You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waiwaya ta kalli nadra da huda,sai ta juya tana
ficewa suma suka bi bayanta,duk kuwa da cewa fuskokinsu sun nuna sam zuciyarsu bata
gamsu da abinda ta fada ba.

Kanta ta cusa sosai cikin lallausan pillow dinta,ta shaqo qamshin ciki
tana fesarwa ta baki. Wacce irin qaddara ke bibiyarta haka?,ta kowacce fuska
barazana rayuwa takeyi mata da lamarin aure?,tabbas ko sama da qasa zasu hadu ba
zata taba aminta da wannan shirin wasan kwaikwayon na kawu ba......kamar yadda ta
gama shirya komai don bacewa wadancan azzaluman matan.

Kamar ana jira takai nan wayarta ta dauki qaramin sauti tana
haske......ta daga kanta a nutse ta zubawa wayar idanu. A nata zabin bata da sauran
wani dangantaka ko dalili naci gaba da sauraronsu.....to amma yaqi dan zamba
ne.....wannan wata rubutacciyar magana ce data jima da haddaceta tare da adanata
cikin dictionary dinta.

Sai data zauna sosai sannan ta daga wayar ta sanya a kunnenta tana
cije labbanta.

"Salamu alaikum" Tayi sallama da muryar nan tata da tun randa ta fara furta mata
manufarta a kanta ta haddaceta tsaf......sannann ta sakayata a gurbi na musamman da
take ajiye dukkan wasu abubuwa da suka zame mata dole takatsantsan dasu.

Cikin wannan miskilancin nata daya zame mata jinin jiki ta amsa mata.
Hakan sam ba damuwar maamah bane.......tana da tarin abubuwa da takeson sake sani
tsakaninta da fu'ad.

"Ina fata zuwa yanzu dukiyar auren d'ana ta ruskeki?". Tadan shiga mamaki
kadan,kamar zata tambaya amma miskilanci ya hana,sai ta zabi ci gaba da yin shuru
har zuwa sanda maamah ta fahimci ba zatace komai ba.102
"Magana nakeso nayi dake masu tsananin muhimmanci.....naso ta kasance fuska da
fuska.....to amma inason dauke idanu da hankulan mutane daga kan plan da dukka ma
wani tsare tsare namu......na tsinci cewa yarona da nake nemawa ke shima ke yake
nemawa kansa......abune me matuqar mamaki da daure kai.....nayi mamaki kaina ya
kuma daure akan ya akayi hakan ta faru?.....ban samu wani tsoro ko kuma fargaba
ba......saboda dukkan wata alama da zata bani cewa auren soyayya ne ake shirin
qullawa babu shi......ya akayi kikasan muhammad jadda?.......meye naku shirin akan
aurenku..... Duk da ba lallai ne na sani ba......amma zan gaya miki abu guda daya a
taqaice......koma meye kuka shirya ke dashi ki tabbatar shirinku baici karo da nawa
ba".

Sosai kanta yayi wani irin daurewa,sai taji kamar ta fara daina gane
komai. Tana nufin ita din mahaifiya ce ga.......ya salam......." Ta furta cikin
zuciyarta da murya qasa qasa. Wai su din wadanne irin mutane ne wadannan?,da d'a da
uwa dukkaninsu kowa da irin kalar tasa alqiblar?,da d'a da uwa kowannensu nada
karkatacciyar manufa?,kuma duka ba'a kan kowa ba?,a kanta?.

"Ina fata kin fahimta?" Maamah ta tambayeta ganin koda tarinta bataji ba.

"Akwai wani abu me muhimmanci daya dace ki fadan ki fadi ba?" Ta motsa labbanta a
nutse tana tambayar maamah duk da yadda kwanyarta da zuciyarta suke cakude da
rudani.

"Shikenan.....qaramar magana ce kuma gajeriya,amma me matuqar muhimmancin daya
kamata ayi mata riqon tsauri" Qaramin murmushi ta saki me sauti,sautin daya ratsa
ta wayar ya isa kunnuwan maamah. Wai ta yayama ita zata tsaya a dinga tambulin da
rayuwarta tsakanin UWA da DANTA?. Ta yaya ma zata tsaya ta zuba musu idanu suna yin
yadda sukaga dama rayuwarta?,rayuwartata da ba mallakin kowa bace ba kuma wanda
yake da iko da ita?. Rayuwar da aka fusgeta da qyar?,tsananin kuma nisan kwana ya
kawota inda take zaune a yanzu?.

Isar murmushin kunnuwan maamah ya haifar mata da 'yar fargaba
kadan,saidai kuma lafazin sabreen din ya danne dimuwar

"Baki da damuwa.....ki qirga kwanakin kawai da kike jiran komai ya kasance"

"Da kyau.....naji dadi dana sameki ame saurin cika alqawari.....sati uku.... Sati
uku kadai ya rage ki zama daya daga cikin familyn jadda......nasan kuma bakisan
wanne irin family zaki shiga ba......cikin qasa da sati daya kafin sannan ina
buqatar ganawa dake don ki karbi jadawalin tsarin yadda nakeso komai ya kasance".
Idanu ta lumshe ta kuma budesu lokaci daya tana gyada kai. Karon farko a rayuwarta
da tasan murmushi yana iya fita daga fuskar dan adam a yayin da yake cikin bacin
rai.

"Baki da matsala" Ta furta da ma'anoni daban daban.

"Okay.....inason ki saki jikinki.......bayan hidimar dashi da uban goyonsa zasuyi
miki......karkiji nauyin tamabayata komai......ko nawa kike da buqata a shirye nake
dana kashe miki shi......inaso surukata tafi kowacce suruka daga cikin surukan
sanannu kuma attajiran families.....biki zamuyi na kerewa sa'a.....irin bikin da
zai kauda zato da kuma dukkan zargin me zargi a kanmu".

"Ba damuwa bane....na fahimci komai,amma ina buqatar hutu........zamuyi magana wani
lokacin" Ta qarasa fada tana yanke kiran ba tare data jira cewar maamah din ba.
Gefe tayi jifa da wayar tana nutsa hannunta cikin sumarta

"Ya ilahi.....ya akayi dukka haka ta kasance?ya akayi komai yazo a daidai?" Tayi
zancan a fili
"Kiyi aurenki adda......kiyi aurenki" Taji muryar huda dake rawa,wadda ke tsaye
daga gefanta.

Hannayen nata ta zare daga sumar,ta daga kanta a hankali tana duban
huda dake tsaye. Idanunta cike fal da hawaye,ta qaraso da sauri ta tsugunna gaban
Sabreen gami da riqo hannayenta

"Adda....."

"Shshsh" Ta dakatar da ita tana dora yatsanta akan lips dinta.

"Nayi aure a wannan situation din kike fadi huda?.....na kaiku ina?.....waye zai
kulamin daku?"

"Allah......Allah ne adda" Ta amsa mata har yanzu muryarta na rawa.

"Na sani huda.....na sani,amma kinsan wanne irin aure ne wannan auren
nawa?.....rayuwar addanki sukeson jefawa cikin wani game da ake bugashi tsakanin
D'A da UWARSA.game din da ba wanda yasan meye ainihin ma'anar bugashi,zasu tsoma
rayuwar aminatu a ciki bayan bata cancanci ta fuskanci raba uqubar rayuwar kowa
ba.....me nayi da zasu nemi na zama silar cutar da dayansu?". Tana kaiwa nan sai ta
samu kanta da kecewa da kuka,wani nannauyan kuka me siririn sauti,irin kukan data
dauki sama da shekara shida tana tarashi a qirjinta,don bata da kafadar da zata
kwantar ta fiddashi ta rage wannan radadin.

A yau hudan ta zame mata wannan kafadar,har ta zama jarumar data dinga
sharewa sabreen hawaye dukka jikinta yana rawa

"Daga yau zamu dinga raba wannan tsananin da quncin adda......ba zaki sake kuka ke
kadai ba....kiyi haquri kada su nadra su jiyoki"

"Ba wanda zai rabamu huda.....dole na nemana muhallin da zamuyi nisa da dukkan
wannan qullin.....bazan fuskanci wannan abun ba". Tayi maganar tana zare kanta daga
kafadar hudan,ta miqe tsaye kai tsaye tana dosar bakin gadonta.

𝙒 𝘼 𝙎 𝙃 𝙀 𝙂 𝘼 𝙍 𝙄


*******Daidai lokacin da su huda suka wuce tahfeez a safiyar asabar din. Ta shirya
kanta tsaf cikin turkey dress da suka maidata tamkar daya daga cikin kyawawan
'yammatan turkey din.

A nutse take rufe qofar parlor dinsu,ta zuge qaramar jakar hannunta ta
jefa key din duk da yadda takeji a jikinta akwai idanuwa masu yawa a kanta cikin
jamaar dake zazzaune a tsakar gidan.

Tsakanin jiya da yau din ta karanci an samu yawaitar jama'ar dake zama
a tsakar gidan nasu. Wani irin zama da yake kama da zaman gulma tsurku da kuma
zunde.....a wani yanayin kuma yafi kama da zaman jajantawa da kuma jimamin da
batasan ma sunayi ba. A nata ganin dukkan kai kawonsu bazai wuce akan tatsuniyar
qirqirarren aurenta da kawu ya gabatar cikin gidan ba,labarin daya girgiza kowa
cikin gidan harda 'yan uwanta da suke uba daya wanda suke aure a wani
gidan.....lamarin da inda suna da yadda zasuyi suka tsige mata shi me yiwuwa ta
sanyasu cikin jerin masoyanta da bata da kamarsu.

Idanuwa sunyi yawa a kanta sanda take ratsawa tsakar gidan,idanuwan
dake cike da hassada da jin haushinta,sannu a hankali ta samu ta isa ga soronsu ta
bulla farfajiyar gidan da zata danganata da gate na qarshe na gidan.
Motar dake lullube cikin tempol qarqashin rumfar data kasance
ma'ajiyar motor mahaifinsu sanda yake raye idanunta suka fada.....

Ido ta dauke daga kanta tana jin wani zafi yana ratsa zuciyarta. Da
gaske yake kawun kan lallai saita karba komai harda motar da anata idanun daidai
take da motar daukan gawa.

"Komai ya kusa qarewa" Ta fada qasa qasa sanda take gifta motar,tana buqatar isa
inda tayi niyya don shirya yadda zata nesanta kanta da qannenta da wannan
Cakwakiyar da ake shirin tsomata.

"Ke.....ina zuwa?,ina zaki haka?" Muryar kawu rufai ta ratsa dodon kunnenta,kawun
dake tsaye qofar wani daki dake can qarshen katangar gidan. Dakine da ashekarun
baya mahaifinsu kr jibge kayan abinci a ciki.

Duba daya tayi masa ta kauda kai taci gaba da takawa abinta don fita. Ya
fahimci maganarsa sam bata dadata da qasa ba,hakanan sautinsa bazai taba dakatar da
ita ba,don haka ya saki aikin gyara kwalayen da yasa akeyi ya tako da sassarfa
cikin burin cimmata.103


Har ta murda hannun qofar ta bude sai kuma ta dakata saboda wani tunani
da yazo mata. Tsaf kawun zai iya binta waje ya tara mata jama'a,don shi din bai ita
magana qasa qasa ba.

"Ina zaki nace ke aminatu" Yayi tsaye a gabanta yana fada idanunsa a kanta yana
daure fuska.

"Kin tambayi mijinki?,da izininsa koda saninsa zaki fita?" Ya sake jefa mata
tambayar da gaske yana adan tsorace.

"Mijinki" Kalmar tayi wani amsa kuwwa cikin kunnenta. A duk sanda taji ya ambaci
wannan Kalmar sai abun ya zame mata wani irin baqon abu.

"Bazan hanaki fita ba.....amma sai na tabbatar da izininsa kika fita din,don a
yanzu ke amana ce a hannunmu,bazan Kuma yi wasa sa wannan amanar ba har sai na
tabbatar ta fita daga hannu na".

A nutse ta daga ido ta kalleshi,abun yana bata mamaki gaba daya,wai
yau kawu shike haqiqancewa haka akan lamarin da ya shafeta?,wai yau shike
tambayarta ina zata fita?,lallai kudi sun zamewa rayuwar wasu bayin jarabta. Abune
da bata taba sanyawa cikin kanta ba......wai akwai wata rana da zata zo har wani ya
damu da inda ta fita ko kuma ina zata je?.

"Ki sanar dashi sannan kije duk inda kikeson zuwa din" Ya same maimaitawa yana tura
qofar da qafarsa.

"Oh......inda ranka kasha kallo....duniya juyi juyi wai kwado ya fada ruwan
zafi......dama idan bakayi sharar masallaci ba ai kayi ta kasuwa,kudi
shu'umai......iska kuma na wahal dame kayan kara.....ayi dai mu gani idan tusa zata
hura wuta". Wannan jerin gwanon habaicin suka fito daga bakin bibo wadda ta iso
daura da wajen don zubda sharar sa ta kwaso daga dakinta.

Waiwayawa kawu rufai yayi yana dubanta
"Wai dukka wadannan gayyar gamayyar haibaicin akan waye kike?,indai da Sabrina kike
aikin banza kikeyi,kinfini sanin halinta,uwa uba kuma a yanzu ita din me arziqi
ce.....me arziqi kuwa baya fada da talaka......ni kuwa kinsan warki nike daidai
qugun kowa.....to saiki banbance".
Tsaiwa tayi sannan ta waiwayo tana zabgawa kawu harara,wani irin
tsanarsa da haushinsa suna cikata

"Magana kakeyi ne ko bakinka ne a haka?,aini rufai na jima da sallamaka cikin
lamurana.....ashe da gaske aboki yana iya juyewa ya koma maqiyi?,dadin abun ba'a
fimu iya 'yan shige shigen nan ba,to na meye ma zan damu banda abinka rufai?" Ta
qarasa maganar tana yarfe hannu cikin son boye damuwarta da lamarin.

"To barkanki.....gwanda da kika gyara zancanki kika samawa kanki salama....".

Kunnuwanta ba zasu iya ci gaba da sauraron wannan quruciyar ta
kawun da bibo ba,wanda har yanzu suka kasa dainawa,duk kuwa da cewa kansu da
bakinsu a hade yake,yanzun ne abun duniya yake shirin hadasu,don haka suna tsaka da
sa'insarsu ta tajuya tana takawa da nutsatsiyar tafiyarta dinnan da 'yan bani na
iya suka sawa suna

"Maciji me tafiyar mutuwa" Nutsuwarta a tafiya a cewarsu sam bai dace da halinta ba
a tasu fahimtar.

A falo tayi wurgi da jakarta ranta yana susa,tun komai baiyi nisa ba
har kawun ya soma!shiga gonarta da kuma nuna mata iyakarta?. Dankwalin kanta ta
zame sassalkar sumarta ta zare daga ribbon din data matse gashin,ta koma da zafi
zafi ta zauna saman kujerar tana furzar da iska daga bakinta

"Ta yaya ma zata zauna a maida rayuwarta haka?,ya zata zauna ta rayu kaman
haka?,dole ta matsa qaimin tattare komai dama kowa nata zuwa bigiren da zata ci
gana da gudanar da rayuwarta cikin 'yanci kuma a yanayin duk da takeso.

Idanunta dama kunnuwanta gaba daya suna a tsakar gidan nasu,tana
bibiye da kowanne motsi na gidan. Jira takeyi kawai kawun ya matsa daga gidan ya
tafi tashi sabgar itama ta fice nata. Kaman yadda takeji koda sama da qasa zasu
hade ba zata taba daga waya ta kirayi mutumin da bata taba jin burbushin
muhimmancinsa cikin rayuwarta ba......hakanan fitarta a yau ta zama wani abu na
tilas don laluba yadda zasu gusa daga wannan muhallin zuwa wani 'yantaccen gurin.

Tana ji a jikinta idan bata aiwatar da hakan ba a yau tamkar bata da
wani sauran lokaci da ya rage mata,kamar lokaci ya riga ya qure mata,kamar yaune
kawai damar data rage mata.

Saidai duk yadda take zirga zirga da sanya idanu,kowanne motsi sai
ta juyo muryar kawun ko gilmawarsa. Tun lokacin dawowar yara daga makaranta baiyi
ba har yayi. Ba nutsuwa a tattare da ita sanda suka shigo,don ko abinci bata dora
musu komai ba,burinta kawai kawun ya matsa ta samu ta fice,amma qemem wunin gaba
daya yau a gidan ya yishi.

Bata samu ya bar gidan ba sai kusan biyar na yammaci,tasan kuma
yayi hakanne saboda yasan ita din bamai fitar dare bace,saidai a wannan rana ta
karya record dinsa,ta shirya a gaggauce ta fice abinta.

Cikin nasara ta kammala komai,saidai hakan ya dauketa har zuwa bayan
sallar ishai,tanata fargaba ta shigo gidan,ta wuce kai tsaye cikin dakinsu,wanda
tana sanya qafa shima ya sako tasa qafar,saita zarce bedroom kawai,don tasan dole
zai fahimci ta fita,koda bai fahimta ba a cikin gidan nasu ba zaa rasa masu gaya
masa ba,a yadda suka canza su kansu,komai yana shirin canzawa gaba daya.

*******K'arar wayarta shine abinda ya farkar da ita daga nannauyan baccin daya
dauketa,hannunta daya mata nauyin ta miqa ta jawo wayar tana duba me kiran. Ganin
sunan titi ya sanyata miqewa ta zauna sosai tana amsa wayar.
"Anjima da yammaci jirginmu zai tashi zuwa qasar India,najeeb ya gama komai"

"Alhamdulillah" Ta furta a sarari tana jin kamar an cire mata daya daga cikin
nauyayan duwatsun dake danne saman zuciyarta. Ciwon aishatu shine cikar burinta na
farko da take fatan gani kowacce rana.

"Zan shigo naga aishatu.....zan shigo da wuri titi in sha Allah" Ta fada tana jin
farinciki yana ratsata . Murmushi titi din tayi

"Koda baki shigo ba sabreen kin gama yiwa aishatu komai ai,tsakaninmu dake sai
fatan alkhairi".

Idanunta ta maida kan agogo bayan sun gama wayar,takwas saura na
safe. Tayi mamaki da motsinsu huda bai tasheta ba,suma kuma cikinsu ba wanda ya
tadata,sai ta jawo dan qaramin farin hijab dinta data cire sanda zata kwanta ta aza
saman kanta ta zuro qafafunta qasa ta sauko tana fitowa falon.

Dukansu sun gama shirinsu,kowa sanye da uniform,fitowar tata taja
hankalinsu,suka soma gaidata sanda take zama kusa da haneefa,saita karba saka mata
socks din tana cewa

"Auta ta daina neman me saka mata socks yanxu ko?,girma yanata zuwa" Dariyar jin
dadi tayi tana cewa

"Amma adda kullum ya nadra cewa takemin yarinyar nan...."

"Rabu da ita,harda ke za'a raba aiki idan muka koma sabon gida" . Furta sabon gidan
da tayi sai dukansu suka zuba mata ido,bata bada hankali ba sai data gama sawa
haneefa socks din.

"Adda......wani gidan zamu koma?" Haneefa ta riga 'yan uwan nata tambaya fuskarta
na nuna farinciki sosai.

"In sha Allah.....gobe.....kaman ko yaushe bana buqatar masaniyar kowa,idan an
tashi daga school yau ba islamiyya.....koda kun dawo baku sameni ba zan shiga duba
aishatu,ku fara shirya kaya huda cikin manyan bags din can kafin na dawo"

"Tom" Huda ta amsa mata saidai nata jikin a sanyaye yake. A nata hasashen tana
ganin kaman idan addan nata tayi auren shine zaifi dacewa da ita......auren zai
zama wata hanya ta wanketa daga dukkan zargi da mummunan kallo da society din da
suke rayuwa a ciki suke mata,bataga alfanun ture wannan auren ba.....duk da tayi
mata nata bayanin gwargwadon yadda zata fahimta.

Addua ta musu na dawowa lafiya,saita jawo wayarta tana son taba
JIB ya qara mata bayani akan wanda titi tayi mata,sannan shima suyi handing over
akan komai.....tana buqatar sabuwar rayuwar da babu kowa cikinta daga ita sai
qannenta da kasuwancin da takeso ta fara wanda shi take sanya ran zai zame musu
madogara

_ni kuwa nace ummmm inji me ciwon haqori,anya kuwa sabreen?,haka siddan zakici
bagas?😂,to bari dai mu gani_

Wayar bata shiga ba saiga nadra da haneefa sun dawo cikin dakin,ta
ajiye wayar ta maida hankalinta a kansu tana shirin tambayarsu lafiya huda itama ta
shigo. Tsoro sosai saman fuskarta,ta qaraso cikin falon tana dubanta.

"Adda.....ina tsoron faruwar wani abu"
"Me kenan?" Sabrin ta tambayeta tana tattara hankalinta sosai a kanta

"Wasu manyan qatti ne guda biyu a qofar gidan nan.......duk wanda zasu shiga ko zai
fita su zasu bude masa qofa.......nayi qarfin halin tambayarsu su waye amma ba
wanda ya amsa min a cikinsu". Shuru sabreen tayi tana qanqance idanunta cikin
alamun zurfafa a tunani. Kwanyarta ta gaza cafko komai,sai ta maida dubanta kan
haneefa.

"Akwai wani alamu na cutarwa a tare dasu?,hayaniya tsawa ko wani abu daban?". Kai
ta girgiza

"Ba daya,kawai zasu kalli fuskarka ne sannan su bude maka qofar"

"Haka kowa yake fita daga cikin gidan?.....akwai wanda kukaga sun hana fita?"

"Kowa yana fita,amma cikin tsoro,ba kuma wanda suka hana".

Sosai ta jijjiga kanta zuciyarta tana d'arsa mata wani abu,saidai
kuma bata tunanin hakan zata kasance.

" Ba damuwa,ku wuce kuma ku fita kaman kowa,basu da alaqa daku". Cak sukayi suna
kallonta,da alama dukkaninsu itace damuwarsu,kada ma huda taji labari saboda
sanayyarta da abubuwa da yawa da sauran basu sani ba.

Tattausan murmushin nan nata dake tsananin qara mata kyau ta saki
tana girgiza kai

"Karku damu......muna da yawa a gidan,ba abinda zai faru damu,a dawo lafiya" Tana
ganin yadda suka kama hannun juna da kyau kaman kowa na shirin karewa dan uwansa
wani abu me cutarwa,wannan sai ya tsinka mata zuciyarta sosai,ta sake jin ruwa da
iska zata ci gaba da zamewa rayuwarsu garkuwa har abada.

Tana dauke idonta daga kansu kankatsin salatin bibo ya rusketa

"Daada.......tani......wai bakuga yau kuma bala'in da muka wayi gari dashi bane
yau?,karta kartan garada sun tsare mana qofar gida kamar gidan tsaffin 'yan
damfara.....koda yake biri yayi kama da mutum.....kuma sai da karen gidanka kake
ganin na wani gidan......wannan masifa da take shirin afko mana gida ya ubangijin
Allah ka tsaidata iya kan wansa ya jajibota....."

"To wannan balai mudai bamu taba ganin irinsa ba tsahon rayuwarmu da mijinmu sai a
wannan karon" Tani da suke dan juma da dan jummai wani lokaci ita da bibo kafin su
hautsine kuma ta fada tana tafa hannuwa

"Yo kome zamu gani aisaidai mu nemi tsari.....wanna masifa duk yadda akayi silar
wannan gafalallen auren ta samemu.....wai daada ba zaki fito bane sai an cimmaki?".

"Me zan fito nayi?,ina ruwan biri da gada?,tunda dai basuce ni suke nema na ina
ruwana ni dasu?,maza ku zafafa damuwa dasu sayi awon gaba daku idanma zuwan nash ba
naku bane ku jawa kanku da shegen bakinku"

"Bakinki ya sari danyen kashi wallahi,.....saboda abun arziqi bai karbi kare
ba,daga abun arziqi sai ki juye mana da fatan tsiya?,sha zamanki idan an cimmaki
wani cikinmu aka cimmawa"

"Ke kika sani" Daada da bata fiya jurewa dogon cece kuce ba ta fada.

Tana danna number jib kunnuwanta suna saurarensu. Wannan dabiar
tun bata mallaki hankalin kanta gaba daya ba tasan bibo da ita,har kwanan yau kuma
ba abinda ya canza a tattare da ita.

Waya sukayi da jib din ta minti talatin kacal,daga nan sai ta soma
shirin shiga wanka. Ta dawo daki ta tsane jikinta da towel,ta shirya cikin glitter
wax me tsananin kyau data dace da kalar fatarta da kuma yanayin qirar
jikinta,dinkin half bubu da straight skirt da aka tsaga bayansa,ta dauki Chantilly
veil me asalin tsadar peach color adon jikin atamfar,ta hada da plate shoe da hand
bag dinsa bagco.

A tsaitsaye ta hada tea da biscuit tasha,ta yafa mayafinta ta
daura agogon hannunta don buri take taje taga farincikin dake kwance fuskar
aishatun.

Hankali kwance take takawa a harabar gidan nasu tana nufan
qofa,tana jin ta gama da dukka wata matsala yanxu dake gabanta,so saura ya rage na
wadanda suka gayyatota cikin matsalar susan yadda zasu warware qullinsu.

Tana taba handle din qofar taji an budeta,sai ta daga kanta a
hankali ba kaman dazu da yake a qasa ba tana kallon gabanta.

"Good morning madam" Kakkaurar muryar ta fada cikin tsananin girmamawa har yana
rusunar da kansa duk kuwa da cewa ya ninkata a tsaho da shekaru,girman jiki kuwa
sam ba'a maganarsa don bata kawo koda gefansa ba.

"Good morning madam" Ta sake jin wata muryar ta daban a daya gefan nata shima ya
fada a girmame.104


Da idanu ta sake binsu,murdaddune a tsaye,wanda babu alamun
tsoro ko shakka a tattare dasu,zubin tsayayyun masu damarar nan da akan samu akan
hanyar shiga fadar shugaba wasa,wanda rana ko ruwa basa sanyasu motsawa ko canzawa
daga muhallin tsaiwarsu.

Sosai ta tattaro dukka dauriya da qwarin gwiwarta,ta azawa
fuskarta wani mugun daurewa,tasa hannu tadan tura qofar tana amsawa ciki ciki da

"Morning" Tana sanya qafarta zuwa waje

"Sorry maaa........kiya haquri ki koma ciki..... Isn't allowed maaa". A mamakance
ta dakata gami da ja baya saboda yadda yayi bake bake a gabanta,bataga ma hanyar
wucewar ba komai qanqantarta

" Isn't what?......waye kai?" Tayi masa tambayar kai tsaye saboda bata da lokacin
batawa tayi wani dogon nazari.

"My name is abdulgafar......ni da abokin aikina kuma duka munzo ne don tsaronki" Ya
fada da matuqar girmamawa kansa a qasa,baya iya wani cikakken hada ido da ita.
Haushi da mamaki duka suka hadu waje daya suka tsaya mata a wuya

"Tsarona like how?.....ni na buqaceku?"

"No maaa.....bake bace......umarni ne daga wajen boss" Dayan da baiyi magana ba sai
yanzu ya fada da tasa girmamawar

"Who's boss?" Ta fadi da mugun fusata saboda ta fara shanshano wani abu

"Sir muhammad jadda....."

"Enough......ya isa.....ku bani hanya na wuce,daku da boss din naku da gadin nawa
duka matsalarku fe ba tawa ba".

Rusunawa kadan yayi yana hade hannayensa waje daya

"Am sorry maaa......ba'a yarda mu barki ki fita ko ina ba har sai boss ya dawo".
Kadan ya rage bakinta ya furta kalmar ashar saboda tsananin mamaki,sai tayi tsaye
kawai tana kallon baqar fuskar mutumin mamaki yana zagayawa da ita duniyar
tunani,yayin da shi kuma yake ci gaba da furta mata kalmar rarrashi da kuma ban
haquri duka a cakude cikin harshen hausa da karyayyen turancinsa.

A wannan karon tana jin tura takai bango,ta inda kuma aka hau ta
nan ake sauka,bata kuma da

Please Login or Register in order to submit comment