You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

riqe a
hannunta.....amma sai ta kasa matsa toothpaste a jiki,saita buge da kallon fuskarta
ta jikin madubi data fito tarwai kaman ka saka hannu ka ciro.

Daren jiya ke faman mata yawo cikin kwanya......tanata tuna shudewar
kowacce daqiqa a tsakaninta dashi. Iya yawan abun kunyar data tafka bazai barta
hada idanu dashi ba,ba zata iya ba sam koda daidai da minti daya.

Duk yadda take tunanin abun zaizo kaman na farko sai komai yazo mata da
ba zata,saida komai ya kammala sannan ta tsinciki kanta tsakanin hannuwansa,bata da
wani zabi illa fashe masa da kukan kunya. Ya sani sarai......yasan abinda takema
kukan,amma sai yayi kaman bai fahimta,ya lalace sosai wajen rarrashinta......daga
qarshe ya juye mata tashi kalar shagwabar data sake tsumata,ta sanyata tayi luf ba
shiri tana jin kunya da nauyinsa suna kamata.

Zare brush din daga hannunta da taji anyi ya sanyata firgita

"Good morning sleepy head" Ya fada yana tsaye daga gefanta ya kashe mata idanu yana
qoqarin saka mata toothpaste din.

"Morning" Ta fada tana sadda kanta qasa tana jin wani irin nauyinsa da bata taba ji
ba. Tunda taji ya tashi ita taqi koda motsawa,har yayi wanka ya fito yayi sallah
yadan fita a dakin,fitar nasa tayi amfani dashi tayi wuf ta shiga wankan da xummar
ta shirya kafin ya fito tayi sallah ta sake boyewa cikin duvet.

"Feel free......brush kawai zanyi na fita" Ya fada yana matsowa bayanta. Dab da ita
ya tsaya,har jikinsa yana gugar nata,fuskarsa ta fito bayan tata ta cikin
madubin,ya zube idanunsa fes da suka qara wani irin haske saman tata fuskar ta
cikin madubin. Wani irin murmushi ne kwance a fuskarsa.....wata irin shimfidaddiyar
walwala da makamanciyarta bata taba wanzuwa saman fuskar tasa ba da annuri suke
fita daga fuskar tasa. Qwayar idanunta yaketa laluba yana son ya kalla amma ta hana
mishi kallo,ta zura brush din kawai a bakinta tana wankewa tana kuma jin yadda yake
sake shigewa jikinta da sunan brush zaiyi.

Ta gefe da gefen cikinta ya zura hannuwansa ya zari brush dun,ya saka
toothpaste duk a hakan yana sake shige mata,ya tura brush din bakinsa ya soma
wankewa shima a hankali yana sake maida idonsa ga fuskarta data futo sosai ta
madubin. Wani kallo yake mata ko qiftawa baya yi,yana fatan tayi kuskure ko sau
daya ta daga kai ta kalleshi,yana son karantarta ta cikin idanunta sosai,ya sake
matsawa sosai jikinta yana sansana kanta dake fidda wani irin sassanyan qamshi.

Ta gama nata brush din amma tanata juyashi a hannunta,ta rasa yadda
zata gaya masa.....ta kasa daga kai ta kalleshi ma bare ta samu qwarin gwiwar gaya
masa. Ya karanci hakan,murmushi ya qwace masa.

"Wannan kunyar daga ina?" Ya tambayi kansa da kansa daga can qasan zuciyarsa.

Yana sane yaci gaba da cinye musu lokaci,yanason tayi magana amma kuma
ta gaza,har zuwa sanda taji ta soma tuqewa,saita ajiye brush din,ta kuma juyo da
hanzari tana fadin.

"Ni na gama" Qurjinsa ta fada kai tsaye,don babu wani space da zai bata daman
wucewa. Kan qirjinsa idanunta suka fada,ni'imtaccen gargasar qirjin tayi maraba,ta
daga idonta a hankali tana kallon tazarar nisan tsahon dake tsakaninsu. Ya fita
tsaho sosai,duk da cewa ita din ba gajeriya bace,idanunta suka sauka kan Adam's
apple dinsa daya fito sosai ta maqogoronsa kaman zai fado.

Wani abu guda daya tal da yake burgeta ga halittan namiji
kenan......batasan meyasa yake burgeta ba,amma dai tasan yana bata mamaki,ta jima
kuma tanason taji abun ya yake,tauri ne dashi?,yana musu zafi ko kuwa?,ba tare da
tunanin komai ba ta miqa yatsanta a hankali zuwa wajen ta tabashi.

Cikin kowanne jini dake harbawa a jikinsa yaji saukar yatsan nata,ya
hadiye wani abu daya sanya Adam's apple din motsi yayi qasa ya sake dawowa saman.
Kasa jurewa abinda yakeji din yayi,sai ya fincikota sosai zuwa jikinsa ya matseta a
qirjinsa da kyau yana dora fuskarsa saman wuyanta.

"Wannan tsokana ne ai......yanzun kuma inda zan ritsaki kona nema fansa saiki
isheni da kukan banza......har a kiramin anni ma da momma ko?". Kunya ce ta kamata
me tsanani,akan jiya yake tsokanarta ta sani......sannan ita kanta batasan ma'anar
abinda tayin ba yanzun,taji tana sha'awar tabawa ne kawai.

"Nifa wannan gaisuwar baiyimin ba......ina buqatar zuzzurfan alaqa tsakanin da
iyalina......inason ki zama
qawata.....aminiyata......mamana.....yayata.....qanwata....oh" Sai kuma ya tsaya
yana dagota daga jikinsa gami da dan dukan goshinsa.

"Ashe fa ance sai anyi shawarar za'a soni ko aah ko?" Ya fada yana ware mata
idanunsa. Kauda kanta tayi gefe daya zuciyarta na bugawa,wani murmushi yana son
kubce mata amma tana hana hakan,bata ankara ba taji ya dagata cak ya azata gefan
sink din bandakin,hakan ya bawa santala santalan cinyoyinta daman bayyana don
bathrobe din ta dage kadan.

"Kinsan me?" Ya fada yana tsayawa tsakanin cinyoyinta,hucin numfashinsa dana
daddadan turarensa yana sauka a fuskarta.

"Karki wahalar da kanki DUNIYATA kice saikin koyawa kanki sona......" Daga kai tayi
ta kalleshi abinda yakeson gani kenan dama tun dazu,saidai ita din tayi hakanne
saboda mamakin maganarsa. Girarsa ya dage mata dukka biyun yana jin dadin ganin
qwayar idanunta. Oily eyes daya jima yana kokwanto shin akwaisu?,sai gasu a jikin
abinda yake mallakinsa gaba daya.

"Yes.....iya soyayyar da nake miki ma ta ishemu mu rayu ni dake.....bake kadai
bama.....har babies din da zamu haifa nan gaba" Ya fada yana dora hannunsa saman
plate tummy dinta,abinda ya sanyata jan wani irin numfashi saboda tafin hannunsa
guda daya daya dora saman budaddun cinyoyinta.

"DUNIYATA....Kinsan yara nawa nakeso ki haifamin?" Kasa amsa masa tayi,tafi buqatar
ya matsa baya kadan kada ya dagula mata lissafi,abinda ta fahimta kaman yana son
sake mata wayo ne kawai yake saka kusanta kanshi da ita.

"Karka zaqe da yawa.....har yanzu ban gama yanke hukunci ba" Ta fada cikin tsanani
dakiya. Dariya yakeso yayi sosai amma ya dake,ya fahimci qarfin hali irin nata da
zallar qi fadi dake dawainiya da ita.

"Don't worry.....kedai ki tayani ji ma kawai ya wadatar dani" Yana kaiwa nan ya
sunkuceta gaba daya tamkar ya dauki 'yar jaririya yana takowa zuwa bedroom din.

"Ka saukeni" Ta fada a narke,saboda ta lura gaba daya ya raina dagata,ya maidata
kamar wata 'yar bebin roba.

"Ta yaya zakiyi nauyi kina wasa da abinci?,indai kinason mu shirya saikin koyi cin
abinci irin na muhammad fu'ad" Yakai qarshen maganar yana direta saman sofa
bed,sannan ya fara takawa a hankali zuwa saman dressing table yana kwaso kayan
shafanshi data tabbatar yafi qarfin talaka irinta.

Gabanta ya zubesu gaba daya sannan shima yabisu ya zauna a gabanta yana
tankwashe qafa tamkar bawa da uban gidansa. Ya soma bude cream cream din da wasu
irin abubuwa da batace ga sunansu ba ya fara tatsawa a hannunsa sannan ya kamo
hannunta yana juye mata su a ciki.

"Zaki iya haifamin yara dozen biyu?" Yayi maganar murya a sanyaye da wani zuzzurfan
sauti yana riqe da hannunta da yake maida cream din daga hannunsa zuwa nata.
Idanu tadan wara tana dubansa da kyau.

"Please am serious.....ko through IVF ne.....a dinga saka miki biyar biyar.....nayi
alqawari ba zaki sha wahala ba.....zan biya ko nawa ne a ciresu cikin
aminci.....zan kashe miki ko nawa ne DUNIYATA.....nayi alqawari" Mamaki sake
kasheta yayi ganin yadda yake maganan da dukka gaskiyarsa,hakan ya bayyana itama a
idanunta,sai ya saki wani murmushi yanayin fuskarsa yana canzawa.

"Kina mamaki ko?" Ya tambayeta yana sakar mata hannu don ta samu daman shafa man
daya tatso mata.

"Naso mu da yawa abbanmu ya haifa.....nayi wannan burin saboda gidan masu yara da
yawa yana burgeni,saidai kuma mu biyu aka haifa.....inaso na tarawa abbana zuria me
yawan gaske.....zuri'ar da zasu dawwama suna masa addu'a da sadaqa jariya.....bani
da sha'awa ko burin auren mata biyu.....dake kadai nakeso na rayu DUNIYATA shi yasa
nakeso ke din daya ki zama uwar dukka yarana" Ya qarasa fada yana dubanta.

"Baga fareeda ba?" Tayi zancan da wani yanayi da ya sanya murmushi kubce masa,yadan
dafa goshinsa yana cewa.

"Maganan fareedan bai wuce ba?..... apologize din da nayi jiya baiyi ba?.....okay
am ready to repeat it" Ya fada yana jinjina yadda abun yafi tsaya mata a rai fiye
da komai. Kafadunta duka biyun ta daga tana kauda kai

"Ina ruwana nikam.....am temporary......"

"Temporary?" Ya katseta cikin maimaitawa yana dubanta da kyau ba tare da ya barta
ta qarasa fada ba,sai ya ajiye boyayyen numfashi

"You're my world.....kece DUNIYATA sabrrrrr....na rantse da Allah.....banda
ubangijin daya haliccemu ba wanda ya isa ya qwaceki a hannuna.....ke kanki baki isa
ki raba kanki dani ba.......ko mutuwa ina kai qararta wajen Allah.....muddin tana
da nufin rabani dake ubangiji ya hukuntamin ita". Sosai maganarsa ta ratsata,taci
gaba da shafa wa hannayenta man cikin wani irin kasala ba tare data dago idanunta
ta kalleshi ba.

"Ya kamata muje kiyi break" Ya fada yana katse shirun hadi da miqewa. Batasan me ya
matsa yayi ba sai daya miqo mata rigar saman cinyarta.

Rigar jiya ce dai da bata saka ba,saita daga ido tana masa kallon Why?.
Kafada ya daga yana watsa hannuwansa.

"Zan iya saka miki if ba zaki iya sawa ba" Kai ta girgiza masa da sauri,don ta tuna
jiyan,daga saka rigar labari yasha banban.

"To ka fita sai na shirya" Ta fada a shagwabe still

"Inje ina?,bayan ko na fita dinma saina dawo na taimaka miki na daure miki rigar
kin manta?" Ya fada hannuwansa na goye a qirjinsa yana qare mata kallo,don hatta
cikin bathrobe din ba qaramin kyau tayi masa ba.

"Na rufe idona.....inkin gama sakawa ki gayamin" Ya fada yana juya mata baya gami
da maida kallonsa qofa yana ganin gilmawar ruwa ta tsakanin labulayen da basu gama
rufuwa ba.

A gurguje ta saka rigar,tanayi tana waiwaye wai kada ya juyo ya ganta bata
sani ba. Dariya yakeyi abinsa can qasan ransa,don yana ganinta tarwai ta wani glass
dake gabansa ba tare da ta sani ba.
"Zan iya juyowa?" Ya tambaya yana danne dariyarsa.

"Eh" Ta fada tana turo baki gaba,abinda yayi matuqar burgeshi har yaji kaman ya
kama lips din ya shanye.

A nutse ya dinga bin igiyoyin yana daure mata,kowacce daya saiya
tambaya

"Tayi haka?" Kai take daga masa mafi yawa,ta koma kaman kurman qarfi da yaki,ta
tabbatar kaf halittun bayanta ya gama qare musu kallo,tana jin yadda yake sakin
ajiyar zuciya time to time. Yadda maroon din rigar ta zauna daga bayanta kadai ya
qawatar dashi gami da tafiya da hankalinsa. Ya dora yatsunsa a hankali saman fatar
wuyanta,inda wajen ya danyi jajaja. Hannunta ta dora saman nasa tana dan danne
wajen,guri kusan uku duka haka sukayi,yasan kuma shine sila,zare hannun nasa yayi
yana juyo da ita tana fuskantarsa.

Idanunsa ya lumshe yana kuma budesu duka samanta.

"You look so gorgeous" Ya motsa labbansa yana furtawa da wani irin sassanyan yanayi
yana duban qirjinta da yayi redness shima guri uku. Yatsantsa yakai wajen yadan
taba sannan yace

"Does it hurt?" Fuska ta kwabe masa cike da shagwaba kaman zata sake masa kuka,sai
ya yarfar da hannunsa yana fadin.

"Ayyah.....sorry,bari na fanshi wannan ciwon" Ya fada yana ja da baya fuskarsa da
murmushi. Luggage dinsa ya kwantar ya bude,ya ciro wani dan mitsitsin box ya tako
gabanta.

"Qaramim gift ne....for you duniyata" Ya fada yana ciro wani siririn agogo dake
zuba qyalli. Koda bakasan meye ba kasan abune me matuqar daraja,kallo daya zakayi
masa kasan abune me tsadar gaske,bashi da girma ko fadi amma yana daukan ido sosai.
Matsowa yayi kusa da ita sosai,ya miqa mata hannunsa yana kallonta da ido. Ta
fahimci me yake nufi amma saita noqe,bai wani tsaya jiranta ba yasa hannunsa ya
kamo hannun nata sannan ya fara saka mata agogon.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 103


103


"Ya subhanallah" Ya fada yana juya hannun cikin tafin hannunsa. Ya mata
wani irin kyau kaman saboda ita aka qirqireshi,ya zuba idon hannu yana jujjuyashi
kafin a hankali yace.
"Our latest wrist watch...2025,kin masa kyau duniyata.....nayi accepting wannan
design din saboda ke,koda baiyi daidai da ra'ayin dealers dinmu ba,i love it for
the sake of you" Ya qarasa maganar a tausashe yana kai hannunsa yayi kissing hannun
nata,still idanunsa a kanshi,ya zura hannunsa a aljihunsa ya fiddo wayarsa ya
laluba wata number ya kira. Bugu daya aka dauka,da hausa taji yana magana.

"Mun siya design dinnan......sannan madam ta ninka price din da wasu dollars din
akai ainihin price din". Ya fada a nutse da alama yana magana da wasu ne

" Alright " Taji ya sake fadi yana katse kiran,yana maida wayar aljihunsa tana
dubansa idanunta a warwaje,sai daya daga kai sannan suka hada ido,fuska ta narke

"Wacce madam din?" Ta tambaya da siririyar muryarta dinnan,miskilin murmushi ya
sake mata

"Akwai wata bayan ke?" Saita sake fidda idanun

"Ban da kudin siya fa....thought dai bansan nawa bane"

"Amma kina da muhammad jadda ko?" Ya furta yana ja baya kadan idanunsa a kanta.
Yana jin dadin kallonta sosai,sai yakejin duk wata tsohuwar kewa ta rayuwarshi tana
sulalewa,yana jinsa wani sabon mutum na daban.

Duban hannun nata tayi,haka kawai taji kaman ya saka mata wani abu me
daraja da yawa,sai takejin hannun ya mata nauyi.

"Na gode.....na gode sosai" Ta samu kanta da furtawa a sanyaye. Wani tsadajjen
qaramin murmushi ya saki yana girgiza kansa.

"No.....no need duniyata.......ba irin wannan godiyar nakeso ba.....the only one i
want........" Sai bai qarasa ba ya mata nuni da shimfidadden gadon. Da sauri ta
juya masa bayanta tana kasa hada ido dashi,ta fahimci yana bawa abunnan muhimmanci
tamkar baisan kayan kunya bane?.

A nutse taji ana yafa mata abu ta baya,ta daga kanta sai taga wata
baqar sassalkar abaya ce,manal alhammadi shine tambarin da yake maqale a hannun
rigar,ta fidda idanunta tana jin wani abu yana girmamarta,ta taba jin company
din,wanda dukka abayas da yake fitarwa luxury ne masu tsada da aji sosai,ta sansu
ne saboda ita din masoyiyar abayar ce.

"Ba wani kunya tsakanin muhammad fu'ad da duniyarsa......ba kunya tsakanin muhammad
fu'ad da matarsa......abinda kawai yake buqata......madawwamiyar soyayya da zata
mamaye rayuwarsa.....ta bashi wani farinciki da nutsuwa daya rasa a
rayuwarsa.....duk da cewa ina zaqewa da yawa.......amma wannan abun nake bara" Ya
rigata fada kafin ita ta fada. Boyayyen murmushi ya subuce mata,wato daga jiya zuwa
yau ya fara haddace irin kalmominta kenan da take yawan maimaita masa?.

Juyo da ita yayi yana zura mata hannayen rigar ya furta

"Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen.....komai saikin masa kyau?" Yayi maganar yana
dage girarsa.

"Komai saina masa kyau?.....ko komai sai yamin kyau?" Ta tambayeshi tana mamakin
yadda yake juya maganar daga qarshe ta koma farko.

"Kece kike musu kyau basu keyi miki ba.....don dama kedin me kyau ce.....you're not
ordinary duniyata" Yayi maganar sanda ya dago daga tsugunnan balle mata button din
da yayi har qasa. Mayafin ya warware yayi mata lafiyayyen rolling tana tsaye tana
kallon ikon Allah,ya kama hannunta zuwa gaban mirror yayi tsaye a bayanta.

"Duk wani abu me daraja rufeshi akeyi a killaceshi" Ya furta a nutse yana duban
kyakkyawar fuskarta ta cikin madubin,yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa saboda
ita,kishinta yana sake ratsashi da kyau,yana sake jin tabbas......lallai ba wanda
zaisha ba kuma wanda zaici bulus daga cikin mutanen dake hannunsa a yanxu.......tun
daga kansu mashkur har zuwa kan zuwaira da bibo.

"Ga aro nan na baki.....idan munci abinci mun dawo zaki bani kayata" Ya fadi wannan
karon yana dan sanya seriousness saman fuskarsa. Dan dubansa tayi kadan,sai ya
gyada mata kai alamun tabbatarwa. Yanaso ne yayita kallonta,yanason wucewar kowacce
daqiqa tayishi bisa idanunsa,yanaso yaci gaba da kallon baiwa da ni'imar da Allah
yayi masa,yanaso su kasance a haka shi da ita......da zaiyiwu su qare rayuwarsu
cikin irin wannan yanayin na dagashi sai ita.

Yana maqale da hannunta suke sauka zuwa bangaren cin abinci,private ne
wanda ya dauko musu cook dinne musamman saboda iya su biyun. Sun samu dining room
din cike da cima kala kala,abincin Africa da wasu na Nigeria. Macace da batace ga
daga qasar da take ba,ta tarbesu cikin haba haba sannan ta fara serving nasu cikin
kulawa,lokaci lokaci tana magana da fu'ad da hankalinsa ke waya cikin yaren
Dhivehi,har ta kammala ta juya ta fita tana basu guri.

Juya spoon din take kawai a plate din tana hadiye wani abu a
qirjinta. Batasan meye ba amma ya tsaye mata a wuya. Bai ankara ba,sai daya gama
uzurinsa da waya sannan. A mamakance yake dubanta.

"Start mana madam....banason wasa da abinci fa?".

"Itama fareedan ce?" Ta tambayeshi da wani salo daya sanyashi karantar zallar
kishin dake kwance a idanunta,saidai kuma a sarari qwalla ce kwance saman oily eyes
dinsa,sai suka qara wani sheqi.

Dariya yakeson mata saboda wani irin farinciki yaji yana lullubeshi,tun
daga saman zuciyarsa yana sauka ta kowanne sashe na gangar jikinsa. Har ya fara
winning haka da wuri? Ya tambayi kansa yana taya kanshi murna,amma a bayyane sai ya
lanqwasa fuskarsa alamun tausayi.

"Me kuma nayi?". Muryarta na rawa kadan tace.

"Kunata magana da yaren da banaji.....tanata maka hira kana amsawa?". Wannan karon
kam kasa boyuwa dariyarsa tayi,abinda ya tunzurata kenan.

" Karki wuce gona da iri sabreen,karki rudu ki fada soyayyar abinda ba yafi qarfin
ajinki.....abinda yafi qarfinki,abinda baki da tabbas a kansa.....shin kin Manta
maamah tana nan?". Tambayar data tarwatsa duk wani qwarin gwiwa da take qoqarin
tattarawa kanta,taji kuma komai ya tsaya mata cak.

Dab da ita ya dawo ya zauna,ya kama hannayenta ya saka cikin nasa
yana matsawa a hankali.

"Kin taba ganin mutum ya canza DUNIYARSA?" ya mata tambayar kai tsaye,qasa tayi da
kanta don sai takejin tana son jefa rayuwarta cikin hadari ne kawai,muddin ta
sakewa zuciyarta ta fada sonshi to ba shakka ta fada babban tarko......babban
tarkon da zai bawa maamah daman walagigi da rayuwarta yadda taga dama.

"Amsar itace aah......ke duniyata ce,babu daman na sauyaki ko na hadaki da wata ko
wani abun......ni muhammad jadda naki ne ke kadai,don ke kadai aka halicceni.....ki
rubuta wannan ki ajiye"
_to zamu gani,anya hajiya maamah zata qyale kuwa???_


*ANNI*


Tun a jam'in sallar asuba da sukazo yi taga bata ga fu'ad ba.....still da
tace farouq ya turo mata shi komin dare baizo ba,har suka gama waya da abba Alhaji
hamza kibiya dake tashi umrar ta kwanta amma ba fu'ad din ba dalilinsa.

Sanda suka kammala sallar sai tayi zaune kawai tana lazimi,tunaninta
yana rarrabuwa,bataga fu'ad ba......bataga sabreen ba,duka ina suka shiga?. Ta wata
fuskar sai takejin relief na rashin ganinsu su duka biyun,don zuciyarta na qissima
mata wani abu,ta wani bangaren kuma bataso ta sake jikinta akan hakan,saboda tasan
wace mariya din.

Takwas saura farouq ya shigo gaidata. Yana daga zaune gabanta ya dan
dubi amna dake kwance tana shirin komawa bacci

"Ta duba qur'aninta kuwa?". Kai anni ta daga masa

" Ta duba" Sai ya jinjina kai. Wani sabo ne da raino data musu dukkansu,dole
kowacce safiya....komai uzurinka ko meye kakeyi ka fara duba qur'ani kafin komai.

"Kiramin fu'ad.....ka gwadamin dukka layukansa" Anni ta fadi tana gyara zamanta.

"Na gwada wani tun jiya a kashe,amma bari na gwada sauran" Farouq ya fada
hankalinsa kwance,don shi kam ya gama hasashen inda aka haihu a ragaya ma. Baya
tunanin ko maamah ta yiwa fu'ad farin sanin da shi yayi masa.

Daya bayan daya yabi layukansa yana kira amma kowanne gaya masa ake
a kashe yake,sai ya daga ido kawai yana duban anni da fuskarta ta shiga damuwa.

"To ina ya shiga?,ina kuma sabreen?". Dariyarsa ya danne yana dan saka alhini a
saman tasa fuskar shima

"Karki damu anni in sha Allah jikina yana bani suna tare,bari na tura masa email da
SMS duka" Ya fada yana fara rubuta saqonnin ya kuma aike masan kaman yadda yace,duk
da yasan zai wahala ya gani a kwanakin nan,lallai indai ya samu nasarar dauke
sabreen ne tofa sai baaba ta gani.


*MAAMAH*

Idan tace hankalinta a kwance yake daga daren zuwa safiyar tayi qarya.
Ta kirashi ta kirashi har batasan adadin sau nawa ba. Tabbas ta sani,a yanxu duk
duniya idan ameenatu tace itace mahaifiya ga fu'ad,kuma tana tuhumarta batan
sabreen ba wanda ya isa ya hana a daureta,ba wanda zai fiddata idan ba fu'ad din
ba,da sauran mutuncinta,bataso wasan ya qare a haka,saidai hakan ya sake ninka
qiyayyar anni sosai a ranta. Ita daya taketa shawa kanta alwashin saita yiwa
ameenatu abu mafi munin da ba zata tabawa mantawa da ita ba,idan don tayi wannan ne
don ta nuna mata iyakarta ne ganin suna qasar da ba tasu ba.....to tabbas ita kuma
zata bar mata wani babban tabo a rayuwarta da ba zata taba mantawa dashi ba.

Musaddiq ta kira ta sanyashi nema mata fu'ad din,saidai shima kiran
duniya wayar sunqi tafiya.

"Maamah wayoyinsa a kulle suke" Maganan data sake sakata a taraddadi da tunane
tunane iri iri.
"Kada fa ya zamana ameenatu ta salwantar mata da yaro ne takeson tayi garkuwa da
ita akan batun haka da wuri?" Wannan shine tunanin daketa mata kai kawo.

"Ya kamata ki xama cikin shiri.....ki xama a ankare.....karki nuna mata tsoronki,ki
tabbatar mata da.naki zargin kema" Abinda zuciyarta take nanata mata kenan,wanda
shine kuma ya bata qwarin gwiwa.

Cikin kwanakin sai ya zamana wani irin zama ake a gidan,kallo kallo
kawai akeyi tsakanin maamah da anni din. Duk da maamah tana cikin d'ari d'ari da
tunanin inda fu'ad da sabreen dinma suke......amma ta azawa ranta wani dakiya. Ta
fannin annin kowanne taku na maamah din saman idanunta yake,ba komai take dubawa ba
sai idanun yaransu da suke rayuwa guri daya,zai zame musu wani abu na daban kuma na
tashin hankali idan suka ga wani sabani muraran a tsakaninsu,banda hakan a shirye
anni yake akan maamah wannan karon.....duk da tana danjin relief idan farouq na
bata tabbacin fu'ad da sabreen din suna lafiya.

Farouq din ya fahimci abinda ke faruwa,saidai bai nuna musu komai
ba,yayi ma kaman bai sani ba,saidai time to time shima yana neman fu'ad din ta
waya,amma dif kakeji ko sau daya bai taba katarin samunsa ba.....a haka sannu a
sannu sai gashi an kwashe sati guda cif ba wanda yaji motsinsu ko yasan inda suke.

Zuwa sannan hankalin anni ya tashi sosai,kusan kullum sai tasa farouq
ya kira mata shi,mafi qaranci sau biyu a rana,saboda kwanakin barinsu Maldives
kusan za'a ce yayi,kwana uku ko hudu suka rage musi,gashi babu shi ba sabreen din.

Tun tana yiwa maamah din kara har abun yaci tura,ranar daya rage
kwanaki uku subar qasar,da wani yammaci suna parlor. Amna ke mata kalba saman dogon
gashinta da tafi masa kalba akan kitso,maamah tana daga gefe zaune tana kallo cikin
tv. Ta tsiri wannan zamanne kawai don ta nunawa anni ba abinda zai
tsoratata,hakanan itama me cikakken iko ce,duk da cikin rashin cikakkiyar nutsuwa
itama take. Ba sabreen ce ma damuwarta ba danta shine damuwarta,idan tana da damuwa
akan sabreen din bazai wuce na yadda take gudun kada anni ta fake da wannan ta
tozartata a idon duniya ba.

Farouq ne ya shigo da sallama,kaman yadda suke koyi da tarbiyyar anni da
umarninta,ya yiwa maamah barka da gida,ta amsa masa a d'age kaman yadda ta saba.
Mugun haushinsa takeji.....tana ganinsa a asalin tantirin munafuki tun daga
quruciyarsa kawo yanzu,kai tsaye zata iya cewa shine kanwa uwar gami da yaja mata
yaro cikin gidansu ya hadashi da mayun iyayensa da suka kasa sakar mata kurwar
d'a,suka hanata taci arziqin d'anta yadda ya dace. Ko a yanzun gani take cutar
fu'ad kawai yakeyi yana amfana da arziqinsa,yana tatsarsa ne shima.....ba wani tare
da suka samo arziqin,ba kuma wai iya harkar noma da kayan abinci yake wannan
fantamawar ba,dukiyar gold da diamond din d'anta ce.

"Farouq......kwanaki uku suka rage mana mubar Maldives.....ka samomin 'ya'yana?"
Tayi maganar cikin salon son isar da saqo ga maamah.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK

Please Login or Register in order to submit comment