You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

siriryar sarqarsu saman dogon
wuyanta,abinda ya sake mata kyau kenan.

Ido ya saka da baki yana kallon kyakkyawan dokin wuyanta,tunda aka
fidda design din shi sai yau yaga kyansa saman wuyanta,ya tako a hankali ya sumbaci
wuyanta nata,abinda ya dauke mata wuta na sakanni.

"An bani izinin sauka na dubasu?".

"An baki duniyata" Ya fada cikin kulawa da shauqin qauna.

Basa dakinsu koda ta duba,don haka saita yanke duba parlor dinsu.

"Salwa.....Allah yasa ba rigima suke miki b......" Bata samu daman qarasa fadin
abinda yake bakinta ba komai ya maqale mata yadda ta zuba mata idanu itama haka ta
zuba mata,cikin wani irin kallon me cike da matsanancin mamaki da gigita.

Maamah ce zaune saman wheelchair dinta,an dora mata farouq fawwaz da
almustapha fawad saman cinyar tata. Yatsanta cikin nasu yatsan tana tabawa a
hankali,duk da bacci sukeyi amma idanunta yana kansu gaba daya.

"Ba wata rigima hajiya......tun dazun suna hannun kakarsu,har sukayi
bacci.......fauzan ne ma yaqi zama gashican an goyashi" Salwa ta bawa sabreen amsa.

Maamah ce ta fara cire idanunta akan sabreen din sannan itama sabreen
din ta dauke kallonta daga kanta cikin matuqar mamaki jikinta yayi wani mahaukacin
sanyi.

"Tun yaushe tazo?" Ta tambayi salwa da harshen larabci data tabbatar maamah bataji
murya qasa qasa

"Mintuna kusan arbain kenan,a rubutunta tambayeni ma haka kuke barin yaran a qasa
gurinmu kuna sama?" Salwa ta fadi tana murmushi. Ta fada ne saboda yadda taga
maamah din tana qarewa yaran kallo,kallon dake nuna zallar qauna da shauqi da kuma
kulawa. Tunda tazo idanunta yana kansu,bata kuma saukesu ba ko sau daya.

Kai sabreen ta jinjina,abun yana sake fadada mamakinta.

"A samo mata abinci da abinsha" Ta fadi tana maida hankalinta kan maamah tana
takawa cike da qwarin gwiwa.

Ganin maamah a gidan nata ba abu bane me sauqi,ba wani abu bane da
zatayi zaton zai kasance haka a nan kurkusa ba.

Gabanta ta qarasa ta kuma tsugunna tana fadin

"Sannu da zuwa maamah......barka rana,ya jikin?,Allah ya qara lafiya". Wani kallo
ta dago ta dan watsa mata. Da tana da iko zata tambayeta ne uban me sukeyi a sama
kusan sama da awa daya suka bar kula da yara hannun masu aiki?,haka sukeyi kenan
cikin gidan?,shi ya ajiye fita office ita ta saki ragamar gida kamar su kadaine
suka rage a duniyar?,kaman ba wani abu me rai da yake rayuwa a duniyar saisu?.

Saidai ba wannan damar,sai dai kallon tuhumar data gabatar mata tana jin
ya kawo mata dan sassauci a zuciyarta. Sarai taga kalar kallon,to amma ita kanta
tasan yasha banban da kallon qiyayya da takeyi mata,wannan din akwai sassauci
qwarai a cikinsa,duk da cewa akwai alamu na jin haushi a cikinsa da batasan haushin
meye ba?,sai daga baya zuciyarta ke raya mata na barin yaranne a hannunsu salwa?.

Saida salwa ta kawo komai sabreen ta jera mata a gabanta,sannan ta
umarceta ta karbi yaran ta bata abincin taci,amma qememe taqi bayar da yaran.

Sanda fu'ad ya sauko ana wannan drama din,don sabreen ta haqura ta koma
gefe tana kallon ikon Allah,yadda ta tattara dukka hankalinta akan yaran,kamar bata
da wani sauran abu me muhimmanci a duniyarta sama dasu,duk kuwa da cewa ita din
daga wannan kallon guda biyu bata sake samun wani kallon ba.

Shima nasa kallon aka aje masa,sannan ta kauda kanta bakinta yana
motsawa kaman meson yin magana amma kuma ba dama. Mutuwar tsayen da yayi yafi na
sabreen,don har sai da maamah din ta sake daga idanu ta kalleshi tana masa nuni da
ya zauna ya tsaya mata a kai.

Kaman yadda sabreen tayi mata shima still hakan,saidai shi dinma ba wani
muhimmanci ta bashi ba. Ganinta riqe da yaransu kuma gudan jininsu cikin hannuwanta
da wata qauna data gaza boyuwa daga cikin qwayar idanunta yafi komai yi musu dadi
shida sabreen din. Suna zaune zaman kurame kawai,amma lokaci lokaci suna satar
kallon juna shida sabreen din,har zuwa sanda tayi alama da hannu aka bata abun
rubutu.

"Ka kiramin driver ya maidani gida,kada ku sake barin yara har tsahon sama da awa a
hannun masu aiki ba tare da kuna zagayosu kuna dubasu ba" Iya abinda ta rubuta
kenan da rarrababben rubutunta.
Ya dauka idanunsa ne suke masa gizo ko suke nuna masa ba daidai ba,sai
kawai ya miqawa sabreen din paper ya qarasa ya karbi yaran ya ajiyesu sannan ya
tura wheelchair din da take kai da kansa.

Sanda yake turata da kansa sai taji wani abu yana sauka saman
zuciyarta,tana iya qididdige takunsa da kuma yadda yake tura kujeran cike da
karsashi,sai takejin kaman ba'a taba tafiya da ita saman wheelchair din irin haka
ba.169



Koda suka isa key ya karba hannun driver din,yace su biyoshi a
daya motar. Shi yayi driving nata har gida,ya kuma danganata da bedroom dinta.
Tsugunnawa yayi a gabanta a hankali,yana jin wani abu me kama da qaqqarfan
farinciki yana dawainiya dashi.

"Zan koma......ba wani abun?" Kai ta girgiza masa alamun ba komai,sai ya miqe a
nutse yana furta.

"Sai da safe,Allah ya huta gajiya" Ya fada yana dan rage Ac din dakin. Idanunta ta
lumshe,wasu hawaye masu dumi suna silmiyo mata wanda ba nace ga dalili ba,ta miqa
hannunta da qyar dake yawan yo mata nauyi tana goge hawayen fuskarta.

Riqe da paper din kuma a inda ya barta ya sameta a zaune tsakanin
yaqini da kokwanto. Cak ya dagata yana juyi da ita sannan ya direta yana duban
tsakiyar idanunta.

"Na gode sosai duniya.....na gode da tayani siyawa yaran nan soyayyar
maamah......koda ni ko ke mun rasa soyayyarta.......soyayyar da zata bawa su fauzan
ta ishemu". Da mamaki take kallonsa,sai ya lakace mata hanci.

" Ko an gaya miki bana sane da boyayyar addu'ar da kikewa iyalinki.....ni number
one,addu'ar kariya samun nasara da cikakkiyar lafiya,yaranmu shiriya da zama
nagartattu.....sai samun qauna daga wajen kakarsu" Kunya ta kamata,ashe dukka
kukenta da fatanta cikin sallolinta na dare fakare yakeyi mata?.

★Cikin kwanakin kwanciyar hankali da nutsuwa ta samu ga kowa,ci gaba ta
fuskokin rayuwa kala daban daban.

Wata irin soyayya ake murmushewa cikin gidan me jadda me license,irin
soyayyar da yaran da suka fito ma daga jikinsu saidai a sanmusu. Tsakanin DUNIYOYIN
guda biyu wani irin dangantaka ce me qarfin gaske.....wadda ta gwada musu lallai WA
YASAN GOBE? banda Allah?. Wata irin DANGANTAKAR ZUCI me tsakanin qarfi da
power,wadda take sake basu yaqinin ABADAN ba wanda zai iya rayuwa ba dan uwansa.
Sau da dama idan suka zauna labarin rayuwrsu ta baya suna jinjina lamarin ubangiji
kan yadda ya tsara KUNDIN QADDARAr junansu,wani ALQAWARIN ALLAH ne wanda baya
tashi. Komai na sabreen din tana qoqarin saitashi ya zama daidai da ALQIBLAr fu'ad
din,komai nata tana qoqarin ganin bai saba da muradi da abinda me jadda yakeso ba.
SIRADIN RAYUWArta kaf akan gidanta ne da yaranta,ta zage sosai wajen koyan abubuwa
da dama da zasu maidata cikakkiyar matar gida,irin matar gidan da soyyayarta da
kulawarta ke tsayawa a zuciyar mijinta.

Duk wata DABI'AR ZUCIYA da tasan zata kawo rauni a mu'amalarta da
fu'ad tayi qoqarin nesanta kanta da ita,ta sake qoqarin zame masa GURBIN IDO ta
fannin mahaifiya dama mu'amalarsa tako da yaushe. Kusan duk bayan kwana uku ko
zataje ko bazataje ba ta koyawa faud daukan yaran bayan sallar ishai suje su gaida
maamah. Hakan yana sanya maamah cikin farincikin da har baya kasa boyuwa saman
fuskarta,tana jin yaran a jikinta qwarai,can qasan zuciyarta kuma idan ta kalli
mahafinsu takanji kaman ta zama butulu KUFAN WUTA a wani zamani can baya daya wuce.
Tun zuciyarta bata gaya mata harta fara gayawa kanta da kanta cewa A RUBUCE TAKE
qaddarar kowanne bawa,ba wanda kuma ya isa ya sauya qaddarar wani face marubucin
qaddarar.

Sabreen zata iya cewa ita din tana daya daga cikin matan da suka
qaryata kalmar nan ta NAMIJI TABARMAR K'ASHI. Mu'amalar fu'ad da komai nasa na
musamman ne kuma ya banbanta dana sauran maza. Duk da cewa GUDUN K'ADDARA GUZURIN
TARAR DA ITA amma tayi imanin cewa addu'a tana iya sauya qaddarar bawa......tana
fatan yadda ko yaushe ta sanya goshinta a qasa take roqar Allah madawwamiyar lafiya
da zaman lafiya a gidanta.......ta kasance ita daya a rayuwar fu'ad din a matsayin
matar aure,tana da yaqinin Allah bazai juyar da addu'arta ba duk da tabbacin data
samu daga bakinsa.


★Cikin dim light din dake kai kawo a dakin ta qaraso gabansa,sanye da
wata sassalkar rigar bacci data qawata surarta dama fatar jikinsa. Duk da sau daya
ya daga kai ya kalleta amma sai data fusgi hankalinsa,ya kalli agogo ya maida
dubansa kanta sanda take tsugunne gabansa tana zuba masa hadadden kunun ayar data
koya,kunun da tunda ta koyeshi ya zame masa JARRABI kullum sai yasha shi.

Sai data sake masa murmushi sannan ta miqa masa cup din,ya miqa hannu da
nufin karba yana cewa.

"Inda malami kika saka yayimiki aiki akan soyayyarki a zuciyata,tabbas dana qara
masa kudi ya qara tsananta aikinsa,don nasan babu me mace irin tawa a duniyar nan".

" Hamma....sonkai?" Ta fada da muryarta me sanyi,wadda shi daya take maidawa ita
haka a kebantaccen guri irin wannan. Zai bata amsa zafin da bayan hannunta yayi ya
dauki hankalinsa.

"Subhanallah.....zazzabin nan wai bai tafi ba?" Ya tambaya cikin tsananin damuwa
yana ajiye cup din hannunsa.

Kai ta gyada masa a shagwabe

"Bai tafi ba hamma....."

"Bari na yiwa doctor mubeena waya ta shigo ta dubaki......zazzabin nan ya isa haka
nan". Tasan koda tace masa ya bari bazai bari ba,yana damuwa da ciwonta fiye da
yadda ita take damuwa da kan nata.

Sannu kawai yake jera mata,tayi tayi ka yasha kunun yace ta maida
fridge.

Baa rufa awa ba doctor mubeena ta iso da kayan aikinta,kai tsaye
suka wuce dan qaramin dakin daya zuba qananun kayan aiki a ciki saboda lafiyar
iyalin gidan.

Shi da ita duka idanu suka zuba mata sanda take duba gwajin data
mata saboda ganin murmushi yana fita kan fuskarta.

"Mr and mrs jadda......congratulations,madam nada juna biyu". Banda yasan doctor
mubeena na tsananin girmamashi da sai yace tana wasa da hankalinsa ne,saidai duk da
haka sai daya ce.

"Say it again please".

"I said madam nada juna biyu......she's pregnant". Suratul ikhlas kawai ya hau
karantawa qafa uku,daga nan ya miqe ya sunkuci matarsa,daukan data saka Dr mubeena
soma hada ya nata yan nata ta basu waje,saidai tana iya hangen tsoro sosai fuskar
sabreen.

Abinda kawai yake yawo a kanta shine watansu fauzan hudu,cikin week dinma
duka duka aka fara koya musu zama......likita yace aqalla tayi shekara daya so samu
har biyu bata dauki wani cikin ba saboda ta warke yadda ya kamata,yanzu kuma dr
mubeena na gaya mata juna biyu ne da ita?.

Cikin qasa da mintuna biyar dukka wannan tsoron yabi ruwa,cikin daqiqa
kadan komai ya kwaranye daga zuciyarta. Yadda idanun fu'ad ke fidda qwallar
farinciki......yadda bakinsa ya gaza hutawa dayi mata addu'ar

"Ke 'yar aljanna ce in sha Allahu sabrrrr.......ke alkhairi ce sabrrrr......don
Alla ki gayamin me kike da burin mallaka a rayuwarki bayan gidan marayu da
gajiyayyu da tallafawa marayu?". Kai ta girgiza a hankali,lallai ta jahilci irin
tsananin son da fu'ad yakewa haihuwa.

"Babu.....babu muffin,iya wannan qaunar da soyayyar da wadatar......iya wannan
shauqin na samun iri daga jikina ya isheni farinciki har qarshen rayuwata". Ta
furta maganar da dukka zuciyarta tana tuna wata mata da mijinta yayi mata duka ya
watsota waje ya kuma saketa dukka a iqirarinsa na ta fiya haihuwa......da an tabata
sai ciki.....dukka ubangiji ita bai jarabceta da wannan ba?.

Wani irin dare ne da bacci ya gagari idanun fu'ad,yayi sallah yayi
addu'a har baisan iyaka ba. Itama da take kwance lamo kawai tayi,zuciyarta na sake
cika da mamakin yadda yake tsananin son haihuwa,saita samu kanta da maimaita.

"Alhamdulillah......alhamdulillah" Har sau babu adadi.

★Cikin lokacin wani kulawa yake bata data ninka ta baya,yana gida ko yana
office dukka yana kula da motsinta. Ya sake qaro mata aminttatun masu aiki da suka
sanya komai ya sake zame mata da sauqi,goyon ciki me 'yanci,kuma Allah ya bata da
sassauci akan nasu fauzan,duk da cewa har a lokacin tana shayar da yaran,yace bai
yarda ta yaye masa yara ba,idanma biyanta ne shi zaiyi a barsu susha nono su qoshi
ko don saboda ginuwar kwanyarsu yadda akeso.

To shi ciki dai d'an duma ne inji hausawa,a hankali jikinta da
dabi'unta suka fara nunata,duk da yadda take gocewa shiga cikin mutane don kada su
fahimci cikin. Kunyar cikin take sosai,sau tari idan shagwabarta ta motsa sai
tayita masa rigimar banza akai.

"Hamma don Allah kada ka gayawa kowa.....don Allah hamma kada ka fada,yayi wuri fa
hamma.......duka duka watansu fawad nawa ne?,Allah kunya nakeji"

"Sabrrrr" Ya kirata kai tsaye a lokacin tana saman cinyarsa yana raba mata doguwar
sumarta biyu hagu da dama don ta dameta.

"Wallahi wallahi ko cikin shege nayi miki bazan boye samuwarsa ba.....kuma zanso
abina fiye da tunaninki,ballantana 'ya'yan halaliya 'ya'yan so". Yadda yace 'ya'yan
so din har tsakiyar zuciyarta,tun daga ranar saita daina cewa komai akai,ta kuma
tayashi da duk yadda yakeso.

Tasha tsokana sosai wajen fannah wadda itama nata cikin ya fara
girma,amna da huda kuwa dukkaninsu yaya take a Wajensu,ba tsokana sai gulmarta a
boye,uwa uba suma duk ta kansu sukeyi don cikinsu ya tsufa sosai.

Wata tara da bikinsu amna amna din ta dire nata yaron namiji. Maamah
bata sanu ba sai bayan kwanaki bakwai,tana zaune saman wheelchair dinta sanda
musaddiq ya ajiye mata goro da alewar radin suna. Hamza ya saka shima still saboda
nuna yabawa bisa hidimar abban a kansu,sun masa laqabi da HILAL. Ba wani feeling
data samu zuciyarta a ciki akan haihuwar,so ko qi itama bata san wanne layi take
kai ba,saidai bata wani dorawa kanta tsananin tunani akan komai ba ta ajiye
maganan,duk da lokaci lokaci idan aka kawo mata su fauzan yaron yana fado mata a
rai.

Tsakaninsu da huda wata biyu kacal itama ta dire nata sojan. Saddiq ya
nuna kara sosai,ya sanya masa sunan mahaifinsu sabreen wato ahmad,suna masa alkunya
da NASEEM.

Ta kowacce fuska anni jinta take cikin alkhairin ubangiji,saidai a
yanzun kwadayinta a samu 'yanmata kuma,don tana fatan samun garabasar nan na wanda
ya raini diya mace biyu ya aurar dasu na alqawarin aljanna kai tsaye.

Irin girman da nauyin cikin ya sanya fu'ad wucewa da ita a wata tafiya
da yayi zuwa spain ya tafi da ita. Bawai don yana da nufin tayi anti natal nata a
can ba,saidon kawai a duba mishi ita duk da bata da matsalan komai,saina wani irin
cin abinci da takeyi,abinda shi kuma yakeyi masa dadi sosai,har yakan zauna yana
kallonta abinsa.

Scan din farko ya nuna twins ne a cikin nata. Wani iri ya dinga
ji,tsoron Allahnsa yana sake kamashi. Dukka cikin addu'arsa ba wadda bai gani ta
tabbata ba.....shin cikin ni'imomin Allah wanne ne a ciki zaiyi inkari?.


_Allah ka wadatamu da dukka ni'imominka na zahiri dana badini,ya Allah karka
jarabcemu da gushewar ni'imominka a kanmu_

_on our way to the last episode's in sha Allah_😄😄😄170



Tattalinta ya dinga yi,nan nan da ita yakeyi,baya yarda komai ya taba
walwalarta ko kuma jin dadinta.

Duk wani abu da yasan zata iya buqata ya ajiyeshi......komai da yasan
zata iya nema kafin ma takai ga tambaya ya tabbatar da samuwarsa.

Bata aikin komai,ba aikin fari bare na baqi,komai nata dana yara tana
da amintattun masu aikin da take jinsu kaman 'yan uwanta na jini,musamman da suka
kasance kusan dukkaninsu marayu ne wadanda basu watsar da maraicinsu ba.

Duk wannan gatan data samu.....duk wannan kulawar bata sanya ta saki
hidimarsa ki qwaya daya ba. Yayi yayi ta barshi amma ita kanta tasan ba abu bane me
yiwuwa tabar kula da mijinta,sai ya qyaleta a bisa dole,amma duk wani motsi nata da
zatayi shike tayata,shike kama mata. Misali wani lokacin yakan yi mata wayo ya
rigata tashi da safe. A kitchen din sama zai hada breakfast abinsa ya aje mata
nata,ya hada ruwan wankanshi da kanshi yayi,ya watsa undies dinsu cikin washing
machine ya wanke musu,ya kwashe komai dake tsananin parlor zuwa Bedroom din da suka
bata. Idan ta farka saidai ta taras da sauran aikin,wanda baya wuce shayar dasu
fauzan da kuma qarasa kintsa saman nasa,sai tayi wanka shikenan ta zauna cikin masu
aikinta.

Idan ta gaji tana buqatar fita shike katse komai nasa ya dawo ya fita
da ita,idan ma qasar ko garin takeso su danyi balaguro daukanta yake ita da duk
wanda takeso su wuce suyi iya kwanakin da takeso.

Irin gatan da yake gwada mata saita dinga jin kaman ya mata yawa,kaman
bata cancanci tattali irin haka,ranar data fara magana a kai suna tsaye ne saman
balcony na wani qawataccen madaidaicin gida daya siya a dubai a satin. Gidan yana
area me tsada ne wanda yake da clear view na garin dubai da guraren kallo masu
kyau.

Ta baya ya rungumeta yana dora hannunsa guda daya saman qaton
cikinta. Ta miqa hannunta ta bayan itama ta shafo sajensa tana sakin murmushi.

"Tunanina kike?" Ya furta a tausashe,saita gyada masa kanta.

"Ya akayi kasan sirrin zuciyata".

"Ruhi daya......zuciya daya.....qwaqwalwa daya.....gangar jikince kawai guda
biyu,to menene zai boye a wajena?" Ya qarasa maganar yana tura mata wani file ta
gefan cikinta. Murmushi ta saki tana jin maganarsa ba wani kuskure ko gyara a
ciki,ta karbi file din ta bude.

Takardar shaidar mallaka ce ta wannan gidan da suke ciki,wanda ya
rubuta da sanya hannunsa da komai kan ya mallaka mata gidan. Ganin komai take kamar
a mafarki,batasan adadin gidaje da estate nawa ya mallaka mata ba.......amma wannan
ya zama na daban. Mallakar gida sukutum da guda a dubai?,abun sai kanta ya kasa
dauka,don a satin a gabanta ya bada izinin tura Dirham's masu nauyin gaske ga
kamfanin da sukayi cinikayyar gidan.

A nutse ta juyo suna fuskantar juna,hannunta yayi sanyi sosai ta riqe
nasa hannun.

"Hamma.......wannan kyautar tayi girma da yawa,wannan gatan yayi yawa". Sassanyan
murmushin nan nasa ya saki,ya kama qugunta ya riqe yana mata wani tattausan kallo
kaman zai hadiyeta.

"Me akayi ma my world?,wannan gidan wai?,kinsan gidaje na nawa a qasar nan?,wannan
din kuma dama tun asali saboda ke aka siyeshi.......sabreen" Ya kirata da wani
sound yana kama fuskantarta cikin hannunsa.

"Na'am muffin" Ta amsa masa idanunta suna cika da hawayen farinciki.

"Komai na fu'ad naki ne.....komai na muhammad jadda kin cancanceshi.........gata
kuma ban nuna miki komai ba sabrrrr.......bana buqatar komai a wajenki illa ki
cikamin gida da yara......ki cikamin gida da zuri'ar da zasu zamemin ababen
alfahari.....haihuwa nakeso kiyita yi......ni kuma nayi alqawarin bazan barki kisha
wahalar komai ba banda ta basu tarbiyya". Rungumeshi ta matso zatayi amma cikin
jikinta ya tokaresu,sai taja baya kadan,yana dariya ya nuna cikin da
yatsarsa,sannan ya juyata yana baga kyakkyawar runguma ta baya.

★Wata takwas da sati biyu wanda yayi daidai da shekararsu fauxan daya da
wata daya akayi mata wani CS din a garin madeena.

Kyawawan 'yan biyu ya haifa dukkaninsu maza. Manya manya har sunfi su
fawad girma da wani irin kyau me daukan hankali,don kuwa kamanninsu bangare biyu
suka debo,fu'ad din da sabreen din,saika kasa tantance da wa suke kama?.

Kasuwar 'yan uku ta tsaya,kowa so yake a bashi yaran,duk kuwa da cewa
dasu aka tafi karban haihuwar 'yan uwansu. Amna naso,huda naso,fannah da farouq
dinta sunaso,ga maamah a gefe da sai a ranar tayi kukan rashin magana da bata
iyayi. Kuka tayi sosai me yawa,don kuwa taso tana da baki,da tabbas ko fu'ad baya
so sai ta karbi wadannan yaran.

Wani irin kwarjini yaran ke dashi kaman ubansu ya roqa musu,ga wani
irin energy da suke dashi da wani girma kai zaka ce shekara biyu suke ba daya ba.
Bugu da qari kowannensu tafiya yake sosai,don tun suna wata bakwai suka fara
miqewa,yanayin kulawar da suke samu ya sanya ba wani wanda yayi wani abu wai kashin
haqori,banda zazzabi da sukayi na wasu kwanaki,sai bullar haqora kawai a bakinsu.

Energy dinsu ya sanya suke da fitina,haka suke fafatawa da anni. Gidan
su kuwa tuni fu'ad ya sanya an dage komai sama wanda zasu iya jawowa ya
illatasu,wanda bazai dagu ba yasa an daukeshi anyi replacing da wani abun na daban.
An kwashewa sabreen flower verse dinta da yawa da take ado dasu,a ranar ta dinga
fushi tana tura baki gaba.

"Tsakani da Allah......haka kawai a hana mutum ado......". Duba daya yayi mata ya
dauke kai yana ci gaba da yankewa fawwaz farce sanda yake bacci saman cinyarsa.

" Yara dai da gidansu ba wanda zai hanasu sakewa,ni ba ta flower vase dinki nake
ba.....ta lafiyan yarana nake,inda bazai cutar dasu ba zan bar musu suyita
fasawa......qarqari ace dai mu biya ko?,mu kuwa baza'a mana gorin biya ba". Mamaki
ya cikata,tayi sakato tana kallonsa yadda ya basar yana wani shan mur,ta danne
dariyarta tana sake daure fuska

"Amma dai ba haka akewa yaro tarbiyya ba,a barshi idan ya fasa a zane masa hannu
don yasan ba abun tabawa bane". Nail cutter din ya subuce a hannunsa,ya waro ido
yana dubanta.

"Du me?,ke waye ya dakeki?,ashe kina so anni da abba su shigo sulhu kenan......wa
yace miki akwai duka cikin tarbiyya?,wait.......tsaya ma......bakisan yaro muddin
ba'a barshi yayi wasa yadda ya dace ba hakan yana zame masa naqasu a gaba?,ina
manya da zakiga sun girma suna wasanni kaman yara?,har wata tsokanar idan sun maka
ya baka haushi?,alhali bawai tarbiyya ne basu dashi ba?,to yawansu rashin barinsu
suyi wasan da zasu qoshi ne". Dole dariya ta subuce sabreen ganin yadda ya gyara
zama yake mata jawabi bilhaqqi da gaske.

"Malam hamma....ban taba jin karatun nan ba sai a kanka".

" Zaki jine da kyau.....nidai na fada abar yarana suyi yadda sukeso". Ya fada yana
ci gaba da yanke masa farcen

"Hamma" Ta kirashi a tausashe,kai ya daga ya kalleta ganin yadda ta kirashin.

"Ina gudun kada soyayyar yaran nan ya rufe maka ido ka kasa tayani basu tarbiyya me
kyau". Wani murmushi ya sakar mata yana ci gaba da aikinsa.

"Zaki gani.....Allah ya bamu aron rai" Abinda ya fada kawai kenan. Shi kadai daga
shi sai Allahnsa sukasan irin burin da yaci akan yaran,shi daya yasan kalar rayuwar
da yayi musu tanadi.....ba iyasu fauzan ba,dukka yaran da zai samu daga nan har ya
qare rayuwarsa.

Ranar da zasu bar asibiti zuwa gida tana zaune suna hira da huda dake
rungume da babynta wanda ya gama rigima bacci ya soma daukansa taji sallamar kawu
rufa'i.

Farar jallabiyya ce a jikinsa harda hirami,ga wani farin carbi a
hannunsa.

"Assalamu alaikum warahmatullahi

Please Login or Register in order to submit comment