You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaiwa ga wancan wajen.

Hannunsa take qoqarin riqewa....bai hanata ba amma kuma ya soma zare
duk wani qarfi da take dashi saboda dumin numfashinsa da yake sakarwa sasannin
wuyanta zuwa cikin kunnenta,take kowanne sashe na jikinta ya dauki rawa harda
muryarta.

"Ka bari don Allah" Ta fada cikin rawar murya,sai ya dakata cak yana hautsinota ta
dawo suna fuskantar juna. Da rinannun idanunsa da suka fara canza kala yace mata

"Ke kinsan girman Allahn ne?" Yafada yana dage mata girarsa duka biyun. Samun kanta
tayi da kasa kallonshi,saita kauda fuskarta gefe. Hannu yasa ya dawo da fuskartata
daidai saitin tasa yana dubanta.

"Uhnnn.....nace kinsan girmansa?.....kinsan aure dukansa sunansa aure a wajen
Allah?,kina matar aure amma baki iya kula da mijinki ba?.....baki iya komai
bafa.....idan nace komai ina nufin komai irin na mata....matan ma matan
aure........kinaso na mutu ne sabreen?" Mamakinsa ya kamata,ya gama rungume
rungumensa sannan yanzu ya mata wata magana ta daban?.

"Bakya kishina ne?"

"Sonka nake da zanyi kishinka?" Ta fada a tsiwace tana murguda bakinta.

Idanunsa ya lumshe ya kuma budesu kusan lokaci guda,siririn murmushi
ya kubce masa yana kallon baby face dinta da danjaririn bakinta data murguda masa.
Ba abu me dadi ta gaya masa ba,don maganar ta sokeshi a tsakiyar zuicyarsa,saidai
kuma ta masa wani mugun kyau,kuma yaji ta bakinta ko ba yawa a wannan fannin.

Sake jawota yayi ya matseta da kyau kaman zai rabata gida biyu,ya
sanya yatsarsa guda daya ya fara zagaye labbanta sai tayi sauri zata turasu ciki,ya
shammaceta ya hada mata da yatsan nasa,dole ta saki labban nata,abinda ya bashi
daman riqo fuskarta da kyau ya kuma hade labban nasu waje daya.

Wani irin sarrafasu yakeyi a tausashe da nuna zallar qauna,abinda bata
zata ba daga gareshi. Ta dauka anytime kiss abune me zafi ga labba,cikin minti biyu
taji kowacce gaba a jikinta tana saki,kafin kwanyarta ta ankarar da ita suna
kitchen sakamakon qarar qofar kitchen din. Tureshi tayi da sauri,ta saka bayan
hannunta tana goge labban nata. Da fushi a muryarta tace.

"Banason wannan abun.....wannan ai qazanta ce" Tayi maganar ne da harara,harara
data fidda farare sol din idanunta. Kamar dafi haka yaji ta zuba masa jikinsa dukka
ya amsa,ya shammaceta ya jawota ya sake matseta yana same hade bakunansu,ya tattara
miyau din bakinsa duka ya dure mata. Bai barta ba sai daya tabbatar ta hadiye
sannan ya sake boyeta a qirjinsa sanda ta saki siririn kuka.

"Am so sorry.....inason mu sake zama abu daya ne bayan wanda muka sake zama
din.....amma tunda na miki ba daidai ba.....biyani yawu na" Ya fada yana qoqarin
sake kai bakinsa cikin nata. Ta gama fuskantar wayo ne kawai yake son ya mata,don
haka ta fara qoqarin hanashi amma bai bata dama ba,haka ya dinga zuqe duk wani yawu
dake bakinta sai da numfashinsa ya fara fita daban daban daga qirjinsa sannan ya
sake ta yana maida numfashi.

"Duk abinda na miki idan bakiso zaki fara biyana daga yau......ki karbi wayarki a
hannun amna" Yana kaiwa nan ya juya yana barin kitchen din saboda jin yana neman
loosing control dinsa. Ya riga yayi alqawarima ransa indai ba takura yayi maqurar
iyaka da zai iya shiga halaka ba.....bazai sake karbar komai ta qarfi ba....zaiyi
iya yinsa ya amintar da ita.

Idanunshi a rufe suke,sam bai kula da farouq dake zaune a parlor din ba
sai da yaji muryarsa yana cewa

"Ranka ya dade sir" Yana dunqule hannunsa irin na girmamawa. Kallo daya ya masa ya
fahimci zai wahala bai shiga kitchen da zummar dauko wani abun ba idanunsa sunyi
masa gamo,don haka baima tsaya biye ta tasa ba ya wuce daki abinsa yana jin dariyar
farouq din. Saidai qasan ransa yasha alwashin tasu ce shi da farouq din,yaga alaman
bazai taba barinsa ya sake ba.....baya jin zasu qare zamansu a Maldives a wannan
gidan....musamman da maamah ke dab da isowa,yana jin gidan tabbas ya musu
kadan ,don haka ba wanda ya sani bayan ya sakarwa kanshi ruwa ya fito,ya yiwa
Jordan maganar duba musu wani apartment din a siya zuwa nan da jibi yalwatacce
sosai da yafi wannan.

Sulalewa tayi a nan tana dafe da kanta,da qyar ta iya saita kanta ta
miqe tana gyara yamutsatsen hijabinta da tuni ya saukeshi daga kanta. Can qasan
ranta tana mamaki,wanne irin tsafta ne dashi haka?,duk sanda yayi kusa da ita irin
haka qamshin mint leaves ne ke fita a bakinsa,wanda da alama ya kama bakin nasa
sosai,wanne irin freshener na baka yake amfani dashi haka?. Tsaki taja qasan ranta
tana ture wannan tunanin daga ranta,ta matsa gaban sink ta ringa watsawa fuskarta
ruwa don kada ta koma anni ko amna wani ya gane wani abu,sai data tabbatar taji
daidai sannan ta dauki gorar ruwa daya ta fita a kitchen din. Farouq din yasan
tabbas zata fito,bayaso kuma taji kunya ko nauyinsa,don haka sai ya wuce dakinsu
bayan shigewar fu'ad,wannan ya bata daman shigewa dakinsu salin alin.

Qin yarda tayi ta hada ido da kowa kota zauna,sai tayi shigewarta duvet
kawai tana qundundunewa waje daya. Amna tana toilet,batasan kuma ta shigowa ba sai
data fito. Cikin hanzari ta qaraso dakin tana cewa.

"Albishirinki adda?" Daga can qasan maqoshinta ta amsa da

"Goro". Tana bin amna da kallo wadda ta dosota da kwalayen waya guda biyu ta zauna
gefanta.

Duka biyun ta zaresu daga kwalinsu,bakinta ya kasa rufuwa.

"Ya Allah kaban miji irin hammana.....you're luckiest woman adda....." Idanu
sabreen tadan fidda

"Bakwa kunyar anni amna?,yanzun da tana dakin haka zaki ce?" Dariya ta qyalqyale
dashi.
"Ki zabi daya.....idan nice ma duka zance inaso......falcon supernova.....the most
expensive phone in the world.....it's worth more than 77mil in naira......irinta
hamma na ke using,ita kuma wannan itace ta biyun ta a tsada" Amna ta fada tana juya
duka wayoyin tana duban sabreen.

Adadin kudaden kawai sai da suka sanya kanta yayi tsawa,million saba'in
da bakwai?,ina zata kai irin wannan wayar?,wacece ita?,waye ubanta a Nigeria?,idam
shi ya riqe matsayinsa yakai ne.....arziqinsa yakai....amma kuma ita fa?,ita da
take dorin dosano?,kwanaki nawa ya rage mata ra barshi ma kwata kwata?.

Numfashi taja ta lumshe idanunta tana kullesu,ba zata iya gayawa amna kai
tsaye bata so ba.....ba zata kuma karba ba,don haka tace.

"Ki ajiyesu,zan duba gobe"

"Done.....amma please ki dauki irinta hammana please adda"

"Naji" Tace da amna don kawai ta bata wuri ta shaqata.

_nikuwa nace ya kamata sabreen ki karbi wayar nan don ki gigita surukarki hajiya
maamah da ita,kin bata tabbacin mallakar fu'ad da taketa fafutuka taki ce kenan_
πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

Tana sane ta narke tun daga daren ranar har wani daren,tayi qaryar
zazzabi don kada anni tace taje suyi sallama da fu'ad da zai tashi zuwa macca kai
tsaye gobe da safe. Ta samu nasara kuwa.....don har ya shigo ya musu sallama tana
kwance tana baccin qarya.....duk da cikin jikinta tana jin idanunsa a kanta suna
yawo,ya juya ya fice su anni suna taka masa.


_Turqashi......maamah bisa hanya_

_komai fa yana shirin faruwa me karatu_

_idan nace komai.ina nufin komai maπŸ˜‚_

_pages din gobe masu zafi ne,kada ka yarda su wuceka_

_Ya zata kaya tsakanin maamah da sabreen ga anni a tsakiyarsu?_

_yaya zata kaya sanda maamah ta fahimci zazzafar soyayyar sabreen a idanun
susutaccen d'anta?_

_shin zata iya dauka?,ko zata cika qudurinta na rabasu?_


_Shikenan fareeda ta haqura?,ko zata sake wani motsin?_

_waye da waye ne suka shiga hannu?_

_ita kanta fareedan ta sha ko kuwa?_

_akwai ragowar zafafan al'amura fa masu karatu,muje zuwa ga gangarar labarin_🧏🏽




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 89




89



Iska me zafi ya furzar daga bakinsa yana dan dafe goshinsa,duk wani energy
nasa yaji yana tafiya,ta yaya zai iya tafiya wani qasar ba tare da sunyi sallama da
ita ba?. Ya sani ya kuma fahimci tana sane duk tayi hakan,wayarma daya batan baiga
alamun ko guda daya a hannunta ba. Iska ya sake furzarwa yana jin tsoron kada dai
furucinta na rannan ya zama gaske da tace bata sonshi. Sai ya zura hannunsa a
aljihunsa ya fito da wayarsa ya fara kiran number amna.

Ita da anni ce kawai a dakin,annin ita ta karbi wayar saita miqa mata
tana cewa.

"Hammanku ne......basu tafi ba kenan" Ba zata iya musu da annin ba bata kuma fita
ba bayan ta bata wayar bare ta aje wayar yadda ta saba masa. Ta latsa ta sanyata a
kunnenta,ta motsa labbanta a hankali tana amsa yin sallama.

Har tsakiyar zuciyarsa yaji saukar sautin sallamartata. Yayi jarumtar
daidaita yanayinsa don bayaso ta fahimci komai,don yana son komai zai gaya mata ta
daukeshi da muhimmanci.

"Ina kika shiga?" Ya mata tambayar a gajarce data rasa amsar da zata bashi. Shuru
tayi tana kame kamen abinda zata gaya masa,bata samu ba har ya sake cewa.

"Kinsan tafiya zanyi yau really?" Can qasan zuciyarta tayi qaramin tsuka tana cewa

"To mene ruwana da tafiyarka?,ka wuce mana ta can ma karka dawo Maldives,amma a
fili sai ta zabi jan bakinta tayi shuru.

"Alright......yayi kyau....ina wayar dana bawa amna ta baki?,baki dinne bata yi
ba?". Ya sake tambaya da wani irin shan qamshi da bata taba ji ya mata ba,hakan sai
ya mata kwarjini gami da taba zuciyarta.

"Ta bani" Ta amsa masa a hankali kaman wadda batason tayi magana. Amsan ta bashi
haushi kadan,don shi daya yasan yadda ya matsu da jin muryarta amma taja wayar ta
ajiye.

"Bakiga daman amfani dashi ba kenan?.....well....bazan miki komai ba a
yanzun.....amma kika sake har na dawo na samu wayar a yadda na baki ita.....sai
nayi punishing naki ta hanyar da bame iya karbanki......and idan ma kin bude kin
fara using da ita....if kika ce zakimin abinda kikemin a wayar anni da amna bawai
kin tsira bane.....take care of your self......byee" Ya fada yana sauke wayar. Sai
a sannan yaji zuciyarsa ta koma daidai,duk da ba irin wannan sallamar yaso suyi
ba,amma at least ya samu nutsuwa kadan. Bayaso ya fiya zafafa mata da yawa....don
baida tabbaci ko yaqinin zuciyarta ta karbeshi,saidai ko meye yana da yaqinin bazai
qyelata haka ba,sai yayi mata dashe da kuma ginin da bazai kankaru ba.

Wayar tabi da kallo kafin ta ajiyeta a gefanta. Sau tari idan yana wani
abun sai zuciyarta ta dinga gaya mata plan ne kawai da siyasa irin ta 'yan
kasuwa,kamar kawai yanaso yaci gaba da mata wayo yana amfana da jikinta ne. Har
yanzu ta gaza gasgata kanta wai mutum kamar muhammad fu'ad da mutunci ko arziqi ba
shine silar gamuwarsu ba ace dare daya don kawai ya amshi budurcinta ya koma haka
ba. Kulawa qauna soyayya da wani irin mayataccen yanayi da bata taba ji ko gani ba.
A duk mazan da sukayi alaqa dasu a baya bata taba ganin wani abu na musamman
kebantacce tattare dasu irin wannan ba. Da gaske wannan shine son?,da gaske wannan
din ake kira da soyayya ko kuwa yaudara ce zallarta?.

_to masu karatu ku bata amsa_


β˜… *_Makka/Jeddah_*


Tafiyar awa biyar zuwa shida ta kaisu garin jedda,a nan ya tsaya yayi
wanka ya saka hirami ya dauki niyyar umararsa. Daga nan kuma lafiyayyen train ya
daukesu kai tsaye zuwa makka.....motar da aka tanadar masa ta qarasa dashi masauki
cikin hotels mafi tsada dake dab da harami.

Fairmont makkah clock Royal tower nan ya zaba,ko maamah dinma yasa an
maidata can,hotel ne dake da kusanci sosai da haram,kai tsaye daga dakinka kana iya
hango ka'aba. Baida gurin sauka duk zuwan da zaiyi sai nan din,saboda samun kusanci
da Allah da samun daman yin addu'o'insa sosai koda cikin dare ya farka. Sau tari
yakan jima gaban window din dakinsa yana qarewa dakin Allah kallo,cike da shauqi da
tsoron azabarsa da kuma fatan samun rahamarsa,yana jin inama yayi zamansa a nan ya
qare rayuwarsa.

Nutsuwarsa da samun salamar ruhinsa daban yake jinsu a ransa duk
lokacin daya shigo wajen,yana jin kansa sosai kusa da Allah,don haka koda ya iso
wucewa yayi kai tsaye yayi dawafi da sa'ayi yayi sallarsa raka'a biyu ya sauke
umararsa. Bai nema ganin maamah ba sai daya sauke faralin umran da bayajin zata
isheshi. Zuwa yanzu baisan sau adadin nawa yayita ba.....bayajin kuma zai daina yin
nata muddin da numfashi a jikinsa da kuma damar zuwan.

Dakinsa ya koma royal suit ya sallami abdulbasit da abdul gaffar da
abdus sabur wanda su ya sanya suzo su zauna tare dashi. Hiraminsa ya cire ya nema
wasu kayan ya sanya yana duba lokaci. Akwai gajiya sosai tattare dashi,yana buqatar
ya hutawa kwanyarsa sosai don ya samu space din yadda zai iya tunkarar ko meye
maamah zata zo masa dashi. Labulen dakinsa ya daga,idanunsa suka sauka akan dakin
Allah,wajen tarwai yake da cikakken haske kamar kullum,da tarin bayin Allah masu
neman duniya dama lahirar gaba daya. Bayason wani babban abu ya faru tsakaninsa da
maamah a irin wannan wajen,dole yana buqatar neman taimakon Allah.

Nannuyar ajiyar zuciya ya sauke sanda fuskarta ta dawo masa tarwai
cikin idanunsa. Idanunsa akan ka'aba din,ya sanya hannunsa saman qirjinsa ya dafe
yana jin yadda qirjin nasa ya cika da soyayyarta,a hankali ya furta.

"Ya raheem......kada ka bawa mahaifiyata galaba a kaina muddin da sabonka da kuma
son zuciya tazo". Sai ya dakata yana jan numfashinsa sosai.


"Ya ubangiji.....kaine mahaliccin zukata.... Kaine ke iya jujjuyasu a duk sanda
kakeso,ya rabb,kafin kowa sanin menene abinda ke zuciyata na ainihi a kanta,ban
aikata mata komai ba don na zalunceta ko na cuceta ba,ban aikata mata komai saboda
qiyayya ko abisa sanina ba....ya rahman....ka sanya mata matsananciyar soyayyata a
zuciyarta,ka sanya ta soni irin son da nagartacciyar uwa kewa d'anta......irin son
da bashi da misali.....irin soyayyar da na jima ina fata da burin samu daga wajen
macen aurena.....ya ubangiji,na gode maka abisa kowacce ni'ima da kayi a
gareni.....na yadda cewa mahaifiyata itace jarrabawar rayuwata......na rasa
soyayyarta soyayya ta ainihin da aka santa daga zuciyar uwa zuwa 'ya'yanta.....ya
Allah yadda kayimin madadi da anni.....na roqeka kayimin madadi da ameenatu
sabreen.....ka maidata sanyin idaniyata......Allah ka azurtani da salihan yara ta
tsatsonta.....ka sanya albarka cikin kowacce tarayya da zanyi da ita....Allah ka
wankemin idanuna da samun qarin 'yan uwa nagartattu bayan su musaddiq,wato yaran da
ameenatu zata haifamin" Ya qarasa addu'ar labbansa suna sanyi,zuciyarsa tana jin
wani irin sassauci da sauqi,a take kuma sai kewarta ta cikashi. Baisan me ya sanya
dukkanin burinsa a yanzu ya fara karkatawa kan samun 'ya'ya ba......abune daya jima
a ranshi,amma halin maamah da yadda ta watsar da rayuwarsu ya kashe wannan burin.
Yana ganin duk macen da zai dauko ma haka zata kasance akan 'ya'yansa kaman yadda
maamah tayi musu ta kuma yiwa abbansu.

Sakin labulen yayi a hankali,yana ji a jikinsa tamkar dukkanin
addu'o'insa sun amsu,sai ya koma ya zauna bakin gadonsa yana daukan wayarsa.

Maamah din yaso kira don ya shaida mata ya iso,amma cikin rashin sa'a
sai ya kasa samunta. Hakan ya masa dadi,don ko ba komai zai samu ya matse gajiyar
daya debo,don haka ya aje mata tex kawai,sai ya tsinci kansa da neman layin wayar
sabreen din.

Bai taba zaton zai samu wayar a bude ba,bai dauka zataji warning dinsa
ba,amma ga mamakinsa dab da zata tsinke aka daga. Lumshe idanunsa yayi yana jin
qarin wani sassaucin da rangwamen yana sauka a zuciyarsa,ya koma da baya ya kwanta
akan gadon bayansa bayan ya sanya pillow qasan kansa.

Shuru kawai tayi tana sauraren iskar dake fita ta wayar.

"Baki iya sallama ba?.....me yasa kullum kike maida kanki yarinya sosai?" Ya
tambayeta a tausashe yana jin ba dadi baqin halayenta. Ta maida kanta wata sokuwa a
gabansa,ba dogon magana sam.....musu ko tsiwarma sai taga dama takeyi masa su.

"Assalamu alaikum" Ta samu kanta da masa sallamar. Qasan ranta a tsorace take da
maganansa kadan kadan. Tanaso su rabu ba tare daya sake taba jikinta ko ya kasance
da ita ba......amma ta duba ta dubo ba wani hanya daya rage illa ta bishi ta yadda
ya bullo mata,ba tare daya ankara ba zai wayi gari babu ita.

Wani sauti na daban yakeji yana shiga kunnensa tamkar yau ya fara jin
amsuwar sallama.

"Amincin Allah kema ya tabbata a gareki DUNIYATA.......gani kusa da dakin
Allah.....me kike buqatar na roqa miki?". Ya fada da wani kwantacce kuma sassanyan
sauti da shauqi da kewa suka cikashi.

Har cikin jikinta taji maganarsa ta mata dadi,tana da tarin buqatun da
zata roqa a wajen Allah idan har qaddarar zuwa wajen ta tabbata a kanta. A yanzu
dukka ta qosa subar Maldives,tana jin nauyin tambayar amna wanne guri zasu je
next.....amma a nata zabin a ture dukka kowacce qasa a barta a tsakanin saudiyya
zuwa madeena. Tana tsaka da wannan lissafinne taji muryarsa yana cewa.

"Na roqo ubangiji yasa ki soni....irin matsanancin son da ba zaki iya rayuwa ba
tare dani ba.......na roqi Allah ya sanya ki zama madawwamiyar ni'ima a
gareni......na roqeshi kada ya baki ikon barina koda kina da nufin aikata
hakan.......ya mallakamin rayuwarki gaba daya daga farkonta har
qarshenta.......sannan na roqeshi ya bani 'ya'ya masu yawa ta jikinki.....duk
shekara so samu ki haifemin tagwaye ko uku uku......"

"Please mana" Batasan sanda ta tsaidashi da fadin wadannan kalmomin ba. Tunda ya
fara jero mata abinda ya roqa din zuciyarta ke wani irin bugu,ta sani gurin da yake
wajene da babu wasa a cikinsa.....wajene da komai ka roqa amsashshe ne a wajen
Allah......tana tsoron kada addu'arsa ta cita.....kada ta kamata,idan hakan ya
kasance ina zata saka burin rayuwa tare da 'yan uwanta bisa kyakkyawar rayuwa?.

Dan qaramin murmushi ya subuce masa yana jiyo alamun tsoro cikin
sautinta.

"Tsoron me kike haka?,akwai cutarwa cikin addu'ata?" Ya tambayeta yana ji a ransa
inama hirar zatayi tsaho tsakaninsu.

Kai ta girgiza kaman yana gabanta,da gaske tsoro yana sake cikata.

"Wannan son kai ne.....zallar son kaine a cikin addu'arka,ka roqi Allah wani abun
daban ba wannan ba" Tayi.maganar da dan hasala a muryarta tana ganin kaman da gayya
yayi hakan. Boyayyen murmushi da bai bari taji sautinsa ba ya subuce masa.

"Me ruwanki da abinda zan roqa Allah yayimin?"

"Ina da ruwa dashi.....saboda a kaina ka roqi ubangiji...."

"Ke kuma kina tsoron hakan ya tabbata?.....to idan akan wata daban na roqa fa?"
Shuru ya ratsa kunnensu na wasu sakanni kafin yaji tace

"Wannan kuma ruwanka bana sabreen ba" Ta samu kanta da fada,sannan ta gimtse wayar
tana kasheta gaba daya.

Yaji saukar layin nata,sai ya zame wayar daga kunnensa murmushi yaqi
barin fuskarsa. Me yasa tun asali baiyi dabarar bata waya ba kaman haka ya kuma
kafa mata sharuda ba,haka hira da masoyi take da dadi dama?. To amma wani hanzari
ba gudu ba.....me yasa tayi shuru sanda yayi mata tambaya ta qarshe kafin tace
ruwansa?.

Maido fuskar wayar yayi saitinsa,ya rubuta mata gajeran saqo ya tura
mata,ya koma ya kwanta rigingine wayar ba rungume a qirjinsa. Wani murmushi ke fita
saman fuskarsa kadan kadan,zuciyarsa cike da fatan saisaita kansa akan
yarinyar.....don da haka ne kawai zai saitata a hanyar da yakeso ta tabbata a kai.

Shidai baisan ya akayi bacci yayi awon gaba dashi ba,saidai ya cika
mafarkansa duka,cikin kowanne gani da zai mata cikin qauna soyayya da kuma kulawa.
Harda wanda ya gansu kewaye da yara qananu masu kama dashi sosai. Wannan mafarkin
shi ya haska asubarsa,ya shiga bandaki ya daura alwala cike da wani kwantaccen
farinciki qasan ransa.

Cikin jallabiyya 'yar Indonesia fara qal ya shirya ta maza,ya shafe
jikinsa da lallausan turarensa ya saka hular tashi ka fiya naci saman kansa fara
qal itama,ya dauki tasbaharsa counter data kasance farar itama.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 90



90


Wayarsa ya zura a aljihunsa bayan ya duba number dakin maamah. Kai tsaye
can ya nufa yana tafiya da cikakkiyar nutsuwa a tare dashi,bakinsa dauke da ambaton
Allah. Yanaso ya samu sahun gaba gaba,wannan ya sanya yake tashi da wuri koda
yaushe,ya kuma isa masallacin da wuri.

Kallon kallo suka yiwa juna shi da maamah din,alamu sun nuna tashinta
kenan a bacci. Bata ce masa komai ba ta saki qofar ta juya zuwa ciki ya bita a
baya. Guri ya samu ya zauna yana duban dakin dake cike da kaya wanda ya tabbatar
tsaraba ce. Yaushe ma taxo?,yaushe ta samu daman yin ibada sosai har ta fada yin
wata tsaraba?. Duk abinda zata siya din ba abinda bata dashi a gida,amma fadan
hakan kaman laifi ne a wajensa.

Bandaki ta shiga ta daura alwala sannan ta fito,tana sauya hijabin
jikinta ya soma gaidata kaman yadda ya saba cikin bata haqqinta na uwa daidai
misali na girmamawa.

"Ka shigo tun jiya.....sai yanzu aka baka daman zuwa inda nake?". Idonsa ya
kawar,shi yasan ko.meye zai faru tsakaninsa da maamah din bame sauqi bane,saidai ko
meye ya gayawa Allah yana kuma da yaqinin komai zaizo masa cikin sauqi.

"Nayi qoqarin kiranki ban sameki ba,na aje miki saqo na dauka zaki amsa,banyi zaton
a irin lokacin zan sameki a daki ba shi yasa na koma na huta,sai bacci ya daukeni"
Ya fada a taqaice. Qwafa kawai taja tana qare masa kallo a fakaice. Ita kadai tasan
me takeji a ranta,ita kadai kuma tasan me ta shirya zata aiwatar.....tana ji a
ranta idan har bata sanya fu'ad ya auri fareeda ba lallai ta cika lusara
asararra,wala'alla fareeda din itace wannan hasken nasarar guda daya da boka ya
mata albishir dashi.

Har ya gama shiryawa suka fice tare bata sake cewa komai ba,dama ba wani
sabo ko shaquwa tsakaninsu ballanta hira me kama da irin wannan ta biyo baya.

Zata iya cewa bata taba samun sallar asuba irin haka ba kaman yau,basu
bar masallacin ba sai da gari yayi haske,suka hadu gaban hotel din nasu ya dauketa
yin breakfast duk da akwai bada breakfast a tsarin hotel din nasu.

Ba wani abu ya karba ba illa coffee,itakam abubuwa da yawa yasa aka
ajiye mata,yana sipping coffee din nasa amma hankalinta yana kanshi. Inama ace
wannan kulawar ita daya a duniya yake bawa irinta?,inama yadda suka zauna a haka
haka yake zama da ita koda yaushe yana kula da duk wani motsinta......yana jira
yaji umarninta ko haninta?.

"Muhammadu" Ta krashi bayan ta gama tauna yadda zata fuskanceshi. Burinta a yanzu
bai Gaza ganin fitar sabreen cak daga rayuwarsa ba. Da idanu kawai ya amsa mata ta
hanyar kallonta.
"Wacce irin mace kake aura mara hankali da tunani kuma mara kirki Muhammadu?". Gaba
daya sai maganar tazo masa a bazata,ya kasa kuma fahimtar abinda maamah keson cewa.

"Banda yarinyar nan bata da kirki bata da mutunci batasan girman uwar mijinta
ba.....bata taba kirana ta gaidani ba?,bata taba tambayar lafiyata ba.....bata ma
taba nemana ba wai sunan tana auren d'ana?,ni kuwa wallahi ba'a haifi diyar da tana
auren dana kuma zata min riqon sakainar kashi ba" Ta fada cikin fada sosai tana dan
dukan table din da suke kai kadan.

Zame hannunsa yayi daga jikin mug din yana zubawa maamah din idanu.
Zaren tunanukansa suna qulluwa waje guda cike da wani irin mamaki. A nan dimma
akwai wani qullin?, ya tambayi kansa da kansa. A abinda yake kallo akwai cikakkiyar
fahimtar juna tsakanin maamah da sabreen wanda shi ya zama silar daukota zuwa
rayuwarsa,a yanzun me ya bata wannan alaqar da jikinsa ya jima yana gaya masa
gurbatacciya

Please Login or Register in order to submit comment