You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma tsoron fitinar maamah
yana neman dakushe masa komai,duk da yaji cikin ransa ruwa da iska.....ko zaa saka
kanshi gabas a yanka bazai iya rabuwa da auren amna ba.

Qofa yasa aka bude masa ya nuna masa hanya,musaddiq ya kalli fu'ad din
sai ya sauka salin alin daga motar,yasan ba lallai a yanzu ya wani bawa ban
haqurinsa muhimmanci ba.

Abu guda daya tak daya tuna yaji ya kwaranye masa duk wani bacin
ransa.....cikinsa dake kwance cikin mararta wanda ita kanta batasan dashi
ba,murmushi ya subuce masa ya sauka a hankali daga cikin motar yana komawa
asibitin.

A hankali ya tura qofar falon yana shiga,idanunsa suka fada kan anni.
Tana tsaye da takarda a hannunta tana dubawa,shigowar tasa ya sakata daga kai ta
kalleshi.

Wani kwantaccen farinciki me ban mamaki ya gani saman fuskarta wanda
bai taba ganin irinsa ba. Ya zare idonsa yana duban takardar sosai. Takardar dazu
ce da maamah ta saki,take ya fahimci dalilin wannan murmushin,kawai sai ya shafa
sumar kansa,karon farko yaji kunyar annin ta saukar masa,ya taka da dan hanxari
yana wucewa cikin dakin.

Sosai murmushi ya subuce mata,ta saki sassanyan ajiyar zuciya tana jin
zuciyarta na wankewa daga dukkan wata fargaba da bacin rai.

"Ubangiji ka rabasu lafiya,ka yiwa abinda aka samu albarka" Ta furta a sarari tana
ninke takardar.

Wani sanyi ne yaji yana ratsa zuciyarsa sanda yayi ido hudu da ita.
Tana zaune tsakiyarsu huda......haneefa tana gefanta a zaune hannunta cikin nata.
Hira sukeyi irin hirar da kana kallon fuskarsu zakasan qauna da soyayya gami da
shaquwa irinta 'yan uwantaka ta huda su. Murmushi ne kawai ke fita a fuskarta,wani
irin murmushi da yake sake qawata fuskarta da wani irin lallausan kyau me daukan
hankali.

Jingina jikinsa kawai yayi da jikin qofar,ya langabar da kansa yana
qare mata kallo. Kallo yake mata irin kallon da mutum yakewa DUNIYARSA a sanda tayi
masa dadi.....irin kallon da mutum yakewa ruhinsa a sanda yake tsananin buqatarsa
da kuma sonshi. Duniyarsa rayuwarsa dama nutsuwarsa gaba daya yake gani tattare da
ita.

Daren jiya yake tunawa,wani irin dare me tsayawa a tsakiyar zuciyar
masoyi,ta shayar dashi wani zazzaqan abu da bai taba hasashe ko mafarkin akwai
irinsa ba sai a lokacin.
Cikin jikinta ta dinga jin kamar akwai wani ido na musamman dake
kallonta. A hankali tayi slow da hirar tana watsa idanunta cikin dakin,sannu a
hankali ta hango fuskarsa a tsakiyar qofar yana qare mata kallo. Murmushi ya sakar
mata wanda ya qara mata nauyinsa,sai ta danyi qasa da kanta,shi kuma ya tura qofar
gaba daya yana shigowa.

Tsam momma ta miqe tana fadin

"Qaraso mana......dama masallaci nakeso mu wuce ai,ita ta riqemu wai lallai zamu
barta ita kadai,tunda gaka kazo alhamdulillah" Momma ta fada cikin yanayi na
surukuta tana maida takalmanta.

A nutse ya qarasa gaban gadon ya bawa haneefa dake zamowa tana sauka
daga saman gadon hannu fuskarsa qunshe da murmushi yayi bump din hannunta data miqa
masa yana kuma amsa gaisuwar huda da basu hadu da ita dazu ba

"Muna da meeting anjima" Ya fada yana dubansu,sai suka sanya dariya suna bin bayan
momma bayan sun amsa masa da

"Yes hamma". Shi da ita duka da kallo suka bisu har suka fice,shine ya fara dawo da
dubansa kanta kafin itama a hankali ta maida duban nata kanshi.

"Karki ma fara cewa zaki tambayeni akan mene" Ya rigata fadi,sai murmushi ya qwace
mata tayi qasa da kanta.

Idonsa ya lumshe a kanta sannan ya taka a nutse ya jawo kujera zuwa
gaban gadonta. A hankali ya zauna yana sake matsowa kusa da ita har gwiwoyonsu na
gogar na juna,ya saka lausasan tafukan hannayensa a nutse ya kamo nata cikin nasa
yana murzawa a nutse.

"Ameenatu" Ya kirata a tausashe murya a karye kaman wanda baison kowa yaji
sirrinsu. Kiran da yayi mata har cikin tsokar naman jikinta,ya kuma aike mata da
saqo ta cikin jinin dake gudu a jijiyoyin jikinta. Labbanta ta motsa kadan tana
amsa masa da
"Na'am" Sai ya lumshe idonsa labban nata suna daukan hankalinsa.

"Ina dauke da wani albishir ameenatu,yayi girma da nauyi sosai a qirjina" Ya qarasa
fada yana zame hannunsa daga cikin nata,sannan ya maida kansa ya kwantar saman
cinyoyinta kamar wani qaramin yaro.

A hankali ta daga hannunta ta dora saman sumarsa tana nutsa yatsunta a
ciki,laushin sumar da santsinta suka ratsa yatsun nata,sai suka sauke ajiyar zuciya
lokaci guda shi da ita kowa yana jin soyayyar dan uwansa tana keta jininsa.

"Ameenatu wannan zuciyar da wannan gangar jikin duka naki ne.....kulawarki take
buqata kici gaba da bata muddin kinaso ta rayu yadda ya dace" Ya fada yana jin
yadda bugun zuciyarsa ke daduwa daga yadda take yamutsa sumar kansa kawai.

"Zaka samu sabreen fiye da yadda kake fata.....zaka samu dukkan wani cikar
burikanka a tattare da ita.....harma abinda tunani bai taba baka ba". Maganarta ta
tsumashi sosai,ta kuma sakashi daga kanshi daga cinyarta. Idanu ya zuba mata sosai
yana kallon qwayar idanunta,sai itama ta samu kanta da mannewa kallon nasa,kafin ya
miqe a hankali tsaye a gabanta.

Hannuwansa ya miqa mata,sai itama ta aza nata ciki ya tashe tsaye
sannan ya buda qirjinsa ya sanyata a ciki ya maida hannuwansa ya lullubeta da kyau.

Ajiyar zuciya ce ta subuce masa,ya kwantar da kansa saman kafadarta.
"Sabrrrrr........kinsan kin bani wata kyauta da ba wani dan adam daya taba bani
makamanciyarta?" Ya soma da jefa mata tambayar data kasa gane ma'anarta. Shurunta
ya fahimtar dashi cewa ya sanyata a duhu,don haka ya zare jikinsa a hankali sannan
ya juyata ya rungumeta ta baya yana sake nutsata sosai cikin jikinsa. A tausashe ya
dora duka tafin hannunsa saman mararta,ya dora habarsa saman kafadarta yana saka
tausasan labbansa saitin kunnenta.

"Sabrrrrr......you're pregnant......ciki ne dake,cikin muhammad jadda......zaki
zama uwar 'ya'yana ameenatu". Wani irin abu ne ya tsarga mata tun daga tsakiyar
kwanyarta har tafin qafarta,bugun zuciyarta ya qaru sosai. Samun kanta tayi da saka
nata tafin hannun saman nasa dake mararta tun dazun,ta kasa fadin komai,don duk
kalmar data kamo sai taji ta qwace mata,tana ci gaba da sauraren saukar numfashinsa
cikin kunnenta.

"Are you happy sabrrrrr?" Ya tambayeta a raunane yana fatan ya sameta cikin irin
yanayin da yake jin kansa shima.

Kai ta gyada a sanyaye,tanajin wani irin yanayi yana ratsata,mamakin
yau itace wai dauke da ciki?,itama zata zama UWA?,zata haifi d'a ko 'ya a
cikinta?,abun kamar cikin mafarki.

"Alhmdlh" Ya fadi yana sauke mata tattausan kiss a wuyanta,a hankali kumya ja dawo
da ita tana facing dinsa sai ya rungumeta tsam a jikinsa.

Shuru ya ratsa tsakaninsu na sakanni,tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa
ta cikin kunnuwanta dame kwance a qirjinsa,sosai kaman akwai wani abu dake taba
zaman lafiyarta,kusan minti biyu sannan ya sauke sassauqar ajiyar zuciya a sanyaye
sannan ya dagata daga jikin nasa yana kallon fuskarta. Qwayar idanunta ya laluba ya
saka nashi a ciki,da wani irin coolness ya sake kiran sunanta.

"Kinji yadda zuciyata take bugawa ko?" Ya jefa mata tambayar yana lalubar tafin
hannunta ya matse gam cikin nasa. Kasa amsa masa tayi da baki sai kai data gyada
mass,saboda cikin idanunsa abubuwa ne masu yawa ta gani suna yawo.

"Sabrrrr.....na gode da kika karbi ajiyata da sauri haka......inajina kaman ni
kadai nake rayuwa cikin duniya......ashe rashin haduwa da tawa DUNIYAR shine
sila......sabrrrr......bansan dame zan saka miki ba......bansan kuma da meye zan
gode miki ba....kome na kalla sai naga kamar yayi kadan,alfarma daya kawai nakeso
ki yiwa rayuwata.

Kallonsa da kalamansa gaba daya qara kashe mata jiki sukeyi,mamakin
irin tsananin son da yakewa yara ne yake sake kamata,ta motsa labbanta a hankali

"Tame?"

"Kiyimin alqawari zaki rayu dani....kiyimin alqawari ba zaki taba rabuwa dani
ba.....kiyimin alqawari zaki zauna dani,da dadi ko babu.....cikin wadata ko
talauci.....sabrrrr kiyimin alqawari ba zaki taba tafiya ki barni da yara
ba.....zaki zauna dani dasu a duk yadda nake ko suke,mu rainesu tare.......kiyimin
wannan alqawarin sabrrrr cikin wannan garin me tsarki". Idan ba qarya idanunta
sukayi mata ba hawaye ne kwance cikin idanun muhammad jadda din......taja numfashi
sosai har kaman kayan cikinta zasu hade waje daya. Ita daya ce mutum na farko a
duniya data taba ganin wadannan tsadaddun hawayen da suke zuba SILAR QAUNA daga
idanun me jadda......tana fata ta zama mutum.na qarshe da zata gansu,kuma ta zama
sila na goge hawayen daga idanunsa gogewa ta har abada.

Abu daya ta lura dashi har yanzu yana da tsoro game da halin
mata......har yanzu wannan ciwon da maamah ta dasawa rayuwarsu yana masa zugi da
radadi.....har yanzu yana jin kaman abinda ya faru da abbansu zai faru dadshi,a
yanzu haka a shirye take ta goge masa dukkanin wannan fargabar da shakkun,don haka
ta zame hannuwanta daga nashi,ta sulale tana duqawa saman gwiwoyinta,sai ya gaza
tsaiwa ya silale shima ya bita.

Hannuwansa ta riqe da kyau tana kallonsa cikin tsakiyar idanunsa.

"Allah ya zama shaida.....annabin Allah ya zama shaida,ni ameenatu sabreen na
shirya rayuwa dakai da dukka abinda zamu haifa......na sadaukar maka da dukka
rayuwata sadaukarwa ta har abada......dadi ko wuya sunyi kadan su raba
tsakaninmu.....zan zauna dakai tamkar dominka kadai aka halicceni,bazan barka ba
muddin bakai ka buqaci hakan......". Ai bai iya barinta ta qarasa fada ba ya hade
bakinsu guri guda.

Sai daya tabbatar ya kwashe ragowar maganar tass daga bakinta sannan
ya zare bakinsa daga nata yana kallonta da birkitattun idanunsa.

"Ta yaya zan iya rayuwa ba'a duniyata ba?.......ta yaya dan adam zai rayu babu
duniyarsa?,indai babu ta yadda hakan zata kasance....to ki sanya a ranki ni
Muhammad jadda don ke kadai MAAMAH ta haifeni". Batasan sanda ta zube saman
kafadarsa ba tana jin wani irin alfahari yana ratsata,tana jin tabbaci da yaqini
suna ratsata.....ashe akwai sauran maza irin muhammad jadda din?.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 117


117


Guri kawai ta samu ta zauna cikin dakin daya kasance ita daya ce qwallin
qwal a ciki. Duk yadda taso ta cinye ta kuma jure ta kasa,bata ankara ba kawai taji
ta fashe da kuka.

Ta yaya haka zata kasance?,bata tsira da komai ba sai hawan jini?.
Wanne irin kafaffen yaro ta haifa?.....aure tsakanin musaddiq da amna?,wacce irin
asara ke bibiyarta har haka?,da gaske kamam yadda boka ya gaya mata taurarin
nasararta ke bacewa?,taurarin nasararta ke dakushewa?,ina dukka kaifin hankalinta
da zallar iya takunta suka tafi?(ta mance cewa shi Allah gwanin hikima ne,yana iya
yiwa bawa talala,yayi shekaru aru aru yana zalinci,a nasa hangen da tunanin nasara
ce,sai Allah ya barshi da wayonsa da tunaninsa,ya turo.masa nasara a gabansa,plan
dinsa yayita tafiya daidai,kwatsam idan yaso kamashi zai da damqeshi a tsakiyar
wannan plan din da shirin nasa da yake tunanin sune mafita a gareshi,sai ya zurma
yayita bundum bundum. Idan yana da rabo sai ya gane zunubansa da kuma kusakurensa
yayi gaggawar tuba....idan baida rabo kuwa,zaiyita ganin INA DA SAURAN DAMA,INA DA
SAURAN LOKACI yana tsaka da wannan lissafin sai ubangiji yayi ram dashi,dauri gaba
dauri baya,me kwanceshi kuma sai ubangijin daya qulle abinsa. Duk runtsi.....duk
tsanani,duk yadda za'a je a dawo karka yadda ka cuci kowa,daka cuci kowa gwara kowa
din ya cuceka. Duk juyin da za'ayi ka tabbatar zuciyarka wankakkiya ce......kana
bacci amma sai ubangiji ya zama jinka ya zama ganinka,ya zama me jagorantar
al'amuranka,ubangiji ka barmu a naka duniya da lahira,karka bari duniya da abinda
yake cikinta ya rufe mana ido don girman zatinka,karka bamu damar cutar kowa don
isarkaπŸ™πŸ½πŸ™πŸ½πŸ™πŸ½).

Abune a rayuwarta data manta rabon data yishi wato kuka,shekaru masu
yawa da suka shude mata,amma sai gashi yau tana zubda hawaye sanadin anni amna da
sabreen.

"Lallai dole fansa ta biyo baya.....lallai dole ku biya bashi da fansar zubar
wadannan hawaye......dole sadaukarwa ta biyo baya.....wala'alla akwai rayuka da
zasu salwanta......rayukan da shudewarsu shine silar wanzuwa da samun nutsuwar
zuciyata" Ta fadi a fili tana kallon idanunta da suka tasa saboda kukan data share
mintuna tana yi.

A gaggauce ta sake goge fuskarta ta,sannan ta koma wajen luggage
dinta ta soma ninke kayan ciki tana zuba wadanda suke gefen gado da kuma cikin
toilet din dakin. Tanajin ta qagauta gari ya waye,tana jinta.kaman saman qaya,a
jikinta da ruhinta takejin bata da wani sauran zama a garin,bata da sauran abinda
ya rage mata da zata zauna tayi cikin qasar(subhanallah).


β˜…Sau tari wata soyayyar tana zamewa madubi kuma abar sha'awa ga wanda ke gefe
yana kallo. Wani memories din na wasu masoyan kan samu wajen zama na din din din
cikin kwanya ya kasa gushewa saboda girman tsumammiyar soyayya zallar kulawa da
qauna me gusar da hankali saboda tsananin kusanci da kulawa tsakanin masoya.

Fu'ad da sabreen......soyayyarsu ta zamewa wasu tamkar
makaranta.....ko kuma allon da zaka kalla ka karance ilimin dake shimfide a kanshi.

Wucewar maamah Nigeria ya samar da nutsuwa me tarin yawa ga wasu
zukata,wadanda sam basusan gaibun dake tattare da tafiyartata ta barsu ba. Wani
lullubabben gaibu me cike da duhun sirrikan da ita kadai ta barwa zuciyarta shi.

Samun sararinta da gushewar wanzuwarta a family din ya bada damar baje
kolin soyayya masu dauke da nau'ika kala kala. Sabreen da fu'ad,suna rayuwa da
nunawa juna soyyaya da kulawa tamkar sun manta da akwai wasu halittun dake gewaye
dasu suna tasu rayuwar.

Sau tari idan fu'ad yayi wani abun saidai kowa ya runtse idanunsa,don
ba wanda yake gani sai sabreen da cikinsa dake manne a jikinta. Gaba daya kaman ya
mance da kowa sai ita sai hidimarta,wani lokacin hankali yafi zuwa jikinta
akanshi,don takan tuna da anni a wajen ta rage wani abun.

Duk da abun ya zowa anni a sabo,amma saita zama suruka me yawan bada
uzuri da dauke kai. Bata shiga tarayyarsu ko kadan,saita dinga nesa nesa dasu gudun
ji masu kunya duka ita dasu.

Wannan soyayyar sai ya hura wuta biyu......tsohon tsumin soyayya ya
balle tsakanin musaddiq da amnansa,duk da cewa daga nesa nesa ake komai don anni
bata bari abun ya zurfafa da yawa. Su dinma duk yadda sukaso su boye dole ita
soyayya bayyana kanta takeyi koda an boyeta. Sannu a hankali sai wata wutar
munafukar soyayyar ta soma kunnuwa kuma daban tsakanin saddiq da huda. Duk wani
nuqu nuqu da sukeyi hakan bai hana sabreen karantar komai ba,ranar sun dawo daga
masallaci take tseguntawa fu'ad hancinta ya lakace mata.

"Kin iya sa ido duniyata.......banda nidin ina da qarfin kurwa banjin zan qwace
filin soyayyar da akewa su huda.......Allah ya taimakeni nayi hasashen tsaf zaki
iya guduwa ki barni.......nayi miki yankan baya na kawo miki su.....to me ya
rage?". A mamakance ta zare idanu dariya tana qwace mata,sai ta boye kanta cikin
qirjinsa tana qoqarin musanta maganar.

Saidai kuma a zahirin gaskiya cike take da mamaki,wanne irin mutum ne
fu'ad din me tsananin kula har haka?,ta yarda dari bisa dari baya wasa da duk
abinda yakeso.

Duk wadannan abubuwan da yake faruwa bai hanasu ibada ba
tuquru........zamansu tsakanin makka da madeena yafi yiwa fu'ad dadi sama da
kowa,tunda ko banza yace za'a qiri halittar danshi ko 'yarshi a guri me tsarki da
tsarkakken ruwan zamzam wanda shine komin sabreen. Komai da zamzam takeyi,shine
ruwanta nayin komai,iya falalar ruwan zam zam kawai ya sanya yake qara jin nutsuwa
da zamansu a nan.

Tuni ya mata register da komai na zuwa awo da haihuwa,don yace indai
yana da rai da lafiya to tabbas a garin madeena yakeso a haifa masa yaransa,ya
tsara komai ba tare daya gayawa kowa bama.


*_K'ADDARA KO GANGANCI?_*

_KALLON KALLO_


Sau uku tana rolling sassalkar luxury Egyptian abaya din tana warewa.
Kawai sai tayi zaune gaban madubin tana ware hannuwanta gami da binsu da kallo.

Batasan me yasa ba......batasan kuma me yake faruwa ba,shagwabata da
yayi da yi mata hidimar komai ne sila ko kuma cikin jikinta ya sanya ta zama
raguwa?.

A karo na hudu ta sake gwadawa sai veil din ya sabule salin alin daga
hannunta. Ido ta zubawa fuskarta,sai taji hawaye kawai ya kubce mata.

Murmushi ya saki yana qarasa sanya link din hannun kuftan jikinsa,ya
soma takowa a hankali zuwa bayanta. Tun daxun da taketa drama ita da dankwalin yana
kallonta,yasan qarshen maganar dama ta sanya kuka tunda ta zama rigimammiya ta
gaske.

Kafadunta ya kama ya tasheta tsaye,suka hada ido sai yayi qoqarin danne
dariyarsa,saidai tuni ta riga ta gani.

Daga hawaye sai ta sakar masa kuka me qaramin sauti.

"Subhanallah......me kuma nayi?" Ya fada yana dora damuwa saman fuskarsa duk da da
gasken dariya yakeson yayi.

"Ya isa....am sorry if I offend you" Ya fada yana sakata a qirjinsa. Shaqa daya ta
yiwa turarensa nutsuwa ta fara saukar mata,sai ya bata lokaci sai daya tabbatar ta
nutsu sannan ya dagata yana duban fuskarta.

"To mene ne?,.....uhmmm.....tell me" Tabe baki tayi,ta miqa hannu taja kumatunsa.

"Ba mayafinne yaqi dauruwa ba,sannan kuma kai kazo kanamin dariya saboda ina ramewa
kai kuma kina qiba". Wannan karon kecewa yayi da dariya sosai harda riqe ciki. B
wani bane ya jawo masa wannan jagwal din ba sai amna,haka kawai ta sashi gaba
vanilla ice cream takeson sha,suka yiwa anni wayo suka fice wadda ta jima da hanata
shan kayan zaqi da sanyi. Koda sukaje kasa sha tayi.ma gaba daya sai ya fita a
ranta,shi kuma duk da bai dameshi ba amma sai yaji ya masa dadi,yasa aka kawo masa
ya soma sha,ashe tana ankare,ke amna kika ce

"Hamma madeena ta karbeka Allah,ka karbe jikin adda ka hada da naka,kanata kumatu"
Ta fada tana dariya.

"Lovey dovey.....kin manta ni yayan mijinki ne kenan?" Ya fadi hakanne don shine
abu daya yanzu da yake kashe bakin amna,ya kuma fadi hakanne don ya fuskanci
sabreen din har ta kumburo fashewa kawai take jira tayi. Ashe abun dashi ta kwana
sai yanzu ake fashe masa shi.

Sulalewa yayi ya durqusa gabanta,ya zagaye hannunsa a bayanta yana dora
fuskarsa saman mararta.

"Kazo mu bawa mama haquri....mun hanata qiba mun hanata cin kayan dadi....mun
tuba....zamu gyara halinmu" Ya qarasa maganar yana hade hannuwansa guri daya.

Da ido ya bita ganin daga kuka ta koma buga murmushi,ya girgiza kai
kawai a ransa yana gulma,wato me ciki sai a barta kawai.....abun kuka ko bacin rai
baya mata kadan,cikin dabara ya jata ya sauya mata yalwataccen mayafin rolling din
ya daura mata da kanshi,don bayason wani sashe na jikinta ko kadan ya fita wani ya
gani.

Yana gama mata ana knocking qofar,yasan waye farouq ne,qiri da muzu
ya zama fusataccen qarfi da yaji,yace fu'ad ya jawo masa raini,ya hada tuxurantaka
da aure da qannensa,in fact ma qanin bayansa ya rigashi amsa sunan me aure,wannan
ta saka dole qasa daya data rage musu akayi cancelled trip din sai bayan wani
lokaci,aka aikewa da iyayen fanna date na bikin sati biyu masu zuwa wato sati biyu
da komawarsu nigeria kenan.

Hannunta cikin nashi yadda suka saba suka fito a dakin,ta zame hannun
nata a dabarance ta qarasa gaban anni ta gaidata,ta gaida momma wadanda zasu sauka
duka a nigeria,da yammaci kuma jirgi zai wuce dasu mali saboda washegari huda
zatayi ton prints na jarabawar kammala secondary school.

Haka suka wuce airport cikin motocin da a nan qasar yake barinsu sai
kuma zuwa na gaba.

Anata zuba soyayyar munafunci tsakanin amna da musaddiq,huda da saddiq
daketa babbasarwa kaman ba komai tsakaninsu,angon gobe farouq kuwa anata sallama da
fanna ta waya shima ya bude wuta sosai don shirye shirye sun gama kammaluwa,ranar
kawai suke jira.

Ita kuwa kanta yana kwance kawai saman kafadarsa. Tun bata saba ba
har ya riga ya saba mata,wata kasala take fama da ita,bata iya cikakken zama ba'a
jikinsa.

Tunda jirginsu ya tashi take jin gabanta yana faduwa lokaci
lokaci,tadan rufe idanunta kadan tana jan sunan Allah,ko shima sabuwar faduwar
gaban tana cikin laulayin ta yiwa kanta da kanta tambaya.

Idonta ta rufe tana fatan bacci yayi awon gaba da ita wai ko zata samu
sassaucin abinda takeji,tana iya jin sanda ya sanya blanket ya lullubeta,sannan ya
sake rufeta da faffadan qirjinsa yana rufeta tsam cikin jikinsa,ajiyar zuciya me
sanyi ta subuce masa ya dora habarsa saman kanta a tausashe.

Cikin zuciyarta take roqon Allah......kada ya bata ikon butulcewa
wannan bawa ko juya masa baya.......ita kanta wani lokaci irin yadda yayi nisa a
soyayyarta tana jin kamar tata zuciyar zata narke a kansa. Tsakanin ita dashi
batasan waye yafi wani yin nisa ba,waye yafi wani yin zurfi bs,fatanta kawai shine
kada su zama masu butulcewa juna a tsakaninsu.

Tafiyar awanni biyu jirginsu ya sauka a filin sauka da tashin
jiragen sama na malam aminu kano dake kano. Sai takejin farinciki yana ratsata duk
da ta baro wani guri mai muhimmancin gaske a rayuwar duk wani musulmi.

Abu guda daya da yaci gaba da farautarta shine faduwar gaban dake
qara tsanantar mata,duk sai take jinta a rikice har zuwa sanda suka qaraso inda
jerin gwanon motocin jadda diamond suke jiran qarasowarsu.

Kusan dukkanin guards dinsa sun zo tararsa cike da girmamawa da kuma
kewarsa da sukayi na tsahon lokaci.

Sabule hannunsa yayi daga cikin nata,abinda ya sanyata daga kai ta
kalleshi kenan.

Murmushi ya sakar mata me taushi yana dubanta.

"Zaku fara yin gaba saboda ki samu zama dasu huda kuyi sallama......zan qaraso
yanzun......nasan a gajiye kike amma ma'u ta tanadar miki komai.....kada kice zaki
jirani,kiyi wanka kici abinci kiyi bacci sosai......yau akwai biyan bashi" Ya furta
maganan qarshen qasa qasa yadda ba wanda zaiji musu sirrinsu.

Duk da yadda gabanta ke tsananta faduwa,duk da yadda takejin kaman
zaini wani wawan nisa da ita......irin nisan da takejin tazararshi tayi yawa amma
saida murmushi ya subuce

Please Login or Register in order to submit comment