You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

'ya'yana
ba.....banda qaddara me zai hadani da riqon 'ya'yan wasu?" . Idanunsa a zube fes a
kanta,ya gyara zamansa sosai yana sake ci gaba da kallonta

"Inaso ki cire a ranki riqo kikeyi.....ba 'ya'yana na cikina bama.......hatta yaran
dana kawo yanzu,inaso ki ji a ranki Tamkar suna rayuwa ne cikin gidan mahaifinsu a
gaban uwa da kuma ubansu". Dukka haqurinta ya qare,ya tuqeta ta kuma kai bango,tana
jin ba zata iya ci gaba da zama tana sauraronsa ba,don haka ta miqe tsam,ta kuma
gegara ta gabansa tana barin falon.

Da ido ya bita har zuwa sanda take shirin bacewa ganinsa. Ya jima yana
ganin alamun da suke alamta masa akwai matsaloli masu yawa cikin rayuwar su
farouq,amma yayita qaryata hakan gudun kawo damuwa da matsala cikin zaman uwar wani
da d'an wani wanda keda wuyar sha'ani,sai gashi a qanqanin lokaci komai yana
bayyana kansa daki daki.

Numfashi ya zuqa ya fesar yana rufe idanunsa,qoqari yake ya saita
kansa yana tunanin hanyar da zai daidaita komai.

Tray din da faruqee ya ajjiye yabi da kallo,a dawowarsa daga lagos
wannan karon ya fahimci kamar ma suke yiwa kansu girki harma su hada da ita idan ta
kama,babu sakewa babu walwala sam tattare dasu. Ya lura da raguwar kuzarinsu kyara
da kuma hantara daga gareta,saidai dukka ya kauda kai don bai kamaci a karon farko
ya fidda soyayyar yaransa kai tsaye daga zuciyarsa har haka ba,bayaso yabar wani
tabo ko targaden da zai kasa gyaruwa tunda wurwuri haka.

Da idanu kawai yake bin dakin da kallo sanda Faruqee yaketa masa
bayani zuciya da fuskarsa cike da zumudi da farinciki.

"Kayi shuru?,ka tsaya a bakin qofa,ko dakin baiyi bane na gayawa abba a qaro wasu
abun?" Faruqee ya fada jikinsa yana sanyaya da yadda yaga fuskarshi. Don a yadda ya
zata zayaga farinciki sosai a fuskarsa kaman kwatankwacin nasa farincikin na
dawowarsa cikin gidansu,farincikin samun aboki me hankali irinsa,farincikin samun
aboki da yayi daidai da shekru da hankalinsa,ba aboli irin qaninsa ba da sam.baya
gane wsu abubuwan saboda sabanin mizanin hankali da fahimta dake tsakaninsu.

Karon farko yayi qoqarin sake fuskarsa da kyau yana kallon faruqee.
Dakin gata kuma dakin yaran gata irin wannan da shi din bai taba samun
kwatankwacinsa ba ta yaya zaice baiyi masa ba?. Dukka alatu da yayi saura a dakin
bashi yake daukarsa ba.......duk da qarancin shekarun daka iya dakusar da tunanin
yaro a sannan......amma shi sun bawa qwaqwalwarsa damar budewa da yin tunani me
nisan zango akan

"Wacce irin rayuwa zasu fuskanta a matsayinsu na agola bayan su kansu tsatson gidan
basu tsira ba?,mene ne makomarsu?,meye farko da kuma qarshensu?" Tarin tambayoyin
da baisan ta ina zaa fara sauke masa su ba

"Nayi murna farouq" Ya furta a sanyaye,sunan da shi daya yake furtashi daidai yadda
yake,don har yau bai taba kiransa da faruqee ba.

Yadda qanin nashi ya zuba masa idanu ya sanyashi qoqarin sakewa,ya
qaraso ainihin cikin dakin kamar yadda sauran suka kai ga shigowar.

Qoqarin kauda komai ya dinga yi daga zuciyarsa,yana zaune daga
falon yana iya jiyo muryoyinsu sama sama,saidai har yanzun baiji tashi muryar ba.
Baiyi mamaki ba,don ya sani,yadda komai nasa ya fita daban daga cikinsu,haka
dabi''arsa da halayyarsa ma ta zama daban.

Abincin yaja ya soma ci bawai don cin abincin yana masa dadi ko yana
burgeshi ba. Tunaninsa yayi zurfin da har ba komai dake wakana cikin falon yake
ganewa ba,bai taba zata ba,bai kuma taba kawowa rabuwa da rabi'atu zai iya zame
masa qalubale ba sai yanzun da dukkan alamu suka fara bayyana kansu. A karon farko
har yaji ya fara tuhumar kansa da kansa,tare da nacin son gano meye ainihin laifin
rabi'atu ne har ta cancanci a saketa?.

Baici da yawa ba ya ture,ya miqe yana irgen lokaci,sai ya juya ya
fara takawa zuwa dakin yaran.

Dukkansu sunyi shirin bacci amma bandashi,yana zaune gefe daya na
gadon farouq,ya goye hannayensa a qirjinsa tamkar wani babba da yayi nisa cikin
nazarin wani abu.

Motsin abban ya sanyashi waiwayowa,da sauri ya sauke hannayensa yayi
qasa da kansa yana niyyar zamowa daga saman gadon

"Yi zamanka me babban suna......tunanin me ka zauna kana yi?,duk 'yan uwanka sunyi
shirin kwanciya banda kai?" Farouq dake zaune tsakiyar gadon yayi hanzarin karbar
maganar dama tana damunsa tun dazu

"Abba yaqi ya canza kaya,na bashi kayan bacci yaqi ya saka tun dazu" Hannu kawai
abban ya miqawa farouq din,sai ya saka masa kayan baccin dake gefansa.

Kayan abban yabi da kallo yana jujjyasu a hannunsa,sannan ya maida
dubansa zuwa jikinsu dukka su ukun dake sanye da wasu kalolin kayan.

"Amma faruqee ban gaya muku a bada kayan nan ba dukansu?,ina kayan dana kawo muku
wancan tafiyar da nayi?" Ya qarasa tambayar yana maida idanunsa kan saddiq qaninsa.

Har wani juyawa saida cikin saddiq din yayi,saboda tunawa da yayi da
kakkaifan warning din da suka samu daga wajen matar gidan akan batun.

"Abba,dukka mama ta karbesu,ta kuma gargademu kada mu sake mu sanar dakai,idan ba
haka ba saita tsoma kawunanmu a ruwan zafi" Ba abba kawai ba,hatta me babban sunan
saida maganar ta ratsashi duk da qananun shekarunsa,amma zuwa yanzu ya dade da yiwa
kansa karatun qalubalen da suke shirin fuskanta

"Ruwan zafi?" Abba ya furta cikin tsananin kaduwa da mamaki,sai faruqee ya gyadawa
abban kai. Maganar ta ladabtar d abba ta sanyashi samun waje ya zauna. Yana tsoron
ci gaba da wannan tafiyar tasu......yana tsoron garin neman lada ya rufta ya buge d
wucewa jahannama,ya debo marayun Allah da nufin basu rayuwa me inganci,muddin
Mariya bata goya masa baya ba meye makomar yaran?,ya gobensu zata kasance?.
Tambayoyin da suka dinga karafkiya kenan a kansa.

Indai haka ne ya zama dole yayi jan ido,ya zama dole yayi wuta wuta
akan gidansa da iyalinsa. Ya sauke dukka nauye nauye haqqunan da suka zama wajibi
dama wadanda basu zama wajibi bs,ya zama dole to itama ta bishi yadda ya kamata.

"Ba komai,tashi me babban suna ka shirya,idan kun kammala ku kashe kayan wuta gaba
daya kuyi addua ku kwanta" Yayi maganar ne yana sake nazartar dakin tare da kallon
guraben da ga siya ma yaran abubuwa da dama ya ajjiye saboda jin dadin Rayuwarsu a
yanzu ba komai a wajen sai gurbinsu.

Sai daya kammala komai daga ainihin dakinsa sannan ya zarce dakin
mariya. Ta gama shirin kwanciya tsaf tayi rub da ciki tsakiyar gado tana latse
latsen waya. Fuska a hade ta daga kai ta kalleshi sau daya saita dauke kan nata ta
maida ga wayarta tana sake tsuke fuska.

"Tashi zamuyi magana" Ya fada cikin yanayin dake tabbatar mata da gaske yake,da
kuma zafinsa ya shigo. Sai da tayi kamar ba zata tashi ba sannan ta miqe ta zauna
sosai tana gyara wuyan rigar baccinta tare da tsuke fuska da kyau.


*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA
TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_
*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*πŸ₯°πŸ₯°


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

*Arewabooks:Huguma*

Page 05 last free page




"Asama'u" Ya kirayi sunanta da wani irin yanayi da har cikin zuciyarta ta tabbatar
cewa......dukka maganar da zata gita yanzu haka daga bakinsa ,yankakkiyar magana ce
wadda babu janyewa a cikinta ko kuma wani sauyi bare sassauci

"Ban rabu da mariya ba don na auro wata matar tazo ta azabtar min da 'ya'ya ba,ina
tsananin qaunar 'ya'yana fiye da soyayyar da nake yiwa kaina,duk soyayar da zaki
gwadamin bata da alfanu rana ko kuma fa'ida a gareni muddin ba zaki so 'ya'yana
ba......asama'u,na rantse da Allah,dai dai da rana guda na samu wulaqanci cin amana
ko tsanantawa diyoyina bisa ganganci bawai kuskure ko ajizanci irin na dan adam ba
bazan raga miki ba"..... Wani dum taji har tsakiyar kabta,batabtaba kawowa dukka
maganganunsa zasu kai har wannan iyakar ba,bata tana tsammanin abun yayi zurfi haka
haka ba,da ake gaya mata yana da son yara batabtaba kawowa yakai har wannan bigiren
ba.

Zuwa sanda zatakai qarshen tunaninta shi din ya jima da miqewa
yana kallonta

"Bazan fasa tafiye tafiye na wajen neman halak da neman abinda zan rufawa kaina da
iyalina asiri ba......ba kuma zan kwashe diyoyina na kaisu wanin guri ba,gaki gasu
nan asamau,dukkan abinda kika qudirta yi kada ki fasa koki sauya ra'ayi" Ya qarashe
fadi yanajin wani irin daci saman harshensa,bai kuma dakata ya saurareta ba ya juya
a nutse yana barin dakin nata.

Har sanda ya bacewa ganinta bata dauke dubanta daga bakin qofar
dakin ba,ta qanqance idanu tana kallon qofar tare da jin dacin kalamansa suna
gauraya kowanne sashe na jikinta. A taqaice dukka bayanansa suna auna mizani da
kuma adadin iya matsayinta kenan a wajensa?. Bata shigo gidansa don ta fita ba,don
muhallin dame muhallin duka sunyi mata,amma kuma bata shigo bautar d'an kowa
ba,hakanan bata shigo don a takata ko aci mata zarafi ba bare kuma a hanata sakewa.

Shawara take buqata kawai a yanzu hala,don gaba kura ne baya
sayaki,ta kula dasu ko ta barsu komai ta fanjama fanjam?,to amma fisabilillahi zai
yiwu kuwa ace ta buge da bautar d'iyoyin da ba ita tayi Jigilar daukar ciki da kuma
rainonsu ba?.

Matsawa tayi kusa da wayar landline dake gefan gadonta,ta latsa
lambobi tana fatan sashen kamfanin sadarwar ya sadata da matar data kira take
mararin magana da ita. Ba'a dauki dogon lokaci ba sukayi mata hakan,saita qarasa
sauke dayar qafar tata qasa tana zama sosai yadda zatafi jin dadin amayar da abinda
ke cikinta.

Yanayin yadda suka gaisa kadai zai gaya maka akwai shaquwa me zurfi da
tsohuwar sanayya a junansu.

"Ya nake jinki haka sama sama?" Daga saya bangaren ta tambayeta. Sai data aje dogon
tsaki sannan ta fara magana,zuciyarta cike da wannan bacin ran da batasan ranar da
zai wanke daga zuciyarta ba

"Barni kawai......dukka shirina har yanzun bai tafi a yadda na jima ina tsarawa ba"

"Wani abunne kuma?" Kai ta rausayar tana jin kamar ta qifta idanuwanta ta budesu ta
tarar babu kowa tsakiya da gefannin rayuwarta da mijinta,daga ita saishi

"Yarannan haleema......bayansu ya sake kwasomin riqon marayu,bayan wadannan din har
yanzu ban gama da matsalarsu ba......" Daki daki ba tare data rage komai a abinda
yake faruwa ba ta shimfida mata,sannan ta dora da fadin

"Inajin kamar naje gurinsa ayita ta qare haleema,na meye zaa dinga doramin nauyin
da bai zama wajibi a kaina ba?" Ajiyar zuciya haleeman ta sauke

"Ashe qarya kikeyi,baki shirya zaman auren ba" Haleema ta katsi numfashinta sanda
taji tana shirin sake dorawa da wata mitar

"Kamar yaya?,ya zakice haka bayan kinsan komai?" Ta tambayeta tana tsuke gira tare
da mamakin amsar data bata

"Eh to ai dole nace haka,wani lokaci sam baki da wayo asama'u,yaransa biyu da yake
mutuwar so ki gaza riqesu?,bakisan ta hanyar riqon da zaki musu bane zaki samu fiye
da abinda kike hange ko hasashe daga jikinsa?" Ta qarashe maganar da sigar
tambaya,tambayar data dauki dukka tunanin asama'u ta jefashi wani guri me nisa

"Amma haleema,saina zama baiwar yara har hudu?" Ta yiwa haleema tambayar tana
jinjina girman abun,tamkar wadda aka dorawa nauyin wanke kashinsu da fitsarinsu
gami da ci dasu tsahon kowacce rana da wuni na rayuwarta
"Bance haka ba,ban kuma goyi bayan hakan ba,yaransa sune dolensa,su zaki kama ki
riqe,saura kuwa wannan baida hurumin tilasta miki zama dasu,idan ma baki riqesu ba
bakiyi laifi ba,kedai yaransa su zama makamin zamanki a gidan,yo asama'u kona ganin
ido ne ke ba zaki iya ba?.......".

Dadewar da sukayi saman waya sa haleema iya adadin karatun data samu
daga gareta,ta kwanta ne tana juyawa tare da tauna yadda zata dauki shawarwarin
haleema tayi aiki dasu,ta yaya zata danne zuciyarta da dukka wani abu da takeji
tayi yadda haleema ta kwatanta mata?.

*_W A S H E G A R I_*


Dukka su hudun suna zaune a gabanshi,yana jansu da hira cikin yanayin
da zakayi tsammanin shi din wani babban yayane a garesu bawai uba ba.

Da idanu yake karantarsa,har yanzu dai bai sake ba kamar yadda
ragowar 'yan uwansa uku suke a sake. Har yanzu a darare yake,dararewar data
sanyashi yaji a ransa akwai abinda ya hanashi sakewar.

Har cikin rai da gangar jikinsa a yanzun da suke gabansa yake jin
kamar dukka su hudun mallakinsa ne,shine ya haifesu. Inda yana da iko tabbas zai
maida agogon rayuwarsu baya ya mantar da al'ummar da suka sanshi dama na unguwar
cewa shi din ba shine ya haifesu su biyun ba.

Tun daga nesa da take takowa cikin falon idanuwanta yake kansu.
Sunyi wanka dukkaninsu sun kuma shirya cikin shaddodinsu masu kyau,wadanda tayi
imani cikin sabbin kayan daya saba tahowa da yaranne. Sake maida idonta tayi a
kansu,a nutse yake qwarai fiye da dan uwansa,ba wani karsashi a tare dashi ko kuma
rawar kai,saidai kuma haka siddan takejin muguwar matsananciyar tsanarsa shi da dan
uwansa.

Ta yaya tun bata aje nata yaran ba ace wasu yaran sun shigo sun sake
cinye gurbi da muhallin mutum biyu bayan gurbin mutum biyun da yaran gidan suka
cinye?. A yanzun idan har ta soma aje nata yaran kenan saidai su tashi daga na
biyar?,ya za'ayi ta bari haka ta kasance?.

Sai data iso dab dasu sannan ta iya controlling kanta tayi sallama.
Dukkansu suka daga kai suna dubanta banda abba da ya kauda nasa kan kadan gefe don
da haushinta ya kwana.

Qoqarin gaidata sukayi,ta amsa tana binsu da kallo daya bayan
daya,wannan ya sanya kowa ya sake kama kanshi a cikinsu,bansa me babban suna wanda
tun daga kallon farko bai sake daga kansa ba bangaren da take.

"Ina kwana abba?" Ta gaidashi cikin matuqar qoqarin daidaita kanta idanunta zube
kan kayan breakfast dake gabansu.

"Lafiya lau" Ya amsa mata a taqaice yana rufe plate din fried egg din daya gama ci.

"Yau nayi bacci me nauyi ban samu tashi na hada abincin safe ba"

"Eh laraba tayi.......don dama fita nakeso muyi" Ya amsa mata yana miqewa.

"Ina haka da safiyar nan?" Tayi masa tambayar cikin son sanin komai

"Makarantarsu Faruqee,inason na yiwa su me babban suna registration,next week idan
Allah ya kaimu su koma tare baki daya" maganar tayi mata kama da almara ko kuma ba
zata. Tana tantamar akwai hikima ko hankali kuwa cikin maganganun abban?,ta yaya
zai dauki yaran maqota ya kaisu makaranta me kudade masu ciwo haka?,makarantar dako
yaran cikinsa da taji nawa ne school fees dinsu saida taji kishi da baqincikin
abun?,ta kuma bashi shawara a fakaice ya kusa sau biyar akan ya sauya musu da wadda
bata kaita ba.... Ko don yadda shima wani lokaci ta lura kaman yawan school fees
din yana dan takurasa?.

Abinda ya darsu a ranta me girma ne,tana da abubuwan da takeson ta
fadi masa amma girman bacin rai da kuma abinda ya tsaya mata a wuya ya hanata cewa
komai har suka tarkata suka fice daga falon.

Idan nace ta samu nutsuwa tun daga fitarsu har dawowarsu to zance ne
kawai. Sanda suka tashi dawowa din kuma sun dawo da dukka tarkacen kayan amfani na
buqatar rayuwa na yau da kullum. Komai hurhudu ya siya,amma kaf cikin siyayyar
bataga tsinke nata ba

"Somin tabi kenan hatsin gara a buta......tun yanzu?" Wani sashe na zuciyarta ya
ayyana mata. Ai juma'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta. Tun a rana ta
farko ta soma karantar iyakokinta?,dukka kuma akan yaran da suka kasance tamkar
wata tsintacciyar mage?. Yaran da basu da GATA ASALI ko wani GALIHU?. Ita kuwa
asama'u yaushe?,yaushe zatayi wannan SAKEN?. Muddin bata bazama su ba lallai anyi
asarar haihuwarta,muddin bata ganar dasu kuskuren maida UBAN WANI NASU BA bata cika
MACE BA....

*_BAN TABA KOMAI BAFA CIKIN LABARIN......BAN FARA KOMAI BA A CIKI_*

*_zazzafan labari ne tsakanin SABREEN DA MUHAMMED FU'AD_*

*_BANBANCIN RA'AYI TSARI DA AQIDA_*

*_MUMMUNAN ZATO DA GURGUWAR FAHIMTA_*

*_TA YAYA RUWA DA WUTA ZASU HADU GURI DAYA?_*

*_ZALLAR QIYAYYAR MAHAIFIYA HALITTA MAFI SOYUWA A DUNIYA_*

*_BAHAGUWAR BIYAYYA BISA TILASHIN ZUCIYA BA DON RAI YANA SO BA_*

*_GWANA KUMA QWARARRIYA WAJEN SACE ZUKATA DA ALJIHUN MAZAJE DAMA ASUSUNSU GABA
DAYA_*

*_KARKI SAKE AYI BABU KE_*

*_WANNAN SALON YASHA BANBAN DANA SAURAN_*

*DUNIYATA(MUHAMMAD JADDA)*

*DUNIYATA(SABREEN)*

_GA HANYA MAFI SAUQI DA ZAKI KASANCE DA ZAFAFABIYAR FAMILY IN SHA ALLAH_πŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎ


*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*
*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA
TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*πŸ₯°πŸ₯°


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*
*Arewabooks:Huguma*

Page 06
___________________________

*_TURQASHI_*

*_BIGI SAI BIGI_*

*_BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE_*

*_TASTED AND TRUSTED_*

*_TASTED AND TRUSTED_*

*_TASTED AND TRUSTED_*

*_Kina da burin samun ingantaccen TURAREN WUTA me TSANANIN KAMA GURI?_*

*_TURAREN WUTAR DA ZAKI SANYAWA DAKI AMMA HATTA DA LABULAYE KAYAN SAWAN DAKE SAQALE
A DAKIN SU KAMA DA QAMSHI?_*

*_TURAREN WUTAR DA KUJERUNKI ZASU KAMA QAMSHI DARAM?_*

*_KI BANKADA LABULAYENKI KIJI SASSANYAN QAMSHI?_*

*QAMSHI IYA QAMSHI 24HR*

*HUMRA ME TSAYAWA A ZUCIYAR ME GIDA*

*NASAN ZAKI TAMBAYI KANKI A INA ZAN SAMU WANNAN?*

*INCENSE BY KABO DAUGHTER*

*_tayi muku tanadin abubuwa da yawa irinsu_*

Khumra
Turaren wuta
Kulaccam
Lablab
Oil perfumes
Original musk tahara
Multipurpose spray

*karki kuskura kada kiyi ganganci ayi babu ke,kai tsaye tuntubeta ta wannan number*

08032119803

Ko ki lalubeta ta nanπŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎ

*Instagram handle_incense by kabo daughter*

*Facebook_kabo daughter*

*Twitter_kabo daughter*
__________________________
Tayi zaune kawai saman kujerar falon tana duban kowa d'ai d'ai da yadda
yaran keta walwalarsu da sabgoginsu. Ta yita juya zancan haleema a ranta,anya zata
iya kuwa?,zata iya jurewa?,daga bisani data tabbatar muddin taci gaba da zama a
wajen zata karya dukka tsarinta saita yunqura kawai ta miqe tana bar musu falon.

Cikin satin ya tabbatar yayi musu dukkan abinda ya dace,ya kuma sauke
duk wani abu da uba zai saukewa 'ya'yansa,tun daga suturunsu xuwa takalmansu,kayan
makaranta hadi da jaka takalmi da duk wani abu daya zama dole ga dan makaranta.

Zai iya cewa Kansa da kansa sauyi ne na dare daya yazo cikin
rayuwarsu,duk kuwa da cewa har yanzun.....daidai da second dayahasashe,koda da wasa
irin na qwaqwalwa zuciyarsa bata taba hasashen ta manta da abubuwa guda ukun nan da
suka shafi rayuwarsa ba......suka shigeta da wani irin yanayi,yanayin daya tilasta
canzawar zubi da kuma tsari na dukkan feeling na zuciyarsa da gangar jikinsa.

Abbansa
Jadda

Da kuma uwa uba mahaifiyarsa da zuciyarsa ke mata wani irin bahagon kallo.

Halitta mafi girma da daraja cikin rayuwarsa......amma kuma dukkan wani
matsayi da girman suna da halittar ta mallaka baya jinsa ko dis cikin jininsa da
zuciyarsa.

Eh tabbas......a tsukin kwanakin rayuwarsu tayi wani wawan sauyi,saidai
nashi sauyin ya tsayane cak iya zahirinsa. Darare da yawa suna wucewa cikin
idanunsa. Alfijir dake cikin kowacce asubahi da Ubangiji ya halittama kwanakinmu
sun sha ketowa ta cikin qwayar idanunsa. Ta tsakiyar qwaqwalwarsa yana jin kamar an
tsatssagarta da wani abu me kaifin tsini

"Me yasa maama taqi zama damu?,me yasa ta kasa jurewa lalurar Abbey?"

"Saboda bashi da komai yanzun,saboda shi talaka ne" Amsar da kullum yakeji ana rada
masa kenan cikin kunnuwansa. Sau tari yakan sanya dukka tafukan hannayensa ya toshe
qofofin kunnuwansa wai ko zasu daina jiyo masa wannan amsar......waiko amsar
tambayarsa zata iya sauyawa?.....saidai aah,koda wasa bai taba jin amsar nan ta
sauya ba. Tun baya daukar gaskiya ake rada masa ana kuma sake jaddada masa har
zuciyarsa ta gamsu da hakan.

"Indai haka ne maama ita tayi silar mutuwar Abbey......indai haka ne maama itace
tayi ajalin jadda" Abinda yake gayawa kansa kenan a duk sanda ya kalli fuskarsa
dake dauke da qananun shekaru

"Amma ta yaya ta kashesu?" Tambayar da daya kasa lalubo amsarta,saidai yasan koda
duniya zata taru ta hanashi wannan tunanin bazai taba kankaruwa daga qwaqwalwarsa
ba har ABADA.

*******

Safiyar litinin ce dake dauke da yawaitar hazo da kuma lullumin sanyi
daya soma tun a daren shekaran jiya. Cikin dakin nasu a cikin su hudun kowanne
shirin tafiya makaranta yake yiwa kansa don ba wanda baya iya yiwa kansa da komai
da komai a cikinsu,daga su Faruqee da suke 'yan gidan,har su da suke baqi ko kuma
ace 'YAN RIQO. Kusan za'a iya cewa banbancinsu dasu Faruqee din shine,mamarsu da
babansu dukkansu suna a raye,sannan komai tsanani suna da gatan dangi da kuma
muhallin da zasu kwana a ciki. Amma ta fuskar samun cikakken gata da kulawa na
iyaye,sun tashi kusan a mizani guda,don sun rasa kaso tamanin a cikin dari
sanadiyyar RABUWAR AUREn mahaifansu.
"Ya kamata kayi ka gama,wannan laqai laqai din naka ba abinda zai haifar mana sai
bata lokaci,kasan dai abba ya koma a motan haya zamu je yau" Faruqee dake saba
school bag dinsa yace da saddeq dake kurba shayin da Faruqee ya hado musu dukkansu
suka gasa cikinsu.

Kusan ya zame musu jiki,duk randa mahaifinsu ya sanya qafa ya koma
Lagos lunch box dinsu yakan koma hoto,zancan breakfast kuwa saidai da tsananin rabo
Faruqee ya faki idanunta ya hada musu tea susha su wuce kaman yau. Tasha kamashi
bayan anyi hakan,tasha gargadarsa amma a banza wai man kare,gobe ma sai ya qara.
Tun tana hukuntashi ta hanyar duka har yakai shekaru sha biyar. Tayi niyyar masa
wani wawan duka,amma da yake ance qashin namiji dana mace ba daya bane saita samu
targade a hannun nata madadin shi yaji rauni.

Yayi dariyar ranar kaman ba gobe,ya dinga maimaitawa qaninsa

"Alhakina ne". Hakanan taji jiyyar hannun nata ba tare da kowa ya sani ba. Tun daga
ranar ta canza kalar horo,saita hadashi da aiki me tsanani,kota hanasu abinci a
ranar gaba daya. Irin wannan horon yafi mata dadi idan ya zamana abba baya
gari,idan kuwa yana nan abubuwa

Please Login or Register in order to submit comment