You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga yau har wani satin an maka uzuri fa.......ka samu nutsuwa yadda ya
dace dudu" Ya rigashi katse wayar wannan ya hana fuad gaya masa abinda yayi niyyar
fada din,sai kawai ya zame wayar daga kunnensa,qasan ransa yana fassara maganar
farouq da kuma sakata a inda farouq din ke nufi

"God forbid" Ya fada qasa qasa. Hasashen gaba days banbarakwai yayi masa sanda ya
dora tunanin a muhallin da farouq ke nufi,tattara tunanin yayi ya azashi a mizanin
shirme gaba daya,ya fara lalubar number amna.

Sai data kusa yankewa sannan ta daga

"Hamma" Ta fada a shagwabe.

"Hamma ka manta dani.....adda tayi taking dinka away.....as far as yadda zata iya"
Ta qarasa fadi da qaramar dariya a muryarta da ba sosai ta bayyana ba

"You amna.....lovey dovey will never be forgotten........hayaniya yayi yawa
amna.......bansan haka ake abun ba"

"Hamma yafi haka fa.....don kaqi bada hadin kai ayi komai" Hannunsa ya dora a
goshinsa yana furzar da qaramar iska. Shikam ko zancan bayaso,abinda yake gabansa
kawai yanzun shine damuwarsa.

"Ya gidan?" Ya tambayeta.

"Full with 'yan biki dake jiran walimar anni......ina yini hamma" Ta hade amsa
tambayar tasa da gaisuwa.

"Alhamdulillah.....how about anni da abba?"

"Abba dai ya fita tun dazun.....kuma ina jin sai dare zai dawo........anni tana
daga baya da mutane"

"Okay.....bata wayar"

"Okay hamma" Ta amsa shi tana miqewa gami da ficewa.

Bai yanke kiran ba saita maida kunnenta,tana tafiya wajen annin tana ta
bashi labarai kala kala. Bai yanketa ba yayi shuru yana saurarenta. Yasan halin
amna sarai,bata gajiya sam sam da hira.

"Kice ameh ya kirani....."

"Okay hamma.....ga anni" Saita miqawa anni wayar,ta samu plastic chair daya daga
cikin kujerun dake wajen ta zauna tana kallon yadda aka qawata wajen walimar da
wani irin tsari me kyau,tamkar wani hamshaqin event center.

"Barka da warhaka anni......ya hidima ya rana?" Murmushi ta sauke,har cikin ranta
farinciki yana mamayarta idan ta tuna a yau muhammad dinta ya zama cikakken
magidanci

"Barka kade me babban suna.....mun tashi lafiya zance ko mun yammata lafiya?".
Tambayar tata tadan sakashi yaji nauyi,kada itama fa ta dauka wani abune ya
boyeshi,kada ta fassara wani abu na daban akan yarinyar ma da bai samu daman
ganinta ba

"Lafiya anni alhamdulillah"

"Haka akeson ji.....na aika baraka takai muku breakfast da lunch.......nayita so
nace idan ta isa ta hadani da d'iyata mu gaisa saina sha'afa......in tana kusa bani
ita" Rasa abinda zaice yayi,yadan diririce kadan har hakan yaso ya nun alamu a
muryarsa,yayin da annin ta dauka wani abunne na daban ya kawo hakan,kodai baiso aji
muryarta a fahimci wani abu,don haka ta katseshi

"Kaga rabu da ita.....anjima idan kun iso wajen walima ma gaisa.....za'a fara
immediately after asr prayer"

"Allah ya kaimu anni.....Allah ya qara girma da lafiya"

"Ameen ya hayyu ya qayyumu" Ta fada tana jin dadin yadda sam baya gajiya da mata
addu'a.

Ita ta fara katse wayar,sai shima ya sauke yana kallon fuskar wayar.
Inda anni ta sani data qyale walimar nan,duk da ita walima duk inda take albarka
ce. Agogo ya kalla har daya na rana yayi,sai ya aje wayar yana jin zuwa yanzu ya
kamata ya laluba kitchen ya samu koda tea ne ya sanyawa cikinsa. Duka wani abu daya
saba sha da safe irinsu goji berries water da turmeric tea,cinnamon tea da
sauransu,wannan ya sanya yake da wani irin cikakkiyar lafiya da kuzarin da idan ya
shiga cikin maza kuzarinsa yake fita daban,kaman yadda yake da cikakkiyar lafiya
irin ta d'a namiji,wanda yayi imanin banda busy da business daya saka a gabansa
suka fatali da komai da yakeji......tabbas da bai isa yakai har wannan lokacin haka
ba,dalilin da yasa ya janyewa amfani da wasu abubuwan irinsu ginseng tea,sai time
to time idan yana da buqatar hakan,ko ya kwana biyu bai sha ba.

Fararen loopers slipper ya sakawa qafafunshi,wadanda suke mahadi ne na
fararen pyjamas din jikinsa da suka fidda siga da surarsa. Yanayin fatarsa kadai ya
isa ya fadi maka irin wadata da nutsuwa da yake ciki,skin dinsa so fresh da ba
lallai ta wata macen ta samu irin wannan kyan da glowing din ba.

Sai daya shiga toilet ya daura alwala,ya dauki qaramin towel ya tsane
ruwan jikinsa sannan ya maida takalmin ya nufi qofa yana gyara hannun pyjamas dinsa
daya tattare.

A nutse ta idar da sallara azahar tana maida idanunta wajen sujjadarta.
Tana jin idanun a jikinta sunyi mata nauyi,nauyin da bata raba dayan biyu yunwa ce
da kuma bacci. Baccin kam tana da tsananin buqatarsa,ita kanta ta sani,saboda ita
kanta tasan cewa taci bashin baccin yadda ya kamata,abincinne bata jin akwai
muhallin da zata sakashi a cikinta,saidai jikinta na sake gaya mata ya zama dole ta
nemeshi.

Dole ce ta sanyata miqewa,a nutse ta nade abun sallar,ta gyara yafen
dan madaidaicin hijab din data dauko daga closet din nata ta daure igiyar sannan ta
juya tana lalubar qofa bayan shawarar da zuciyarta ta bata nata duba cikin kayan da
aka kawo ko zata samu abinda zata saka a cikinta.

A nutse ya sauko daga saman yana sake jin nutsuwa da gidan da tsarin
gidan. Ya dauke idanunsa daga hallway din da yake kyautata zaton shiyyarta ne.
Qofan dake damansa ya karya zai bude sai kuma ya fasa,ya koma ya kama handle din
wooden door din ya bude yana isa ga falon.

Ko ina da komai yana nan kamar yadda ya barshi a jiya,da alamu ba'ayi
amfani da parlor din ba kwata kwata. Zarcewa yayi parlor din farko wanda keda
kitchen din,ya sauka daga kan step din a nutse sannan ya zarce zuwa dining da hake
hango basket akai,da alama saqon da anni tace ta aiko ne.

Yana daga tsaye ya miqa hannu a mamakance ya jawo basket din,yadda aka
kawoshi haka aka ajiyeshi,da alama ba'a ko budeshi ba ballantana a taba komai a
ciki.

Waye to ya karba saqon ya shigo dashi?. Ba kowa sai ita wannan shine amsar
daya bawa kansa,don ya sani ba wanda zaiyi gigin shigowa cikin gidan saboda sunsan
doka da kuma tsarinsa. Duk wani ma'aikaci dake aiki a qarqashinsa,daga cikin
company har zuwa cikin gida kowa yana tsayawa iya limit dinsa ne,ba wanda yake wuce
qa'idar aikinsa ko kuma limit dinsa.

Komai anni ta zuba na duka irin abinda tasan yafiso yaci da safe ya kuma
ci da rana,ya sauke qaramar ajiyar zuciya yana sake jin qaunar matar da martabarta
suna hauhawa a zuciyarsa. Baiga wani abu da zai taba annin ya bari ba ko
wayeshi,take sai yaji ransa yadan baci,ganin kamar ta wofantar da kayan da aka kawo
din. Daidai abinda cikinsa yake buqata ya zuba,kafin ya gama duka ya bata wajen
saboda rashin sabo,ya manta when last yayi serving kanshi,duk wani motsinsa akwai
masi hidimta masa.
Tsaki kadan yaja ganin bacin da wajen yayi,ya soma wassafa yadda zai
aje masu masa hidima cikin gidan kaman yadda ya saba,don bayajin zai bari ya takura
har haka,ya dauko komai cikin qaramin serving tray ya dawo ainihin parlor din,sai
ya azashi saman side table. Har zai zauna sai ya fasa,ya dauko remote yana lalubar
channel din dake haska rate na dollar pounds da rate na diamond da sauran harkokin
kasuwanci. Har yanzu yana cike da mamakin yadda abun ya kasance,duk da iya
bincikensa har yanzu ba wanda yasan daga ina faduwar gold din haka rugu rugu ya
samo asali.

Ya soma sipping pomegranate juice kenan idanunshi suka sauka akan
basket din. Tun basket din jiya da farouq ya hadoshi dashi,wanda shi kansa baisan
anihin meye da meye a ciki ba. Bacin ran da yaketa qoqarin boyeshi dole a wannan
karon ya bayyana kanshi.

"What's all these nonsense?" Ya fada can qasa labbansa suna motsawa.

Kamar jira akeyi yayi tambayar yaji alamun motsin mutum. Fararen
idanunshi ya daga still cup din yana saitin bakinsa,baikai bakinsa ba bai kuma dire
ba,ya zube manyan idanunshi a kanta. Karon farko da ya fara mata kallon kai tsaye a
rayuwarsa,karon farko da yayi mata kallon da zai iya gane face dinta.....don kuwa a
baya zai wahala ya iya cireta cikin mata goma ko biyar idan aka zube masa su.

Kwata kwata bata lura da mutum ba sanda take sauka daga steps din zuwa
qasa don nufar kitchen,amma da yake cikin dabi'arta akwai sanya idanu da kula da
motsin komai da komai dake kewaye da ita,da kuma sanya hankalinta bisa yanayin
kowanne abu saita dinga ji a jikinta kamar akwai wani baqon abu da babu shi dazu a
parlor din. Juyi biyu ana uku idanunta suka sauka akan nasa........itama karon
farko kuma lokaci na farko a rayuwarta datayi masa duba nakai tsaye.....duban dake
rataye da abubuwa masu yawan da suka faru.

Wani nannauyan abu taji yana fita daga idanunshi zuwa nata yana neman
kwarjanta mata shi da wani irin madaukakin kwarjini da bata taba siffantashi a
dukka hasashenta dashi ba,sai ta janye idanunta daka kaf sashen da yake tana jin
wani bala'e'en haushinsa yana sauka mata a hankali a hankali da wani yanayi me kama
da tsanar mutum. Shine silar komai da komai,shine kuma maja ragamar kowacce kalar
qaddara data sameta da kuma zata iya samunta a nan gaba.

Tashi zuciyar kuwa ta cika da mamaki a yanzun da idanunsa ke sake
haska mata qarancin shekaru qarara dake tattare da ita. Wani irin qyanqyaminta da
wasarta suna nasar zuciyarsa. A wannan age din nata da duka duka idan tayi wuta bai
wuce ace tana level one ba......amma s irin shekarun har take da fikirar SATA SANE
FASHI DA MAKAMI TA YANAR GIZO.....abu mafi muni kuma shine KARUWANCI BIN MAZA.

Wannan abu na qarshe daya tuna kadai ya sanyashi yaji zuciyarsa ta
sake matsewa. Koda aboki ne dashi yake da dabi'ar neman mata......ba aboki ba,koda
abokin kasuwancinsa ne kai muddin wannan din dabi'arka ce.....muddin kuma ta
bayyana ya sani to yana haqura da huldar kasuwanci dakai.

"Zunubinsa daban dude......haka mu'amalarku ma daban.....shi da Allah wannan halin
nasa,baka da ikon canzashi" Kadan daga cikin abinda Farooq ke yawan gaya masa.
Harara yake balla masa wani lokacin

"Bani da sha'awar karbar kudi daga hannun ma'abocin sabon ubangijinsa,wattaqu
fitnatalla tusibannal lazina zalamu minkum kaaassah(kuji tsoron fitinar da idan
tazo bata shafar iya wadanda sukayi zalinci kadai a cikinku).idan kana neman
albarka ubangiji cikin samunka....kayi qoqarin kaucewa masu saba masa,sai taka
dukiyar tayi albarka". Irin maganganun nan sun jima suna fafatawa a kansu shida
farouq.
Ji tayi kaman jikinta na neman rasa duk wani confidence.....hakanan
batason wanzuwa a muhallin da yake fesar da iska tana shaqa,sai taji kamar wadda ya
fitar ita take zuqa,don haka ta juya a nutse da zummar komawa inda ta fito,tana ji
har cikin ranta ta haqura da duk uzurin daya fiddota.

"Ke!" Ta tsinci husky voice dinsa da bata taba jinta kamar haka a kusa kusa ba sai
yau......karon farko kenan,wannan ya hadu da saukar tsawar tasa ya sanya gabanta
wani mummunar faduwa.....kafin ta samu tayi hanzarin daidaita nutsuwarta da tattara
dukka qarfin ta.

Zuciyarta ke qarfafarta kada ta tsaya.....salon kiran da yayi mata
din zallar raini ne.......yayin da ta nashi gefen ya fita hasala.

Ya za'ayi ya kirata yarinya qarama irin haka tace zatayi ignoring
nasa?,yarinyar da yayi imanin tsakanin musaddiq da saddiq ma babu sa'anta......koda
ta girmi amna ma kuwa yayi imanin ba zata bata sama da shekara uku ko hudu ba.

"Na rantse qafarki ta sake taku daya daga nan saina kakkaryaki na zubar" Ya fadi a
hasale,saboda abinda tayi masan bazai tuna mutumin daya taba masa hakan ba tun
sanda sunansa ya shiga duniya a matsayin muhammad fu'ad jadda.

Batasan me yayi mata birki ba,har ta daga qafar zata taka step na
farko saita mayar ta ajiye. Zuciyarta na mata wani irin suya a qirji. Ita yau
sabreen wani d'a namiji ke kwatsawa tsawa har haka?,saboda kawai yana tutiyar ya
aureta?.

"Dawo ki zauna!" Ya sake fada a kausashe har sai da taji kaman yana daf da ita ne.

"Ki sake na maimaita miki kuma....wallahi yau a cikin dakin karnuka zaki yini" Ya
furta muryarsa na bawa me sauraro tabbacin da gaske yake.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 17


18


Wasu maqalallun hawaye da bata tsammacesu ba taji suna tsatsafowa daga
cikin qwayar idanunta,tayi hanzari da gaske ta dakatar dasu cikin bawa zuciyarta
umarnin

"Ba faduwa.......ba bada damar ganin lago.....i want to win". Abinda ya saka
hawayen komawa kenan,saidai har yanzu tana jin alamunsu.

Ta koma ko ta wuce abinta?,duk abinda zaiyi ma yayi?,ko kuwa ta zauna
ya lissafa nasa qa'idojin itama ta sanya mishi nata iyakokin?. Bata tantance wanda
zata dauka ba saiga kira ya shigo wayartata. Kallon wayar kawai sai taji tamkar
wata sabuwar barazanar ce ta shigo cikin rayuwarta,sunan matar datayi saving dai
still shi yake yawo. Abisa son ranta bata da Sha'awar sauraronta.....amma bisa
tilastawar zuciyarta sai taji ba zata iya tsallakewa kiran ba,a sanyaye ta daga ta
saka wayar a kunnenta.

"Tun dazun nake zuba idanun ganin kiranki ai.....na dauka zaki nema taimakon abu na
farko da zaki fara girkawa a gidan" Muryar maamah kenan da kalamanta na farko data
fara jerowa baya ga amsa sallamarta da tayi. Idanunta data lumshe ya tilastawa
boyayyun hawayenta saukowa,amma sai tayi hanzarin daukesu tana sauraren muryar
matar.

"Na manta na gaya miki wannan ko zasu taimaka miki wajen cimma nasara........yana
da zafin rai.....yana da kafiya,bayason raini bayason musu.......bayason
qazanta........kiyi duk yadda zakiyi ki zama ke kike ci dashi......ki sadaukar da
komai masa......ki qarar da tunaninki kan duk hanyar da zaki maido cin abincinsa
hannunki.......wannan shine kadai abinda zai sama miki 'yanci....." Saita dakata
kamar me shirin bata damar cewa wani abu kafin ta qara

"Idan kina da tambaya ko buqatar qarin bayani qofa a bude yake......zuwa anjima
kina da baqi......saidai mutum daya ta qaru.....zan miki bayani a kanta.....af na
manta na gaya miki.......dazu huda ta tsallaka shop din tsallaken titin gidanku
fa". Mummunar faduwa gabanta yayi da ambatar sunan huda kawai a bakin maamah... Da
gaske mutanen suke......sun mata tarko da 'yan uwanta,da gaske suke suna bibiye ne
da rayuwar 'yan uwanta mahadin numfashinta?,da gaske kowanne motsi nasu a lissafe
suke dashi?. Tabi maganar maamah ta tseratar da rayuwarsu?......a yanzu tana jin
kamar shine babban haqqin daya zame mata dole ta sauke.

Batasan ya iso wajen ba,kawai abinda taji shine zare wayar daga
kunnenta. Ba qaramin firgita tayi ba,saita waiwaya da hanzari tana fuskantarsa
sanda ya zubawa fuskar wayar idanu lokacin da kiran yake yankewa da sunan mariya
b'aro baro akai.

Ci gaba yayi da kallon fuskar wayar har sunan yayi disappearing yana
sake maimaita full name din nata qasan zuciyarsa. Wani abu ya taso
masa.......zarginsa yana daduwa daga kaso sittin cikin dari zuwa kasu casa'in da
tara cikin d'ari.

A nutse ya maida qwayar idanunsa kan fuskarta,haka kawai taji
qafafunta sunyi laushin da kafin ya sake cewa komai ta koma ta zauna saman kujerar
dake daura da ita,tana mamakin yadda nature da colour na idanunsa suka sauya kadan.

Wayar ya cilla mata ta sauka daidai saman cinyarta,sai ya soke duka
hannuwansa cikin aljihun wandonsa yana dubanta kai tsaye.

"Kada ki dauka zakiyi duka irin rayuwar da kikaga dama,kada ki dauka zakiyi kalar
rayuwar da kikeso.....kada kuma mi rudu da cewa kinzo nan gidan don ki huta......ki
debi adadin kudi da dukiyar da kikeso daga jikin muhammad jadda.....idan kin dauki
duka wadannan abubuwan a ranki......" Sai kawai wani siririn murmushi ya kubce
masa,ya cije redlips dinsa yana dage kafadunsa sama

".......kina ruwa" Ya qarasa fada yana jawo wata ottoman chair 'yar qarama zuwa
gabanta yahau kai ya zauna

"Kisa a ranki nan kin shigo gidan tarbiyya da gyaran hali ne......gidan qare
kukanka.......gidan bin daidai.......wadancan kayan duka da aka shigo dasu kin
dauka a caca aka ciyosu?,ko kuma fashin yanar gizo da kutsewa account din al'umma
akayi aka samosu da zaki bar komai cikin jakarshi?,salon idan ya lalace baki da
asaran komai?" Wasu irin zafi sosai maganganunsa sukayi mata,irin zafin da bata
taba kawowa ba. Ko mahaukaciya ce ita ta fuskanci inda batunsa ya dosa ballantana
da hankalinta fes,zafin maganar ya tilastata daga oily eyes dinta masu sheqi dake
shige da nasa ta kalleshi dasu.

Duka girarsa ya dage sama yana dubanta da fuskar da babu digon walwala ko
sassauci a ciki

"Yes.......gidan nan dama komai da zai gilma a ciki zallar halak ce ta samar
dashi.....so that bazan dauki almubazzaranci ba......dole ki kula da komai a daidai
sanda ya dace da yanayin daya dace.....zaki zauna a cikinsa kiyi aiki irin na
kowacce matar aure......zaki zauna a cikin gida kamar yadda musulunci ya
tanada......zaki kuma zaman gyara halinki yadda zaiyi daidai da halin mataye na
gari,ta yadda wataqila a gaba idan kin hadu da wanda kika dace da ra'ayinsa,zai
dauki mace ta gari ba makwadaiciya me qarancin duka wata siffa me kyau ba.......".

Banda sunansu huda,da zabin maamah dake mata amsa kuwwa cikin kwanya
batajin zai fadi dukka wadannan kalmomin bata zazzage masa fiye da abinda ya gaya
mata ba. Ba zata iya tuna cin mutuncinta da akayi a duniya da yakai wannan muni
ba......cin fuska irin wannan a gaban idanunta,cikin salo na gadara da ganin isa.

A nutse ta daga idanunta da wani irin coolness ta watsasu saman
fuskarsa. Kallon kallo suka yiwa junansu na wasu sakanni,kowa da abinda ke gudana
cikin zuciyarsa game da dan uwansa. Fuska ya sake tsukewa sosai ya dage dukka
girarsa biyun

"I told you.....your attitude needs a serious adjustment.......bazanyi tolerating
any nonsense ba.....just obey all of my rules" Yana kaiwa nan ya miqe a nutse yana
ajiye mug din sannan ya sake zuba hannunsa a aljihun wandonsa still yana kallonta.

"If you have any plans i beg you kada ki fasa......if you collect some money or
something else.....kiyi duk abinda kike ganin kin tsara" Yayi maganar wani abu
yana taba zuciyarsa,zarginsa kuma yana sake qarfi a kanta da ganin sunan maamah
kawai cikin wayarta. Wani mahaukacin bugun zuciya ya haifar mata,ba shiri ta sake
daga kanta zuwa gareshi sanda yake barin wajen. Wannan karon kam duk qwarewarta
wajen iya boye hawayenta abin ya faskara,fara tsiyaya sukayi kafin ta sake jin
muryarsa yana fadin

"Qarfe hudu akwai walima wajen anni......bana african time don ban sanshi
bama.....i hope you get it" Ya sake fada ba tare daya waiwayeta ba.

Kasa tashi tayi a wajen wani irin baqinciki yana nuqurqusarta.
Tsantsar tsana da haushin maamah yana sukar zuciyarta. Bata qyale ire iren wadannan
abubuwan.......ba abinda yake sakata sarewa ko fargaba,amma ta mata mugun qulli da
dabaibayi da 'yan uwanta?,why?.....me su huda sukayi da zata sakasu a wannan
wasan?,me yasa ba zata bari suyi tsakaninsu ba a nan zata fahimci wacece sabreen
din....muhammad jadda......yana buqatar ta karanta masa karatun d'iya mace,if gana
expecting taka kowacce mace don yana da dukiya da kuma kyau......zata so ta zama
macen farko da zata banbance masa tsakanin aya da tsakuwa,amma a yanzun hakan kuwa
zai yuwu?.....she needs to be very humble don ta kubutar da 'yan uwanta......but ba
zata dauki raini wulaqanci da kuma cin fuska daga wajensa ba,wannan shine lokaci na
qarshe da zata bari ya jera mata maganganu masu zafi irin wannan,zata saka dukkan
effort dinta donta gamawa maamah aikinta cikin sati biyu ta kauce ta barsu da
rayuwarsu su qarata,idanma gasashi zatayi ta cinye dukka damuwarsu ce.....itama
nata familyn ta sani,zaman lafiyarsu da kwanciyar hankalinsu shine first priority
dinta.

A nutse ta miqe ta ta soma kauda komai badon maganganunsa ba....sai
don da gaske bai kamata abar komai a wajen ya lalace ba. Neman abinci da samunsa
abune me matuqar wahala wanda itace shaida akan hakan. Ta killace komai sannan ta
tattara ta wuce zuwa dakinta,saidai qasan ranta cunkushe yake da wani irin bacin
rai tare da lissafe lissafe masu yawan gaske game da yadda zata tunkari rayuwar.

"Don't be sad.....kada ki takura kanki da yawa.....just live your life normally
yadda ba zaki cutu ba" Abinda zuciyarta ta dinga nanata mata kenan.

Akan idanunta biyu ta buga uku tazo ta shude aka doshi hudu. Bata dako
niyyar shirin komai bare akai ga batun zuwa walima. Komai nasu baya
burgeta......bata da buqatar kuma ta cudanya dasu sam sam.

Daidai lokacin da yake samanshi bayan dawowarsa daga sallar la'asar.
Yaga kira daga security din dake waje sun shaida masa yana da baqi gasu zasu shigo
ciki. Tunda yaji haka yasan 'yan gida ne.....inda baqin fuska ne lallai saisun nema
izini an basu kafin su barsu su shigo,sai ya qarasa shiryawa cikin shaddar daya
dauko,don already wandon yana jikinsa kafin yayi receiving call din.

Wagambari ce a jikinsa,asalin tsadajjiyar wagambari sky blue da aka yiwa
wani irin dinki na alfarma dake nuna zallar zamani da kuma sanin darajar ado da
dinki. Ba wani mutum da zaiga sutura a jikinsa ya sake ganinta ya maimaitata,kusan
sakawa daya yakewa kaya ya gama dasu,shi yasa duk sati cikin fidda suturunsa ake.

Gaban madubi ya tsaya yana karya hular da zai sanya,shi gaba daya a
takure yake,ire iren wadannan sabgogin bai saba dasu ba kwata kwata,wani harkar
taro na biki,idan kanason ganin karsashinsa kazo sashen maganar kasuwanci. Kayan
jikinsa kansu nauyi sukeyi masa,baisan ma me yasa a kayansa na wannan watan aka
hada masa da dinkin manyan riguna ba,amna daya tuna farouq sai ya tabbatar shirinsa
ne kawai.

Halfcover ya sakawa qafarsa dan qasar italy da akayi cinikinsa da
dollars masu yawa. Ya sanya hular saman kansa take wani irin mutum.....lafiyayyen
half cast ya fito me matuqar daukan hankali da kwantaccen kwarjini daka iya wucewa
da zuciyar kowacce d'iya mace.

Waya daya ya dauka kawai sannan ya soma barin dakin. Yana sauka ne
cikin takunsa dake bayyanar da nutsuwarsa jin kansa da kuma kamun kansa irin na
cikakken namijin daya hada abubuwa da dama.

"Wow summa wow.....hammana" Muryar amna ta fara sauka a kunnensa sanda yake fitowa
zuwa parlor din.

Yadda tayi maganar ya sanya murmushi subuce masa,ta kuma tuna masa da
lokutan baya da yake very free ba kaman yanzu ba. Kullum ita ke bawa kwalliyarsa
mark,anni na zaune a gefe tana musu dariya,saddiq na tsokanarta wani lokaci harsu
sanyata kuka,shike tare mata shine ke hanasu.

"Hamma ka sake zama ango sak......don Allah BB farouq,kalli ta nan gefen" Sai
datayi maganar ya lura da farouq dake zaune kujerar qarshe riqe da wayarsa yana
dannawa. Kadan ya daga kai ya kalleshi ya maida ga wayarsa

"Yayi kyau mana amna.....amma kubarni nima soyayyata nake qoqarin
gyarawa......Allah bazan qara wata uku a qasa ba.....guy dinnan daga jiya zuwa yau
kalleshi ya sake canzawa?".

"Stop it farouq......" Fuad yayi saurin fadi yana duban amna kafin ya maida
kallonsa ga farouq din. Ya fahimci sarai abinda yake nufi,akwai amna a wajen

"Hamma........am eager to see my aunty wallahi.....where's she?" Ta furta alamunta
na nuna da gaske sabreen takeson gani,tana jin qaunarta sosai har cikin zuciyarta
saboda hammanta.
"Jeki fito da ita" Ya fada yana yiwa amna nuni da hanyar. Bata ko tsaya sauraren
komai ba ta wuce wajen da sauri saurinta.

Qarasa takowa yayi wajen da farouq ke zaune bayan wucewar amna din,aje
wayar farouq din yayi yana dubansa.

"Mutumina......akwai labari kenan" Ya qarashe zancan

Please Login or Register in order to submit comment