You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko daya a gidan nan fa.....baka dade da tafiya ba ta
koresu,tunda.ka tafi suma suka koma kwana a gidansu" Faruqee ya fada gaba gadi,yana
jin cewa shima yau yakai bango,komai ta fanjama fanjam.

"To baqin munafuki,na koresu din,kuma wallahi wallahi koni ko su a gidan nan"
Maganar faruqee ta dagawa abba hankali. A cikin gidan da bashi da maraba da kango
suke kwana?,gidan dake cike da memories na iyayensu da suka gushe?,ta yaya suke iya
bacci su biyu rakkin wanda har zuwa yanzu ba wanda yakai shekara sha bakwai ma bare
sha takwas a tsakaninsu?.

"Abba abinci ma aiki me babban suna yakeyi a tasha kullum yana kawo musi gari ko
dan wanke" Musaddiq ya fada a dan tsorace yana satar kallom fuskar mama bayan ya
riqe hannun mahaifinsa da kyau yana boyewa a jikinsa.

Sosai maganar ta dakeshi,zaka fahimci hakan ta yadda kalolin
idanunshi suka sauya duk kuwa da tarin haqurinsa. Farat daya yaji asama'u ta fita a
kanshi gaba daya. Duk matar da zata iya yiwa maraya haka tabbas ya sani nashi yaran
ba zasu tsira ba wadanda suke da uwa da uba,Allah ne kawai mafi sanin haqiqanin
abinda su kansu su musaddiq din suke kwankwada daga hannunta idan baya nan.

Bai taba barin garin ya tafi gurin neman kudinsa hankalinsa a kwance ba
tun daga ranar daya saki mariya. Tun daga ranar daya rabu da mariya bai sake samun
nutsuwa cikin gidansa ko aminci akan 'ya'yansa ba.

"Asama'u?,bakya tsoron fushin Allah kike cutar da marayin Allah?"

"Ni babu abinda Allah zaiyimin,don su din ba dole na bane,wadanda ma suka zame musu
dole sun yakicesu sun zubda bare ni da aka tsinceni da haqorana talatin da
uku.....don haka wallahi bazanyi riqonsu ba,yaranka dai ba yadda na iya dasu saboda
ubansu nake aure"


*_TAFIYA DA GWANI ME DADI_*

‍*ZAFAFA BIYAR*❀‍πŸ”₯
*zafafa biyar* ❀‍πŸ”₯
*ZAFAFA BIYAR* ❀‍πŸ”₯

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA*

_FITATTUN GWARAZAN MARUBUTAN LITATTAFAN NAN NE MASU DAUKE DA SALON LABARAI IRIN
πŸ˜‡_
DABAN DABAN BISA TSARIN TAFIYA DAYA SUKA SAKE YUNQUROWA☺️

_WADANDA SUKA SABA GABATAR MUKU DA QUNSHIN ZAFAFAN LITATTAFAI DA LABARAI MASU
TAFIYA DA HANKALI DA TUNANI_

*_IRINSU_*

BURI DAYA
INAYA
AMEENATU
DALAAL
BAQON MUNAFUKI
KAIMIN HALACCI
TSUTSAR NAMA
WUTSIYAR RAQUMI
BAQAR INUWA
SIRADIN RAYUWAR BILKISU
TABARMAR QASHI
KUFAN WUTA

*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA
TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*
*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*πŸ₯°πŸ₯°


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

*Arewabooks:Huguma*

https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
___________________________


PAGE 12




"Qarya kike,wallahi tallahi yarana dinma ba riqonsu kikeyi ba,koda basu taba gaya
min ba amma na tabbatar ba irin riqon uwa da 'ya'yanta kike musu ba.....irin riqon
da mukayi alqawarin zakiyi musu" Qaramar shewa tadan saki tana tafa hannuwanta hadi
da qare masa kallo tsaf ido cikin ido

"Dama waye yace maka uwar wani zata iya riqon dan wani tamkar nata?,au ashe bakaji
abinda bahaushe ya fadi ba kenan,riqon uwar wani da dan wani ai sai Allah"
Mamakinta ne ya qarasa kasheshi,ransa yakai qololuwar bacin da har ya mance da yara
ma a wajen

"Haka kika ce?,to bari kiji na gaya miki......muddin ba zaki riqe wadannan marayun
ba saidai kisan inda dare yayi miki" Idanu ta fidda tana kallonsa cikin maqurar
mamaki,wato ya fifita matsayin yaran a kanta kenan?,ta yaya zata ma zauna ta karbi
wannan fifikon?,ya za'ayi ma tayi sake har yaga warginta haka?,a gaban yaran ya
kafa mata irin wanna sharadin?,ai duk yadda taso ga son zama dashi ba zata karba
irin wannan mulkin qarfa qarfan ba.

Hannayenta ta sake hadawa ta tafa ta kuma riqe qugunta da kyau tana
dubansa

"Wallahi kaji na rantse bazan riqe su ba,har nakanma na gaji ai bamuyi abinda zanzo
nayi kenan cikin gidan nan ba"

"Tunda kuwa kikace haka saidai ki qara gaba" Gabanta yadan fadi,amma batajin zata
bari ya gano lagonta

"Hakan shi yafi sauqi,amma bazanje nayita zama da dakon aurenka ba,ka gayan meye
matsayin tafiyar tawa idan na yita?" Ta kuma tambaya tana watsa hannuwa

"Na sakeki saki biyu"

"Innalillahi wa 'inna ilaihi raji'un" Me baban suna ya furta yana saka hannuwansa
dukka biyu ya toshe kunnuwansa,sannan ya koma ya sulale yana zama tsakanin kujerun
falon.

"Tafi nono fari,sai me?,dadin abun ai ba kai kadai bane namiji" Ta qarasa fada tana
ture kujerun dining din ta sauka a gaggauce zuwa dakinta gabanta yana wani irin
bugawa da sauri da sauri.

Daga su har abban ba wanda ya iya cewa komai,falon ya dauki shuru
kawai sai motsinta daga can uwar daki tana hada kaya gami da sakin maganganu wanda
basa iya jin ainihin me take fadi.

Mintuna goma kacal ta fito janye da akwatunta da qaramin mayafi yafe a
kafadarta. Daga inda yake ya daga rinannun idanunsa yana kallonta. Abba ya saketa
ne saboda su,me yasa abban zai saketa saboda dalilinsu?. Fitowarta sai tayi masa
kama da fitowar mahaifiyarsu sanda take shirin barin gidan mahaifinsu.

Me yasa ake tafiya ne ana barinsu?,farinjini ne basu dashi ko
kuwa?,ko wani maqalalle kuma boyayyen abune dasu?,me yasa iyaye mata basa
tausayinsu saidai maza?.

Baisan yaushe ya yanke wannan hukuncin ba,shidai ya tsinci kansa a
gaban mama ne,cikin matuqar tashin hankali da karyar da muryar yake fadin

"Don Allah mama kiyi haquri,kada ki tafi saboda mu......"

"Na rantse da Allah zan zabga maka mari idan baka bani hanya ba,munafukan banza da
wofi wadanda babu alkhairi sam a jikinsu sai masifa da balai nau'i nau'i,ai daya
sakenin sai ku ya aureku,gaku nan gashi,kara da kiyashi daukan mara sani" Sai ta
wuce abinta ta barshi da zafafan maganganun daya gaza mancewa dasu.

"Dawo ka zaun me babban suna,waye yace maka ka bata haquri?,waye yace maka zan iya
zama da ita bayan bata sonku?,ba zata iya zama daku ba?,ba zata iya haquri daku
ba?......in sha Allah na muku alqawarin dawowa da mamanku nan da sati guda kacal"
Maganar data Haifar da wani irin farinciki mara misali a zuciyar faruqee musaddiq
harma da sadeeq din da baima mamansu musaddiq din farin sani ba. Yayin da me babban
suna yake binsu kawai da idanuwa,don kunnuwansa da zuciyarsa harma da qwaqwalwarsa
sunyi nisa qwarai da abinda ke wakana a falon.

Jarin maganganun mutane masu tsananin dafi daya soma girma da jinsu
yaketa aunawa. Kullum kwanan duniya wayewar gari zuwa faduwar rana sai yaci karo da
wata mummunar kalma da zata zamewa zuciyarsa tabo wadda ta shafesu da
mutuncinsu,duk kuma MAAMA itace sila,dama uwa tana iya zama silar bacin suna da
rayuwar 'ya'yanta?. Tambayar da amsarta ta kasa samuwa a gareshi kenan,musamman
lokacin da MARIYA mahaifiya ga faruqee da musaddiq ta dawo ainihin dakin aurenta da
zummar riqe yaranta harma da marayun Allah MUHAMMAD DA ABUBAKAR SADDIQ

***************

Faffadan tsakar gida ne ma'abocin yalwa da kuma tarin dakuna da zasu nuna
maka yawan adadin mazauna gidan dake cikinsa.
Tun daga qofar gida,zauruka guda biyu masu girma har zuwa farfajiyar
gidan da wani filin tsakar gida da gidan ya mallaka zakasan cewa asalin ginin gidan
anyi gine na masu wadata a wani qarni can baya daya shude.

Duk kuwa canzawar siffar ginin zuwa zubin ginin daya dauki
shekaru,amma yanayin yadda akayi zuba ginin da kyakkyawan tubali hakan ya hanashi
muguwar lalacewa ko muzanta daga suffar kyau zuwa ta tsufa.

Dakuna guda hudu manya manya gidan ya mallaka lailaye da siminti
da tsakar gidan ya wadatu dashi da fulasta wadda ke nuna yau ta jima da samuwa a
jikin ginin gidan. Kafin idanunka yakai ga duqurqusar matakalar bene dake qarshen
qofar daki na hudu a jerin dakunan gidan. Rijiya ce da aka dan dagata kuma aka
rufeta da murfi na langa langa. Idan ka sake kai dubanka kuma can zuwa sashen
hannun hagu na gidan,bayan ka wuce bishiyar mangwaro data samu muhalli na dindin da
Tsakiyar gidan,kai tsaye kana iya hangen qofar da tafi kama data makewaye,da kuma
qofar babban kitchen na gidan daya hada kowa da kowa.

Akwai gurabe daga jikin bangon gidan da zai sanyaka ka fahimci a
baya akwai wasu shuke shuke da sukayi zamani daga bangwayen gidan,saidai yanzun
babu ko wanne tsiro idan ka cire bishiyar dake a Tsakiyar wadda gushewarta ita din
ba abu bane me sauqi.

A tsaftace gidan yake ba laifi,wanda kusan gado ne da kuma asali da
tsafta daya samo cikin gidan koda kuwa bayan gushewar me gidan da rasuwar mace daya
cikin matan aure uku da ma gidan ya mallaka a lokacin rayuwarsa.

Safiya ce sosai,kusan qarfe bakwai da rabi na safe agogo ya nuna a
daidai lokacin. Kowacce qofa ta gidan a sakaye take,sai wata qofa guda daya qyaure
ta ya banbanta da sauran qyamaren gidan kafataninsu.

Ba zaka gama fahimtar yadda banbancin yake bai tsaya daga qyauren
kawai ba.....aah,har sai ka samu nasarar kutsa kanka cikin ainihin falon dake hade
da uwar daki kaman kowanne daki na gidan.

Kyawawan labulaye ne da aka yiwa dakin qawanya dasu ruwan toka wadanda
sukayi daidai da sofas guda biyu dukkansu 3sitter da aka gewaye falon dasu hakanan
suka dace da lallausan daddumar da aka shimfida a tsakaninsu qirar qasar turkiya.

Akwai lausasan pillow guda hudu manya dake zube a qasa dukkaninsu kala
daya da labule zuwa kujerun. Daga bangon dakin ta fuskar hagu kuwa,bango ne da
yasha wallpaper me kyau aka kuma yiwa TV plasma me matsakaicin girma da reciever
dinta mazauni na daban. Gaba kadan dasu 'yar madaidaiciyar AC ce ta tsaye wadda ke
amfani da hasken rana da aka yiwa kafatanin dakin wayarin dinsa. Wannan ya sanya
koda babu wuta ko ina cikin gidan,koda babu wuta ko ina a unguwar wannan dakin baya
rabo da ita. Akwai freezer madaidaiciya itama data dace da tsarin dakin,sai manyan
frames masu daukan hankali biyu masu sunayen Allah da ayoyin tsari,biyu kuma masu
dauke da zanen nature me kyau. Sassanyan qamshin turaren icce dake zama a daki ya
kama labulaye da kujeru da kyau falon yake fiddawa ya zarce kuma har uwar
dakin,wanda ya cakuda da qamshin turaren daya zamewa mazauniyar dakin lazim amfani
dasu.

Labulen bedroom din aka daga,sannan kuma a hankali ta bayyana
hannunta riqe da hijabin yarinyar dake tsaye cikin uniform.

Matashiya ce wadda duka duka a qiyasce shekarunta ba zasu haura ashirin
da biyu ke takowa a kasalance.


*_TURQASHI_*
*_BIGI SAI BIGI_*

*_BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE_*

*_TASTED AND TRUSTED_*

*_TASTED AND TRUSTED_*

*_TASTED AND TRUSTED_*

*_Kina da burin samun ingantaccen TURAREN WUTA me TSANANIN KAMA GURI?_*

*_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE
A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_*

*_TURAREN WUTAR DA KUJERUNKI ZASU KAMA QAMSHI DARAM?_*

*_KI BANKADA LABULAYENKI KIJI SASSANYAN QAMSHI?_*

*QAMSHI IYA QAMSHI 24HR*

*HUMRA ME TSAYAWA A ZUCIYAR ME GIDA*

*NASAN ZAKI TAMBAYI KANKI A INA ZAN SAMU WANNAN?*

*INCENSE BY KABO DAUGHTER*

*_tayi muku tanadin abubuwa da yawa irinsu_*

Khumra
Turaren wuta
Kulaccam
Lablab
Oil perfumes
Original musk tahara
Multipurpose spray

*karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number*

08032119803

Ko ki lalubeta ta nanπŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎ

*Instagram handle_incense by kabo daughter*

*Facebook_kabo daughter*

*Twitter_kabo daughter*
__________________________


*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA
TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*πŸ₯°πŸ₯°


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*
PAGE 13
___________________________
*_CIKIN DUBU DABAN TAKE_*

*_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_*

*_NA GWADA NA GANI_*

*_YA SUBHANALLAHI_*

*_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_*

*_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_*


*_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_*

*_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_*

*_ME KIKE JIRA?_*

*WANNAN DIN GUARANTEE NE FA*

*TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT*

*KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA*

*INCENSE BY KABO DAUGHTER*

*_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME
SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_*

*_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON
QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO
NE?_*

*MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_*

*INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803*

*_zaki dariya za kuma ki godemin_*

*_gani ya kori ji_*

*hakanan sai an gwada akan san na qwarai*
________________________


Sanye take cikin lallausar doguwar rigar bacci me kauri me gajeran
hannu off white wanda ta tsaya daidai idon sawunta.

Zaka iya kiranta doguwa saidai ba cancan ba,irin tsahon da yayi daidai da
tsahon da za'a iya kiran diya mace doguwa,wanda siririn jikinta ya sake taimakawa
wajen bayyanar tsahonta,muddin kuma ta samu damar mujewar jiki ko ta dan qara qiba
to tsaf tsahon zai shanye da ba lallai a iya ganinsa ba.

Tana da wani irin launin fata,fari me cakude da sirki sirkin
ja,fara ce tas irin hasken fatar da kana kalla zakasan ba zallar hausa fulani
bace,lallai ita din ruwa biyu ne halittarta ya hada nasaba da wani yaren(half
cast).

Ma'abociyar yalwataccen gashi me santsi da tsahon da kana iya
hangensa ta cikin hular bacci dake kanta,a cukurkude kuma a daure cikin siririn
band. Yanayin zubin idanunta shike fusgar hankalin maza da dama,bama maza kawai
ba,harda mata 'yanuwanta suke kallonta a matsayin me tsananin kyau,duk kuwa da cewa
ita din kanta ta sani,ba wata me mugun kyau bace na azo a gani,amma batasan meye
yake janye hankalin mutane haka a kanta ba?. Tun tana mitsitsiyarta wannan abun
yake tare da ita,FARINJINI
....wanda a sanda take da gatan uwa mahaifiyarta ke yawaita tofeta da addu'a ko
yaya ne idan zasu fita.

Mata ukune cikin falon,matashiya ta biyu wadda shekarunta zasu iya
kaiwa sha shida na zaune dirshan saman lallausan carfet din nasu daya wadatu da
tsafta,hannunta riqe da cup na tea,daga gefanta kuma bowl ne dake cike da chips.
Sanye take da uniform irin na sauran 'yan uwanta dake alamta maka ta kammala nata
shirin zaman tsimayinsu take bayaga breakfast data kasa kammalawa har yanzu.
Yanayin yadda take cin abincin kawai zai gaya maka bawai dadin abincin takeji
ba,idanma ba haka bane to lallai akwai abinda yake damunta.

Ta biyun na gefan kujera tana qoqarin saka fara qal din sucks
dinta. A qiyasce nata shekarun na haihuwa zai wahala ya wuce sha uku. Sannan
qaramar data isa gareta tana gyara hijabin hannunta tana qoqarin sanya mata
fuskarta shimfide da wani sassanyan murmushi nata shekarun tsakanin tara zuwa goma
suke.

Idanunta akanta da wani irin kallo na tausayi da rahama,zuciyarta
na sake narkewa cikin tausayinsu gami da jin qwarin gwiwar basu kariya da samar
musu da komai na buqatar rayuwa duk rintsi,komai wuya komai dadi. Wanzuwarsu a
yanayi na farinciki yafi komai dad'ad'a mata rai da sanyata cikin nutsuwa da
kwanciyar hankali duk kuwa da irin birkitacciyar rayuwar da take fuskanta,wadda
bata da dadi sam sam ballantana ban qaye.

"A'ah.......kaga haneefata anyi kyau" Ta fadi da sassanyan muryarta me wani irin
amo me dadi da daukan hankali idanunta saman fuskar yarinyar data kira da
haneefa......yarinyar da ake cewa duk cikin qannenta ba wanda ke kama da ita
irinta,duk da ansha cewa haneefan ta fita kyau,hasken fata kawai zata darata dashi.

Dariya haneefan ta saki ta daga hannunta zuwa ga 'yar uwartata alamun
su tafa,sai ta daga nata dogayen yatsun ta bata suka tafa din.

Batasan wanne irin son karatu Allah ya dorawa qannen nata ba,wadda
karatun bai fiya damunta ba huda ce,saidai a sannu da tayi tsaiwar daka a kanta
yanzun abun ya shiga jikinta itama. Hudan ma bawai karatun bane bataso,a'ah,kawai
hankalinta yafi karkata zuwa ga wasu bangarori. Kaman koyon abubuwa na
qirqire(creatives),irinsu zane zane,dinki,decorations da sauransu. Bata jin akwai
wanda zata matsawa kan abinda yakeso yayi muddin bai kaucewa hanya ba.....to amma
kafin sannan tana da buqatar suyi karatu.......tana da buqatar su karantu da kyau
ta yadda koda bayan ranta sun zarcewa raini da wulaqanci......tana da buqatar suyi
karatun da duniya gaba daya zata tabbatar sun gagari rainin me raini ta fannin
ilimi.....tanaso suyi irin nau'in karatun da hattana da maqiyi babu yadda zaiyi zai
sallama cewa eh lallai......jinin hindu sun zama wasu taurari na daban a cikin
familynsu gidansu dama unguwarsu gaba daya......zata nunawa wadanda suke ganin ba
zasu iya ba.....ba zasu kai ba......zasu tozarta cewa......zasu iya iya.....za kuma
sukai labarin da su basu kai ba.

A nutse ta waiwaya ta kalleta. Tadan zuba mata idanu na second tana
nazarinta. Tun tuntuni ta fahimci akwai kwantacciyar damuwa a qasan
ranta,kasancewarta mutum me wani irin kakkaifan hange da saurin gano abu. Kaifin
fikirarta ya fita daban dana dukkan wani yaro dake cikin gidan,don haka take saurin
fahimtar kowanne motsi taku da kuma sauyawar yanayin qannenta.

"Huda......wai baki duban lokaci?" Batace komai ba huda din,saita zare cup din
bakinta ta direshi tana niyyar miqewa,abinda ya sakata maida idanunta ga cup din
kenan. Ko rabin tea din bata sha ba,ta sake maida kallonta a kanta

"Kin qoshi kenan?" Kai ta jinjina mata kafin tace

"Banajin yunwa dama kwata kwata" Kyawawan idanun nata masu wani irin shape ta
lumshe,can qasan zuciyarta tana furta

"Alhamdulillah,astgafirullah" A duniya daya daga cikin sauti da take matuqar son ta
yita ji kenan daga harsunan qannenta

"BANA JIN YUNWA" Sauti mafi dadi kenan daga bakinsu zuwa kunnuwanta.

Waiwayawa tayi gefanta ta kalleta sanda ta kammala saka takalmi da
socks dinta

"Nadra......shiga daki gefan katifata ki daukomin jakata na sallameku......yau din
kamar babu me laka a jikinku"

"Tom" Ta amsa tana saukowa daga saman kujerar da saurinta ta wuce dakin. Sanda take
maido dubanta cikin falon sai suka hada idanu da hudan. Huda ta janye daga
kallonta,sai ita din taci gaba da kafeta da kallo tana dubanta

"Huda"

"Naam" Ta amsa mata ba tare da sun hada ido ba

"Wai meke damunki?" Ta jefeta da tambayar tana kebe baki......harta bude baki
zatayi magana ta dakatar da ita a tsaurare

"Karki soma cemin ba komai.......na gani a idanunki da motsinki......"

"Gida......"

"Ba damuwar mutanen gidan nan ba?" Ta jefa mata tambayar tana duban idanunta,a
yanzu akwai sirkin bacin rai kadan a maganarta da idanun nata

"Yaushe kika fara saka maganarsu cikin ranki?" Ta kuma tambayar tata tana kallonta

"Ashe har yanzu baki saba da halayyarsu ba?,bakisan yadda zaki zauna dasu ba?,huda
ina duk qoqarin da nake a kanki ke da kike babba ki fahimci yadda zaki zauna da
kowa a cikinsu?"

"Anty bakisan me suka ce ba a kanki.....bakisan me suke fada ba kullum" Ta qarashe
maganar muryarta tana raurawa sosai da alamun zuciya da ruhinta gaba daya sun sare.

"Kome zasu fada huda su fadi,indai a kaina ne karki azawa kanki damuwa.......kome
ma zakiji sun fada,ba wani baquwar kalma da zakiji daga bakinsu ko sabon abu.....me
yasa sai yanzu zaki fara sawa kanki kina damuwa?" Ta qarashe da sigar tambaya. Qasa
tayi da kanta ba tare data amsa mata ba,ita kanta batasan me yasa sai yanzun abun
ke damunta ba duk da sun share shekaru dasu a haka.

Daidai sanda nadra ta qaraso ta miqa mata kyakkyawar hand bag din
nata fara tas me adon brown duka jikinta dake dauke da tambarin kamfanin Gucci.
Idanunta masu sheqi ta juya zuwa ga nadra,ta saka hannu ta karbi jakar
tana qoqarin zugeta.

"Anata kiran wayarki tunda na shiga" Nadra dake goya jakarta ta fada.

"Okay,barta" Ta amsa mata a taqaice,don ta tabbatar a cikin mutum biyu daya ne yake
kiranta,tafi kuma gasgata zatonta akan dayan.

Zip din da take ajiye canji ta zuge,ta fidda kudin ta lissafa daidai
yadda tasan zai ishesu break da kudin mota,saboda yau din basuyi abinci yadda suka
saba ba kasancewar kayan abincinsu ya qare.

Daga bakin qofar falon nasu tayi tsaye hannayenta goye a qrijinta
tana dubansu har suka kammala ficewa daga gidannasu,sai taja Qaqqarfar ajiyar
zuciya tana sauke hannayen nata ta juya a hankali don komawa falon don kwata kwata
bata samu isashen bacci ba a jiya,tanaso ta runtsa sosai sannan ta shiga kasuwa
tayi musu saye saye



*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA
TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*
_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*πŸ₯°πŸ₯°

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 14
________________________
*_CIKIN DUBU DABAN TAKE_*

*_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_*

*_NA GWADA NA GANI_*

*_YA SUBHANALLAHI_*

*_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_*

*_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_*


*_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_*

*_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_*

*_ME KIKE JIRA?_*

*WANNAN DIN GUARANTEE NE FA*

*TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT*

*KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA*

*INCENSE BY KABO DAUGHTER*

*_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME
SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_*
*_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON
QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO
NE?_*

*MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_*

*INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803*

*_zaki dariya za kuma ki godemin_*

*_gani

Please Login or Register in order to submit comment