You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sabreen.

"Sabreena......ki saurareni kiji.....kuskure kikeso ki aikata wanda zaki dana sani
daga baya.....ta yaya zan zama silar batan yaro na kamar a film ko a rubutaccen
wasan kwaikwayo?" Wani numfashi sabreen ta sauke sannan tace.

"Komai da kika taba aikatawa a kansu a baya din ai hankali bazai dauka
ba......hakanan idan ka saurari labaran ba abinda zai hana kace cikin litattsfan
labarai ne ba cikin rayuwarmu ta zahiri ba....."

"Ba maganar baya akr ba......maganar yanzu akeyi sabreen" Maamah ta fada karon
farko tana sassauta muryarta gudun ballewar sabreen din.

"Da da da yanzun duka daya ne......ba wani abu da zai canzaki......ko a yanzun
akwai wani abu da kikeson cimmawa shi ya sanyaki tsaiwa kina bayanin nan,bawai don
kinga ya dace kiyi ba,ba kjma wai don kin damu da batan dama faruwar komai
ba......kawai abjnda nake buqata daga gareki shine......ki sakarmin mijina.....ki
fice a rayuwata.....kije kiyi taki rayuwar duk yadda kk so kika kuma tsara"

"Bani da masaniyar komai sabreen,karki manta mana.....nifa uwa ce"

"Ni kuma me shirin zama uwar,uwarma kuwa ta gaske ba MUNA UWA BA,uwar data shirya
tsaf don bawa rayuwar yaranta kariya.....wadanda zasu zo dama wadanda basu taho
ba.....kariya daga dukkan wani kalar farmaki daga miyagu da mafarautan mutane,irin
kariyar da sunanta zai tumbatsa da tambarin SADAUKARWA.....sadaukarwa mafi girma
kuwa cikin rayuwar 'ya'ya akan iyayensu.....irin sadaukarwar dake sanya kowanne
yaro cikin alfahari da kasancewar iyayensa su suka haifeshi". Wani irin nannauyan
abu kalamanta suka sauke mata......ta kuma isar mata da saqonni masu yawan gaske
da.maganganunta masu harshen damo.

"Ki huta lafiya" Magananta ta qarshe kenan da ita tana yanke kiran.

Mayar da dubanta tayi kan huda dake zaune a gabanta. Tun dazu da abba
yazo asibitin yace bai gamsu suci gaba da zama ba,Dr mubeena ta sallameta bisa
alqawarin zata dinga zuwa ganinta kullum don samun cikakken kulawa fiye da
asibitinma.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 124



124


"Zaku wuce kaman yadda ani ta buqata.....komai bazai fasa faruwa ba
huda....komai kuma bazai sauya ba sai abinda qaddararmu ta tanadar mana". Hawaye
sosai huda keyi,duk da yadda take qoqarin riqe kanta daga aikata hakan a gaban
sabreen.

"Zamu tafi adda da ciwo da firgici.....zamu tafi ba tare da taqamaimen masaniya
akan ina hamma yake ba......yadda ya kula da lamarinmu muma ba zamuyi qasa a gwiwa
ba wajen addu'ar bayyanarsa........da kuma tonuwar asirin duk wanda keda hannu
wajen kitsa komai da zai illata rayuwar kamilin mutum me taimako irin hamma fu'ad".

Ba qaramin jarumta sabreen din ta nuna ba a sanda suke sallama dasu
nadra din da yammacin ranar,sai takejin kaman zata sake tabbatuwa cikin kadaici,ta
dinga jin kamar ita daya ta rage a duniyar zata ci gaba kuma da rayuwa ne ita
kadai.


*11:30 pm*


A hankali ta farka daga wani nannauyan bacci daya saceta saman abun
sallah bayan ta kammala sallar nafilfilu da dukka addu'o'inta,ta kuma cika da
sallar nan me matuqar fa'ida da kuma alfanu wato sallar wuturi.

Hijabin da dardumar dukka suna jikinta,alqur'aninta yana ajiye a gefe
yayin da tasbahar hannunta ta sulale ta fadi a qasa ba tare data sani ba. Ta qarasa
bude idanunta da fadin

"Alhamdulillahi ala kulli hal" Cikin kowanne lokaci idan ta bude ido tsammani
takeyi zata ga komai ya wuce tamkar cikin duhun mafarki ne da hasken rayuwa da
idanu biyu ya ratsata,saidai duk sanda zata farka din tana samun komai a inda ta
barshi,komai yana nan yadda yake.

Fitsari ne ya cika mata mararta,ta sanya hannu ta zare hijabin jikinta
idanunta yana sauka saman tray din dake table din gefanta. Komai an shiryashi
akai,tasan kuma wannan aikin ma'u ne bisa umarnin anni.

Hatta da dakin suna dawowa annin ta saka aka shiryashi yadda ya dace
saboda jin dadinta.

Qafarta tadan riqe saboda yanayin zaman da tayi a wajen na wani
lokaci,ta miqe a hankali tana nufar toilet. Ba jimawa ta fito daure da sabuwar
alwala,tun daga sanda ta fahimci muhimmancinta ta daina zama babu ita,musamman ita
din da tasan akwai mutum irin maamah dake gefe tana farautar rayuwarsu ta kowanne
fanni. (Koda baka da masaniyar takun saqa tsakaninka da wani wanda kake kyautata
zaton yana 'yan biye biyen shirkarsa,ka tabbatar baka zama ba tare da alwala
ba,koba komai ita din haske ce a gareka,ga kuma kariya da zata baka daga dukkan
sharrin me sharri).

Wani sauqi sassauci da kuma rangwame take ji duk sanda ta tuna ta
sakarwa maamah wani tsoro da firgici,don tana zaune ta shiga shafukan sada
zumunta,kai tsaye ta dinga cin karo da labarin yanata trending,ga 'yan qarawa miya
maggi da gishiri sunata qawata topic din da kalar qarairayinsu. Har ta gama
shawagin ta sauka labarinne ta kowanne handle na bloggers da gidan jaridu mujallu
harma da celebrities.

Har zata koma ta zauna taji qishirwa sosai ya kamata. Koda ta duba
tray din ba zam zam ma'u ta saka mata ba,ruwan gora ne,tana kyautata zaton kuma
batasan ba kowanne ruwa take iya sha din ba sai zam zam shi yasa,don haka sai kawai
ta maida hijab dinta ta zura flipp flops dinta ta nufi qofar.

Sanda take takawa zuwa parlor din sai ta dinga jin wata kakkaurar murya
tana magana,kaman tasan muryar,kafin ta qarasa tunaninta kuwa tuni ta fusgo mata
cewa muryar abdulgaffar ce.

Sunan fu'ad da taji an ambata ya sanya gabanta wani mummunar
faduwa,qafafunta suka fara slow suka gaza ci gaba da tafiya da ita,sai kuma suka
tsaidata cak qirjinta kaman zai fito waje.

"Mun samu nasarar gano inda yake.......farouq da pilot dinsa sun fitar dashi daga
qasar.......suna taipei capital na taiwan,asibitin taipei wellness hospital and
resort,mun samu magana da farouq,saidai na lokaci kadanne ya datse kiran,alamu sun
nuna bayason kowa yaji.....kuma haka mukayi dashi,ya bani information dinne nima na
through waya ba,yace idan zaiyiwu kada kowa ya sani sai abba" Muryar anni rawa
takeyi sosai,yayin da sabreen taji wani murdewa da mararta tayi,tanaso taji ya
fu'ad yake......tanaso taji halin da yake ciki,muddin ta bayyana ba zasu fadi komai
a gabanta ba ta sani.....muddin sukaji motsinta kuma nan ma ba qarasa maganar
zasuyi ba bare tasan me ake ciki,don haka salin alin ta sulale tayi zaman dirshan a
nan tana dafe hannuwanta jikin wata kujera qwaya daya da aka ajiye a wajen.

"Me ya samesu abdulgaffar.....kada kace zaka boyemin komai" Shuru abdulgaffar yayi
yana sadda kansa qasa,har sai da abba ya qagu shima yace

"Zauna ameena.....kaima zauna abdulgaffar....." Dukkansu suka zauna sannan abban
yace.

"Dani da ameena bana jin muna cikin mutanen da zaka boye mana komai,shi kansa
farouq din nasan bazai taba lissafamu a ciki ba,koda zaice kada a fada din zai fada
ne saboda matarsa......tana cikin lalurar da ba komai dama ya kamata a gaya mata
ba".

"Ba gatan da zakuyimin abba sama daku gayamin halin da hamma yake ciki" Sabreen da
jikinta ya soma daukan wani yanayi ta fada cikin zuciyarta,tana jin kamar ta jawo
abdulgaffar ya gaya mata komai da gaggawa.

"Haka ne,sun hari boss ne,a sannan yana tsaye suna magana da jordan,ya kauce basu
sameshi ba,yana daga kai kuma ya hangi wanda yayo harbin,baice da kowa komai ba ya
soma dosar inda yake hangoshin,daga can sama ne wani guri da ba kasafai aka fiya
amfani da wajen bama,ganin ya hangoshi kuma ya nufeshi sai ya sake yin harbin a
jere har sau biyu don kada ya samu isa gareshi,to amma kuma baiyi nasara ba,don
harbin daya ne ya sameshi a damtsansa,dayan ya sake wuceshi,harbin bai hanashi
qoqarin cimma mutumin ba,ganin yana dososhi da gaske kuma dab yake da
riskarsa,jordan da farouq na biye dashi a baya sai ya fara hade kayansa zai gudu.
Har yayi taku biyu ana ukun ya damqeshi yanason cire hular fuskar daya saka ya rufe
idonsa,juyowar da zaiyi kawai sai ya shaqa masa wani abu a handkerchief din
hannunsa yana qoqarin zamewa ya gudu,saidai kafin abinda ya shaqa masan ya kama
jininsa su jordan sun qaraso,qarasowar tasu kuma yayi daidai da zubewarsa a
wajen,basusan waye da waye a wajen yake tare dasu ba,basusan kuma waye ya aikoshi
ba,wannan ya sanya kawai suka yanke shawarar komawa dashi su fitar dashi daga
qasar,shi kuma mutumin sun sakashi hannun hukuma,He's unconscious har yanzu,wannan
dalilin ya hana oga farouq bayyana ko bayyana komai".

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" Shine kawai abinda anni ke maimaitawa. Komai
jinsa sabreen tayi kaman tana saman gajimare ko iska yake faruwa,ta dinga kokawa da
numfashinta tanason kamoshi ta kuma kama ayoyin Allah da zasu taimaketa,saidai ta
gaza hakan har sai da sautin muryar anni ya bayyana.

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!!" Tabi bayan ta anni tana maimaitawa,saidai
tata da wata madaukakiyar murya ce data fusgo sautinta da qyar daga
maqoshinta,sautin kuma ya iske anni dake zaune tana maimaitata. Cak anni ta dakata
tanaso taji sautin daga inda yake fitowa,jin daga inda sautin yake ya sakata
waiwayawa tana duban fuskar abba wanda shima ita din yake kalla.

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!!!" Kalmar data sake maimaitawa da wani irin
gunjin kuka shiya ankarar da anni daga inda sautin yake fitowa.

Da wani gudu anni ta miqe tana nufar wajen hankalinta yana tashi,bai
kamata sabreen taji wannan mummunan labarin ba,bai kamata ba,labarin da aketa
boyonshi ta yaya ta jishi?".

A zaune ta sameta tanata maimaitawa,wasu irin hawaye sun wanke
fuskarta,jikinta kawai rawa yakeyi,durqusawa tayi a gabanta tana kamata yayin da
Alhaji hamza ke tsaye a kansu shima yana tayata maimaitawa.

"Me kika fito yi sabreen?,me yasa kika fito?" Anni ta maimaita a gigice tana riqeta
cikin tsananin tsoron abinda zai iya faruwa da ita. Numfashinta yana wani iri,ta
tabbatar kuma tana da asthma ne irin nata,tana tsoron kada ta sarqeta cikin wannan
daren.

Zuciyarta taketa qoqarin bawa dakiya da juriya.......tanata qoqarin
maido wannan qwarin gwiwar juriya da jarumtartata,tanason dawo da old version of
sabreen dinta. A yanzu bata da wani buri daya wuce ta bude idonta taga fu'ad din,ko
a yaya yake......ko a wanne irin yanayi yake sai yafi mata nutsuwa akan zamanta a
nan.

"Ruwa zan sha anni" Ta fada muryarta tana rarrabuwa.
Da kansa Alhaji hamza ya koma ya dauko mata ruwan,ya miqawa anni ta
bude ta bata sannan yace.

"Maidata daki ameena,muje na bude miki qofa". Riqeta anni tayi har yanzu suna
maimaita hasbunallahu wani'imal wakeel tare.

Saman gadonta ta ajiyeta tana jingina mata pillow

"Anni" Ta kira sunanta kai tsaye tana jin wani jarumta yana shigarta. Kai kawai
anni ta tada ta kalleta,don bazata iya tuna yaushe ta kira sunanta haka ba.

"Kunason nutsuwata da kwanciyar hankalina?" Ta tambayi anni still tana dubanta.
Alhaji hamza dake tsaye daga bakin qofa anni ta kalla,sai ya gyada mata kai,tasan
umarni yayi mata sai ta dawo da dubanta kan sabreen.

"Sosai sabreena.....sosai". Idanunta da takeji hatta su sun mata nauyi a jikinta ta
lumshe sannan ta bude.

"Abu daya nakeso anni da zai bani wannan nutsuwar......abu guda daya take nake da
buqata....." Ta fada tana daga yatsanta daya,idanunta nayin wani iri kaman wadda
tasha abun maye ta maku.......



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 125



125


"Mene sabreen?" Anni ta sake tambaya tana zama gefanta,tana jin kamar an
salube qashinta daga cikin tsokokin jikinta,tana fata ba abinda bazai yuwu bane
sabreen xatayi magana akai.

"Anni ku kaini wajensa" Ta fada a taqaice hawaye suna cika fararen idanunta da tuni
kalolinsu na fari da baqi ya jima da sauyawa daga idanunta.

Da hanzari anni ta kalleta,kai ta dan girgiza mata.

"Kiyi haquri ameenatu......ta yaya kina cikin irin wannan yanayin zaki tafi ki
ganshi a yanayin da yake ciki?,ba abinda yafi buqata illa kiyi masa addu'a ki kuma
kula da abinda yake cikinki......bazai taba iya mantawa ba muddin kika kasa riqe
abinda yake cikinki kika kasa rainan masa su....."

"Bazan iya rainonsu ba anni muddin babu shi a kusa dani.......zan fara lissafin
yankewar numfashi daga gangar jikina daga yanzu zuwa fitarsa na qarshe" Ta qarasa
maganar hawayen da take tarewa suka gangaro saman kuncinta.
Wani abu ya ratsa anni da Alhaji hamza tun daga saman kansu zuwa tafin
qarfinsu. Tsahon rayuwarsu zasu iya cewa basu taba ganin zazzafar soyayya irin
wannan ba.....soyayya da qauna me wani irin zafi da radadi,soyayya da qauna ta
gasken gaske......soyayya ta a mutu da kowanne motsi da yanayi na abokin soyayya ya
tsayema dan uwansa a rai.

Rasa bakin magana anni tayi,ta daga kanta tana duban Alhaji hamza da
shima ya gama sallamawa. Kai kawai ya jinjinawa anni sannan ya dubi sabreen.

"Indai don wannan ne ki kwanta kiyi baccinki sosai,daga gobe zuwa jibi in sha Allah
zan siya mana tickets na fita taiwan......zakije ki ganshi....amma sai kinyimin
alqawarin daga yanzu harmu tafi ba zaki sake damuwa ba......kuma zaki sakeyimin
alqawarin idan munje ba zaki daga hankalinki ba.....ko a yaya kika sameshi zaki
sawa zuciyarki nutsuwa da kwanciyar rai har ya samu lafiya kamar yadda muke
kyautata zaton hakan". Kai ta shiga jijjigawa a jejjere.

"Nayi maka alqawari abba.....nayi maka in sha Allah". Kai ya gyada shima,wani irin
tausayinta yana kamashi,ya yiwa anni alama da hannu sannan ya juya yana fita.

Saida anni ta tabbatar ta kwanta ta kuma nutsu,sannna ta saka mata
karatun qur'ani qasa qasa kusa da ita,ta kira mata ma'u suka kwanta tare sannan ta
fice.

Tana jin fitar annin,saita runtse idonta tana jin wani rauni yana
saukar mata,kuka takeso tayi wanda batasan iyakarsa ba,amma kuma sautin qur'anin da
yake shiga kunnenta ya bata wata irin cikakkiyar nutsuwa,a hankali ta sake maida
idanunta ta rufe,saita dinga jin kaman wani tabbaci take samu daga zuciyarta na
samun nasara da sauqi a dukka al'amuranta,ta sake imani da wannan ayar da take
cewa.
(Ku saurara,da ambaton Allah kadai zukata suke samun nutsuwa).

A dan gaggauce anni ta qarasa dakin Alhaji hamza,ta dubeshi,waya
yakeyi yana daga tsaye a daren,batasan koda waye yake wayar ba duk da dare ya soma
nisa,sai ta zauna tana jiransa ya kammala. Ba jimawa ya kammala din,ya dubeta yana
aje wayar

"Na saka su dubamin tickets ne xuwa taiwan.....na gobe ko na jibi,ina zaton kuma
sai jibi ma za'a samu".

"Amma abba.....kana ganin ya kamata mu dauketa mu kaita ta dinga ganinsa cikin
engine da tashin hankali?kasan tabbas sai muhammadu yafi son rayuwar yaran nan da
nashi rayuwar?,kasan sai yafi qaunar ta kula da kanta da lafiyarta akan tashi?."
Dan murmushi ne ya subucewa abban,sai ya zauna gabanta yana dubanta.

"Ameenatu.....zuciya da ruhin soyayyarsu ba gama gari bace irin ta kowa.....karatun
da na yiwa soyayyarsu shine.....suna sake qaunar juna da tsananin son kasancewa da
junansu a sanda jarrabawa ko musiba ta samu daya daga cikin su,sunfi qaunar duk
tsanani su kusanci juna akan suyi nesa da juna......sabreena ba zata taba samun
nutsuwa ba.....ba zamu taba samun yadda mukeson gani ba muddin bamu sadata da barin
ruhinta ba.....xakisha mamaki idan kikaga tafi nutsuwa a can fiye da anan din duk
da unconscious yake?" Ya qarasa maganar da tambaya yana duban idanun anni. Shuru
annin tayi tana juya maganar abban. Ta jima bataga soyayya me zafi jini da hanta da
zuciya harma da b'argo irin tasu ba.

Kanta ta gyada a hankali bayan ta gama nazarin,ta kuma yarda da
maganganun abban dari bisa dari don itama taga hakan.

"Allah yayi mana jagora,ya taqaita dukkan wahala da sharrin masu sharri"
"Allahumma ameen" Ya amsa mata yana miqewa.


_TAIWAN_
_TAIPEI_
*_Taiwan Taoyouan international airport_*


Yammaci ne sosai sanda suka sauka a taiwan,misalim qarfe hudu na
yammaci,wanda yayi daidai da qarfe sha daya agogon nigeria.

Da yake tafiya ce bata shiri ba,cikin motocin da gwamnati ke ajiyewa
saboda baqi da wadanda ke buqatan hayar da zaiyi driving da kansa,ya gama adadin
kwanakin ka maida inda ka karbo ita suka karba.

Abdulgaffar ke driving din,yana yi yana duba map da address din da ya
samu da zai sadashi kai tsaye da asibitin.

Duk yadda garin yakai ga kyau tsaruwa da daukan hankali ba wannan bane
a gabanta,bama kasafai take iya fahimtar inda suke wucewar wa,burinta kawai.shine
su isa asibitin,burinta kadai shine ta ganta a gabanshi,burinta ta ganshi a gabanta
ta daina jin cewa yayi mata wannan nisan da kowacce rana zuciyarta da gangar
jikinta suke jiye mata.

Tafiyar mintuna arba'in suka fada ainihin titin asibitin,ba wani wanda
yake iya cewa da danuwansa komai. Saddiq musaddiq abba da anni......ballantana
sabreen da take ganin kaman laqai laqai kawai abdulgaffar yakeyi bawai tuqi
ba,kaman tafiyar kunkuru yakeyi,kamar ma bayason ya sadasu da asibitin.

Mintina sha biyar map ya nuna musu suna daidai asibitin,suna shiga
titin shine gini na farko daga hannun dama.

Idonta ta daga a hankali tana kallon tsararre kuma ajiyayyen ginin
asibitin,wanda ko ba'a gaya maka ba kasan cewa gurine me cike da tsari da tsananin
kulawa,guri ne kuma da lafiya ke tsaye da qafafunta.

Karo na farko data soma yarda da gaske ko a qasashen waje akwai rayuwar
masu hannu da shuni akwai ta tsaka tsaki akwai ta talaka. Tun kafin sukai ga shiga
asibitin checking nasu da akeyi kadai ya isa ya tabbatar maka akwai tsaro sosai
cikin asibitin. Checking da ya sanya ta dinga jin kaman wani salo ne na hanata isa
garesa.....kafin yafi tsaye mata a rai sama da zaman da sukayi cikin jirgin kafin
isowarsu taiwan.

A muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci abdulgaffar ya tsaida
motar sannan ya kasheta. Ta daga idanunta tana jira taji wani a cikinsu ya bude
motar da zummar fita amma bataga kowa ya motsa ba. A nutse Alhaji hamza kibiya ya
fiddo wayarsa sannan yayi kira,kiran da duka duka bai wuce minti daya ba

"Muns parking lot" Abinda ya fada kenan ya yanke kiran yana dubansu.

"Muje ko.....ga Jordan nan zuwa". Kiran sunan Jordan kadai ya sanya jikinta ya fara
rawa,a kasalance ta sanya qafafunta waje tana ambatar sunan Allah bayan musaddiq ya
bude mata murfin motar,sai taji jikinta kamar yayi nauyi ta dafa murfin tana
fitowa.

Komawa gefenta anni tayi tana saka hannuwanta cikin nata,ta daga kai
suka hada ido da anni.
"Karki manta alqawarinmu,kada ki sabashi......be strong please ameenatu......na
sani ke din jaruma ce" Kai ta gyadawa anni,bawai don a yau tana jin wannan jarumtar
ba,ta dade da sani da kuma fahimtar indai akan fu'ad dinne bata da wani sauran
jarumta daya rage,ita din raguwa ce ta qarshen qarshe.

A hankali suka fara takawa suna dosar main entrance na asibitin,wanda
basuyi taku goma cikakke ba saiga Jordan din,sukayi kacibus dashi a hallway din
yana fitowa daga elevator.

Kallo kawai sabreen take qarewa Jordan,abinda bata taba yi ba,saidai
koda bata taba qare masa kallo ba amma ta sani yana da qiba da kuma tsaho gami da
murdewar jiki,amma a yanzun abinda idanunta suke iya gane mata shine zubewar da
yayi. Ya rame sosai duk da har yanzu wannan kuzarin yana tattare dashi,abinda ya
sanya dukka gwiwoyinta yin bala'e'en sanyi tana jin tabbas ko meye ya faru da
hammanta ba qaramin abu bane,abun har ya taba jordan har haka?.

"Welcome madam" Ya fadi mata yana tsaye daga gefanta cikin tsananin girmamawa
tausasawa da kuma kulawa. Bata iya amsa masa ba,sai idanunta data zare daga kansa
gudun kada taje ta rasa ragowar qwarin gwiwar data rage mata.

Musaddiq da abba da jordan su suka fara wucewa saman,kafin su kuma su
kuma da saddiq su kira wani elevator din suka shiga suka bi bayansu.

Farouq ne mutum na farko data fara hangowa yana fitowa daga wani
balcony na daban bayan doguwar hanyar da kebantattun amenities suke. Faduwar
gabanta ya sake tsananta saboda ganin irin zubewar da jordan yayi akan fuskar
farouq. Ta kasa dauke idanunta a kanshi,kaman yadda ta lura shima din ita yake
kallo. Suna takawa zuwa inda yake shima yana matsowa garesu,har suka riski juna a
hanya.

"Adda......haka kika koma?" Farouq ya fadi a raunane yana jin wani irin tausayinta
yana ratsashi. Karo na farko da yaji yarda dari bisa dari yau yayi ido da ido da
salon soyayyar da yakeji a ransa a baya cewa babu irinta a duniyar
zahiri......saidai a duniyar litattafai da kuma fina finai.

Kanta ta dauke tana qoqarin hadiye wani abu daya tsaya mata a
wuya.....tambayarsa kulawa ce ta kawota.....amma da zaiyi mata wani abu da yafi
wannan tambayar faranta mata rai. Ya sauketa da labarin halin da hamma fu'ad yake
ciki.....ya gaya mata yanayinsa shi zaifi komai mata dadi.

"Kaima bakaga yadda ka koma ba BB?" Ta qarashe tambayar tana kallon fuskarsa kai
tsaye muryarta tana rawa,tana fatan ganin wani mode da zai bata haske akan yanayin
da fu'ad din yake ciki.

Wani busashen murmushi yayi yana kada kansa,sannan ya maida dubansa gasu
anni.

"Sannu da zuwa abba.....anni sannu da zuwa".

"Muje farouq ciki....muje dakin" Anni data kasa haquri ta fada tana yin gaba
sabreen kuwa ta sanya qafafunta ta rufa mata baya kai tsaye xuwa dakin da sukaga
farouq din ya fito.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 126


*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA
KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA
IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE
SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA
A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*



126
Daga balcony din ma'aikatan lafiyar wajen suka tsaidasu,kowanne aka bashi
riga da hula ya sanya,sannan suka musanya takalman qafarsu zuwa wasu ajiyayyun
tsaftatattun fararen Crocs da suke wajen.

Lafiyayyen parlor ne wanda aka tsarashi cikin wani irin yanayi da zai bawa
me jinya dama wanda ake jinyar yanayi me kyau,bisa wadatacciyar iska da haske,irin
iskar dake fitowa daga tsirran da aka wadata bayan dakunan dasu,wanda kana iya
hangen komai tarwai ta gilasan da dakunan ke dashi daga gaba.

Sam parlor din baiyi kama da asibiti ba,an saka sofas set guda,tv
plasma freezer da side tables da babba guda daya,curtains da komai na parlor din
fari ne qal tamkar hannu baya tabawa saboda tsananin kula da tsafta,hakanan qamshi
ne me kwantar da hankali kawai yake fita.

"Akwai likita a ciki a tare dashi,bibbiyu bibbiyu nake ganin ya kamata a
shiga......" Farouq ya fada yana rarraba idanunshi tsananin fuskokinsu.



Please Login or Register in order to submit comment