You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kudin data lashe.

"Ya ka tsaya a nan kuma?". Girarsa kawai ya dage masa yana zare key din.

"Muje na taka maka kawai.......sabrrrr tana jirana"

"Muma dai Allah ya kawomu dadin abun ko?" Farouq ya fada yana bude side dinshi ya
fice.

Da ido farouq yabi kyakkyawan kwandon da fu'ad ya dauko da kansa.

"Da alama wannan aikin adda ne ko?" Farouq din ya fada yana jin wani girma da kimar
sabreen suna hauha a ranshi.

"Eh.....ai ta rantse sai wannan tsohon tuxurun ya morewa angwancinsa".

"Ta fiyemin kai ai hundred percent" Farouq ya fadi yalwataccen murmushi na subuce
masa.

"Thank god da babu yadda za'ayi dani ai" Fu'ad ya fadi yana yin gaba yana barinsa
da wani nannadadden kwali da shima ke cike da tarkacen kayan qwalama.

A veranda din farko fu'ad ya cake yana miqa masa kwandon.

"Meye haka dude.....ka qaraso ku gaisa mana"

"Da wa?" Ya fada yana zaro idonsa waje.

"Fannah" Ya amsa masa kai tsaye.

"Allah you're mad farouq.........kawai sai in shiga gidan mutane kai tsaye har can
ciki?.....kaga forget about it please...........ka shiga da cikakkiyar sallama
please.....don't forget to recite addu'an da miji yakewa amaryarsa a daren
farko......don't forget to pray two Raka'at........fatan alkhairi ". Wani qaunar
dan uwan nasa yaji yana kamashi,sai kawai ya rungume fu'ad din cikin jikinsa yana
fadin.

" Thank you dude.....thank you,Allah ya cika maka muradinka".

"Kukan zakayi tun yanzun?,akwai sauran awanni" Ya fada jin muryarsa kaman ta karye.
Dariya farouq ya saki da risunannun idanunsa yana janye jikinsa daga na fu'ad.
Hannu fu'ad din ya sanya yadan daddaki kafadarsa,ya zura hannunsa a aljihu ua fiddo
wayoyin farouq din. Latsesu dukka yayi ya kashesu sannan ya miqa masa su yana masa
magana da ido akan

"Ka barsu a kashe,kada ka kunna". Sannan ya juya a nutse yana fita a gidan gami da
bawa guards umarnin su kulle ko ina a gidan.

Yana takawa zuwa cikin gidan yana jin wani yanayi yana ratsashi. Wani
yanayi daba kowanne zai fahimta ba sai wanda yake a matsayi irin nasa.
Da cikakkiyar sallama a bakinsa,tare da qarin addu'ar

"Allahumma adkhilni mudhkala sidqin,wa akhrijni mukhraja sidqeen,waj'alni
minladunka suld'anan naseera,rabbi anzilni munzalan mubarakan wa'anta khairul
munzileen" (Addu'ace me kyau ga amare ko angwaye yayin shiga gida,ko idan kunyi
sabon gida a sanda zaki shigeshi).

Yana yaye curtain din falon duk wani colors da tsari na dream parlor
dinsa ya bayyana,lafiyayyen murmushi ya subuce masa.

"My dude.......miskili kafi mahaukaci ban haushi" Ya samu kansa da yiwa fu'ad
kirari qasan zuciyarsa. Kowanne taku nasa sai yakejin wata rahama da nutsuwa tana
saukar masa,wani irin farinciki yana lullube ilahirin zuciyarsa.

Qawatattun bedrooms din nasu har guda hudu ya dinga budewa daya bayan
daya,sai ana biyar din sannan ya ganta.

Nannade cikin laffayar nan da zata baka tabbacin asalin kanuri dince
ita,turararren qamshinta daya dumame dakin kuma ya sake gaya maka still KANURI CE.

Sallama ya sake jaddadawa,can qasan maqoshi ta amsa,saidai shi yaji
abarsa,murmushi ya sake subuce masa,sai kawai ya duqa yana sabule rufaffen takalmin
Gaziano & Glirling dake qafarsa,ya rage saura socks kawai wadda ita tayi masa
jagoranci har zuwa bakin gadon da take zaune.

Hannuwanta dake lullube da kyakkyawan zanen lalle ya kalla,baisan
sanda ya ajiye wayarsa da keys dinsa gefe ba,ya miqa hannu yana dora tafin hannunsa
saman nata tafukan hannayenta ba ya riqesu sosai. Wata sheshsheqa ya saki gami da
nannauyar ajiyar zuciya duka lokaci daya,wanda suka fito tare da kalmar

"Alhamdulillah". Karon farko a rayuwarsa da hannunsa ya soma taba na fannah bayan
ta zama halalinsa......karon farko da sukayi kusaci da juna har irin haka,duk da
yadda yake tsananin sonta,yake kuma shauqinta,itama kuma haka,amma dukkaninsu sun
killace hakan,sun kuma boyeshi qasan ransu,ba wanda ya bari dan uwansa ya fuskanci
hakan.(qalubale ga matasanmu)

"Babarbariya ta" Ya fada a tausashe da wani taushi da baisan yana dashi ba. Wani
suna qwaya daya da ba soyayya ba da yake kiranta dashi,yake kuma mata tsananin
dadi.

"Taimaki wannan dan bawan Allahn a bude masa wannan fuskar mutanen maidugurin ya
kalla" Ya fada yana zamewa,sosai ya zauna a gabanta gami da komawa kalar tausayi,ya
koma kaman wani dan almajiri,sai yakejin tun yanzun kaman zai fara sakin kukan da
fu'ad ke cewa ya riqeshi tukunna. Kafada ta maqale ba tare datace komai ba,sarai ya
gani,duk saita rudashi.

"Roqo nake badon halina ba" Ya fada yana riqe hannayenta da kyau cikin nasa.

Murmushi ya qwace mata,duk da fargabar da take ciki,sai ta zame
hannunta daga nashi a hankali ta sanyasu tana janye lafayarta baya ba tare data
daga kanta ba.

"Kan uba!....subhanallah" Ya fada yana wani wantsalawa cikin wani irin mamaki.
Fannah ta shammaceshi,tunda suka fari soyayyarsu har suka qare bazaice ga wani
shape nata daya taba gani ba,koda da wasa kuwa,a yanzun saiga wata ajiyayyar
kyakkyawar halitta kuma dukka mallakinsa ce?,yayi yadda yakeso?. Hannu ya miqa zai
zame lafayar daga kafadarta,yanason ya sake ganinta sosai sai ya janye hannun da
sauri yana murmushi,yana jin kaman wani shock ke jansa.
"Dan sake budemin please fannah.....i wanted to see you all". Wuyanta ta langabe
alamun aah,ai baibi ta kanta ba sai gashi ya dawo gabanta. Hannuwansa duka ya sanya
ya dagata,ya miqa hannunsa gefan qugunta inda ta daure lafayar ya wareshi,ya kuma
zarce da wareta gaba daya daga jikin nata.

Tsaf ya ware kayarsa,sai yakejin wani abu yana ratsa sassan jikinsa.

"Subhanallazi lam yattakiz waladan wala saheeba" Ya tsarkake girman zatin Allah a
abinda idanuwansa suka gane masa karo na farko(qalubale gareku mata,wata sai ran
bikinta ma take fidda shape din gaba daya mazan duniya dana media su tayashi
kalla).

Ji yayi idan ya qara koda second daya bai sanyata a jikinsa ba kaman zai
mutu,sai ya jawota gaba daya cikin jikinsa yana lullubeta da hannuwansa,qamshin
jikkunansu suna cakuduwa guri guda.

"Alhamdulillah,first halal hug" Ya fadi a bayyane yana sake godewa Allah da yadda
ya bashi iko ya tsare mutuncinsa.

Sai da yayi da gaske ya zame jikinsa,don ya fahimci wannan al'amarin
bame sauqi bane,idanma har za'a biyewa ta zuciya da gangar jiki,tabbas dukka
addu'o'innan da musulunci ya koyar da sallolin ba zasu samu ba.

"Ki shiga toilet ki daura alwala,ki rage wannan nauyin na jikinki kizo muyi sallah"
Ya fada yana tattare mata lafayarta guri daya. Dama gurin tsira take nema,don haka
da sauri da sauri ta wuce bandakin ta turo qofar.

Wani wawan tsalle ya buga bayan ya isa dakinsa.

"Alhamdulillah" Ya sake maimaitawa yana sauraren bugun da zuciyarsa keyi,sai ya
miqe ya soma shima rage kayan nasa jikin sannan ya wuce bandaki.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 142

*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.....siya ko siyowa wani,reposting
ko sari akan farashin da babu irinsa_*


https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



142


Sai da suka tabbatar an kai amarya,an kuma dawo,kowacce
mota an ajiyeta a muhallinta sannan sukabar farfajiyar gidan shi da saddiq suna
wucewa sassansu da tuni kowannensu shima ya kwashe komai nasa banda furniture din
ciki,aka kuma shirya a tagwayen gidajensu masu tsananin kyau da fasali.

Saida musaddiq din yayi wanka don yaji dadin jikinsa,ya kuma canza
kayansa zuwa sassauqar jallabiyya ta maza. Har zai tada sallah sai kuma ya fasa,ya
koma da baya yana dauko wayarsa da tunda suka gama waya da amna ya sakata a charge
ya kulle ya barta a dakin.

Yayi hakanne don kada ta matsa masa da kira da magiya,taje ta karya
masa zuciya yayi abinda baiyi niyya ba. Sam bayajin zai barta fita a gidan,fita
daya yakeso tayi,daga gidan sai gidanshi a gobe in sha Allah.

Ya tarar kuwa da miscal dinta har guda biyar.

"Rigimammiya" Ya fadi yana murmushi sannan ya koma ya zauna yana yunqurin kiranta.

Kiran farko aka gaya masa layin a kashe yake,mamaki yadan kamashi,don
zai wahala ka kira amna wayarta a kashe,tunda dai su ba rashin wuta sukeyi
ba,inverter ne 24/7 a gidan.

Sake gwadawa yayi aka sake gaya masa hakan,sai ya haqura ya kira saddiq
zuciyarsa na raya masa tayi fushi ne dashi bai kaita ba,shi yasa ta kashe wayar don
ta rama,shikam bazai iya jura ba,gwara ya lallaso abarsa,

"Huda zaka kiramin,kace tace da amna ta bude wayarta badon halina ba". Dariya
saddiq ya bushe da ita.

"Man.....wannan karyar da kai haka?,'yan mazan anni na dab da zubewa"

"C'mon saddiq.....zaka taimakamin ko na shiga gidan da kaina na nemota?".

"Ni na isa?,bari na kira maka ita.....hold on kada ka kashe". Ya fada yana hada
conference call .

"Hubby..." Ta furta da shagwabar data sanya musaddiq jin kunya ta kamashi.

"Love ya akayi?".

"Ina kewarka hubby"

"I know love......but mun kusa kasancewa da juna in sha Allah,awanni kadan suka
rage.....kina ina?" Ya tambayeta calmly.

"Na boye a daki hubby.....kunyar anni nakeji".

"Anni love?....." Ya fada dariya na subuce masa.

"Anni ai bata da surukai sai 'ya'ya,tasha fadin hakan.....fell free please".

"I will tray hubby"

"Good girl....amna fa?"

"Tun dazun da muka karbi adda fannah ban sake ganinta ba,ina tunanin tana wajen
anni".

"Thanks......bari nayi wanka.....get ready zan kiraki ki rage....." Bai qarasa
jinsu ba ya yanke kiran,kada suje suyi masa baranbarama a kunne.
Still ya sake kiran saddiq.

"Ina kunyar tambayar anni please saddiq tambayar min ita"

"A nawa?" Ya sake zolayarsa

"Ka fadi price dinka" Ya fada yana jin zaquwa.

"Bari na kira maka din sai mu tsadance" Ya fada yana yanke kiran.

Minti daya kacal saiga kiran saddiq din.

"Anni tace suna tare da huda,gashi kuma huda tace tana wajen annin". Gaban musaddiq
ne yayi wata irin mummunar faduwa,haka kawai yaji fargaba tana ratsashi.

"Ya akayi haka?....amma,ina zuwa" Musaddiq ya fadi yana yanke kiran,sai ya zura
flip flops dinsa yana fita a dakin.

Kacibus sukayi da saddiq wanda ya fasa wankan shima ya zura tasa rigar.

"Ko wani dakin ta shiga bacci ya dauketa" Saddiq din ya fada shima yana jin haka
siddan tsoro yana kamashi.

"Haka nake tunani"

"Muje cikin gidan" Saddiq ya fada yana yin gaba musaddiq da yakejin kaman an sabule
masa gwiwoyinsa ya bishi a baya.

Harabar gidan ba kowa don kowa ya gaji ya wuce makwancinsa,baqi suna
can shiyyarsu a bangaren baqi na gidan,a haka suka kutsa sassan anni.

"Kira anni kice ta sauko" Saddiq yace da badawiyya me aikinta,ta amsa da to. Harta
fara haurawa saddiq ya dakatar da ita yace ta dawo sai ya haura da kansa.

Ya samu annin tana cire dankunnayenta da sarqa,saita juyo da mamakin
ganinsa a irin wannan lokacin tana kallonsa.

"Ya akayi saddiq?"

"Amna fa bata wajen huda anni,kota gaya miki tana wani gurin?,dakunan wajen nan
kuma mun duba kafin mu shigo,wayoyinta switched off". Yankewa gaban anni yayi ya
fadi,hannuwanta data miqa kunne don cire dan kunnenta sai taji sun mata nauyi dole
ta ajesu tana dubansa.

"Kun gama duba gidan nan gaba daya?". Kai ya girgiza.

"Kusan ko ina dai anni" Hannu kawai ta miqa ta dauki mayafinta ta yafa tana cewa.

"Muje". Tare suka sauko dashi,ta dubi musaddiq.

"Qarfe nawa ta kiraka kira na qarshe?".

"Takwas da rabi anni mukayi waya,tace zataje gidan BB nace ta bari if possible zan
dauketa na kaita taga gida mu dawo....idan bai samu ba tayi haquri,na saka wayar
charge saida muka gama komai na koma daki na samu miscal dinta me yawa,na kira kuma
wayar a kashe take". Wani abune ya tsargawa anni,a jikinta kawai taji wani baqon
abu yana shirin faruwa,don amna bata taba irin wannan ba. Koda garden na gidan zata
shiga saita gaya ma anni ballanta ace ta fita ko tayi nisa da gida irin haka.
"Kiramin duk masu aikin gidannan" Anni ta buqata tana duban badawiyya. Da sassarfa
ta juya,ba jimawa sai gasu kafataninsu,annin ta leqa daga qofar falon ta gaya
musu,matan su bincike cikin gidan,mazan kuma wajen gidan dama kewayensa,saita koma
cikin falon ta zauna kawai tana jin qafafuwanta suna dab da gagara daukarta.

Kimanin mintuna biyar matan suka dawo,saidai kowacce abinda take gaya
mata shine.

"Bamu ganta ba"

"Ba kowa a dakunan"

"Bata nan". Shuru kawai annin tayi tana jan hasbunallahu wa ni'imal wakil tana
dakon dawowar mazan.

Jimawa kadan suka kammala nasu duban suma,har zuwa qofar gidan. Kasa
tashi annin tayi,don haka tace musu su shigo parlor din kawai.

" Mun duba duk inda ya dace ace mun duba din,tun daga cikin gidan nan har street
din daga farkonsa har qarshe amma bamu sameta ba,bamu samu kuma komai nata ba"

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,hasbunallahu wa ni'imal wakil" Anni ta fada
tana runtse idanunta,fargaba tana kamata.

Gaba daya rasa abun yi tayi,hakanan kuma ta rasa abun fada kwata
kwata,kwanyarta ta daure tamau kamar bata tunani me kyau ba tunda take.

Fu'ad da farouq dukkaninsu suna gidajensu da matayensu,abba kuma baya
nan,a yadda sukayi magana a safiyar gobe qarfe takwas zuwa tara jirginsu zai sauka.
Kai ta girgiza,ba wanda zata bari ya sani a cikinsu,ba wanda zata dagawa hankali.

"Anni ko su yaa fu'ad za'a kira?" Saddiq da tuni hankalinsa yayi qololuwar tashi ya
fada. Kai ta girgiza tana miqewa.

"Ban yarda ku gayawa kowa komai ba a darennan,don ba abinda hakan zai amfanar
saidai ku daga musu hankali,bayan koda sunzo ba zasu yanke abun yanzu yanzu ba,sai
wanda ya qaddara faruwar hakan ya qaddara warwarewar lamarin...." Ta fada cike da
tauhidi da qarfafa imaninta,duk kuwa da cewa ita kadai tasan abinda takeji.

"Kuje kuci gaba da kula da aikinku....kuma ku wuce zuwa safiya ko asuba muga abinda
Allah zaiyi" Annin ta fada tana duban kowa.

Kowa din ya juya ya fice,amma banda musaddiq dake qame a wajen,tamkar
ma baisan abinda yake faruwa ba.

"Musaddiq" Anni ta kirashi cikin dakiya. Kansa kawai ya daga ya kalli annin,don
yasan baida sautin da zai iya amsa mata.

"Kayi haquri kaje ka kwanta"

"Kwanciya anni?" Ya tambayeta kaman baya fahimtar hausa.

"Ta yaya zan iya kwanciya bansan halin da take ciki ba?,anni ina aka kaita?,waye ya
dauketa?,me tayi musu?,me sukeso?,amna ce fa?.....kwata kwata shekararta nawa?,waye
ta tsarewa wani abu?" A nutse anni ke karantarsa,ta fahimci kaman abun yanason fin
qarfin kwanyarshi ne,don haka ta kira saddiq.

"Ko baka kwanta ba kaje kayi addu'a musaddiq mu barwa wayewar gari" Tsam.ya miqe
ba tare daya kalli koda saddiq dake jiransa ya tashi su tafi ba.
"Ina zaka?" Saddiq ya zaburo yana tambayarsa gami da shan gabansa.

"Zan fita nemanta ne,tunda kai baka damu da ita ba" Ya fada da alamun tashin
hankali muraran akan fuskar sa. Kai saddiq ya girgiza

"Akwai hadari a fitarka musaddiq,tunda ko su waye sukayi hakan bamu sansu
ba,bamusan dalilin daya sanya suka aikata hakan ba,bamusan kuma meye manufarsu ko
target dinsu ba".

"Ko report sai naje na shigar,ba zasu dauke mana mutum.sukutum da guda mu kulle
qofofinmu mu kama bacci ba kaman kaza suka dauka" Anni ta fahimci da gaske abun ya
soma haurawa tunaninsa ne,don haka ta tako gabansa tana kiran sunansa.

"Kanason jefa amna a hadari bayan wanda take ciki?" Kai ya girgiza da qarfi.

"Yayi....to kada ka soma wani motsi ko aikata komai har sai munji daga bakin
yayyenku.....qila fitar da zancan shine zai zama namu kuskuren.....kayita karanta
ya hayyu ya qayyumu birahmatika astagis". Kafin ta dire ya kama,a hankali sai yaji
hankalinsa yana daidaita,ya miqa hannu ya kama hannun saddiq da kanshi yana cewa

"Muje".

A parlor dinsu ya zaunar da saddiq shima ya zauna yana matsowa dab
dashi,ya kalli saddiq din sosai muryarsa tana Rawa

"Saddiq tsoro nakeji su waye?,tsoro nakeji karsu cutar da ita,saddiq munaji muna
gani a hannunsu zata kwana?,wanne irin gurin kwanciya zasu bata?" Wanne kalan ruwa
da abinci zasu bata?" Sosai saddiq ya riqe hannunsa yana fadin.

"Kayita maimaita fadin ha hayyu ya qayyumu din kamar yadda anni tace......bamu
zalunci kowa ba in sha Allah ba wanda Allah zai dorashi a kanmu".

Sun jima yana riritar musaddiq kafin ya samo nutsuwarsa 'yar
kadan,saidai ko cikakken zama ya kasa bare ayi maganan kwanciya,kai kawo.kawai yake
tsakanin qofa window zuwa farfajiyar gidan,yana jin kamar ya zura da gudu ya tafi
neman amanansa.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 143


*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA
KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA
IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE
SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA
A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*




143


β˜…A nutse ya shafa addu'a daga sallar asubar da suka idar shida fanna
din tasa,koda bai kalli madubi ba yana iya jin yadda qwayar idanunsa suka
tasa,wanda bana komai bane saina kukan farinciki daya dinga yi a daren jiya. Yaso
yayi haquri ya kauda kai saboda walimar da za'a gudanar a yau,amma inaaaa.......ya
gaza jurewar,har sai da yakai ga inda zuciya ruhi da gangar jiki suke muradi.

Juyowa yayi gaba daya gareta,tana zaune a takure,kanta a qasa tana
duban yatsun hannuwanta.

Ita dinma fuskarta duk ta tasa,saboda kusan tare akayi kukan,tana yi
yana tayata. Idanu ya lumshe ya budesu yana jin nishadi yana saukar masa. Kullum
cikin zulumin yadda zai taddata yake,saboda ya sare da halayen 'yammatam yanzun duk
da cewa yana da cikakken yarda da dabi'unta,to amma wani lokaci abun ba'a kama bane
ko siffa.
"Taho nan flower" Ya fada da sassanyan muryarsa yana miqa mata hannunshi. Bata wani
musa ba ta miqa masa nata,don tana buqatar inda zata jingina taji dadin zaman.

Jawota yayi zuwa jikinsa yana rungumeta tsam,yana jin wata shaquwa tana
tsaga jikkunansu,yana jin kamar ta tabbata a rungume a jikinsa kaman haka.

Qoqarin gaidashi takeyi,ya amsa mata yana shafa kanta ya amsa cikin
kulawa. Sosai ya dinga jero mata addu'o'i,kanta a qasa tana amsa masa da matuqar
alkunya. Mintuna kusan goma sha biyar suka debe a haka kafin ya gyara mata
zamanta,ya ciro alqur'ani guda biyu ya bata daya ya dauki daya.

"Ko na minti biyar ne flower,saboda mu bude wunin rayuwarmu na farko da neman
albarka". Ya fadi yana miqa mata. Rainon anni ne wannan ta saba musu da farawa da
qur'ani,kaman yadda yasan itama fannah din 'yar gado ce wajen iya sarrafa harshe a
qur'ani.
(Ina kira a gareku iyaye,kiyi qoqari a mazauninki na uwa ki wadata kwanya da
harshen 'ya'yanki da qur'ani,su zama gwanaye wajen karanceshi daga bango zuwa
bango,idan da hali suna karantawa suna fahimtar ma'anar,saboda hakan yana taimakawa
wajen zaunar dashi a kansu yana kuma taimakawa wajen sake jin asalin gard'insa da
dadinsa. Allah ya sani ina mamaki naga babban mutum babbar mace ko sangamemiyar
buduwa musulma,amma ba zata iya karance miki qur'ani daga bango zuwa bango ba,ko ba
zata iya biya miki wani adadi me yawa ba,don kwanyar da aka horata da qur'ani zaka
sameta da kaifin basira da fikira me tarin yawa,Allah ya bamu ikon tarbiyyantar da
yaranmu akan hakan,ya shirya mana zuria kafatanin musulmi Allahumma ameen).

Suna kammalawa kira yana shigowa wayar tasa. Fannah ce ta miqo masa da
hannu biyu ya karba yana murmushi

"Allah yayi miki albarka" Saidai sunan daya gani mamaki ya kamashi,baiyi zatonma
zaa kirashi da safe da wuri haka ba shi yasa ya bude wayar.

"BB ba'a ga amna ba tun daren jiya......ga musaddiq nan ya rikice mana,kaman
yanason rasa nutsuwarsa,ka sanar da hamma don Allah" Abinda saddiq ya fada kenan
yana katse Kiran.

Innalillahi yakeso yaja,amma kuma bayaso yayi abinda zai tashi
hankalin fannah daga wayewar garinta a rana ta farko,ballantana yasan mata da
rudewa qwarai,dan qanqanin abu sai su maidashi babba,don haka ya miqe tsam da wayar
a.hannunsa yace.

"Ina zuwa" Ya soma takawa yana fita a dakin. Tadan bishi da kallo kadan,sai kuma ta
miqe tana ninke abun sallar da suka idar.

Wani dakin daban ya bude ya shiga,sannan ya fara qoqarin kiran fu'ad
yana kuma laluban kayan da zai sauya a jikinsa,idanunsa akan agogo yana duba qarfe
nawa.

Su dimma rufe alqur'aninsu kenan,don a yanzun shine malaminta. Tayi
sauka tun kafin rasuwar mahaifinsu,tana da tilawa a kanta,amma sai yanayin
karatunsa da qira'arsa suke mata dadi,wannan ya sanya ya zame mata malami duk bayan
sallar asuba suke tilawar abinda ya sawwaqa tare.

Wani lokaci ido take zuba masa idan yana karatun. Komai Allah ya
bashi,duk wata baiwa da take nuna cikar dan adam ya sameta,abu guda daya ne ya masa
cikas da naqasu shine MAHAIFIYA.

Kashingidar da yayi da wannan damar ta samu ta zame jikinta zuwa
kitchen. Wata irin mahaukaciyar yunwa take fama da ita a dan tsukinnan,ko cikin
dare ta tashi abinci takeci,ba jimawa kuma take rasa komai,cikinta yake yayewa
tasss kaman an mata yasa.

A tsaitsaye ta hada oats ta madara tasha,kafin sannan saiga ma'u ta
shigo.

A mutunce suka gaisa,zuwa sannan ta fara gane inda sabreen tasa gaba
na bawa mijinta kulawa da karan kanta.

"Me zamu dafa?"

"Ummm.....bari muga.....bari na fara dafa masa paw paw tea tukunna" Ta fadi tana
nufar tsararren store dinsu.

Duk kusan ganyayyakin da yakesha akwai a ciki,busassu anyi packaging
nasa cikin wani leda ta musamman da ake kawowa daga china. Packet na Paw paw leave
din ta dauko ta dawo,ta wankeshi da kyau ta tafasa ta juye masa cikin wani
Traditional English tea set sannan tace da ma'u.

"Ki fiddo naman kai bari naje na dawo".

Ta shiga daidai sanda ya fito daga toilet yana goge ruwan alwala.
Idanunsu suka gauraya waje daya,kowannensu ya sakarwa dan uwansa lallausan
murmushi.

"Barka da tashi sleepy head" Ta fada cikin salon tsokana. Fadada murmushinsa yayi
har fararen jerarrun haqoransa suna fitowa.

"Barka kade my super girl" Ya bata amsa yana karbar tea tray din yana ajiyewa saman
drawer. Hannunsa ya miqa mata yana jawota cikin jikinsa,saidai kuma sulalewa tayi
ta tsugunna tana gaidashi. Amsa mata yayi cikin murmushi kafin ya miqa hannu ya
sake jawota ya rungumeta tsam,fitinannen qamshin kabbasarta na incense by kabo
daughter daya hautsina har cikin gashinta da kuma lab lab dinta suna tashi da wani
sassanyan qamshi daya manne a fatarta.

"Fatan shalelena ta tashi lafiya.....addarmu.......matar babban yaaya" Yadda ya
fadi maganan ya sanyata tuntsirewa da dariya,ya sake kamota yana qanqameta a
jikinsa.

"Ina yara na?,fatan sun tashi lafiya?" Ya furta yana

Please Login or Register in order to submit comment