You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baya bai sauyani ba bare yanzu dana 'YANTU.....karki bari
zargi shakka ko kokwanto a kaina ya ratsa zuciyarki har ya samu gurbi......bazan
iya zama ba huda......bazan kuma iya daina fita ba,don haka ki cire damuwar wannan
daga ranki" Ta amsa mata tana miqewa a nutse daga saman kujerar,saidai dukka
gabbanta sun saki da gajiya da kuma damuwar data saukarwa ruhinta.
Ta qasan idanu take bin sabreen din da kallo har ta shige dakinsu.
Ta janye idanunta tana sanya hannunta gami da dauke qwallar dake tsiyaya daga
idanunta. Anya ta kyauta idan har ta sanya zuciyar data sadaukar da komai nata
saboda farincikinsu da ingantuwar rayuwarsu.....ta kyauta idan tayi silar sanyata a
damuwa?.

Babu kyautawa ko kadan,idan har ta aikata hakan kenan bata da maraba
da sauran gama garin jama'ar gari?. Bata da banbanci dasu?,tafi aminta dasu kenan
akanta?. Nadama taji tana saukar mata a hankali. Bawai tayi komai bane da
gangan,kawai ta kasa controlling din kanta ne akan batun,ta kasa jure abubuwan da
takeji take kuma gani kulliyaumin,ita daya kuma tasan yadda takeji a duk sanda
akayi magana akan yayartata halitta mafi soyuwa a gareta.

Tana zaune a wajen tana feeling guilty akan maganar,har sabreen ta
sauya kaya zuwa wasu riga da wando silk me dogon hannu,rigar tadan sauko mata har
saman cinyoyinta,yayin da wandon ya sauka har saman qafafunta. Tayi alwala ta dawo
ita da haneefa,nadra na daga waje bakin fanfo tana dora nata ta kalleta

"Ki tashi kiyi alwala,ko kina fashin sallah ne?" Tayi mata tambayar cikin basarwa
tana qoqarin zura jilbab dinta. Kai ta girgiza,ta miqe tana takawa a sanyaye tana
ficewa. Sanda nadra ta shigo sai tace ta sanya hijab su jira huda din ta shigo sai
suyi jam'i kamar yadda sukeyi lokaci lokaci. Zama tayi gefan kujerar falon kafin
shigowar hudan tana duba saqonnin cikin wayarta. Tana jimawa bata duba saqon sms ba
don bata fiya bashi muhimmanci ba.

Sama sama ta fara jiyo hayaniya daga tsakiyar gidan nasu,saidai bata
wani bada hankali ba,don ba baqon abu bane cikin gidan nasu musamman lokaci irin
wannan. A hankali hayaniyar ta fara yin yawa,sai kuma ta fara jin kamar muryar huda
cikin hayaniyar. Abinda yaja hankalinta kenan,ta daga kanta daga wayar tana duban
nadra da itama tayi kasaqe tana sauraro,saidai batace komai ba,ko wala'alla itama
tanason gane cewa muryar hudanne ko ba ita bace. Baqon abune ga dan dakinsu wato
yin hayaniya ko daga murya kaman haka. Basu da abokin fada ko adawa,kamar yadda har
mahaifiyarsu tabar duniya bata da abokin fadan,saidai kai kayi dasu idan kaso
hakan. Hudan ce ma mai dan zafin rai wani lokaci da kuma rashin dagawa duk wanda ya
shiga gonarta. Sabreen ta shafeta sosai......amma yana da wahala ka gano haka
saboda miskilanci da rashin son shiga shirgin mutane.

A sannu ta tanqwarata ta koya mata hadiye fushi,a dole kuma sukaci
gaba da tafiya kan wannan bigiren har kawo inda yanzu rayuwa ta ajiyesu.

"Dubamin.....kamar muryar huda nakeji" Sabreen ta fadi tana duban nadra. Da
hanzarinta nadra din ta miqe,don dama abinda take jiran ji kenan daga sabreen. Bin
nadra tayi da kallo har ta fice,saidai kafin dawowar nadra dakin kunnuwanta sun
bata tabbacin huda ce,saita ajiye wayarta gefe tana duban haneefa

"Auta qarasa karatunki.....kada ki fito ina zuwa" Kai haneefa ta daga idanunta a
raunane tana bin sabreen da kallo har ta fice.

Kusan duk wani ahali na gidan dake cikin gidan yana tsaye a tsakar
gidan banda mace qwaya daya.....mace guda daya tak da koda mutum zaa dafa a gidan
sai tayi niyya ko ra'ayi zaka ga gilmawarta a shiyyar tsakar gidan ma bare akai ga
farfajiyar gidan.

Tun kafin ta qarasa idanuwanta suka gane mata da wadda akeyi. Huda da
hadiyya......suna tsaye tsakiyar mutane kowaccensu tsamo tsamo a jiqe da ruwa,ruwan
da bata raba dayan biyu ruwan wankin da hadiyyan takeyi ne da kuma wanda ke zuba
yanzu haka daga famfo.
Kwalar huda na hannun hadiyyan cikin zafi da zafafa

"Zanga uban daya tsaya miki cikin gidan nan.....kibar ganin kamar kun isa kun
bunqasa......kun riqar da ba'a saku ba'a kuma hanaku......ni bariki da duk wanda ke
cikinta baya bani tsoro wallahi" Ta fada tana waro idanunta waje.

Idanu sabreen tadan runtse kadan tana jin wani abu me zafi yana
saukar mata. Ta sani yau Allah kadai yasan adadin tarin maganganun da kunnuwansu
zasu amsa cikin gidan. Maganganu ne da aka tarasu cikin qiraje ana neman ranar
zubda su,amma ba'a samu ba saboda kiyayewarsu da shiga hurumin kowa sai
nasu......yau kam da dama ta samu ba shakka sai iya abinda sukaji.

Bata cewa kowa komai ba sai kutsa kai cikin mutanen data dinga yi a
nutsenta sanye da hijabin sallarta,abinda ya dinga jan hankalin kowa da fitowarta
kenan.

Bata tsaya ba har sai data isa tsakiyar inda suke abun,a sannan ran
huda yayi bacin da itama ta cakume hadiyya. Abinda ya tunzura hadiyya kenan ta daga
hannunta a zafafe ta saukewa huda lafiyayyen marin daya sanya huda din sakinta ba
shiri.

Cikin tsananin fushi hudan ta zabura don maida martani sabreen ta iso
tsakaninsu

"Karki soma" Sabreen din ta fadi duk da ita kanta tasan marin da hadiyyan tayi
shiryayye ne da ko waye aka yiwa shi sai yaji matuqa a jikinsa.

"Barta.....barta.....ta tsammaci ni din sa'arta ce,batasan ko yayartata da take
kallon kanta jan wuya ba ni nasha gabanta wallahi faufau"

".....yaaya.....kina jin abinda take fadi?,kina ganin abinda tayimin?" Huda ta fadi
muryarta na rawa,kuka yana shirin qwace mata amma bataso tayi kukan don bata shirya
yinsa a gaban wadannan azzaluman ba. Mutanen da babu rahama tausayi jin qai ko
imani a zukatansu a tattare dasu. Mutanen da d'ai basa kallon maraicinsu basa kuma
kallon komai a tattare dasu face zallar sharri da mugun fata tare da mummunar
makoma.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 40


Idanunta ta lumshe tana gyada kai

"Ya isa huda.....ki wuce daki.....karki sake tsaiwa a nan" Ta fadi tana duban
idanun huda. Kai hudan ta jinjina,da alamu umarnin sabreen din ya mata nauyi da
yawa,da alama a yau ta bata umarnin da takejin matuqar nauyin bi da
dauka.....umarnin da zuciya ke raya mata kamar ta takeshi

"Aikin banza aikin wofi.....ni wallahi na riga na tserewa mutum.....duk iya
barikinsa saidai ya ganni ya qyale,ba wanda nake tsoro ko shakka,hakanan babu wanda
zan dagawa qafa" Hadiyyan ta fadi tana jujjuya jiki cike da jin taqamar ta daki
hudan a bulus.

"Ke meya kaiki ma kulasu?,mutumin da yake kan hanyar samun kwalin degree a fannin
likitanci?" Cewar bibo tana bin bayan sabreen da harara wadda tuni ta fara takawa
tana barin wajen

"Qyaleno bibo....wani lokaci ajjiye karatun akeyi ai ka nunawa mutum kaima fa ka
iya barikin nan ehe...tarbiyya ke sawa kake dage qafa"

"A'ahhh.....akul,zuba ruwa ki kurkure bakinki,'yar nan meye hadinki da
bariki?,bariki fa?,suma jaza musu akayi.....don ko yaya ka taba bariki dai dole a
samu me gado kota nono sa zuqa" Cak ta tsaya daga tafiyar data fara yi zuwa
daki,bugun zuciyarta nason qara yawa dajin lafazin bibo

"Aikuwa dai an tafi lahira an bar musu gado mara amfani wallahi" Hadiyyan ta fadi
tana gyara daurin zaninta tana gatsina fuska.

Lafazin hadiyyan ya sanyata waiwayowa,wani irin zafi takeji yana sauka
mata a qirji,ranta yana wani irin mummunan baci

"Akul hadiyya.....kul dinki......hawainiyarki ta kiyayi ramar iyaye na...." Kammala
daura zanin tayi da gaggawa ta maida hannunta ga qugunta duka tana riqe dasu,fuska
da bakinta cike fal da isgili rashin mutunci da wulaqanci,idanunta tsakiyar na
sabreen

"Idan naqi ji fa?,kina da sauran wani abu da zakiyimin ne sabreen?". Kai ta dauke
sabreen din,tana hadiyar wani yawu me tauri tamkar dunqulallen dan waken da ya
tsaya a maqogaro. Kamar ba zata tanka ba kafin ta waiwayo,a nutse ta kalli idanunta
tace

"Ki gwada qinjin gargadina mana hadiyya koda na minti guda ne kiga abinda zaya
faru?" Ta qarashe maganar cikin jin zuciyarta da ruhinta sun taurare. Akan batun
iyayenta kuma komai tana iya aikatashi muddin hakan zai sanya ta kare mutuncinsu
daga baki da aibantawar mutanen da basusan me ake nufi da daraja da kuma kimar dan
adam ba

"Hadiyya.....rabu da ita.....karki sake ce mata komai don ke din tsatson mutunci
ce......kuma muddin hassada tana dawainiya da mutum akan ci gaban daka samu da
kulawa ta iyaye komai ma zai iyayi maka don ganin kun dawo daya kai dashi" Kalmar
HASSADA ta sanya sabreen waiwayowa ta kalli hadiyyan da bibo din gaba dayansu.
Banda yadda ranta yakai maqurar baci da babu abinda zai hanata murmusawa. Wata
kalma ce da take daidai da hali da kuma abinda ke cin zuciyarsu a kanta,shine
sukeson sanya dukkan qarfinsu su juyar da ita zuwa kanta.

Tana jiyo bibo tana ci gaba da soki burutsunta,sai bata bi takai
ba,ta dinga takawa a hankali abinta har ta wuce zuwa dakin su.

Wani zafi da zugi zuciyarta takeyi mata. Wani irin radadi data jima
bata ji irinsa ba saboda kawar da kanta daga harka da sabgar kowa a gidan. Tana
kallon yadda huda ke zaune tana kuka amma batace mata komai ba. Tasan kukanta guda
biyu ne,na tadda hadiyyan taci mutuncinta dasu gaba daya amma sabreen din ta hanata
maida martani.

Ita nadra da haneefa sukayi sallansu,don har suka idar huda din tana
zaune tana kuka. A hankali ta maida idanunta kan hudan,tana jin tausayinsu dukka
yana kamasu. A hakan a sanda rayuwa ta fara musu kyau. A hakan a sanda ta jajirce
akansu.....a sanda basu nemi komai a gurin kowa ba......a sanda asirinsu yake a
lullube ba tare da sunyi ROKO ko bara ba.....ba kuma tare da sun nema komai a wajen
kowa ba......ya rayuwa zata kasance musu a sanda dukka babu wadannan ababen data
lissafa?.

"Ki tashi ki dauki pure water kiyi alwala cikin kitchen" Tace da ita tana ci gaba
da sauke kanta qasa. Abubuwa ne cunkus masu yawa qasan ranta. Har tayi sallar nadra
ta zuba musu abinci daga ita har hudan ba wanda ya samu damar sanya komai a
cikinsa. Ta kama haneefa ta tsefe mata kanta,don ba abinda take bari suyi cikin
unguwar,bata bari kowacce kalar mu'amala ta hadasu da kowa,tana kaffa kaffa da
komai nasu,ta nesanta su da mu'amala da kowa don kiyaye jinsu da kuma ganinsu,tana
dubansu tace musu

"Gobe zamu fita kitso,ke nadra kece me nauyi,bazanyi jira ba me yawa don da wuri
zamu dawo gida in sha Allah".

"To" Suka amsa mata gaba daya. Ta miqe a nutse ta barsu a falon,don tasan ba zasu
kwanta yanzu ba har sai sun gama kallon film din da ake haskawa.

Numfashi ta sauke me nauyi sanda ta zube ruf da ciki saman gado tana
lumshe idanunta,sai takejin fitar numfashin tamkar raguwar radadi ne daga
zuciyarta. A haka idan ka kalleta zaka dauka bacci takeyi,amma idanunta biyu tana
ci gaba da sauraron motsin su nadra jifa jifa daga falon. Radadin da rayuwa ke tafe
dashi take tunawa daki daki. Ba wani majibancin al'amari da zata sanya kanta saman
kafadunsa tayi kuka.....ba wanda zata amayarwa da irin radadin da takeji.....ba
abokin shawara.....ba abokin raba dadi da akasinsa,sai nauye nauye dake aje saman
kanta masu tarin yawa.

Har suka kammala komai sukayi shirin bacci suka kwanta tana jinsu,sai da
kusan bacci ya daukesu sannan ta miqe don samawa kanta abinda zataci,daidai lokacin
taga motsawar huda.

"Huda?" Kai tsaye tayi kiran sunanta don ta tabbatar batayi bacci ba kenan. Abinda
kuma ke alamta mata bacin ran da take ciki ne har yanzu yake nuqurqusarta.

Qasa qasa ta amsa mata,sai ta umarceta ta tashi ta zauna. Ba musu
ta yaye abun rufar ta miqe ta zauna tana dubanta. Takawa tayi zuwa gaban gadon ta
zauna idanunta a kanta. Ta zuba mata idanu na wasu mintuna ta zuba mata,abinda ya
yiwa hudan nauyi tayi qasa da kanta,ta buda bakinta a hankali tana jin tsanar gidan
dama duka mutanen ciki

"Kiyi haquri adda"

"Yanzu meye ribarki huda?,wace riba kikaci bayan kin tsaya kin biyewa
hadiyya?,shikenan kalaman da kunnuwanki keson ji daga bakinsu kinjisu hankalinki ya
kwanta?". Hankalinta taji yadan tashi,tsanar rayuwar gidan tare da ci gaba da
rayuwa ma a cikin gidan duka tana saukar mata. Ta girgiza kai idanunta suna tara
qwalla me yawa

"Ba haka bane adda......bakiji abinda suke fada a kanki bane?,bakiji mummunan jifa
da qazafin da sukeyi miki ba?" Ta fada hawaye na saukar mata.

Yawu itama ta hadiya tana qoqarin hana nata qwallar fita,duk da ba
qaramin abu bane yake sanya fitar hawaye daga idanunta ba

"Ki barsu suyita fada mana huda?,meye zai gutsireni?,mene ne kena zai
gutsireki?......shin kin manta su din su waye?,ko kin manta ne huda?" Kai ta
girgiza qwaqwalwarta na tunano mata abubuwa da dama daga halaye da dabi'un mutanen
gidan.

"Wannan ya zama lokaci na qarshe da zaki sake maida kai cikin shirginsu"

"Kiyi haquri" Ta fada bayan ta gyada kai

"Ya wuce......ki kwanta hakanan" Ta fada tana dan taba kafadarta.
Dukka wayoyinta ta dauka harda ma wadanda ta basu hutu na satittika
dana watanni,sannan a nutse ta wuce zuwa falon. Bata zauna ba sai data zuba
abinci,duk da cin abincin nata har kullum tamkar wasan yara yake. Takan tuna
umminta duk sanda ta zauna irin haka zataci abinci

"Kedai saidai addu'ar shiriya sabreen.....yarinya kamar mage?,ki dinga lasar
abinci?,zakici ba zakici ba?,shi yasa kikejin jiki idan ciwonki ya tashi". Numfashi
ta sauke,ta saka hannu tana goge qwallar data cika mata idanu.

Babu wani lokaci ko yanayi da zaizo bata tuna umminta ba. Ba wani
dan qaramin sakan ko minti da zaizo ba tare da tuna umminta ya sanyata zubda
hawaye. Bangwaye guda biyun da zubewarsu ya sauya rayuwarsu daga wani abu izuwa
wani abun na daban.

Kunna wayoyij tayi gaba dayansu ta kuma jeresu a gabanta,ta jawo
abincin tana qoqarin tilastawa kanta ci,idanunta na yawo tsakanin fuskokin wayoyin.
Haske kusan dukansu suka dinga yi alamun shigowar saqonni zuwa gareta kena. Ta saba
da irin hakan duk sanda ta baiwa wayoyinta hutu toba shakka zata samu saqonnin da
basu da adadi. Da yawansu tana gogesu ne ba tare da tako duba ba,d'ai d'aiku daga
ciki take tsaiwa dubawa


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

*_Arewabooks:@Huguma_*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997
__________________________

PAGE 41


Kusan a tare wayoyi uku suka dauki ruri dake nuna alamun ana kiranta.

Mashkur mikail da ya'aqoub,abubuwan farautarta da batasan waye a ciki
zai fada komarta ba. Ta dinga bin sunayen da wayoyin da kallo cikin canki cankin
wanda zata fara daga wayarsa a ciki har sai da suka katse,sai ta barwa ranta wanda
ya soma sake kira. Saidai kuma cikin rashin sa'a sai ga mashkur da mikail suna
kiranta lokaci guda. Plate din hannunta ta ajiye,ta sanya hannu tana daukan kiran
mikail. A lissafinta shine mutum na farko da takeson saukewa daga layinta. Dukka
wani binciken halayya nasa suna gwada mata tsantsar dacewar ya karbi sakamako da
horo yadda ya dace. Ita kanta batasan adadin abinda zata diba daga gareshi
ba,saidai ko banza ta sanya zata sanyasu a muhalli da guraben da suka dace.

A jirkice yayi mata sallama da muryar data sanya ta saka masa ayar
tambaya. Ta daga wayar daga kunnuwanta ta duba fuskar wayar tana mamaki

"Bayan neman mata harda caca da harqallolinsa harda shaye shaye?" Ta tambayi kanta
cikin mamaki,sai ta maida wayar kunnenta kawai tana saurarensa.

"Sai yaushe zaki bani dama ne?......ina tsananin kewarki......ina son kasancewa
dake" Abinda ya fada kenan yana jin kamar ana fusgarshi zuwa gareta. Katse wayar
tayi tana jan dogon tsaki. Baci kawai takeji ranta yana yi kota ina tare da
azalzala mata akan mikail. Sai ta jawo wata qaramar waya daga gefanta wadda bata
hasken komai ba ta turawa JIB qaramin saqo. Tana jin ya kamata aikinta ya fara ta
kansa.

Yadda mashkur yaketa kiranta ba daga qafa ya sanya ta share kiran
ya'aqoub ta daga nashi. Kiran ya'aqoub din ma bata mata rai yakeyi,ta tabbatar
dukkan wani magidanci me mata irinsa a yanzun yana cikin gidansa ne koda a dakinsa
ko a sassan yake. Taga maza da yawa da halayensu,daya daga cikin halayyar tasu kuma
da tafi baqanta mata rai take tunzurata shine wannan. Wai ta yaya ma zatayi
Aure?,bayan bataga komai ba a tattare da mazan sai munanan dabi'u dake girgiza
zukatan matan su haifar musu da muguwar illar hawan jini ko ciwon zuciya?,ko
mummunan zawarcin da har ki mutu bazai fita a tarihinki ba?. Har abada tana kallon
zaman 'ya mace me cikakken 'yanci a yayin da ya kasance babu igiyar wani a kanta.

"Saura kadan ki kashemin raina muhseena......hala bakisan girman soyayyar da nake
miki ba har yanzu?......kinsan Allah?,banqi a daren nan ace an daura aurena dake
ba?"

"Aure?" Ta furta a hankali tana jin kalmar tayi mata girma da yawa.

"Yes aure muhseena....." Ya maimaita fada yana gyara zamansa cikin tattausar sofa
din da yake kai. Yana fatan samun gamsashen amsa tare da mamakin kansa yadda
yarinyar ta sauya masa tsari gaba daya.

"Gaskiya ne" Ta amsa masa a taqaice tana aje numfashi.

Hira ya dinga qoqarin janta dashi,duk da ita din bame doguwar hira
bace amma ta dan sake masa,don itace hanya guda daya da take dashi da zata haska
mata hanyar gano gurbin da zata dasa bomb dinta.

"Kiyimin alfarma daya mana......ki gaya min credit dinki na yimin rakiya dubai for
just one week......ni kuma nayi alqawari zan biya ko nawa ne" Ya fada yana sake jin
kowacce gaba tasa tana narkewa da sha'awarta da sonta. Yanajin koda bata shirya
aurensa ba......zai kashe mata ko nawa ne suyi irin rayuwar da yake
muradi......idan da yiwuwar ta zama tashin a gaba sai ta zama.....idan ma hakan
bata samu ba yana ganin duk inda ta kwana sha ne muddin ya tsira da abinda yake
qulafucin samu.

"Zan baki dama kiyi tunani......sannan ki yanke ko nawa kikeso muhseena.....ko nawa
ne muddin raina zaikai ga muradinsa".

Maganarsa t qarshe kenan data sake sanyawa sabreen mummunan zato ga
maza......maganarsa ta qarshe data sanyata ta kusa raba dare tana kuka......ta kuma
dinga godewa Allah ta wasu fannin.

Mashkur din data tura masa mabanbantan mabuqata da buqatar neman
tallafin da duka duka baikai ko digo cikin abinda ya mallaka ba yasa aka
koresu?......yace bashi dashi?.....yace bazaya bada ba?......wannan mashkur din yau
shike bada damar a nemi ko nawa ne zai iya mallaka mata bisa rashin sanin WACECE
ITA?.

Hakan tamkar wata dama ce a gareta kenan da zata samu dukka kudaden da
takeso......amma bisa sharadin sadaukar da abinda yafi komai mutunci a tare da
ita?.

Koda ta saba ko tana da damar accepting masa abinda yazo
dashi.......tabbas ba zata lamunce ba......tanaso ta debi kudadensa ta hanyar data
saba azabtar da sauran.......tanaso ta debesu ta hanyar da zaiji ciwon da bazai
kankaru ba a zuciyarsa.......tanaso ta debi kudin da zai tsaye masa a rai......yayi
masa ciwo fiye da yadda rayuwa da zukatan matan da ya fadawa mutuncinsu sukayi musu
ciwo......tanason bashi darasi me girma a rayuwa.......tanason shima ya girgiza
girgizar da zata tsaida masa komai na rayuwarsa cakkkkk koda ba tsaiwa bace ta har
abada......to amma kuma ta sani.......babban plan da yake buqatar nutsuwa da tsare
tsare masu yawa. Don haka da safiyar washegari ta tura JIB wani saqon da sunan
mutum biyu.

Tana tsaye tana shan ruwan dumin da takesha duk safiya kafin
shigarta wanka saqo ya shigo wayarta. Sanda ta duba sai ta samu alert na kudi daga
wajen ya'aqoub. Five hundred thousand ce,sai ta gyada kai a hankali tana sakin
murmushin takaici. Don kyauta yana da kyauta ya'aqoub ba daga baya ba......abinda
bata da yaqini shine haka yake a cikin gidansa?,ko shima fankan fayau ne?.

Saqon godiya ta tura masa a gajarce,ta aje wayar tana shirin wucewa
wanka wani saqon ya sake shigowa

"Patiently waiting for you" Share saqon tayi hade da sauran. Tasan me saqonsa ke
nufi a gajarce. Kowacce safiya izina ce a gareta,kowacce rana kowanne sati da kuma
kowanne wata cikin rayuwarta yana bude mata babi na abubuwa da yawa cikin
rayuwarta. Waishin akwai ragowar NAGARTATTUN MAZA kuwa?,tambayar da kullum idan ta
yiwa kanta ita take bawa kanta da kanta amsa da BABU.

Kanta tsaye take takawa cikin tsakar gidan nasu ba tare data daga kai
ba bare ta lura da waye a hagunta ko damanta?. Ba tare data damu da kallon nan nasu
data tabbatar a safiyar yau zai ninka ko ma ya canza salo saboda abinda ya faru a
jiya.

Dab da zata sanya qafarta a qofar toilet din nasu dake da sassa biyu
bathroom da toilet ta jiyo muryarsa yana koda sallama. Sallamar da muddin ya yita
duk wani dake da hadin kai dashi take masa dadi......duk wani wanda yake da qulli
dashi Kuma yake neman yin ta kansa,mutane kuma kamar ita sukejin kamar su turashi
ya koma muhallin da ya fito.

Koda taso tayi shigewarta toilet din ta tabbatar sai ya ganta don ya
iso dab da wajen. Don haka ta tsaya a nutse tana bude toilet din ta hanyar murza
handle,abinda ya bashi damar qarasa shigowa farfajiyar tsakar gidan.

Da ita ya fara hada idanu kamar yadda nata idanun suka zube a
fuskarsa. Kamanni dai da mahaifinta har kullum sune,bata kuma fasa ganinsu shimfide
a fuskarsa,saidai nisan tazarar halayya da dabi'un sun kai girman tazarar dake
tsakanin sama da qasa.

"Yauwa alhamdulillah......ai gwara dana sameki cikin gidan.....zuwan dama naki ne"
Kallonsa kawai tayi ba tare da wani mamaki ba,dama wanne zuwa ne zaiyi gidan ba
nata ba?,koda yayi zuwan daba nata ba to lallai daga qarshe sai ya zama nata ko
kuma ya hado da ita a abinda bai zama damuwarta bama bare y shafeta. Amma tun a
jiya tasan tabbas dama zayazo,shi yasa taso su fice kitso da wuri yazo ya taras da
sararinsu kawai.

"Ina kwana kawu?" Ta fada cikin girman nan da bata fasa bashi shi kaman yadda kowa
cikin gidan ke bashi duk kuwa da farin sanin da tayi na waye shi?,sanin da kaf
gidan tayi yaqinin ba wanda ya masa shi......sanin da a qa'ida ya cancanci ta
rainashi......amma sai kuma batayi hakan ba.......sanin da ko yaushe ta tunashi
dashi take jin kaico da bacin rai da rashin sanin son ganin gilmawarsa.

"Lafiya qalau......idan kin baro bandakin ki sameni a dakin bibo" Ya fada yana saba
babbar rigarsa yana wucewa ciki tare da jaddada sallamarsa.

Da kallon takaici ta bishi,tasan dama zaa rina,ba wani abu da zai
fari cikin gidan ya kwana ya hhantse baije kunnuwansa ba.......yana kuma zuwa
kunnuwan nasa ne ta hanya guda daya rak wato BIBO. Idanma akwai ta biyunta to bata
bayyana ba tukunna. Cikin rashin damuwa da lamuransu gaba dayansu ta kada kanta ta
wuce bandakin.
Babu wani abu da zai sanyata gaggawa a zuwa kiran data tabbatar babu
alkhairi sam sam a

Please Login or Register in order to submit comment