You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaman cin abincin
abban yayi dare da yawa,ba zata iya jiransa ba da wuri takeso ta kwanta.

Kallon kallo sukayi tsakanin maamah din da amna. A kallon farko ta
fahimci wacece duk da wannan shine karon farko da ta fara ganin yarinyar ido da
ido. Autar alhaji hamza kenan,yarinyar da ake gaya mata irin sabon dake tsakaninta
da fuad......yadda take ji dashi da yadda shima yake ji da ita

"Idan har kikayi da wasa kina zaune zakiji ance 'yar gida akayi.....wannan matar
zata aura masa autarta..... Kinga shikenan komai ya qarasa watsewa" Muryar hajja ta
dawo mata akai cikin tattaunawar da sukayi da hajjan a dazu dazu kan hanyarsu ta
dawowa gida.

"Ke amna......dubamin abbanku idan ya kammala,kice maza maza yayi baquwa"

"To" Ta fada tana ajiye plate din sannan ta miqe tana nufar qofar da zata sadata da
sassan abban nasu ba tare da tabi ta ainihin farfajiyar gidan ba. Tana tafe tana
waiwayen maamah,itama ta lura da hakan,sai taja wani tsaki me matuqar qarfi abinda
ya sanya amna din maida kanta tana yin gaba.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 58
___________________________
https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy


Assalamualaikum

Yar uwa kinason kiga kitchen dinki a cike da kayan amfani masu kyau da inganci amma
Kuma kina tunanin chake kudi kisaya a dunkule??
Koda yarinyace Dake da takusa aure kinason kifara Tara mata kayan kitchen??
To damuwarki tazo karshe Yar uwa kinzo inda za'a share Miki hawayenki *ALFAT
KITCHENUTENSILS* (Adashen Yar gata), sun shirya tsaf dan ganin sun sama Miki
ingantattu Kuma masu kargo Yan zamanin kayan kitchen.
Zaki dinga tura kudinki idan yakai wani minzali saiki karba duk abunda kikeso daide
kudinki.
Ba iya nan muka tsayaba, farashin kayanmu daban yake a ko ina.
Dannan link dinnan domin kisamu damar shiga group dinmu don zabar kayanda kikeso da
Kuma ganin yadda abubuwan suke kasancewa. Nagode

https://chat.whatsapp.com/D4mOQ8gmKb7EXZ2sNcmLdy
_________________________


Farfajiyar gidan ba kowa sai qofar dakin malam saidu da yake iya hangowa
wanda yake a bude. Juyawa yayi zuwa sassan da spare din famfo dake bawa shukokin
gidan ruwa yake,ya xame takalminsa,ya kuma xare agogon hannunsa ya jefa aljihu
sannan ya matsa ya kunnashi. Dukkan hannayensa ya tara yana kallon saukar ruwan,sai
yaji wasu kalamai suna dawo masa a ka

_"ka mutu mana......ai ba a kanka aka fara mutuwa ba,kuma ba'a kanka zaa daina
ba......talauci da fatara tafi mutuwarka yimin barazana......ta kuma fi mutuwarka
dagamin hankali"_

Wani abu yaji ya tsaye masa a tsakanin numfashinsa daya sanya ya cire
hannayensa daga famfon. Wasu daga kalaman maamah kenan a can shekarun baya a bakin
famfo tamkar irin haka,daidai sanda abban nasu yake daura alwalar sallar magariba.
Takalmansa kawai ya mayar yana jin bazai iya ci gaba da xama a cikin gidan ba. Ire
ire wadannan abubuwan da ba wanda ya sansu saishi,.....koda musaddiq
kuwa......suna sanyashi yana jin kamar numfashinsa zai fita a wasu lokutan.

"Ko buta zaa baka ranka ya dade" Muryar malam saidu ta ratsa kunnensa sanda yake
dab da qofa. Kansa kawai ya gyada masa yaja ya koma ya zauna,ba jimawa ya dawo da
butar,ya karba ya fara dora alwalar a gaggauce,ya gama ya bashi ya karba ya maidata
wajenta

"Zo muje malam said" Fu'ad ya fada yana ware hannun rigar sa.

Tare suka jera shida malam saidu din,duk da yadda yaso ya zuqe saboda
girmamawa,me sunan malam kuma yana daga bayansu kadan ta yadda bazaiji wani abu da
suke tattaunawa ba

"Magana zamuyi" Ya fada a nutsensa

"To....to" Ya fadi da hanzari

"Tambayoyi ne amma sai bayan mun idar da sallah zan saurari amsoshinsu"

"To ba laifi ai" Ya amsa masa,don ya saba lokaci lokaci dama yakan masa tambayoyi
game da gidan ya kuma buqaci amsarsu.

"Waccan matar da suka shigo da hajiya meye sunanta?,wace ita a wajenta?,yaushe ka
fara ganinta a gidan?,sannan kamar sau nawa ta taba zuwa ko take zuwa?,ita kadai ce
koda wasu?,tana dadewa cikin gidan?,suna yawan fita tare ko aah" Yakai qarshen
dukkanin tambayoyin nasa sanda suka kai bakin masallacin,don haka yayi shuru yana
adduar shiga masallaci a madadin tarin tambayoyin.


"Lallai na sake yarda da maganar bokan can.....lallai akwai aiki qwarai akan
yaronkin nan" Hajja ta fada duk da nata yaron da matarsa data shanya a waje kowanne
cikin motarshi yana jiran fitowarta.

Labba maamah ta cije kadan sannan ta saki sanda take maida riga maras
nauyi a jikinta

"Ni kuma cewa nayi miki zan qyale wannan aikin ya cimmani?,na zuba idanu naga iya
gudun ruwansa na yau kawai......amma duk abinda yakai gobe zakiji kirana......a
gobe nakeso mu koma a fara aikinnan"

"Ai da zafi zafi akan bugi qarfe....." Hajjan ta fadi zuciyarta na saqa mata
abubuwa masu yawa.

Har bakin gate din farko ta tako tana yiwa qawartata godiya da ban
gajiya. A nan suka gaisa da yahaya da matarsa. Yadda ta samesu a jere kowanne da
mota yana jiran dakon fitowar hajjan ba tare daya isa yabar wajen ba ba bisa
umarninta ba ya sake ninka kwadayinta itama na kaiwa wannan bigiren,sai taji kamar
ta jawo wadannan kwanakin da tayi imanin suna dab da zuwa......ranar ea zata nunawa
aminatu da hamza cewa ruwa ba sa'an kwando bane.....hakanan koda giwa ta fadi tafi
qarfin wawa.

Haka siddan?,daga maqotaka?,ba sidi ba sadada a kama mata yara a musu
muguwar mallaka?,bayan ko sanda ta tafinma suna da wayon da zasu iya kula da
kansu?. Da wannan qananun mitocin ta isa cikin gida.

Ya kusa minti ashirin yana fuskantar gate din gidan,harde da
hannayensa kawai yana duban qofar kwanyarsa tana digesting maganganun da sukayi da
malam saidu daga hanyar masallaci zuwa dawowarsu. Baisan a wanne matsayi zai ajjiye
maamah din ba.....karo na uku da wani abu ya sanya yake tunanin ANYA ITA DINCE TA
HAIFESU?,anya ita din UWACE?,akwai zuciya irin ta uwaye a qirjinta kuwa?. Me yasa
kullum DUNIYA itace a gabanta sama da komai?,yayi tunanin shi da kowa ma zata canza
ko kuma ta canza din.....amma sai kuma akasin tunaninsu ya biyo baya.....akasin
tunanin da shi kadai gani na zuciya da lura da bin takunta sannu a hankali suke
karanta masa komai a kanta....karatun da idanuwa kadai sunyi kadan su iya fahimta
ko ganeshi.

Hannayensa ya sauke jikinsa a mugun mace,baya jin zai iya komawa cikin
gidan nan,idanma yace zai koma din abinda zai wanzu tsakaninshi da ita bame dadi
bane. Ko haduwarsu na 'yan mintuna kadai ya sake wani karatun. Ya dawo
lafiya?,wacce nasara ko qalubale ya riska?,duka ba damuwarta bane......damuwarta
shine KUDI.....me yasa bai turo ba?. Abu guda daya da bai taba faruwa tsakaninshi
da anni ko abba ba......basu taba neman anini taro ko sisi daga hannunshi ba.....a
hakan take neman kudin da zata rabashi da Alhaji hamza da aminatu?,mutanen da su
suka bashi RUHI na rayuwa da yake yawo a jikinsa a yanzu?.

Kansa ne yaji ya sara,sai ya sake qara azamar barin qofar gidan ya
juya zuwa nasu gidan. Gidan da a baya shine gidan maqota a wajensu amma a yanzun
basu da gidan daya kaishi.

Tun a gate ya sallami kowa,ya gaya musu da wuri zai kwanta don gobe
zasu fita da wuri,duk da baida yaqinin goben a yadda zai tashi saboda wani
nannauyan ciwon kai daya saukar masa yanzu yanzu.

Tun bai qarasa sassansa ba ya kashe duka wayoyinsa,yabi ta qofar
baya don bayason kowa yasan ya shigo din ya wuce sassansa.

Bai kunna kowanne fitila na sassansa da zai bada alamar yana ciki ba,sai
ya wuce a hankali kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki zuwa study room dinsa,ya
tura qofar ya shiga ya maida ya rufe.

Zaune kawai yayi saman sofa idanunshi a kulle,yayi nisan nazarin da shi
kansa baisan wane zare a tunanikansa zai kama ba. Abu daya ne da yafi daure masa
kai da dagula masa lissafi,qoqarin da takeyi da gaske na sai ta raba
tsakaninsu,indai haka ne wannan fitar tasu tana da alaqa da qudurinta.....indai
haka ne kudin da take nema lallai yana da alaqa da qudurinta......indai kuma haka
ne tabbas wannan BAQUWAR FUSKAR akwai tata rawar cikin mission din......duk da
yasan wannan din tsohon quduri ne dake ranta.....amma dukkan alamu sun nuna ta samu
MAKAMASHI.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 59
Shuru ne ya biyo baya tsakaninsu,babu wanda yace da dan uwansa komai
tsakanin ita da anni din. Daga yanayin tsaiwarta da yadda take bin komai da wani
irin kallo ta tabbatar ba alkhairi bane ya kawota,don haka taci gaba da abinda
takeyi din ba tare data ce komai da ita ba.

Baifi minti biyu ba kacal sai ga amna ta dawo

"Yace gashi nan...." Ta bata amsa tana sake binta da kallo tamkar a tsorace,sannan
ta qarasa ta dauki plate dinta ta koma kusa da annin ta naniqe ta zauna tana ci
gaba da satar kallon maamah din.

Da sallama ya shigo falon cike da kamalar nan tasa dake shimfide saman
fuskarsa,sanye yake da jallabiyya ruwan qasa,kansa sanye da qaramar hula tashi ka
fiya naci.

Amna da anni ne suka amsa sallamar tashi,yayin da maamah ta dubeshi kadan
kafin ta dauke kanta

"Mariya ce?,....bismillah......zauna mana" Ya fada yana zama kujerar dake daura
data anni. Kamar tace ba zata zauna ba,to amma kuma zaman yafi kamata tayin,don
tanason daga qarshe ta gasa masa maganganun da indai ya haifu zai fara janye
jikinsa daga dukkan wata mu'amala ta fu'ad dama rayuwarsa gaba daya,yabar mata
'ya'yanta kamar yadda kowacce uwa keda iko da nata yaran.

"Muna lafiya.....ina fata kuma lafiyar ko?" Gyara zamanta tayi sosai tana dora
qafarta daya kan daya,sannan ta saka idanunta sosai cikin nasa

"Wajenka nazo hamza" Ta fadi kanta tsaye,abinda yaja hankalin anni kenan tadan daga
kai ta dubeta,sai kuma ta saukar tana son kwashe hankalinta sam sam daga kansu.

"To ai gani.....Allah yasa lafiya" Fuska ta qanqance tana dubansa idanunta a ciki.

"Al'amarinku yana bani mamaki hamza yana kuma dauremin kai.........duk duniya ban
taba ganin inda ake irin haka ba sai a kanku,hankaka mai da dan wani
naka?......amma mu ajjiye wannan batun......tunda kun zab lallai sai na zama
maqasqanciya a gabanku akan 'ya'yana?......ba laifi don komai da ka gani a rayuwa
lokaci ne.....kuma iyaka gareshi......" Ta furta qasan ranta tana hangen iya adadin
lokacin da ya rage musu wanda alaqar uwa da uba zata wanzu a tsakaninsu.....da
tazarar lokacin da alaqar zata juye zuwa alaqar gagarumin abokin adawar da duk
duniya fuad din zai wayi gari bashi da abokin adawa irinsa. Burinta shine ta bude
idanu taba tsabtsar gaba da adawa mai qarfin gaske ta qullu tsakaninsu......irin
adawar da zata bawa kowa mamaki ta kuma shiga sahun tarihi......tabbas saita fanshe
dukkan wani baqinciki da suma cusa mata......hakanan ba zata qyale ba sai sunyi
aman duk wani da sukaci daga cikin arziqin fuad......koda kuwa wannan gidan da suke
ciki yana cikin jerin sahun mallakar fu'ad din.

"Wai nikam hamza.......ban sani ba ko cikin duhu ne a sannan?......hadaka da kuma
gamayya kukayi da ubansu fu'ad yayin samuwar cikinsu?,ma'ana tare kukamin cikinsu
ko kuwa?" Ba alhaji hamza kibiya kadai ba,hatta anni dake zaune daga gefe ba tare
da shiga shirginsu ba sai data cira kanta da sauri maganar tana dukanta

"Subhanallahi.......innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Alhj hamza ya fada zallan
mamaki yana saukar masa,idanunsa akan fuskar amna wadda ta yunqura tana miqewa ba
tare data tsaya daukan plate din abincin ba saboda yadda maganar ta girmimi
kunnuwanta.

"Mamaki kukayi?,to ai ba abun mamaki bane duba da yadda kuka qanqame min rayuwar
'ya'ya hamza" Ta kuma fadi cikin izza ba shakka ko d'ar a cikin idanunta.
"Mariya cikin hankalinki kike kuwa?" Anni ta gaza jurewa ta fada tana kafeta da
idanunta. Wurga kallonta tayi zuwa ga annin

"Kinga ina iface iface ne ko yage yage da zakiyimin wannan tambayar?"

"Shin mene marabar dambe da fada mariya?,ai hauka nau'i nau'i ne.....nakin ina
kyautata zaton ta wannan fuskar yazo"

"Kamar yadda cutarwarku tazo da sigar yaudara da damfara ba.......na rantse da
Allah a yau inda fu'ad yana a faqirinsa bashi da komai da tuni kun watsashi shi da
dan uwansa........."

"Kaman yadda zamantowarsu halittar da zaki iya mora ta sanya kika dawo cikin
rayuwarsu ba?....bayan kin watsar dasu a sannan kina zaton su din ba masu amfani
bane,nauyi ne kawai a wuyanki?". Anni ta maida mata amsa ta hanyar katse
numfashinta bacin rai yana fara nuna alamun tasiri cikin muryarta

"Ya isa aminatu......ban yarda ki sake cewa wani abu ba" Alhaji hamza ya fada yana
daga mata hannu. Ya gama karantar akwai abubuwa masu tarin yawa a bunne cikin
zuciyar maamah din,biye matan da annin zatayi shi xai bata damar furzar da
maganganun da idan suka qyaleta basu tanka mata ba har ta mutu saidai ta mutu dasu
a cikinta.

Dole ta ninke dubban maganganun da suke tsinkulinta a rai kawai don ta
bawa abban girmansa,amma bawai don abinda take da shirin furtawa itama ya qare
ba,ta kauda kai tana hadiye fushinta ba tare data sake jefa baki a maganarsu ba

"Ka gaya masa ya bini.....domin kuwa duk duniya ba wanda akace aljannarsa tana
qarqashin qafarta face ni.....komin lalacewata......ka taimaka ka sakar masa mara
ya rabu dani lafiya kaman yadda na tabbatar ka rabu da naka lafiya......ka shaida
masa yazo ya bani kudin dana buqata a hannunsa.......bawai alfarma nake nema
ba......ka gaya masa dole ne yayimin...." Tana kaiwa nan ta miqe tsam,idanunta akan
anni da tayi kaman batasan da wanzuwarta a wajen ba. Taso ace annin taci gaba da
ja,don tana da tarin maganganun da takeso ta amayar mata

"Wallahi duk d'an da ya hana uwarsa bacci.......shima bazai huta ba" Ta furta tana
juya hankali kwance tana barin falon.

Shuru ne ya biyo baya,duk kuwa da cewa ta gama ta kuma fita daga gidan
ma gaba daya

"Hasbunallahu wani'imal wakil" Alhaji hamza ya furta gauraye da wata ajiyar
numfashi me nauyi idanunsa na kallon waje daya.

Baisan wanne irin abune yake dawainiya da mariya ba......baisan kuma
wanne girman laifi sukayiwa rayuwarta haka da take musu kallon wasu manya manyan
abokan adawarta ba. Anni batace komai ba kaman yadda shima bai buqaci tace
ba,tanata qoqarin sarrafa bacin ranta da ganin ta hadiyeshi ba tare data barshi ya
mata tasiri ba

"Ina muhammadu?" Alhaji hamza yayi tambayar yana duban annin

"Bansan ina yayi ba.....mun rabu dashi a dazu kan zai shiga wajenta" Ta amsa masa a
taqaice. Karkacewa yayi ya ciro wayarsa daga aljihun jallabiyyarsa ya soma trying
number din fuad din.

Sosai yayi nisa cikin tunani,a haka idan ka ganshi zaka dauka bacci
yakeyi,saidai ba ko guda daya. Wasu mintina ne daketa wulga masa tsakanin bacci da
ido biyu wanda a ciki baisan ainihin abinda yakeyi ba
A silent wayar take,amma hasken da take fitarwa ya ratsa rufaffun
idanunsa a cikin duhun dakin.

Kamar bazai bude idanun nasa ba amma sai ya budesun a hankali yana
saukesu akan wayar. Yayi tsammanin ya kashe duka layukan,sai a sannan ya lura guda
daya ya kashe. Sunan daya gani saman wayar ya sanyashi sauke qafafunsa a hankali
yana maida hankalinsa a kanta,ya miqa hannu ya daukota daga inda take ajiye yana
qoqarin dagawa.

Sallama yayi amma muryarshi ta maqale,yadanyi gyaran murya sanda yajiyo
muryar abban yana masa sallama

"Ina ka shiga ne?" Alhaji hamza ya tambayeshi

"Ina cikin gida abba"

"To fito......inason ganinka.....ka sameni falon anninka"

"To abba" Ya amsa masa a ladabce. Remote ya laluba ya dauko ba tare daya tashi a
gun ba ya maida hasken dakin. Take yayi tarwai da haske kaman yadda ainihin dakin
yake

"Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla.....wa'anta taj'alil hazna iza shi'ita
sahla" Ya furta muryarsa can qasa,yana jinsa gaba daya ba kuzari,tun daga zuciyarsa
har zuwa gangar jikinsa.

Bai wani bata lokaci ba ya sauya kayan jikinsa sannan ya wuce sassan
annin. Sallama yayi hankalinsa na kaiwa fuskar anni. Tun bai zauna ba jikinsa ya
bashi akwai wani abu,don ba kasafai kake ganin fuskar annin a haka ba. A nutse ya
qarasa shiga ciki,kai tsaye kuma ya nufi inda Alhaji hamza yake,wanda bai motsa ba
daga wajen tunda maamah din ta fita ta barsu.

"Bismillah.....zauna" Alhaji hamza din ya masa nuni da kujerar dake kusa dashi.
Sanda ya zauna din ita kuma anni ta miqe da zummar barin wajen,abban ya maida
dubanshi kanta

"Zama kema zakiyi......ina zakije?" Duban abban tayi,kaman zatayi magana sai kuma
ta fasa,ta koma ta zauna ba tare data sake cewa komai ba.

"Muhammadu" Abba ya kira sunanshi kai tsaye,abinda ba kasafai hakan ke kasancewa
ba. Mamakin ya hanashi amsawa saidai ya daga kai kawai yana duban abban.

"Muhammadu ya ina yabonka sallah zaka kasa alwala?" Abban ya sake fada idanunsa
still akan fu'ad din,tausayinsa kuma yana ratsa zuciyar abban.

"Abba....." Fu'ad ya motsa labbansa a hankali da zummar yin magana

"Me dame mariya tace maka tana da buqata wanda bakayi mata ba?" Ya masa tambayar
Kai tsaye don sauqaqe masa wahalar tunani.

"Abba.....ba wani nauyi ko haqqi daya kamata na bawa maamah wanda bana bata
shi......bana tunanin akwai wani abu da ya zama nauyi ko haqqi da ubangiji ya
doramin wanda na gaza dauke mata shi". Har cikin zuciyarsa abban ya gamsu da
wannan,saboda shi kansa ganau ne bawai jiyau ba akan hakan

"Na sani Muhammadu......amma don me yasa idan tana da buqatar kudi daga hannunka
kake hana mata?". Sam baima kawo wannan zancan bane,sai ya sauke boyayyar ajiyar
zuciya yana sauke kanshi qasa.
Rashin amsawarsa ya bawa abba amsar tambayarshi

"Me yasa kusan ko yaushe matsalarka da ita akan tana neman kudi ne ka hanata?,bayan
Allah yayi maka wadatar da zaka iya bata ko nawa ne Muhammadu?" Ya qarashe maganar
ta sigar tambaya idanunsa a kanshi,can qasan ransa yana mamakin abinda ke kawo musu
matsala akan abinda yasan ya jima da fin qarfinsa. Km

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 60



"Ka sani cewa......duk d'a aljannarsa tana qarqashin qafar iyayensa?,kuma haramunne
jayayya dasu bare su buqaci abu aqi ayi musu?"

"Na sani abba.......amma bazan iya bawa maamah ko sisi ba". Sosai maganar ta bawa
abban mamaki,har anni dake zaune daga gefe itama ta daga kai tana kalleshi

"Akwai abubuwa masu yawan da baka gama saninsu ba abba akan maamah......akwai
boyayyun sirrikan dana ajewa cikina abba.......akwai wasu abubuwa masu yawa wadanda
ba zasu fadu ba......amma koma meye cinta shanta lafiyarta dama suturarta wani abu
ne da bazan taba iya hana mata su ba ko don albarkacin haihuwa da Allah ya
bata........amma batun kudi abba........bazan iya bata ba"

"Dalili?,dalili nakeso naji Muhammadu" Abba ya sake tambaya cikin tsananin mamaki.
Bai taba umartarsa da abu ba ya saba.....sai gashi s yau yana qoqarin bijire
masa.......tabbacin akwai wani qaqqarfan dalili da kuma hujja kenan

"Abba...." Ya kirayi sunansa yana jin nauyin abinda zai furta din. Shurunsa ba
abinda zai harfa tsakaninsa dashi sai gurguwar fahimta,bayaninsa din kuma bawai abu
bane me dadin ji ko sauraro ba.

"Kasani Muhammadu.....koda baka bayar ba ni zan dauka na bata da kaina"

"Zan bayar abba.....zan bata amma bawai don zuciyata tana so ba......"

"Zuwa yaushe kenan?" Ya sake tambayar sa

"Zan yiwa sadiq magana,zai saka mata"

"Kirashi yanzu yanzu" Ya sake bashi umarni kai tsaye. Dole ya fidda waya ya turawa
sadiq din saqon umarnin fidda kudaden,sannan ya aje wayar yana duban abban

"Zai sanya mata in sha Allahu". Ajiyar zuciya abban ya sauke. Shi kansa yasan akwai
qalubale masu tarin yawa cikin rayuwarsa,to amma ko meye zaiyi yana yine saboda
kyautatuwar rayuwa da kuma gobensu.

Kamar yadda ya saba lokaci bayan lokaci baya gajiya da yi musu nasiha
dukkaninsu,yanzunma nasihar ce dai yayi masa.

Haka kawai sanda yake barin falon yaji hankalinsa bai kwanta ba. Muddin
maamah tazo gidan to ya tabbatar akwai wani abu maras dadi daya biyo baya. Ko mene
kuma ya farun yasan babu me gaya masa cikin gidan,daga amna sai musaddiq wanda baya
gidan.
Yana takawa a farfajiyar gidan yana lalubar number amna din. Bugu daya
ta daga tana amsa sallama a nutse

"Fito waje inason magana dake"

"To hamma" Ta amsa masa tana sauke plate din hannunta data gagara cin abincin ciki.
Wayar tabi da kallo har yanzu muryar matar tana amsa kuwwa a kunnenta. Maganganunta
sun girmi kunnuwanta,batasan komai a kanta ba amma tana ganin rashin kirki qarara
daga dukkan wani motsi nata.

A tsaye ta sameshi idanunsa saman qananun shukokin dake bawa wajen
iska me kyau da yanayi me dadi

"Zauna" Yace da ita yana nuna mata kujerar dake gabansa tare da qoqarin karantar
fuskarta. Ba musu din ta zauna tana jin jikinta yana qara sanyaya daga kallon da
taga yana yi mata

"Akwai baquwar da tazo gidan nan dazun?" Ya tambayeta yana kallon tsakiyar
idanunta. Kallonsa itama tayi sai tayi qasa da kanta tana tuna gargadin da anni
tayi mata

"Ba ruwanki da abinda tazo ta fadi,wannan ba abinda ya shafeki bane.....ba'a gaban
kowa kuma akayi ba saike kadai...... Kada na soma jin zancan nan ya fita" Gargadin
annin kenan bayan ta bar falon ta isketa a kitchen.

"Ehnnnn......kina nan sanda ta shigo na tabbatar......akwai wasu abubuwa data cewa
anni da abba?" Ya sake tambayarta yana kallon fuskarta. Ba zata iya kallonsa kuma
tayi masa qarya ba......hakanan ba zata iya saba maganar anni ba,don haka ta zabi
sunkuyar da kanta ta kuma girgiza masa kai. Qaramin murmushi ne ya subuce masa
wanda ba komai cikinsa sai bacin rai

"When kika fara yiwa hamma qarya amna?" Tambayar tasa saita rudata gaba daya,taji
bata da sauran zabi illa ta shaida masa gaskiya.

Tambayar farkon data jefawa abban ita ta sanya fuad jan kujera shima ya
zauna wani nauyi yana saukar masa. Ya ilahi.....wannan wacce irin jarabawa ce?,me
yasa UWA take jin tasu jarabawar rayuwar?.

"Tashi kije" Ya bata umarnin daya sanyata miqewa da sauri tana barin wajen.

Tafin hannunsa ya sanya yadan daki goshinsa yana lumshe ido. A mizanin
hankali da tunani da sanin ya kamata......yayi zaton maamah zata kasance ne cikin
sahun farko na mutanen da ko kansu sukan sanya a gaba suka yanka ba zata ce komai
ba.

****A hankali take takawa cikin layin zuciyarta na bugawa a hankali a hankali.
Bugun zuciyartata ne batasan meye ainihin dalilin faruwarsa ba. Tsoron ganinsa
takeyi ko kuma shauqin ganin nasa?.

Tun daga wancan ranar daya aike mata wasiqa ta qarshe bata sake jinsa
ko kuma ganin motsinsa ba,har kawo yau da suke shirin cinye satin gab daya a kuma
shiga sabon sati.

"Assalamu alaikum" Sautin sallamar daya sanya zuciyarta wani irinn bugawa ta ba
zata,mamaki kuma da tsoro suka hanata amsawa saboda yadda taji alamun muryarta a
shaqe take. Kasa waiwayawa tayi har zuwa sanda ya tako yana cimmata a inda take,ya
zagaya kuma yana yiwa kansa matsaya a gabanta dab da ita. Yanayin kallon daya
rutsata dashi ya hanata janyewa baya kaman yadda takeyi a duk sanda ya tsaya kusa
da ita kamar haka
"Banga alamar kinyi kewata ba......inacan soyayyarki zata kasheni?" Ya furta yana
karyar da wuya tare da komawa kalar tausayi ainun.

Idanunta ta fiddo waje tana dubansa

"Me ya sameka?" Ta samu bakinta da subucewa gami da tambayarsa kai tsaye.

"Ciwon sonki" Ya fada wani mayaudarin murmushi yana subuce masa. Nasararsa yake
hange muraran daga idanun yarinyar,ya tabbatar yana dab da cika burinsa......yana
kuma gab da daukan fansa.

Wata ajiyar zuciya taja tana sauke numfashi

"Bakiyi kewata ba huda sam sam" Ya sake fadi yana kalmashe wuya idanunsa cikin
nata,yanason ya sake dasa mata dafin da zaiyi wahalar gogewa daga ranta. Yanason ya
cimmata sosai,ya kuma nutsar da ita cikin tafkin qaunarsa fiye da yadda yayarta ta
jefa masa qugiyar da har yanzu ya gaza zameta daga ruhinsa. Baya jin akwai wata
mace da zata iya kashe masa

Please Login or Register in order to submit comment