You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya
fara dawo miki,wataqila ameenatu ta sallama ne" Wata zuciyar ta gaya mata,don haka
ta dake tana dubansu sanda suke yowa kanta yuuu.

"Ranki ya dade......samun tabbaci da neman sahihancin rahotanni yasa mukazo
gareki.....da gaske kece mahaifiyar muhammad fu'ad jadda?.....mamallakin kamfanin
jadda diamond chores resources?" . Wani murmushin alfahari ya kubce mata,murmushin
da ya dusashe duk wani bacin rai da tashin hankalin data tsinci kanta yanzu yanzu a
cikinsa.

"Qwarai da gaske.....nice"

"Ma sha Allah......kina tare da laila d'iyar qawarki kenan?". Da farko tambayar ta
mata banbarakwai,amma zuciya batan basira da neman suna suka gina mata tunanin
wataqila suna kallon ita din uwar kowa ce da take riqon yara turmus,don haka ta
daga kanta kawai tana cewa.

"Eh haka ne".

"Yauwa.....mun samu cikakken labarin qawancenku......yadda kikayi silar hada auren
d'anki da matarsa ta yanzu sabreen da dukkan wasu hujjoji na riqe qannenta a bisa
cikar wannan buri naki.....kidnapping diyar alhaji hamza da kidnapping tata d'iyar
wato laila da a yanzu kika bamu tabbacin kuna tare....". Wani jibgigen abu ne taji
ya saukar mata tsakiyar kanta wanda ya sanya numfashinta yaso riqewa iya wuyanta.

Ita hajja zata yiwa haka?,ita hajja zata wulaqanta?,ita hajja zata
jajibowa taron manema labarai?,ita hajja zata tonawa asiri?,ya akayi ta manta da
ita bata sanyata mutum ta uku daya kamata ta shafe labarin su ba,me yasa bata
b'atar da ita ba?,me yasa ta barta taci gaba da shaqar iskar 'yanci?.

Juyawa tayi kawai don komawa ciki,saboda tana jin bai kamata tace
komai ba gudun tonuwar asirinta gaba daya wanda ta fahimci fiye da rabinsa ya yaye.

"Ranki ya dade ya zaki koma kuma?" Zaqaqurin dan jaridar ya fada. Waiwayowa tayi ta
zube masa wani kallo.

"Ni ba uwar qaramin mutum bace,bani da lokacin magana daku kai tsaye haka.....idan
ka matsa kuma kasan waye d'ana,ba aikinka kawai zaka rasa ba.....har....." Sai kuma
ta dakata tana kwabar kanta duba da irin cameras din dake fuskantarta. Kallon
kallon suka farayi tsakaninsu,don kowa da abinda ransa ke raya masa da yanke
maganar da tayi bata qarasa ba. Ganin ta dauke musu wuta gaba dayansu saita taka
tana komawa ciki cikin jan qaqqarfan tsaki.

"Akwai batun aika b'ata gari da kikayi gidansa don yiwa matarsa fyade da sunan baki
sonta.......wannan batun gaskiya ne?". Wani irin suka maganar tayi mata a
qirjinta,har batasan sanda ta saka hannu ta dafe saitin zuciyarta ba. Haki ta soma
yi tana jin kamar qafafunta ba zasu dauke ta ba,dole ta fara kiran sunan laila
saboda tasan duk 'yan aikinta yau basunan cikin mancewa da tarin 'yan jaridar da
suke neman tabbacin lailan tana tare da ita kaman yadda cikin rashin sani ta basu
tabbacin.

Kome takeyi,komai girman bacci ko uzurinta muddin maamah ta kirata
saita bar komai. Kaman yanzun da take zaman cin abinci haka ta watsar dashi ta
kwaso da gudu. Fitowar tata ta sake maida hankalin mutane kan laila din da dukkanin
kamanninta da hajja harira da suka fito.

"Lafiya maamah?,me sukayi miki?,me ya faru?".

"Kamani muje ciki" Ta bata umarni a tsawace,abinda ya sanyata kamata dukka jikinta
suna rawa.

"Da gaske kece diyar hajja harira?" Wata cikin su tayi caraf ta jefa mata tambayar
sunason tabbatar da maganar juya mata hankali da sukayi.

"Eh 'yarta ce......amma yanzun daidai nake da baiwa wajen maamah......yadda takeso
take buqata haka zanyi,koda ya kama na rabu da ita hariran"

"Ke laila kama bakinki mu wuce ciki!" Maamah ta fada da hanzari gudun kada tsananin
mallaka ya sanyata nunawa duniya abinda zai sake zame mata abun fada.

"Laaaaa haila ha'illallahu.....muhammadurrasulillahi" D'aya daga cikin mata 'yan
jarida dake wajen ta kasa daurewa abinda ya farun ta saki kuka tana tafa hannu.

"Wallahi 'yar hajja harira ce,da gaske ne,da gaske aikin juyar da hankali tayi mata
bayan tayi kidnapping nata......da gaske ne,gashinan diya tana neman mancewa da
uwarta?" Wannan kalaman sun sauka daidai kunnen maamah,wanda hakan ya sanyata
runtse ido,tsananin jin zafin hajja yana sake ratsata tare da alwashin daukan fansa
a tare da ita.

"Ki gayawa malam sa'adu ya fidda mutanen nan,idan ba haka ba zai fuskanci fushi na"
Umarnin data bawa laila kenan,ta kuma saka kunne tana jiran daina jiyo hayaniyarsu
daga nan inda take.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 151


*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX




151

Tsahon mintuna talatin ta sauke idonta akan takardar da fu'ad ya ajiye
mata,ta zubawa littafin idanu tana lissafa adadin yawan shafukan da yake dasu. Ya
fadi cewa zata iya cika littafin harma ta qaro wani....tayita rubuta dukkanin
abinda takeso.......wannna babbar dama ce a gareta kenan na zama Mulitibillonier?.
Murmushi ta saki ta soma yunqurin daga hannunta ta miqashi don dauko littafin,amma
abun mamaki sai taji hakan ya gagara. Ta sake yunqurawa a karo na biyu da zummar
gwada daukar nan ma shuru ne hannun yaqi sarrafuwa.

A zabure ta maida dubanta ga hannun nata cikin wani irin kidima da
dimuwa tana kallonsa. Hannunta ne dai......hannunta ne data sani shekara da
shekaru......hannunta ne da ba wani abu daya canzashi.........amma meye ya kawo qin
daguwarsa?.

A karo na uku ta tattaro dukkanin qarfinta zata dagashi ya sake
motsuwa koda wasa,a birkice ta maida hankalinta kan daya hannun tana qoqarin
motsashi shima.

Still shima abinda dan uwansa yayi shi yayi mata. Matuqar qololuwar
tashin hankali taji ta shigeta,wani irin mahaukacin gumi ya yanke mata.

"Me hakan yake nufi kenan?,wani ne yayi min asiri?,ko wani ne yayi min tsafi?" Ta
tambayi kanta da kanta.

"Kai inaaaa.....a irin wannan lokacin?,a lokacin da dama tazomin?" Ta sake tambayar
kanta a fili kaman wata tababbiya.

"Bazai yuwu ba" Ta fada tana qoqarin miqewa don ta gani ko qafafunta suna aiki?.

Miqewar datayi aniya jikinta ya gaya mata bashi da wani sauran motsi
me qarfi,qafafun suma suka shaida mata basu da wani sauran qarfin da zasu dauki
nauyin gangar jikinta ta hanyar warbar da ita ta zube a qasa tana kifawa saman
fuskarta.

Wani irin matsanancin ciwon kai yakeji,wani irin yanayi da yakejin kamar
jikinsa yana dab da gazawa. Yana dafe da kanshi tsahon mintunan da suka dauka suna
tafiya a motar,har zuwa sanda ya buda bakinsa a hankali yayi magana da driver din

"Badawa zaka kaini......ba gida ba" A yanzun ba abinda yafi buqata irin ya kebe,so
yake ya kebe shi daya,bayason magana da kowa bayason kuma hayaniya.

Karya kan motar yayi suna komawa daya hannun. Tafiyar mintuna ashirin
ta kaisu m,already yasan gidan,gida ne madaidaici daga waje,saidai kuma daga cikin
yana da yalwa da wani irin yanayi da aka tsara me tsananin burgewa. Yakan jima
baizo gidan ba,yana ma mantawa dashi sau tari,saidai duk sanda yake buqatar ya kebe
ko ya huta a nan din yake zama har zuwa sanda ya gamsu da yanayinsa ya koma normal
mode dinsa.

Tun a parlor din ya zube,karo na farko da yaji yana buqatar yayi
kuka,karo na farko da ya buraci inama ace shi din yana cikin sahun mutanen da
hawaye ke fita a fuskarsu da wurwuri?. Hawaye yake da buqatar ya zubar sosai saboda
qirjinsa dama zuciyarsa sun gaji da daukan abinda suke dauka din. Koda zai iya hana
kanshi fitar dasu to ba a irin wannan lokacin ba,a yanzun kuka yafi buqatar yayi
bawai yaci gaba da nuna jarumtarsa ba.

"Astagfirullah ya Allah......astagfirullah" Shine abinda labbansa dake motsawa suke
maimaitawa yana jin yadda qirjinsa ke sake suya idanunsa suna sake d'aurewa da wani
irin zafi da kuma radadi.

Wani sabon babi ya bude na tariyar rayuwarsu,tun daga sanda ya bude
idanunsa ya zama mutum cikakke zuwa yanzu. Bai tsinci komai tattare da maamah ba
banda haihuwarsu da tayi......ko a sanda take rayuwa tare dasu,yadda take mu'amala
dasu haihuwarsu ta zame mata kaman wani nauyi wahala ko dawainiya.....abbansu kusan
shine komai nasu......abbansu shine duk wata wahala da dawainiya tasu,abbansu shine
wankansu abincinsu,shirin makarantarsu da komai na dawainiya......yayi a gida ya
fita yayi a waje ya kawo musu. Zuwa yanzu baisan sadaqaul jariya na abubuwa daban
daban dubu million nawa yayi saboda shi ba......yana fatan ko a ina yake ya bishi
cike da samun salama cikin kabarinsa da rayuwarsa ta barzahu.

Da taimakon ambaton sunan Allah da yakeyi ya samu nutsuwa ta fara
dawo masa. Yayi amfani da wannan damar ya miqe ya shiga toilet ya daura alwala.
Dawowa yayi ya kunna ya kunna TV din dake kashe,ya lalubi tashar saudi qur'an ya
qaro volume din ya karade parlor din gaba daya.

Cikin kujera ya nutse,idanunsa a lumshe yana sauraren karatun gami da
bin ayoyin tare da shaik abdurrahman assudais. Yana karatun yana fahimtar ma'anar
ayoyin,abinda ya sake taimakawa wajen bawa zuciyarsa da ruhinsa nutsuwa.

A nan gurin yayi sallar la'asar,magariba ma ta ruskeshi duka ba tare da
ya sani ba. Itama magrib din a nan yayita,ya jima saman abun sallah yana addu'o'i
har baisan adadin lokutan daya shafe ba,yadai duba ya tarar da lokacin isha'i har
ya shiga.

Isha'i dince ya fita a daddafe zuwa masallacin dake cikin layin cikin
shiga ta bad da kama,baya son kowa ya tsaidashi don bazai iya dogon magana ba. Ana
idarwa ya taso shida jordan sukayo gida,jordan din ya dan dubeshi cikin matuqar jin
tausayinsa qauna da kuma kulawa.

"Sir......ko za'a aika a karba maka abinci gurin madam?,if not a maka order daga
wani eatery din?". Kai ya girgiza,a halin yanzu bayajin yunwa,still kuma bayaso ma
sabreen ta ganshi a yanayin da yake ciki. Tashin hankalin da take fuskanta ita
kanta yayi yawa,tunda ta dauki cikin nan bata huta ba,tana stressing kanta da yawa
akan duk abinda ya shafeshi......is over,ya kamata ta huta hakanan,ya kamata ta
samu peace of mind......yana shawarwarin yin nesa da ita har sai abubuwa sun
lafa,shi kansa yana jin zaya dauki hutu har sai komai ya koma daidai.

"Sakamin order lite abu please" Yace da jordan din yana wucewa cikin gidan.

Saman sofa ya zauna,ya dauki wayarsa dake yashe a wajen wadda sam yama
mance da ita. Saqonni da miscalls rututu,amma duka na sabreen din yafi yawa. Ya
saki dan qaramin murmushi bayan ya gama karanta wani saqonta na qarshe.....finally
ya samu wata kyakkyawar zuciya data damu dashi da gasken gaske,finally ya samu wani
ruhi dake craving for him.......finally ya samu wannan madadin da yake qishirwar
samu.

_"na kiraka na maka saqo har sau babu adadi amma babu guda daya daka
amsamin.....tom.....Even if you're ready to live without me,I'm not ready to let
go,ko yaushe zan kasance a tare da kai,koda hakan baida tsada ko daraja a
wajenka,bana saba alqawari,forever. Yours mom of triplet"_

Har tsakiyar zuciyarsa yaji saukar da saqon yayi masa. Wata soyayya ta
musamman tana sake huda zuciyarsa,qaunar 'yan tayi guda uku dake kwance a cikinta
suna sake lullubeshi.


_You're the missing piece that makes me whole,without you,life wouldn't be the
same,forever with you is where i want to be.....you're my forever adda
sabreen......am safe.....karki damu da yawa,ki bani aron wadannan awannin,zamu
kasance tare da juna in sha Allah,ma'u zata kasance tare da ke,ayimin afuwa"_ sai
kawai ya tura mata,yana buqatar isashen time da zaiyi healing daga nan zuwa
safiya,bayaso ya jefata a damuwarsa,wadda batasan sadda ta samo asali ba,yana ganin
kamar yin hakan rashin adalci ne kawai.
Yanaso yaji muryarta shima......yana kewar wannan lallausan sound din
nata wanda koda fada takeyi ko masifa laushinsa sai ya bayyana,but definitely idan
taji muryarsa saita gane damuwarsa.

Cikin taqaitaccen zaman kusa da kusa da sukayi da juna,yana mamakin
yadda take da saurin karantarsa,sauyawarsa ko damuwarsa,walwalarsa ko akasinta.

Abu daya daya sani shine baiwa ce,ba duk namiji Allah kewa baiwar mace me
kula da dukka damuwarsa da matsalolinsa ba.

Sauran kiran da saqon nasu farouq ne,duka sai ya share,saidai akwai
saqo guda daya daya dauki hankalinsa.

"Maamah is sick,she was admitted to the hospital" Idanunsa yaja ya lumshe,baisan me
zaice ba?,me zaiyi?,sai kawai ya kashe wayar gaba days ya cillata gefe.

Ya samu yaci abincin kadan,sai ya maida hankalinsa kan tataccen ruwan
blood orange natural da aka hado masa dashi,da kuma wadatar kayan fruit,cherry pear
jujube sai gooseberry da suka hado masa dashi. Dasu ya danyi fresh up,yadan jira
abincin ya narke kadan sannan ya wuce bedroom Kai tsaye.

Duk wani haske da komai da zai bashi sauti sai daya kasheshi,ya zamana
daga zallarshi sai sautin alqur'ani da yake tashi kadan kadan ta wata qawatacciyar
fitila dake tsakiyar gadon,wadda ke zuwa da qaramar fanka me bada sanyi
kwatankwacin na ac da Bluetooth da zaka iya using nashi,sai ya kashe hasken fitilar
dake jikin yabar iya sound din.

Yayi lamo saman gadon kaman dazu yana bibiyar karatun,bai tashi gane
kuskurenshi ba sai da bacci ya qauracewa idanunshi fafur.

Juyi ya dinga yi saman gadon shi kadai yana jin yadda kadaicinta yake
neman hallakashi,kowanne sashe a jikinsa sabreen din yake buqata,kowanne bangare na
jikinsa kewarta yakeyi.

"Ya salam ya al-hadi". Yana sawwara ta yadda zai iya yin nesa da ita dalilin tafiye
tafiye na kasuwanci......ta yaya hakan zata yiwu?" Ya tambayi kansa da kansa.

Daga qarshe dai ya tabbatar hakan bame yiwuwa bane,ya tashi zaune yana
duba qaramin kyakkyawan agogon dake saman side drawers na gadon.

"Oops" Ya furta yana dafe goshinsa,dare yayi,yayi imanin zai wahala idan bata fara
bacci ba yanzun,idan kuma har ya zama silar tadata a baccin bazai yafewa kansa
ba,sai ya maida kansa ya cusa tsakiyar pillow din yana qagara asuba tayi.

β˜…Tunda ya dawo sallar asuba ya wuce gym,yana fatan hakan ya dawo masa da
kuzarinsa daya rasa a kwanakin nan saboda tashe tashen hankulan da suka durfafoshi.
Waya ya dauka kai tsaye ya kira Jordan ya bashi umarni ya koma gida ya dauko masa
duniyarsa. Yana so nan din ya zame musu wani kebantaccen guri da ba kowa bane yasan
da zamansa,da qwaqwalensu zasu huta na koda kwanaki uku ne kafin su koma cikin
jama'a.

Sanda ya kammala shiryawa cikin sassauqar shirt da trouser sai ya wuce
parlor. Da kansa ya shiga kitchen ya tafasa madarar shanu fresh one da turmeric dan
kadan ginger da cloves ya dawo falon yana sipping kadan kadan yana kamo tashoshin
daya saba kalla a lokuta irin wadannan da ake labarai na qasa.

Tashar farko cikin headline na news din hoton maamah ya gifta da anyo
briefing na case dinta daga qasa. Zuciyarsa ta motsa tana bugawa da wani irin
yanayi,sai kawai ya matsa remote din yana canza tasha.
Channel din daya kama sun fara news tuni,the next abinda ya faru shima
dai hoton maamah ne da title tafka tafka na zargin kidnapping.....wannan channel
din sun samu nasarar saka wani d'an yanki na tambayoyin da 'yan press din sukayi
mata a Farfajiyar gidanta,wanda kusan duk me hankali idan ya kalla yasan maganganu
ne kama kai.

"Subhanallah" Ya fadi yana sauke canza channel.

Already su sun gama,saidai.maimaicin kanun labarai da shima hoton maamah
dana hajja harira harma dana fareeda da suka cika screen din. A nan ma baida
buqatar yaji komai,yasan tunda haka ta faru duk inda zai kunna ma abinda zasu nuna
masa kenan tamkar sunsan yana da alaqa da ita.

Wani zafi zuciyarsa ke mass,wani irin kud'a da quna take masa. Ya dauka
ko meye maamah tayi....kuma ko meye akayi mata ba wani sauran abu daya rage da zai
tada masa hankali a kanta ko ya qona masa rai,sai gashi bayyanarta a screen na TV
dinsa yana neman hana mishi nutsuwa.

Har addu'a yakeyi......har fata yakeyi ta zabi adadin abinda take buqata
daga gareshin.....mutanen dake kewaye dashi a yanzun,mutanen da yake rayuwa dasu a
yanzun suna da matuqar muhimmamci a tattare dashi,mutane ne da bayajin idan wani
abu maras kyau ya samesu ta sanadinsa.....ko ta sanadin arziqinsa lallai ba shakka
bazai yafewa kansa ba,bazai iya jurewa ya rasa koda rai guda daya a cikinsu ba.
Koda maamah ta karbi abinda takeso ta koma inda ta fito,har kullum,muddin da
numfashi a gangar jikinsa bazai fasa mata addu'a ta shiriya ba darajar haihuwarsu
da tayi.

Idanunsa basa wajen,amma tsaiwarta a bakin wajen yaji a jikinsa,don
haka ya daga risunannun idanuwansa yana dubanta.

Tayi wani irin kyau da shigar mutanen turkey,wasu irin riga da wando da
dan hijab dinsu me suturce jiki. Ya sauke idanunsa akan cikinta,sai yaga kaman ya
qara tasawa,kaman ya qara girma a kwana daya tak da yayi bai ganta ba. Wani sanyi
da rahama yaji yana sauka a zuciyarsa,sai ya miqa mata hannuwansa yana lumshe
idanunsa,abinda ya bata tabbacin lallai yana buqatarta kusa dashi.

A nutse ta tako,wanda tun kafin ta iso inda yake qamshin nan
nata,qamshin kabbasar nan tata ya soma kasheshi daga inda yake a zaunen(incense by
kabo daughter....duniya ne sis,ki gwada ko sau daya,basai nace miki gobe ki koma
ba,wannan tasted and trusted ne,bawai just normal tallan da bakasan ya kan abun
yake ba(+234 803 211 9803).

Kasa dauke idonsa yayi daga kanta saboda wani salon tafiya da takeyi da
yake fusgar hankalinsa,har ya qagu ta qaraso inda yake ya shaqi ni'imtaccen qamshin
nan da yakejin inama kowanne second da zai shude a rayuwarsa zai samu daman
shaqarsa?.

Kaman tasan da hakan,tana zuwa dab dashi saita cake ta tsaya,ta
yamutse fuska,ta turo lips dinnan nata ta kuma juya masa qeya.

Ya masa nisa ya tsaya tambayarta abinda ya faru,don haka kanshi tsaye
ya miqe,ya taka ya zagayo gabanta. Tsaiwa yayi yana duban kyakkyawan fuskarta data
soma nuna yanayi na masu ciki,yasa hannuwansa duka biyun ya kama kunnensa.

"Na tuba......bazan qara ba" Kafadarta ta maqale.

"Ni saidai kayimin tsallen kwado".
"Done madam" Ya fada yana dan ja da baya still idanunsa a kanta.

Hannuwan rigarsa ya tattare,ya durqusa a nutse ya tattare qafafuwan
wandonshi,sannan yayi bismillah ya tsugunna ya fara.

Da idanu take binsa,tanaso taga alamun ya gaji amma saita lura kaman ko
a jikinsa. Bata rai tayi ta soma buga qafa.

"Ni ban yarda ba Allah.....so nake ka gaji fa". Murmushi ya kubce masa,da gaske
mata rigimammu ne,suna kuma rigimar da ba dalili,musamman masu juna biyu,don haka
yana kaiwa qarshen bangon ya zube warwas yana numfarfashin qarya gami da jujjuya
kanshi.

Dariya dole ta kubce mata da abinda taga yana yi din,ta qarasa gabansa
tana dan dukan qirjinsa a tausashe.

"Wannan duka cuwa cuwa ne......kawai yi kayi kawai badon haka bane". Dariya me
siririn sauti ya saki,sai kawai ya jawota jikinsa,yayi mata kyakkyawar runguma yana
fadin.

"Na gaji da wannan qwalelen da kikemin,qamshi duka ya buwayi hancina,amma kin
hanamini jinsa yadda ya dace?,haka akeyi?" Ya qarasa fadi yana yaye hijabinta ya
salubeshi ya wurgar gefe sannan ya cusa fuskarsa tsakanin wuyanta da qirjinta.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 152


*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA
KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA
IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE
SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*
*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA
A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*



152


β˜…K'arfe goma da rabi na safe motocinsa suka shiga farfajiyar harabar
asibitin. Shi da duniyarshi ne,wadda tayi kyau abinta cikin wata tsadajjiyar cotton
lace lafaya me asalin tsada da taushi. Butter color ne da aka yiwa adon maroon da
golden,wannan ya saka takalmi da handbag da earrings data sanya duka suka kasance
maroon color,kalar daya zauna sosai a farar fatarta dake glowing saboda cikin dake
manne a jikinta.

Wani lafiyayyen yadi ne a jikinsa fari qal me taushi,wanda baida kauri
ko nauyi ko kadan,hasalima kana iya hangen fara qal din vest din dake sanye a qasan
rigar. Kusan komai nasa fari ne yau,hatta da takalmi da kuma agogon da yayi amfani
dashi dukka farare ne,sai wata hula saman kanshi irin ta mutanen qasar Morocco
wadda itama fara ce kaman kayan jikinsa.

Tunda suka fito daga gida take satar kallonsa,ya mata wani irin
fitinannen kyau kamar yau ta soma ganinsa,sun maidashi kamar wani jarumin fina
finan india.

Waiwayowa yayi gareta sanda motar ta qarasa tsayawa sai suka hada idanu.
Ta janye lumsassun idanunta daga kanshi tana sauke boyayyen murmushi da wata 'yar
kunya can cikin idanunta.

"Sabrrr" Ya kirata a tausashe da wani kwantaccen sauti yana dubanta duk da data
dauke fuskarta a wajen.

"Na'am" Ta amsa masa ba tare data waiwayo ba.

"Sabrrrr" Ya sake fadi yana jin shauqin kallonshi daya samu tana yi.

"Na'am hamma" Ta sake amsa masa still ba tare data waiwayowa din ba.
"Please mana sabrrr" Ya fadi a shagwabe har abinda ya fusgi hankalinta ta waiwayo
tana sakin dariya.

"Hamma shagwaba?" Ta fada pink lips dinta dake qyallin man lebe yana fadada da
fara'arta. Girarsa dukka biyun ya daga mata yana duban qwayar idanunta.

"Kina kallona ina jin dadi.....kuma sai kawai ki dauke kanki?". Murmushi ta
sakeyi,a hankali ta motsa labbanta.

"Kayimin kyau muffin,kayimin kyau sosai......kyanka da kamalarka suna sake tsananta
kishinka a raina.....wani lokaci ni kadai ina tunani......ina tunanin ranar da zaka
raba wannan soyayyar......wannan qaunar......wannan kulawar......wannan
jikin........wannan baiwar da wata diya macen......iya tuna haka kawai idan nayi
sai naji kaman zan zauce,sai inji kaman numfashina zai tsaya,sai naji komai ya
dainamin dadi.....kokwanto me yawa sai ya cika zuciyata......iya tunawa kadai idan
nayi nakejin haka.......ta yaya zan iya fuskanta da d'aukan haka a gaske?" Ta
qarasa maganar tana maida dubanta cikin idanunsa.

Idonta kawai ya kalla ya fahimci ainihin zallar
gaskiyarta......idanunta kadai sun gaya masa da gaske take......duk abinda take
fada din ainihin gaskiyarta kenan.

A hankali ya miqa hannunsa daya ya kamo fuskarta yana dubanta da
kyau,yanayin fuskarsa ya sauya zuwa ga yanayin wanda zaiyi magana me muhimmanci.

"Kin aminta daga wannan tsoron,kin aminta daga wannan firgicin har
abada.......bazan taba iya jurewa ba naga ruhin da yake tsananin sona yana wahala
har haka akan abinda nake da ikon yi masa ko bashi ba......sabreenn,mace daya tak
qwaqwqqara na roqi Allah ya bani......nagartacciyar mace na nacewa Allah da roqo ya
bani,koda zanci wahalar samu ko nemanta.....koda zan jima banyi aure ba amma dai ta
gari nakeso......nasha wahalar.....na kuma fuskanci qalubale.....kuma Allah ya bani
ke.....ke kadai kin gamsar dani,bana buqatar qari......kece reality na......bana
buqatar gaibu.....muhammad fu'ad naki ne ke kadai har abada........muddin kina nan
a sabreenn dinnan dana sani baki sauya hali da dabi'a ba....."

"Koda na tsufa?".

Please Login or Register in order to submit comment