You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Uwa uba
akwai tasiri na girman kai da rashin tsoro tare da ita,yanaso yaga ya zatayi
handling wadannan attitude guda biyun da wadannan shekarun nata?.

Kaman zaiyi magana sai wayarsa ta dauki tsuwwa,manhajar da yakanyi
amfani da ita wasu lokuta da zata gaya masa cikakken sunan wanda ke kiransa koda
bashi da number wayarsa ta karanto masa sunan fareeda Khaleed mustapha. Kusan a
tare suka kalli wayar shi da ita,a nutse ya cire hannunsa ya kashe wayar gaba daya
bayan yayi rejecting call din,amfanin manhajar kenan ta gaya masa wanda ke
kira,basai ya saki aikinsa ya dauka ba ya zamana me kira baida wani muhimmanci har
haka,saboda mutum ne shi mai darajta lokaci.

Agogo ya kalla sannan a nutse ya maida dubanshi kanta bayan ya sauke
qafafunsa duka qasa,abinda ya sanyata sake kame ganinta gudun kada idanun nata su
gano mata abinda yafi qarfinta,don ta lura kamar bayajin nauyin zamansa a haka.

"Kin tsallake iyakarki,kin shigomin part ba tare da Neman izini ko sallama
ba......and kin tsaya kina ban labari akan abinda bai shafeni ba.......wai...." Ya
fada yana tsuke fuskarsa sosai gami da maida qafafunsa saman table sabanin dazu
dake kan sofa
"Meye amfanin zamanki a gidan nan?.. Kina zaton na kawoki ne don na killaceki
waje daya kiji dadin rayuwa?,ki samu tsaro kiji dadin ci gaba da qwamushe asusun
mutane?,ko na kawoki ne don kizo kicinye min abinci na?,ko kin dauka na daukoki ne
don wani abu daban?,thought ma dai nasan ba zaki taba mafarkin wannan shirmen ne
wato SO ya sanya na kawoki ba....." Wani radadi takeji yana taba zuciyarta,abu daya
da zata iya yabonsa akai takuma san ya qware akai shine baqar magana kamar tsohon
mahauci,idaninta da suka fara canza launi takai kansa,ya gyara zamanshi sosai yana
hade yatsun hannunsa guri daya yana maida dubansa kanta.

"Kina magana akan sharadi yarjejeniya da sauransu......for now ma yakamata kisan me
ya shigo dake cikin gidan nan.......Initially don ki gane me ake kira da
respect........attitude dinki su koma irin na kowanne mutum.....secondly
kuma..........ki maida min dukka kudina da kika debe.....don ban nema kudina saboda
mata irinku su mora ba......" Wani kallo harrr ta bishi dashi,sai ya daga dukka
girarsa sama

"Yes......duk wanda zayaci kudina to yana da cikakkiyar hujjar da zata bashi daman
cin in a polite way.......da naso a ranar da kika diba a ranar zan saka a kawomin
ke har nan..... " Idanu ta zubawa Kyakkywar fuskarsa yadda yake bayani a nutse
hankalinsa kwance. Ashe shi din ma mayen kudi ne?,kallon kitse akewa rogo?. Eh
tasan tabbas ta cire kudade masu nauyi da yawan da ita kanta sai data girgiza,amma
kuma bata dauka har xai sanya qulafucinsa akan kudin daya tsere musu ba har haka.

"Baki da hanyar da zaki biya Muhammad jadda kudinsa?......zan taimakeki tsill dai
don kada kiyi prison a banza.........daga yau ya daukeki aikin shara da gyara masa
bedroom da kuma wanke masa toilet dinsa......zan biyaki kaman yadda yake biyan
kowanni ma'aikaci dame aiki a qasansa.......but.....i will not pay you
anything.......zanyi writing down komai har ki kammala biyana" Yakai qarshen
maganar gaskiyar abinda yake fada tana fita daga cikin idanunsa. Soma tattare
takardunsa yayi

"You can go" Ya furta cikin halin ko in kula.

A lokacin tana jin kamar ta qarasa gabansa ta amayar masa da dukka
abinda ke zuciyarta,tana jin kamar ta isa gabansa ta nuna masa wace real
sabreen,amma kuma wani sashe na zuciyarta yana kwabarta tare da gaya mata any
mistake idan tayi itace a ciki.

"Ya soma cin abincinki shine abinda ya kamata ki damu dashi bawai maganganunsa
ba......if kikayi abinda zai sake sanya masa shakkan sakewa da gidan dukka
ayyukanki zasu koma baya.... Sisters dinki zasu ci gaba da zama qarqashin hadari"
Maganganun da suka fito daga qasan zuciyarta kenan,suka kuma sanyata tsaiwa cak
daga takun data fara don matsawa zuwa gareshi.

Remote din ya dauka ya bude mata qofar yana ci gaba da abinda yakeyi

"Hey" Taji ya sake fada sanda ta sanya qafarta daya a waje,saita dakata ba tare
data waiwayo ba

"Mind you....banason qazanta,i don't want it,ki kiyaye". Da sassarfa da kuma
hanzari ta soma sauka saga stairs din har kamar zata fadi. Kuka ne yakeson qwace
mata amma bataso yaji ko ya gani,don ta yiwa kanta alqawari ba zata taba bari yasan
lagonta ba.

Baqincikinta yadda ya fadi mata dukka maganar da ke ransa,nata zuciyar
da ruhi cike maqil da maganganu amma TARKON da take ciki yasa bazaiyuwu ta fiddasu
ba.
*_Washegari_*


Tun shida na safe zuwaira ke kai kawo tsakanin shiyyarsu zuwa ainihin
falon da kuma kitchen din. Jin shuru ba alamun tashi sai ta fara aikin gyaran dukka
falukan da kuma kitchen din. Duk wani motsi da zataji hankalinta yana kai,tanaso ta
samu cikakken bayani akan komai yadda zata zama cikakkiyar informer na maamah.
Tanason bata duk kalar bayanan da takeso don tana son ta doke matsayin hajja harira
wajen maamah. Ta kowacce fuska da kuma yanayi tanason ta taka matsayin da zata zama
aljihun daman maamah a sanda burin maamah ya cika din. Itama tata zuciyar da ruhin
cike suke da nata kalar burin da take fatan zuwan ranar wanzuwarsa.

Wani irin qarfi ta sanya ta danne zuciyarta ta fito shirya masa
breakfast,duk da asara akayi daren jiya na dukka girkin da sukayi,sai tashi tayi
tsakiyan dare ta kwashesu ta zuba a inda ta saba zubawa.

Yau din cikakkiyar shiga tayi,ta rufe jikinta sosai tunda ta fahimci
ba ita kadai bace cikin gidan. Idanunta duka sunyi nauyi saboda kuka da rashin
cikakken bacci. A hankali take ratsa falon hankalinta yana qofar kitchen din.

"Barka da fitowa ranki shi dade" Taso ta tsorata kadan,don gaba daya ta manta da
wata baba zuwaira a gidan. Ta sauke dubanta a kanta sanda zuwaira ke qare mata
kallon qwaqwaf. A jiya batayi cikakken bacci ba sai data gama fahimtar inda
kowannensu yake kwana ita dashi. A gaban idanunta ta sauko daga samanshi a gaggauce
cikin bacin rai ta fada dakinta,abincin dataxo ta kwashe kuma baici ba,a daren
itama bata kwanta ba ta sharhantawa maamah komai.

"Ya zama dole na matsa mata lamba ta yaudaroshi ya zama a tafin hannunta" Abinda
maamah ta furta kenan,tsoron taurin kai irin nasa yana damunta. Tasan halinsa da
kafiya akan abinda baida niyya baiyi masa ba......amma zata sake yin amfani da
qarfinta a matsayinta na uwa karo na biyu.

"Barka kade" Ta amsa mata a taqaice ba tare data sake dubanta ba tayi kitchen

"Nace ba,ba abinda za'ayi kuma?"

"Babu....kije saina nemeki" Ta amsa mata a taqaice,don kwata kwata batason doguwar
magana gaba daya. Da kallo zuwaira ta bita har ta shige kitchen din,sai ta saki
murmushi tana ji a ranta ya kamata taci tudu biyu fa......bangaren maamah din da
bangaren yarinyar.....abinda ta kwana kenan tana tunani akai,gwara tayi amfani da
damarta,ta yadda koda gaba kome ya faru zai zame mata ribar qafa,salon maganar nan
da hausawa kance idan tayi ruwa rijiya,idan kuma batayi ba masai.

Dukka 4glass stove gas din ta kunna kowanne ta dora abu akai. Da
zafi zafinta ta saka 'yar basirarta ta kammale breakfast din cikin taqaitaccen
lokaci,ta gyara inda zata gyara ta fara daukan luxury Warmers din tana jerasu saman
dining.

Cikin ginshira da wani irin tsanaki gami da nutsuwa yake saukowa daga
saman stairs din,kunnensa manne da Bluetooth yana amsa waya,lokaci guda kuma yana
qoqarin gyara tie dinsa.

Hankalinta yayi nisa sosai cikin duniyar tunani,fargaba kuma na sake
cikata kamar kullum na kada a sake tafka asara yaqi cin komai kamar kullum,asarar
da take sake kusantata da faduwarta da samun matsala a rayuwarta.

Tun daga nesan idanunshi suna kanta,duk da baiga fuskarta ba amma ya
gane itace. Sai ya dauke dubansa yana haurawa zuwa steps din ya wuce zuwa kitchen.
Qamshinsa kadai shi ya ankarar da ita,ta daga kanta tana bin bayansa da kallo
gabanta yana wani irin faduwa,cikin mutuwar jiki ta ajjiye spoons din hannunta taja
kujera daya tana jiran fitowarsa cike da hope.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 35


_Daga abdullahi dan abbas R.A yace,Lokacin da aliyyu R.A ya auri nana fadima,sai
manzon Allah S A W yace"ka bata wani abu(a matsayin sadakinta),sai sayyadina Aliyyu
yace "ba komai a wajena" Sai manzan Allah S A W yace "ina sulkenka?"_



35


Coffee ya hadawa kansa,yayi tsaye jikin kitchen cabinet yana kurba a
hankali. Kwanakin nan duka baici wani abincin arziqi ba,sai kame kame da cin
abincin waje,wanda yasan totally isn't safe musamman ga mutum sannanne irinsa da ta
kowacce fuska cikin barazana da qoqarin kawo musu hari ake ta duk wata siririyar
kafa da za'a samu dama. Iya lamarin maamah da yarinyar ya isa zama izina a
gareshi,abu a cikin gidan.... Amma kuma farautarka akeyi.

Sai yaji gaba daya coffee din ya fice masa a kai,yana qaramin tsaki
ya ajiye cup din,ya ciri paper towel ya goge lips dinsa duk da ba baci sukayi ba ya
fara takawa a nutse yana fita a kitchen din.

Sau daya tak ya kalleta ya dauke kansa,ya taka a nutse yana isa
gabanta. Tsaiwarsa ta sanyata daga kanta,akwai inches tsakaninsu amma tana jin
kamar ba wani gap daya rage musu. Idanunsa saman lips din nan nata da suke very
smooth,ba digon komai akai sai ainihin color dinsa. Smart key na qofarsa ya dora
saman table din,ya kuma harbasa gabanta. Ya motsa labbansa zaice wani abu wayarsa
ta fara fidda wani tattausan ring me kama da sarewa,irin ring din da zai iya
haifarwa da mutum karyewar zuciya musamman ga masu karyayyiyar zuciyar. Fareeda
Khaleed mustapha sunan wanda ke yunqurin samun sadarwa dashi kenan aka sanar
mishi. Maimaita kiran sunan me kiran wayar ta soma yi kamar ba zata dakata ba.
Saman kunnuwanta sunan ya sauka,irin sunan da taji a wancan daren. Iska ya furzar
daga bakinsa yana sauke numfashi,sannan yana qaramin tsaki gami da ciro wayar da
wani dan zafin nama yana yanke kiran ya jefata aljihun yana sake sakin tsakin. Baki
ta tabe qasa qasa tana kauda fuskarta wani sashen,can qasan zuciyarta kuwa gulma
take,tasan za'a rina.....koda dukka jikinta kunnuwa ne ba zata taba yarda mutum
kamar muhammad jadda bashi da kowa ba.....mutum kamar muhammad jadda baida
ajiyayyun 'yammata da yake debe kewarsa dasu ba......ba zata yiwa kanta qarya
ba,idan tace mummuna ne ko bai hadu ba tasan tabbas wannan din gundumemiyar qarya
ce ta zabgawa kanta......to kuwa tasan zai wahala a rasashi da wasu halaye da
sukayi kama da wannan. A iya rayuwarta.....a iya mazan data hadu dasu harda wadanda
basu kaishi bama,masu kudi sosai matasa masu jini a jika,taga dabi'u kala daban
daban da halayen da bata ma tsammaci ganinsu ba,yaga yadda matan aurensu suke ba
komai ba a wajensu......taga irin qalubalen da shuke fuskanta a tattare
dasu....matasan cikinsu harma da masu yawaitar shekaru,wannan abun ya sake cire
mata sha'awar abubuwan nan guda biyu a ranta SOYAYYA da kuma AURE. Gadai guda daya
nan ya cimmata,saidai tana da yaqinin ba zata bari yayi galaba a kanta ba,yayin da
take bawa kanta tabbacin tafi qarfin wata soyayya taci galaba a kanta,don idan ka
dauke soyayyar qannenta bata taba tsintar kanta cikin soyayyar komai ba,wannan
shine yake sake bata yaqini tabbaci da nutsuwan ba zata taba yin soyayya
ba....saidai ita a sota
(Nace uhmmm....maji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta). Idanunsa ya maida saman
fuskarta,a nutse ya fara magana kamar wanda ya hada jini da gidan sarauta.

"You can start your work today.......but......ya kamata ki sani,nasan komai da yake
every single room......sannan nasan place dinshi,so do your own business......kiyi
iya abinda akace kiyi" Daga haka sai ya juya a nutse don sauka a wajen,saidai kuma
muryar da yaji tana gaidashi ya sanyashi tsaiwa yana juyawa wajen.

Zuwaira ce a durqushe a wajen,da yanayin da yake tabbatar masa ba yanzu
yanzu ta shigo ba. Sunkuyar da kanta tayi sanda ya zube mata kaifafan idanun nan
nasa,yayi mata wani irin kwarjini da bata taba ganinsa idanun kowanne mahaluki ba
sai a kansa. Wannan kwarjinin nasa ya sanya suke qauracew waje duk sanda ya shigo
gaida maamah. Sosai goshinta ya soma tsatstsafo da gumi,tana ganin kamar a iya
kallonsa kadai zai iya bankado komai ya kuma fallasashi.

"Who are you?" Yayi tambayar kai tsaye ba wani wasa ko sassauci a muryarsa,abinda
ya sanya zuwaira ta ida rudewa,ga turancin daya jefeta dashi wanda ya saka a duhu

"Eh....na'ammmm.....eh"

"Wacece ke?" Ya maida mata tambayar da hausa. Caraf ta kama maganar tasa

"Nice zuwaira.....zuwaira ce,me aikin da hajiya maamah ta aiko don taya uwargida
sabgogi da hidimomin gida". Ta qarashe fada tana daddafe hannuwanta a qasa,saboda
ji tayi kamar zata fadi daga tsugunnen.

Hannayensa kawai ya zube a aljihun wandonsa yana ci gaba da
kallonta,yana kuma son ganin fuskarta sosai. Duk wani daya rabi maamah yana da
nashi question mark din a wajensa.....duk wani wanda maamah zatayi qoqarin hada
connection tsakaninsa dashi baida aminci ko nutsuwa kwata kwata dashi,don haka yake
sake shawarwarin qarawa musaddiq kwanakin zamansa a qasar da ya aikeshi ba tare da
wani qwaqwaran dalili ko kuma buqatar hakan ba.

Hannayensa nasa ya sauke ya soma takawa yana sauka daga wajen,zuwa
sannan qiris ya ragewa zuwaira ta saki fitsari a wando.

"Kada na sake ganin gilmawarki cikin gidan nan indai ina nan......duk ranar kuma da
kikayi sake hakan ya faru.....ki fara hada kayanki na barin gidan nan....basai nace
ba"

"In sha Allahu ranka ya dade,tuba nake" Ta fada dukka jikinta yana rawa.

Daga ita har sabreen ba wanda yacewa da dan uwansa komai. Kusan minti
biyar da fitarsa sannan ta tattara qarfinta ta miqe tana sake hawa steps din dining
da sabreen ke zaune akai. Fuskarta qunshe da munafukin murmushin nan ta soma
gaidata

"Barka da asuba ranki ya dade.....ashe har kin gama aikin?,ba zaki jira nazo
ba?,hidimar ai sai tayi miki yawa,da sai na rage miki ai.....iyaka idan na gama
abincin ki bada kalar maganin da za'a zuba a ciki......kedin abar tausayi ce ranki
ya dade,kullum addu'ata da fatana ki kubuta daga hannun hajiya mariya lafiya"
Zuwaira tayi maganar cikin matuqar sanyin muryar.....tsantsar alhini da kuma nuna
damuwa.

Tunda zuwaira ke maganganun nan a jejjere sabreen bata daga kai ta
kalleta ba sai da tazo gabar qarshen maganar tata. Kalmar tausayi data furta a
maganar nata yaja hankalin sabreen ya kuma tsaye mata a rai. Sosai ta zubawa
zuwaira idanu tana son tantance gaskiyar abinda ta fada,saidai kuma abun mamaki
haka kawai sai taji ta kasa gamsuwa da ita.

Boyayyen numfashi ta sauke,sannan ta tattara hankalinta a kanta tana
hade ranta tsaf

"Wannan duka ba huruminki bane.....kiyi abinda ya cancanci kiyi kawai" Sai ta miqe
daga saman kujerar tana niyyar tafiya. Da sauri zuwairan ba tare da ta ji ciwon
tsaidata a wata iyaka da tayi ba tace

"To ranki ya dade abincin fa?,yauma saidai a zubda?"

"Idan kina da buqatar ci kya iya ci ai" Ta amsa mata da gatse tana sauka daga step
din idanunta yana sauka kan laila dake shigowa parlor din.

Sanye take da robber gown wadda tabi kowanne shape na jikinta ta lafe
mata. Fuskar nan fes da kwalliya zaka rantse ba safiya bane ba. Ba komai a kanta
sai wani qaramin bandana da bai rufe komai a gashin kanta ba. Wani mahaukacin
tashin qamshi jikinta keyi,wanda turaren turare ne na musamman da aka tanada saboda
wani mutum na daban.

Duk da fuska ko kuma jikinta ba wata kwalliya.....amma haka kawai ta
fusgi hankalinta. Sassanyan kyan nan nata da baya buqatar kwalliya ko wani abu
makamancin haka yana nan shimgide saman fuskarta. Haka kawai taji ta muzanta duk da
kwalliyar dake jikinta,amma duk da haka sai taji ta raina kanta. Tashin farko wasu
kalmomi na hajja suka dawo mata fes cikin kwanya suka qara mata azama da qwarin
gwiwa. Muhammad jadda kawai take da buqatar gani,don haka taci gaba da shigowa
falon tana jin izza tare da fatan ko yaya ta gwadawa sabreen wani abu da zai sosa
ranta.

Kallo daya ta yiwa lailan ta watsar da ganinta a wajen,taci gaba da
wucewa ciki ba tare data damu da kallon qurillar da laila ke mata ba. Ita sam bata
ma dauketa a sunan damuwarta ba,damuwarta ta tsaya ne kan yadda yake neman maidata
boyi boyin qarfi da yaji. Ta share masa sassa ta hada da wankin bandakinsa dama
underwears dinsa,tana jin koda sama da qasa zasu hade ba zatayi wannan aikin ba.
Lumshe idanunta tayi tana qara jin takaici yana cikata. Bashi da masaniyar hatta da
girkin da take masa dole ce ta sanya take masa ba?,har wani qyashi da baqinciki ke
rufeta gami da kasalar bacin rai duk sanda ta tsinci kanta dumu dumu a kitchen tana
hidimar dafa masa abinci.

Dakinta kawai ta wuce bayan ta saqale masa key dinsa jikin qofarsa,tana
fatan ya dawo ya samu sassansa da muqullansa a inda ya barsu.

Dining din laila ta wuce kai tsaye tana wani taku kai kace itace
matar gidan,ranta ya cika maqil da kishi da hassadar sabreen din. Ko daga nesa ka
hangosu sabreen din ta fita quruciya.......amma miskilancin yarinyar da shegen
girman kanta mamaki yake bata. Bata taba mata kallo biyu ba....kai zata ma iya
rantsewa sau daya ta mata nutsasten kallon cikin idanu Randa taso blocking mata
hanya. So take ko yaya taga wutar kishinta a idanunta,to amma kullum suka hadu tana
yin kamar babu aka kawo gidan aka ajiye ba dan adam ba.

"Ma aka dafa?" Ta tambayi zuwaira Kai tsaye tana latsa wayarta sanda zuwaira ta
kusa gama kwashe warmers din.
"Sai yanzu Allah yayimin tashi,don haka saiki jira na gama da aikin matar gidan
tukunna" Zuwaira ta gaya mata gatse gatse gami da satar idanunta ta gasa mata
harara. Kullum ta tuna warning da kuma jan kunnenta akan ta yiwa yarinyar biyayya
da hajiya mariya da hajja uwar yarinyar suka mata akan tabi yarinyar sau da qafa
bama matar gidan ba.....sai taji kamar ta zabge yarinyar da mari.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 36


_An karbo daga abu hurairah Allah ya qara yarda dashi yace,manzon Allah S A W
yace,idan miji ya kira matarsa zuwa shimfida taqi zuwa,mala'iku zasuyita la'antarta
har gari ya waye_

*_qarqashin wannan hadisin akwai qarin haske,idan a wannan qin da tayi kuma ta samu
ciki koda ta rasu wajen haihuwa wasu malamai suna ganin bata samu wannan shahadar
da mace me naquda ke samu ba idan ta rasu_*



36


"Ki gaggauta da Allah.... Am starving,ko ki bani wannan da kike debewa
in fara dashi"

"Sannu akuya......" Zuwaira ta fada a ranta,amma a fili saita ajiye mata warmer din
tana cewa

"Zaki iya ci mana.....amma kafin kicin ki fara sanarwa tsohuwarki gudun maida laifi
a kaina" Ta fada dadan zafin rai. Haka kawai sai laila tasha jinin jikinta,don haka
ta miqe tana sauka daga wajen

"Fresh nakeso.....kada ki wuce minti talatin" Bata ma iya amsa mata ba ta dauke
ragowar warmer din tana wucewa kitchen din gami da jan tsaki qasa qasa.

Tafiyar minti arba'in da shida ta sadashi da mansion House din alhaji
hamza kibiya. A qofar tafkeken gate din dake qara nuna alfarmar dake cikin gidan
motocin suka tsaya bisa umarninsa,don yanaso ne ya gaida anni ya fito......ya kuma
haida maamah din sannan ya wuce office din. Akwai cushewar ayyuka sosai yau din
bisa schedule din da saddiq dinsa na yau da saddiq ya tura masa tun jiya da
dare,wannan ya sanyashi fita da wuri. Wani irin qarin investors suketa samu a dukka
kamfanoninsu,duk da yana yin komai bisa kula don ya tabbatar akwai mutanen dake
bibiye dashi,kuma nasararsa a wancan lokacin yayi imanin ta tarwatsa musu dukka
shirinsu..... Faduwarsu kuwa da shurunsu yayi amannar bawai suna nufin komai ya
wuce bane.

Gidane dake cike da tsari,da kuma kusan duk wanda yake gidan bisa
tsari da sanin ya kamata yake zaune. Kowa yasan aikinsa,tun daga kan security
guards da sauran masu aiki na cikin gida dama farfajiyar gidan,hakanan bayin Allah
da suke daukan nauyi dake wani sashe daban na cikin gidan me kama da qaramin estate
kowa bisa tsari da sanin ya kamata yake.

Duk girman gidan ko.ina fes yake da wani irin tsafta da qamshi. Ya zuqi
qamshin har cikin hunhunsa sanda yake zama saman sofas na qaramin falon anni da
mutanen da suke mafi kusanci da ita ne kadai ke iya haurowa har nan. Ba abinda ke
saukar masa da nutsuwa kasala gami da tayar masa da wnai Tsunammen feelings irin
qamshi. Duk sonshi da qamshin wannan ya sanyashi haqura dashi kan bedsheets da
duvet nashi da pillow,wanda muddin ya kwanta akai da qamshi irin wannan to zai
wahala bai kwana cikin wahala ba,ko kuma ya tashi da mafarkin da zai wajabta masa
wanka kafin yakai ga sallar asuba.

Normally yanaso kowanne kusurwa na inda zaiyi mu'amala dashi ya zama
kaman haka,sai ya lumshe idonsa kafin ya budesu sanda yaji sallamar anni.

Da dogon hijabin nan nata har qasa ta shigo wanda ke alamta masa
sallar walaha take ya tasota. A wajenta ya koyi sallar walaha,tun yana yi yana
fashi batabi jininsa ba har takai ya saba,ko a ina yake,kome kuma yake yi sai ya
katseshi yayi,saidai idan abubuwan sunsha kansa ko sunfi qarfinsa ba yadda zaiyi.

Fuskarta shimfide da kararramammen murmushin nan nata ta qarasa
shigowa,tayi bismillaha tana zama saman kujerar abinda ya sanyashi zamowa daga
samanta yana gaidata.

"Tashi ka koma ka zauna" Tace dashi don ba kasafai yake iya zama saman kujerar ba
idan suna kai ko ita ko abbansu,harma da maamah din kanta.

Kai ya girgiza yana tanqwashe qafafunsa saman carpet kamar qaramin
yaro

"Nan ma ya isa anni.....akwai kunun tsamiya?" Kai tadan daga tana dubansa. Batayi
tsammanin zai qara tambayar abinci ba sam sam daga wajenta,don kuwa a yanzun
magidanci sunansa,saidai kuma ta masa uzuri,don tunda akayi auren bai taba neman
komai ba,don haka tace dashi

"Akwai.....kasan dole ne kullum sai an yiwa abbanku.....har yanzu gargajiya taqi
barinku,bari nasa a kawo maka" Ta fada da murmushi. Shima tsadajjen murmushin nan
da kusan annin tafi kowa ganinsa a duniya ya sake


"Anni akwai abubuwa masu muhimmanci me tarin yawa a gero,inda mutane sunsan meye
gero anni da kusan duka mun koma cinsa". Murmushi ta kuma yi tana miqewa gaba daya

"Gaskiya mana naga kun qulla kyakkyawar alaqa da fura.....nikam wannan traditional
doctor din naka ya sake canzaka gaba daya" Murmushi kawai ya saki,shi kansa ya sani
kalar cimarsa ba iri daya bace data kowa,sau tari a wani taro ko a sanda ya buqaci
cin abinci da baqinsa na Africa ko nan Nigerian,sukan cika da mamaki idan sunga
kalar abincin da yake ci.

Da kanta annin ta shiryo komai saman tray,harda qarin lafiyayyen qosai
da kuma farfesun kan rago da yasha kayan qamshi tafarnuwa da wadatacciyar albasa.
Akwai abinda takeson ta karanta a tattare dashi a fakaice a matsayinta na uwa bawai
kai tsaye ba. Tun daga ranar da amna ta gaya mata zaunuwar zuwaira a gidan ko sau
daya bata taba hutawa da tunani ba. Ta kasa aminta hakanan ta kasa gamsuwa. Fu'ad
dan maamah ne halak malak,duniya ma ta shaida hakan,saidai tana jin bai kyautu
tabar mata rayuwarsa ba,rayuwar da aka fafata aka sha fama kafin fara daidaituwar
komai a cikinta. Allah shine ya raya muhammad fu'ad din,amma kuma itace sila,tasha
fama qwarai da gaske,faman da har batason tunawa,faman da shine ya zama silar
shaquwa tsakaninsu me yawan gaske. Har batason tuna wahalar da tasha dashi

Please Login or Register in order to submit comment