You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka shirya
motoci ta fice zuwa gidan anni.

Ta samu amare sunata wani glowing kaman wadanda anni ta dauka ta jefa
cikin engine aka sauyo mata da wasu,duk da dama daga amna har huda kyan fata
garesu.

"Aah,mrs saddiq and musaddiq" Sabreen ta fada cikin salon tsokana. Abun mamaki wai
yau ita suke kunya,kowacce sai ta sadda kai,saidai kuma yanayin amna data gani
kaman ba yadda ta saba ganinta ba.

Duk da akwai surukuta sosai tsakaninta da anni,amma ta dan sake wasu
abubuwan da ba zasu zamto zaqewa ba ta shiga anyi da ita. Lefen data gani wajen
anni akwati ashirin da hudu na huda ashirin da hudu na amna,guda biyu arba'in da
takwas kenan. Daki daban anni ta saka ta shiga tana nuna mata wasu designers
akwatunan guda sha biyu samfurin shekara mai zuwa,wanda akayi lunching nasu a dubai
cikin satinnan. Ita tsoro ne ma ya kamata da anni take gaya mata wai nata ne,ya
ilahi ina zatakai wadannan?,kada ya jawo mata baki fa na jama'a.

A daren suna video call take jeranta masa kalaman godiya,kalaman da
suka sake kashe masa jiki da zuciyarsa,yaji kaman zai narke saman sofa din da yake
kwance akai.

"Sabrrrr" Ya kirayeta,wanda kiran kawai ya gaya mata yanayin da yake ciki.

"Anya ba gobe zan taho ba?,anya duniyata?". Dariya ta qyalqyale masa dashi tana
tsokanarsa.

"So kake BB da fannah suce nice na hanaka?,kayi haquri please,awa arba'in da takwas
ne kawai".

"Allah ka bani juriya" Ya fada yan lumshe ido,yana jin wata kewarta tako
ina,tattausan skin dinta me qamshi laushi da santsi.

β˜…Randa FU'AD ya sauka ranar fanna tayi bridal dinta,baije ba farouq ma bai
matsa ba tunda yasan bame son zuwan bane. A rana ta biyu ne akayi zaman ajo,wanda a
wannan zaman kudi sukayi rana.....dukiya tayi kuka da idanunta,ya nunawa BB dinsa
qauna irin wadda ta sanya farouq tara hawaye sosai a Idanunshi.

"Karka yadda kayi mana kuka gaban mata da tarin mutane,idan kayi hakan bamu yafe
maka ba.....wannan kukan ka riqeshi sai sanda kuka kebe......idan ba haka ba za'a
dauka lusari ta aura" Ya fada kadan a kunnen farouq bayan ya gama zazzage pound
cikin abinda aka ajiye saboda zuba ajo din,don yana gama zubawa aka dauke abun,ya
riga ya cika sai wani aka sanya.

Tofa......nan idanu dama hankulan 'yammata dama zaurawa masu lokaci
yayo kan FU'AD din,taron mayu bawai na maita ba......mayun mata.....ma'abota son
kyakkyawan namiji me abun hannunsa hankulansu ya tashi. Kowacce isassace me aji
tana jin takai,don me qaramin class ma baya suka dinga ja suna rufawa kansu
asiri,saboda sunsan kalar zaren ba kalar yadin bane......saidai su kansu isassun
sai rab'e rab'e,an rasa zaqaqura me qarfin halin tunkarar me jadda din.....kwarjini
yanata aikinsa.

Mota ya koma yayi zamanshi suns hira da duniyarsa,video call kaman ko
yaushe,ta daga masa hannuwanta da sukasha wani irin jan lalle,tun daga tafin hannun
har zuwa bayan hannun nata.

"Ya salam" Ya fada yana jin wani abu ya harba a jikinsa.

"Nawa me qunshin nan takeso a bata?".

"Anni ta biya mana ni dasu amna.....beside ma ai ka ban kudin da zai isheni kalar
kowacce hidima".

"No....kudin dana baki ban bakishi bane don kiwa kanki komai ba,na baki shine don
ki wata hidimar daban,zan saka miki a dollar account dinki,saiki cire".

"Allah yabarmin kai jadda na.....Allah yajamin da ranka uban 'ya'yana" Ta fada tana
jin kanta yana fasuwa,bada komai ba kuma,da zallar kulawa.....da kalar mijin kuma
data samu.

Sanda suka koma guest in dinsu farouq shine qarshen shigowa,bai kuma
tashi shigowa ba sai daya na dare. A sannan FU'AD yana zaune saman abun sallah yana
addu'o'insa,wanda duka ta neman dacewa da alkhairai ce duniya da lahira shida 'yan
uwansa dama dukkan wani masoyinsu(harda ku fans na DUNIYATAπŸ˜„).

Ido suka hada FU'AD ya janye idanunsa yana hade rai.

"Wanne irin abune wannan?,zaka ajiye.mutane kuma ka tafi,baka tashi shigowa ba sai
tsakiyan dare kaman wani barawo?" Wani dariya sosai Farooq ya saki yana qoqarin
cire babbar rigar jikinsa.

"So sorry dude.....kasan abinka dame iyali kuma farin shiga.....inacan ina
lallashinta wai yatsunta sun gaji......ga tafiya kano gobe donma flight ne.....".

" A gidan ubanwa ta zama iyalin naka?" Ya fada adan fusace,don ya kira sabreen yaso
suyi hirar dare bai sameta ba.

"Ka rabo mutane da iyalinsu kuma kazo ka ajiyesu?". Ido farouq ya fiddo,yanason
fashewa da dariya amma ya danne

"Ikon Allah....to ni me zan muku idan nazo din?,qarqari muyi hira fa?,kuma yanzu
tsakani da Allah saboda rashin imani wanda keda sabuwar amarya ai abun a masa uzuri
ne ko?.....to kuma ma naga wancan lokacin naka daurin auren.....qasarma ka bari
kaqi dawowa ka barni da amaryar da abokan gaba daya.....wannan rashin adalci ne
dason kai dude".

"Farouq....gori zaka yimin?....gate out please ka barni naji da damuwana" Wannan
karon duk yadda yaso boye dariyar ya kasa,sai kawai ya saki abarsa yana nufar
toilet.

"Bani nakar zomon ba.....ratayar ma ba'a bani ba.....iyali me dadi.....ashe haka
lamarin yake dama" Ya qarasa fada yana shigewa gami da turo qofar.

Qwafa fuad ya saki,sai kuma murmushi ya qwace masa. To meye ma laifin
farouq a ciki?,ita kanta sabreen din bata da laifi tunda tace masa zata aje wayarta
dama,kawai dai iya shegensa ne ya motsa,da alama kuma ramuwa yakeson yayi masa.
*_ALQAWARIN ALLAH baya tashi_*


"An daura auren umarul farouq hamza kibiya,da fannah maisharif
babaghana......jama'a kun shaida?". Sautin daya sanya fu'ad sakin tattausan
murmushi yana furta.

"Alhamdulillah......alhamdulillah"


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 140


*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA
KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA
IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE
SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA
A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_
08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*



140


Daga nan inda yake yana hangen sadakin fannah dake bada tabbacin ta
zama ta farouq dinsa halak malak......hakanan yana iya hango farouq dake tsakiyar
abokansa wanda shigarsa bata da maraba data jikin fu'ad din,sak da sak kaman yadda
sukayi a bikin fu'ad din.

Lafiyayyen walima aka gudanar a gidan gwamnatin jihar borno bayan
kammala daurin auren da tarin abokansu masu jini a jika,wanda kowannensu wani ne
shi ta fannin ilimi da abun duniya.

Ana gamawa fu'ad ya wuce masauki yabar farouq da tarin abokanshi,don
shi bazai iyama wannan iya shegen nasu ba,sun sanyashi a gaba sunata abubuwansu
daya tabbatar sai yayi trending a social media. Tunda akayi hotuna wajen reception
din yayo gaba,don akwai shirin da yakeso yayi.

Ruwa ya fara watsawa ya fidda wayarsa,kai tsaye ya kira duniyarsa.
Daidai lokacin tana zaune suna kallon reception da daurin auren da ko awa guda
ba'ayi da yinsu ba amma har an warwatsa a media.

Kishin fu'ad ke taso mata sosai saboda ganin tarin comment din yammata
a kansa. Shi kadai amma ya fita daban a cikinsu,komai nasa daban yake,wani irin
kwarjini me hade da nutsuwa da suka qarawa fuskarsa kyau da kuma kamala.

_"Lallai baaba ma da babansa fa.....duk kyan azurfa bata kai ya gold ba.....the
jadda.....guy dinnan daban yake fa❀️‍πŸ”₯
"_ comment din wata daya gilma kenan daya sanya
zuciyar sabreen quntata,ta kuma ture screen din daga fuskarta tana jan wani qaramin
tsaki,can qasan ranta kuma tana mita.

"Bansan me yake damun 'yammatan yanzu ba,kamar mayunwata suke akan maza.....idan
suka saka namiji a gaba baji ba gani?,ba kunya ba aji ba kamun kai?" Daga huda har
amna sun fahimci me takewa qunquni,sai suka qunshe dariyarsu saboda zuwa yanzun
suma suna jin tasu soyayyar da angwayensu har cikin jininsu.

Kayanta take hadawa dama,saboda tanason wucewa gida ne kafin su
qaraso,tanaso ta kimtsa ta tarbeshi da kyau,idan yaso gobe sai ta dawo gidan annin.
Kiran wayarsa ya sanya ta ajiye duk abinda takeyi,ta kuma daga kiran tana samun
wajen zama.

"A ina kake?" Tambayar data fara masa kenan wadda ta bashi mamaki.

"Na dawo guest house masauki.......me ya faru?" Wata sassanyan ajiyar zuciya ta
saki,tana jin dadi daya dawo din,at least ya tsira daga kallace mata shi da
wadancan mayunwatan 'yammatan sukeyi.

"People are commenting about you everywhere
You're all over social media muffin" Ta fada da wata irin narkakkiyar shagwaba.

"What?" Ya fadi dariya nason qwace masa.

"Like nine angon?" Ya sake tambayarta.

"Am serous muffin" Ta sake fadi tana narke masa.

"Am all yours......am yours forever my World" Ya fadi da wani irin calmness daya
bawa zuciyarta nutsuwa. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta soma gaidashi.

"Ya taron?"

"Alhmdlh.....but babu dadi coz bakya kusa dani".

"Nan da awanni kadan zamu kasance tare in sha Allah" Ta fada tana bashi confidence.

"In sha Allah" Shima ya maimaita. Lafiyan yaranshi shine next abinda ya qara
tambaya,tayi murmushi tana dora hannunta saman mararta data fara tasawa tana bashi
amsa.

"They're fine.....suna gaida abbunsu.....sunyi missing nasa"

"Me too my world.....akwai kyakkyawar gaisuwa tsakaninmu idan na dawo.....so get
ready,be at home as soon as possible"

"Yanzun nake shiri in sha Allah"

"But.....karkice zaki fita da mota daya....ki jira su abdulgafar zasu kaiki har
gida.....and nace su qara yawan security na gidan". Ya fada da serious murya.

"I hope komai lafiya ko?" Kai ya jinjina,kawai yana jin wani abu daban a jikinsa.

"Lafiya.....in sha Allah" Ya fada yana son tabbatarwa da kansa haka.

Cikin nuna tsananin kewa da qaunar juna sukayi sallama shida ita,kai
tsaye kuma ya kira abdulgafar.

"Zamu qaraso gurin qarfe biyar......get ready please,a qara yawan security a
airport da gida na harda gidan anni......har gidan farouq.....if possible inaso
kowa cikin ku ya zama ankare da kowanne parts".

"As you wish sir" Ya fada cikin girmamawa.

"Ku rakata gida safely abdulgafar......bazan iya jurewa ba if something happen".

"Bazai faru ba sir in sha Allah"

"Good abdulgafar" Ya fada yana yanke kiran.

Iska me zafi ya furzar daga bakinsa yana dan wani gajeram tunani da shi
kansa baisan na meye ba,sake daukan wayarsa yayi ya tura rubutaccen saqo ga duk
wani guard da suke tare dashi a halin yanzu haka a maiduguri,sannan ya sauka yana
laluben wayar farouq don jin yadda zasu shirya tahowa kano kada lokacin tashinsu ya
fita.


β˜… Daga samanta tana iya hangen yadda duk wani shige da fice yake gudana
cikin gidan hamza kibiya. Wani ajiyayyen qullutun baqinciki ne yake tsaye a
wuyanta,shi bai fita ba shi bai sauka ba. Idan akace mata a baya nasararta zatazo
da irin wannan salon tsaf zata qaryata......a irin wannan yanayin zata iya cewa
bikin d'anta akeyi.......amma koshi yaron nata bata samu martabar ganinsa ba bare
ta shiga lamarin bikin,balle kuma ta samu girma da daraja irin na kowacce uwa.

Agogo ta kalla,tana jin ta matsu ta kuma qagu komai ya faru,tana jin a
ranta afkuwar komai din shine zai bawa abinda ya tsaya mata a wuyan damar fadawa.

Knocking akayi sannan aka turo qofar dakin. Bata damu ta waiwaya kota
tambayi waye ba har zuwa sanda ta fara magana.

"Maamah ga abincinki fa,tun na safe bakici ba.....na rana ma haka,ga na dare a
hanya,kuma likita yace ki dinga kula da abinci ko don yanayin ciwon...."

"Ciwon ubanki?.....nace ciwon ubanki?". Ta fadi tana katse laila da dukka tashin
hankalinta ya tattaru ga ganin alamun maamah din tana cikin damuwa,tashin hankalin
da takeji tana jin yafi wanda maamah dimma ke ciki.

"Maamah kiyi a hankali ki daina fushinnan ko don lafiyark......".

"Waini sa'arki ce?,to kiji na gaya miki na rantse da Allah kika qara Dangantani da
wani cutar hawan jini saikin gwammace uwarki hajja bata haifoki na......idanma
qullawa kukayi don ku cuceni ku kasheni saboda ba idon 'ya'yana ko to?,to kunyi
qarya kun kwana da yunwa,ni mariya warki ce daidai qugun kowa.....ni mariya kuma ni
kad'aice gayya......fita kiban guri" Ta dakawa laila tsawa tsawar da har saidata
zabura.

"Allah ya baki haquri" Ta fada ta juya tana fita a dakin kaman zata kifa.

Fitar laila sai ya zama kamar ta fita da iskar da take shaqa ne,take taji
iska tana mata kadan,wuyanta ya soma riqewa iskar bata samun daman isa ga hunhunta.
A daddafe ta samu waje ta zauna tana qara gudun fanka da Ac din dakin,wani irin
haki yana sarqeta. Likitan ya gaya mata,kada ta yarda ta fadi muddin irin hakan ya
sameta tana a tsaye,idan ba haka ba komai zai iya faruwa.

Ta kusa mintuna talatin a haka kafin taji a hankali numfashinta yana
daidaita har ya koma normal. Wayarta ta jawo,ta kira number wayar da take sanya ran
shigowar kiranta tun dazu.

"Baki da damuwa.....muna ankare da kowa da kuma komai.....ki jira jin sakamako daga
yanzu zuwa gobe da safe"..

"Godiya nake" Ta fadi tana ajiye wayar tana kuma sake jin relief sosai a ranta.

Cikin wani irin mugun matakan tsaro jirginsu ya sauka,yayin da baqaqen
motocin dake dauke da tambarin JADDA kimanin ashirin sukayi convoy cikin wani irin
tsari me daukan hankali da kuma matakan tsaro sosai bisa umarnin fu'ad.

Lafiya lau suka qaraso unguwar,suka kuma jera kansu zuwa kyakkyawa
kuma makadediyar harabar mansion House din alhj hamza kibiya.

Duk wani dake da jibi da ahalin alhj hamza kibiyan yayi tattaki ya fito
daga cikin gidan,yayi tsaye a farfajiyar saboda girmamawa ga fannah,wadda aka fito
da ita nannade cikin wata lafiyayyar Cotton lafaya butter colour da ratsin maroon.

Yana daga cikin motar amma yana iya ganin komai,yabi kowa da ido da
yadda abun ke kasancewa,sai yaji wani abu yana taso masa,don haka ya maida idanunsa
ya lumshe.
Lallai babu wani babban arziqi a duniya irin uwa ta gari......babu wani
babban jin dadin rayuwa irin samun uwa ta gari.......alhmdlh yana godiya ga Allah a
bisa dukkan ni'imomin da yayi masa,kuma ya karba cewa tasa qaddarar tana kan
MAHAIFIYARSA tasa jarrabawar tana kan UWA da Allah ya bashi.

Amna dake nade cikin tata lafayar sai wani irin farinciki taji yana
lullubeta,tana jin kamar suna dab da gina wani babban ahali ne,yau BB farouq
dinta.....ya saddik,ya musaddiq da hammanta dukkaninsu yana da matar aure,wadannan
matan kuma kowacce ana sanya ran zata basu baby,babies din da zasu taru su zame
musu wata tawaga kuma family na musamman.

Kasa jira tayi a qaraso da fannah,saita taka da dan hanzarinta tana
cimmata ta riqe hannunta,abinda yasa matar dake riqe da fannah din sakin hannunta
taja baya,wannan ya bawa amna daman magana da ita qasa qasa.

"Welcome to alhj hamza family,welcome to jadda family adda fannah......bansan ya
kuke cewa adda da kanuri ba.....anyway muna miki maraba".

"Na gode" Siririyar muryar fannah ta fita wanda ta tabbatar ita daya ta jita.

Cikin girma da martaba dangin anni dana abba suka amshi fannah aka
qarasa ciki da ita,bayan anyi addu'a an kuma bawa su anni amanarta,sai annin ta
sanya aka ware daki daban aka bawa fannah din ta huta suci abinci sannan sai a wuce
da ita gidanta,hakanan danginta suma aka basu wani dakin daban.

Sai data tabbatar babu kowa a dakin sannan ta yaye lafayar dake kanta.
Amna da huda ke dakin,hudar da sam ta kasa sakewa,ta hana kowa ma ya ganta
throughout saboda surukuta da takeyi da dangin anni.

Musayar murmushi sukayi,amna ta nuna huda.

"Wannan itace huda.....qanwar adda sabreen,matar ya saddiq" Lokaci daya huda ta
yiwa fannah,ta miqa mata hannu sukayi musabaha. Ita da amna sai take jinsu karon
farko kaman qannenta,don ta tabbatar ta girme musu,saidai ba wani da yawa bane.

Qaramar walima akayi cikin gidan,baqi sukaci suka qoshi suka
huta,sannan anni ta bawa fannah kyauta irinta surukuwa kaman yadda ta yiwa sabreen.


*_ME FARUWA!_*


Tun bakwai da rabi aka soma shirye shiryen qarasawa da fannah gidanta.
Musaddiq da saddiq ne akan komai na game da shirya motocin da za'a dauketa a qarasa
da ita ainihin gidanta dake maqociyar unguwarsu.

Tunda aka fara jera motocin daga harabar gidan zuwa qofar gidan amna ta
kasa zaune ta kasa tsaye. Tana bala'in son zuwa gidan ya farouq,wannan yana daya
daga cikin mafarkanta tun kafin tasan rayuwa zata juya lokutan aurensu guri
guda,tun kafin ta taba tunanin zata kasance qarqashin igiyar auren yaa musaddiq a
wannan lokacin.

Yadda kowa ya shirya haka ta shirya,tanason ta tambayi ya musaddiq ko
shi ya dauki mota subi ayarin kai amare,a qalla tana tunanin bazai hanata ba,tunda
zai wahala idan ta shiga nata gidan ya barta fita da wurwuri,don musaddiq din wani
irin tsaro ne dashi tun wancan lokacin ballantana yanzu data zama mallakinsa.

Zaune tayi tana gwada wayarsa,sai data kirashi a qalla sau hudu
sannan ya daga.
"Ya akayi baby doll?" Cikin shagwabar nan tata ta narkar da kai.

"Besty.......gidan amarya please,don Allah muje" Idanunsa ya waro waje kaman tana
gabansa.

"What?.....aah karmu fara haka dake babe.....zakije amma bayan munyi wasu
watanni" . Kukan shagwaba ta sakar masa wadda ta qarasa susutashi,da qyar da ban
baki ta shawo kansa.

"Amma kinsan anni zatayi fada ko?".

"Karka gaya mata please,nayi alqawari muna zuwa zamu dawo". Shuru ya danyi,bayan
wasu sakanni yace.

"Ban miki alqawari ba gaskiya babe... Kema amaryarce kaman kowa,kodon kinga ban
tada rigima a kaiki yau ba?"

"Am sorry besty....don Allah"

"Nace banyi alqawari ba,but ki jirani idan hali ya yiwu zan miki magana saiki fito"
A haka suka rabu da musaddiq,duk sai taji ranta ya jagule,tunda taji ya fadi hakan
probability na rashin zuwanta yafi na zuwan nata yawa,saita buga tagumi tana zaman
jiran tsammani,har sanda aka shigo aka fita da fannah alamun tafiya zasuyi.

Kasa zama tayi,ta lafe a farfajiyar gidan tana ganin yadda motocin
suke tashi suna ficewa. Ta duba agogo,ta tabbatar tunda har musaddiq yakai wannan
lokacin baice ta fito ba to tayi loosing chance dinta,tabbas bazai kaita ba.

Hawaye taji ya silmiyo mata,daya daga cikin talalar aure kenan,idan
dane anni kawai zata gayawa ta fice abinta.

Ko a yanzun ma ji tayi ba zata iya haqura ba,tunda duka motocin gidansu
ne zata iya basaja ta bisu,idan an tashi dawowa da dangin amarya ta biyosu ba
lallai a gane ta fita harta dawo din,don haka ta silale a hankali tabi ta jikin
motar dake fita daga gidan ta saje a jikinta suka fice tare.

Sai data fita din tahau raba ido,ba wata mota a wajen duka sun dauki
hanya wata nabin wata,caraf idanunta suka sauka kan wata baqa guda daya dake fake a
gefe,sauri take kada musaddiq ya cimmata yace ta koma gida,don haka bata lura da
number ba irin ta gidansu bane kawai ta doshi motar kai tsaye.

Sosai abun ya musu dadi,ya kuma yi musu sauqi na ganin ta kawo kanta
da kanta,sai ya bude motar kawai yana jiran isowarta,wanda tana isowar ta bude
bakinta da zummar tambaya sai kawai ji tayi luuuu an jata cikin motar an maida qofa
an rufe. A gaggauce ta bude idonta tana son gani ko musaddiq ne yake mata
wasa?,saidai fuskar data gani din a gabanta ba wata alaqa ta kusa ko ta nesa da
imani a tare dashi bare a alaqantashi da sunan musaddiq ma.....kafin kuma ta sake
tantance komai,sun badeta da wani abu da ya sanyata atishawa,cikin qasa da second
biyu ta daina fahimtar komai.


_masu karatu kuyi haquri nayi baqi ne yau din,mu tara gobe in sha Allah......sai
ince kowa ya shirya,ranar da kuke jira ce ta tunkaro mu_

Sonso🫢🏽πŸ₯°πŸ₯°


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 141

*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET........siya ko saidawa,reposting
ko sari_*πŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎπŸ‘‡πŸΎ


https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



141


Tsararren gida ne da akayi masa wani irin qawataccen gini mai dauka
hankali. Tun daga qofar gidan zuwa cikin gidan dole ya burge me kallo saboda yadda
komai yake a tsare da wani irin yanayi me jan hankali. Komai favourite na farouq
aka saka,fu'ad yayi masa ba zata kaman yadda shima yayi masa.

A hankali ta rufe turaren data gama fesa masa tana dubansa,yayi
masifar kyau cikin wani lallausan yadin vicuna da aka yiwa riga da wando da wata
'yar sama me kama da alkyabba. Tsadajjen dinkin hannu da aka shiryashi da zare me
daraja.

"Kayi kyau muffin" Sabreen ta fada tana lumshe idonta gami da budesu akan fuskarsa.
Hannunta ya riqo a tausashe yayi kissing dinta

"Soyayyarki ce ta saka my world.....but bakisan kin fini kyau ba?" Ido ta zaro waje
kana ta saki dariya tana girgiza kai gami da ja baya

"Zolayata kake muffin.....ta yaya haka zai kasance?,kar ka tsaida BB hamma......yau
ranarsa ce aje a miqawa sister fannah shi" Murmushi ya subuce masa ya soma zura
rufaffun takalmansa tana daga tsaye tana morewa kallon abinta. Sai ya fito fes
kaman wani shaihin malami.

Har bakin mota ta masa tattaki,bayan ta tabbatar an saka komai a motar
daya dace a kaiwa amarya da angon. A yau kadai data sanya order Youghourt da sauran
wasu snacks daga wajen deeja beerva aka kawosu tsaf.......sai ta dinga jin sha'awar
koyon duka nau'in wadannan abubuwan. Ta duba handle dinta na tiktok da Facebook,ita
dai a rayuwarta zata iya cewa batasan mace kamarta ba. Komai ta iya,idan nace komai
ina nufin komai da komai din,kama daga kayan gashe gashe,girke girke,kayan mata da
na mazan ma da zaki hada da hannunki.....kayan maqulashe,man kitso,man shafawa kai
duk wani abu da dan adam zai buqata musamman mace cikin rayuwarta. Hatta fannin
gyara mu'amala da zamantakewar auratayya ta hanyar shawarwari. Kai tsaye ta nemeta
ta number dinta ta yanke yin register da ita,kafin ta qara nauyi tanason ta zama
cikakkiyar mace tako ina,itama ta hada wadannan baiwawwakin.+234 907 927 4454
(Ba sabreen ba,ni kaina magana ta gaskiya na jima banga mutum irinta din ba,akwai
qaruwa sosai tattare da ita,in sha Allah bazan gajiya da kawo muku duk wani mutum
da zamanku tare dashi zai amfaneku kuda iyalinku ba).
Home service takeso sukayi tsada ta gama komai. Tun bata ganta ba
kirkinta a iya waya kawai yasa hankalin sabreen sake kwanciya da ita.

A nutse ya kashe motar gaban gidan,duk da mai tsaron gate din gidan ya
dage qofar tun isowarsu.

Ango farouq dake zaune a seat me zaman banza.....sanye da wata danyar
dakakkiyar shadda da iya kallo kawai da idanu zai ganar dakai

Please Login or Register in order to submit comment