You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce?,to kodai zai samu wani hint din a nan ne?.

Tabbas inda a watannin baya da suka shude maamah ta fadi haka akan
sabreen bazai dameshi ba.....in fact ma zai dauka ta fara gane wacece menene kuma
halinta,amma kuma a yanzun sai yaji kalaman kaman sunyi tsauri da yawa. Ya shirya
tare mata fada ko batanci kowanne iri ne kuma koda waye,don haka ya gyara zamansa
yana fadin.

"Maamah.....inajin kinfi kowa sanin wacce iri ce sabreen.....tunda daga hannunki ta
fito,kuma na tabbatar ba zakimin zaben tumun dare ba.....amma maganan waya bata da
waya,duka wayoyinta suma hannuna". Har tsakiyar kanta taji wani abu ya tsarga
mata,wato ita yarinyar zata gwadawa bariki ta bashi wayoyinta?,a tunaninta yin
hakan shine zai sanya ta tsallake tarkunanta?. Ta jima tana zaton salwantar da
wayoyin tayi,wannan yayi saving nata bata taba gwada Kiran layukan ba,inda ta kira
din kenan yana iya zargar komai ko ya binciko komai?.

"Sannan kiyi haquri zan mata fada zata gyara" Ya sake fada yana kallon reaction na
maamah din. Yadda ta daga kai da sauri tana dubansa ya sake bashi wani qarin
percentage na zarginsa a kanta. Yaushe alaqa tayi nisa tsakaninsu da yake
kareta?,yaushe ma duka duka ta kirashi ta masa jan kunnen ya kula da ita?,bariki ce
ko nata kalar tsubbun ta shayar dashi kaman yadda jikinta keta bata zata aikata
haka?.

"Ai karma ta gyara....ni d'ana bazai auri mace daya ba ballantana ta samu daman
juyashi da zaton nata ne ita kadai,don haka ka shirya........na zabar maka fareeda
mazaunin matarka ta biyu......muna komawa da sati biyu kacal zaayi komai a
gama.....don banajin tafiyarka da sabreen zatayi nisan zango,akwai canje canjen
dabi'u da halaye da nake ji a tattare da ita" Sosai yake kallonta,ba kuma don komai
ba sai don maganganunta masu kama da almara. Auren fareeda wannan yasan wani abune
da bashi da maraba da tatsuniyar gizo da qoqi,uwa uba ma fareedan dukkaninta ba
damuwarsa bace,don tana under control nashi,kowanne motsi nata yana sane
dashi.....abinda kawai yaja hankalinsa shine zancan sabreen. Wanne sauyin halaye
take ji game da ita?,meye dalilinta dukka na damuwa da al'amuranta?. Wanne laifi
mutumin da baka jinsa ko ganinka yayi maka da zata dinga zarginsa da aza masa laifi
kacokam haka?.

"Kar kayi kuskuren cewa zakamin gardama akan auren fareeda,nasani sarai shurunka
yana nufin abubuwa da dama.....muna dab da muhallin amsa addu'a,zanje gaba ga Allah
na roqeshi ya fiddamin haqqin haihuwarka da nayi" Idanunsa ya lumshe maganganunta
suna sukarshi. Baisan me yasa ako da yaushe barazanarta iri guda bace a kansu,yadda
ta damu da neman haqqin Allah a kansu bata damu da nema musu albarka haka ba?.

"Relax.....cool down.....badai fareeda bane matsalar?" Kai ta jijjiga

"Itace"
"Done" Ya fada da wata ma'anar ta daban. Shi kadai yasan me ya sake shiryawa me
kuma zaiyi. Binta da kallo yake kawai sanda taci gaba da cin abincinta,yana hangen
tarin sassauci data samu can boye cikin fuskarta da karbar zancan fareeda da yayi.
Wani irin quna zuciyarsa keyi musamnan idan ya tuna duk wannan abun da takeyi fa
siyanta fareeda kenan tayi. TO TA YAYA TA HADU DA SABREEN?,MENENE SILAR HADASU AURE
DA ITA?,MEYE MANUFAR?. Wasu tambayoyi da suke masa susa a qirji,ya tabbatar tunda
take muradin hadashi da fareeda bisa wats manufar.....tabbas haduwarsa da sabreen
ma akwai manufa,saidai ita sabreen yasan bata da kudin da zata siya maamah.....to
meye SILA?. Ba wadda ta fado a ransa a sannan sai hajja,a take kaman an cillota
cikin tunaninsa,saboda muhimmancin abun a take ya ciro wayarsa ya tafa qaramin
massage ya tura yana cewa.

_ina buqatar kowanne motsi na rayuwarta ya zama abun bi kafin na qaraso,bata
buqatar kamu,amma ina buqatar ayi mata daurin talala_ sai daya tabbatar da shigar
saqon sannan ya maida wayar aljihunsa.




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862




𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 91



91


Sosai maamah tayi amfani da wannan damar ta dinga karbar kudade daga hannunsa tana
tsaraba. Baice komai ba don ba wannan muhallin bane,bai kuma hanata siyan abinda
duka take so ba.


β˜… *_makka to Maldives_*

Kwanaki shida sukayi a maimakon kwana biyu ko ukun da ya tsara zasuyi.
Kusan ita ta dinga jan kwanakin duka a nufinta na tafi da tsarinta yadda takeso.
Abu daya ne kawai yake dan bata mamaki,yadda take kasa samun wayar fareeda kwata
kwata,ta gwada dukka layukanta amma ta gaza samunta,mamakinta yana sake daduwa idan
ta irga kwanakin taga ko sau daya bataga gilmawar kiran fareedan ba.

Sun sauka Maldives dab da sanda rana ke shirin faduwa,wannan ya sake
haska tsibirin ma'abocin ruwa da wani irin yanayi me daukan hankali.

Baki kawai maamah ke tabewa,a zahirin gaskiya ba zata ce island din
baiyi mata ba,saboda guri ne da yafi kama da aljannar duniya,amma baqinciki da
bacin rai suna cikata idan ta tuna cewa ahalin alhaji hamza suka zabi wajen. Ranta
ya sake baci sosai cikin wani irin baqinciki da fushi sanda taji tsadar da rayuwa
cikin tsibirin yake dashi,da kuma yawan adadin kudaden da ake kashewa kowanne kwana
daya cikin resorts da sauran guraren dake kewaye da wajen.

"Nikam banga abun burgewa a nan waje ba.....guri duk ruwa,koda yake ba lafinka
bane.....kai ka zama dan amshin shata ne kawai sai abinda aka tsara maka,kuma
tsabar zallar mugunta ne saboda basusan zafin dukiyar ba,ba tasu bace......dolla
million nawa ka kashe musu?" Ta maida tambayarta ga fu'ad dake zaune a gefanta
cikin motar da Jordan yazo daukarsu.

Boyayyar ajiyar zuciya ya sauke yana rufe idonsa gami da budesu,tunda
yake bai taba jin kwanaki masu wahalar wadannan ba,wadansu irin kwanaki ne da sam
babu armashi a cikinsu. Ya sanya ran samun nutsuwa daga wajen sabreen tun ranar
farko data daga wayarsa,saidai kuma bai sake samunta a waya ba har yau da suke
dawowa qasar.

"Farouq ne ya dauki nauyin komai" Ya bata amsar da azahiri haka take,gida ne kawai
zai iya cewa nashi sai jet din da suka taho a ciki. Idanu ta dauke tana tabe
bakinta.

"Haka dama zaka ce,saboda kana qoqarin basu kariya,ina jiye maka ranar nadamar
damqa ragamar rayuwarka a hannun mutanen da basusan ciwon haihuwarka ba.....gefe
daya ga matar da nake kyautata zaton zuwa yanzu sun hada baki da ita don su sake
cimma manufofinsu" Gaba daya maganganunta baya qaunar jinsu,baya iya daukan
kowanne mummunan kalami a kan ahalin alhaji hamza kibiya din. Sun masa komai a
rayuwa,idan yace komai yana nufin komai din,don wataqila idan bacin su da yanzun
baisan rayuwarsa a wanne matsayi take ciki ba.

Duk maganganunta yayi shuru yana jinsu,qananun mitoci ne da basu da
tushe ballantana makama. Banda zata fassara abun da wani yanayi na daban tabbas da
gida daban zai kamata tayi zamanta ita kadai,saidai hakan yasan ba mafita bace,ba
abinda zai sake jawowa sai wani damuwan na daban.

Tun anesa ya hangi musaddiq da saddiq zaune daga gaban gidan. Sanye suke
da kaya iri daya black jeans da white din t.shirt. Tsaf zakayi tunanin twins ne
saboda yadda komai nasu ya kusan zama iri daya.

Sosai maamah ta qanqance idanu tana dubansu,wani irin abu yana tsarga
mata

"Turqashi" Ta furta qasa qasa. Da alama ameenatu tana ci gaba da mamayar komai daya
kasance mallakinta. A sanda hankalinta yayi nisa,ta dogara kuma da sabreen hakan
sai ya zamana kaman ta bawa ameenatu wata qofa ko dama naci gaba da baza mallakarta
tsakanin yaranta. Ba zata iya tuna watanta nawa bataga musaddiq
ba,jininta.....tsatsonta,ya gaya mata fu'ad dinne ya aikeshi wani aiki dubai da
Qatar,amma yanzun gashi tare da ameenatu,gashi manne da ahalin alhaji hamza kibiya.

Tsaiwar motan yaja hankalinsu su duka,motar ba baquwarsu bace don
haka dukkaninsu suka miqe zuwa gaban motar.

"Barka da zuwa maamah" Musaddiq ya fada yana niyyar karbar jakar hannunta. Kasa
jurewa tayi ta jefeshi da harara duk data sakar masa jakar.

"Uwarka ta taso daga wani gurin amma ka gaza zuwa airport tarbarta kana nan manne
da uwar wasu?". Maganar ta masa ba dadi har hakan ya bayyana saman fuskarsa. Yadan
basar yana amsar jakar sannan yace.

"Hamma ne.....bai bada assurance na yau din zaku taso ba".
" Barka da zuwa maamah ina yini?" Saddiq ya fada yana dan matsowa kusa da musaddiq.
Waiwayowa tayi,ta aje masa wani kallo tun daga sama zuwa qasa kafin ta amsa masa
sheqeqe tana bin bayan fuad zuwa cikin gidan. Koda riga ta gani a jikinsu
baqincinta takeyi,gani takeyi kudin fuad ne ya siya musu wannan riga takalmi da
kuma daular da suke ciki ma gaba daya. Tana ganin sunyi amfani da nasibin danta ne
kawai suna morarsa bayan sun rabata dashi.

Tunda ta idar da sallar la'asar take manne da earpiece a kunnenta tana
sauraron karatun littafin umdatul ahkam. Sanye take da Indonesian set skirt ne da
hijab dinsu madaidaici sai rigar da iyakarta qugunta. Dark green ne da suka haska
fatarta sosai,ta tattare gashinta ta daureshi tsakiyar kanta bayan amna ta gama
jagwalgwala matashi da sunan zata mata kitso. Ta kasa kitson saboda santsinsa,don
haka ta bisu da hair clips ta tattare mata shi,ita kuma ta daureshi da ribbons don
tace ba zata saka mata hair ppin ba. Kayane masu taushi da sakewa a jiki,duka anni
ce ta saya mata su kusan kala shida.

A kwana biyar din sauqi ya samu sosai,ita kanta a jikinta takejin ta
warke da taimakon wasu irin herbs 'yan Indonesia da anni ta bata.

A kwana biyar din ta wani murje,hankalinta kwance bata ganin
wulgawarsa bare fargaba ta dameta. Hatta anni ta karanci yadda hankalinta ya sake
kwanciya,ta daiyi murmushi kawai saboda tasan tsakanin miji da mata sai Allah,bare
wadannan data fahimci yanzu ne yake fafutukar gina gwamnatinsa.

Batasan me za'ayi ba a gidan,don duka hankalinta yana kan
karatunta,itadai ta shiga kitchen tana taya amna da anni girki. Annin ta fara fita
ta barsu a ciki,amna ta fidda Warmers din tana shiryawa,ita kuma ta tsaya tana
gyaran kitchen din.

Idanunta d'ai d'ai cikin parlor din tana kallon wata sabuwar
duniyar. Fuad ya dauke idonsa a kanta yana sallama don sanar da anni da amna dake
dining suna magana shigowarsu.

"Wa'alaikumussalam......marhaba da matafiya" Anni ta fada da murmushi saman
fuskarta tana saukowa daga dining area din tana nufosu.

Tun bata qaraso ba maamah ta fara qare mata kallo,tayi kyau cikin
super embellished me asalin tsadar. Kwanciyar hankali nutsuwarta da riqonta da
ibada sun sanya wani irin kwarjini akan fuskarta gami da fidda ainihin
quruciyarta,kai bakace itace uwa ga saddiq da farouq ba.

Tako ta ina sai take ganin annin ta fita samun duniya ne,wannan shine
sirrin wannan kyan da take gani tattare da ita. Dom ta sutura tana sanya sama da
suturar dake jikin annin a yanzu.

"Barkanku da zuwa.....saddiq ku dauki luggage dinta zuwa daki......me babban suna
ya akayi baka bada exact time din da zaku sauka ba?" Anni ta fada tana dauke kai
daga irin duban da maamah ke mata

"Na sha'afa ne anni.....amma gamu mun iso alhamdulillah" Yayi maganar yana shafa
sumar kansa,gaba daya hankalinsa yana wajen amna yana tunanin ganin sabreen tare da
ita.

"Alhamdulillah.....haka akeso ai.....bismillah Mariya mana kunata tsaye?" Anni ta
fada tana jifan maamah da murmushi. Idanu maamah ta janye a kanta,tana jin wani abu
yana tokare mata wuya. Yau ita akewa tayin zama a gidan d'anta?.

"Da baki gaggawa ba ameenatu,zama kam nina cancanceshi" Ta fada tana son maida
maganar cikin yanayi na wasa wasa. Sosai maganar ta samu muhalli a zuciyar anni,ita
kuma ta sani bawai da wasa mariya ke maganar ba,saidai koma meye ta shiryama zama
da mariya din albarkacin muhammad fu'ad din.

"Zo mana amna" Anni ta fada tana kiran amna dake zaune kawai. Haka kawai takejin
batason rabar matar......bata son yanayin kallon da take binta dashi. Qarasowa tayi
inda annin take,ta sani sarai anni na iyayi mata fada don haka ta rusuna tana gida
maamah data fidda mayafinta ta aje gefe da bawa kowa na wajen tabbacin tazo gurin
data isa ne. Kaman yadda ta saba amsa musu gaisuwa haka ta amsawa amna.

"A gabatar mata da ruwa....sun sha hanya ita da hammanki".

"Karki kawomin zallar ruwa,lemo nake buqata da wani abun tabawar bawai dangin ruwa
kadai ba" Daga amnan har anni ba wanda ya nuna yaji abinda tace,illa anni ta dubi
amna

"Ki duba fridge kiyi warming pizza da samosa ki hado dashi". Kai amna ta gyada a
sanyaye tana nufar kitchen din. Har yanzu ta kasa aminta da gamsuwa matar wai itace
mahaifiya ga hammansu.

Gefe anni ta samu ta zauna tana gayawa kanta da kanta. Maamah ta cancanci
kawaicinta kawai saboda fu'ad din. Sam sabreen bataji shigowar amna ba sai data
gama hada kayan zata fita sannan ta riqota tana cire earpiece din kunnenta.

"Ki cewa anni an kammala,sai meye za'a dora mata?". Kai kawai ta gyada mata ta
fice,tanason ce mata hamman ya dawo amma kuma yanayin sanyin jikin data tsinci
kanta a ciki ya hana mata.

Sake daga kansa yayi cikin matuqar zaquwa yana sanya ran ganin fitowarta
a kitchen din tare da amna. Saidai a yanzun ma amnan kawai ya gani ta fito. Iska ya
zuqa sosai yana fesarwa

"Me take buqata dashi ne?,hauka take so ya fara gwada mata tuburan?" Ya tambayi
kansa yana jin zuciyarsa tana quntata waje daya.

Sheqeqe maamah tabi tray din da amna ta shiryo,ta tabe baki wanda
muraran duk wanda ya kalleta zai gani. Baya amna taja tana gayawa anni saqon
sabreen,abinda yasa ruwan da maamah ta kurba yayi mata cak a maqogaro.

Juya zancen takeyi tsakanin rai da zuciyarta. Me haka yake
nufi?,kyakkyawar alaqa tsakanin sabreen din kena da ameenatu?,yarinyar ke niyyar
zame mata qadangaren bakin tulu ko.kuma ameenatun?,waye ainihin matsalarta a cikin
su biyun?.

Ta bangaren fu'ad din sai ya dinga ji ransa yana sake baci....dole
ya sake tabbatar mata ita mallakinsa ce,dole ya sake tuna mata muhammad fu'ad
mijinta ne.....mijin da bazai juri qaurace masa ba.....mijin da bazai juri bada
umarni tasa qafa ta take ba saboda raini.

"Kice ruwan zafi kawai zata dafa......ta fito ga baqi sunzo tazo su gaisa". Anni ta
fada tana duban amna. Baisan ya miqe tsaye ba,shidai yaji yana gayaw anni

"Bari na samo warm water.....nasha sanyi a haram da yawa" Yayi maganar yana jin
wani magnet yana jansa zuwa kitchen din,ba tare da ya tuna waye da waye a wajen ba.

Ajiye cup din hannunta maamah tayi tana binsa da kallo sanda yake
takawa hankali kwance zuwa kitchen din. Tuni amna ta wuce dakinsu don ba zatayi
gangancin komawa kitchen din ba tunda can hammansu ya nufa.

Wani mamaki yake kashe maamah tana daga zaunen. Ita din ba yarinya
bace haihuwar jiya ko yau,ta sani sarai ita yabi....sabreena yabi bako shakka. Daga
yanayin fu'ad din kawai tasan akwai abinda ke jansa zuwa can din,wani dakiya da
shariya ta gani tattare dashi wanda bata taba ganin irinsa ba. Yadda yake tafiya
zuwa kitchen din hankalinsa kwance kaman ba wani idon kunya a wajen?.

Sanda tayi nisa da binsa da kallo a lokacin anni itama tayi nisa da
qare mata kallo da kuma fahimtar rudewarta da kuma canzawar yanayinta lokaci guda.

"Ya rabb......kasa addu'ar dana bata tsahon dare ina yinta ce ka amsa.....ubangiji
ka sanya wannan mummunan qullin ka juyar dashi zuwa kyakkyawa". Anni ta sake
jaddada addu'arta can qasan zuciyarta wani murmushin nishadi yana subuce mata.

"Tabbas kina dab da ganin yadda ubangiji ke jujjuya al'amura......kina kuma dab da
samun ciwon hauka muddin akan Sabreen da fu'ad ne" Anni ta sake fada qasan ranta.

Ba jiya yau ko shekaran jiya ba take karantar duk wani motsi na fu'ad
ba.....me babban suna ya canza gaba daya.....ya shiga wata gawurtacciyar koma ta
soyayya wadda tayi imani shi kansa baisan girman abinda ya fada a cikinsa
ba......karantar irin wannan yanayin kuma sai uwa ko gawutaccen masoyi.

"Zan shige daki na shirya.....naga magarib tana dab da isowa.....ga masaukinki
can,a huta lafiya" Muryar anni ta dawo da ita daga rudanin data shiga. Bata sake
cewa maamah din komai ba,saidai ta barta da kallon murmushin dake kwance akan
fuskarta. Ita ba zata bari fu'ad ya fito ya sameta ba ballanta yaji kunya ko ya
raga daga soyayyar da yayi niyyar nunawa matarsa ba.....ta barwa maamah ta fara
kallon sample kafin anihin abun ya bayyana a idanunta gaba daya.

Idanunta ciki ciki tabi anni da kallo har ta isa dakinta.

"Ta ina kuma ameenatun ta sake bullomin?" Ta yiwa kanta tambayar zuciyarta cike da
kokwanton murmushin data gani saman fuskarta.

_turqashiπŸ˜‚πŸ˜‚,anya maamah nan din gidan zamanki ne kuwa?_

_maji ma gani dai_



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 92



92


A hankali ya tura qofar kitchen din sannan ya maidata ya rufe a nutse
bayan ya karanci earpiece ne a kunnenta,sai ya maida bayansa jikin qofar kitchen
din,ya goye hannayensa a qirji yana qare mata kallo.

Ta fidda hijabij jikinta ta saqaleshi a hanger na kitchen din don
tafi jin dadin yin aikin,bata da damuwa kan musaddiq ko saddiq,dukkaninsu idan zasu
shiga wani guri cikin gidan saisun tsaya daga waje sunyi sallama. Sassalkan
gashinta da amna ta kame mata su da hair clips masu kaloli da shapes daban daban
jelarsa ta baje sosai a bayanta. Baqi sidik ne yanata shining saboda ko da can ita
din bame wasa bace da gyaran jikinta ma gaba daya. Idanunsa ya lumshe yana bin
sauran sassan jikinta da kallo,qugunta ya bude sosai ta cikin skirt din dake
jikinta,shape dinta ya fita sosai da duk wani sura na kyau da Allah ya bata.

"Ya salam" Ya furta qasan ransa saboda wani irin magnet dake fusgarsa zuwa gareta.
Wani sashe na zuciyarsa ya raya masa inda wani tsakanin musaddiq da saddiq ne ya
shigo a haka zai ganta?. Raba jikinsa yayi da qofar ya fara takawa a nutse yana
dosarta.

Dukan hankalinta yayi nisa wajen killace plates din data wanke. Kwata kwata
bata kawowa ranta wai dawowarsa ba ballantana shigowarsa kitchen din ba. Ta gama
jerawa tayi taku biyu baya don matsawa daga wajen,santsin man daya diga a qasan
tiles din ya kwasheta,tayi baya zata fadi a matuqar tsorace. Hannayensa ya sanya
duka biyun ya tarota,take ta samu masauki a faffadan qirijinsa.

Gam ta sanya hannu tana riqeshi ba tare data fahimci a jikin wanda take
ba,tunaninta duka ta samu wani abunne ta kama.

Fadowarta jikinsa ya bashi daman qarewa kyakkyawar fuskarta kallo.
Karon farko da wannan tsiwatacciyar fuskar ta fito a matsayin matsoraciyar fuska.
Sauke idanunsa yayi saman qirjinta dake sama da qasa alamun tsoro muraran da kuma
yawan adadin bugun da zuciyarta ta qara. Cikin qasa da second ashirin hankalinta ya
fara dawowa jikinta bayan ta tabbatar batasha qasa ba,ta zuqi numfashi sosai wanda
hakan ya taimaka mata wajen isar lallausan qamshinsa qofofin hancinta ya kuma isar
da saqon waye me turaren cikin kwanyarta.

Idanunta ta ware da sauri,take suka fada saman fuskarsa dake dab da
tata,sukayi wani zuzzurfan musayar numfashi daya hautsina masa tunani karon farko.
Kyakkyawar fuskar nan tasa dake shimfide da wani irin kyau da ba kowacce fuskar d'a
namiji ke da baiwar irinsa ba.....wani irin kyau me cakude da kwarjini musamman
cikin narkakkun idanunsa da kallon cikinsu yasha banban da idanun kowacce d'a
namiji data taba kalla.

Cikin sauri ta tura qirjinsa baya tana zamewa daga jikinsa,saidai ya
gwada mata halittar sam ba daya bane ta hanyar miqa hannunsa ya damqota. Wata
kyakkyawar runguma yayi mata ta baya gana matseta cikin jikinsa,ya aza fuskarsa
saman kafadarta,sannan ya motsa labbansa da wani irin nannauyan numfashi.

"Am back.....am home.......but......" Ya fada yana dagata gami da juyo da ita gaba
daya tana fuskantarsa sosai. Raina kanta tayi sosai ganin yadda ta koma 'yar qarama
a gabansa,ya kuma ritsata da wannan kallon nasa yana duban duka qwayoyin idanunta
kafin ya jefa mata tambayarsa.

"You break my rules hajjaju.....don't blame me indai na tashi hukuntaki" Yayi
maganar cikin nuna mata da gaske yake yana miqa hannunsa zai shafi gefan fuskarta.
Baya taja da sauri,abinda ya sanya ya tsaya ya zuba mata ido. Da gaske take batason
koda yatsarta ya taba.....ko yaya ya kusanta kanshi da ita saitayi wani abu da zai
nuna bataso.

"Ya kamata kabar kitchen din nan kafin wani ya shigo ya ganka" Ta fadi masa tana
qoqarin maida hijabinta. Taku uku ya isa gabanta,ya sanya hannu ya fusge hijabin
yana kuma jawo kujera dab da ita ya zauna ranshi a hade yana fadin.
"Wace irin mace ce ke?.....bakiyi kewata ba?" Yayi tambayar da gasken gaske tun
daga qasan zuciyarsa,yana fatan ko sau daya yaji tace tayi kewarsa.

Wani kallo ta watsa masa sannan ta janye idanunta,ta taka tana kashe
gas din sannan ta soma tafiya a nutse zuwa bakin qofa. Iya hakan ya bashi tabbacin
ficewa zatayi,ba kuma zaka kulashi ba kenan. A zafafe ya miqe yana wurgi da hijabin
nata,ya sake shan gabanta yana mata wani duba nakai tsaye. Ko ba'a gaya mata ba
zuwa yanzu tana saurin gane abinda ya taba zuciyarsa. Sauyawar yanayinsa wani abu
ne da yake saurin razanata.

Soma hade tazarar dake tsakanin su yayi yana duban idanunta sosai.

"Na tsani nuna halin ko in kula......na tsani wannan attitude din.....Please
behave.....or I'll have to take disciplinary action" Yayi maganar har zuciyarsa
yana nufin abinda ya fada din soft lips dinta masu kalan red dake motsawa kadan
kadan alamun tsiwa na cinta suna fusgar hankalinsa. Yasha imagination na sanda zata
mallaka masa su ba gardama ba tare daya qwata da qarfi ba......bama iya su kadai
bama.....dukkaninta yakewa wannan fatan da kuma burin. Lallausan tafin hannunta ya
matsa yana sauraren Jin muryarta. Muryar data zame masa abokiyar hirarsa a mafarki
tun waccan ranar data amsa wayarsa a garin makka.

Idanunta ta jjanye daga kanshi,har yanzu batajin zata iya kulashi
din......duk sanda ta kalli fuskarsa fareeda take gani kwance cikin
qirjinsa.....duk sanda ta kalleshi munanan maganganunsa a kanta take
tunawa.....muguntarsa da musguna mata da mugayen maganganu,don haka ta taka zuwa
side din hagunsa da nufin rabeshi ta fice.

Cak ya dagata ya azata saman kitchen cabinet din ba tare da tunanin tayi
kusa da qofa ba,ko kuma jama'ar dake gidan ba. Hannayensa ya sanya ya zagaye
bayanta dasu,ya hana mata kowacce dama da zata raba jikinta da nasa,ya kuma yi kane
kane a fuskarta ya hanata matsawa ko kadan,da wannan daman ya samu ya riqe lips
dinta da suke tsone masa idanu ya fara aike mata da wani irin tattausan kiss. Ba
wannan zafin ba kuma wannan hanzarin,wani irin sarrafata yakeyi da wani irin sanyi
da salo daya soma zare mata duk wani kuzari da takeji da kuma zafin da takeji a
kansa.

Duk wani tunani nata ya tsaya cak tun daga sanda ya wuce cikin
kitchen din. Wani abune da yazo mata a bazata wanda bata taba tunanin zai faru ba.
Yau fu'ad ne a gabanta ya tsallake yabi mace kitchen da zummar zai samo ruwan
dumi?.

Cup din hannunta ta ajiye tunaninta yana komawa baya,ta saita dukkan
idanunta da hankalinta akan qofar kitchen din tana lissafin mintuna nawa zaiyi
kafin ya fito. Falon yayi shuru saboda wucewar kowa sai ita daya data rage,ta dauke
kanta tana duban agogon hannunta bayan shudewar

Please Login or Register in order to submit comment