You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da dama saidai tayi haqurin dole ta tarasu sai
randa ya wuce.

Saddiq da musaddiq ne a gaba,sai shi da Faruqee a bayansu.

Kana musu kallon farko zasu burgeka,ka kuma dauka set din tagwaye
ne guda biyu,don dukkansu kusan sa'annin junansu ne. Yanayin zubin kyan halitta da
suke dashi,ga kuma wadatacciyar tsaftar uniform da Faruqee bai yarda wahalar cikin
gidansu ta sanyashi qazanta ba.

Ba wanda gabansa bai fadi ba cikin su ukun bayan ratsowarsu ta falo
da zummar fita daga gidan idan ka dauke me babban suna da ya dauke idanunsa daga
kanta tuntuni.

Qafarta daya saman daya tana karkadata a hankali,kamar yadda ta zube
musu idanunta tana binsu da kallo kamar qwayar idanun nata zasu zuba a waje.

A darare dukkansu suka gaidata,saidai idanunta suna kanshi ganin yadda
ya gaidata hankali kwance,sam kuma kwata kwata babu wannan razani da kuma d'ar d'ar
dake kwance a fuskokin 'yan uwansa dake takawa cikin sanda suna fatan wucewa daga
falon lafiya.

"Zo nan dan qaruna!" Ta furta da wata kakkausar murya tana sake jin haushi da
tsanar yaron. Dukkansu suka waiwayo,ta sake binsu da ido

"Duk ku dawo nan" Ta kuma fada tana gyara zamanta.

Ba wanda ya musa mata suka tako dai dai da dai dai suka zube saman
carfet din

"Kai don ubanka waye yace ka shiga kitchen ka taba madarar gidan nan?" Ta jefawa
Faruqee tambayar tana watsa masa zagi da hannayenta.

Kiran uban da tayi shi ya sauka har tsakiyar zuciyarsa ya sosata. UBA
wani abu mafi daraja da yake ganin kimarsa cikin DUNIYARSA fiye da uwa,ubansa da
kuma ABBAN Faruqee mutane biyu da basu da tamkar da bayajin zai iya jurewa zaginsu.
Idanunsa ya maida ya lumshe yakuma yi qas da kansa yana hadiyar wani abu me tauri
da zafi tamkar shi mama ke tambaya. Wai haka iyaye mata suke ne marasa
tausayi?,marasa imani?,me yasa iyaye maza yaketa gani da tambari da dukka wani tabo
na tausayawa 'ya'ya?,me yasa kalmominsu suke tsauri akan 'ya'ya cikin rashin
tausayi da kyautatawa?.
"Makaranta zamuje,kuma yunwa mukeji"

"Ubanka nace......saboda ubanka ne ya kawo madarar shine kake ganin kana da right
na shigarmin kitchen yadda kakeso?"


*_Dukkan godiya sun tabbata ga Allah_*

*_yadda muka fara lafiya Allah yasa mu gama lafiya_*

*_kusa kurai da zaa gani a ciki ajizanci ne irin na dan adam,da fatan za'ayi afuwa
a kau da kai_*

*_Don Allah don Allah ina roqo da fatan zaku zama masu uzuri a gareni,saboda
yanayin sabgogin rayuwa,kowa ya sani yau da gobe tana iya sauya bawa daga ainihin
yadda aka sanshi_*

*_duk sanda kuka samu wani sauyi tattare dani game da tsaiko na posting,tsahon
pages da sauransi,ina kyautata muku zaton soyayyarku gareni zata sanya ku zama masu
yimin uzuri_*

*_ina godiya qwarai game da yadda bakwa gajiya da bibiyata,da bibiyar zafafa biyar
gaba daya_*

*_alkhairin Allah yakai muku a duk inda kuke,tare da fatan ubangiji zai tsareku
kuma daga dukkan abunqi_*

*_na gode qwarai,kuma in sha Allah a duk sanda dama ta samu zaku samu komai fiye da
yadda kuke so ma cikin wannan tafiya ta DUNIYATA_*

*_LABARIN ZAI TABO BOYAYYAR MATSALAR DA MUKE FAMA DA ITA,na muku alkawarin nishadi
da sassanyar soyayya kan bigiren salon da kukafi so😍_*

*MU KASANCE TARE IN SHA ALLAH DAGA FARKO HAR QARSHE*

*HUGUMANKU CE*


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

*Arewabooks:Huguma*
Read My Book "DUNIYA TA🌏" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?
id=675041625c3130f457519997
________________________

Page 07


Dif sukayi dukkansu,ba wanda ya iya tanka mata a cikinsu. Daga can
qasan zuciyarsa yake jin wani irin zugi fushi da kuma radadi,don meye zata dinga
zagin iyaye a gaban 'ya'yansu?,shi abban me yayi da har ya cancanci a zageshi?.

"Badai makaranta zaku ba?,ku tashi ku bacemin da gani". Kaman dama suna jiran
wannan umarnin ne daga gareta dukkansu suka miqe din kusan lokaci guda,kowa yana
yunqurin barin gabanta kamar yadda ta buqata
" Harda su kaza a cin danqo?" Ta furta tana kama haba idanuwanta a kansa

"Kai dan qaruna ina zakaje?"

"Makaranta mana maama,ko kin manta tare muke zuwa?"

"Na manta uban masu gida,saika karanta min,don ubanka da can makarantar suka damu
da zuwa?,shine yanzu saboda wuce gona da iri da samun waje har suke rawar jikin
tafiya?.to wallahi kuda makaranta saidai idan anfi qarfina" Ta fada tana kada hannu
da kyau cikin hargagi tana nunasu da yatsa.

Hukuncin nata yazo masa a bazata,don bai taba tsammanin zatayi
hukunci me tsauri har irin haka ba. Yaji abun ya taba ransa qwarai,domin a yanzun
bashi da wani buri daya rage masa saina KARATU. KARATU shine cikar burinsa qwaya
daya tal daya rage bai qarasa mutuwa daga zuciyarsa ba,yana jin zai iya bada
kominsa don yayi karatu,zai kuma iya jure dukkan wata wahala tsanani ko tsangwama
saboda karatu. Ko a yanzun yana daya daga cikin abinda ya sanya zuciyarsa ke
qarfafa,tana sake jadda masa zai dauki komai ya kuma jure komai din saboda
ingantaccen ilimin da yake hangowa zaya samu. Dole ya daga idanunsa da suka fara
sauya launi ya kalleta dasu

"Kalleni da kyau......ba wani karatu da zakuyi cikin gidan da ba na ubanku ba,idan
kuma kallon mamaki kake yimin ai uwarka yafi kamata ka yiwa wannan kallon,ita kanta
ta kasa jurewa zama daku sai ni da bani da galihu akeson hadani da alaqaqai,to
wallahi yadda ban samu yadda nakeso ba,haka kuma ba zaku samu ba......."

"Me kikeso ayi mama?" Ya furta tana aje numfashinta daga tijarar da takeyi.
Tsananin mamakin yaron takeyi yadda yakeyin komai cikin dakiya da taurin rai dana
zuciya

"Ko baka tambaya ba ai zan gaya maka kuma dole kabi,ka sauke wannan munafukar jakar
ku wuce ciki,sudai da babu yadda zanyi dasu gidan ubansu ne saisun dawo,a sauka
lafiya" Ta fadi tana nunawa su Faruqee hanya da yatsa.

"Mama.....amma" Zakayimin shuru ko sai ka jawo kuma na hanaku?" Wani dunqulallen
abu ya hadiye can qasan ransa yana jin kamar ana masa suya

"Kudin mota"

"Kudin ubanka dai,sayyadarku zaku taka sisi bazan bayar ba" Ya fada tana zazzare
masa idanu hadi da dukan hannun kujerar da take kai

"Ku tafi Faruqee don girman Allah" Ya furta da rinannun idanunsa da kuma muryarsa
da tayi laushi qwarai yana duban Faruqee din,don kunnuwansa sun soma gajiya da jin
zagin da take nausawa bawan Allahn da baisan hawa ba baisan sauka ba.

Kallon kallo suke ma juna shida Faruqee din,kowanne cikinsu
zuciyarsa cike take fal da zallar bacin rai daya haurawa shekarunsu. A zahiri
tausayin me babban suna shi yafi rinjaye a zuciyar Faruqee. Ba yau ba ba kuma jiya
ba ya sani......muddin ka ambaci kalmar UWA ko mahaifiya a gabansa takan zame masa
kamar tabo ko kuma ciwo koda ba dashi kake ba,ballantana a yanzun da aka kirata
muraran.

Abun ya jima da zame masa kamar wani ciwo,tunda zancan ya bulla
cikin unguwa sai ya zama abun yamadidi da magana tsakanin maqota da mazauna
unguwar. Sam baa tallafi rayuwarsu ba,ba'a agajesu ba,ba wanda ya waiwaya ya dubi
tsanani bayan tsananin da suke ciki,ba wanda ya bawa rayuwarsu tallafin da zai rage
musu radadin da sukeji,a maimakon haka,sai suka debo DAFI na cecekucen maganganu
akan rayuwarsu suka sake watsawa ciwuka da raunukan dake ciki zukatansu shi da d'an
uwansa.

"Kaje Faruqee" Ya sake maimaita masa yana tsareshi da ido. Ya karanci komai ta
cikin idanunsa,ya karanci abinda yake nufi da maganarsa,don haka bai qara koda
minti daya ba ya kama hannun musaddiq suka suma takawa suna barin falon.

"Na dawo gareka" Ta furta cikin izza da dagawa tare da jinta can saman qololuwar
isa da kuma 'yanci

"Ka koma ka zare wadannan kayan,don basu dace da agola irinka ba,tabbas da 'ya'yan
da mahaifiya zata wofantar dasu,ta tsallakesu ta gudu ta barsu to ba'a banza
ba......don haka banga dalilin da uwar data haifeku bata tausaya muku ta zauna daku
ba ni zan tausaya muku ba......tunda kun iso inaga ya kamata me mana wanki da guga
ya tafi hutu hakanan,ka shiga dakin ajiyar kayan wanki ka debo duk kayan da ka gani
ka fita dasu bayan gida wajen fanfunan can ka wankesu......wallahi wallahi kace
zaka saka iskanci a aikin kaga ikon Allah,banaso kuma azahar tayi maka baka kammala
ba". Baice komai ba yakau da kai ya soma takawa yana komawa dakinsu ranshi yana
wani irin tafasa da suya. Tsanar maama tana sake wani mahaukacin tasiri cikin
ransa. Inda bata tafi ta barsu ba duk tsanani duk wuya,komai girman talaucinsu
sunfi gaban a goranta musu,don da iyaye ake ado,sune abun adon diyoyinsu.

Me yasa ta aikata hakan?,me yasa ta kasa jurewa?,tsabar son kai ne
irin na jinsin DIYA MACE da ya tabbatar a yanzun haka halittarsu take?.ko kuma son
duniya da qyale qyalen cikinta ne ya rudeta?. Me yasa batayi haquri ba kaman yadda
Abbie ya dinga kira mata?. Har yau har kwanan gobe sashen qwaqwalwarsa da ya nadi
muryar Abbie ta qarshe.....magiyar Abbie ta qarshe akan roqarta ta zauna ya gaza
goge su......ya gaza goge wannan rarraunan sautin nasa daga nemory dinsa. Abinda ke
sake aza masa wata mahaukaciyar wuta,tare da dasa masa fara kallon halittar diya
MACE a baibai.

Yana cire kayan saddiq yana kallonsa,a duk sanda zuciyar dan uwansa
ta motsu shine mutum na farko dake fara fahimtar hakan. Ya kammala cire kayan tsaf
ya musanya dana gida sannan ya juya ya adana na makaranta yana musu kallon
tsanaki,dukka ruhinsa da zuciyarsa tana makarantar,yana wassafa malami na farko ya
fita zuwa yanzu,malami na biyu kuma na dab da shiga ajin komai yana ciki.

Hannu ya sanya ya share fuskarsa yana qoqarin lanqwasa zuciyarsa.
Farat daya qaunar da yakewa karatu ya ninku a zuciyarsa ganin abba ya bashi dukkan
wata dama da zaiyi karatun,sai gashi farat daya tana nema ta zama silar da zaiyi
nisa sosai da MAFARKINSA?.
_________________

*_CIKIN DUBU DABAN TAKE_*

*_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_*

*_NA GWADA NA GANI_*

*_YA SUBHANALLAHI_*

*_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_*

*_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_*


*_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_*

*_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_*
*_ME KIKE JIRA?_*

*WANNAN DIN GUARANTEE NE FA*

*TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT*

*KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA*

*INCENSE BY KABO DAUGHTER*

*_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME
SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_*

*_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON
QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO
NE?_*

*MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_*

*INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803*

*_zaki dariya za kuma ki godemin_*

*_gani ya kori ji_*

*hakanan sai an gwada akan san na qwarai*
_________________

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*
*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*πŸ₯°πŸ₯°

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 08
__________________________

*_CIKIN DUBU DABAN TAKE_*

*_TABBAS AKWAI TURARE AKWAI MUNA TURARE_*

*_NA GWADA NA GANI_*

*_YA SUBHANALLAHI_*

*_QAMSHI NA TASHIN KAN ME GIDA_*

*_QAMSHIN DAKE DAGAWA KISHIYA HANKALI_*


*_NATACCEN QAMSHI DAKE KAMA GURI DARAM_*

*_WANNE GANGANCI NE YA SAKAKI TSAIWA SANYA?_*

*_ME KIKE JIRA?_*

*WANNAN DIN GUARANTEE NE FA*

*TASTED AND TRUSTED 100% PERCENT*

*KI SIYA KI GODEMIN HAJIYA*

*INCENSE BY KABO DAUGHTER*

*_DUNIYAR TURARE ME BADA ASALIN QAMSHI ME KAMA JIKI DA MUHALLI,NUTSATSEN QAMSHI ME
SANYAYA ZUCIYA DA DADEWA A WAJE_*

*_IDAN KINA DA MATSALA KINA NEMAN TURARE ME KAMA WAJE,KINASON SAKEWA OGA SABON
QAMSHIN DAKI DA PARLOR,KE KANKI KINASO KI SHIGA WAJE A DINGA TAMBAYAR WACE TA ISO
NE?_*

*MAZA MAZA JEKI KI GWADA WANNAN_*

*INCENSE BY KABO DAUGHTER 08032119803*
*_zaki dariya za kuma ki godemin_*

*_gani ya kori ji_*

*hakanan sai an gwada akan san na qwarai*
___________________________



"Hamma" Ya tsinkayi muryar saddiq tana kiransa,sai ya waiwaya ya zubawa
qanin nasa ido

"Wai sai yaushe maama zata dawo?,yaushe za'a daina yi mana gori?" Tambayar ta
tsinka zuciyarsa sosai ta kuma sake yi masa tabo. Ya zuba masa idanu sosai,kamar
bazai ce komai ba sai ya motsa labbansa

"Duk tsanani duk wahala.....kada ka sake zancanta sadiq,ta tafi kenam,ba kuma zata
sake waiwayomu ba.....ni zan tsaya dakai a kowanne yanayi da.mataki na rayuwa,bazan
bari kasha wahala ba in sha Allahu,bazan bari ka zubda hawaye irin wanda na zubar
ba.....kayimin alqawari ba zaka sake zancan maama ba?" Ya qarashe maganar yana
ritsashi da idanu.

Kai ya jinjina a sanyaye yana maida jikina ga bango ya jingina,wani
abu sosai yaron yakeji da baisan yadda zai fasalta shi ba

"Ka cire uniform din" Ya bashi umarni ya sanya kai yana nufar qofa bayan muryar
mama ta karade ilahirin gidan ta cimmasa har dakin nasu

"Yaaya zan tayaka wankin" Sadiq ya fada a gaggauce

"Aah banaso,kayi zamanka" Ya amsa masa yana qarasa ficewa.

Tun daga wannan rana ta sauya lokutan zuwansu makaranta zuwa lokuta
na bauta da wahalar ayyukan gidan da basu ratayu a wuyansu ba. Duk wani aiki ta
kallafa masa,har takai ta bawa ainihin masu gudanar da aikin hutu tace saita
nemesu,hutu ba tare da an yanke musu albashi ba.

Dukka yawa da azabar aikin aikin banza ne a garesa idan aka
kwatantashi da maganganu masu dafi da take jifansu dashi. Duk kalmarta guda daya me
tsananin guba ce tana kuma same zuba masa dafi da guba me daci ne cikin zuciyarsa.
Rashin ko inkula dinta a kansu da dukka dabi'unta basi fiya bashi mamaki ba,saboda
ya riga da ya yiwa mata kudin goro gaba daya,tunda ya fara ganin sample daga kan
mahaifiyar data tsugunna ta kawoshi duniya kuma. MATA BASU DA IMANI,BASU DA
KIRKI,BASU DA TAUSAYI,BUQATAR KANSU CE A GABA DATA KOWA.

Wannan shine rubutaccen abu daya zauna radam cikin kwanyarsa da
zuciyarsa,wanda baya jin akwai lokacin da zaizo wanda wannan zai wanke daga cikin
kundinsa.

Duk yadda Faruqee ke cikin tsananin fushi da daukar alwashin sai ya
gayawa abba idan ya dawo,in yaso ta kamashi ta gutstsira namansa ta kacalcala amma
me babban suna ya danneshi ya kuma haneshi

"Maama ma data haifemu ta gujemu,ta gaza tausaya mana?,ta kasa haquri damu?,ina ga
mama......mu din ba dolenta bane Faruqee,iya abinci da take sawa ana bamu da gurin
kwana ma kawai tayi qoqari"

"Abincin nata ne?,ko gurin kwanan nata ne?,sannan shi kansa abincin waye yake
qoshi?,bayan store din gidan nan cike yake da kayan abinci?" Qaramin murmushi ya
saki. Duk da qarancin shekarunsa amma kwanyarsa tana aiki yadda ya kamata. Dukka
wannan bai cika masa ciwo bafa,abinda maama tayi ya danne dukka wadannan ciwo da
zafi da kuma tsaiwa a zuciya. Abu daya ne yakejin yana dab da kasa jureshi,hanashi
zuwa makaranta......yana qaunarta yana qaunarta yana qaunarta har baisan iya adadi
ba. Abu na biyu indai saddiq dinsa yana lafiya to komai me sauqi ne.

A haka suka debi wata guda cur babu abinda ya sauya. Yadda kowacce
safiya da ubangiji zai bullo da ranarsa haka zata fidda wani sabuwar muguntar don
quntatawa cuzgunawa a garesu. Duk fushi zafin zuciya da rashin daukar raini irin
nashi bai taba daga kai ya kalleta bare ya tanka mata ba,yana duba cewa ta girme
masa,gaba take dashi,a qalla ta ninka shekarunsa sau biyu. Duka duka shekarunsa sha
shida basu kai adadin shekarun da zai tsaya yana jayayya da babba ba.

A hakane ALHAJI HAMZA KIBIYA ya waiwayo gida cikin iyalansa.

Yaran suna ranshi matuqa,babu kuma ranar duniya da zata bullo ta bace
bai tambayeta su ba idan suna waya,amsar kuma daya ce suna lafiya lau. Koda ya
buqaci magana dasu tana gabatar masa ne da wani uzurin a kansu.

Wanda ya rigaka kwana zai rigaka tashi. Sanda ya sanar da dawowarsa
kaf ta hadasu ta musu mummunar jankunne data tsoratasu ainun. Saidai ko kadan shi
bai tsorata ba,don ba komai yake bashi tsoron ba,bare a yanzun da zuciyarsa ke
qarasa bushewa da qeqashewa akan komai na rayuwa.

Yadda aka saba haka ta sakar musu,sukaci gaba da zuwa makaranta
abba yana kaisu da kanshi kamar yadda yakeyi idan har yana gari.

Ya tsumu sosai,zuciyarsa kuma ta cika da takaici da bacin rai me
yawan gaske sanda ya isa class dinsu yaga yadda aka tsere masa a karatu. Kusan
ranar duka ya qarar da ita wajen bibiyar dame dame akayi da baya nan?,ya karbi note
books na classmate dinsa da dama ya taho dasu gida .

Da yake abba yana nan akwai isashen lokaci 'yanci da kuma hutu,babu
tarin aikace aikacen nan marasa dalili marasa kuma tushe ballantana makama,sai ya
zauna ya qarar da dukka wuninsa a daki wajen ganin ya daidaita karatunsa dana 'yan
uwansa.

Bashi da matsala da saddiq,don ajinsu daya da musaddiq,kuma duk sanda
suka dawo gida Faruqee yana hadasu su sake maimaicin karatu tare ta yadda zai
zamana ba'a wuce saddiq din ba.

Yana da wata irin baiwar basira ta gasken gasken,sharp brain dake da
saurin koyo da kuma riqe abu tun yana dan mitsitsinsa ballantana a yanzun da yake
shirin fara shiga shingen samartaka,danyan jini yana zagayawa da gudu a jikinsa.
Wannan ya taimaka cikin sati gudan da abba ya musu hutu ya gama kammala komai,ya
kuma tarar dasu tamkar dama dashi ake karatun. Sai a sannan ya samu sukuni ya soma
dawowa daidai. Saidai kuma a satinne qarshen satin,a yammacin juma'a abban ya
tattara ya koma lagos,abu guda daya dake alamta musu zasu koma RAYUWAR GIDAN JIYA
kenan cikin gidan.

*********


*_MONDAY_*


Tushen aiki,bai sare ba ya shirya tsaf kamar yadda su Faruqee ke
shiryawar,yana shirin Faruqee na rantse rantse da cewar ba abinda zai hanasu fita a
makaranta yau din. Ya lallaba kitchen ya hada musu tea kaman yadda ya saba ya dawo
ya bawa kowa,saidai ya tsallake me babban suna don yasan bazai sha ba,don kuwa tun
daga wancan ranar data zagi abban bai sake ci ko shan wani abu da Faruqee zai dauko
musu ba,ya tsani zagin iyaye matuqa,mutum ne kuma me fushi da gudun zuciya,wannan
ya sanya yake takatsantsan,akan komai bai fiya zura jikinsa ba.

Fitowa sukayi kamar wancan karon,saidai a yauma sun sameta hakimce a
falon. Idonsa yadan lumshe yana addua daga qasan zuciyarsa. Ya tabbatar wannan
zaman ta yishi ne saboda su,son a lokutan da abba yake gari kwata kwata nasa ganin
qyallinta sai kusan shada zuwa sha biyu na rana.

"Eh......wato akuyar daure an samu sake,to kuzo nan" Faruqee ne na farko daya fara
cakewa guri daya,amma ya kama hannunsa ya jashi suka qarasa wajen.

"Me zakuyimin ku?,tunda kuna da uba ya daure muku gindi?,ku tashi kuban waje,ku
kuma ku koma ta inda kuka fito a cire uniform azo a kama aiki ko?" Cikin tsananin
bacin rai Faruqee ya miqe yana nufar hanyar fita yana kuma qananun maganganu qasa
qasa

"Zagina kekeyi farouqu?,ka kuskura ka zageni ubanka zanci wallahi la'ada waje" Ta
furta da hargagi tana nunashi da yatsa sanda suke kusa da ficewa daga falon. Abinda
ya sanya me babban suna miqewa yana jin nauyi da kuma zafin zaginnan. Ko meye
zatayi me ya gamo da iyayensu?,me su sukayi mata idan su din masu laifi ne a
gareta?.

"Don Allah mama ki barmu muje muma,idan mun dawo zamuyi miki duk aikin da kikeso"

"Kai.....wasa nakeyi dakai?,zaka tashi ka bani waje ko sai na zagi uwarka mara
daraja da ubanka dake qarqashin qasa?" Kamar saukar mashi haka kalamanta suka soki
zuciyarsa,har sai daya kasa jurewa ya waiwayo yana dubanta.

"Don Allah mama ko meye,ko meye mukayi miki ki mana hukunci ba tare da zagin iyaye
ba......"

"Ubanka da uwarka,shegen yaro me tsaurin ido,kaci ubanka" Ta fada har tana zullo
tare da watsa masa daquwa. Ta jima da tsanar dama wannan kamewar tasa,ta jima da
tsanar yadda yake da dauke kai da rashin hayaniya akan komai da zatayi masa,duk
yadda takai ga tama masa wajen bashi baqin kashi da baqar wahala don ya magantu
dukka ya shanye sai a yau din.

Cikin qasa da minti guda launukan idanunsa suka sauya,baice qala ba
amma kunnuwansa suna suna iya jin zafafan muggan kalaman da take jifanshi dasu. Ya
tako a nutse ya iso gaban saddiq dake durqushe a gabanta ya sanya hannu ya damqi
hannunsa ya tasheshi tsaye,abun sai ya masa kamanceceniya da sanda saddiq din ke
tsananin roqon mahaifiyarsu akan kada ta tafi ta barsu.

Bai waiwayeta ba,bai kuma dakata ba ya durfafi qofar fita daga falon
kanshi tsaye,ba tsoro ba shakka ba kuma shayi

"Ina zakaje,bance ba zakuje makaranta ba?" Ta furta da qaqqarfan sauti. Bai dakata
ba bai kuma waiwayo ba ko ya nuna yasan tanayi har ya fice daga falon. A yau ta
rushe dukkan wani ragowar kara da dagin qafa da yakeyi mata. Baya wasa da kalmar
UBA sam a rayuwarsa,IYAYEN MA guda biyu,abba da Abbey.


https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997

________________________
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*πŸ₯°πŸ₯°


*D U N I Y A T A*



*_H U G U M A_*

*Arewabooks:Huguma*

https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997


PAGE 09
Ko Faruqee baisan da zuwansa makarantar ba sakamakon banbancin abinda kowannensu
yake karanta,har sai sanda aka fito break.



Har a sannan ranshi a jagule yake,bacin rai kowanne second yana sake motsa
zuciyarsa. Faruqee ya sameshi daga bayan makarantar zaune qasan bishiya saman
rairayin dake wajen,hannunsa riqe da busashen siririn reshen bishiyar yana tona
qasa dashi,ya kafe qasar da idanu kamar me nazarin samar da wani abun amfani daga
gareta. Ta gefansa ya zauna,yayi masa tambayar duniya akan ya akayi ya taho
makarantar amma ya gaza cewa komai. Na Faruqee ba,tunda ya shiga class din baiyi
manana da kowa ba,don bayajin koda ya bude bakinsa akwai wasu kalmomi da zasu iya
fita daga cikinsa. Dole Faruqee ya haqura ya kuma tayashi zaman shurun,don dukkansu
dama babu me 'yanci ko damar yin break,to inama kudin?,dukka dana transport din da
komai ta hada ta kalmashe.



Sai a hanyar komawa yaji komai daga bakin saddiq. Qwafa yaja yana girgiza kai



"Duk yadda kake tunanin matar nan ta wuce nan,duk kuwa yadda zan fasalta maka,ta
samu sassauci ne daga garemu shi yasa take abinda taga dama,ace mutum ya shiga
shekara ta sha biyar,kana girma amma baka da 'yanci?" Shikam baima iya cewa komai
ba har zuwa sanda qafafunsu suka maidasu gida.



Sai da suka gilma ta gaban gidansu kafin su cimma gidan RIQOnsu a yanzu,idanunsa
zube bisa fuskar gidan dake garqame da kwado. Take yaji wata matsananciyar kewar
gidan da kewar Abbie da jadda suka saukar masa. Duk da suna rayuwa ne cikin
matsakaicin matsayi na rayuwa,amma rayuwarsu rayuwa ce me 'yanci da kuma dadi. Duk
da suna rayuwa da maama cikin wani baqon hali da murdaddiyar dabi'a.......hakan
yafi musu sauqi a kan rayuwarsu ta yanzun cikin gidan RUQO.



Ya janye idanunsa sanda ya dubu daidai wajen da mahaifinsa ya dogaro da qyar ya
biyo bayan maaman yana cike da fatan zata dakata daga aiwatar da qudurinta nayin
nesa da rayuwarsu,wani zafin akan na dazu ya sake yunqurowa ya mamaye

Please Login or Register in order to submit comment