You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya cin komai...." Dubansa
ta sakeyi kadan sai kuma ta dauke kanta tana qirqiro murmushi

"Kowa time table zai bani na abinda yakeso yaci kullum har sati guda koma sati
biyu.....masu girki na musamman zan ajiye muku.....burina naga kun kusanta
dani......na maida tsohuwar alaqar dake a tsakaninmu" Ta qarasa maganar tana duban
cikin idanunsu.

"Fu'ad" Ta sake kiran sunansa,ya daga fararen idanunsa da suka fara rusuna saboda
gajiya da zama a wajen,sam baya jinsa comfortable sam sam

"Me yasa kabar musaddiq tare da farouq......duk da ba laifi bane.....amma kaman
zaifi cancanta ya kasance tare dakai qarqashin naka kamfanin" Shuru ya biyo baya na
second uku,sai ya maida idanunsa ya kulle yana jan boyayyen numfashi. Shikam yayi
imanin ba zata canza ba,ya tabbatar abune me wahala da girman gaske da zai sauya
mata hali farat daya. Wannan ya sanya kowanne taku ko motsi nata yake sanya masa
ayar tambaya,wani lokaci idan tayi wani move din sai yaji gaba daya kanshi ya juye
yana tambayar kansa anya da gaske maamah din itace uwa ta asali a garesu?.

"Kowanne bawa da abinda yafi shaawar yi yafi qwarewa a rayuwarsa......yadda abba ya
ginemu shine kowa ya dauki zabinsa da ra'ayinsa a rayuwa muddin bai kaucewa hanya
ba....inda kikaga farouq da musaddiq su suka zabi wannan sashen duk kuwa da cewa
tare da farouq mukayi gwagwarmayar samar da abinda na gina din a yanzu.....ba wanda
ya zaba masa ko ya tursashi gashinan maamah ki tambayeshi" Juyawa tayi tana duban
musaddiq ranta duka a jagule,bata son kowa ya rabi fu'ad a duniya idan ba dan
uwanshi ba,batason kowa yasan sirrin dukiyarsa idan zaiyuwu sai ita daya,wannan
tunanin ya sanya ta yanke shawarar sanya ido me tsananin a alaqar fu'ad din da
amna......don ba zata taba yarda amina ta dauki d'iyarta ta qwaquma masa ba su
qarasa nadeshi.

"Shikenan,Allah ya taimaka" Ta fadi tana sauke numfashi bawai don ta haqura a
zuciyarta ba. Kawai tana ganin tunda komai yana kan turba bai kamata ta bata
lokacinta tana dogon zance dasu ba,lokaci kadan take jira ta soma bada umarnin
wanda zai shiga ko ya fita daga rayuwarsu.

"To yaya sunan surukar tamu musaddiq?....koda wasa baka taba attempting kawota ta
gaida mamarka ba?" Ta yiwa musaddiq tambayar tana dubansa da murmushi,cike da
zaquwa da son jin kalar matan da suke shirin kawowa rayuwarsu. Wani babbab abu da
yake cikin tsarin abubuwan da takeso ta yiwa garambawul idan damar da take tsimayi
ta samu,tanason surukanta su zama qarqashin ikonta fiye da yadda hajja ke juya nata
mulkin a gidan.

Murmushi kadan ya saki,karon farko da yaji 'yar kunyarta ta sauko masa

"Minal bata iya zuwa ko ina,daga makaranta sai gida.....zata zo wataran in sha
Allah". Ba haka takeson ji ba,don haka ta gyara zamanta tana sake sakin fuskarta

"Aah wataran yaushe kenan?,ina buqatar ganinta mu tattauna ka shaida mata mamarta
nason ganinta......" Ta fadi din don da gaske tanason ganin wace ita?. Zuwan nata
kuma a nan ne zata samu amsoshin tambayoyib data tabbatar ba zata samesu daga bakin
musaddiq ba.

"In sha Allah" Ya fadi a taqaice yana auna yadda abun zai kasance.

"Kai kuma fa?" Ta waiwaya tana duban fu'ad daya tattara hankalinsa duka saman
wayarsa tamkar ma baya jin abinda suke fadi. Gajiyayyun idanunsa dinnan ya daga ya
kalleta,sai kuma ya maida dubansa ga musaddiq. Kan musaddiq din a qasa yana satar
kallon fu'ad din ta qasan idanunsa,boyayyan murmushi nason qwace masa.

"Me maamah?" Ya tambayeta da sautin muryarsa da tayi laushi sosai.

"Wa ka daukomin a matsayin suruka?" Ta sake maimaita tambayar tata.

"Babu fa maamah...." Musaddiq ya fadi muryarsa na nuna murmushin da ya boye.

Debe kallonta kacokam tayi ta maida kan musaddiq tanason sake samun
tabbacin hakan

"Kamar yaya kenan?" Satar kallon fu'ad yayi sannan ya dubi maamah,yayi qasa sosai
da muryarsa,duk da yasan dole ya jishi don yana da wannan baiwar ta kaifin ji

"Ba wata budurwa.....tsoronsa ma suke......ba wadda take iya tararsa maamah tace
tana sonshi"

"Very good" Ta fada qasan zuciyarta. Tsananin farincikin da taji ya bayyana har
saman fuskarta,tadan danne tana hada rai

"Garin yaya?.....har yanzu halinka dinnan bai canza ba?" Ta watsa masa tambayar .
Karon farko kenan da magana kwatankwacin wannan ta taba hadasu,don haka ya rasa ma
da abinda zai bata amsa illa cewa da yayi

"Ba yanzu ba....lokaci baiyi ba.....in fact ma da sauran lokaci"

"Lokacin lokaci na ne,yana kuma tafe" Ta bawa kanta da kanta amsa a zuciyarta,amma
a fili sai tace

"Allah ya nuna mana lokacin".

Duka hirar ba wani armashi gareta ba,amna haka suka sadaukar da
lokacin har zuwa sanda ta basu izinin tafiya sukayi mata sallama suna ficewa.

Suna tafe ne kawai suna dosar gidan,daga shi har musaddiq din ba wanda
yace da dan uwansa komai. Sai da sukazo mabanbantan qofofin sassansu,fu'ad din ya
murza key yana bude qofarsa yace da musaddiq

"Shigo ciki ka zauna muyi magana" Ba tare daya dubeshi ba,ya gama budewa ya shige
musaddiq din yabi bayanshi.

Zaune kawai tayi tana duban kwanukan abincinta da suka barta
dashi,banda ruwan gorar dukkaninsu ba abinda suka taba ko qanqani. Lemon data zuba
ta turawa musaddiq din ma tana saka ran zaiyi koda kurba daya ne amma baiyi din ba
shima sai ya buge da shan ruwa. Ta fahimci yana bin sahu tare da matuqar kwaikwayo
ga fu'ad,iya wannan ya isa ya bata amsar cewa,muddin ta samu fu'ad ta samu
musaddiq......wanda kuma wannan din shine babban qalubalen da aikin data sake
amanna ba qarami bane.

Furzar da iska tayi me zafi daga bakin ta,kusan komai data tsara ya
wargaje babu shi,dan abinda ta amfana dashi daga zuwan nasu bai taka Kara ya karya
ba.

Akwai damuwa sosai a ranta da take da buqatar abokin tattaunawa,don
haka ta sauka daga dining area din zuwa ainihin falon ta dauki wayarta ta lalubo
hajja.

"Musaddiq" Ya kira sunanshi kai tsaye sanda yake zaune saman wata qawatacciyar
kujera da irinta qwaya daya ce tal cikin falon.

"Na'am" Ya amsa masa. Shuru kaman bazaiyi magana ba,sai kuma ya zauna sosai yana
goye hannuwansa a qirji

"Inaso ka zama me takatsantsan sosai......inaso kuma ka zama me kula.....bazan
hanaka zuwa gidanmu ba duk sanda kake da muradin hakan......amma kayi aiki da
hankalinka da kyau......yanzun kai ba yaro bane.....ba wannan musaddiq din da ko
yaushe sai hammansa yana gefansa bane don ya kula da abinda zai cutar dashi ko ya
amfaneshi bane.....abubuwa sun yiwa hammansa yawa......kula da rayuwarsa yana
hannunsa".

Wadannan kalaman na hamman su suka dinga juyawa cikin kanshi. Duk da
bai fito qarara ya masa bayani a bayyane ba,amma kamar yadda yace din shi ba yaro
bane yanzun,hakanan shi a karan kansa hankalinsa ya fara dauko masa wasu abubuwan a
iya zuwansu gidan yau kawai.
Haka kawai ya kasa bacci a daren,har yanzu musaddiq baisan ainihin wace
maamah din ba. Iya matakin da idanuwan basira da hankalin musaddiq kadai ya kaishi
bai sadar dashi da ainihin wacece maamah ba........meye zata iya yi?,da wanda ba
zatayi ba.......dole koda a fakaice ne ya sake nesantashi da tunkudeshi daga dukkan
abinda yake ganin zai iya zama cikas a rayuwarsa.

Bugu biyu tak hajja ta dauka,hakan ya yiwa maamah dadi,sai ta miqe da
wayar tana nufar bedroom dinta

"Na zaci kinyi bacci ai"

"Aah inadai shirin tashi.....labaran ne ya zaunar dani muna lissafin abinda
kamfaninsa ya samu na shekara". Ido maamah tadan fiddo cike da mamaki

"Kamfaninsa fa?,yanzu lissafin shima tare kukeyi?". Dan qaramin murmushi me sauti
hajja ta fidda tana aza hannunta saman kan budurwar dake kwance saman cinyarta tana
amsa waya itama

"To meye a ciki?,nice uwarsa fa?,akwai wani abu da suka isa su boyemin?,koda cikin
gidajensu akayi abu koda da darene da safe kuwa rana bata bullowa bansan komai
ba......ke banda ma ina taka birki ma wasu abubuwan......ai hatta sunnar aure da
matansu sai sanda na bada iznin a yita,kuma idan anyin sai an fada min"

"Innalillahi......ke hajja?" Maamah ta furta cikin tsananin mamaki

"Ke?.....zauna kina wasa da lamarin yaran yanzu,kina sake musu hanya sai linzaminsu
ya koma hannun matansu,keda wahalar raino da daukan ciki amma wata ita keda
d'an,kin zama 'yar kallo,sai abinda tace a tsakuro a sammiki.....tun daga kan
yahaya na fara daukan izina.....ban kuma zauna ba har yau har magajin gobe" .

Duka mamaki ya gama kashe maamah,amma kuma bayanan hajja din sai suka
gamsar da ita,ta kuma yarda cewa gaskiya ta fadi,gashi yanzun ita tana fafutukar
karbar 'ya'yanta daga hannun wata ma tun basuyi aure ba?.

"Yanzun ya ake ciki?,komai ya tafi dai dai ko?" Ajiyar zuciya maamah ta saki tana
maida hankalinta ga hajjan

"Hajja ba abinda sukaci fa?.....duk wahalar nan kin ganni da kayana suka
barni....."

"Karki gaggawa,idan ba yau akwai gobe,idan ba gobe akwai wani satin"

"Haka nake gayawa kaina......kana iya target din abu amma shekara goma gaba kake
hangowa.....zamu zuba dasu in sha Allah......wannan karon banga abinda ya isa ya
hanani ko ya dakatar da burina ba" Ta fadi har qasan zuciyarta tana jin confidence
akan wannan.

"Sirrin samun nasararmu dama itace jajircewa naci da kafiya". Hajjan ta qara mata
qwarin gwiwa.

Sun tattauna sosai har na kusan mintuna talatin kafin su yanke kiran.
Hajjan ta sauke wayar wani murmushi na fita daga fuskarta,tadan tsuke bakin ta
lissafinta yana tafiya da nisa sosai.

"Mommy ga adeel zaku gaisa" Budurwar ta fadi tana daga kanta daga saman cinyarta
hadi da miqa mata wayar. Sai data kalleta sannan ta amsa wayar ta sanya a kunnenta.

Ba yabo ba fallasa ta amsa gaisuwar nashi,ba jimawa sukayi sallama ta
miqawa yarinyar wayar tana kallonta. Kallon hajja kawai a garesu yana da
fassarori,don haka tayi masa sallama ta katse wayar ta ajiyeta a gefe tana kallon
hajjan

"Momy lafiya?" Numfashi ta ajiye tana dubanta duba na kai tsaye

"Ina sake gaya miki......nayi miki tanadi,kada ki kuskura ki zurfafa a soyayya da
kowa....don kowa a cikin rayuwarki temporary ne......akwai target dina.....kuma
bazanyi missing target dina ba tabbas" Tayi maganar da sautin da zai gaya maka
tayi maganar ne da gasken gaske daga zuciyarta,ta kuma yi maganar tana kafe
autartata da idanu don ta sake jaddada mata girman maganar.

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 66


Itama duban momyn nata take yi,ta sani tabbas momy din nata tana matuqar ji da
ita.....kaman yadda ta sani taci buri sosai a kanta. Duk da hakan tana da buqatar
qarin haske a maganarta,don haka ta motsa kadan

"Momy.....wanne irin buri ne?,ta yaya zan iya sallamar dukkan kuma wadanda muke
tare dasu yanzu?"

"Bance ki sallamesu yanzu ba,tukunna dai.....amma dai abune da kika sani
cewa.....ke din ba kalar qananun maza bace....ban haifeki don wani me jaririn
arziqi a hannunsa ya aureki ba.....plan dina kuma idan lokaci yayi zakiji....don ku
yaran yanzu kwata kwata bakusan me ake nufi da sirri ba".

*****Ta jima zaune gefan gadonta tana juya wayarta a hannu. Mikail takeson kira,ta
kuma shirya haduwarsu kaman yadda ta tsara zata kammala da babinsa ta kuma rufeshi
kwata kwata cikin shafukanta kamar yadda ta binne maza masu yawan gaske. To amma
haka kawai duk sanda tayi attempting na kiran nashi sai taji kaman kada ta kira
din.

Wani sashe na zuciyarta na bata qwarin gwiwar ta kira

"Ya cancanci ya fuskanci komai......ya kuma cancanci kowanne irin hukunci,jin
kunyar mara kunya asara ce!" Ta sake jin wani sauti daga can qasan zuciyarta yana
rada mata maganar har zuwa kunnuwanta.

Danna kiran tayi,ta kuma tattara dukka nutsuwarta akan wayar tana
sauraren yadda Kiran ke tafiya kai tsaye zuwa layin mika'il din.

A kasalance yake shiryawa,kasancewar daren jiya ya shawu. Duk da ya
tsagaita shan ma,bai wani sha yadda yakeso ba,saboda ya sani safiyar yau din
litinin tana cikin ranaku masu muhimmanci da zai gana kai tsaye da CEO. Mutum na
farko kaf rayuwarshi dake masa wani irin kwarjini,kwarjinin daya tabbatar yana da
alaqa da kamewarsa......da yadda fara'a ko murmushi sukayi nesa da fuska dama
rayuwarsa gaba daya.

Ya jima yana so ya shiga rayuwarsa fiye da matsayinsa,amma kuma ya gaza
samun wannan fuskar. Mutum ne da idan ya zauna aiki kawai,baya daukan wata magana
da ba cikin aiki take ba,kamar yadda baya daukan wasa ko kuma wargi.

Yadda dukkan ma'aikatan dake aiki qarqashin kamfanin suke da
iyakoki......haka nan dukkan wata magana da zaiyi dakai akwai iya adadin lokacin da
yake baka.

Qarar wayarsa ta ja hankalinsa sanda take saka links na rigarsa,sai
ya dakata cak daga abinda yakeyi din cikin tsananin mamaki yana kallon wayar.

"What a wonderful day" Ya fada qasa qasa yana daukan wayar ya zauna gefan kujera.
Wani mamakin yana sake kasheshi da idanunsa suka tabbatar masa eh itace take
kiransa

"Yau kuma da kanta?,da wanne irin sa'a na tashi?" Ya yiwa kansa tambayar yana daga
kiran ba tare daya tsawaita dogon tunani ba.

Kamar kowanne lokaci tayi masa sallama wadda shikam ba kasafai yake
iya tunawa da ita ba. Sai yadan daburce kadan kafin ya amsa sallamar ya dora da
fadin

"Good morning queen....nayi kira nayi kira har na gaji anqi a dagamin waya....
Kwatsam sai gashi na tsinci wani abu da ban taba kawowa zai faru ba".

Murmushi ta saki kadan wanda ko kusa da gefen zuciyarta bai kai
ba,yayin da shi kuma kunnuwansa yaji kaman zasu narke da fitar sautin sassanyan
murmushin nata. Kowanne tsiga na jikinsa sai ta shiga tashi

"Ka sani ko yanayin alaqa da dangantakarmu ne suka dauko hanyar sauyawa?"

"Da gaske!" Ya fada da wani irin murna daya kasa boyuwa yana fidda idanunsa waje

"Eh mana....." Ta amsa masa a taqaice.

"Yes!" Ya sake fadi da wani irin dadi yana mamayarsa

"Indai haka ne kiyimin proving mana......"

"Kamar?" Ta jefa masa tambayar da zazzaqar muryartan nan,don wajen da takeso azo
kenan tana tunanin kuma ana gab da zuwa din,saidai ita ba zata iya requesting ba
har sai ya nema da kanshi

"Mu hadu yau.......don Allah kada kicemin aah". Shuru tayi cikin salon jan
aji,kaman bataso

"Please mana.....please,kice to" Ya fadi murya a raunane cike da fatan samun
amincewarta

"Shikenan"

"Oh god......" Ya sake fadi yana dukan kujera da hannunsa,yana kuma ji duk duniya
ba wani d'a namiji da yakaishi sa'a yau dai a duniya. Yana nashi bidirin amma nata
qasan zuciyar a quntace. Wani mugun tsanarshi take ji da haushinsa. Da gaske wannan
din dabi'arsa ce bazai kuma taba canzawa ba,ko shin mata nawa ya lalata da kalar
wannan mummunar dabi'ar tasa?.

"Bansan da wanne irin yare zan gode miki ba....amma zakiga godiya a aikace har
saikin rasa da meye zaki maye min gurbin hidimata a gareki......tabbas zan ninka
darajarki.....zan daukaka martabarki a idanun duniya......zan maidake tauraruwa
cikin mata....zan miki ado da gold irin adon da sai 'yar gata...."

"Thank you......thanks" Kawai tace dashi don tanaso ya dakata daga zubo wannan
dogon sharhin nasa. Tana tausaya masa a daren yau irin barnar da zatayi masa,ta
tabbatar wadannan maganganun da yake jerowa a yanzu saisun koma sumbatu.
"Zan shiga company akwai lissafin da zamuyi da boss dina.....duk inda la'asar yayi
koda bamu gama ba zan dauki excuse......zan kama mana daki a Bristol,zan tura miki
details da komai da komai".

Baki ta tabe tana jin wani haushi yana cikata. A daren yau bashi
ba,hatta da boss din nasa saita sakasu a lissafin da babu fita. Tanaji a jikinsa ma
shi da boss din basa zaiyi wahala idan ba zamuje ta tadda muje mu ba. A yadda yakan
bata labarinsa lokaci bayan lokaci......irin kudaden da yake wasa dasu da kuma
shekarunsa talatin da bakwai a duniya amma ace ba macen aure?,to idan ba sheqe
ayarsa yakeyi ba me yakeyi kenan?.

Ture wannan tunanin tayi daga zuciyarta don a halin yanzu bashi da
amfani,abu guda daya ta sani ba sassauci,kuma a yau din takeso mika'il ya zama
tarihi cikin rayuwarta,shi kuma ta bashi darasin da zai sanya rayuwarsa tayi laushi
da kyau.

"Ba laifi...." Ta amsa mass,bata kuma jira cewarsa ba ta dora

"Ina fata kasan rule din.....zaka rigani isa gurin da wasu mintuna......kuma bana
buqatar kowa yasan muna tare ne da kai"

"Dukka dokoki da qa'idojinki kisa a ranki an gamasu......ranki ya dade.....da zaki
bani dama da kin fadi inda zan aiko driver ya daukomin ke.....don bana buqatar kiyi
wahala" . Wani sirrintaccen murmushi ta saki

"Na maka uzuri saboda baka jima cikin rayuwata ba bare ka fahimci wacece
ni......zanzo da kaina,bana buqatar kowanne driver"

"As you wish.....saidai zan saka kudin transportation.......please karkice min aah"
Idanunta ta lumshe sannan ta budesu,har ta fara gajiya da dogon hirarsa

"Alright....byee" Ta furta a taqaice tana tsinke wayar.

Ajiyeta tayi gefe tana furzar da iska daga bakinta. Inda ace dukka haka
mazan aure suke ba shakka a jiya da kunnuwanta basu jiye mata abinda taji ba saman
dogon layin masu lalurar ciwon zuciya dake dakon ganin likita......tabbas da
idanunta basu gane matan auren da hawan jinin bacin rai da baqincikin d'a namiji ya
jefa musu hawan jinin daya juye musu zuwa ciwon zuciya ba......da bataga matar data
yanke jiki a wajen ta fadi ba......wadda daga qarshenta gawarta aka fitar a
asibitin 'yaruwata na kuka dukka sanadin baqinciki namiji.

Ita kuwa me zatayi da aure?......wanne tsautsayi ne zai kaita damqa
rayuwarta hannun d'a namiji guda daya yayita hajijiya da rayuwarta ba gaira ba
dalili?.

Abubuwan data gani din dasu ta kwana,su suka yita yiwa kunnuwa da
idanuwanta gizo,kuma suka hanata komawa duba ayshatu.....suka kuma sanyata jin ta
matsu ta kora mika'il mashkur harma da ya'aqoub din daga rayuwarta gaba daya.

Kafin tabar wajen taji alamun shigowar saqo. Koda ta duba alert ne daga
banki da sunan mika'il wanda ya sanya mata 1mil a matsayin kudin mota kawai. Ta
juya wayar a hannunta,ta sake juyata,sai kuma ta saki siririn tsaki tana ajeta a
gefe.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*
PAGE 67


Kamar kowanne lokaci,yakanyi breakfast dinsa ne a sassansa,saboda duk
wani abu da zaiyi breakfast dashi yasha banban da cimar mutanen gidan. Wannan ya
sanya ya aje cook dinsa daban wanda yasan tsare tsare na cimarsa. Koda a ranar
baida ra'ayin cin abincin cikin gidan,nashi cook din zai masa irin abincin da yayi
dai dai da ra'ayinsa,zai shiga ne kawai ya taya anni zaman cin abincin.

Yau din ranar litinin ne daya tsara abubuwa da yawa da zaiyin. Bakwai
da mituna goma sha shida ya murza handle na bedroom dinsa ya soma takowa a nutse
zuwa ainihin parlor dinsa.

Yayi wani sassanyan kyau cikin tsadajjen yadin Qiviut fabric me
tsananin taushi da kuma rashin nauyi,daya daga cikin favourite yadiddikansa duk da
tsadar da suke dashi amma baya jin wannan. Metro blue ne da yayi matuqar haska
fatarshi,ya kuma fidda sura haiba da cikar kamalarshi.

Fuskan nan a dinke kaman ko yaushe,wanda kusan duka safiya anni ko abba
ne ke jefa murmushi a kanta,sai kuma fitinannenshi farouq musamman idan a sassan ya
kwana,to fa kafin su rabu kowa ya wuce wajen aikinsa sai ya addabeshi har ya zare
wannan yanayin daga kan fuskarsa din..

Yau din budadden takalmi ya sanya,abinda ya bawa zara zaran yatsunsa
daman fitowa kenan cif da cif cikin takalmin da ya soma zareshi daga qafansa sanda
ya iso dining area dinsa.

"Good morning sir" Cook din nasa daya kasance yaren igala ya furta cikin girmamawa
yana rusunawa

"Morning ameh.....how are you?" Yana jan kujera zai zauna

"Fine sir...." Ya amsa masa yana matsowa da sauri gami da kama aikinsa na serving
nasa komai. Wannan kuma shine ya bashi daman duba wayarsa da yaji tana
vibration,wanda kusan koda yaushe idan zai kwanta bacci yana barinta ne a hakan
gudun takura.

Sunan daya gani ya sakashi dan furzar da iska kadan daga bakinsa. Duk
da cewa a yadda suka rabu jiya bayajin yau zata kira ta assasa wata matsalar ko
damuwar,shidai baisan me yasa duk sanda zaiga kiranta hakanan ba sai wani abu ya
tsirga masa ba.

Daidai sanda Ameh yake barin gurin ya daga wayar,ya ajeta daga gefansa
bayan ya sakata a handsfree yana jawo mug din da ya zuba masa dafaffiyar madarar da
aka watsa mata turmeric guda guda,wannan yadan sauya mata kala zuwa yellow kadan.

"Barka da asuba" Ya fadi cikin nutsuwar nan tasa. Murmushi ta saki daga daya
sashen,cikin son nuna zallar kulawa tace masa

"Barka kadai.....kira nayi naji lafiyar d'ana ya ya tashi?,na kira dan uwanka
wayarshi a kashe,ina fatan komai lafiya?" Kaman ko yaushe,duk wani motsi nata yana
masa banbarakwai,yanzun ma haka ne,sai ya aje mug din yana hade hannayensa waje
daya

"Mun tashi lpy alhmdlh.....da fatan kema haka......musaddiq ban fita cikin gidan ba
tukunna,bamu hadu dashi ba". Fuska tadan yamutse,amma bata bari sautin muryarta ya
canza ba
"To yayi ba damuwa.....amma ya kamata dai ace kasan kwananshi da
tashinsa......banason yadda kuke nesa nesa da juna fa?".

Sai yaji maganar kamar ta saukar da murmushi cikin zuciyarsa,murmushin
dake nannade da mamaki,amma sai ya basar

"In sha Allah"

"To hakan yayi.....nace ba?" Ta fada don janyo hankalinsa

"Ina tare dake maamah" Ya amsa mata tana duba agogon hannunsa da kuma qaramar wayar
dake ajiye a gefe,wanda kiran saddiq yake shigowa

"Cewa nayi bari nayi muku tuni,dinner by 8pm yau......ina fatan zaku cikamin burina
na kasancewa tare daku duk dare?". Idanunsa ya sake lumshewa,tsananin rashin
gamsuwa da tsarij yana tsarga masa. Da can da waye da waye taci gaba da kasancewa
duk daren a sanda ta tattarasu ta baiwa duniya kyautarsu?. Bayajin a stage din da
ake kai yanzun zai yarda da ita ko ya gasgatata. Furucinta da kuma alaqarta da
hajja harira ba zasu taba barin zuciyarsa ta nutsu da ita ba

"Okay.....we will be there in sha Allah"

"To yayi na gode.....sai na ganku" Ta fadi tana yanke kiran. Wayar yabi da
kallo,har tayi maganar da tafi damunta,ta fadi kuma dalilin da ya sanya ta kirashi
suka kammala wayar baiji addu'a guda daya daga bakinta ba.

Yaja numfashi me nauyi yakaishi xuwa cikinsa,ya tabbatar babu yadda
za'ayi anni ta kirashi......walau yana qasar nan ko yana wata qasa su kammala
maganar su bata bishi da kyawawan addu'o'in da ko yaushe yake jinsu har cikin
tsakiyar zuciyarsa ba. Addu'a da tsaftaccen niyya da kuma manufa na alkhairi.

Hasken wayar ya sanyashi maida dubansa gareta,sai ya daga itama ya
sakata a handsfree yana sake janyo mug dinsa yaci gaba da kurba

"Saura mintuna goma lokaci ya cika hamma"

"Gani nan......Moses ya qaraso?" Ya tambayeshi yana bude daya plate din dake
gabansa

"Muna tare dashi"

"Okay.....get ready" Ya fada yana katse kiran tun kafin saddiq din ya katse nasa.

Kamar kowacce safiya,ya shiga wajen annin cikin nutsuwa mutuntawa da
kuma qaunar daya tabbatar daga ubangiji take....irin qaunar da yayi imanin Allah ne
ke sanyata cikin zukatan bayinsa aduk sanda yakeso. Ta gyara lullubin laffayarta
tana masa addu'a,addu'ar data sanya rauni me yawa a zuciyarsa,raunin da yaso nunawa
har sanda yake cikin motar da dagashi sai saddiq sai driver,sauran guards suna
gabansa wasu a bayansa cikin wata motar ta daban.

Wacce irin rayuwa ce hakan wai?,wanda zai hafoka daban?,wanda zai gina
maka rayuwa da kyakkyawan fata da kuma addu'o'i daban?. Wannan shine abinda ya
dinga yi masa yawo akai,har daga qarshe ya samu ya yakice komai a ransa kafin su
isa kamfanin.

Kamar kowanne lokaci isowarsa cikin kamfanin kadai yakan sanya kowa
shiga hankalinsa. Hakan kuma yana da nasaba da rashin daukan wasansa da yadda yake
daukan komai da muhimmanci. Wannan ya sanya duk wanda ke aiki dashi

Please Login or Register in order to submit comment