furta din ya saka hadimar sake
dubanta da kyau,saidai bata ce komai ba don bata da hurumin cewa komai din,ta taka
a hankali ta kama stairs tana hawa a hankali don isar da saqonta ga anni.

Kafin anni ta furta nata hasashen knocking dinta ya dakatar da firar
tasu. Firace da yawancin lokuta musaddiq din yakan qaraso har quryar bedroom din
anni ya tayata don debe mata kewa lokaci lokaci da hanata zaman kadaici. Duk da
cewa gidan cike yake da hadimai wadanda suka aiki qarqashinta ta kowanne fanni da
take da buqata na rayuwa. Hatta hirar akwai masu tayata cikin masu aikin,wadanda
aikinsu kenan,gwanaye ne wajen iya hira da mutum,debe masa kewa da sanyashi
nishadi......musamman FU'AD ya daukesu aiki saboda haka kawai,amma ko kusa ko alama
hira dasu bai kama qafan hira da yaranta ababen soyuwarta ba.


"Waye?" Musaddiq ya riga anni tambaya

"Badawiyya ce"

"Bismillah qaraso" Anni ta bata umarni tana gyara zamanta saman lallausan abun
sallarta.

A nutse kuma cikin girmamawa ta qaraso cikin dakin. Ta tako a hankali
zuwa gaban annin ta tsugunna

"Baquwa kikayi anni" Ta fadi kanta a qasa

"Baquwa kuma?,daga ina?" Tayi tambayar cikin dan mamaki,saboda yau din ba ranar
ganin baqi bane,tana cikin ranakun hutunta,sannan tun bayan dawowarta ma daga
asibiti fu'ad ya hana kowa ganinta,yace saita murmure ta huta tukunna.

"Ban dai kai ga gane fuskarta ba.....tadai ambaci asalin sunanki,tace kuma a gaya
miki babar fu'ad da musaddiq.......kuma...." Tadan fadi tana daga kai kadan ta dubi
fuskar musaddiq da ya

Please Login or Register in order to submit comment