You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mintuna biyar din data tabbatar ko
dafa ruwan za'ayi wadannan mintunan sun wadatar. Kujerar da take kai din sai
takejin kamar ta mata nisa da bakin qofar. Miqewa tayi tsam tana canza kujera mafi
kusa da bakin kitchen din tana sauke wani zazzafan huci,tanata qoqarin hana
zuciyarta ci gaba da hasashen abubuwa daban daban da zuciyarta ke saqa mata.

"Da gaske yarinyar nan 'yar bariki ce.....da gaske bariki takeson gwadamin?.....wai
uban me yakeyi a kitchen din?,da gayya ta tsareshi kenan don ta gwada mata
iyakarta?" Wadannan tunane tunane su sukaci gaba da kai kawo tsakanin zuciya da
kwanyar maamah. Sake matsawa tayi kujera ta gaba tana sake zurfafa jinta da kuma
idanunta akan qofar kitchen din,amma bata iya jiyo komai,abinda ya sake assasa
baqincikinta. Wai wanne tsautsayi ne ya hanata tsaiwa a nigeria tasa ayiwa fu'ad da
sabreen din mummunan farraqu?,irin farraqun da ko me irin sunanta zai tsani
ballantana ita da kanta.
Maida idanunta tayi ga agogo tana duba adadin lokutan da aka shafe. To
badai dafa ruwan dumi ba....ko dan mutum za'a dafa a wannan gabar yaci ace ya dahu
wani irin tsalle zuciyar ta keyi,wani sashe na zuciyar na bata shawarar shiga
kitchen din da kanta taga qaryar rashin kunya. Sau uku tana miqewa sai ta koma ta
zauna cikin shakka da kokwanto. Batasan ya zataji ba idan taje ta tadda daidai da
abinda tunaninta yake bata. Qaqqarfan motsin da taji daga kitchen din ya qarasa
tunzura zuciyarta,ta miqe da wani irin gaggawa ta durfafi kitchen din.

Baya fahimtar komai sai sabreen din dake gabansa......kowanne sashe na
jikinsa karbar saqo yakeyi iyaka,baisan wanne irin kebantaccen shauqi yakeji haka a
kanta ba. A yadda yakejin kansa a lokacin yana jin kamar duniyar ma tayi musu kadan
shi da ita. Ya sake zurfafa harshensa cikin bakinta yana sake zare mata duk wani
kuzari nata. Qwace masa numfashinsa ya dinga yi yana kamoshi da qyar,a daidai
wannan lokacin maamah ta qaraso bakin qofar kitchen din cikin zaton zata samesu
tsakiya ko qarshen kitchen din.

Tamkar an juya kwanyarta daga sama zuwa qasa haka taji. Wani irin shock
jikinta ya dauka na tsakanin mamaki da kuma tsoro,jikinta da qafafunta gaba daya
suka dauki kyarma,saita juya da matsanancin sauri tana jin juwa na shirin kayar da
ita. Tana juyawa yana zare bakinsa a nata,baiganta duka ba,amma yaga wani sashe na
rigarta. Zazzafan numfashi ya furzar yana cure hannun sabreen dukka cikin kasa hadi
da kifi fuskarsa a bayan hannuwan nasu yana qoqarin daidaita numfashinsa.

"Maamah" Ya fada can qasan ranshi,kwata kwata ya manta ya barta a parlor,amma yayi
tsammanin yadda anni ta wuce daki itama dakin ta nufa. Daga fuskarsa yayi data
sauya launi yana zubesu saman tata fuskar. Fuskarta ta kawar tana qoqarin dauke
hawayen dake shirin zubo mata. Ya gansu,don haka ya sanya hannu da nufin dawo da
fuskarta saitin nasa,saidai ta rigashi ta hanyar ture hannuwan nasa. A wahalce a
kuma kasalance yace.

"Na jima ina baki wannan shawarar......zanci gaba kuma da maimaita miki ita....kada
kice zaki gwada raba kanki dani......zaki wahalar da rayukanmu ne kawai......don
fu'ad bai shirya rabuwa da duk macen data sanshi a d'a namiji ba......fu'ad bai
shirya rabuwa da sabrrrr ba" Yana kaiwa nan ya zame hannuwansa daga nata,yaja baya
still idanunshi a kanta yana tunanin maamah na parlor din har yanzu ko tabar wajen.

Har takai qofar dakinta ta fasa shiga,ta samu kujera ta zube tana
qoqarin qwato koda abu guda ne cikin tarin abubuwan da suke karakaina a kanta.

Da gaske bariki ne zalla za'a gwada mata?......ta samu nasarar
mallakarsa ne?,yaushe ta ingizashi zuwa soyayyarta?,tayi imani a banza fu'ad
bazaiso mace irinta ba......matar da karuwanci da bariki suka zama shaida kuma
tambarinta na farko koda mutuwa tayi?.

Hannuwansa ya miqa mata bayan ya gama daidaita mode dinsa. Bata ko
kalleshi ba bare yasa ran zata bashi hannun nata.

"Musunki da gardamarki zasu iya tunzurani na aikata abinda banyi niyya ba.....karki
manta kawaici kawai nakeyi miki.....karki yadda kawaicina ya qare......kika bari
hakan ta faru.....to tabbas ki rubuta ki ajjiye zan daukeki na kaiki wata duniya da
ba wanda ya isa ya ganki sai muhammad fu'ad shi kadai". Fararen idanunta da suka
sake glowing saboda siririn hawayen da yake a ciki ta watsa masa,kai tsaye ya saka
hannu yana dafe qirjinsa hadi da lumshe idanunsa kafin ya sauke hannun nasa ya saka
hannu ya kamo lallausan tafin hannunta yana sauko da ita.

"Kinci bashi da yawa na rashin kula da abubuwan da suka ratayi a kanki
nawa......duk wani abu nawa daya kamata ace kinyi bakiyi ba ki rubuta ki ajiye ya
shiga sahun bashi". Kasa musanta masa tayi sanda yake riqe da hannunta suna fita a
kitchen din.

Hannun kujera ta koma ta zauna tana hade hannayenta a qirji
zuciyarta tana mata wani irin zafi. Bata jin zata iya daukan wannan abun sam ba
zata jura ba.....tana da shakka idan har zata iya barin sabreen a gefen danta har
xuwa lokacin data tanadar mata.

Sanda ta daga idanun nata don sake duban kitchen din sai tayi
kyakkyawan gani,yana riqe da hannunta gam da taketa qoqarin zamewa.

"Kina qarawa kanki laifi akan laifi......please ki hutar da kanki" Ya fada yana
lumshe idonsa gami da jin yadda riqe hannunta kadai ke sakarwa jikinsa wadansu
kaifafan makamai.

"Muhammadu" Ta kirashi da wani kaifi da yake nuna zallar bala'i da bacin rai da
zuciyarta ke ciki,musamman data lura bai ankara da wanzuwarta a wajen ba.


_ayimin afuwa a karbi wannan ba yawa,mu hadu gobe in sha Allah_



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 93



93


Kiran data masan yaja hankalinsu shida sabreen din,idanunsu suka hadu karon farko
ita da sabreen suka sakarwa juna wani kallon kallo kafin sabreen din ta janye
idanunta salin alin tana kuma sulale hannuwanta daga cikin nasa. Ta kowanne fanni
jikinta ya bata al'amura da dama akan matar daga kallon farko kawai,ta danne
zuciyarta tadan ciji labbanta na qasa ta taka a hankali tana qarasawa gabanta.

Abinda bata taba kawowa zai faru ba,sabreen din ta zame a gabanta
tana fadin.

"Barka da yamma". Ruwan mamaki ya gama kasheta,ta dauke idanunta daga kanta tana
maidawa kan fuad din. Sam idonsa bai kansu,kamar ma bashi a wajen.

"Turqashi.....ni zaki saka cikin kokwanto?" Ta ayyana a ranta. Cikin kwanakinsu
dashi a saudiyya ta dinga jeranta masa huduba da qorafin rashin kirkin matarsa da
fatan samun wata kafa da zata sake nesantata daga rayuwarsa.......a yanzun kuma sai
ga yarinyar da take complain a kanta zube a gabanta tana kwasan gaisuwa.

"Ta yaro kyau take bata qarko......idan kinsan wata bakisan wata ba yarinya".
"Lafiya qalau......sai yau kika iya tunawa da wanzuwata?" Tayi maganar tanason
tabbatar da maganarta ta farko a zuciyar fu'ad da ya fara wucewa zuwa dakinsu.

"Aah fa.....wannan d'iyar tamu sai kin mata uzuri.......tunda mukazo Maldives ba
lafiya.....yanzun haka jinya take" Muryar anni ta ratsa plan din maamah din ta kuma
wargazashi,sannan ta saukar mata wani irin gigitaccen yanayi daya hautsina kwanyar
maman.

"Bata da lafiya?,me kuma ya sameta?" Tayi subul da bakan jefa tambayar dake yawo
tsakanin zuciya da harshenta.

"Tashi daga tsugonan nan karki wahala da yawa.......jeki watsa ruwa ki huta,Allah
yayi albarka" Anni ya fadi tana taya sabreen ta miqe. Ko waiwayen maamah din
sabreen bata sake yi ba......zubewarta a gabanta yana da nasaba da
musaddiq.......mutum ne cikakke d'aya da d'aya,wanda ke tsananin ganin kimarta da
kuma mutuncinta......idan har zata iya wuce mahaifiyarsa saboda wani abu daban da
tsakaninsu ne kawai.....to tabbas bata mutunta mutuntawar da yake mata ba. Ya
girmeta amma baya iya gaidata a tsaye ba tare daya duqa mata ba.....dame zata
biyashi.

Yadda maamah tabi sabreen da kallo zuciyarta na wani irin duka ya
sanya anni sakin gyaran murya. Dawo da dubanta tayi kan annin ita kuma ta basar
tana cewa

"Dazun kina tambayar me ya sameta.....lalurarmu ca ta mata......matar aure ai ba'a
rabata da qananun lalurori" Anni ta fada tana ajjiye diffuser din da dama ita ta
fito da ita ba tare data sake kallon fuskan maamah ba.

Wani dummm taji kunnuwanta har qwaqwalwarta sunayi. Maganan anni
maimakon bata haske sai duhu ma data sake sanyata a ciki. Lalura ta mata ciki ko
bari?,wanne anni ke nufi a ciki?. Tsaye tayi a wajen kamar sakarya,kafin wani
lokaci falon ya sake zama sai ita daya a ciki.

A daren tayi nadamar da batasan adadinta ba na tsananta bincike har
kunnuwanta sukaji mata maganar da ta gaza samun amsarta. Magana me harshe damo
mafi rudani data taba ji. Idan tace a daren tayi bacci to tabbas me karatu ma yasan
tayi qarya,ta qulla ta kuma kwance har batasan adadin sau nawa ba. Tayi rantsuwa ta
kuma lashi takobin muddin ciki ne da yarinyar......muddin tayi kuskuren samun juna
biyu da muhammadun lallai saita sakata cikin nadama da dana sanin da babu ranar
fitarta. Daga qarshe ta yanke shawarar sanya idanu a dukka motsinsu don tasan wanne
mizani zata dora mataki na gaba

β˜…Jiyan tunda wuri ta gama shirinta ta kwanta abinta,don haka daga maamah har d'an
nata babu wanda yaga gilmawarta sam. Cikin rashin sani maamah din ta tsareshi
wajenta da hirarrakinta marasa armashi,a nata tunanin Daki daya suke kwana,duk da
tana kokwanton hakan a ranta,amma zargin cikin da takeson tabbatarwa ya kasa bata
nutsuwa ko tabbacin taren suke ko ba tare ba.

Duk da akwai cook dinsu ta musamman dake zuwa musu girki tun a wancan
gidan,amma sai ta kasa kwanciya bayan gari ya fara haske. Daga amna har anni da
bacci ya dauke saman abun sallah tana tsaka da karatun qur'ani basusan da fitar ba.

Haka kawai takejin bai kamata ace ita da amna duka suna kwance ba har
sai sun jira cook tazo. Ta san ba wani qwarewa tayi da kalolin girke girke irin
nasu na masu hannu da shuni ba,amma ko yaya tana da rawar da zata taka,tana kuma da
gudunmawar da zata bayar,zata kuma iya dafawa aci ba qorafi ko mummunan rashin
dadi.
Shuru parlor din nasu,kowacce qofar daki kuma a rufe,haka ta ratsa a
nutse har ta isa kitchen din. Bata da tabbacin ya tashi,amma still sai taqi fidda
hijabin nata,don ma qarami ne bazai hanata kowanne aiki ba,ta fara duba freezer da
ma'ajiyar abincin tana tunanin me dame zata fara aiwatarwa kafin matar ta iso?.

Tunda ta idar da sallah tana saman abun sallar,bawai kuma zikiri ko
karatun qur'ani takeyi ba.....aah babu ko guda daya. Ta zauna ne kawai tana gadin
lokaci,ta zauna ke kawai tana sanya kunne da idanu akan kowanne motsi da zata iya
jiyowa daga parlor din.

Tunda yayi sallar asuba shi dinma bai koma ba,wani irin bacci ne mara
dadi kwata kwata ya daukeshi. Zuwa lokacin yana jin kamar haqurinsa yana dab da
qarewa,cikin sati hudu anci sati uku.....baisan wanne haqurin zaici gaba dayi ba
sama da wannan. A jiyan sanda ya baro wajen maamah yayi zaton daya koma dakinsa zai
samu anni ta turo ta,ya fuskanci anni ma kaman tana bayanta ne,banda haka yaci ace
an duba lamarinsa an bashi matarsa. Farouq kadai yasan zai iya masa wannan
aikin,saidai kuma shaqiyancin farouq din kawai yasan ya isheshi kafin ya samu yayi
masa abinda yakeso din.

Kayan jikinsa ya canza zuwa kayan motsa jiki da suka fitar da
murdaddiyar surar nan tasa da ginannen jikinsa. Kwana biyun da bai motsa jiki ba
sai yake jin jikinsa kaman yana masa ciwo,ya sanya rufaffun takalma a qafarsa ya
kashe wayoyinsa ya ajiye ya fito.

Already ya samu gym nan kusa dasu,ba wani nisa ne tsakaninsu ba,don a
qasa ya qarasa da sassarfa. Awa guda kacal ya gama ya kammala ya fito,suka jero
shida jordan suna magaganu jifa jifa akan abinda ya shafesu.

A nutse ya buda qofar parlor din yana takawa a hankali,idanunshi still
akan qofar dakin anni. Idanun nasa ya janye yana lumshesu,yana jin inama zaya samu
daman da zai qarasa gareta. Wata kewarta ke ratsashi....kewarta ba kuma iya kewar
fuskarta kawai ba......dumin jikinta.....qamshinta.....da tausasan
labbanta.....harda tsiwar nan tata da wani lokaci take maidata qanqanuwar yarinya
ba tare data san da hakan ba.

Har zai wuce dakinsa yaji yana buqatar ruwa,tunda baishan ruwa yawanci
bayan kammala motsa jiki sai bugun zuciyarsa ya daidaita.

A nutse yake takawa xuwa kitchen din,cikin jikinsa da zuciyarsa sai ya
dinga jin kaman akwai wani abu me muhimmanci a wajen,kaman yana qara kusanci da
wani bangare na musamman daya tsage daga zuciyarsa.

Idanu ya zuba mata sosai sanda yake hangota,kaman shigen jiya saidai
yau tana maqale da farin mayafi,tana tsaye gaban tarin Irish potatoes din da take
barewa a nutse da peeler. Idanunshi ya lumshe yana kuma budesu duka lokaci
guda,yana jin wani abu yana taso masa. Tun daga waccan ranar.....tun daga kuma
wancan lokacin zuciyarsa bata sake samun nutsuwa ba,yana jinsa kaman bashi
bane,yana jin kamar an sauyashi ne da wani mutum na daban ba muhammad jadda ba. Ta
hana zuciyarsa hutawa tun daga wancan lokacin,ta kuma hana masa damar sanin WACECE
ITA?. A jikinsa yake jin akwai wani daban tattare da ita.....akwai wani boyayyen
labari a bayan wannan matsiwaciyar fuskar.

Kaman jiya dai,yau kam baisan me ya dauke hankalinta har haka ba,gwara
jiyan akwai earpiece a kunnenta,wanda sai bayan ya zare yaji abinda take saurara
din. Takawa yakeyi a hankali har ya isa bayanta.

"Salam alaikum" Ya fada yana harde hannunsa a qirji qamshin turarenta me wani irin
sanyi yana buso masa. Wani irin faduwa gabanta yayi,ta tsorata ainun da jin
muryarsa dab da ita,amma sai ta dake taqi waiwayowa,ta motsa labbanta muryarta can
qasa ta amsa

"Wa'alaikumussalam" Ba tare data waiwayo ba tana ci gaba da bare dankalin. Shuru ya
ratsa tsakaninsu,ya fahimci ba zata juyo bane don haka ya taka yana zagayawa ta
gabanta a nutse ya tsaya a gaban nata,tazarar inches kadan tsakaninsu.

Hannu ya miqa kawai ya zare peeler din daga hannnunta,ya kuma miqa daya
hannun ya zare irish din da take barewa. Fararen idanunta ta daga da zummar masa
tsiwar tata,saidai cikin sa'a caraf suka shige tsakiyar nasa idanun. Da sauri ta
kauda qwayar idanunta gefe,duk wani rashin kunya data tanadi yi masa ya soma
zurarewa gefe.

"Duk karatun da kukeyi har yanzu baki koyi gaida miji ba?" Ya tambayeta calmly da
wani irin sassanyan sauti. Gaza dubansa tayi saboda yadda kwarjininsa yake neman
cika kitchen din gaba daya. Wadannan muscles din nasa ba qaramin tsoratata suke
ba,har bata qaunar ya sanya qananun kaya. Ita daya tasan me takeji idan ta
gansu,ita daya tasan irin qwarin da suke dashi,saita zabi matsawa daga wajen ko
zata samu daman shaqar iska me kyau wadda bata gauraya da dumin numfashinsa ba da
kuma na turarensa daya qara sanyi saboda cakuduwa sa gumin jikinsa da yayi.

Da qafa kawai ya tokareta,sannan ya daga nashi fararen idanun ya
watsa mata,tayi zaton zai janyesu daga kanta don haka bata janye nata ba,idanunta
suka sauka a hankali saman redlips dinsa masu tudu da wani irin shape,quarter
million din dake zagaye da habarsa zuwa zaman labban nasa ya sake zamewa labban
nashi wani ado na daban. Haka kawai tsigar jikinta taji ta tashi,abinda bata taba
ji ba tsahon ganinta da duk wani d'a namiji. Qoqarin janye idanunta tayi,da qyar ta
samu nasarar yin hakan kowanne sashe na jikinta taji yana daukan sanyi,rudewa taji
tana shirin yi kaman barawon daya shiga tuhuma a hannun hukuma.

Wani siririn murmushi daga can qasan zuciyarsa ya qwace masa

"Dama bakisan ni naga dama nake qyaleki ba yarinya" Ya fada can qasan ransa,amma a
sarari sai ya juya gefansa saman cabinet din,ya ajiye peeler din da Irish din,ya
sanya hannuwansa ya zagayesu ta mazaunanta yana jawota jikinsa da dan zafi
zafi,abinda ya bata daman zubewa a qirjinsa kafin ta daga kai tana neman qwacewa.

"Stop ita DUNIYATA" Ya fada softly idanunsa a kulle yana yadda fatar singalilin
hannun ta ke gogar nashi tana tayar masa da tsigar jiki.

"When.....sai yaushe zaki fahimci cewa KECE DUNIYATA?" Ya qarasa maganar yana ware
idanunshi gaba daya akan fuskarta. Wannan karon kasa jure kallonsa tayi,saita
runtse idonta tana hade rai sosai.

"Banaso kana tabamin jiki.....bana so"

"Am addicted to you.......tabaki shine favourite thing a rayuwata gaba daya" Ya
maida mata amsa kai tsaye yana me bata tabbaci ya kuma sake matso da ita sosai yana
mannata da jikinsa.

Gigicewa tayi sanda taji ta saki ajiyar zuciya tare da tashi ajiyar
zuciyar,kunya da wani irin takaici ya lullubeta,abinda taji haduwar jikinsu ya
saukar mata ba zata iya shanyeshi ba idan bata bawa zuciyarta daman numfasawa
ba......to amma kuma ta dauka a boye ta saki nata ajiyar zuciyar. Fitar sautin
ajiyar zuciyar tata ya sakashi ware dukkanin idanunsa a kanta yana dubanta,duba ne
na qurilla da son gane meye ya taba wannan zuciyar?.

A gaggauce gama shiryawa tsaf cikin Holland vlisco me asalin tsadar,an
xuba mata dinkin manyan mata na buba,ta kuma cika wuyanta da hannunta da kayan ado
na gold. Macace me son izza da alfahari,wadda idan tazo guri so samu kowa ya
dusashe a gurin sai iya tauraruwarta kadai. Ta tsaya gaban madubi ta tabbatar komai
yayi a shigarta sannan ta juya ta dauki wayarta tana nufin fita a dakin. So take ta
kasa ta tsare......so take komai zai dinga wakana cikin gidan ya dinga kasancewa
saman idonta,bataso tsakanin sabreen ko fu'ad wani yayi wani motsi da zai zarta
ganinta da idanunta,wannan karon salon da zata bullo musu dashi na dabanne,har sai
ta samu tabbatuwar nasara a gareta. Tanaso da iya dressing dinta kawai ameentu ta
fahimci wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,ameenatu ta sake tabbatarwa da kanta cewa
ita din fa itace mahaifiya ga muhammad jadda.......ba wata mace a duniya ta
biyunta.

Cikin takun isa take fita parlor din tana qarewa ko ina na parlor din
kallo. Siyan gida a qasashen waje musamman gidaje irin wadannan ba abu bane da
za'ayi maganan qananun kudade ba. Abinda ta lura dashi wasa wasa ameenatu ta maida
mata yaro saniyar tatsa kenan,taja wata irin qwafa tana samun sofa guda daya ta
hakimce a kanta.

Daga inda take ta sanya remote ta kunna tv,tayi sa'a tashar farko ta
kamota a inda suke gabatar da abincij breakfast na yaren mutanen qasar china.

Minti uku kacal taji tunaninta ya koma ga kitchen din gidan,tanaso ta
tantance dame dame ya jibge musu suke ci?,wanne irin gadara kuma ake gwadawa a
wajen?,don haka ta miqe tsam tana maida flats shoe dinta tana nufar kitchen din.

Yau kam sai data shigo sosai sannan idanunta ya sauka a kansu. Mugun
gigicewa tayi fiye da jiyan,saboda yanayin data gansu a yau din yafi na jiyan munin
gani.

"Na shiga uku ni mariya!" Ta fada muryarta na rawa tana yunqurin juyawa,wanda
saurin da take ta matsa a wajen santsin gurin ya debeta ta kusa zamewa,cikin
taimakon Allah ta kama murfin freezer ta riqe tana tsaiwa saman qafafunta.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 94



94


Daga shi har sabreen din sai a lokacin suka dawo hayyacinsu. Ita ta
fara zamewa ta tsakiya tana raba jikinta da nashi haushi yana cikata. Yana son
lalla qarfi da yaji sai ya koya mata dabi'ar da ba tata ba......lallai lallai sai
ya sanyata tana yin abinda ba halinta ba.......batasan me zata masa da zai sanyashi
nesanta kansa da ita ba. Batason yadda yake warning nata kan bata isa ta raba kanta
dashi.......a nata wajen ba wani abu me sauqi a wajenta sama da wannan
din......zaman Maldives ya bashi wannan damar,isarsu Nigeria kuma zata yanke
kowacce alaqa da yake tunanin ya qulla da ita.

Juyawa tayi tana fita a kitchen din ba tare data sake kallonsu ba.
Qirjinta ne kawai yake bugawa da wani irin bacin rai da kuma rudanin abinda ta gani
din.

"Wanne irin asiri tayi masa?,wanne irin asiri ne wannan?,maqale mata?" Ta dinga
jerawa kanta tambayar da bata batasan amsarta ba. Yadda zuciyarta ke matsewa da
bacin rai sai takejin idan tayi shuru tsaf zuciyarta zata iya bugawa......don haka
ta soma sakin ruwan sababi.

"Wanne wacce irin masifa ce?,gida sai kace gidan arna?,to wallahi ni bazan lamunci
wannan ruwan tantirancin da barikin ba ehe....dole kowa ya gyara zamanshi,ni ba
shashashar uwa bace ko banzar suruka,kome mutum yazo dashi ina daidai dashi ne".

"Oops" Abinda fu'ad ya fada kenan yana dafe goshinsa da tafin hannunsa,zuwa yanzu
yanajin anya zai iya rayuwa da mutane kuwa muddin yana tare da sabreen din?,anya
gidan nan duk da haka bai musu kadan ba?,wannan zaman zai yuwu kuwa?. Duba daya
sabreen tayi masa ta zare idanunta tana lalubar hanyar fita daga kitchen din ranta
a bace.

Jiya tayi zargin giftawar mutum dama a kitchen din,koda suka fita
sukaga sai ita kadaice a falom zuciyarta ta dinga raya mata ita ta shigo......amma
ba kasafai ta fiya son dorawa dan adam zargi ba,don haka ta cire abun a
ranta,qarshe ma ta gayawa kanta.

"Idanma itace ita ta jiyo......zaiyi mata dadi idan idanunta suka gani ta kuma
tayata rabata da maqalallen d'anta. Dab da zata fice a kitchen din yayi caraf ya
kamo hannunta yana sake janta jikinsa. Dubansa tayi idanunta na bayyanar da bacin
da ranta yayi

"Bayan maamah din ko akwai wanda kakeso ya sake shigowa ya ganmu ne?" Ta masa
tambayar da salon gatse kanta tsaye tana duban qwayar idanunsa duk da tsaurin da
kallon yake mata.

"Yes" Ya bata amsa shima kai tsaye yana kallonta

"Saura anni.....anni ce akwai ta rage bata gani ba.....ita nakeso ta gani.....don
ta hakanne kawai zata fahimci ina tsananin buqatar matata". Har tsakiyar kwanyarta
taji yadda ya fidda sautin maganar,wani abu me kama da jin kunya da nauyinsa ya
danso kamata,saidai tana ganin ya kamata ta fito masa a mutum don ya sasssuta yadda
yake yawan hada jikinsa da nata. Da alama da gaske yake fadi....da gaske yakeson
annin ta gani,tunda daga nan inda suke tsayen tana iya jin muryar annin na tambayar
maamah

"Lafiya mariya?" Batajira jin amsar da zata bata ba ta soma kokawar qwatar kanta.

"Annin ma?" Ta fada tana ware idanunta cikin kallon me kama da harara harara. Yadda
ta yiwa idanun nata kusan kasheshi yaso yi,hannunsa ya miqa a hankali ya nufi
gashin idanunta da suka sake zara zara saboda buda idanunta da tayin,abinda yadan
saukar mata da tsoro ta rufe idonta da sauri. Kusan dariya abun ya bata,ya zuba
mata idanu yana ganin yadda zuciyarta ke bugu sosai tun daga wuyanta zuwa qirjinta
dake lullube da hijabi.

"Bakisan harsashin da kika sake jefamin ba da wadannan idanun naki ba......a karo
na gaba tsiwar nan zan cire gaba dayanta na maida gurbinta da zazzafar
soyayya....." Ambatar soyayyar ya sakata bude idanunta a kanshi,tanason nuna masa
tawayenta koda ta hanyar murguda baki ne amma tana kokwanton kada ta jawa kanta,sai
kawai ta zabi zame jikinta daga nasa gudun kada annin ta samu isowar kitchen din.
Still sake riqe hannunta yayi,ga mamakinta hankalinsa kwance yake janta zuwa falon
kaman wani dan jagora. Daga can qarqashin zuciyarsa kuma wani kokwanto da mamaki ne
fal ransa. Me yake tunzura maamah din a duk sanda ta gansu haka a tare?,bayan tafi
kowa sanin igiyar aure ce ya hadasu?,me yasa yake ganin

Please Login or Register in order to submit comment