You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Rusunawa qasa tayi cikin matuqar taushi da karyar dakai ta hade
hannuwanta biyu waje daya

"Taimako nake buqata yallabai......don Allah ka taimaka min da duk abinda
Allah......"

"Wait.....wait mana" Ya fada a tsawace har hakan ya sanyata miqewa ta tsaya saman
qafafunta. Waiwayawa yayi zuwa ga waitress din

"Yaushe wajen nan naku ya lalace?,yaushe kuka fara bawa mutane irin wadannan daman
shigowa gurin nan.....wait.....wai bakusan kowa na zuwa irin nan bane don ya huta
ya kuma yi uzurin gabanshi ba tare da kowa da komai yayi disturbing nashi ba?".
Duk joint din da basusan fuskar mashkur ba to tabbas ba cika joint
ba......imma darajar wajen tsada da kuma darajarsa batakai ba......ko kuma dai
kawai wajen bai cikin tsari da ra'ayinsa. Wannan abun ya sanya cikin rudewa ta soma
bashi haquri tare da qoqarin nesanta matar daga wajen,duk da yadda kuwa take roqon
su taimaka mata.

A nutse Sabreen ke kallon matashiyar zuwa ma'aikaciyar ma gaba daya. Yar
uwarta nace ke qoqarin rabata da gurin don dai kawai kada ta batawa customer rai ta
hanyar da babu girma arziqi ko darajta dan adam. Yanzun inda ace cikin kyakkyawar
shiga take.....inda ace cikin dressing me kyau take......inda ace jikinta a gyare
yake......inda ace zata koma hakan tabbas basai ta tsaya bagging a taimaketa ba. Ta
cikin ruwan sanyi matasa dama manyan ire iren wadanda ke zaune yanzu haka a wajen
zasuyita miqo mata buqatunsu,wanda yadda ta karba da hannu
bibbiyu......kwatankwacin hakanne zata samu nata biyan buqatar.

"Dakata......barta ta dawo" Sabreen din ta samu kanta da furtawa idanunta da suka
canza launi suna saman fuskar waitress din.

"Kamar yaya?,ki barta......" Mashkur ya furta yana maida idonsa ga matashiyar data
fara takowa a hankali zuwa inda suke din

"Nooo" Ta amsa masa da wani sauti da yake tafe da wani irin zafi da ya motsa mata
zuciya. Ganin matar kawai ya tuna mata abubuwa masu yawan gaske,ganinta ya fama
mata wani babban ciwo,sai ta sanya hannunta cikin mitsitsiyar handbag dinta sannan
ta zaroshi da dukkan kudin dake cikin jakar ta miqa mata.

Cike da mamaki take kallon fuskar sabreen din. Saita motsa kanta tana mata
nuni da kudin. Wani irin karyewa zuciyar matar tayi,sannan ta sulale da wani irin
qarfi ta tara hannuwanta tana amsar kudin. Jiki da muryarta dukka rawa suke sanda
ta fara jera mata addu'a da godiya

"Ya isa jeki" Mashkur din ya fada yana fatan ta gusa ta basu waje ba tare data bata
masa budget ko ta bata masa lokaci ba.

Cikin jikinta taji cewa ita din mashkur yake kallo. Ta lumshe
idanunta tana qoqarin daidaita mode dinta,sai kuma daga bisani ta sauke mata wannan
kallon nata dake saurin waftar hankali

"Are you okay?" Ya jefa mata tambayar cikin matuqar nuna kulawa. Sai da ta danyi
gyaran murya sannan ta gyada kanta

"Am okay....."

"Am sorry ko?,irin wadannan mutanen dear ki daina gaggawar amincewa dasu ko basu
taimako.....they are wicked wallahi at so many times......yanzun kalli yadda ta
bata mode dinki gaba daya?" Gyara zamanta sosai tayi tana maida qafarta daya ta
dora saman dayar,sannan ta sarqafe yatsunta saman qafarta tana sake zuba masa
idanu. Rashin tausayi rashin imani da kuma rashin bawa dan adam darajarsa yana fita
fes a tare dashi,wanda hakan ya sanya taji a ranta yayi deserving ayi punishing
dinsa qwarai da gaske fiye da yadda ta shirya yi a baya.

Ya daddage yana sharhi akan baiwar Allahn da baisan wacece ba?,meye
matsalarta?,meye damuwanta cikin sararin subhana?.

"Is okay ya wuce" Ta amsa masa a taqaice tana kallon agogon da yake daure a
tsintsiyar hannunta.

Hankalinsa yadan dauko kadan,a duk sanda yaga tayi hakan alama ce
dake nuna tana dab da yin layar zana,layar zanan da idan tayin baka isa bincikota
ba sai sanda taga damar bayyanar maka.

"Times up?" Ya fada yana qureta da ido. Kadan ta saki murmushi

"Eh.....kusan haka ne"

"Ban yarda ba.....dole kici wani abu"

"Nop......banjin wannan.......zan wuce.....but soon zamu sake haduwa"

"Am......bamu tattauna komai bafa......if possible a qaramin minti goma
kacal.....in sha Allah bazan haura haka ba" Hannuwanta ta aje daga daukan handbag
dinta da tayi niyya,ta koma ta sake harde qafafunta tana kallonsa.

Shima idanun ya zuba mata yana jin yadda kowanne sashe na jikinsa yake
da buqatarta

"Wai sai yaushe zaki soni kaman yadda nake sonki fateema?" Ya tambayeta bayan ya
sauke wata wawiyar ajiyar zuciya. Dukka girarta guda biyun ta dage tana sake
nazarinsa ta cikin qwayoyin idanunsa

"Ta yaya zaka zargeni da abinda ba haka bane?"

"U mean......kina sona kaman yadda nake sonki?" Sai data lumshe ido kadan as usual
sannan ta gyada kai

"Okay,prove it" Ya fada da wani irin zumudi yana gyara zamansa sosai tare da
rinjayar da gangar jikinsa zuwa zuwa mazauninta.

Ido tadan juya,reaction na fuskarta na nuna masa bata fahimta
ba,a nutse ta motsa labbanta

"Like?....."

"Dis week nakeson zuwa dubai nayi annual leave dina......zanji farinciki fiye da
yadda baki tsammani.....zanyi alfahari dake zan kuma mallaka miki komai da kike
buri cikin rayuwarki......." Sai ya bude wallet nashi dake aje gefe,ya zaro wani
qaramin littafi me abun rubutu a gefansa,ya buda tsakiyar littafin ya sanya
biron,sannan ya aje mata shi a gabanta yana cewa

"Write it down.....,ko meye.....komai girmansa kada ki gaza rubutawa,and zai
kasance ne as you wish" Fararen idanunta ta dora akan littafin kamar me nazarin
launin takardar

"Musayar mutunci" Zuciyarta ta raya mata hakan. Wani zafi taji har cikin qwayar
idanunta,saita dauke idanunta dama kanta daga wajen ta maidasu gefe. Cikin qasa da
second biyar zuciyarta ta gama tsara komai,don haka ta waiwayo ta fuskanceshi sosai
sanda yake fadin

"What happened fateema?....." Yana leqen fuskarta. Murmushin da ta fuskanceshi
dashi ya sanya yaji relief,fatan samun nasararsa daya soma zagwanyewa duk sai yaji
yana dawo masa.

"Nothing......kawai gani nayi kazo da qaramar buqatar da bata buqatar dogon sharhi
da roqo har haka......kaman ma bata buqatar tafiyarmu wata qasa......nan ma zata
iya zama dubai dinmu"

"Really?" Ya tambayeta da wani irin excitement a jikinsa dama fuskarsa.
"Yes" Ta amsa tana daga masa kai da nata guntin murmushin daya tsaya iya labbanta.

"Thank god.....thank you fateema......ban taba tunanin it gonna be easy kaman haka
ba"

"Why?" Ta tambayeshi tana dubansa

"Ba zaki gane ba.....your are so unique fateema......alright.....now"

"Not now......am tired.....inason na koma gida na kwanta.....see you next time
saimu qarasa tattaunawa"

"When?,ina gudun ki kufcemin fa?" Bata amsashi ba sai data gama gyara zaman rolling
dinta

"Wannan ma kai kayi finding dina out ko nice"

"You are the one"

"Tom" Ta fada kawai tana shirin daukar jakarta,saidai kuma shi din ya rigata ta
hanyar jawo jakar gabansa.

Duk da bata saka ido da kyau ba,amma idanunta sunga tamkar takardun
kudin waje ya saka mata

"Thanks" Ta furta a gajarce ba tare da taga qima ko farinciki da kudin ba ko
qanqani.

Ya sani,daya daga cikin rules nata shine baa yi mata rakiya idan
zata tafi,don haka a nan yayi tsaye goye da hannayensa yana kallom nutsasen takunta
har ta fice daga gurin.

Ko daya bata jin me busari yake fadi sanda suke tafiya a hanya. Gaba
daya tunaninta yayi nisa zuwa wata duniyar ta daban.

Lissafe lissafe ne fal kwanyarta,tama rasa da wanne zata fara?,daga
ina zata fara?,a ina kuma zaren lissafin nata zai katse. Zuciyarta da idanunta
sunason zuwa ganin aishatu,to amma kuma bata so taje ta ganta a halin da take ciki
alhalin bata tanadar mata da komai da zaya fiddata daga wannan yanayin ba. Jib ya
kirata,ya tabbatar mata aiki duka ya kammalu daga bangare biyu,amma ta gaya masa ya
saurara ta isa gida tukunna.

Goma saura busari ya ajiyeta daga gaban gidan nasu,ta sauke hand bag
dinta ta zuge don masa ihsani kaman yadda ta saba,duk da shi din bai kawo komai
cikin balance din da ha kamata ace ya kawo din ba amma bata damu ba. Sai data zura
hannunta a jakar ta tuna bata da komai sai irin kudin da mashkur ya zuba mata.
Tadan jawo kudin gaba kadan tana dubansu,sabbin US dollar ne qar dake qyalli da
qamshin sabunta,saita maida dubanta a kanshi

"Zan saka maka wani abu busari ta account,ka bayarma inna kace tayimin addu'a,saida
safe"

"Kinfi gaban haka......Allah ya bamu alkhairi" Ya fada yana dan bin bayanta da
kallo. Yana mamakin kirki irin nata......duk da ita din zuma ce a wani lokuta idan
bataso ba,ga zaqi ga kuma harbi. Ya tayar da napep din yana janyeshi da qofar
gidan,qasan ransa kuma yana qididdige adadin alkhairinta a tattare dasu.

*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*
*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA
TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰
*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 28


Sanda ta isa falon dukkansu ta samesu qudundune saman kujera,kowacce
nannade da blanket dinta. Huda ce kadai zaune saman carpet nannade da hannayenta
tana kallo a tashar Arewa24.

Tayi mata sannu da zuwa ta amsata tana wucewa ciki don rage kayan
jikinta ta sauyasu zuwa da na bacci,gashinta ta kama ta daureshi waje daya ba tare
da tasa komai ba,don bata fiya son abinda zai takurata ba duk sanda zata kwanta,ta
shafe jikinta da daddadan turarenta me sanyin qamshi data wareshi ne kawai don
kwanciya ta dawo falon.

Tsam huda ta miqe ta gabatarata da abinci,saidai bat jima da fara cin
abincin ba wayarta ta dauki tsuwwa. Jib ne,qaramin tsaki ta saki,a lissafinta ta
gama amsa kowanne kira don bacci take da buqatar tayi,tanaso gobe ta shiga wajen
aysha taga yadda jikinnata yake. Abun ya tsaye mata a rai,tana jin cewa idan tana
da dama a rayuwa zata sauya rayuwar Yarinyar ne gaba daya.

A kasalance ta kara wayar a kunnenta bayan tayi sallama ya amsa

"Ya akayi?" Ta tambayeshi

"Komai ya kammalu" Ya gaya mata kai tsaye. Dan shuru tayi tana saurarensa,daga
yadda yake mata magana ya tabbatar mata fuskarshi qunshe take da fara'a duk kuwa da
bata iya ganinsa.

"Okay.....meye result?"

"Bari na fara da abinda yafi damuna yafi kuma yimin dadi......da farko dai zan iya
ce miki congratulations.......ina kyautata zaton indai zakiyi amfani da damarki
sosai yadda ya dace,kin kusa fara shiga jerin sahun mata masu arziqi......kawai
dai" Ya fada yana dan sauke qaramin numfashi

"Wani lokaci duk wani opportunity sai naga kamar kina shuresu ne da gangan......"

"Jib...." Ta ambaci sunansa

"Ina tare da ke,sai na yita tunanin fa me yake damunki?" Yadda yayi maganar a wani
sanyaye ya sanyata murmushin dole. Tasan me yake buqata a nashi son rai ace tana yi

"Ka rasa wani abu ne?" Kai ya girgiza

"Ko kadan.....kawai daman da kike samu ya zarta yadda kik amfani da ita......"

"Bani labarin aiki na" Ta zabi shafe wancan maganar gaba daya,don ba me amfani bace
a wajenta kamar yadda nashi hasashen yake bashi.

Ajiyar zuciya ya sauke,har tana iya jinsa ta cikin wayar

"Congratulations once again.......daga mashkur har mika'il.....suna daya daga cikin
mutanen da suka mallaki manya manyan dukiya........sunyi tarayya ta wajen hali da
dabi'a.........amma ta gurin source of income nasu sun sha banban"
"Ehnnnn" Ta fadi tana juya abincin gabanta da spoon ba tare da takai ko loma guda
bakinta ba tun bayan kiran nata da yayi

"Mashkur dan kasuwa ne kamar yadda yace.....yana aiki tare da
mahaifinsa......mika'il kuma wani babba ne a wani babban kamfani daya boye
sunansa......don kamar yana cikin policy na kamfanin ma'aikata irinsa su dinga
exposing kansu da rank dinsu cikin company din......saidai iya abinda hangena
yakai......company ne babba dake samu da kuma biyan kowanne ma'aikaci albashi me
matuqar tsoka" Yakai qarshe yana sauke numfashi tare da sararawa.

Ajiye spoon din tayi tana gyara zamanta, bayanan sun mata dadi
sosai,kuma su suka haska mata akwai nasara akan mission nata. A hankali tadan aza
dubanta akan huda,duk da hankalinta yana ga kallo,to amma kuma bata bari tayi
dukkan wata magana data shafeta a gabansu

"Good job......na gode.....akwai sauran bayanai nasan,ina da sauran tambaya da
qarin haske.......amma......bari zuwa gobe mayi waya"

"Alright.....to hakan yayi"

"Allan ya tashemu lafiya" Ta fada tana gintse kiran.

Wayar ta sauke tana bin fuskarta da kallo,tunani ne cinkus cikin
zuciyarta. Fuskar matar dazu kawai ke mata yawo a idanu

"Meye amfanin dukiyar da bazaka bayar da ita ba fisabilillahi saidai qarfi ya
qwata?" Ta furta a qasan ranta tana tambayar kanta da kanta. Daga mashkur har
mika'il tayi imanin cikin budin da Allah yayi musun,inda zasi fidda abinda suka
mallaka su dinga narkasu cikin nutsuwa a hanyar data dace......dubban jama'a zasu
samu sauqi da radadin da yake damun zukatansu da gangunan jikinsu.

"An kawo miki saqo" Taji muryar huda daga gefanta tana fada. A nutse ta daga kai
tana duban hudan kafin ta maida dubanta ga akwatin data jawo gabanta.

Zuba masa idanu tayi tanason tuna daga ina?. A hankali sai kuma abun
ya fado mata,ita sam ta manta sunyi dashi ma zai bada saqon

"Kaishi daki" Ta fada tana maida kanta ga waya. Wata number ta lalubs a gajarce
kuma ta tura mata gajeran saqon karta kwana

"Received......thanks".

Shi daya ne cikin qawataccen falon da aka qawatashi da dukkan wani
nau'in kayan alatu da qawa na rayuwa. Madaidaicin falone wanda ke da saurin janye
idanun me kallo da kuma sauqin shiga rai lokaci daya ya kuma dace da kowanne mode
da mutum yake ciki.

Shi daya ne tal cikin falon,sanye yake da shirt me gajeran hannu sky
blue,sai gajeran wandon da duka duka iyakarsa gwiwarsa.

Yana a tsaye ne yana fuskantar qatuwar t.v plasma dake zaune dirshan
saman kyakkyawar tv stand suna haska wasan qwallon qafa,saidai fiye da rabin
hankalinsa baa wajen yake ba.

Bayan gilmawar kowanne minti ko second sai fuskarta ta dawo masa. Ya
lumshe idanunsa sanda aka buga qwallo na qarshe cikin tazarar bada sa'a game rabo
wato penalty,ya daga ragowar tsadajjiyar giyar data rage a qasan glass cup din
hannunsa ya qarasa kurbeta,ya dire cup din yana fidda iska daga bakinsa.
Tsakanin awannin daga dazu zuwa yanzu ya gama tsara yadda zai
baibaye rayuwarta da tsadajjiyar rayuwa......yadda zai narkar mata da zuciya da
masu gidan rana......yadda zai maidata tashi shi kadai......yadda kuma zai siye
mata zuciya da kuma rayuwa da kudi wadanda yayi imanin a wannan lokacin da muke
ciki sune maganin kowacce matsala.....suke iya siya maka dukka nau'in macen da
kakeson ka mallaka.....don babu yaren da matan sukafi ganewa irin yaren LUXURY
LIFESTYLE.

Kallonsa ya mayar saman system dinsa dake kunne,yana jiran kirane
daga wajen CEO na JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES (JDCR).

A duk sanda sunan ya fado masa a rai,ba abinda yake fara zuwa ransa
sai GIDAN KUDI. wanna shine sunan da yafi kiransa dashi......wannan shine full
definition nashi da yake ganin ya dace dashi gaba da baya.

Sake matsawa yayi ya gani koda ya nemeshi?,amma ba wani saqo ko kira
kai tsaye ta yanar gizo. Mamaki yadan kamashi,saboda sanin da yayi masa na
zamantowarsa mutum me girmama lokaci tare da bawa lokaci muhimmanci,yasan tabbas
akwai abinda ya riqeshi ne hala.

Baiso yasha komai ba har sai sun kammala duka maganganun da zasuyi
through video call. Yasan halinsa,yana da tsananin zafi yana kuma da masifar kaifin
karantar mutum,wanda banda shima ya zama mutum me tsananin iya takunsa yayi imani
da tuni labari ya jima da shan banban.

Yaci wuya ya kuma tsallake turaku gwaji da jarrabawoyinsa sosai kafin
yakai matsayin da yake kai a yanxun. Saidai kuma tsakanin jiya zuwa yau burinsa ya
fara fadada. Ya fara jin cewa yana buqatar budawa a harkokinsa fiye da wannan da
yake ciki a yanxu,yana buqatar qarin kusanci da CEO fiye da wannan
kusancin........yana so matakin da suke kai sufi haka shi da shi na qullewa da
kusanci tare da sakar masa ragamar komai na kamfanin fiye da yadda yake kai a
yanzu.

Sai ya zagayo saman kujera ya zauna saboda yadda yaji jikinsa ya
fara week,alamu dake nuna abinda yasha din ya fara tasiri a jikinsa,duk da giya ce
me tsadar gaske da yake kashe kudade masu kauri wajen siyota,bata bugar dashi
buguwar da zata sanyashi fita daga hayyacinsa gaba daya.

A sannan sai yaji bashi da wani sauran muradi daya wuce yaji
muryarta,gaba daya taswirar qwaqwalwarsa ita take hasko masa cikin shiga da
dressing daya dinga ji kamar yayi fiffike ya kamo ta,don haka ya jawo wayarsa ya
fara gwada number dinta. A karo na uku kenan daga dazu zuwa yanzun da ya fara kiran
nata bai samu isa gareta ba,saidai a yanzun cikin sa'a......har ya fidda rai da
tsammani......dab da zata tsinke sai aka daga.

"Kin barni da kewarki ko?" Ya fada murya can qasa. Shuru tayi tana sauraren yadda
muryar tashi ke fita kafin ta motsa bakinta a hankali

"Ka wuni lafiya?"

"Ba lafiya ba......nayita kewarki ne kamar na zauce.....don Allah.....ki bani daman
ganinki koda zuwa gobe ne MEENAL".

Wani siririn murmushi ta saki,irin wanda take saki din a duk sanda wani
cikinsu ya kirata da stamp name dinsa

" Ba yanzu ba" Ta bashi amsa,amsar da a zahiri da gaske take,ta fito ne daga qasan
zuciyarta. Ba kasafai take baka damar ganinta ba a sanda ka damu da ka ganta
din,muddin akwai mission a kanka saita kaika matakin da take da buqatar kaje din.
"Zan katse kiran,bacci ne a kaina,zan sauka saida safe?" Tayi furucin da sigar
tambaya,bawai don tana da buqatar amsa ba.

Bai samu sararin cewa komai ba t gintse kiran tana aje wayar a gefanta
tare da bin wayar da kallo

"Mika'il" Ta sake maimaita sunan tana gyada kai.

Shima bin wayar yayi d kallo kaman sakarai

"Zatayi girman kai,zatayi izza tun a ganin farko na sani......amma kuwa zuwanki
hannu bazaiyi wahala ba 'yammata" Ya fada a sarari yana lashe baki hadi da sakin
wani shu'umin murmushi.

Yana shirin aje wayar wani kiran ya shigo masa. Mato sunan dake rubuce
da number dake kiran nasa.

Wani zunkudawa yayi sanda ya gama hada haruffan me kiran nasa saboda
yadda kanshi ya fara nauyi,ya daga wayar ya sakata a hands free ya ajiyeta,sannan
ya koma da baya ya jingina yana saurarensa

"Sai ogaaaaaa.......sai bosssss"

"Ya akayi mato......nasan kiranka alkhairi ne da kuma samuwa"

"Ba kadan ba kuwa.......na samo mana wani sabon zone na caca.......harka ruwa
ruwa.......kudi faca faca.......A wanki gara......abun kuma babu kama" Gyara
zamansa yayi sosai yana bashi hankalinsa. Baya wasa da harkar caca kwata kwata,suna
daya daga cikin abinda ke kawo masa maqudan kudade bayan kamfanin jadda
DIAMONDCHORE da ya zame masa lamba daya

"Kaman yaya?,yimin dalla dalla,don wutata ta kusa daukewa" Ya fada muryarsa tana
dan rangaji.

Yasan waye ciki da bai dinsa,tunda ya fadi hakan kuma ya gama
fahimtar abinda ke faruwa,don haka ya tattara bayanansa ya gyara zamansa yana cewa

"Wani gurin caca wanda na tabbatar a wajenka me gida local ne......akwai 'yan wasa
na haqiqa amma kuma kai tsaye na fahimci cewa gidadawa ne.......basu da wani wayewa
kwata kwata a cikinta.......akwai kudade amma fa a qasa,na tabbatar a bugu daya
zaka tarwatsasu ka kuma yi gaba da duk wani abu da suka shigo cacar dashi" Wata
shu'umar dariya ya saki

"Mato nawa" Ya furta maganar mato din na masa yawo saman kai,saidai gajimaren da
yahau ya hanashi tsaiwa su qarasa maganar,don haka ya sanya hannu ya katse kiran
kawai yana furta

"Munkaila bisa kansu" Cikin mutuwar jiki da kasala.


*_ALBISHIR A GAREKU!!_*

*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA
KUNYA KUWA?_*

*_KAMAR SU_*

Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes

*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries

*_inganci da kwalliya shine muradinmu_*
_________________________
*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA
TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*
*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

*Arewabooks:@Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997

PAGE 29



*SOUTH KOREA*

*_THE CAPITAL OF SOUTH KOREA (SEOUL)_*

*_Yanghwa-ro to hongdae geori_*


Yanghwa-ro daya daga cikin lafiyayyun street dake da wani irin daddaden
yanayi a kowacce safiya cikin anguwar hongdae dake tsakiyar south Korea. Yanayi ne
me me dadi dake wanzuwa a kowacce safiya cikin street din dake da wani irin shuru
da nutsuwa gami da nisanta da kowacce irin hayaniya daka iya damun ruhi ko
matsantawa nutsuwar dan adam.

Ga duk ma'a bocin fitowa da sassafe tsakanin yanghwa-ro zuwa hongdae
geori zai zame masa abu me wahala baisan baqin fuskar matasan Nigerians din guda
biyu ba. Zaratan matasa masu wani irin kyan zubi na halitta da kuma ajiyayyen
kwarjini da kuma haiba. Yaya da qaninsa wanda fitowa jogging kusan kowaccw safiya
ya zame musu kamar al'ada.

Muhammed FU'AD,da kuma musaddiq hamza kibiya wanda yake daga gefan
Muhammed FU'AD din. Idan yayi kamar zasu daidaita wajen sassarfa me kama da gudun
da sukeyi sai ya zame har sai FU'AD din ya wuceshi yana fadin
"Eheennn......don't stop.....don't stop" Da wata iriyar husky voice da Allah ya
huwace masa wadda ke cakude da nishi kadan na gudun da suka dauko.

Yayi kaman zai tsaya din ya kusa sau biyar......hakanan shima yake
zaburar tashi har zuwa sanda suka iso daidai wani guri. Guri ne da kusan kowacce
unguwa take da nata wanda aka tanadeshi aka killaceshi domin hutawar jamaar unguwar
cikin wasu kujeru da shimfidaddun tsirrai da suka wadatu da tsafta suke kuma samun
kulawa yadda ya kamata.



Please Login or Register in order to submit comment