You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Qara ta saki cikin tsananin azaba......azabar da bata hanata ci gaba da
qoqarin qwatar kanta ba,cikin sa'a santsin bedsheets din dana hijabinta suka
sanyashi ya zame zaman lallausar katifar,saita miqe itama,amma ta kuma zamewa take
fuskarta ta bugi gefan bedside din still.

Bata damu da radadin daya sake ratsata ba.....sake miqewa tayi tana
harin qofa,abinda ya lura dashi kenan shima ya miqe da azama,tana isa qofar shima
yana qarasawa sanda take kici kicin bude key din,ta finciketa ya watsar ya saka key
ya kulle qofar. A zafafe yabar bakin qofar yana nufar qofar toilet yana cewa.

"Yau zaki gane waye mashkur.....tunda baki zabi komai ya kasance ta hanyar maslaha
ba" Key din jikin qofar toilet din shima ya murza ya kulle,tana kallonsa sanda
take qoqarin sake tashi saboda buguwar da tayi a hannu da fuska,yadan bude window
din waje ya watsa Keys din sannan ya sake waiwayota.

"Kaji tsoron Allah mashkur......kada ka keta haddin aure.......da auren wani a
kaina.......ba bazawara ko budurwa bace!"
"Allah yasa tattabara ce ke" Ya fada cikin rashin damuwa yana durfafota da sassarfa
kaman me wasan motsa jiki.

Cafka ya sake kawo.mata ta sake samun nasarar gocewa abinda ya sake
qona masa rai,sai kawai ya zabi ya galabaitar da ita.....don duka alamu sun nuna
masa cewa gwana ce wajen iya zilliya,kada ta bata masa time ta kuma bata masa
plan,don haka yakai mata naushi.

Ya sameta ta kafadarta ne yayin da nashi hannun ya wuce ya daki
bango,abinda ya sanya wata azaba me tsanani ratsa kwanyarsa.

"Ouch!" Ya fada cikin tsananin jin zafi,yayin da zuciyarsa ta sake tunzura

"Ni xaki sanya naji rauni?". Yana kaiwa nan ya shammaceta yakai mata qafa ya
kwasheta,take ta fadi ta bugu da qasa.

"Wayyo Allah na" Ta fada cikin tsananin radadi tana riqe qugunta gami da runtse
idanunta. Wannan shine abinda ya bashi daman isowa gareta,ya kama bayan kanta inda
ta tattare gashinta tayi gammo dashi ya riqe gam. Wata azaba ta ziyarci tsakiyar
kanta zuwa qwaqwalwarta,ba shiri ta sake qwalla qarar da zuwa yanzu ta yanke
tsammani akwai me cetonta.

Yana riqe da kan nata ya turata har saman dressing table dinta,baiyi
wata wata ba ya buga goshinta samanshi,take goshin nata ya fashe,saidai kuma tana
dagowa ta dago da bedside lamp da akayi ado da ita saman mirror din ta kwatsa mata
ita tsakiyar kanta,abinda ya sanyashi sakinta ba shiri yana dafe da wajen.

Duk da wajen bai shafe ba amma take yayi wani malulu azaba ta shiga
ratsashi tako ina.

Ya kalleta sanda jini ya fara diga jikin sky blue din hijabinta yana
jin wani fushi mara misali yana saukar masa. Bai taba tunanin zaiyi minti biyar ba
daga sanda ya shigo dakin ba tare daya samu galaba a kanta ba,sai gashi yanzu
wankin hula yana neman kaishi dare...

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 57


57

_Daga abu hurairah RA yace,manzon Allah S A W yace "mafi falalar sallah bayan
sallar farilla itace sallar dare_

*_ga falala ga kaifi,biyan buqata kaman yankan wuqaπŸ˜„,Allah ya bada ikon jurewa_*


Ga mamakinta sai taga ya samu waje ya zauna yana mulmula wajen. Tsahon mintuna tana
tsaye tana kallonsa tana dafe da inda jinin keci gaba da diga bata da abun tareshi.
Ko na minti guda taqi yarda ta dauke kallonsa a kanta gudun kada ya mamayeta bata
shirya ba. Hannun nasa ya sauke,ya fidda kwalin wiwi,ya zari guda biyu ya kunna
musu ashana sannan ya sanya duka biyun a bakinsa ya soma zuqa cikin gwanancewa.
Yadda ya tsara zaiyi da ita sai yaji me yasa bai taho da kayan mayensa ba?,ko banza
yafi samun kalan nishadin da yakeso?,ya yanke ya fara zama yasha wiwi dinne don
yadan huce kadan ta yadda zaifijin gardin abun.

Tunda ya kunna wiwi din hankalinta yayi mummunan tashi. Ta san tabbas
zata shiga wani mummunan yanayi ne da idan batayi wasa ba xai galabaitar da ita.
Asthma dinta,ba kalar hayaqin dake saurin tayar da ita irin hayaqin wiwi taba da
shisha. Matsawa baya ta dinga yi tana duban yadda hayaqin ya fara gauraye
dakin,yana canxa yanayinsa daga ainihin qamshi xuwa gurbataccen warinta maras dadin
shaqa.

Dukka hijabin ta cukuikuyeshi tana rufe hancinta dashi,a hankali tana jin
yanayinta yana son ya fara sauyawa.

"Zaki fahimci abinda ake nufi yau da asalin fyade" Kamar mugun dawa haka ya miqe
zumbur ya kuma nufota,ta juya itama da nata hanzarin da nufin barin gurin,saidai
tuni ya miqa hannu ya danqo hijabinta ya dawo da ita gabansa tana fuskantarsa.
Yadda take qoqarin toshe hancinta a nasa tunanin ya karanci batason warin wiwin
ne,don haka ya zuqeta sosai ya kuma soma fesa mata ita saman fuskarta. Kauda kanta
tayi sosai tana dauke numfashin da zuwa sannan tana jin kamar ya fara daina isarta

"Ba wannan hijabin ba?" Ya fada yan yamutsa hijabin cikin hannunsa,abinda ya sanya
ta takurewa gaba daya guri guda tana qoqarin neman hanyar da zata samu iska me kyau
gudun gushewar hankalinta,wanda wannan na daya daga cikin damar da zai samu
cikakkiya kan ya aikata komai hankalinsa kwance.

Wata wawiyar zuqa ya yiwa wiwi din ya sake fesa mata kan fuska,sannan
ta birkitota gaba daya yana kici kicin fincike hijabin daga jikin ta.

Dole ta daga fuskarta,duk da yamutsewar hazon dakin dole ta bude kafofin
shan iskarta ta fara masa magana a rarrabe

"Kada ka ketamin haddi na,kada ka lalatamin mutuncina" Tayi.maganar sanda ya samu
nasarar salube kan hijabin daga kanta. Bayyanar sassalkar sumarta ya sanyashi sake
gigicewa,bai taba tunanin ta mallaki suma har haka ba.

"Wow" Ya fada yana qoqarin samun wuyan hijabin don itace hanya mafi sauqi da zata
bashi damar tsarge hijabin cikin sauqi daga jikinta. Ta fahimci abinda yake shirin
yi,saita tattara dukka dan qarfinta ta cukuikuyeshi da kyau tana kiran sunansa
cikin qaraji gami da fadin

"Kada ka aikata!.....ka qyaleni mashkurrrr!!!!".

A hankali ya bude idanunsa wadanda basu sauka akan komai ba sai agogon
dake gefan gadon nashi. Idanu ya zuba mishi kafin ya miqa hannu a hankali yana
jawoshi yana duba time da weather na gari. A nan yaga alamun saukar ruwan sama,sai
ya maidashi sannan a hankali ya furta addu'a yayin saukar ruwan sama
'ALLAHUMMA SAYYIBAN NAFI'AN'.

A nutse ya tashi daga kwanciyar,ya motsa kadan yana sauke qafafunsa daga
qasan gadon wanda suka sauka daidai bedroom slippers dinsa yana jin yadda gaba daya
ciwon kan da yakeji din ya sauka. A yanzun tsabar ta'ammali da home remedies ya
sanya ba kasafai ya fiya afawa kansa qwayoyin bature ba yayin zazzabi da ciwon kai
ba.

Miqewa yayi ya fara takawa zuwa qofa yana mamakin yawan baccin da
yayi,yadan shafi cikinsa yana jin yadda yunwa ta fara yamutsa hanjinsa,don haka ya
yanke shawarar ya sauka qasa kawai yaci abinci,yadan duba ayyukansa koda na awa
biyu ne kafin ya sake kwanciya.
A parlor ya tsaya ya duba wayarsa,ya samu tarin miscal amma ciki na
farouq yafi yawa,ya samu saqonsa da yake masa mita akan bai bada komai na tafiyarsu
ba bayan saura sati guda. Qasan zuciyarsa kawai yayi murmushi yana sauka daga duba
saqonnin. Har ya aje wayar wani tunani ya fado masa,sai ya tsaya ya zubawa qofa
idanu.

Yana tuna tahowarta ne jiya daga bedroom dinta zuwa qofan falo.
Tabbas idan idanunsa ba qarya sukayi masa ba kallo yaga tanayi.

"A ina ta samu waya?,waye ya bata waya?" Ya yiwa kansa tambayar a bayyane yana
zurfafa nazarin ta inda zata samu waya tana cikin gida.

Kaman yadda ya sanya doka ya sani ba wanda ke shiga gidan,sai amna da
tazo baifi sau biyu ba. Amna kuwa yayi imanin ba zata taba bata waya ba musamman
idan ta gaya mata shi ya karbe. Duk abinda yayi ko ya aikata amna tasan yana da
dalili,ta fita saninsa,so ba zata karya dokarsa ba.

Kai ya jinjina yana tuna fitar da tayi ba tare da sani ko izininsa ba
rannan,tabbas wayar tana da alaqa da wannan fitar duk da ya bincika babu wani abu
da yayi kama da gurin wani taje.....amma how and when ta samu waya?.

Tambayar data masa susa kenan a qirji. Yanaji kaman ya kamata ya
maida hankali a saka CCTV din. Company din yazo har sau biyu shi yace su bari ya
zama free ya kirasu,yana jin kamar gamsuwa daya fara bawa kansa don tana karatun
addini sosai a yanzu ta hannun jikar malam.....kaman bai kamata ya bata amanna har
haka ba.

Da wannan tunanin ya bude smart door dinsa,ya kuma fara sauka zuwa
qasa.

Abinda ya soma bashi mamaki shine jin gaurayar wani qamshi qamshi me
kama da wari wari da gauraye stairs din. Koda ya kawo qarshenta sai yaji warin yana
dada qarfi,ya tsaya cak yana buda hancinsa sosai,a nan yaji daga inda warin yafi
qarfi.

Mamaki ya kamashi sosai,yana da wani irin experience na iya hasashen
abu da gano sauyawar motsi ko yanayi kaman wanda ya karanci aikin binciken tsaro na
sirri. Fara takawa yayi zuwa cikin hallway din a hankali,yana sake shiga ciki
xarginsa kuma na sake qarfafa saboda daduwar warin da sai a sannan ya fahimci warin
wiwi ne.

"Wiwi?" Ta maimaita sunanta can qasan maqoshinsa sanda ya iso bakin qofar dakin.

Tsaiwar da yayi duka baifi ta minti guda ba,amma sai yaji jikinsa bai
aminta da dakin ba,baya buqatar yayi knocking don ba qa'idar bincike bace akan
abinda kakeson ganin gaskiyarsa quru quru,juyawa yayi da sassarfa yana tuna inda
yaga an tanada a dakin nasa saboda ajiye kowanne key na kowacce qofa ta gidan a
matsayinsa na mamallakin Master bedroom.

Dubawa daya ya hango master key,sai ya daukoshi yana juyawa gami da
saukowa kai tsaye yana nufar hallway din.

Ta riqe ya riqr,yaja taja,har daga baya ya fahimci kamar hayaqin wiwin
din kawai ke iya bugar da ita. Hakan ya sakashi tsugunnawa ya dauki guntuwar data
rage,ya jata da kyau ya fesa mata a fuska. Numfashin ta ne ya soma yankewa,ta
jawoshi da wani irin hanzari tana tuna komai zai iya faruwa idan ta sake ta rasa
numfashinta. Ci gaba yayi da bulbula mata tana ci gaba da riqe numfashin nata da
taimakon hasbunallahu wa ni'imal wakil da take ambata cikin maqogoronta.
Dariyar mugunta ya saki,sai kuma yace

"Are you asthmatic?" Bai jira komai ba ya danna mata wiwi din a baki,abinda ya
birkitata kenan ya sanyata hautsinewar da batasan sanda ta daki al'aurarsa da
gwiwar qafarta ba,tsananin zafi ya sakashi sakinta gami da hankadata....dukka
jikinta ya gama saki,numfashinta kuma yayi qaura daga gangar jikinta,wannan ya
sanyata tafiya luuuuu bakin qofar dakin,wanda haka dama ya saita da nufin fuskarta
ta daki qofa ta kuma suma kafin ya gama daidaita radadin daya ziyarceshi.

Saidai kuma tana isa bakin qofar sai yayi daidai da sanda ya murza
handle ya bude,abubuwa biyu duka dakeshi,warin wiwi da fadowarta qirjinsa da guntun
wiwin a bakinta,sulalewarta a jikinsa ya sanyata ta gangara ta fadi ta gefen
bakinta,ta qarasa zubewa a jikinsa unconscious.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 58



58

_Daga ibn abbas RA,manzan Allah S A W yace"duk wanda yaji kiran sallah baije yayi
sallar ba(ya zauna ya yita a gida).to bashi da sallah,saidai idan wani uzuri ya
hanashi fita(kamar yanayin firgici na rashin tsaro ko tsoro)_


Dukkanin hannayensa ya sanya tallabota jikinsa yana bin guntun wiwin din daya fadi
da kallo. Maido dubansa ya sakeyi fuskarta cikin wani irin yanayi dashi kansa
baisan yadda zai fassarashi ba,sannan ya sake daga kansa yana bin mashkur dake
tsaye da wani birkitaccen kallo. Na wucin gadi tsaf tunaninsa ya tsaya kafin
qwaqwalwarsa ta dawo da aiki,yayi hanzarin maida dubansa fuskarta da take bayyanar
da gushewar numfashi a tattare da ita.

Tattarota yayi sosai sannan ya dagata cak yana jin wani abu yana zagayaw
a gangar jikinsa. Waye wannan cikin dakinta?,waye wannan da yanayin da ya tabbatar
masa ba mutumin kirki ko aziqi ne ba.....me ya kawo qaton gardi cikin tsakiyar
dakinta daya kaure da mummunan warin wiwi. Duka yana da buqatar wadannan
amsoshin,to amma kuma hankalinsa ya rabu gida biyu yana jin kamar ya fara cetar
numfashinta da ya dauke shine abu mafi muhimmanci na farko a tare dashi.

"Ina zakaje da ita?" Muryar mashkur dake a shaqe ta sauka a kunnuwansa sanda ya
fara dosar qofar dakin da ita. Wani mahaukacin mamaki ya kasheshi daya sanyashi
waiwayowa ya zubewa mashkur idanunsa. A karon farko kaifin birkitattun idanun fu'ad
din suka ratsa nasa jijiyoyin idanun suka kuma aike saqo ga sassan jikinsa,saidai
kuma a yadda yakejin zuciyar tasa a tsike......ba muhammad jadda ba...koma waye zai
iya fito na fito dashi indai akan cikar muradinsa ne.

"Shawara zan baka ka ajiyeta ka rufe mana qofa......don ba suma ba......ko mutuwa
tayi tabbas sai na biya buqatata a kanta.......ita ta kira wannan ruwan.......ita
ta kira fitina a sanda fitinar take bacci". Wani dummmm fu'ad yaji kunnuwansa sun
masa na wani lokaci,take wani irin gumi ke dumi ya soma fesowa ta kowacce kafar
gashi ta jikinsa. Idanunsa suka soma sauya launi tamkar an diga jan zabibi a
cikinsu.

Murna da mamaki suka cakude suka saukarwa mashkur sanda yaga ya sake
turo qofar dakin yana dawowa. Saidai shakku sun cikashi a sanda yake tuna waye
muhammad fu'ad?......wanne risk ya tsallake kafin ya zama abinda ya zama
yanzu?,kafin ma ya mallaki asalin abinda ya zama shine silar arxiqinsa a yanxu?.

Kyakkyawar ajiya yayi mata saman sofa din,da wani irin zafi ya miqe
yana nufar inda mashkur yake tsaye yana danne da inda ta doka masa bedside lamp da
har yanzu wajen yake masa matuqar zugi.

Tun daga yadda idanunsa suka jirkice da kuma yadda jikinsa yake wani
irin shaking hankalin mashkur ya fara dawowa jikinsa.

"Dakata!......kada ka qaraso nan wajen!" Mashkur ya fara da qarfi shima yana
qoqarin ciro bindigar dake maqale a qugunsa.

"Waye kai?!" Fu'ad ya watsawa mashkur tambaya da sautin tsawar data sanya dukka
dakin ya dauki amsa kuwa ba tare daya damu da bindigar dake riqe a hannun mashkur
din ba.

"Sanin koni wanene bazai maka amfani ba......abu daya zan baka shawara kaman dai
dazu,ka juya ka fita salin alin ka barni da ita". Kalmar tasa ta qarshe ta sake
zamantowa tamkar digar ruwan dalma saman sabuwar fatar jariri. Ya daga qafarsa ya
soma takawa da wani irin fushi zuwa inda mashkur ke tsaye idanunsa na sake ninka
rinewarsu,kai kace bai fahimci da gaske bindiga bace a hannun mashkur ba.

"Waye kai!!!" Ya sake maimaitawa kaman zai tsaga dakin da muryarsa yana jin wani
bala'i daga saman zuciyarsa. Takowar tasa da yadda yake durfafarsa ba wani sauran
tsoro......yana tunkararsa ne kai tsaye kaman bindigar wasan yara ce riqe a
hannunsa bata gaske ba shine yake saka dulmiya mashkur a matsanancin
mamaki......mamakin da yake qarasa dauke ragowar duk wata nutsuwa dake jikinsa yana
kuma dagula masa lissafi da Kalar jarumtar da yake hange tattare dashi.

"Ina sake gaya maka,kaman yadda ta jawoni rayuwarta......yau ko zaka mutu sai na
kwanta da matark......." Bai samu daman qarasawa ba saboda saukr kwalbar turare
saman daidai bakinsa,ta kuma fashe a take,abinda ya bata daman yankan wani sashe na
fuskarsa.......ya kuma sanya jini soma diga.

Saukar kwalbar a fuskarsa ya sanya bindigar subucewa daga hannunsa.
Jinin daya soma diga a fuskarsa baija hankalinsa ba fiye da faduwar bindigar daga
hannunsa. Yayi imani bashi da garkuwar data wuce masa bindigar,kuma muddin ta
subuce masa to tabbas dukkan wata dama ta subuce masa,tuna wannan ya sanyashi
durqusawa ya saka hannu yana laluben inda ta tsalle ta fadi.

Daga can gefan gadon ya hangota,da azama da kuma sassarfa ya zura
hannunsa da zummar daukota,saidai kuma ya makara,don yana dora hannunsa akai qafar
fu'ad na sauka saman hannun nasa.

Da dukkan qarfinsa ya take masa hannun,wani irin zafi da radadi suka
ziyarceshi yana jin kamar dukka yatsunsa biyar sun karye. Daya hannun nasa mashkur
ya sanya da nufin ture qafar fu'ad din,amma ta nan ma ya rigashi ta hanyar sanya
daga qafar tasa ya daki tsintsiyar hannun fu'ad din,bai kuma bari radadin ya gama
ratsashi ba ya sake take daya hannun da dole ta sakashi ya zare hannun daga saman
bindigar. Da qafa fu'ad ya daki bindigar ta qarasa shigewa can qarqashin
gadon,abinda ya daga hankalin mashkur kenan
"Komai zai iya kwabemin......dole na samu abinda nazo nema koda guda daya ne cikin
biyu...." Bai qarasa qulla mafitar data dace dashi ba wani kyakkyawan naushi ya
saukar masa a tsakiyar kansa.

Azaba ce ta ratsashi tun daga tsakiyar qwaqwalwarsa har zuwa tafin
qafarsa,bai murmure ba wani lafiyayyen naushin ya sauka a kumatunsa. Qarfin naushin
ya sakashi yin baya,yayu taga taga zai fadi ya dire da qafarsa. Cikin abinda bai
gaza second daya ba yaji wani abu me yauqi da gishiri ya cika masa baki,dole ya
hadiye ko ya zubar wanda zubarwar yakejin zaifi masa,sai ya furzar din yana jin
yadda kansa ya sake qullewa da azabar data zarce har cikin bakinsa. Furzar da jinin
saman marbles din ya bada sauti,saiga haqoransa nan jere reras guda hudu da
haskensu ya bayyana cikin jajur din jinin.

Idanu warwaje yake duban fu'ad,ya tabbatar ya masa illa ta farko
kenan da har ya mutu da ita xai tafi lahira?,zuciya ta ciyosa,ta yaya yana namiji
shima haka ya tsaya ya masa irin wannan barnar,wannan tunanin ya sanya koda yakai
masa naushi na uku ya kauce ya naushi iska,sannan kuma hannunsa ya zarce zuwa ga
glass din madubi dake daura da wajen,take ya tarwatse zuwa piece's,ya kuma samu
lallausar fatar hannunsa ya yanki inda yakeso. Cikin qasa da second daya shima jini
ya soma diga da mugun gudu a a tafin hannunsa da bayan hannun nasa,wannan shine
abinda ya baiwa.mashkur qwarin gwiwa,ya kuma Tunxura fu'ad ya sake kai masa wani
naushin ba tare daya damu da jinin da yake zubarwa ba. Ya sake samunsa still a
wuyansa,zuwa sannan qaramin fitsari ya qwace ma mashkur saboda azabar da yaji ta
sauka akan kowacce jijiya tashi. Yanke hukuncin maida martani yayi,cikin nasa
fushin yakai masa nasa naushin yans cewa

"Bari na nuna maka iya tawa bajintar" Saidai baiko qaraso inda yake ba ya yiwa
hannun nasa wani mummunan bugun da sai da yaji qarar qaramin qashin dake riqe da
tsintsiyar hannun nasa.

Wani ihu ya kwarara don azaba,ihun da lallai inda qaramin gida ne
wala'alla har jama'ar dake farkon layinsu sai sunji......sautin ihun nasa ya samu
ratsawa tsawa ta kowacce kafa dake dakin,ta kuma isa ga kunnen daya daga cikin
securities na gidan dake on duty a daren,yaketa kuma kai kawo domin tabbatar da
tsaron gidan da amincin masu gidan.

Tsayawa yayi sosai yana son tantance daga inda qarar ya fito,a
lokacin fu'ad ya sake isa inda yake ya kuma daki gwiwarsa da qafa,abinda ya
sanyashi zubewa saman gwiwoyin nasa shima yana sakin ihu karo na biyu saboda yadda
yaji qoqon gwiwarsa kaman ya fice fit daga jikinsa.

"Zan saka kayi nadama,zakayi dana sanin abinda kakemin......wallahi sai na d'an
d'ani xumarta kamar yadda kuma kuka d'an d'ana......saina huce fushina a kanta,sai
nayi mata fata fata......" Wani mulmulallen abu me kama da wuta yazo ya daki
zuciyarsa,har baisan sanda ya sake saka hannu yakai masa dukan daya sanya haqoransa
na gaba wannan karon suka baqunci waje ba yana wani irin huci kamar tsohon kumurci.

A gigice ya sake fidda idanunsa yana kallon haqoransa guda biyar
zube a gabansa cikin jini,a qiyasi ya rasa haqora aqalla goma sha biyar,sha biyar
suka rage masa a baki......sai ya saki wata kururuwar data tabbatarwa security din
daga cikin gidanne.

Wayarsa ya zaro ya fara kiran number gaggawa ta cikin gidan,saidai
kiran daga parlor hallway xuwa sassansa ya tsaya,bai kawo dakin sabreen ba saboda
datse layin da mashkur yayi. Cikin gunji duk da yadda jini yake ambaliya a bakinsa
amma bai fasa duban fu'ad dake jawo wata cable me kauri ba yace

"Saina lalata rayuwarka......sain......" Maganan ta katse saboda wani naushin daya
sake xuba masa a tsakiyar kai,take wuta ta dauke masa,sashen maganarsa kuma ya
dakata na wucin gadi,sannan ya tafi yifff ya fada akan jininsa jikinsa yana
saki,komai baya aiki illa numfashinsa dake fita a wahalce.

Da qafa ya dakeshi ya juyashi,ya tsugunna yana sanya cable din daga
hannunsa zuwa qafafunsa,sai daya tabbatar ya daureshi sosai sannan ya fara jansa
kaman mushe ko kayan wanki yana bude dakin ya fiddoshi.

Sai daya kawo parlor na biyu sannan ya zubeshi a tsakiya. Jijiyar
kansa na wani mugun gudu da harbawa ya qarasa gaban telephone ya fara kiran sashen
tsaro na gidan.

"Yes sir......" Security din dake tsaye yana jiran kota kwana ya fada sanda kiran
fu'ad ya riskeshi.

"Ku bincika min cikin gidan nan da kewayensa.......ina kyautata zaton akwai wani
mutumin daban.....na baku minti goma kacal" Yadda yaji muryar boss din nasu a yau
sai yaji wani tsoro da razani ya kamashi,bai taba magana dasu da irin wannan sautin
dake cike da fushi da tsawa ba. Maida wayar yayi sannan ya matsa cikin hikima ya
qyasawa abokin aikinsa.

A zuciye ya wurgar da kan wayar,sannan ya juyo yana takowa zuwa inda
ya ajiye mashkur.

Zagayashi yayi har kusan sau uku,zuciyarsa na masa wani irin tsalle a
qirji,ba abinda zuciyarsa ke gaya masa illa ya dauko bindigar ya fasa tsakiyar
kansa da ita. Numfashi yaja sosai,sai ya juya yana komawa ciki bayan tunawa da yayi
da ita,sa'annan muddin yaci gaba da zama a gaban mashkur zai harbeshi dinne abinda
yaketa qoqarin hana kansa aiwatarwa.

A bude qofar dakin yake,wannan ya bashi damar shiga kansa tsaye. Dakin
da zuwa sannan gaba daya komai na cikinsa ya hargitse,banda fasasssun glass da
kwalaben fitilar data kwatsawa mashkur ba komai a qasan,sai wargatsatstsun kayan
dake saman dressing table dinta da suka tarwatse a qasa.

Inda take kwace ya maida idanunsa,har yanzu tana kwance inda ya barta
din,idanunsa kafe a kanta ya qarasa gabanta. Sauka idanunsa yayi a saitin
bakinta,pink lips dinta da suka sauya launi kadan suka kuma bushe qamas,hoton yadda
wiwin ta zauna akan lips dinta ya dawo masa,wani mulmulallen abu ya tokare masa
wuya,da sauri ya ture hoton daga kwanyarsa,ya tsugunna a gabanta yana tunanin me
zaiyi mata?,me ya kamata ya fara yi?.

Sake maida dubansa yayi ga fuskarta wadda har dogon dokin wuyanta ya
bayyana,hakanan wani sashe na kafadunta saboda saukar hijabin da ya fara samun
nasarar yagawa. Sauka dubansa ya qarayi xuwa saitin qirjinta,inda a daidai nan
hijabin ya nuna muguwat cukuikuyewar da zata gaya maka an riqe wajen ne da mugun
riqo. Qirjinsa yaji ya wani doka,yawun bakinsa kuma yaji ya dauke qaf kaman ba'a
taba halittar yawu

Please Login or Register in order to submit comment