You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dade tana fatan zuwan wannan ranar,ta dauka duk
sanda taxo din zata kasance mutum da tafi kowa murna a duniya,amma kuma sabanin
murnar mutuwar jiki taji.

Matsawa tayi sosai gaban table din,ta ware qananun luxury table mat
din ta sake shimfidasu,sannan ya zari plate da bowl ta soma zuba komai tsaka tsakin
quantity sannan ta jera masa a gabansa.

Wayar ya ajiye a gefansa,ya miqa hannu da kanshi ya ciro spoons guda
biyu ya saka cikin abincin sannan ya dubeta

"Oya.... Let's eat together" Ya furta yana matso da drinks din da aka aje a wajen
duk da ba abun shansa bane sam sam duk wani drink da company ta sarrafa.

Ba shiri ta bude idanunta a kansa,ji tayi kaman an dauko guduma an
shirga mata. Cikin qasa da minti daya tayi qoqarin daidaita nutsuwarta dukka a
qoqarinta na daidaita komai,ta girgiza kai tana fadin

"Na qoshi". Sake ware idanunshi sosai yayi a kanta yana dubanta,abinda ya sake
sanyata kenan a tsilla tsilla,tana kyautata zaton akwai wani abu me nauyi da
idanunsa ke dauke dashi,wanda muddin ya kama zuzzurfan kallo irin wannan sai
kajishi har qashinka.

"I think kin fito ne ke debi abincin right?" Daburcewa tayi yanda ya kama abinda ya
fito da ita din kansa tsaye kamar me gani har hanji. Bata saba qarya ba koda wanne
irin hukunci aka tanadar mata,wannan ya sanya kai tsaye ta bashi amsa da eh.

"Good.....kinga wannan shi yafi kamata muci tare ko?" Ya fada cikin sigar saukar
dakai yana turo abincin gabanta. Kanta ta sake kadawa,gaba daya yana birkitata
ganin yadda yake matsantawa saita zauna sunci abincin

"Seat down!" Ya fada da wani irin husky voice yana buga hannunsa saman table din
har abincin dake cikin plate din yana watsewa saman table din. Batasan sanda ta
zauna ba kaman yadda ya buqata tana qoqarin kaucewa kallon fuskarsa da har hancinsa
ya fara yin ja alamun tsananin bacin rai wajen farin mutum kenan.

"Kinsan abinda zan gaya miki guda daya?" Yayi maganar qasa qasa kamar ba shine
yanzu ya buga wannan tsawar ba,bai jira ta amsa ba ya dora da fadin

"Duk sanda kika qara yimin girki a gidan nan saikin cinyeshi tsaf!". Gigicewa ta
sakeyi da abinda yace,maganar daya fada kawai ta sanya hasashenta ya tsaya daidai
inda take zatonsa

"Be warned!" Ya furta yana ranqwafowa sosai saman kanta har tana iya sheqar dumin
numfashinsa da yake futarwa daga hancinsa. Baya yaja ga kwashe wayoyinsa,zuciyarsa
na masa wani irin zafi ya soma sauka daga wajen yana dosar hanyar da zata sadashi
da stair dinsa.

Maamah uwarsa ce,ba yadda zaiyi da ita,amma zaiyi dukkan abinda zai
iya ya toshe kowacce qofa da zata samu nasarar budeta a kansa ko kuma waninsa
muddin yana da iko da masaniya.

Koda ya koma saman duk yadda yaso yayi keeping kanshi busy ya manta da
komai sai ya kasa. Mahaifiyarsa......macen daya biya kudade aka daura mata
igiyarsa..... A duniya idan akwai wasu mata da sukafi kowa kusanci dakai suna sama
da wadannan ne?. Me suke nema a tare dashi?,amsar daya kasa laluba kenan. Sosai
abun ya dinga masa ciwo,shi yasa ko sau daya bai taba aminta da ita ba,ko sau daya
bai taba jin ya gamsu da ita ba......takowacce fuska tana da qatuwar lam'a da tabon
da shi shine babbar shaida......bayan tarin shaidun da ya samu har abinda be nema
bama an bashi,ta yaya zai iya kallonta a matsayin wankakkiya?,ta yaya zai iya yafe
mata?. Yanason ya zame mata lesson me girma a rayuwarta,zai kuma ganar da ita
kuskurenta na shiga rayuwarsa hakanan kai tsaye.

Daga qarshe dai dole ya kunna karatun qur'ani daya karade ilahirin
sassan nasa,yayi kwance kawai idanunsa a lumshe sautin yana shiga kunnensa,sannu a
hankali kuma nutsuwa ta fara samuwa a jikinsa.

Ko qwaqwaran motsi kasa yinsa tayi ballantana ta tashi daga
wajen,batasan adadin lokutan data shafe zaune a wajen ba,har sai data daga idanu
taga agogo yana gaya mata qarfe goma da rabi saura mintina biyar sannan ta iya
miqewa.

Zuwa sannan hatta da qafafunta sunyi wani irin nauyi da sanyi,saita
gaza shiga kitchen din ta zarce hallway din sannan ta fada dakinta. Rasa abinda ya
kamata ta tuna tayi,ganinta yayi kenan koko yaya?. Karon farko da taji wata irin
nadama na saukar mata. Ya akayi ta biyewa mamah din ta yarda ta ciyar dashi gubar
da batasan ranar yankewarta ba?,wacece maamah din?,me kuma take qullawa?,me take
buqata ne a rayuwarta sama da rayuwar da take ciki?.

Zafi sosai takeji cikin ruhinta,tunda take bata taba sha'awar ciyar da
wani ko shayar d wani wani abu me illa irin wannan ba,koda sanda take shirya gyara
zaman mazan da suka zabi harka da mata kuwa.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 42


_Daba abu hurairah RA yace,manzon Allah S A W yace "mafi falalar sallah bayan
sallar farilla itace sallar dare_

*_ga falala ga kaifi,biyan buqata kaman yankan wuqaπŸ˜„,Allah ya bada ikon jurewa_*
____________________________


β˜…Qarfe tara na safiyar alhamis ce wadda aka wayi gari da lullumi
qwarai,sakamakon hadarin farko daya fara hada jikinsa tun bayan sallar asubahi. Bai
bada ruwa ba amma kuma ya yiwa rana shamaki daga fitowa tayi rawar gaban hantsi
kamar yadda ta saba kowacce safiya saman sararin samaniya.

Yanayin sai ya haifar da yanayi me dadi da kuma sanyaya zukatan da suke
cikin wani yanayi.

A irin wannan lokacin ne muhammad jadda mamallakin kamfanin jadda
diamondchore resources yake saukowa a hankali daga samanshi. Cikin shigar
aiki,saidai kuma yau zaka dauka juma'a ce saboda shigar kaftan yayi. Dinkin zamani
daya zauna masa sosai,ya kuma fidda sigar kyan nan nasa da kana kallonsa zaka
tabbatar tabbas halfcast ne shi din wato ruwa biyu.

Cikin parlor din ya samu tuni ameh ya kammala shirya masa komai na
breakfast dinsa. Ameh din shi ya koma masa girki tun bayan wancan abun daya
faru,yaja daya daga cikin kujerun wajen ya zauna ameh din ya gaidashi cikin
rusunawa. Amsawa yayi da kulawa sannan ya fara serving nasa,yana yi yana dibansa da
labarai,wanda kusan dukansu labaran da suka fita ne a jaridar safiyar. Ameh din
yana da karance karance da yawan sauraran kafafen yada labarai,don haka a mafi
yawan lokuta idan bai samu damar duba news paper ba shike bashi latest na cikinsu.
A nutse ta maida littafin amdatul ahkam da take dubawa,ta kuma d'auki
zaduzzaujaini ta sakashi a ciki don yin alama akan inda ta tsaya din. Saman side
bed drawer tayi masa kyakkyawar ajiya tana jin wata nutsuwa tana ratsata. Sati guda
kacal kenan da fara karatunsu da rumaisa'u d'iyar malam amma wani nutsuwa takeji da
gamsuwa da karatun. Rumaisa'u din da tayi tsananin mamakin ganinta a matsayin
malamarta da ya dauko mata domin daukan karatun addini a hannunta. Zuwanta kusan
uku tana rejecting tana qin fitowa......sai ana hudun ta fito da zummar yiwa
malamin ko malamar bayanin ta daina wahalar da kanta tana zuwa......ta gayawa wanda
ya aikota dalibar bata da buqatar wani karatun. Ganin rumaisa'u din sai ya zagwanye
komai daga zuciyarta,ta cika da mamakin zuwanta gidan,saidai daga baya rumaisa'u
din ta gaya mata

"Hamma muhammad tsohon dalibin malam ne"

"Gwara da kika ce tsohon" Sabreen ta furta a ranta. Don tako ta ina bataga ta inda
ya dace ko ya cancanta mugu maqetacin mutum kamar fu'ad din ba ya hada alaqa da
malam ba. Daga haka ba wani zance daya qara shiga tsakaninsu,sai hiran duniya kawai
da kuma karatun daya biyo baya.

Da farko kawai dai tana sauraren rumaisa'u dinne,amma karatun kwata
bayayi mata wani armashi ko burgeta. Saidai lokaci guda kuma a rana daya data arawa
rumaisa'u hankalinta sai taji karatun ya fara shiga kanta,mafari kenan data fara
hada hankalinta da zummar Tsintar abinda ta Tsinta,saidai tafi tafi sai ta fahimci
karatun yafi qarfin ka tsinta kawai. Ita kanta rumaisa'u mamaki takeyi
ainun....mamakin yadda karatun yake gudu saboda yadda suke qara karatun da yawa. Ta
sallama da gaske karatun yana gudu ne saboda wata irin sharp brain da Allah ya bawa
sabreen din,irin kwanyar da bata taba ganin irinta ba. Don duka karatun da sukayi
da yammaci,zuwa wani yammaci din sabreen din ta narkashi ya koma cikin kwanyarta.

Tun asali tana da bala'in son karatu,musamman na addini din,saidai wani
dalilin me zuwa ya ture wani. Ratayuwar hidimar qannenta saman wuya da kafadunta ya
sanya tilas ta haqura da komai ta tattara ta ajiye,a yanzun kuma data fara shiga
cikin abun sosai sai takejin komai kamar an yaye mata wani hijabi ne da da ya
lullube kwanya da idanunta.

Tun sanda ta fahimci ya ajiye cook dinsa cikin gidan saita saita lokacin
ta,sanda zata fito tayi sabgarta daga shi har cook din nasa basa gidan,hakazalika
kafin su dawo ta kammala komai ta koma daki abinta.

Tayi mamakin yau da taji yunwa da safe da wuri haka,to amma kuma idan ta
tuna ba wani abun arziqi take ci ba musamman jiya da dare bata saka wani abu me
muhimmanci a bakinta ba sai taga ba abun mamaki bane.

Indonesian hijab down squeeze ta saka saman soft and cotton nigh gown din
jikinta da bata fidda siffarta ba,saidai tadan lafe mata a mazaunai saboda
taushinta. Hijab din ya qara qawata mata fuska,fuskar data fita sosai ta tsakiyar
hijab din da wani irin kyau kai kace itama haifaffiyar Indonesia dince. Ta qarasa
gaban mirror ta qara turare a jikinta dan kadan kamar yadda ya zame mata wajibi,sai
ta tsaya tana duban fuskartata. Wani irin glowing skin dinta yakeyi wanda ita kanta
ta rasa dalili,saidai a yawancin lokuta tana bawa kanta amsa da wataqila zaman guri
daya ne,sabanin baya da kullum muddin gari zai waye rana ta fito to zata saka
qafarta a waje ta fita.

A hankali take tako hallway din,yau kawai tana jin nishadi cikin ranta
sosai da cikakkiyar nutsuwar da batasan dalilinta ba,kwanyarta tana bitar wasu daga
cikin karatuttukan data haddace,a haka ta rasa parlour na farko ta wuce zuwa na
biyu.

Tana murza glass door din ta sanyo qafafunta ya daga idanunsa a
hankali daga inda yake zaune ya zubesu fes saman fuskarta,idonta ya shiga nasa,sai
ta janye nata idon a hankali,ta kuma ja da baya tana komawa da bayan a maimakon
fitowa da tayi niyyar yi. Sam bata qaunar gamuwa dashi,a kwanakin data janye kanta
daga komai da zai sanya su hadu ta kama karatunta sai take samun wata irin nutsuwa
a zuciyarta. Ta dauki kwanaki rabon daya sanyata cikin idanunsa,daga shi har maamah
sai takeji kamar Allah ne yayi mata maganin matsalarsu.

Janye nasa idanun yayi shima bayan ta koma da baya tana kuma komawa ciki.
Yadan jijjiga kai kadan yana daukan mug din gabansa ya sanya a bakinsa. Tana gyara
bedroom dinsa kamar yadda sukayi sharadi,saidai daga wannan ko gilmawarta bai sake
gani ba tun daga ranar. Can qasan zuciyarsa tana cike da wasi wasi da kuma qiyasi
akan abubuwa da dama. Sai yake zargin shurunta dana maamah dukka kamar akwai wani
magana a qasa,don haka ya jawo wayarsa ya kira me sunan malam. Cikin qasa da second
ashirin suka gama magana,ya shaida masa ya nema farouq ya turo amintacce kuma
sirrintaccen me musu installing CCTV.

Mules din qafarsa ya maida,sannan ya ciri napkin guda daya yana goge dan
abinda ya bata masa hannu kafin yace da ameh.

"At night.....ka dafa paw paw leaves ka ajiyemin da duminsa.....daga yau inaso ya
zama first drink dina for morning". Kai ameh ya jinjina cikin girmamawa

"As you wish sir". Sai ya sauka a nutse amma hankalinsa yana dan kan qofar
kadan,yanason sake tabbatarwa komawa tayi ta fasa shigowa saboda yana wajen?.

Murmushi ameh yayi yana binsa da kallo,sosai boss dinsa yake burgeshi,yayi
aiki kafin wajensa gidajen manyan attajirai da dama,amma baiga mutum me kiyaye
lafiyarsa da yasan sirrin abinci ba irin boss din nasa ba. Yasan duk wani abu da
zai gyara lafiyarsa a matsayinsa na namiji,yasan duk wani abu da zai gyara masa
lafiyar ido da fatarsa,hakanan yasan duk wani abu da yake natural anti aging
remedies kala kala. Ire iren abubuwan da shi yake tanadarwa manyan da yayi aiki a
qarqashinsu don inganta lafiyarsu da gina garkuwar jikinsu suke qin ci ko sha don
ba dadi a baki ko basusan muhimmancinsa ba......sai gashi shi kullum ne sai an
tanadar masa da wannan abun morning and evening. Akwai hadin salad daya dinga
mamaki sanda yaga yana cinsa farkon xuwansa,musamman da yake yasan yadda yake
inganta qarfi da lafiyar d'a namiji,da yawan wasu abubuwan ma shike qaruwa dashi a
wajensa. Baya son maggi da yawa a abinci,kaman yadda sanyi zaqi da kuma maiqo da
abokansa bane sam sam
(Mata da yawa suna complain din rashin lasting din mazansu a other room,sunsha
magani sunsha maganin amma a banza,anata samun sabani da sauran masu matsaloli,to
wallahi wallahi da yawansu maggi shine yake kashesu,inda kinsan yadda maggi yake
kashe lafiyar mazajenmu da kinyi mugun gudunsa kuwa,kiga mace ta saka farin magi a
abinci,tazo ta saka wadancan cubes din kala daban daban,ta hada drink ta laftawa
miji sugar,ga uban sanyi,abinci mai yana kwanciya,ba ruwanki da manja ma sam sam,to
billahillazi kunji na rantse muku haka zaita zame miki mace,kuma duk irin maganin
da zaisha fa a banza,muddin ana kan cin magin nan,tashi daya ba zaki iya dainawa
ba,amna gradually zaki dinga janyewa,idan goma kike sawa ki koma bakwai daga haka
ki koma hudu,tabbas indai zaki dimanci haka zaki ga canji,ki ajiye farin maggi
kwata kwata,zaqi da maiqo duka ki rage masa,hadin wancan salad din in sha Allah zan
kawo muku shi a gaba,ya gwada cin na sati biyu bayan kin janye magin kiga ikon
Allah,koda me gida yana da lafiya ma normal ne kina iya hada masa shi ya dinga
ci,amma ina maimaita muku ku raba kanku da kayan d'an d'anon nan,Allah yasa mu
dace).

Kamar kowacce safiya muddin yana da isashen lokaci......ba baqi ba
meeting na early morning da sauransu,zuwa duba lafiyar anni da gaida maamah din
yana cikin schedule dinsa na kullum.

A farfajiyar gidan kamar ko yaushe ya samu guard dinsa,kowa na tsaye
akan aikinsa. Bai qaraso bama amma tuni Jordan ya buda masa bugatti dinsa yana
jiran qarasowarsa.

Cikin girmamawa da nuna kulawa suka gaidashi ya amsa yana bincikar
lafiyar kowa kaman kowacce safiya,sai daya tabbatar da kowa lafiya sannan ya miqawa
saddiq da kusan a makare yake isowa kayan hannunsa,wannan dalilin ya sanya baya
samun shiga cikin gidan duk zuwan da yakeyi.

Sun dauki hanya sosai kiran musaddiq ya shigo masa,ya fidda wayar yana
connecting nata da Bluetooth dinsa yana amsa wayar.

"Hamma na gama komai......sai yaushe zan dawo?" Musaddiq din ya amsa a karye da
alama gida yakeson dawowar.

"Ka dawo kayi me?" Ya tambayeshi yana jin tantama a dawowar tasa.

"Hamma nayi missing anni......nayi missing saddiq". Iska kadan ya furzar daga
bakinsa wadda ta fita da qamshin mint leaves saboda mouth fresh dinsa kenan na
dindindin

" Anni kuna waya haka saddiq.....kuma ko ita nasan bata da damuwa me yawa a
tafiyarka.... Dude ne kawai nakeji ban kyauta masa ba dana dauke masa personal
assistant......shima nasan ya fahimceni.....oops......anyways......nan da sati biyu
zamu hade a madeena in sha Allah,it was family trip time". Har a muryarsa yaji dadi

"Hamma na Manta da lissafinma.....okay..."

"Hope komai naka ba matsala ko?,daga can zaka iya shiga koda Jeddah ne sai ka
qaraso madeena"

"Direct entry zanyi hamma.....i can't wait to see my family".

"Alright....ka kula da kanka" Ya furta cikin kulawa

"Na gode hamma" Ya ambata suna ajiye wayar. Wayar ya zubawa idanu yana tuna wasu
abubuwa da suka shude..... Ita rayuwa dukanta tana komawa tarihi ne
watarana......bai taba zaton a rintsin da suka fuskanta shi da musaddiq ba akwai
ranar da zatazo kamar haka komai ya wuce ba......yadda kula da musaddiq da bashi
rayuwa me kyau ya sanya hannuwansa sukayi kanta.....tunaninsa ya dimauta,kwanyarsa
ta kusa jirkicewa da daina iya tuna kome me kyau.....ambaton sunan maamah ya zame
musu kamar wata jarabawa.

Hannunsa yasa ya shafi fuskarsa yana son ajiye tunanin a
gefe.....yanzu yanzu zai iya rasa kowacce nutsuwa tasa,ya kuma rasa duk wani
courage na aiki daya fito dashi a yau din.

"Gidan maamah zai fara tsayawa" Yace da saddiq don ya shaidawa driver din shi kuma
ya sanar da ayarin motocin. Yayi hakanne don yasan muddin ya shiga gidan maamah a
yanayin da yake ciki na tuna munanan abubuwan data aikata baga rayuwarsu kadai
ba......anni itace zata zamewa zuciyarsa yayyafin ruwan sanyin da zai wanke duk
wani baci da ransa yayi.

Kamar kullum da qafa ya taka daga inda suka ajiye motocin zuwa cikin
gidan. Malam sa'adu ya matso da sauri yana bude masa qaramar qofar kasancewarsa
shugaban masu gadi na gidan a yanzu. Tunda aka mallakawa maamah din wannan gidan
yafi qarfin gadin malam sa'adu shi kadai,dole sai daya hada mata da security,amma
kuma kowa yana qarqashin malam sa'adun ne wanda shike da permanent chair. Har
kullum burgeshi hali da dabi'ar muhammadun takeyi,ya taka dukkan wani matsayi da
bawa zaizo ubangiji ya kaishi a rayuwa,amma bai dauki hakan a bakin komai ba.
Gaisawa sukayi kamar kullum,sannan ya taka yana shigewa cikin gidan
da ma'aikatan dake bakin aiki kowa yake zubewa yana gaidashi.

Daidai sanda yake sallama a falon daidai sanda take fitowa daga
kitchen din gidan,Hannunta dauke da qatuwat warmer kamar ma rinjayarta takeyi.

Huda ce,ta bishi da kallo tana amsa sallamar tasa cikin kallon
baqunta. Yadan sake dubanta kadan,sai yake jin kamar yasan fuskar,amma kuma sai ya
kauda wannan tunanin yana neman wajen zama,daidai sanda take gaidashi cikin ladabi
daya zame musu jiki tun tale tale

"Ina kwana?" Ko daya maida dubansa kanta sai yaga har ranqwafawa tayi irin na ban
girman nan

"Lafiya la....." Amsa gaisuwar ta katse saboda yadd warmer din taso subuce mata
daga hannunta. Cikin zafin nama ya isa ya karba yana fadin

"Kibi a hankali......" Sai ya taka yana kaita saman dining din ya ajiye.

"Maamah ko?" Ta tambayeshi qasa qasa kaman me tsoron tambayar,don itadai yana mata
kama da mijin adda sabreen din su. Kai ya jinjina kadan a ransa yana mamakin ina
kuma maamah ta samota?.

"Bari na kira maka ita" Ta fada da dan saurinta,can qasan ranta yana cike da
murna,yau kam taga wani daya danganci addansu.....ko gaisuwa ta aike mata tunda
yawan lokuta maamah tana cewa ta kira basa kusa. Wayar hannunta da maamah ta bata
kuwa da komai akai,hasalima suna waya kusan kullum da momma bahijja,amma batasan me
yasa number adda sabreen din kota kira sam sam bata shiga ba.




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 43



A step na biyu taga maamah din tana saukowa daga saman,hannunta cikin na
haneefa daketa bata labari.

"Yammatana ya akayi?" Ta tambayi huda tana dan sake mata murmushin nan nata da
kusan sun sana dashi.

"Baqo ne kikayi" Ta fada tana dan waiwayawa inda fu'ad ke zaune,hannunsa dauke da
remote yana sauya tasha,bawai kuma don yanason kallon bane aah....sai don kawai
bayason kallon fuskar maamah din sakamakon abubuwan daya tuna da suka motsa ranshi.

"Muje to" Ta amsata har qasan ranta tana jin dadin yadda huda din ta kasa gane
wanene. Tanason sanyata ta koma daki don kada suyi wata magana da zata fahimci
wayeshi a wajensu?,amma kuma ta rasa wanne uzurin zata bata tunda dai abinci zataci
akan dining. Uwa uba kowanne motsi nata da maganganunta tana yinsu ne a ankare,bata
bari tayi wani abu da zai sanya shakka a ransu ko ta gaza juyasu yadda takeso.

Tunda suka sauko din haneefa ta zubawa fu'ad ido. Tabbas shine mijin
adda sabreen,ta ganshi har sau biyu bata kuma mance ba,sannan bata sake ganinsa ba
sai yau.

Saman kujerar maamah ta zauna,haneefa ta zauna a gefanta still idanunta
suna kanshi ta kasa daukewa. Sanda ya gama gaida maamah din sai nasa idanun suka
sauka akan yarinyar. Kamanninta suka fusgi idanunshi sosai,ya sake ganin wata kamar
ta daban bayan wadda ya baro dazu tana me komawa falo bayan sun hada idanu.
Murmushi haneefa ta sakar masa sanda taga shima ya dan kafeta da ido. Ya murmusa
kadan tana shirin janye idanunsa sai yaga ta zame tana fadin

"Ina kwana mijin adda sabreen?". Kallon mamaki yake bibta dashi,mamakin da bai gama
sakinsa ba tace

"Sunana haneefa nice autan adda sabreen,'yar mitsisiyar dakinmu". Baisan ya akayi
murmushi ya ratsa miskilar fuskar nan tasa ya bayyana ba,ashe masu son sarautar
autancin suna da yawa. Yanayinta sak sai ya tuna masa da yanayin amna.

" Ya isa haka haneefa....kije kuyi break ko ki koma daki wajen nadra ku kalli
cartoon" Maamah tayi hanzarin dakatar da tattaunawar tasu. A nutse ya cira kansa
yana duban fuskar maamah din,haka kawai sai yaji yana da buqatar ci gaba da magana
da yarinyar.

"Qyaleta muyi hira maamah....she's very smart" Ya fada da wani irin tone a
muryarsa,wasu abubuwa da wani irin gudu suka fara bijiro masa,yayin da gumi ya fara
tsargawa maamah ta cikin rigarta.

Ta sani,tafi kowa ma samin haneefa she's very smart,fiye ma da
zatonta,wannan ya sanya tafi janta a jiki da kuma kaffa kaffa da ita.

"Indai surutun haneefa ne saika gaji dashi......ni kuma magana nakeso nayi
dakai,next time idan kazo sai kuyi hirar" Ta fada tana dan hade rai gami da gyara
zama.

Sake dubanta yayi a karo na biyu,abubuwa biyu suka hade masa waje
guda. Har yanzu dabi'ar nan tata tarashin son yara tana nan?,banbanci qarara me
kuma fadin gaske na farko tsakaninta da anni. Indai haka ne yara uku ne cikin
gidanma kenan?,akwai daya a cikin daki?. Me ya kaita dauko yara har uku?,ita da
basu dameta ba?. Meye abun damuwa don yana hira da yarinya qarama?.

Agogonsa ya kalla,sai ya maida dubansa ga fuskarta.

"Ba damuwa ai,yau muna da enough time sama da kullum". Kafin ya sake cewa wani abu
haneefa tace

" Zaka kaini naga adda sabreen?......don Allah hamma kada kace aah" Ta fada tana
narke murya. Maganar taja hankalin huda dake saman dining,itama saita ajiye spoon
din abincin da takeci ta maido hankalinta kansu.

Gumin dake tsatsatsafowa maamah din ya sake yawaita,da sauri kamar
ana tankadata tace

"Aah fa haneefa......ni da kaina mukayi zan kaiku haka ne?".

"Eh amma har yanzu baki kaimu ba maamah,shi kuma hamma ma daga can yake ko?" Ta
maida tambayar kansa. Kansa ya gyada a nutse yana karantarta.

"Maamah ki barshi ya kaimu ko anjima ne,in yaso saimu dawo da kanmu" Huda itama ta
saka baki,don da gaske sunyi tsananin kewar sabreen din.

Sanda ta waiwaya da nufin yiwa huda din magana sai maganar fu'ad ta
dakatar da komai.

"Jeki dauki hularki kuzo muje nasa a ajiyeku" Yayi maganar kansa tsaye,maganar data
daki tsakiyar kan maamah da wani irin ba zata.

Har ga Allah kanshi tsaye ya fada kuma hankalinsa kwance,kawai dai a
cikin zuciyarsa ya dade da rashin aminta da kowanne motsi na maamah din. Bashi da
gamsuwa akan abubuwa da yawa sa suka shafeta,shi yasa a kusan komai idanu da
zuciyarsa suna akai.

Cikin qasa da minti uku sai gasu kowacce da mayafinta. Dab da zasu fita
daga falon ta kirayi sunan huda da yanayin da tunda hudan

Please Login or Register in order to submit comment