You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dake da baiwar narkar
da zuciyar diya mace ya kuma mantar da ita komai. Abinda yayi imani dashi
shine,yadda kowacce diya mace a kullum take fadi tashin neman hanyoyin faranta ran
namiji da burgeshi,haka ya kamata kowanne namiji shima ya kasance cikin sanin
hanyoyi da salon mallake zuciyar matarsa......wannan dabi'ar tasa ta sanya yayi
zarra a zuciyar sabreen din.

Sai data tabbatar ta samar masa da nutsuwa sannan ta baiwa kanta hutu
tana aje numfashi,ya birkitota yana maqaleta a jikinsa bayan sunyi alwala sun dawo.
Shuru ne ya ratsa tsakaninsu,kafin daga bisani taji saukar numfashinsa a hankali
bacci me cike da nutsuwa yayi awon gaba dashi.

Sai bayan sallar isha'i ta samu saukowa daga wajensa,a lokacin ya fita
sallar isha'i,da wannan damar ta samu tayi wanka tayi kwalliya kuma cikin atamfa
kaman yadda ta saba idan zasuci abinci nasu duka.

D'as d'as take takawa kaman ba wannan jikin bane ya fidda rai goma
ba,har ta iso babban parlor din da anan aka gina katafaren dakin cin abinci.

Ta samu kowa yana gurin,kowa kuma yasan mazauninsa yana kai a
zaune,sauran wadanda basu hadu ba sai a sannan irin musaddiq saddiq da farouq duka
a nan suka gaisa suna tayata murnar ci gaban da aketa samu.
Kowa ya hallara kuma faud din ake jira,shine qarshen shigowa,yana
takowa a nutse da wata irin haiba da kwarjinin da ya qara yawa sanadin shekaru da
kuma riqo da addini da yake dashi,kwarjinin da yake hana mutum musu dashi ko yin
abu ba daidai ba,kwarjinin da hatta sabreen a yawancin lokuta yakan daketa duk kuwa
da cewa dazu dazu suka rabu a daki cikin wani sirrintaccen yanayi,amma yanzun data
kalleshi kwarjinin nan ya dawo fes saman fuskarsa.

Kusan yara yaran a tare suka gaidashi,su sabreen huda fannah da amna
suka fara serving na kowa da kowa a nutse ba wani hayaniya kaman ba taron mutum
kusan talatin ba.

Cikin qauna da tsabar sabo da juna suke cin abincin,hirarraki suna
gudana a tsakaninsu. Har yau har kuma gobe yana maintaining class dinta a
idanunsa,bata duba an dade tare.....an jima da juna ta dinga wasu abubuwa da babu
aji sam cikinsa a wajen diya mace( mata yana da kyau ku kula da wannan,stay classy
please,karki dinga abu gaban miji wargazaza koda shekara dubu kukayi ki tabbatar
masa ajin nan fa akwaisa,idan ba haka ba ya hango wadda bata kaiki ba nata ajin ya
dinga dibansa yana burgeshi).

Shi dinma satar kallonta yakeyi,yanason gano meye ya banbantata da
sabreen din shekaru goma sha baya?. Ya dade yana against in din maza da yawa akan
suna da babban laifi da muhimmiyar rawa da suke takawa wajen wargajewar
matansu,mace 'yar tattali ce.....'yar a bata kulawa ce,mace tamkar fure take,dole
idan anaso aci gaba da ganinta sharshar a tsaya mata da ban ruwa,wato cima sutura
muhalli abun sha me kyau,a debe mata damuwa daga zuciyarta.

Ta samu daman zama da amaren nadra da haneefa har kusan sha daya na
dare,don shima sun kebe dasu musaddiq suna tasu tattaunawar,har suka kammala ya
dawo ta parlor din.

Daga tsaye yake dubanta da lumsassun idanunsa,hannayensa cikin aljihun
rigarsa.

"Madame.....baa kammala bane?".

"Saura kadan hamma" Agogo ya kalla sannan ya sauke dubansa.

"Kubar addan nan ta huta mana.....da safe sai a qarasa" Dariya nadra da haneefa
suka saki suna miqewa gami da tattare kayan da take dubawa,haneefa tace

"Hamma babu ruwanmu fa,tun dazu mukace mata xamu qarasa gobe tace yau xaa
gama.....saida safe" Ta shilla da dan qaramin gudunta tana bin bayan nadra da tuni
ita ta fece.

Ta dawo da idanunta daga kan haneefa tana murmushin wai auta itace yau
da aure?,saiji tayi kawai anyi sama da ita.

Wutsil wutsil ta fara yi da santala santalan qafafunta kamar qaramar
yarinya.

"Hamma......please mana,kada wani ya ganmu mana?".

"Who cares?" Tunda taji ya fadi haka tasan zai wahala ya sauketa idan ba fita
sukayi ba,don haka ta kwantar da kanta saman qirjin da duk duniya yafi mata ko ina
dadi da samun cikakkiyar nutsuwa.

β˜…Kwanaki uku kacal da dawowarta aka fara bikinsu nadra din,iya events din
data fada din kusan haka aka yisu. Saidai fa tun ranar bridal shower fu'ad din bai
sake barinta taje komai ba,saboda wani irin sassanyan kyau da tayi me daukan
hankali cikin wata butter color gown ita da iffa da tayi order dinta tun daga
Egypt,tana yawo kuma da tag din bride sister daya sake bata ranshi. Lallaba kayanta
kawai takeyi,tasan halinsa sarai a kanta baida sauqi,ta samu ta saukeshi ta kuma
kiyaye dukka dokokinsa har aka gama bikin lafiya. Saidai ko bayan bikin still mitar
bridal shower day din ya dinga mata,saida ta samu ta bashi wani zazzafan dare guda
daya sannan ta wanke kanta.


*_GRADUATION DAY_*
*@KING ABDUL'AZEE INTERNATIONAL SCHOOL*


Triplet din 'yan qasa nigeria kuma haifaffun qasar madeenatul
munawwara......wasu irin yara ne da sunansu dasu kansu sukayi fice cikin makaranta
dama wajenta. Bawai don kawai farinjinin 'yan uku ba.....aah hatta da kaifin basira
da Allah ya zuba musu,matsanancin nutsuwa da sanin ya kamata.....inda daga qarshe
kuma suka zama dalibai madiya hazaqa da qoqari cikin daliban da makarantar ta
fitar.

Sanda makarantar ta tasosu ta tsaidasu saman stage tana wassafa kyawun
dabi'u da hazaqar yaran sai sabreen ta kasa daurewa,ta kifa fuskarta tsakanin
tafukan hannayenta tana jin wani irin alfahari da yaran da kuma qaunarsu tana
ratsata.......wani irin farinciki da batasan yadda zata misaltashi ba na kyauta da
baiwar yaran da Allah yayi mata,wanda a yanzun haka cikin amsa kuwwa ake sanar da
kowa cewa su din cikakkun 'yan qasa ne.....gwamantin saudiyya kuma sun dauki nauyin
komai da komai nasu saboda girmamawa da jin dadin yadda suka zauna da kowa cikin
makarantar dama qasar lafiya.

Da qyar ta iya isa tsakiyar yaran nata don karba musu kyaututtukan
karramawa da suka samu,duk da jikinta a lullube yake kirif,baka ganin komai nata
sai zagayayyar fuskarta,amma duk da haka wasu sun cika da mamakin cewa itace
mamansu. Tun tana iya amsa har gifts din sukafi qarfinta saida jadda dake sanye
cikin wata rantsatsiyar shadda ya tako da sanyin nan nasa da nutsuwarsa ya
tallafeta da wasu kayayyakin.

Ranar wata rana ce da bazata gushe ba a zukatansu,cike da tarihin da bazai
kankaru ba cikin rayuwarsu.

Already sun tsara ana kammala taron zasu koma makka su sauke umra gaba
dayansu,saboda nuna godiyarsu ga Allah da kuma sake roqon ubangiji ingantacciyar
rayuwa me dorewa.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


*_NACE BA......._*🧏🏽🧏🏽

*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*

*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*

*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_*

*_Da yardar Allah saikin godemin_*

*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*πŸ˜‚πŸ˜‚
Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray

*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*

*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*

*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI*

*SUNA NAN A*

*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_*

*BA'A KANO KIKE BA?*

*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin
aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*

*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*πŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎ
wa.me/+2348103155915

KO KI KIRATA TA NAN

08103155915


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 175


*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
____________________________
*_PLEASE FOLLOW MY TIKTOK PAGE_*πŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎ
https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1
__________________________



175
A maimakon jirgi a babbar lafiyayyar mota suka taho zuwa makka. Wata
irin tafiya ce ta iyali me dadin gaske,hirrraki da labarai duka sun cika motar dake
dauke da JADDA FAMILY.

Saidai duk da hakan daga can seat din baya ita da fu'ad ne zaune,tadan
dora kanta saman kafadarsa tana jin kasala da wani saqe saqe da cikinta yayi mata
wanda batasan Meye dalili ba.

A fili kuwa hotunan graduation din take kalla daya bayan daya. Duk
inda zata wuce fu'ad da yaran sai tayi zooming ta kallesu sosai,tana jin kaman ba
yaranta ba,kaman wani imagination ne a cikin duniyar mafarki ma,har sai da fa'ad
daketa sauraron shirmen yaran daga gaban motar yana murmushi kadan kadan ya ankara
da ita.

"Kina mamaki ne?" Kai ta daga ta kalleshi sannan ta maida saman kafadarsa.

"Ina mamaki mana hamma......yau sabreen da kowa ke mata kallon KARUWA da yara irin
wannan?,sabreen din da kowa ya gaza janta a jiki yaji meye damuwarta,meye kuma
uzurinta yau ita keda yarannan?......sabreen din da tafi kowacce yarinya nutsuwa da
hankali saboda ita din rainon ummee ce yau ta zama haka meye sila?,ba hujja ba
dalili sai yanke hukunci babu bincike". Bata tsaya jin ta bakinsa ba ta dora.

"Alhaji ahmad me citta shine asalin sunan mahaifina,wanda ya shahara da sana'ar
saida citta kanunfari da sauran kayan da suka danganci wannan da wasunsu ma daga
qasar larabawa ake shigo musu dasu. Abbana ya auri ummeena ne a sanda yake da matan
aure biyu da yara mata goma sha biyar,ummena ce ta uku,mace me tsananin haquri da
kawaicin daya sanyata taci nasarar zama da sauran matan abbana,wanda cikin su take
da babbar abokiyr adawa wato bibo,wadda ita ummee ke bi. Abban mu ya tsaya sosai a
kanmu,shanmu cinmu tarbiyya da iliminmu,don har yanzu tasirin dagewarsa ce a jikina
na ilimin dana samu daga private school daya sakamu me tsada,tun daga matakin free
nursery har secondry,duk da cewa ina js 3 abbanmu ya koma ga Allah,ummenmu itace ta
jajirce naci gaba da wannan makarantar har na shiga ss3 second semester,a lokacinne
Allah yayi mata rasuwa,a lokacinne asirinmu ya tonu,maraici kuma ya afko.mana gadan
gadan,ummenmu ba 'yar qasar nan bace,don haka bamu da kowa a kusa damu da zai
tallafemu. Sh momma sunso tafiya damu amma kawu ya saka kuka,wai ya za'a tafi da
zuri'ar ahmadu yana raye?,shi yayi alqawarin kula damu kaman yadda abbanmu ya kula
da rayuwarsa. Abbanmu ne ya riqeshi bayan rasuwar iyayensu tun auren abban ma na
fari,bai kuma qyale kawu ba sai daya aurar dashi ya hadashi da jari yana saka ran
wasu halayensa da bayaso zuwa sannan kawun ya dainasu. Da wannan yaqinin suka barmu
hannunsa,ashe kuma lokaci lokaci suna masa aike da sunanmu,amma ko labari bai taba
bamu ba bare muga abinda suka kawo.

....... Tom ko bayan mutuwar abba kowacce mace ita ta koma hidimar kanta da
kanta,to yanzun da bamu da uwa sai ya zamana ba wanda ya damu damu,ba wanda yake
dubamu,ba wanda yake damuwa da munci bamu ci ba,munsha ko bamu sha ba,mun tashi
lafiya?,waye baida lafiyar?,dukka ba wanda ya saka hakan a tsarinsa. Da farko na
dauka abun na wasa ne,na dauka zasuji qanmu,saina fara nema mana abinci daga
dakunansu kafin na fahimci ba wanda zai iya cida mu,don da zagi nake fita a dakin
da qyama da tsangwama,daga bisani dole na koma roqarwa su huda a maqota,donni ban
damu naci ba,muddin sukaci shikenan tawa me sauqi ce,zan iya kwana uku ma banci
komai ba,saidai nasha baqin ruwa na kwanta. Sannu a hankali suma maqotan suka fara
hanani,sai ya zamana mun qarasa galabaicewa,ciwon yunwa yanason kama huda da
haneefa da bata gama sanin ma me ake ba idan yunwar taji ba. Ba wanka ba wanki don
ba wanda zai bamu sabulu,saidai da yake ummenmu ta saba mana da tsafta hakanan
mukeyi da zallar ruwa.

Maqociyarmu kuma qawa ga bibo ita ta fara bani shawara.
"Kina da kyau sosai sabreen,kaf gidanku ba yaro me kyanki.....me zai hana ki
tallata hajar jikinki?,wallahi abinci ma saikun bawa wani" A ranar hankalina yayi
mugun tashi,mukayi uwaka ubaka da ita,kaf kimarta ta zube a ido na,ita kuma ta
kamani tamin shegen duka akan na mata sata kuma na mata rashin kunya. Ba wanda ya
damu yaji ba'asi saboda basa sonmu bamu da gata,saima tayata da bibo tayi,haka nayi
kwana uku kwance ina zazzabi ba magani a dole na warke. Sanda naga yunwa na neman
rayuwarmu saina fara da tambayar alhaji baqo,aboki na kusa ga mahaifinmu wanda nake
kyautata zaton zai iya taimaka mana" Shuru tayi tana hadiyar wani abu me ciwo.


"Saidai abun mamaki abinda kuma ko yau na tuna yakemin ciwo,ya nemi yaci amanar
amintaka,ya nemi na bashi mutuncina yaci gaba da ciyar damu duka. A nan ne naci
masa mutunci saboda mamakin daya bani,kamar yadda mukayi da waccar matar shima duka
yayimin ya hadamin da sharri,abu na farko daya fara qeqasarmin da zuciya,na fahimci
kaman ba wanda zaiji tausayinmu a unguwar,binda yasa na kasa mantawa ko yafewa,na
koma na kunna masa gobara a dakinsa data jaza masa asara me yawa,ya gano nice,yace
zai kaini ga 'yan sanda,na gaya masa ina da shaidar cewa muddin ya aikata haka ni
kuma nizan babbake gidansa duka da 'ya'yansa da matansa,abinda ya sakashi haqura
kenan,tun daga ranar idan na ganshi sai tsaki habaici da tsartar da yawu,sai duka
ya tsargi kansa yana tsoro kada na tona masa asiri,sai ya koma kaman sirikina. Daga
nan saina fara yawon nema mana abinci,duk da ba cikin kyakkyawar kama nake ba,amma
duk wanda ya ganni ringidi ringidi zai jani ya kaini gun cin abinci a zubamin,saina
juyewa su huda a leda,sukance ki cinye,indai kin bamu hadin kai lallai abinci
saikin ture. Mutun na farko daya fara nunan me hakan yake nufi na samu na gudu ina
zaginsa,akayi na biyu na uku na hudu na biyar shida har goma,duk wanda yaga bazai
samu abinda yakeso ba saiya qwace abincinsa. Maza da yawa haka muka dinga yi,abinda
ya sake dasamin duniya ba imani.....babu me taimako don Allah sai don wani abu na
daban,dana fahimci haka saina fara tunanin ta yadda zan amfana da kudadensu ba tare
da mutuncina ya tabu ba.

.....salis shine mutum na farko dana fara gwada hakan a kansa,na saka masa
maganin bacci a lemo,na kuma debi kudade masu yawa na gudu. Wannan kudin su suka
fara canza rayuwata,na siya mana abinci me yawa,suturu da komai na fara kwalliya
muka fita daga qazanta.

Da bincike salis yasa aka samoni,aka kamani,kamun da dashi bibo tayi
amfani ta fara bugamin tambari da batamin suna,tunda tana baqinciki kwana biyu muna
cikin abinci da duk kayan wadata na rayuwa,saita saka idon lallai sai tasan inda na
samo,saiga case din salis.

Sanda ake tuhumata na kasa bada amsa,na tsinci dai wata murya tana cewa.

"Ku saketa fa,nine shaida bata da laifi,ya cinye kudinsa ne kawai zai laqabawa
wata" Wani matashin dan sanda ne ya fadi haka. Wannan shine jib,silar haduwarmu
kenan,mayen computer na gaske da salis da yake kawunsa yaqi taimaka masa da
registration a shekarar qarshe da yake ciki saboda rashin kirki,wannan ya sanyashi
rasa damar karatunsa,da cuku cuku ya samu aikin dan sanda da qaramin albashin da
bai wuce ladan ganin ido ba.

Haduwarmu uku da jib magana ta hadamu. Shima maraya ne,banda wanda nake
gayawa damuwata amma ganin kirkinsa da yadda da nayi da nutsuwarsa a ranar mukayi
dogon hira dashi.

"Basa taimako Don Allah,ni shaida ne.....amma idan basu taimakemu don Allah ba,zamu
diba ta qarfi da yaji" Da taimakonsa muka soma gudanar da plan dinmu,ranar farko na
fadi,aka biyo sawunmu,Allah ya hadamu da busari ya daukoni kyauta,wanda tun daga
ranar ya zama dan adaidaita sahuna,daga baya bayan uban gidansa ya qwace abun
hawansa,na hada dukka kudina na siya masa wata,sanadin haka kwananmu biyu ha
abinci,saboda shi dinma marayanne,kuma shike daukan nauyin tsohuwar mamarsa wadda
shi kadai Allah ya bata a duniya"

"Sannu a hankai aikinmu ya dinga tafiya daidai,indai zan fita sai nayi nasara,ina
yin nasara ina gane cewa maza babu Allahba ransu,wasu mazan sukan daukaki matan
bariki su wulaqabta iyalinsu,wasu mazan kuma saidai ki bada jikinki su baki
kudi,don haka mukayi tsare tsaren da duk wayonka bani zuwa gurin da kakeso,saidai
na sameka a guri public mu qarqareta a nan,na zare kudin ta hanyar taimakon jib
dake sarrafa na'uarar,daga ranar kuma ba zaka sake jina ko ganina ba,bazan sake
kuma zuwa duk wani guri da muka taba haduwa dakai ba. Nasha samun barazana amma
Allah ya kiyeyeni,ban taba yarda ko farcena wani namiji ya tabamin ba duk kuwa iya
wayonka,wanda ni nasan hatsari na saka kaina me girma,ba wayona ko dabarata bane
kuma ya qwaceni ba,zuciyata akwai Allah ya duba.

Duk namijin da zan hadu dashi ina fara karantarsa,adadin son matanka da
fasiqancinka.....adadin barnar da zaka gani a dukiyarka......akwai nutsasun maza
daidaiku dakeson aurena da tun tafiyar farko nake zamesu daga gareni saboda basu
cancanci na cutar dasu ba,amma kuma bani da wani nufin aure kai ko sha'awa ma baya
bani.....mazanma dukkaninsu haushi suke ban,saina sallamesu salin alin duk iya
nacinsu kuwa.

Yadda nake shiga me kyau nake fita da yadda duk wata buqata nake sauke
mana ita ba tare da anga ina sana'ar komai ba sai bacin suna yahau kaina......yayin
da shaidar zur dasu bibo ke qarawa 'yan waje ya sake basu qwarin gwiwar yadda da
komai a kaina,ban damu sosai ba sai dana qara hankali,amma damuwata ta dadu qwarai
sanda naga suna qoqarin brainwashing ma su hud akan qazafin karuwanci da zina.

Kudi suka fara shigowa har suka fara fin qarfin buqatuna,sai a sannan na
lura akwai tarin marayu a unguwanni daban daban,mabuqata marayu da iyayensun harma
da marasa qarfi......saina saka marayu guda hamsin nauyin su saman kaina,duk wani
abu da zan samu kuma kasonsu yafi nawa yawa,a haka na dinga kula dasu da nawa
qannen......har xuwa sanda na hadu da mika'il komai kuma ya faru" Ta qarasa
maganar tana sanya gefan mayafinta tana share qwallar data jiqa mata fuska.

"Ki yafemin......ki yafemin sabreen don girman Allah......ku tayani roqar anni ta
yafemin" Muryar maamah data sauka musu a baza wadda ta saka sabreen sake sakin
kuka.

Ashe dama akwai rana irin wannan da zatazo?. Sautin kukan ya taso anni
tana dubawa ko cikin yaranne suke rigima,saidai sanda ta kawo qarshen motar taga
sabreen ce saita zauna a wata kujerar tana shirin tambaya,amma yadda maamah ta riqe
hannunta gam cikin nata ya tsoratata ya kuma bata mamaki.

"Ameenatu ki yafemin........ki yafemin,iya abinda zan iya cewa daku
kenan....kunyimin halaccin da bazan iya biyanku ba amma baqar zuciya da shaidan
gaba daya sun sanya idanuna rufewa,kin yafemin don girman zatin Allah ta yadda idan
na tashi mutuwa zan mutu cikin salama". Sosai qirjin fu'ad yayi nauyi saidai wani
farinciki kebantacce yana dawainiya dashi. Har yanzu ya daina jin sautin kukanta na
daren jiya,sanda ta sanyasu a gaba shida musaddiq akan su yafe mata. Wani irin kuka
dake dauke da zallar nadama cikin ido murya da kuma lafazinta. Daga shi har
musaddiq ba wanda baiyi kuka ba......wani hukuncin Allah da lamari na uwa
kuma.......cikin awanni biyu kacal da sukayi zaune da ita tana qoqarin basu labarin
komai da hardaddiyar muryar ta,saiga zukatansu dukka sunyi wani irin sawai. Basu
bar dakinba saida tayi bacci tsakanin qafafunsa shida musaddiq,wanda ko bayan sun
fito a dakin shi da musaddiq din ganin komai suke kaman mafarki,sai suka samu kansu
da rungume junansu. Fu'ad ke lallashin musaddiq

"Ba abinda yafi qarfin addu'a......ba wani lamari da yafi qarfin
Allah,alhamdulillah da Allah ya qaddara mata shiriya tunda sauran damarta" Wadannan
kalaman su suka tsagaita kukan musaddiq.
"Anni ki roqamin hamza ma......na cutar da mutane da yawa ta fuskoki da
dama......amma yanzu kune nake gani kune tare dani ku kuka rage.....ku yafemin naji
dana sauran mutane.....hajja da laila dukkaninsu babu su bare na nema yafiya a
garesu........fareeda ta haukace bata da cikakken hankalin da zamu yafewa juna nida
ita".

"Allah ya yafe mana gaba daya" Cewar sabreen qwallar farinciki na fita a idanunta.

"Allah ya tabbatar damu kan hanya madaidaiciya.....Allah ya kyautata qarshemu" Anni

bata mutu da haqquna ba saina wadanda suka rigata gidan gaskiya.𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
ta qara da wannan tana goge Qwallar farinciki da Allah ya qaddarawa maamah shiriya

_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 176


*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
_____________________________
*_PLEASE FOLLOW MY TIKTOK PAGE_*
https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1




176



Zuwa yammaci sun daura niyyarsu suka kuma fara gabatar da umarar wanda
cikin awa biyu suka sauketa.

Itakam sabreen kusan duk sanda sukazo tana yin nesa ne da ayarin
familyn jadda,don tana jin kamar tafi kowa yawan buqata a cikinsu.

Sau tari bata sake haduwa dasu sai a masauki. Abinda ya gudana kenan
yau dinma,don bata tashi komawa hotel dinsu dake daura da harami ba sai tsakiyar
dare.

A gajiye ta bude dakinsu wanda yake cikin jerin dakuna mafiya tsada
dake hotel din da BB farouq ya kama musu. Kowa da iyalinshi,sai kuma babban daki
dake dauke da bedroons guda biyu,anni ta dauki daya maamah ma ta dauki daya da
jikokinsu da masu aikinsu.

Da sallama ta shiga dakin,muryarta can qasan maqoshinta da wata irin
gajiya a jikinta.

Yana zaune da farin soft and cotton shirt me zagayayyen wuya,sai boxer
da bai qarasa idon sawunsa ba.

Littafine a hannunsa wanda yake bayani akan hajji da umra da kuma
falalar madeena yana dubawa,ya daga kai a nutse yana amsa mata gami da zuba mata
narkakkun idanuwansan nan. Qafafuwansa ya janye yana gyara mata pillow din dake
wajen,da idanu ya mata nuni tazo ta zauna,saita qaraso tana zubewa saman kujerar.

Hannu ya miqa ya zare mata hijabin jikinta bayan ya karbi handbag dinta
da carbinta ya ajiye,ya zare mata hular saman kanta,wanda hakan ya bawa gashinta me
sulbi daman bajewa.

"Yanzun nan nake shawarwarin binki.......daren yayi yawa duniyata......me kiketa
roqa hakane wanda Allah bai baki ba?" Ya qarasa tambaya da murmushi kan fuskarsa
yana miqa mata ruwan daya tsiyaya mata a cup.

Sai data maida masa murmushin sannan ta karba ta shanye,ta ajiye cup
din tana dubansa.

"Na godewa Allah......na gode duniyata......haqiqa Allah yayimin komai tunda ya
bani kai......saidai 'ya'yanmu....uwa bata da wani sauran bacci a sanda ta tara
zuria,kullum addu'arta shine yadda zasu samu rayuwa me kyau,ba irin rayuwar da
iyayensu sukayi ba suka tsallake da qyar".

"In sha Allah.....tun basuzo duniya ba tun iyayensu ma basu hadu ba muke roqa musu
rayuwa me kyau......ubangiji yaji kuma ya karba da yardarsa" Kai ta gyada cike da
gamsuwa,yayin da shi kuma ya miqe ya wuce toilet.

Ruwa me dumi sosai ya hada mata,ya dauko mata towel ya fito.

"Oya zaki wanka ki dawo ki kwanta ki huta,kin gama hidimar biki kikazo kikayi tasu
fauzan.......ga kuma zaman mana addu'a dana tabbatar idan ba nigeria muka koma ba
bazai barki ki huta ba". Murmushi tayi idanunta suna lullumshewa saboda tsananin
gajiya,ta miqe da qyar ya taimaka mata ta cire kayan jikinta ta karbi towel din
tana wucewa bandakin.

Dumin ruwan ya hanata gama wankan da wuri,har sai da ta gasa jikinta
sosai sannan ta fito,ta daura alwala ta tsane jikinta sosai,saita cire wata doguwar
riga daya zaba mata me taushi dake jikin hanger ta zura sannan ta tako a nutse ta
fito tana qoqarin daure gashinta da yayi mata damshi saboda ruwa daya taba.

"Hamma yau ko yatsana bazan iya dagawa ba......am really tired" Ta fada tana jin
idanun suna mata nauyi sosai. Shuru taji bai amsa mata ba,bayan tana hango
qafafunsa daga qasan idanunta yana daga tsaye.

"Hamma kaina ya jiqe,bazan iya busar dashi ba saida safe" Ta fada tana

Please Login or Register in order to submit comment