You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fitattun idanun nata masu zafi
da basu da sauqi ko kadan.

Kallo kallo akayi tsakaninsu na wani mintuna,cikin jinin jikinta
maamahn ke jin bata aminta da wannan kallon ba. Wani kallo ne da tafi kowa
saninsa......tafi kowa kuma sanin ma'anarsa......tafi kowa kuma fahimtar yaren dake
cikinsa.

"Akwai wani yare da ba kowa yake fahimtar sa ba sai me matsanancin
hankali......akwai wani juyi da idan ya tashi juyawa yake watsi da dukka wani abu
dake kusa dashi ko nesa dashi ma......." Ta fada tana juya idanunta sannan ta sake
maidasu ga maamah

"Na jima ina gurnani......na dade ina gargadi.....na dauki lokaci inata jirwaye me
kama da wanka......amma inajin cewa lokacin yin wankan gaba daya yazo don a batad
da sahun wannan jirwayen.....jirwayen dake cutar da farar tufa yake nakasa kuma
lafiyar jiki......gargadi na qarshe da bazan sake irinsa ba.....saidai fallasa ya
biyo baya.....ruwan kura ne ta fiddo ajiyayyen naman data aje....don kuwa yafi
qarfin bakinta,kalar nama ne da bai ciyuwa a gareta kasancewarsa me dauke da wata
babbar guba.....a wannan karon lokutan bada damar gaba daya awa biyu ne kacal....do
or die" Tsam ta miqe daga kujerar da take kai still idanunta akan maamah da wani
zazzafan kallo tana wucewa ciki itama.

Haka kawai kowacce gaba ta jikinta tayi wani irin sanyi,bugun
zuciyarta ya dinga qaruwa da wani tsoro da batasan daga inda yake ba.

"Kada fa maganganunsa su tabbata.....kada fa lokacin da yake maimaitamin ne yazo"
Take fadi a Karan kanta tana jin wani irin razanannen yanayi yana ratsata.

Fes maganganunsa suke ratsata kaman a sannan yake furta mata su,tsoro ta
sakejin ya saukar mata,ta miqe da zummar barin falon sai taji jikinta ko ina ya
dauki rawa. Qoqarin daidaita kanta takeyi,batasan wacce irin matsoraciya ta koma
har haka ba,batasan dalilin da ya sanya take yawan samun rawar jiki ba idan tashin
hankali ya durfafeta(badai.baki yarda baki da hawan jini ba?).

"Ita din ba komai bace.....ba zata iya aikata komai ba don bata da hujja" Abinda
zuciyarta ta shiga maimaita mata kenan,abinda kuma yadan bata nutsuwa 'yar
kadan,saidai ta gaza samun irin nutsuwar da take da buqatar samu.

K'arfe goma na dare daidai take takawa a harabar gidan tana nufar motar
da fu'ad ke zaune a ciki yana jiran ta qarasl su wuce gida.

Ta madubi ya hangeta,sai ya ajiye wayarsa da system din daya wuni dasu
yana aiki ya bude motara a nutse ya fito ya bude mata qofar yana jiran ta qaraso.

Tun bata qaraso din ba ya karanci baqon yanayi a tare da ita,yadda yasan
sabreen dinsa ba haka take ba,duk da yasan dole akwai damuwa da dukkaninsu suke a
cikinta,

Baice komai da ita ba har ta qaraso,ta shiga ta zauna ba tare da tace
masa komai ba,wannan ma ya bashi mamaki,don komai runtsi.ba haka ta saba yi masa
ba,sai ya rufe ya zagaya ya shiga yana bada umarnin tashin motar.

Hannunsa ya miqa mata,ta dubeshi sau daya ta miqa masa nata,sai ya
jawota jikinsa ya rungumeta sosai yana sauke ajiyar zuciya.
"Ina cikin matsi da tsanani sabrrrr,bana cikin nutsuwata da walwalata.....please
karki bari ki wanzu cikin damuwar nan kema,domin ke kadai ce kika ragemin da zan
samu sassauci da ita". Tausayinsa yayi tsananin tsarga mata,yana tare da abu mafi
hadari da muni ba tare da ya sani ba.....yana tare da halitta mafi zamewa rayuwarsa
barazana ba tare da yasan da hakan ba.

"Zamu kasance tare cikin tsanani da sauqi......zan zame maka garkuwa alqawari ne
wannan,your battle is my battle.....we fight together".ta qarasa fada tana matse
hannunsa da kyau cikin nata. Sosai maganarta ta sake bashi nutsuwa,yadda ta sakashi
a jikinta tana qoqarin bashi dumi daga dumin jikinta ya tattaro hankalinsa dake son
kaduwa waje daya.

"Thank you duniyata" Maganarsa ta qarshe kenan shuru ya biyo baya.

Samansa kawai suka haura shi da ita,don gaba dayansu ba wani me cikakken
kuzari. Yana ajiye wayoyin da yaketa dakonsu tun kiran jiya wayar farouq ta sake
kadawa. Da wani hanzari yakai dubansa ga wayar. Number jiya ce,don already ya riga
yayi marking nata,da wani irin zafin nama ya jona komai yana qoqarin turawa team
dinsa saqon kartakwana don buqatar kasancewarsu dashi koma saman minotti sofa dinsa
ya zauna yana aza kafatanin hankalinsa akan komai. A hankali ta samu kanta da
dawowa da baya,ta samu hannun sofa din da yake kai ta zauna tana jin 'ya'yan
cikinta suna curewa waje daya.

"Mun sake kiranka a karo na biyu,kiran kuma da ba lallai muyi na uku ba,zamu gaya
maka inda zaka ajiye mana wannan kudin....."

"Ni kuma a ina zan karbi qanwata?" Ya tambayesu muryarsa a tsaye. Ya gama shirya
komai,a yanzun bawai lallabawa yake buqatar yayi musu ba,ko na bayan dama akwai
gacin da yaso ya cimma shi yasa ya biyo ta sigar lallami,a yanzun kuwa dole ya
canza hannu ya gani ko zai samu kaiwa ga wannan matakin.

"Au maganar karbar qanwarka ma kakeyi?.....muna maka maganar kudin aikinmu?".

"Wanne aiki kenan kukayi?" Ya tambayesu cikin salon rainin hankalin da yana sane ya
tsiro dashi.

"Lallai kana buqatar mutuwar qanwarka a wulaqance kenan a hannunmu".

"Da na sanya kunyi nadamar haihuwarku da iyayenku sukayi,dana sanya kun gane duniya
sashe biyu gareta". Shuru ya ratsa tsakani kafin yaji an danqaro ashar

"Kuna tunani kuna da qarfin kudin da zaku iya kamamu ko?,to zamu nuna muku kudinku
bai isa ya saka muzo hannu ba.....don ita kanta wadda ta bamu aikin me kudin kanta
ce....kuma tana da nata ikon da ko kamamu kukayi din a dole zaku sakemu".

"Au Allah?,amma ta kasa baku kudi wadatattun da zaku rayu?,saita hadaku da aikin
wahala aikin kidnapping?".

"Bayau muka fara mata aiki ba.....kuma wannan bazai zama na qarshe ba,ko ta bamu ko
bata bamu ba sana'a mukeyi,kuma ba zamu fasa ba...koda ita ko babu".

"Koda ita ko babu din kuwa daga wannan karon ba zaku sake zaluntar kowa ba.....daga
wannan lokacin kun daina aikin ashshsha"

"Kaga dakata malam!" Ya daka tsawa daga daya bangaren,tsawar da har sai data sanya
fuad lumshe idonsa sannan ya budeshi,yana ji a ransa inama ce gaba da gaba suke da
wadannan qananun 'yan iskan.

"Bama doguwar hira da kowa faruqu kake ko wa?,kuma ba zamu fara a kanka ba.......ka
kawo kudi ko qarawa qanwarka tsahon kwana....ko kaqi muyi kaca kaca da namanta
kaman yadda hajiyarmu ta buqata daga nan zuwa wayewar gari"

"Kuyi duk yadda kukeso" Ya fadi yana tsinke kiran don ya kwashi mintunan da yakeso.




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 147


*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA
KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA
IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE
SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA
A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190
*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*



147


"Ya zakace musu haka?,ya zakayi haka hamma?" Sabreen data barke da kuka
cikin rawar jiki ta furta,sabreen din da baisan da zamanta a wajen ba sai a sannan.

"Ba zasu aikata ba.....kudi sukeso,sunsan kuma kudi ba zasu karbu ba muddin suka
tabata......sai hajiyar da....." Cak ya dakata da maganar yana nanata sunan
hajiyarsu da suke fadi.

"Hajiyarsu.....kasan wacece hajiyarsu?" Sabreen ta fada tana miqewa tsaye cikin
wani birkitaccen yanayi. Gaba daya ji takeyi tayi loosing duk wani control nata da
tunaninta......tana jin komai yazo qarshe,komai yazo gaba.....tana jin ko na minti
daya ba zata sake iya ci gaba da rufe sirrin matar nan ba,duk wani signal ya kama
ya kuma nuna kanshi......sannan ya bayyanar da komai da komai.

"Nace kasan wace hajiya suke magana akai?" Ta maimaita tana ware hannayenta gami da
fiddo idanunta waje kaman wadda ta zare. Bata jira amsarsa ba ta dora.

"Ba kowa bace sai MAAMAH!" ta fada da wata irin tsawa da bata tashi tarwatsewa ba
sai a tsakiyar kunnen fuad da wani irin nau'in mafi munin sauti.

Idanunsa da yakejin sun masa nauyi ya aza akan fuskar sabreen da wasu
manya manyan alamun tambaya a kansu.

"Maamah?" Ya maimaita sunan da salon tambaya.

"Eh maamah.......maamah itce ya dauke amna.....maamah ita ta saka a dauke amnah!"
Ta sake fada kuka me qarfi yana kubuce mata.

Daga zaune da yake amma sai yaji kaman duniya tana zpagayawa ba daidai
ba......kaman akwai wasu sautuka da abubuwa da suke tafiya ba daidai ba.

"Kinsan me kike fada sabreen?....maamah fa?.....rashin imani da qeqashewar
zuciyarta har......" Bata jirashi ya qarasa ba wani sashe na zuciyarta ya soma gaya
mata cewa,kariya yakeson bata,qaryatata ita kuma yakeso yayi.

"Abun nata baikai haka ba ko?,haka kake zato?.....kana ina sanda ta tursasamin
aurenka don kawai ta mallakeka......ta tsundumani a rayuwarku don kawai na zama
silar mallakarka gareta ta hanyar yin garkuwa da 'yan uwana......ta sanyani a
kwanaki mafiya tsaho da tashin hankali a rayuwata?......kana ina a sanda ta sake
diban qannena ta riqesu don ta samu damar cimma burinta a kanka da kaina......ta
tirsasamin lallai saina shayar da kai na kuma ciyar dakai da asiri?.....na tufatar
da jikina da rigar da zata zama silar soyayyarka a gareni?.mashkur......dama sauran
wadanda suka kawowa rayuwarmu farmaki kina tunanin yin kansu ne?.....fareeda data
samu nasara a kanka kana tunanin haka siddan ta sameta?......." Dora hannunta tayi
saman matashin cikinta.

"Hatta da wadannan yaran da basuzo duniya ba kana tunanin sun tsira a
hannunta?,banda kiyayewar Allah zuwa yanzu lissafin watana nawa da barinsu
akeyi.........ka duba wannan" Sai ta ciro wayarta daga handbag dinta tana bude masa
inda ta adana videos dinnan da sauri sauri ta dangwarar masa ta juya da sassarfa
tana fita a parlor din tana sauka qasa.

Wayar yabi da kallo yana jin yadda jijiyar kansa ke wani irin harbawa.
Yanajin kira na shigowa ta wayarsa dama system din gabansa,wanda ya tabbatar team
dinsa da suke bincike tare ne suke kiran nasa,saidai baida wani kuzari ko kadan.

Hannu ya sanya ya dauki wayartata,ya kuma bude video din da ta ajiye
masa. Murya da komai ya fita tassss.....baya buqatar neman qarin bayani,sai kawai
yayi connecting wayar da system dinsa,ya shiga aikin duba ingancinsa.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Yaji yana maimaitawa bakinsa yana rawa. Duk da
ya jima yana hasashe.....ya jima yana kwana yana kuma tashi da tarin tulin lissafin
meye da meye maamah zata iya aikatawa dama wanda ba zata iya ba?,amma sai ya samu
kansa da jin komai sabo a tattare dashi.....sai ya samu kansa da jin komai ya zame
masa baqo.

Kaman wanda aka yiwa allurar qaimi,sai ya zabura,ya hada connection da
kowa dake cikin team dinsa suka fara aiki akan kiran mutanen. Koda kowa ya
gaji....koda kowa yana ganin dare yayi a barwa safiya,shi bayajin zai iya
hakan......baya jin akwai abinda zai dakatar dashi daga lalubo maboyarsu daga daren
nan zuwa asubahi......baya buqatar a wuce haka.

Sanda ake qwala kiran assalatu na farko signal ya harba sosai,kai
tsaye kuma ya basu daidai direction na inda network da layin yake motsawa.

"Alhamdulillah" Ya furta yana zarar wayarsa da sauri. Jordan ya soma kira yace ya
yiwa su abdulgafar magana......su hadu yanzun a masallaci zasu fita ana idar da
sallar asubahin.

Sai daya tabbatar ya gama hada komai sannna ya miqe yana nufar toilet.
Yadda yakejin jikinsa kaman yana dab da kasa responding komai......amma ya gayawa
kansa sai ya qarasa aikin daya fara,don haka ya hada ruwa me zafi yayi wanka. Cikin
baqin shirt da wando ya shirya,ya jawo wani boots dinsa ya saka yana dora baseball
cap a kansa. Duk wani abu da zai buqata ya hada a back pack ya rataye,ya maida
baqin eyeglasses a idanunsa sannan ya fara saukowa a gurguje.

Har yakai parlor din farko wani abu ya fusgi zuciyarsa,sai ya koma da
hanzari yana dosar dakunanta. Bai sameta asalin dakinta ba,sai a daki na biyu ya
sameta.

Qudundune ya sameta cikin duvet,da alama baccin me jima da saceta
ba,don ga cups nan da plate da tayi amfani dashi da sauran ruwa. Har ya qarasa
gabanta bata motsa ba,alamu sun nuna baccin daya dauketan me nauyi ne. Saman kanta
ya tsaya yana duban kyakkywar Fuskarta,wani matsanancin tausayinta ya saukar
masa,ya tsugunna a tausashe ya sauke mata kiss a goshinta don baiso ya tasheta,ya
miqe a hankali ya maida hankalinsa ga dakin.

Plates din ya soma tattarewa da cups din,murmushi ya kubce masa. Da
gaske ciki yana canza hali da dabi'a,matar da daqyar sai yayi fama da ita take cin
abinci,yau itace anywhere anyhow kama abinci take bada wasa ba.

"Allah ya qara lafiya" Ya fada yana ficewa dasu ya kaisu kitchen sannna ya fice
daga gidan.

Cikin dukkanin shirin daya kamata suka gewaye area din kafin su sanya
kai zuwa ainihin inda na'ura ke basu direction a kai.
Cikin qasa da minti biyar suka nannade qofar gidan suka nadeta tsaf da
wani irin qarfe.

Sake kutsawa sukayi da wata irin sassarfa suna bada sanarwar suna
qarqashin kamen hukuma,kada kuma wanda ya motsa a cikin su.

Tun kafin sukai ga qarasowa ciki sukayi surrender,ba yau suka fara irin
wannan aikin ba,saboda haka sun tabbatar da cewa sun riga sun kamu,tunda kuma suka
kai ga cimmasu har inda suke lallai ba makawa basu da sauran wani qofa na fita.

Qoqarin dakatar da fu'ad sukeyi wanda shine na gaba sanda yake qoqarin
doke qofar dakin.

"Sir......it may b......." Bai iya bari sun qarasa ba ya yiwa qofar wata Kyakkyawar
duka data sanyata bude kanta da kanta. Bindigarsa ya saita akan mutum na farko dake
tsaye kafin sauran suma su saita ragowan na dakin. Ya jima da koyar harbi da
bindiga,ya kuma mallaketa da license dinta da komai saboda dalilai na tsaro,amma ba
kowa bane yasan da hakan.

"Kowa ya cire abinda yake jikinsa,bindiga ko wani qarfe ku zube a nan" Shugaban
tawagar ya fada yana daka musu tsawa. Jordan ne ya soke tashi bindigar sannan ya
fara zagayasu daya bayan daya cikin qaqqarfan takun nan nasa don tabbatar da kowa
ya cire komai dake a jikinsa.

"Hamma....." Muryar amna ta daki kunnensa da wani irin sauti galabaitacce.

Idanunsa ya daga da zafin nama yana maidashi inda sautin yake. Amna
ce ke takowa a hankali jiri yana kwasarta daga wani daki dake cikin babban dakin.
Maida bindigarsa yayi da wani mugun zafin nama yana dosarta,wanda baikai ga isa ba
qarar sautin bindiga ya tashi a dakin.

Cikin tsarewar ubangiji ya bashi ikon kaucewa ya kuma ture amna ya wuce
ya bula bango ya nutse a ciki. Cikin qasa da second biyu Jordan ya masa wani irin
duka,ya kama hannuwansa ya murdesu ya maidasu baya ya karbi bindigar,sannan ya daki
gwiwarsa ya zube a qasa.

"Zakasan kayi mistake........idiot!" Jordan ya fada cikin tsananin fushi yana masa
wani mummunan dauri.

Amna ya daga da hannu bibbiyu,ya cire rigar daya dora daga saman rigarsa
yana yafa mata saboda yadda take gayarta haka,ba dankwali bare mayafi. Wani irin
zafi zuciyarsa takeyi,ya riqe amna da kyau suna takawa kafin ya kalli jordan

"A yau nakeso su fadamin waye ya sanyasu wannan aikin,a yau basai gobe ba!" Ya fada
da tsananin zafin zuciya.

Yau din ta koma masa lovey dovey dinsa,ta koma masa amnansa sak ta
shekarun baya,ta mance da wani surukuta a tsakaninsu,ta lafe kanta saman kafadarsa
tana rera kuka.

Ita kadai tasan ya takeji a zuciyarta da qirjinta,nata duka me sauqi
ne,tana tausayin fu'ad ne a sanda sakamakon binciken ya fito sunan MAAMAH ya zama
suna na farko cikin wadanda suka assasa dauketa. A baya wani tsoron matar
takeji......a yanzun kuwa sai zuciyarta gaba daya ta qeqashe a kanta. Tayita
kwanciya ne bayan ta farfado saboda tsoro,saboda tanason ta tsira da mutuncinta.
Tana tsoron ta nuna musu ta warke batasan meye next step nasu ba.

Maamah tayi waya dasu har sau ba adadi......taji kuma muryarta ta sake
tabbatarwa da cewa tabbas din itace. Abun ya matuqar bata mamaki ita kanta,ya kuma
girgizata.

"Wacce irin zuciya ce a qirjinta?" Ta tambayi kanta da kanta a mamakance.

Wani abu me zafi da tauri ya dinga hadiyewa,kai tsaye ya bada umarnin
wucewa da amna asibiti don a duba lafiyarta.

Kasa zama yayi ko tsaiwa waje daya,yana jin kaman ya sanya kai dakin da
likitoci suka rufu a kanta suna checking dinta. Bashi da wani qwarin gwiwar sanarwa
kowa an samu amna din har sai ya tabbatar da cikakken lafiyar amnan,har sai ya
tabbatar da cewa ta kubuta da mutuncinta da lafiya da kuma cikakken hankalinta.

A qalla sai da suka kwashe awa guda kafin su fito,cikin lallashi Dr
aswad yace mishi.

"Karka damu sir.....komai nata lafiya yake,ba wani abu daya sameta,saidai jikinta
da yayi weakening saboda hodar cocaine da suka shaqa mata me yawa.......but shima
idan tasha ruwa sosai jikinta zai koma normal in sha Allah".

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ya maimaita yana jin zuciyarsa tana quntata.
Cocaine kuma?,abar da yayi imani ko a ido aka ajiyewa amna ita ba zatace gata ba.

Dakin ya koma,tana kwance tana bacci,ruwan da suka saka mata saboda
samun qarin kuzari yana shiga jikinta. Wayarsa ya laluba ya fara kiran number abba.

Daidai lokacin yake rufe shafin alqur'anisa,inda yakai qarshen suratu
yaseen daya dauki gabarar karantata tunda abun ya faru sau wani adadi. Ya samu
wannan sirrin daga bakin malam,wanda fu'ad ya raba kudi sosai aketa addu'a da kuma
roqon Allah akai.

Bismillah yayi sanda yaga kiran daga fu'ad ne.

"Abba......an karbo amna,lafiyarta qalau alhamdulillah,amma muna asibitinmu tana
dan shan drip saboda jikinta ba qwari"

"Allahu akhbar......alhamdulillah.....tabbas ubangiji yayi gaskiya da yace ku
roqeni zan amsa muku,Allah kaine abun godiya,sannu sa qoqari muhammadu.......inajin
bazan shaida musu ba sai wannan drip din ya qare tukunna ta farka,ni zan taho,kafin
sannan ina sanya ran qila ta farka".

"Hakanma yayi abba" Ya furta yana katse kiran. Farouq ya kira da temporary line din
da yake using nashi a kwana biyun. Kalamansa dukka irin na abban ne......saidai ya
cika da mamakin abinda ya sanya fu'ad ya tunkari gagarumin aiki irin wannan bai
gaya masa ba.

"Ba lokaci dude.....na matsu na dawowa da anni autarta....besides ma waye zaiyi
gangancin dauko ango ya sanyashi a hadari irin wannan bayan bai gama tantance ma
zaqin duniyar daya shiga ba?" Murmushi ya sanya dole farouq din ya saki,sai ya
yanke kiran shima murmushi yana subuce masa.

Saidai kuma cikin qanqanin lokaci murmushin ya tsaya masa cak,yaji
gabansa yana faduwa,sai ya sake lalubar number wayar CP.

Dab da zata tsinke ya daga,yayi apologizing na fu'ad.

"Ba komai.....nace zaiyuwu zuwa nan da azahar na zauna da dukka mutanen nan?".

"Yes sir......zai yiwu,a gida ko a nan?".
"If possible akaiminsu gida,zanwa abdulfattah waya ya bude musu masauki.....waccan
dayar matar dake wancan gidan....me take da suna ma?"

"Bibo ko.....habiba mu'azu"

"Yes......itama a daukota,a hadamin ita a cikin su".

"Okay in sha Allah" Ya fada suna yanke wayar.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 148


*_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽

*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*

*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*

*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_*

*_Da yardar Allah saikin godemin_*

*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*πŸ˜‚πŸ˜‚

Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray

*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*

*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*

*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI*

*SUNA NAN A*

*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_*
*BA'A KANO KIKE BA?*

*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin
aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*

*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*πŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎ
wa.me/+2348103155915

KO KI KIRATA TA NAN

08103155915



148


Ba jimawa sai ga abba,shigowarsa kenan farouq shima ya shigo,abinda
ya sake zaunar dashi suna tattauna yadda abun ya kasance.

"Amma don Allah me babban suna......zuwa yanzu ya kamata ka daina tunkarar abubuwa
haka kai tsaye,bakai kadai bane yanzun kaman baya daka saba abunka gaba gadi,yanzun
akwai nauyi akwai iyali da suka dogara dakai".

"In sha Allah abba" Ya fada ne kawai,amma bayajin akwai wani abu da zai hanashi
sadaukarwa da iyalinsa ranshi da lafiyarsa muddin yana raye din.

Lokaci ya duba,bayason ya saba magana idan ya yita,don haka ya miqe
yana duban abban.

"Abba zanje gida....don sanda na fita tana bacci ne,yanzun haka nasan tana can da
tunanin inda naje da kuma inda amna take"

"Maza ka koma kayi mata albishir,ubangiji yayi muku albarka,ya kareku daga dukkan
sharrin zamani.....ya tsare gaba"

"Ameen abba" Sai ya juya ga farouq yana bashi hannu,shima bashi yayi sukayi
musabaha suna duban juna,a tare a kuma lokaci daya murmushi ya subucewa kowannensu.
Farouq ya gode Allah da abba yake a wajen,ya tabbatar da sai fu'ad ya taba masa iya
shege komai qanqantarsa.

"Ka gayawa su musaddiq saisu dauko anni tazo ta ganta itama hankalinta ya kwanta"

"In sha Allah oga" Harara yadan balla masa,yasan da biyu ya fadi kalman oga din,sai
ya juya yana fita a dakin.

Tunda ta farka daga baccin takejin ta samu sassaucin qunci da bacin
ran da takeji. Kai tsaye daga gadon kitchen ta wuce saboda yadda yunwar data
tasheta a baccin ke neman sabautata. Koda ta duba agogo sai taga ashe ta zarta
lokacinta ne. Tana cin abincin tana sake sallamawa lamarin ciki,tayi imanin banda
cikin a yanayin da take ciki a yanzun ba abinda zai sanya ta iya sakawa cikinta
abinci.

Tsaf ta cinye ma'u na satar kallonta.

"Ko a qara miki?" Kai ta girgiza.

"Doughnuts dina kawai nakeso......ya qare ragowan na cinye yanzu da tea,don Allah
ma'u ki sakamin order,kwali sha biyu nakeso" Ta fada tana goge hannunta da towel
jikinta sam ba wani kuzari sannan ta juya tana fita a kitchen din ma'u ta bita da
kallon mamaki.

Eh dole ace ciki yana saka wasu hauka,batasan ya zatayi da doughnuts
kwali goma sha biyu ba,doughnuts din matar da madarar ciki kawai ta isheka ta sanya
kaji ka qoshi koda kuwa rabin guda daya kaci,ba qaramin jarumi bane wanda zai iya
cinye guda uku ba,komai cinka kuwa idan har kaci ukun nan ba sauran space nacin
wani abincin saboda ka gama qoshi.

"Allah ya raba lafiya" Ma'u ta fada tana jawo waya ta soma lalubar number wayar
maman ummee kada a samu akasi.

Wata lafiyayyar kasala ta saukar mata,sai kawai ta yada zango saman
sofa din falon. Zuciyarta na cike da mamakin yadda bataji motsinsa ba ko
kadan......hakanan kuma bataga alamun ma ya nemeta ba.

"Kodai da gaske yana shirin rejecting maganata da

Please Login or Register in order to submit comment