You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gabbansa suna daukan dumi
kafin daga baya kuma suyi wani irin sanyi kaman ba'a jikinsa suke ba.

_mrs muhammad fu'ad jadda sabreen ahmad_.

Baya jin idanunsa zasu iya ci gaba da kallon abinda ke gabansa,sai
kawai ya hade newspapers din waje daya ya curesu a hannunsa yana takawa zuwa cikin
gidan ba tare daya tsaya tuna cewa magana suke da farouq ba,kuma yabar farouq din
akan line na waya.

Shuuuu din da farouq yakeji ya sanyashi qarfafa zarginsa akwai abinda
ya faru,sai kawai ya aje wayar ba tare daya kasheta ba,ya tada motar da wani irin
hanzari wanda yanayin gaggawar da security na gidan suka ga yanayi ya sakasu dage
masa qofa ya fice tun bai qaraso ba.

Bazaice ga wani abu da ya faru daga sanda yakai kansa samansa ba
banda azababben ciwon kai da yake masa kutufo kota ina. Ba abinda bakinsa ke
furtawa sai Astgafirullah yana me kyautata zaton akwai wani abu daya aikatawa
ubangiji wanda ba daidai ba shi yasa ya jarabceshi da wadannan abubuwan. Dukka
komai akan yarinya daya?.......yarinyar da koda ta zame masa zabi a nasa qashin kan
hakan ba lallai ya tabbataba banda miqewa da kafewar maamah akan lamarin?.

Da qyar ya iya amsa sallamar farouq sanda ya bude smart door din ya
qaraso cikin parlor din idanunsa akan fu'ad. A yadda yaga idanunsa sun jirkita ya
tabbatar labarin ya gama ruskarsa.

Da idanu yabi farouq din,har zuwa sanda ya qaraso,ya tsugunna ya debi
duqunqunannun jaridun ya bude ya kuma rufesu a take.

"Da gayya aka buga wannan news din......."

"To menene qaryar da sukayi a ciki?.....ban karanta sauran labarinta a qasa da suka
saka ba.......amma wanne ne qarya farouq?" Maida dubansa yayi kan fu'ad da yake
dubansa kai tsaye. A zahiri jijiyoyin kansa ke tashi sosai har sun nuna ta farar
fatarsa,wanda abadini yake nuna ciwon kai yakeyi sosai,irin ciwon kan da ya dinga
addaba masa sanda yake fama da matsalar depression dinsa,wanda ya tabbatar ya jima
rabonsa dashi.....

Sakin baki yayi yana kallon fu'ad din daya fara magana cikin sanyi
saidai akwai zafi me yawa a kalamansa.
"Stop dude.....ina gaya maka.....don't judge book by his cover.........ka daina
judging mutane haka"

"Judging nasu nake ma?,bayan ina da full details na evidence akan duk maganan da
nakeyi farouq akan yarinyar?" Yayi maganan da sanyin dai,amma lafuzzansa na nuna
zallar zafin da yakeji.

"Evidence kadai bazasu tabbatar da hakan ba.......kayi managing personal boundaries
tsakaninku kaman na kowanne miji da mata,akwai buqatar wani sensitive......"

"Haba mana!" Fu'ad da yakeji zuciyarsa na matsewa kaman zata fashe ya tsaida farouq
yana zama sosai yana jin jiri daga inda yake zaunen.

"Kada bakinka yakai nan wajen.......bakasan wacece ita bane farouq?,bakasan sunan
da kowa yake kiranta dashi ba?,baka gani jikin newspapers ba?"

"Na gani.....na kuma sani......kuma ka rigani sanin haka kace zaka daukota ka
gyarata......ya akayi ka kasa fu'ad?" Ya jefa masa tambayar yana riqe habarsa.
Kansa ya jijjiga sosai yana duban farouq

"Ban kasa ba......bazan kuma kasa ba......abu daya kemin burki.....duk sanda na
kalleta sai naji tayi qanqanta da yawa nayi mata kalar azabobin dana tanadar
mata......tayi mitsitsiya na sanyata a prison din dana shirya mata......amma duk
sanda ta aikata wani abu kota bullo da wani abun........sai naga nine naketa
kuskuren kallon tayi qanqanta......a abinda zuciyata ke rayamin wannan
karon......duk hukuncin da yazo na dauka a kanta a tunanina na qarshe dashi zanyi
amfani......"

"Banda divorcee......"

"Harda shi idan ta kama" Ya fada confidently.

Ido Farooq ya zuba masa kawai,ga mamakin fu'ad sai yaga ya saki wani
irin murmushi yana girgiza kai. Shima duban farouq din yake kafin yaji murmushinsa
ya bata masa rai. Bayajin a yanayin da yake ciki ya kamata wani abu me kama da
murmushi ya fita a fuskan farouq,don haka ya miqe tsam yana dosar bedroom dinsa. Da
hanzari farouq ya miqe yana kiransa

"Wait dude.....wait" Don ya tabbatar wannan bedroom din nasa me smart door idan ya
shiga ya rufe baka isa ka bude ba muddin bai sakaka cikin wadanda zasu iya budeta
ba. Bai saurareshi ba ya shige dakin abinsa,da qarfi ya rufe qofar yabar farouq a
nan a tsaye. A yanzun da baya ganinsa sai murmushinsa ya ninka na dazu,bayan minti
uku yayi qoqarin daidaita kansa,ya matsa yana daukan telephone na falo din ya kira
cikin dakin nasa.

Yayita kira yana jiyota tana ringing,kaman bazai daga ba kafin ya daga
daga baya,ya sakata a kunne ba tare da yace komai ba.

"Am really sorry dude.....na hango wani abu ne daban da yake durfafoka da matuqar
qarfi fiye da qarfin guguwa......amma it seems like baka ganshi ba baka kuma
fahimceshi ba......anyways kayi aiki da hankalinka da intelligent dinnan dana sanka
dashi.......am always free,and then it's time to act for koma waye behind all these
issues......na tabbatar akwai wani abu boyayye......think wisely......am always by
your side.....take a rest,but please kasha magani".

Sanyaya ranshi sosai maganganun farouq sukayi,yayi shuru kawai yana
saurarenshi bai iya ce masa komai ba......shi kansa baisan me yasa a bangaren nan
kaman qwalqwalwarsa bata iya aiki daidai ba?. Yana jin kamar ya gaji......yana
buqatar hutu da gaske na jiki dana kwanya
"Am tired farouq......I'm feeling burnt,i need some time to unwind and focus on my
well-being......kayi magana da saddiq.....i want him to schedule my annual leave
cikin kwana uku".

"Kowa ma lokacin hutunsa yazo......International gateway to Maldives" Ya furta yana
motsa labbansa gami da jefa hannunsa sama yana kwatanta yadda jirgi yake cillawa
sama yayin daya cirata daga qasa.

"Zan kawo nesa zuwa kusa......zan dawo da mafarki zuwa gaskiya......komai zai
warware.....zan kuma baka mamakin yadda zan juya maka rayuwarka dare daya" Farouq
ya fada yana dariya kaman mummunan abu irin wannan bai faru ba.

Kawai wani nishadi yakeji qasan ransa idan yayi imagination na yadda
komai zai kasance,sai yaji kawai ya qagu shi Kansa lokacin yayi,sai ya juya ya
tattare key da wayarsa yana maidawa aljihu ya soma sauka yana barin gidan,ko saddiq
dinma bazai nema ba.....shi zai shirya komai,sai komai din ya kammala sannan kowa
yaji ya gani.

*_tom......me karatu?,wanne plan kake tunanin farouq yana dashi akan fu'ad?,muje
zuwa_*


Yana driving a mota amma tunani fal kanshi. Tunda yake bai taba hangen wani
abu daya jigata fu'ad komai tsananinsa ba kaman wannan......anya ba burbushin
wannan halittar daya tsirowa zuciyarsa kuwa?, wadda kusan itace jigo na kowanne
tsanani da wahala da zuciya kan iya shiga akan wani dan adam?.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 64


64



Bayason irin fushin da yakeji cikin ruhinsa da jikinsa gaba
daya......yana buqatar yayi cooling down ko yaya ne,a lokacin ayar nan da taxo
cikin alqur'ani me girma ta fado masa

"Ku saurara.......da ambaton Allah kadai zukata ke samun nutsuwa"

"Sadaqallahul azeem" Ya fadi yana miqewa hadi da fara jin sassauci daga tuna ayar
kawai.

Toilet dinsa ya shiga,ya daura alwala me kyau,sannan ya dawo cikin
dakin yana kunna chandelier din dake kafe tsakiyar dakin,wadda ke hade da Bluetooth
da kuma fanka me bada sassanyan iskar data banbanta data sauran fankoki. Remote ya
dauka ya kashe hasken don baya buqatarsa,ya kuma kunna speaker din dake jiki yana
daidaitata da wayarss,take muryar fasihin malamin nan limamin ka'aba wato sheik
abdurrahman assudais ta karade dakin cikin sauti mafi tsarki na karatun alqur'ani.

Relaxing yayi sosai soman sofa din dake dakin yana jin wani sukuni ya
soma ratsahi,kaf a cikin malamai idan akwai wani sauti da yafi so yafi qauna bazai
wuce sautin sheik abdurrahman assudais ba,wannan dalilin yaja ra'ayinsa qira'arsa
gaba daya ta juye zuwa ta sudais din sak.....da wannan qira'ar yayi sauka,kuma har
yau itace a bakinsa.

Idanunsa a lumshe yana ci gaba da bin sautin,bazaice yana jin yunwa ba
ko kadan,zamansa a haka duk duniya yafi komai yi masa dadi,a haka ya shafe kusan
awanni biyu har zuwa sanda wayarsa tayi haske,kira kuma ya shigo wayar tasa.

Hannu ya sanya ya jawo yana dubawa,ganin me kiran ya sakashi daukan
remote din dake gefansa,ya kashe volume din gaba daya sannan ya daga wayar yana
sakata a hands free.

"Good afternoon sir......yanzu haka dukka shugabannin gidan jaridan suna hannunmu".
Zamanshi sosai ya gyara cikin kujerar yana harde qafafunsa waje daya

"Well-done,good job khaleed,akaiminsu housing estate na darmanawa.......by 4 zan
fito in sha Allah"

"Yes sir" Ya fada cikin tsananin nuna ladabi,bai sake jiran komai daga wajensa ba
ya kashe wayar yana ajeta gefe. Bai sake batawa kansa rai da tunani ba ya dauki
remote din da xummar qara volume din,cikin ransa yana jin bazai sake barin komai ya
bata ranshi har haka ba......ko meye ya faru da ita ita ta jawo......amma fa bazai
taba lamunta a taba masa igiyar aure ba,ko kuma sunansa ya fito a ciki ba ko na
ahalinsa.

Wani kiran ne ya sake shigowa dole ya aje remote din. Asp ne yake
kiran,shima bai jinkiri ba ya daga.

"Sir........mun sama musu gurin ajiya na musamman......kuma zamu tuhumesu da kyau
har sai sun fadi gaskiyar wanda ya aikosu".

"Na gode......but inaso ku barmin wannan a hannuna......ku ajiyesun irin ajiyar
data dace dasu har xuwa sanda zasu furta wanda ya basu hanya da daman shigowar"

"Okay boss...."

"Thank you" Ya sake fadi labbansa suna motsawa.

Wannan bacin ran da yaketa son hadiyewa still dai ya sake taso
masa,ya sanya hannunsa ya shafi kansa. Zai iya cewa tun daga guards dinsa zuwa
securities dinsa amintattu ne,bashi da ko kwanto da ko shakka akan koda mutum daya
daga ciki,duk da dan adam tara yake bai cika goma ba......kuma wasu daga cikin 'yan
adam din masu iya canzawa ne a duk sanda sukaso a karan kansu,walau dalili na son
zuciya ko makamancin hakan......amma su kam yayi imanin yadda yake mu'amalantarsu
daban yake da sauran yadda masu gida ke mu'amala da yaran gidansu. Kyautatawarsa a
garesu ta daban ce kaman yadda qaunarsu a gareshi ta daban ce. To amma a yanzun
yadda yakejin zuciyarsa komai ma yana iya faruwa......sannan a yadda yasan ya
gidansa yake,abune me wahala a iya keta tsaron gidan a shigo haka siddan ba tare da
idon sani ko mataimaki sannanne ba.

Volume dinsa ya qaro yana fatan sake samun nutsuwa da daidaituwar zuciyar
da zata bashi qwarin gwiwar fita zuwa yammacin. Bai tashi ba sai da akayi sallar
azahar,ya daura alwala ya fito don halartar jam'in sallah kaman yadda ya saba
muddin yana kusa da masallaci.

Dukkanin ma'aikatan kowa rabe rabe ya dinga yi daga ganin fitowarsa.
Zukatansu a razane yake abinda ya sanya gidan ya sake daukan shuru gaba daya kamar
ba wata halitta a gidan me rai da tayi saura.

Bai dawo cikin gidan ba sai la'asar,don ganinsa yau free haka da rana
ya sanya masu buqata suka dinga shigowa masallacin. Bai hanasu ba ya zauna ya dinga
sauraren kokensu daya bayan daya. Ba wanda ya bari ya tashi a wajen ba tare da
gaggwaban abun alkhairi ba,jordan na tare dashi shi ya tashi sauraronsu,sukayi
la'asar ya miqe ya wuce gida qirjinsa cike da nauyi. Sai yake sake ganin yadda
ubangiji ke tsara rayuwa yadda yaso.......matsalar wani bata wani ba......a yadda
unguwar take baiyi zaton masu qaramin qarfi dake neman taimako na shawagi a cikinta
ba. Ya dubi kansa sanda yake wucewa ta babban glass door din da zaka taras a gate
din farko na gidan. Ubangiji ya azurtashi da dukiya me yawan gaske......lafiya da
wadata......saidai ya samu naqasu ta bangaren uwa da mace ta gari,wanda wadannan
abubuwa biyun sune jigo a rayuwar kowanne dan adam. Ga wasu can su kuma nasu burin
shine INAMA MUNE ME JADDA?,ba tare da sunsan ainihin waye me jaddan ba?,me yake
fuskanta?,wacce rayuwa take going through......(wannan ya zamana izina a garemu
gaba daya,kafin kayi burin inama kaine wane?,kayi tunanin mene rayuwarsa ta
badini?,kayi tunanin wadanne qayoyi ya tattaka da tsinika kafin yakai ga isowa nan
inda yake?,ko yaushe idan kaga wani mutum da rayuwarsa ke burgeka,ma roqa Allah ta
hanya daban bata hanyar Allah yasa na zama kaman wane ba.....bayan fuskar wane
dinnan kawai kake gani bakasan cikinsa ya yake ba,Allah ka kyautata rayuwarmu,ka
bamu tsira duniya da lahira)"

Da tarin tunane tunane yake ratsowa falon daya xama wani irin shuru.
Gaba daya kallon gidan yake wani iri,har a gangar jikinsa yakejin ya gaji da xaman
cikinsa. Wuf ya hangi gilmawarta daga kitchen kaman zata kifa tana nufar qofarsu.
Har yaci gaba da tafiya wani abu ya sauko cikin tunaninsa

"Ke!" Yayi kiranta da wani amon sauti da a take ya tara zazzafar gudawa cikin
tumbinta

"Na'am......na'am ranka ya dade" Zuwaira ta fada wadda ke rungume da wani abu da
baisan meye ba. Hannuwansa ya zube cikin aljihun wandonsa yana qare mata
kallo,zuciyarsa tana raya masa wani abu game da ita. Wani abu me kama da xargi
tuhuma da kuma rashin aminci a kanta yaji yana tsarga masa. Irin kallon jadda din
ba kowanne mutum ke iya jurarsa ba,sai mutum me babbar kurwa,me babbar kurwar ma
wanda ya cika da gaskiya da kuma amana,ba wani ha'inci cikin lamarinsa,wannan ya
sanya zuwaira ta dinga jin kamar yana karance duk wani sirri dake tattare a
qirjinta zuwa cikinta,tamkar ya sanya microscope yana tantance adadin qulla qulla
da harqallar data taba shiryawa tsahon rayuwarta,wannan ya qarawa adadin zuciyarta
gudu,ya kuma hanata ci gaba da daidaituwa akan qafafunta,saita sulale ta duqa saman
qafafunta

"Allah ya taimaka.....tuba nake,bansan kana cikin gidan ba ai......da ba'a fito
ba,wannana bun daya faru ranka ya dade shine ya hanani nutsuwa.......hajiya naketa
son dubawa aga yanayin da take ciki....."

"Ke" Ya sake kiranta yana dage dukka girarsa sama guda biyun.

"Na'am yallabai na'am......."

"Ki tarkata komai naki kibar gidannan cikin qasa da minti goma....."

"To an gama ranka ya dade,aisai a komawa hajiya maamah baya goya marayu" Ta furta
tana jin wani sassauci da rangwame a ruhinta. A abinda takeji yanzun sallamarta
shine babban gatan da yayi mata,duk sanda taji muryarsa sai kowacce kafa ta jikinta
ta jiqe da gumi. Sai a yanxu take ganin cewa da gaske xaman gidan jadda yafi
qarfinta,wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa. A baya tana tunanin duk randa yace taje
ya sallameta zataji tashin hankali maras iyaka......amma a yau sai takejin kamar
'yanci ne daga bata zuwa zamowa halastaccen d'a.

"Kinsan me?" Ya fada yana sake dubanta,saita dakata tana saurarensa.

"Bazan dubi tsufanki ko digon furfura koda qwaya daya dake tsakiyar kanki
ba......muddin naxo na sameki kin koma gifan gidan maamah........ki tabbatar daga
ranar kin tashi daga aiki......kiyi nesa da ita da komai da kowa daya
danganceta.....and hakan bawai xai sakaki kin tsira ba,duk mutumin da yake gidan
nan daga kwana uku baya zuwa jiya da abin ya faru baxai tsira ba a waje
na......wanda kawai zai tsira shine MAI GASKIYA ". Duburbucewa tayi har akwatin
kayan asirin maamah na shirin tarwatsewa daga hannunta. Gab gab gab haka hannuwanta
da qafafunta suka dinga haduwa waje daya,wannan wanne irin kalar tashin hankali
ne?,wanne irin yaro ne wannan maras imani.... Lallai dole mallakarsa ta yiwa mariya
wahala,zuwaira ta furta hakan a ranta sanda take ta qoqarin kai kanta ga sassansu
don ta samu ta sulale kaman yadda ya shawarceta. Ayadda ta sanshi tana ganin ko
cinye namanka yace zaiyi zai iya......musamman shi daya mallaki masu gidan ranar da
babu me tuhumarsa ko bin ba'asin abinda yayin.

Gaba daya wunin yau duka hankalinta yana kan wayoyinta,bama ita
ba.....hatta da fareeda kowanne motsi nata yake kan social media's tana hasashen
watsuwar abun a kowacce kafan sada zumunta. Sanda taga ankai azahar shuru sai duk
wata nutsuwa ta soma barin gangar jikinta,hankalinta ya gaza kwanciya kwata
kwata,ta kuma shirya kai tsaye ta kira driver ya dauketa zuwa gidan maamah.

A sannan ita dinma duban wayar take tayi.......tanaso ta samu wani
haske ko yaya yake.......tunda ta zauna take saqa yadda komai zai
kasance.......take qiyasta irin tozarcin da zata yiwa sabreen. Lallai sai ta
sanyata ta fahimci wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa.......ita kanta batasan adadin
yawan tozarci da qasqancin da zata sanyata ta fuskanta ba.

Mamakinta ya tsananta ainun da rashin samun kai,sai taji ta kasa
jira,kai tsaye ta daga waya don kiran fareeda,amma sai fareedan ta hutashe da ita
saboda turo qofan setting room din da tayi ta shigo tana taunar chewing gum kaman
yadda ya zame mata al'ada,duk kuwa da cewa yau din bata cikin wannan mode din,amma
cin chewing gum din ya zame mata dabi'a.

"Ke nake shirin kira yanzun.......banga tasirin aikinki ko wani motsi na daban ba"
Maamah din ta furta kanta tsaye tana duban idanun fareeda. Idanu tadan xubawa
maamah din,mamakin dabi'arta tana dan kamata. Kanta tsaye take magana akan duk wani
abu daya shafi buqatarta,ba ruwanta da wata matsalarka ko fuskantar yanayin da kake
ciki.

Kanta ta dauke tana qarasowa ciki,sannan ta yiwa kanta mazauni saman
hannun sofa din tana harde hannuwanta a qirjinta

"Wannan shine aiki mafi kashe kudi da nayi......sannan shine aiki mafi jinkirin
samun nasara" Tayi maganar tana duban maamah din.

"Masu aiki sun kammala.......naki aikin da nawa duka ba wanda ya kawo result me
kyau........abu daya ya rage shine,ki kira d'anki ki tuntubi sakamako daga
gareshi". Gyara zamanta maamah tayi tana duban fareeda,ta soma fahimtar wasu
halayenta da inda dabi'unta suka sanya gaba,bata gayawa fareeda tayi failing a nata
agenda din ba.....ya akayi amma ta sani?.

"Na yarda har abada yaro yaro ne.......kina tunanin samun galaba akan duk wani
lamari daya shafi fu'ad abune me sauqi?,inda kuwa hakanne da bakizo gabana
ba......da babu ke cikin babin qaddararmu sam sam" Maamah ta fadi tana duban
fareeda.

"Duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau bishiyar rimi bazai hango ba..........a
naki lisssafin kiran fu'ad kai tsaye na jefeshi da salon tambayoyinki abune me
sauqi da zai sanya mu wanye lafiya?" Ta qarasa maganar tana duban fareeda data
zubawa maamah nata idanun.

"Kina iya kiransa ta wata siga daban ki kuma zaqulo bayanan da kikeso......amma
zai zama babban kuskuren rayuwarki ki biyo masa ta waccan hanyar taki....."

"Amma bisa alqawari da yarjejeniya.......xaki zama tsanina na mallakar fu'ad haka
ne?"

"Har yanxu ina kan wannan bakan.......amma fidda sabreen daga gidansa aikinki
ne......zai iya zama nawa aikin,amma kuma salon aikin nan da yake zamowa ba waji
bi". Sun jima suna kallon kallo tsakaninsu,kowanne da kalar saqar dake cikin
zuciyarsa game da dan uwansa,kafin fareeda ta fiddo wayar da musamman saboda kiran
fuad din ta tanadeta. Da kowacce waya da kuma kowanne layi ta kirashi ba zata
sameshi ba saida wannan wayar kadai.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 65


65


_Manzon Allah S A W bai taba aibata abinci ba,idan ya burgeshi sai yaci,idan kuma
baiyi masa ba sai ya qyaleshi(ba tare daya aibatashi ba)_



Tsaf ya shirya cikin trouser dark blue na yadin vicuna,yayin da sanya
black shirt data fidda ainihin kan sassalkar fatar nan tasa me tsananin haske,wadda
ta cakuda da hutu da jin dadin dake bayyana kansa cikin kowanne hali yake.
Kyakkyawar qasumbar fuskarsa da bata da cika irin ta cukus ta sake qawata fuskarsa
da sanya masa kwarjini,tana da santsi kwatankwacin sumar dake lullube saman kansa.
Baqa ce sidik kaman gashin girarsa dana idanunsa,hakanan kaman sauran gargasar dake
lullube da sassan jikinsa. Agogo fata ya daura a tsintsiyar hannunsa me tsananin
tsada daya dace da shigarsa dama tsadar kayan jikinsa,yabi ko ina na jikinsa ya
feshe da lallausan turaren nan nasa me taushin qamshi.

Tsananin dauriya kawai ta sanyawa ruhinta,tun bayan dawowar amna da
batakai magarib ba kaman yadda anni tace taketa qoqarin shimfida walwala akan
fuskarta,duk da cewa abun ba haka yake ba daga qasan zuciyartata. Amna din ta
dabance,tana da barkwanci da sakin jiki ga duk wanda ta yarda dashi,wannan ya sanya
cikin qasa da awa guda taji nauyin dake qirjinta yana raguwa,lokaci lokaci labarun
amnan suna sake dauke hankalinta daga yanayin da take ji.

Ita ta tilastata da yammacin kan su fito daga daki zuwa kitchen

"Wainan fulawa nake sha'awa.......yakumbo ce take mana,ta tafi ganin gida tun
wancan satin,muje na gwada ko zan iya please adda" Ba zata iya qin tankwabar da
tayinta ba,haka ta maqala hijab saman doguwar rigarta ta bita kitchen din,wanda a
qarshe sabreen dince ta hada Mata wainar ta soya mata ta kuma tara mata a warmers.
Ta cika da mamakin yadda akayi amnan ta iya girki kala kala amma bata iya wainar
fulawa ba. Qwarewar amnan a girki yana bata sha'awa,harma takanji tana sha'awa
itama iya kalolin abinciccika.

Suna a saman dining tana kallon yadda amnan ke santin wainar
fulawan,time to time tana murmushi kawai. Ta sake yarda da gaske rayuwa mataki
mataki ce,kowanne da kuma kalar muhalli da hurbin data ajeshi.

Duk da fiye da rabin hankalinta bashi a wajen,amma hakan ba hanata jin
saukowarsa ba a jikinta. Qamshin turarensa ne ya fara isa ga hancinta,kafin daga
bisani qamshin ya fara mamaye parlor din.

Cikin dabara ta dauke duban ta daga wajen da yake takowa,tanason nuna sam
sam ma bata ganshi ba. Duk sanda fuskarsa zai bayyana a gareta,ba abinda yake tuna
mata sai tambayoyinsan nan data tsana,tambayoyin dake matuqar qona masa rai ba
kadan ba.

"Hamma......barka da yamma" Amna ta furta da murmushi saman fuskarta sanda ta
waiwaya ta ganshi,sai ta aje wayar hannunta tana bashi hankalinta gaba daya

"Barks lovey dovey" Yayi maganar da wani kwantaccen sauti daya sanya sabreen taji
tsigar jikinta ya zuba,take kuma ta daga kanta a hankali kaman me tsoron ganin wani
abun tsoro,duk yadda taso ta yiwa idanunta shamaki amma sai da suka fada kan
fuskarsa,ta kuma ci karo da wani yanayi dake shimfide saman fuskarsa din. Shi ba
murmushi ba sannan kuma ba'a daure fuskar take ba......saidai yana yin ya nuna ya
zama very calm ba kaman yadda take ganinsa kwanakin da duka wadannan abubuwan suka
faru ba.

Zamewa amna tayi tana sake gaidashi bayan gaisuwar daxu,ya amsa yana
motsawa alamun xai wuce. Wayarsa dake riqe a hannunsa ta fara bada wani sassanyan
sautin sarewa maras hayaniya da yawa,kafin daga bisani sunan FAREEDA KHALED
MUSTAPHA ya fita tarwai ta cikin speaker din. Duk yadda taso watsar da sunan daga
cikin kunnuwanta amma hakan ya gagara. Sunane data jima tana jinsa akai akai,har
kuma ya soma zama a kwanyartata. Maida hankalinta tayi ga amna amma saita gaza ci
gaba da hakan,batasan yadda akayi idanunta suka dauketa zuwa fuskarsa ba. Wayar ya
daga zuwa fuskarshi yana duban me kiran,sosai ya zubawa numbers din nata
idanu,manhajar daya dora kan wayar tasa ke harbawa daga gefan hagu na wayar tana
nuna masa abinda fareeda din ke aiki dashi wanda ke fasa duk wani shinge da zai
saka number dinta,duk sanda ta jira kiran ya samu damar isowar gareshi kai tsaye.
Dan qaramin murmushi ya subuce masa wanda iyakacinsa labbansa,saidai a nata idanun
qaruwar murmushin ta gani. Idanunta taja ta lumshe daga kallon dark pink lips
dinsa. Batasan me yasa gabanta yayi wata wawiyar faduwa ba,sai kawai taji bata da
sha'awar ci gaba da zama a wajen. Tsam ta miqe sanda amna ke ce masa

"A dawo lafiya hamma...." Ta fara saukowa daga steps din,a cikin jikinta taji amna
din na satar kallonta,wani nauyi ta sakar mata da bisa dole ta motsa labbanta tana
fadin

"Adawo lafiya" Sosai yaji kalmomin sun zama baqi a kunnensa,har ya motsa kaman zai
waiwaya sai kuma baiyi hakan ba ya amsa
"Allah yasa" Yana takawa gami da ficewa da takun nan nasa da ta dade da haddaceshi.
Wani irin taku yakeyi tamkar namijin toro,zakayi tunanin wani saraki ne,ko kuma
yana qawata takun nasa daidai da yadda zaija hankalin masu kallonshi.

Ficewarsa daga falon ya bata wani qaramin sukuni,sai ta fasa komawa
dakin ta sauka saman sofas din dake falon ta zauna tana maida numfashi. Idanunta ta
maida hanyar daya wuce din

"Fareeda KHALED MUSTAPHA" Sunan ya dawo mata radam a kunne,murmushinsa kuma ya sake
giftawa ta idanunta,ta sake lumshe idonta ta kuma budesu lokaci daya

"Waya sani ma ko ita ta kirashi?,wa yasan inda zasuje?" Ta furta can qasan
zuciyarta

Please Login or Register in order to submit comment