You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mitsitsiyar akwati ce wadda bata fi girman akwatin sanya zobe,ta
saka hannu ta daukota sannan ta bude. Wani qaramin layi ta ciro ta rufe akwatin ta
maidata,sannan ta dauki wata farar qaramar Samsung's ta bude gefanta ta zura layin
ta maida wajen ta rufe sannan ta danne madannin dake gefen damanta. Take ta kawo
haske,bayan bayyanar tambari da sunan kamfanin komai ya dawo daidai yadda ya dace.

Batakai ga danna komai ba saqonni suka fara turmutsutsun shigowa. Tsai
tayi da idanunta tana kallon notifications din har suka gama jerin gwanon
shigowarsu suka qare. Kaman ta sharesu ta isa kai tsaye ga abinda zai sadata da
mashkur sai kuma ta sauya tunani.
Ma'ajiyar saqonnin ta shiga,ta fara bin sunayen mutanen da suka aje
mata saqon daya bayan daya don bata jin tana da isashen lokacin da zata tsaya
budewa da karantawa.

Kamar yadda ta zata,ta samu saqonnin mashkur da yawa fiye dana
kowa,saita wuce kowanne saqo ta tafi saqon daya tura mata na qarshe kwanaki biyu da
suka wuce.

Sallamarsa kadai ta amsa,ta tura masa ta maida wayar ta aje saman
locker tana bin fuskar wayar da kallo,zuciyarta na shirya mata yadda komai zai
tafi.

Ta jima da ajjiye mashkur saboda yadda zalamarsa ta fito a fili. Ta
jima da ganin ta barshi a gefe saboda yadda halinsa yasha banban dana kowa cikin
mutanen da ta taba tarayya dasu cikin rayuwarta. To amma yanzu silar matsalar aisha
tana ganin wannan shine right time da zata koya masa darasi shima yabi sahun sauran
mazan da suka shude cikin rayuwarta.

Agogon dake manne saman kanta ta kalla tana qoqarin dawo da nutsuwarta
waje guda. Zuciyarta ke wani irin rawa tamkar dai ta soma gajiya da al'amuran da
suke tunkarota cikin rayuwa. Wasu su shude,wasu kuma suna ci gaba da fuskantarta da
babbar BARAZANA.

kamar mintuna goma sha biyar sun qaru akan lokacin dawowarsu daga
islamiyya na ainihi. Aje dubanta tayi saman hijabinta na sallah,saita miqa hannu ta
dauka tana miqewa da zummar duba inda suka maqale. Bata wasa da duk wani abu da ya
shafesu musamman fita da dawowarsu gida. Duk da su din kwata kwata basu san ko ina
ba idan ka dauke hayoyi da layukan dakan sadasu da makarantarsu.

Kaman jira akeyi tayi taku uku daidai wayar ta dauki ringing. Duk da
ta jima bataji ringing din wayar ba amma babu abinda ta manta daga sautinta.

Taku ukun ta sakeyi ta dawo tana duban wayar bayan zuciyarta ta gama
ayyana mata waye din me kira

"Mashkur" Kaman yadda ta aje number dinsa. Siririn murmushin da bata shirya ba ya
subucewa labbanta. Tana tsaye tana ci gaba da duban wayar har ta qaraci burarinta
ta yanke. Bata da niyyar daga kiran kwata kwata a yanzun,don ba tsarinta bane samun
komai daga wajenta cikin sauqi ba. Ta yardarma kanta tana da tsada,tsadar data
sanya kowanne namiji da zai ratsa ta cikin DUNIYARTA yarda da hakan,ya kuma bita da
tsarinta a yadda ya sameta.

Kaman yadda ta zata bazai kira sau daya ya bari ba haka taji wayar
ta sakeyin qara,salin alin ta koma ta maidata silent,sannan ta jawo Locker ta
wurgata ta rufe ta kuma soma takawa hanyar falonsu tana zura hijabin saman wuyanta.
Shimfidadden kwarjinin dake boye bayan fuskarta ya sake bayyana sosai tamkar ta
sanya hijabin ne don ado ba domin biyan buqatarta ba.

Slippers dinta masu taushi ruwan hoda dake daga bakin qofar da zura
ma fararen qafafunta,ta murda handle din qofar ta bude ta tura ta fito.

Fayau tsakar gidan nasu yake da wadataccen filin nan da baya rabo da
tsafta duk da iyalin da gidan ke qunshe dashi. Kamar kowanne lokaci kamar kuma
yadda suka maidata ABUN KALLO. Kowanne motsinta yana saman idanun mafi yawa daga
cikinsu,bawai don su bata kulawar data dace ba....bawai don suyi mata gyara idan
tayi kuskure ba......badon kulawa ta qauna ba.......saidai don wani radin kansu da
biyan buqatar qashin kansu.
Tana da wani irin kaifin nazarin fahimtar meke kai kawo a kewayenta.
A zaune take ko tafiya take?. Wani yanayi da a baya baya cikin dabi'unta,kuma bata
dashi,amma yanayi da salon rayuwa ya tilastata kasancewa hakan.

Dab da rijiyar gidan wadda daga ita sai hanyar da zata sadaka da
ainihin farfajiyar gidan ta ganta. Tsaye gaban rijiyar dauke da cup da alama ruwa
ta gama sha.

Sanye take da atamfa classic da aka yiwa dinkin zamani riga da skirt
daya zauna daidai jikinta. Kanta ba dankwali wannan zai baka damar hango baqar
sumarta me sulbi da suka gada ainihi daga mahaifinsu.

Idanunsu cikin na juna na wasu sakanni,sai ta fara janye nata duban
daga kanta tana ci gaba da nufar soron.

HADIYYA......Idan har a baya za'a gaya mata rayuwa zata ajeta a bigiren
da suke kai a yanzun ita da ita zata qaryata......idan har a baya za'a gaya mata
rayuwarsu zata koma kaman yadda take a yanzun zatace mummunan mafarki ne mara
ma'ana....wanda bashi da tushe ballantana makama.

Hadiyya 'yaruwar haihuwarta,wanda mahaifi yayi silar zamowarsu jini
daya......hadiyyan da suka taso qarqashin rainon mahaifiyarta......cikin daki guda
saman shimfida guda,duk da murdadde kuma zazzafan kishin da mahaifiyarta ke
bazawa.......amma hakan bai sauya komai ba na kusancinsu.

Sai gashi a yanzun sunyi irin rabuwar hannayen riga. A yanzun haka
tana nata karatun cikin makarantar koyon aikin jinya bisa daukar nauyi da kulawar
yayan mahaifiyarta......yayin da tata rayuwar tayi matuqar shan banban da ta
hadiyyan.......take neman ta nutse cikin neman dauki da tallafin data gaza me kawo
mata,har sai da tayi wani irin wawan tsalle da batasan zata sauka a daidai ko kuma
garin saukar tana iya gamuwa da karaya da tarin raunukan da zasu zamewa rayuwarta
tabo?. Takai qarshen tunanin sanda takai bakin qofar farfajiyar gidan ta
farko,saita aza tafin hannunta saman fuskarta tadan shafi fuskar. Tasan bawai kuka
takeyi ba,don a yanzun batajin cikin qwayar idanunta akwai sauran ruwan hawayen da
suka rage da zasu bata hadin kan yin kuka. Kawai huci da dumin da fuskarta ya dauka
takeso taji ya huce,idanunta sake mata dan zugi zugi tanason rage musu adadin iskar
dake shiga cikinsu.

Karo sukayi da huda sanda take shirin fita shigowa su suna shirin
shigowa. Suka ja baya dukkansu hudan tana dan riqe goshinta

"Ke kuma ina kuka tsaya haka dukka ku ukun har ana shirin kiran salla?" Ta jefa
mata tamabayar tana tsareta da ido. Kafin huda tace komai haneefa ta tsinke da
dariya

"Anty.......yaa nadra muka tsaya jira......bata bada hadda ba sai malam ya tsareta"
Idanunta ta mayar kan nadra wadda fuskarta ke a daure

"Garin yaya?,kin soma wasa da haddar ne?" Kai ta girgiza da sauri,tana shirin magaa
hudan ta rigata

"Kallo suka tsaya yi jiya da daren bayan kin kwanta" Fuska a daure ta sake maida
kallonta a kansu

"Ashe?,yau zaku jawa kanku,sai na tsinke kowanne cable na kallo dake dakin nan"

"Ah wai.......ni abunnan yana dauremin kai?,wai lalatacce shike tarbiyya" Murya
bibo ta ratsa kunnuwanta sanda take dubansu nadra.
Dukansu ido suka azawa bibo din lokacin da take kutsowa cikin gidan.
Kaman yadda suka fita ne dazu,ita da daada,saidai kaman dazun ma daada ratsewa tayi
ta wuce abinta ba tare data tsaya yiwa bibo tayin su wuce ba kamar dazun.

Motsawa kadan huda tayi wanda motsinta kadai ya sanar da SABREEN abinda
take shirin yi. Yatsarta ta kada mata sautin da ya sanyata tsaiwa can tare da
hadiyar wani abu me tauri a wuyanta



*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA
TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*
*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

*Arewabooks:@Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997

PAGE 26
__________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*

*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA
KUNYA KUWA?_*

*_KAMAR SU_*

Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes

*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries

*_inganci da kwalliya shine muradinmu_*
__________________________


"Ku wuce muje" Sabreen tace dasu,suk sai sukayi gaba tana biye dasu a
baya. Nadra ta hadawa kayan duka ta wuce musu dashi daki. Ita tayi tsaye dasu
kowacce ta gama buqatarta suka daura alwala suka wuce daki.
Sallah sukayi bayan sun sauya uniform. Har a sannan tana ankare da
yadda huda din keta hadiyar zuciya. Ta sani muddin tace zata saki huda tayi abinda
takeso zaman bazaiwa kowa dadi ba......tafi huda zuciya nesa ba kusa ba......tafi
huda dabi'ar take yanke.....amma me?,daga baya ta fahimci me irin wannan dabi'ar ba
kasafai yake nasara ba.

Sai data kammala sallar magariban sannan tabi takan wayar. Ta samu
miscal biyar hade da wasu saqonnin daga gefe. Tabi number tasa da kallo,sai a yanzu
takejin ta shirya saurararsa. Kamar yasan tana riqe da wuyar saiga wani sabon kiran
ya sake shigowa,don haka ta miqe a nutse ta koma daki tana matsawa daga inda su
nadra dake cin abincin dare suke.

"Laifin me nayi dana cancanci wannan uqubar fateema?" Numfashi ta saki wanda
sautinsa ya isa har kunnensa

"Ki gayamin ko meye nayi a shirye nake da na nema afuwa" Shuru ta sakeyi tamkar
bata layin,saidai tana sauraren dukka maganganunsa

"Fateema" Ya sake kiranta da sunan da shine nasa STAMP din,sunansa ne shi daya,duk
duniya shi ta mallakawa wannan sunan

"Naam" Ta amsa a karon farko tunda ya fara maganar

"Kinsan irin rayuwar dana tanadar miki?,kinsan irin gatan da nakeson miki?,kinsan
yadda nakeson maidaki tauraruwa a cikin mata?,kinsan yadda nakeso ki koma tamkar
sarauniya?"

"Dukka wadannan dama abinda ka lissafa basu nake da buqata ba"

"Me kike da buqata fateema......ki gayamin,a shirye nake na mallaka miki su......"

"Zamu iya haduwa?" Ta jefa masa tambayar

"Ko a ina nake a duniya a yanzun haka kika ce kina buqatar ganina zan wanzu a
gabanki" Maida idanunta tayi ta lumshe sannan ta budesu

"Mu hadu yanzu fateema?,ko dan kadanne inaso naga fuskarki"

"Alright" Ta amsa masa a taqaice,abin da yazo masa a bazata,don haka a rude yace

"Venue?"

"Zan gaya maka,i will call you" Bata sake bashi daman cewa komai ba ta yanke kiran.

Wayar ta riqe a hannunta tana juyata a hankali bayan ta zubawa guri
daya idanu. Lissafi ne fal Qwaqwalwarta,dole kafin ta samu abinda take nema saita
yi haquri ta sake masa,dole ta dinga bashi mabanbantan gurare har zuwa sanda
tsarinta zai fada aikinta zai cimma nasara.

A nutse ta miqe tana wassafa yadda zata fita yau din da dare,abinda sam
ba dabi'arta bane saiya zama mugun dole,ba kuma zata iya tuna lokaci na qarshe da
hakan ya taba faruwa da ita ba,amma yanzun dole ta fitan,tanason ta amintar dashi
sosai a kanta.

Kai tsaye ta wuce ma'ajiyar kayanta tana duba suturar da zata dace da
ra'ayinta a wannan lokacin. Da idanu ta gama qare musu musu,daga qarshe ta tsaya
saman wasu Turkish dress masu strip skirt long sleeve shirt da doguwan kinomo sai
madaidaicin veil da zai lullube saman kanta.
Sam bata da ra'ayin sutura me matse jiki duk kuwa da yadda mutane da
yawa suke kallon ita tafi dacewa da irin wannan shigar.

Tsaf ta shirya cikin kayan kalolin navy blue da gray color. Sanda ta
gama nada veil din a kanta sai data sake duban kanta sosai ta cikin madubin. Tayi
wani irin sassanyan kyau me matuqar daukar hankali. Ta miqa hannu a nutse ta dauki
turarenta ta feshe jikinta can qasan ranta tana jin fargaba kadan kadan kan
haduwarta da mashkur,saidai kuma wani sashe na zuciyarta yana qarfafa mata gwiwar
ba komai,wannan ne haduwan farko,nothing will happen.

Asalin wayarta ta jawo tana lalubar number JIB. bugu daya tak ya
dauka,tadan motsa bakinta a nutse

"Ina fatan kana available kuma free"

"Ko ba hakan bane ai ya zama dole nayi creating time wa ke.....me kike buqata?"

"Connection" Ta fada a gajarce

" A daren nan?"

"Haka abun yazo,mashkur......mashkur alqali abdulkreem"

"Done.......wancan aikin ya kusa kammala......akwai ragowar information dana kasa
accessing.....but...."

"Karka damu.....mu sanya wancan a mala.....wannan din shine yafi muhimmanci a
yanzu"

"An gama.....bani code......let me write it" Ya fada yana dan riqe wayar kadan
kafin yace

"Okay.....karanto" A nutse ta karanta masa wasi gajerun lambobi guda uku sannan ta
katse kiran. Ta jawo locker madubinta ta ciro Bluetooth tayi danne danne saman
wayar tata ta bada wasu sakanni sannan ta maqala a kunnenta. Saita aje wayar,ta
dauki wancan Samsung din ta kunnata sannan ta fara yunqurin kira.

Bugu daya tak tayi aka daga,ta kalli wayar da mamaki sanda yake cewa

"Am ready to go princess......ina zaune a mota nida driver a parking lot na gida"

"Yayi.....but if possible ka taho kai daya mana"

"An gama" Ya amsa mata cikin farinciki hankali kwance.

Tana kammala saka takalma huda na shigowa dakin. Kallo daya tak tayi
mata taga yanayinta ya sauya. Hudan tadan ritsata da idanu tana dubanta,saidai tun
kafin takai ga tambayarta ta bata amsa

"Zan dan fita kadan amma yanzu zan dawo" Iya abinda ta gaya mata kenan ta fara
takawa zata fice.

A jikinta taji yarinyar kallonta take,a jikinta taji tana tsaye ne
kawai har yanzu,don haka ta tsaya cak sannan ta waiwayo. Ido suka hada,sai a sannan
hudan ta kauda kanta. Iya hakan ya gayawa Sabreen maganganune sosai cikin
zuciyarta,wataqila girma da kimarta kadai zai hanata ta furta mata su. Taku hudu
tayi ta iso gaban hudan

"Dole ce ta saka zan fita huda......amma bazan wuce awa daya ba,idan na dade biyu"
"Amma anty...." Hudan ta furta fuskarta fal damuwa.

Yatsanta ta dora saman lips tana duban hudan,sai kuma daga bisani ta
dauke yatsan tana aza dukka hannuwanta saman kafadarta,ta kuma zaunar da ita saman
stool na madubin dakin

"Ke daya ce tal cikin mutanen da sukasan wace Sabreen gaba daya baya,kada kiyi
tunanin na canza......ban canza ba huda.....kuma har abada bazan canza ba.....nayi
alqawari......mommu da abba dake qarqashin qasa bazan bari suyi kaico dani ba" Kai
ta gyada a hankali tana kallon Sabreen kamar yadda itama ita din take kallo. To
amma a hankali tana rasa wannan yardar wanda tasirin maganganu daga kowanne saqo da
lungu na layinsu dama unguwarsu ke kai kawo a kunnuwanta

"Don't lose hope huda......alqawari na.....bazan karyashi ba,ki kula da nadra da
haneefa" Ta fadi mata daga qarshe ta juya tana fita a dakin. Nata ruhin yana
motsuwa.

Har abada ba zata daina zargin maraici ba......har abada ba zata
daina kuka dashi ba......a wani sashen na duniya,a irin wannan lokacin,diya kamarta
tana qarqashin kulawar mahaifanta ne guda biyu.......ko kuma qarqashin kulawar wasu
amintattun mutane da zasu zame mata makwafin iyayen.......sai gashi tata DUNIYAR ba
haka bane,dukka kafadunta dauke suke da wani irin nauyi dakeson fin qarfinta ya
kaita qas.

Daga baya baya ta sanya busari ya ajeta kafin akai ga shiga gurin a
yanayi salo na kula da takunta kanta dama dukka wani motsi nata.

Sallamar busari tayi tace zata nemeshi idan hakan ta taso,sannan ta
fara takawa a hankali tana nufar wajen.

A hankali take ratsa wajen cikin nutsuwa data zame mata dabia,tana
takawa a hankali qamshinta da kuma yadda shigar ta amsheta kadai suka soma jan
hankulan matasa da yawa wajen. Guri ne da yakan hada matasa maza da mata,wayayyu da
suke da gogewa a fannin rayuwa kudi da kuma ilimi. Wajene kebantacce da yawansu
suka maidashi gurin nishadi da kuma debe kewarsu,wasunsu a duk daren duniya,wasu
kuma jifa jifa.

Yadda take daukan hankulansu haka kwarjininta ke dukansu,wannan ya
sanya duk wani dakeson kawo mata caffa ya gaza yin hakan,saidai tazo ta ratsashi ta
wuce shi kuma ya bita da kallo.

Tun daga nesa ta hangeshi,ya fita yayi tsaf cikin wani lafiyayyen
jeans da shirt da suka dace da takalmin qafarsa. Kanshi pcap ce daya sauko da ita
tadan rufe masa fuska. Hannunsa dauke da wayarsa yana latsawa a hankali ba tare
daya damu da abinda ke kai kawo a wajen ba.

Ta sani,hankalin gomayyar 'yan mata dake wajen tabbas suna kanshi.
Mashkur din ba irin mazan da mace me muradin jinsin maza irinsu zata kall sau daya
bane ta iya kauda kai kota wofantar,kusan zata iya cewa ya hada dukkan
komai,abubuwa da dama da mazan da suka taba ratsa rayuwarta ba wanda ya gama cikasu
irin haka. Yana da kyau daidai gwargwado wanda kudi suka sake qawatashi,yayi karatu
har zuwa matakin degree,hakanan dan wulaqanci ne shi,wulaqancin daya zame masa ado
a idanun mata marasa kamun kai. Idanunsa a bude suke tarwai,yana da wata irin
wayewa data zarta shekaru da kuma iliminsa,wanda hakan baya rasa nasaba da fita
qasashen waje da yake yawan yi,musamman qasashen turawa.

Dab da zata iskeshi ya daga kansa sai suka hada ido. Zumbur ya miqe
yana zube mata idonshi,har cikin zuciyarsa yana jin wani abu daya qarasa mamaye
gangar jikinsa.

Karon farko daya soma jin ra'ayinsa akan mace na neman canzawa. A
yanzun kallo daya tak.....cikin qasa da minti daya kacal ya soma ji a ransa kamar
ya aureta shine abinda yafi dacewa dashi da ita gaba daya. Kamar alaqar daya shirya
da dangantakar daya shirya ginawa a tsakaninsu ba ita ta dace ba,duk da har yanzu
gaza fuskantar AINIHINTA....a wanne mataki na 'yammatan wannan zamanin take?. Wasu
abubuwan nata na masa kama da dabi'un mace ta musamman.....amma wani motsin nata a
wani lokacin sai ya sanya masa shakku akan haka. Kamar dai yanzun,yadda duk da
duhun dare ya lullube sararin subhanana amma hakan bai dasa mata shakku ko ya zama
dalilin qin fitowa su hadu ba.

A maimakon kujerar daya ja mata don ta zauna saita matsa kujera ta
gaba,saidai kuma fuskarta a sake tana maida masa martanin murmushinsa.


*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA
TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

*Arewabooks:@Huguma*

https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997

PAGE 27
_________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*

*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA
KUNYA KUWA?_*

*_KAMAR SU_*

Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes

*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries

*_inganci da kwalliya shine muradinmu_*
_________________________
Duk da a qasan zuciyarta ba haka bane.

Idanunsa a kanta kaman bazai iya daina kallonta ba yana nashi seat din
ya zauna

"Finally dai after wasu watanni......har na debe tsammani sai gashi......" Ya fada
yana dan watsa hannayensa irin na gogaggun samari

"Me ma bahaushe yake cewa?.....me haquri ko?" Ya aza mata nauyin amsa tambayar ta
hanyar kallonta da idanunsa.

Qaramin murmushi kawai ta saki tana maida bayanta ta jingina sosai
da kujerar da take kai din,yayin data daba hankalinta gida biyu. Wani a
gurinsa,wani kuma yana kan yanayin wajen dake cike da 'ya'ya mata. Tayi imanin
dukkaninsu uwaye ne suka haifesu,koda ace akwai na gaba da fatiha to kadanne. Son
rai son zuciya kwadayi su sukayi musu jagora zuwa ga turbar da suke kai a yanzu?.
Ko kuma suma kamar ita dinne?.

"Yauwa......thanks" Taji ya furta,saita maido dubanta kanshi.

Idanu ya kashe mata cikin salon jan hankali me zafi,ya kuma sake
matsowa sosai har yana rungumar table din da suke kai zuwa qirjinsa,sannan ya aje
manual din da aka kawo ta hannun waitress.

"Choose babe" Ya fadi yana lanqwashe murya kamar wani mace gami da kanne mata
idanu. Manual din da ya tura mata ta sauke idanu a kai. Tarin abinciccika ne iri
daban daban,wanda ko kaffara ba zatayi ba idan ta qiyasta maqudan kudaden da za'a
lasa ta sanadiyyar cinsu. Sai data qare musu kallo gaba da baya,yayin da shi da
waitress din ke jiransa ba tare da sun qosa ba,saita maida ta ajiye saman table
din. Ta motsa bakinta zatayi magana kenan sallamar da akayi da wata raunanniyar
muryar taja hankalansu.

Dukkansu shi da ita suka maida dubansu ga wajen. Matashiya ce mai
matsakaicin haske wadda idan ka kalleta a qiyasin da zaka fara yi mata duka duka
shekarunta ba zasu haura ashirin da bakwai zuwa da takwas ba da haihuwa. Sanye take
fallen zanin atamfa da kai tsaye zaka kirata da atamfa leda ko roba,duba da yadda
ta cukuikuye a jikinta saboda tsufa da rashin quality da kuma yanayi na dan busawar
iska data hadu dashi. Qasan zanin a cinye yake abinda zai wassafa maka kenan
shekarun da atamfar ta dauka a duniya ana amfanarta. Hijabi ne a jikinta daya fara
gajiya da rayuwa,tsananin sussuqewarsa ya sanya ya baiwa me kallo daman hango
yaloluwar rigar dake a jikinta.

"Ke kuma fa?,daga ina wa kike nema?" Mashkur dake dubanta sama da qasa da wani irin
qasqantaccen kallo ya jefa mata tambayar.



Please Login or Register in order to submit comment