You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma qaryatani kaman yadda
mamansa tasha shan alwashin hakance zata faru?"

"Ga alama kuwa.....ya fara doubting akan abinda kika fada". Fada ne ya kacame
tsakanin sassan zukatanta guda biyu,daga qarshe taja qaramin tsaki,ta jawo landline
ta soma neman number gidan anni saboda tata wayar a hannunsa ta barta.

Daya daga cikin masu aikin ce ta daga,cikin girmamawa ta gaida
sabreen.

"Hadani da huda ko.nadra ko haneefa"

"Okay maa" Ta amsa mata a ladabce. Dukkaninsu ta kawo mata,suka bata lokaci sosai
suna hira kafin suyi sallama.

Daki ta koma donyin wanka,sai a sannan ta lura an kwashe duk wani datti
kwanuka data zubar. Mamaki yadan kamata,amma saita samu assurance na shine ya shigo
din ya fidda kayan.

Tsaf ta gyare dakin,ta wadatashi da qamshi daya qarawa dakin wani
irin sukuni da nutsuwa,sannan saita wuce tayi wanka. Tsaf ta shirya cikin wata
chiffon gown maras nauyi,ta lalubo Malaysian hijab ta saka sannan ta fita.

Kaman ba zata haura saman nashi ba amma ta daure. Tasan bai kamata ta
barshi haka bata gyara ba,kaman yadda bai kamata ta bari wani ko wata su hau ba.

Tsaiwa tayi tana qarewa parlor din kallo. Komai yana nan a zube inda
yayi amfani dashi,da alama ma a nan parlor din ya kwana,saita taka tana tattareshi
tsaf,ta kuma sanya vacuum cleaner ta tsaftace saman dukka ta gyare masa toilet din.
Sanda ta gama azahar ta kawo jiki,cikinta kamar an mata yasa,dole ta sauko dining
din qasa neman abinci.

Tunda lalurar nan ta kamata ma'u ta haddace,bata taba barin dining din
wayam ba komai,kaman yadda bata barinta ta dawo sake cin abinci ta samu maimaici.

A nutse ta zauna ta zuba da nufin soma cin abincin amma kuma sai taji ta
kasa. Azahar ta sako jiki sosai,ina yaje?,abunda tun fara shaquwarsu bai taba
faruwa ba.

Ta juya abincin har batasan sau nawa ba amma ta kasa kaiwa bakinta,kaman
ahakan ake jira ya faru sallamarsa ya ratso parlor din.

Duk da hautsine yake amma kallo daya tayi masa shigarta taji ta burgeta ta
masa mugun kyau. Baqi da baqi a jikin fari,saidai duk da hakan saita wani basar ta
dauke kanta tana amsa masa sallamar tan jira taga da wanne irin yanayi ya dawo
gidan.

Tsam ta miqe sanda taji alamun takowarsa nan dining din,ta tura kujerar
tana nufin wucewa,saiji tayi anyi mata wata Kyakkyawar damqa na tare da bata lokaci
ba kuma ya mata wata Kyakkyawar runguma da ta sanya qamshin turarensa mai matuqar
sanya nutuswa isa ga hancinta.

Saman wuyanta ya aje fuskar ta,kullum alfahari yake d wannan qamshin
nata da yasha banban dana kowacce mace.

"Kina bisa wuyana oum triplets......a yafemin,na leqo kina bacci,banaso kuma na
katse wannan daddadan baccin nan.....yaya babies dina" Ya fada yana zamewa ya duqa
a gabanta yana yaye rigarta.

Maganganunsa daya saba yi da cikin nata yayi da nufin da yaransa yake
magana,ta dauka zai tashi kaman yadda ya saba,sai kawai ya jawota yana tsokanarta
ta cibiyarta. Janyewa tayi da sauri ya saki dariya.yana miqewa.

"Anga amna"

"Serious hamma....serous?" Girarshi ya dage mata,saita sauke ajiyar zuciya tana
fadin

"Alhamdulillah alhamdulillah.....please hamma"

"Bani hug daya kawai ya isa tukucin yi miki albishir......tausar dare kuma itace
tukucin kaiki wajenta"

"Zanyi hamma zanyi wallahi" Ta fada tana dan qaramin tsalle. Riqeta yayi da kyau
yana duban tsakiyar idanunta,da wata muryarsa can qasan maqoshi yace.

"Bi a hankali.....yarana" Ya qarasa fada yana dora hannunsa saman cikinta. Kunya ta
kamata,ta kuma sanyata janye idanunta da sauri,daidai sanda kira ya shigo masa.

Bai fasa sakata a jikinsa ya matseta ba sannan ya amsa wayar da cp ne
ya.kirashi.

"Thank you.....gani nan fitowa" Sai ya katse wayar yana dubanta.

"Zanga baqi my world.....zan dawo shortly in sha Allah....ki kulamin da kanki" Ya
fada yana kissing kuncinta duka biyun ya juya yana fita farfajiyar gidan.

Daki ne yalwatacce da aka shimfideshi da lallausan carpet milk color
kaman kalan labulayen dakin.

Daga damansa bibo ce ita da zuwaira,sake maida dubansa yayi ga
gabansa,mashkur ne shi da dan uwan tasa ta'asar.....mashkur din da gaba daya ya
fita a hayyacinsa,tsufa sosai ya kamashi,wani irin tsufa na qarfi da yaji wanda
wawulonsa ya sake tsananta munin abun.

Sauran duka ya bisu da kallo,amma kowannensu munin fuskar mashkur ta
zarta munin da yake gani a fuskokinsu,bawai muni na fuska kawai ba.....aaah muni na
zuciya.

Ma'aikatan gidan jaridar ya fara nunawa.

"Wadannan na gama da case dinsu......aje a hadasu da diyar ambassador......ranar
shiga kotu a hadosu tare qarqashin shari'a guda daya,lawyer na zaiji da komai".

"Wayyo Allah.....mun shiga uku,don Allah sir kayi mana afuwa ka yafe mana,wallahi
bamusan a kanka tace a buga labarin nan ba". Wani banzan kallo yayi masa.

" Okay,idan wanine bani ba kenan zaku iya tozarta masa iyali,idan wani ne bani ba
kenan zaku iya wulaqantashi ku wulaqanta aurensa da shaidar zur.....CP.....bana son
sake jin muryarsa a nan wajen" Ya fada yana takawa ya jawo wata kujera.

Kiiiii ya ajiyeta gaban bibo wadda jikinta ketsa tsuma,ya koma ya zauna
sosai yana dora qafarsa daya kan daya.

"Nutsu sosai.....labari zan baki sannan na sallameki".

"To....to Allah yayi albarka".

" Ameenatu ahmad sabreen takai budurcinta gidan mijinta,wanda ni Muhammed fuad
jadda na karbeshi da kaina....kuma mutanen dake rayuwa damu suka shaida hakan a
lokacin". Dif wuta ta daukewa bibo duk yadda takeji da tsageranci sai taji maganar
ta girmeta.

"Ke din uwace ko?,a kamatance bai dace na gaya miki haka ba ko?,saidai
kash.....nidin bana yafiya bana kuma ragayya ga duk wanda yace zai taba rayuwar
duniyata.....sabreen,a inda kuma aka samu akasi shine.....tuntuni kika sanya qafa
kika take wannan girman daya kamata ki samu......to ina me!miki
albishir.....sabreen takai bantenta......ba wani matsiyaci ko lusarin daya samu
damar tsallake wannan shingen......yadda kika dinga yada jita jitan mutuniyar banza
ce......na baki dama na biyu kisan yadda zaki wanke wannan sunan daga kanta....ki
maida gurbinsa da kyakkyawar shaida,idan hakan bata kasance ba kuwa,a karo na biyu
idan na daukoki batar dake zanyi bat.....a bude mata ta tafi gida". Bata tsaya
tunani ko waiwayen tazarar nisar tafiyar da zatayi a qasa,ba tare da abun hawa ko
kudin mota ba ta fice,tunda har ta samu nasarar shaqar iskar 'yanci
kuwa......bataga abinda zai hanata hada lecture din wayar da kan al'ummarta kan
muhimmancin mutuncin da sabreen ke dashi ba.

Idanunsa ya ware akan mutum uku.....mutum ukun da yakejin laifinsu
yafi na kowa girma,ya sake aza idanunsa akan zuwaira wadda daga ita har bibo sunyi
wani zuzzurmawa. Duk da ajiya ce kawai akayi musu irin ajiyar da take daidai da
aljannar kare.

"Kamata yayi kema a hadaki da wadancan.....sashen manyan laifuka ko?..." Kuka ta
fashe dashi tana hurwa tana neman agajinsa.

"Ki rufen baki,don duk yadda raina yakai ga baci bazan iya zabgawa fuskar dakeda
furfura mari ba,koda furfurar ta banza ce" Gum ta koma tayi sannna ya bude idonsa
yana sake dubanta.

"Kina gidana kina qarqashin inuwata amma kina neman hanyar da zaa shigo a keta
haddin iyalina?!.....abu guda ya rage miki ki gayamin......waye ya sanyaki boyesu a
dakinki kika fiddosu da dare zuwa sassan matata!!!". Wata bahaguwar tsawa daya
sauke mata sai data tattara gudawa me yawa a cikin mashkur,ya rasa wanne.ibtila'i
da bala'i ne yake hanashi furta masa sunan.matar kowa ma ya huta?,fatansa daya
wannan tsohuwar ta kira sunanta,wataqila ko kwatance da ka yayi akan shima ita ta
dauki.nauyinsa duk da akwai nasa shirin.

"Mmm.......maamah ce" Sunan ya saukar masa cikin ba zata. Fuska ya yamutsa yana
dubanta.

"Wacce kenan?"
"Hajiya maamah.....mariya mahaifiyarka" Komai ya tsaya masa na wasu daqiqu,sai daya
koma daidai kuma kwanyarsa ta cika da wasi wasi.

"Cp.....janye matar nan,a hadata da wadancan mutanen". Kallo daya ya yiwa mummunar
fuskar mashkur,wadda ta jima da tashi daga kyakkyawa zuwa asalin mummuna.

"Mariya ce nima!.....maamah ake ce mata" Ya fada da sarqaqqiyar muryarsa da bata
fita yanzu tartar saboda fitar haqora sha biyar daga bakinsa.

Kaman ya dauki takobi ya jefeshi dashi haka yaji,duk wani jini dake
jikinsa yaji yana neman daskarewa,kwanyarsa kuma tana shirin yi masa formatting da
karan kanta irin na kota kwana,saidai kiran wayarsa yaso maida komai muhallinsa,ya
daga kiran bawai don yana gane waye ke kiran nasa ba yana komawa kaman wani
shashasha.

"Jordan ne sir.......sir an jona musu na'urar fidda bayanai cikin sauqi,sun kuma yi
bayanin komai...."

"Me aka samu?" Ya tambaya cikin sarewa da jin komai.

"Am sir.....kayi haquri.....gaskiya bayanansu na qarshe kaman na'urar ta samu
matsala.....sunce zaa sake bincikawa"

"Jordan please tell me.....ka gayamin ko waye ya sanyasu.....bana buqatar jinkiri a
daidai wannan lokacin".

"Sir....sir" Sai ya kama inda inda.

"Tell me nace!" Ya fada a tsawace.

"Mariya......mariya ce maamah". Iya abinda fuad yaji kenan wayar ta sulale daga
hannunsa ta fadi qasa.

Bai sani ba......jijiyoyin hannunsa ne suka daina aiki yadda ya kamata ko
kuma qwaqwalwarsa ce?!.

Tashin hankali!

Allah ka rabamu dashi!

Me karatu sai ince muje
mu qarasa

Hugumanku ce
Na gode


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³
π™‹π˜Όπ™‚π™€ 149


*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX


149


Kowacce gaba ta jikinsa sai yaji tayi wani irin sanyi,sai ya dinga jin
kaman bashi da wani sauran damar ya motsa ko ya sakeyin kuzari a daidai wannan
lokacin.

"Mariya ce.....maaamah ce......itace" Sautukan suka dinga haduwa suna masa amsa
kuwa a tsakiyar kansa.

"Are you okay sir?" Muryar cp tayi kutse cikin tunaninsa,wanda yaga lokaci daya
fu'ad din yanayinsa ya sauya,wuta kuma ta dauke masa. Da qyar ya iya daga idanunsa
ya kalli cp saboda wani dan banzan ciwon kai daya saukar masa lokaci guda.

"Yes.....am okay,akwai wadanda sukayi kidnapping 'yar alhaji hamza kibiya......za'a
canzasu daga can inda suke a kawosu nan a hadesu......duk yadda ta kama ayi musu
hukunci".

" Ma sha Allah....sunzo.hannu kenan?" Kai ya jinjina masa kawai. Bayason doguwar
magana sam sam,don shi kadai yasan yadda kansa yake masa wani irin bala'e'en
ciwo,yana jin yadda zuciyarsa ke tafasa da wani irin mahaukacin fushi da yake
tsoron kada ya illatashi shi a karan kansa. Da zafi zafi ya fita a gurin,ya samu
abdulgaffar suna tsaye suna dakon fitowarsa. Hannu kawai ya miqa masa

"Bani key" Ya fada ba tare daya dubu abdulgaffar ba. Baki ya saki yana kallon boss
din nashi,baisan meye haka da zafi ya tunzurashi ba ko kuma ya sauyashi.

"Sir.....muje na kaika duk inda zaka je.....like kaman baka cikin mode din da za'a
barka kayi driving".

"Just give me the keys abdulgaffar.......ko mutuwa zanyi a hanya kana da
asara?........wanda ya kawoni duniya ma bashi da asara ballantana kai!" Ya fada da
wata irin tsawa data bashi matuqar mamaki. Salin alin ya miqa masa key din,saidai
kuma ya yiwa sauran team nashi alama da ido,don haka fu'ad din yana tada motar yana
fita suka bishi a baya cikin salon da bazai gane shi suke ba. Suna matuqar qaunarsa
da kula da dukka abinda zai cutar dashi,suna matuqar jinsa a jiki irin kusa
kusannan,suna jinsa tamkar wani babban yayansu da yake da ruwa da tsaki a
rayuwarsu,inda suna da hali tabbas ba zasu bari ba ko quda me cutarwa ya sauka a
kansa ba.

Wani mahaukacin gudu yake zubawa wanda ya sake tabbatar musu da ba
lafiya ba,hankalin abdulgaffar akan motar yana duban wanda ya bawa yayi driving.

"Ka kula sosai,kada ka matsi bayansa da yawa kada kuma ka bari ya kufce mana" Ya
fada yana gyara zaman Bluetooth din kunnensa yana magana da na motar baya.

Shi kansa yasan gudun da yakeyi ya wuce qa'ida.......amma a irin zafi
da bugun da tasa zuciyar takeyi sai yakejin ba wani gudu yake ba shi din. Idanunsa
fes bisa kwalta amma tunaninsa yayi nesa sa gangar jikinsa. Baisan kuka yakeyi ba
saida yaji iska na fifita hawayen daya silmiyo masa,karon farko tun bayan tafiyarta
ta barsu.....karon farko tun bayan wasu shekaru masu yawan gaske da ya share wani
abu bai sakashi kuka ba......a yau a zagaye na biyu ta sake zama silar kukanshi.
Hannunsa daya ya saki dava steering din,ya shafo hawayen yana kallon su,a wannan
lokaci yana jin ta gama sanyashi kuka......yayi kuka qarshe a rayuwarsa saboda
ita. Tsananin kunyar anni da abba yakeji,da wanne idanu zai kallesu ya shaida musu
mahaifiyarsa ce ta aikata ma diyar cikinsu autarsu haka?,da wanne bakin zai musu
bayani?,wanne shine kalar sakayyar da suka cancanci su samu makwafin alkhairin da
sukayi mata?.

Wani birkitaccen parking yayi qofar gidan,parking din da ya tada
qura,ya kuma ja hankalin malam sa'adu dake zaune daga cikin gidan a bakin qofa yana
jan tasbaha.

Da sassarfa yake takun nasa,kaman me gaggawar cimma wani abun.
Security na farko ne ya hangoshi,ya kuma taso ya bude masa da sauri kafin yakai ga
qarasowa.

Kusan ba sosai yake gani ba,fatansa kawai ya cimmata......fatansa kawai
ya isa gareta......ya kuma tambayeta dukka akan me?,me yasa?.

Da sauri me aikinta dake saukowa daga samanta taja baya tana zubewa sanda
taga shigowarsa.

"Barka da warhaka yallabai?" Sam ba gaisuwarta bace damuwarsa,bai kuma damu ya amsa
ba

"Tana ina?" Ya tambayeta kai tsaye yana jin jikinsa ko ina yana rawa.

"Tana sama" Ta amsa masa tana rabewa ganin yadda ya nufo saman da sauri bata ko
dire statement dinta ba.

Matakala bibbiyu ya dinga hadawa har Allah ya kaishi saman. Dab da
matakalar qarshe sautin muryarta ya sauka a kunnensa.

"Ta yaya akayi saken da har wani yasan inda suka boyeta.....wanne irin hauka ne
wannan?,baisan muhimmancin yarinyar nan a hannuna ba?,subucewarta da kuma kamasun
da akayi yasan irin asarar da zai jawomin?.....bani da haufi akan zasu iya fadar
sunana......duk da boka baiyi aiki a kansu ba amma kudin dana musu alqawari da
alqawarin dana musu akan koda tsautsayi ta gifta zan fiddasu....iya wannan bazai
bari su fadi sunana ba" Ta furta cikin bawa kanta tabbaci da yaqini da gaibu da
qaryar daka iya fidda bawa daga ainihin imaninsa.

Wani abune ya fusgeshi sosai,da sassarfar data jawo hankalinta daga
wayar da takeyi. Wani irin duba take masa me cike da tsoro da kokwanton ya jita ko
bai jita ba?,zuciyarta gaba daya ta kasa bata nutsuwar bai jita din ba saboda wani
irin kallo dake fita daga idanuwan da suka sauya launi suka jirkice,daga fararen
qwayar idanuwa zuwa kalar makuba kaman an diga jini.

"Why maamah.....why amna?!" Ya furta da wani irin sauti me cike da razani mamaki
dake cakude da karyewa yana wara hannuwansa da kuma watsasu kaman wanda yake dakon
kama wani abu.

Wani irin shock taji,wanda ya kusa sanya numfashinta dakatawa na wucin
gadi.

"Me yasa maamah?.....me yasa?,idan ni kinyimin.......d'anki ne.....idan kin yiwa
musaddiq.......d'anki ne......amma amnah fa?!" Ya fada da wata irin murya dake
neman fara rawa saboda tsananin sarewa da dukkan komai,ya kuma qarasa maganar yana
nuna waje da yatsarsa.

"Me amna ta aikata maamah.....meye laifinta?" Ya kuma fada da yanayin mutumin da ya
soma zarewa.

"Idan kika bada kai bori zai hau.....idan kuma baka iya kama barawo ba saishi ya
kamaka" Wani sashe na rubabbiyar zuciyarta ya sake bijiro mata da wannan
shawarar,shawarar data qarfafi dukkan gabbanta,ta soma qoqarin tattaro kowacce
nutsuwa tata,sannan kuma ta hana kanta shiga d'imuwa.

"Kai fu'ad.....kalleni nan da kyau,idan kana cin qasa ka kiyayi ta shuru....ni
dinnan nice uwarka,baka da sama dani.....ohhhh,wato kaje an karanto maka abinda
zakacemin da kalar rashin kunyar da zaka yimin.....dukka ameenatu ta yo maka
katunsa shine zakazo ka saukemin?!"

"Ameenatu ameenatu dai?,ameenatun da batayi miki komai ba face alkhairi?,ameenatun
da ta rungumi yaran da kikaji cewa baki buqatarsu?,ameenatun data yarda ta zauna ta
kashe tata rayuwar saboda ta 'ya'yan da kika watsarwa duniya?,akwai wani alkhairi
sama da wannan?,akwaishi......wata can daban tayi abinda uwa ta gaza yi?,wata can
daban tayi abinda uwa take ganin ya zame mata babban aiki?" Ya qarasa fada yana
zuba mata ido,qirjinsa yana sama da qasa yana jin kamar ciwon zuciya ne yake shirin
kamashi.

"Kin dawo kin sake kashemu a karo na biyu bayan wancan kisan da kika yiwa
rayuwarmu.......me mukayi miki haka?,laifinmu ne da kika haifemu alhalin baki
buqatarmu?" Ya fada a tausashe da wani irin rauni daya sanya idanunsa fitar hawaye

"Daga kowanne bangare......cikin binciken kowanne laifi Maamah dai mahaifiyar
fu'ad?,mahaifiyarsa?.....maamah dai?,wadda tayi silar zuwansa duniya?,maamahn ita
ta dauke amna?,amna diya ga hamza kibiya?,mutumin daya zame musu uba......bango
madafarsu?,ya tallafesu a sanda duniya tayi watsi dasu,ya rungumesu,a sanda ita da
take Mazaunin uwar data kawosu duniya ta sanya qafa tayi wancakali dasu?.....ya
rungumi farincikinsu da baqincikinsu?,ya rabu da duk wanda zaice baya sonsu?,ya
qara zafin nemansa saboda su.......yayi musu riga yayi musu wando?,yayi kawar da
dauda da duhun jahilci daga qwaqwalensu?,ya daga darajarsu a idanun duniya ta
hanyar haskasu da hasken ilimi?,ya maidasu mutane ta hanyar basu ilimin addinin
islama?,ya karbesu a matsayin 'ya'yan da shine yayi silar zuwansu duniya bawai uban
riqo ba?,yayi musu gatan da ko 'ya'yan cikinsa bai musu ba?.....amnan dai itace
d'iya ga ameenatu......ameenatun data dawowa auren hamza saboda yaran?,ameenatun
data sadaukar da duk wata kulawa da lokacinta akan yaran?,ameenatun da bata yarda
da wani abu me cutarwa ya rabesu ba?,ameenatun da idan kanaso kaga
farincikinta.....ko kaga kirkinta ka yabi musaddiq.......ka yabi fu'ad......idan
kanaso ku bata alaqarku taja baya ka zagesu ko ka kushesu.....ameenatun da ta
sadaukar da lafiyarta saboda su su rayu cikin aminci?,taqi kwanciya ta huta
sabodasu?,taqi ci saboda saboda basuci ba?,taqi sha saboda basu sha ba?......" Ya
sake tsayawa saboda yadda numfashi ke masa wahalar shaqa.

"Laifin ameenatu rainon 'ya'yanki da tayi......laifin ameenatu inganta rayuwar
'ya'yanki.....idan duka haka ne ita kuma SABREEEN FA?!". Wannan tambayar daya jefa
mata tafi kowacce gigitata. Sabreen?,ya tabbata ta qarasa bude mata aiki kenan
kaman yadda taci alwashi?.

"Ni na kawota rayuwarka.....kuma a yanzu bani da buqatar kasancewarku......na nuna
maka ta dukka hanyar data kamata amma saboda banda kima da martaba a idanunka ka
gagara fahimta".

"Sai hakan yanzama license ya zama halaccin da zaki tura wani d'a namiji gidan
aurenta.......dakin da d'anki ya gina saboda matarsa ta sunnah?.....yaje ya keta
hurumin ubangiji?,.......kin auramin sabreen saboda ki.mallaki fu'ad......fu'ad din
da bai mallaki wuta ko aljanna ba......fu'ad din da bai mallaki rayuwa ko mutuwa
ba.......bai mallaki komai ba face wata aba da ake kira DUKIYA wadda ka iya zama
fitina da jarrabawa ga bawa.......". Yana kaiwa qarshe ya jawo littafi da abun
rubutun daya gani ajiye a gefe,ya jawo side table ya ajiye a tsakaninsu ya daga
idonsa yana kallonta duba na kai tsaye.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 150

*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa
wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group
namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



150


"Na baki dama......daga farkon littafin nan har bangonsa ki rubuta
adadin kudin da kikeso......na baki dama ki rubuta adadin alatun rayuwar da
kikeso......na baki dama ki rubuta tsarin rayuwarki na shekaru dari nan gaba idan
har zaki kai sannan......ni kuma zan tabbatar miki da wannan mafarkin,muddin zaki
zare kanki daga rayuwarmu.......muddin zaki fita salin alin daga
rayuwarmu......muddin zakiyi nesa da rayuwarmu......indai kin amince zaki bar
iyalin ameenatu su rayu cikin salama su kuma zauna lafiya........ina fada miki
hakanne cikin harshe na girmamawa.......ina gaya miki hakanne saboda har yanzu
sunanki MAHAIFIYARMU.......Duk da girman abubuwan da kika aikatawa mutanen da
basuji ba basu gani ba......ina gaya miki wannan zabinne saboda shine zaifi mana
sauqi mu dake" Ya qarasa maganar yana jin wani mulmulallen dutsen wuta yana tsaya
masa tsakanin wuyansa da qirjinsa yana qoqarin turashi da qyar. Fata yakeyi inama
ace wani ko wata ce can daban suka aikata musu wannan abun ba maamah ba?......inama
ace wasu mutanen ne daban keda alhakin dukka wadannan abubuwan ba maamah ba?,ya
rantse da Allah da sai ya ganar dashi kuskuren bari da yayi uwarsa ta haifesa zuwa
gidan duniyar ma gaba daya.

"Fu'ad!.....ni kake gayawa wannan maganar?,ni kake cewa zaka rabu dani saboda
ameenatu?" Ta tambaya tana jin wani irin tashin hankalin jahiltar matsayin ameenatu
da tayi a baya. Ashe har zai iya katse alaqar uwa tsakaninsu saboda ameenatun dai?.

"Fu'ad!.....ka saurareni da kyau!......."

"Jaffal qalam" Ya fada yana miqewa daga gabanta. Zuciya da shaidan dukka suna
kusa,duk sanda zai kalli fuskarta fuskar mahaifinsa yake kalla a tayi watsi dashi
cikin tsananin ciwo bayan ta gama illatawa luguiguita lafiyarsa cikin
mugunta.......duk sanda zai kalleta saiya tuna sanda take cida Mahaifinsu da
abubuwan da aka hanashi ci ko sha saboda hakan zai iya zama sanadin komai.....ciki
harda MUTUWARSA.......duk sanda ya kalleta saiya tuna sanda JADDA ta mutu saman
cinyarsu saboda rashin gata suka kwana da gawarta ba wanda ya ko leqosu sai bayan
wayewar gari......duk sanda ya kalli fuskarta sai ya tuna sanda musaddiq ke kwana
yana kuka harda shidewa cikin kewa da qauna yana kiran sunanta.....burinsa shine
kawai ya ganta......har yanzu kunnuwansa sun gaza manta yadda aka saka abun rushe
gini ake dukan ginin gidan da mahaifinsu ya wahala da dukka qarfinsa ya ginashi don
su rayu a ciki......ta badashi a mazaunin jingina ta karbi kudaden ta nausa zuwa
duniya

"Wannan dama ce a wajenki cikin girmamawa da kuma baki abinda kiketa harin mallaka
din tsahon shekaru kina fadi tashi.....ki rubuta!....ki rubuta!!.....ki
rubuta!!!!....ki gayyato wasu ma su tayaki rubutun?!!!,wannan damar ce kawai ta
rage......'yanci muke nema!!!!,yanci muke buqata....." Sai ya hade hannayensa
alamun roqo

"A wannan karon da kanmu muke roqarki ki tafi ki barmu kaman yadda kikayi a baya".
Sai ya fara tafiya da baya da baya idanunshi a kanta yana barin falon. Irin kallon
da ya jima baiyi mata irinsa ba. Ya dade rabon daya sanya idonsa cikin nata,ya dade
rabon daya iya daga kai ya dubeta,tana hango abubuwa da yawa cikin idanunsa.

"Idan kika rubuta hakan yana bawa ameenatu tabbacin kinbar mata su dama dukkan wata
dama ko matsayi da zasu sake takawa a gaba.....kinbar mata su da dukka wani arziqi
da zai sake habaka nasu......kinbar mata dukkan wata alfarma ta amsa sunan UWAR ME
JADDA har abada......iya abinda kika samu daman rubutawa shine kawai naki rabon har
abada.....baki da wani sauran dama ko rabo a jikinsu saidai idan sun rigaki MUTUWA"
Maganar da shaidaniyar zuciyarta ke gaya mata kenan sanda yake dab da fita a
falon,abinda ya sanyata zabura ta miqe,sai wani irin jiri ya taso mata,amma cikin
tsananin taurin rai dana zuciya ta cije ta kuma soma takawa tana binsa da hanzari
gami da qwalla kiran sunansa.

Turus yayi ya tsaya gaban gate din gidan yana kallon tarin 'yan press
da suka cika qofar gidan maqil.

"Da gaske ne kenan yallabai.....mamarka itace tayi kidnapping d'iyar alhaji hamza
kibiya dake kwance a asibiti a yanzu tana jinya?,yanzu haka ma akwai d'iyar qawarta
a cikin gidan nan da tayi!kidnapping nata tsahon watanni ba'a sani ba me suna
laila?" . Wani abu yaji yana neman kayar dashi,abu daya ya saka masa sassauci ganin
yadda dukkaninsu suka sauke cameras dinsu a kanshi cikin nuna masa girmamawa.

Kasa magana yayi cikin tsananin mamakin yadda akayi!maganan ya
fita?,waye kuma ya gayyatosu?,amsar da ya sameta kai tsaye daga bakin wani dan
jarida.

"Mun samu half details na cikakken labarin daga wajen aminiyarta hajja
harira......ta kuma bamu tabbacin zamu samu full din daga bakin hajiya mariya
ahmad" Ya qarashe fadi sanda maamah ki fitowa da sassarfa tana qwala kiran sunan
fu'ad din.

Waiwayawa yayi ya zube idanunsa a kanta a sanda sam bata lura da taron
da dama ita suke kwadayin gani ba.....malam sa'adu ya tsaidasu da qyar ba,sai kawai
ya dauke kanshi ya kuma dubesu da dakakkiyar muryarsannan dake qara masa
kwarjini,wadda a yau take cakude da bacin rai yace.

"Ku bani hanya....bani keda labarin ba". Tsakiya suka buda masa ya fara wucewa da
sassarfa,bayajin akwai wani abu da zaiyi mata.....ba wani abu da yayi saura da zai
iyayi mata shi
"Fu'ad......a matsayina na mahaifiyarka ina me baka umarnin........"

"Yauwa.....shikenan ma.....gata nan ta fito" Yaji muryoyin wasu a cikin su suna
fadi gami da kunna cameras dinsu suka saitasu sannan sukayi kanta.

"Kada ki damu,wataqila sun soma fahimtar kece mahaifiya ga fu'ad din.....girman

Please Login or Register in order to submit comment