You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har suka girma muka aurar dasu,bamu gusa ko nan da
can ba muna gabansu suna gabanmu sabunta ayyukanmu mukeyi akai akai.......munayi
matansu sunayi,wanda keda nasara shike samun rinjaye.....ballantana ke,yaranki ina
da tabbacin suna buqatar gagarumin aiki kafin samun saituwarsu akan bigiren da
kikeso".
"Abinda ya wuce ya wuce hajja harira.....yanzu meye abinyi?" Gyara zamanta tayi
sosai tana bawa maamah dukkan hankali da nutsuwarta

"Akwai plans guda biyu,plan A da plan B......idan A baiyi aiki ba zamu wuce zuwa na
biyu"

"Kamar?" Ta tambayeta cikin matsuwa da jin bayanin komai

"Yauwa......na farko akwai wajen mutumina da zan kaiki wanda shi yakemin aiki akan
komai da kowa......"

"Kai....kai.....amma kin gama min komai" Maamah ta fada tana gyara zamanta da kyau
fuskarta na washewa da madaukakiyar fara'a,saboda ta hangi zuwan nasararta a nan
kurkusa......ta hangeta tana fantamawa fiye da yadda hajja harira ke fantamawa din.

"Ba komai fa.....zaman tare ai ba qarya bane....zaki zayyane masa dukkan abinda
kike da buqata wanda nake da imani a kansa mallaka sai yadda kika juyasu.....akan
mansur ya fara yimin aiki,lokacin da yayi aure sai na fuskanci wani abu,maganata
qasa take da maganar matarsa,dukkan umarni da zabi nata ne sai abinda taga dama sai
kuma abinda tace.....a sannan na farga,amma in gaya miki inayi yarinyar nan tana
nata har daga qarshe na hadu da DAN DUMA....tuni na saka ya qara mata wuta a
gidan,mansur ya saketa tayi gaba,tun daga ranar dukkan wanda zaiyi aure a cikinsu
nice nake zaba masa yarinyar da nakeso ya aura din,wadda zan cimma buqatuna ta
hanyarta,wadda zan juyata ba musu ba kuma damuwa......to kema wannan shine plan B
dinki idan na farko yaqi aiki"

Shuru maamah tayi tana jinjina kai,lallai duk iya yadda take ganin
mulki da isa da kuma izzar hajja harira ta wuce nan. Wannan shine cikakken ma'anar
HAMSHAQIYAR UWA ko kuma CIKAKKIYAR UWA. Idan so samu ne tana son kamar haka ko sama
da haka

"Amma banajin musaddiq zai qara watanni shida ba tare da yayi aure ba"

"Ko yau yau zaa daura auren kina iya ruguzawa,ki maye gurbinta da wadda kikeso" Ta
fada kanta tsaye cikin confidence.

"Waye babbar damuwarki a cikinsu?,muhammadu?" Kai ta jinjina. Tafi damuwa da
kamashi a hannu fiye da musaddiq. Tasan waye fuad din,yana da tsauri da tsananin da
ita kanta tayi imanin mafi rinjayen aikin a kansa zaa gabatar

"To ki manta da batun musaddiq me sauqi ne"

"Haka ne wannan" Ta fada tana murmushi,tana jin cewa qarshen matsalarta yaxo,tana
jin cewa lokaci yayi da zata cika muradanta

"Yaushe zamu tafi zuwa wajen DAN DUMA?,kinsan ba'a bori da sanyin jiki" Ta karkata
tambayarta ga hajja hariran cikin zumudi da farinciki,tana jin bacin ranta yana
zagwanyewa.


Tunda suka fito daga wajen a cikin jikinta kawai takejinta uncomfortable.
Haka kawai take jin kamar akwai wani abu,tayi dukkan research da idanunta hankali
da kuma tunani bata ga wulgin kowa ba,hakanan bataga alamun ana bibiyarsu ko wani
abu da yayi kama da hakan ba. Saidai har suka soma nisa da wajen bata samu nutsuwa
ba,abinda muddin ta soma jinsa a jikinta zaiyi wahala idan baby afkuwar wata
matsalar.

"Me napep idan zaiyuwu ka kaini madabo.....zan qara maka wani abun" Tacewa me abun
hawan. Malam ne yaketa fado mata a rai,dattijo kuma kamilallen mutumin,ma'abocin
nutsuwa karamci da kuma ilimin addini.

Asalin haduwarsu ta fara ne a ranar da zasu rabu da ameen,daya daga
cikin mazan da suka taba shiga rayuwarta dama tarihinta. Abun yaso ya kwabe mata
har ameen din yaso fahimtar ainihin wace ita ba tare da takai ga fita daga layin
ba. Ya sanya aka biyo sahunta tiqa tiqan qattin dake gadin qofar gidan nashi harda
rakiyar karensu guda daya.

Malam din shi ya musu kaca kaca,ya kuma hada harda ameen din daya tako
da kansa,ya nuna masa daraja da martabar mace,sunaji suna gani yayi saving nata a
hannunsu ya wuce da ita sukaci gaba da takawa a qafa har titi.

Ita dinma a hanya bai qyaleta ba,ya dinga yi mata fada bawai don ya
fahimci wacece ita ba?,ko ya fahimci ainihin abinda ya hadosu. Donme tana diya mace
zata bari takai gefin magriba a irin wannan unguwannin?. Haka kawai taji ranta ya
nutsu da dattakonsa da kuma addininsa,rana ta farko da wani ya taba yi mata fada
irin wannan tun bayan shudewar iyayenta. A daren ranar tayi kuka tayi kuka,kukan
kuma kukan dadi ne na yadda yau aka samu mutum qwaya daya daya tsaidata da zuciya
daya yana mata fada kanshi tsaye. Tun daga wannan ranar malam din ya zame mata daya
daga cikin mutanen da suke da martaba a idanunta. A duk lokacin da kudi suka samu
takan dauki wani abu tayi tattaki taje ta gaidashi,ta kuma bayar wa almajiransa
tace ayi ma iyayenta da suka rasu sadaka.

Matarsa tana da matuqar kirkin da ta dauketa kamar diya kaman yadda
malam ya dauketa diya a wajensa. Duk sanda zataje gidan bata gaza fahimtar wasu
abubuwa daga sabreen. Macace mai matuqar hikimar da sai da takai daga qarshe ta
karanci wace sabreen din,sai ya zamana itama bata fiya boyewa inna komai ba muddin
ta tambayeta din,gidan sai yake zame mata wajen samun nutsuwa a wadansu lokutan.

Unguwar madabo,daya daga cikin tsaffin unguwanni dake birnin kano,wadda
take da dadadden tarihi. Hakanan ta tara malamai da masana addini masu yawan gaske.

Tsukukun loko ne da ko adaidata sahun a matse yake shiga,wannan ya
sanyata ta nemi ya ajiyesu daga bakin babban lokon da zaka karya ka shiga qaramin.
Ta bude jakarta ta sallameshi,sannan suka fara takawa ita dasu zuwa ciki.

Tun a rumfar dake qofar gidan ta tabbatar malam baya nan,don babu
tabarmin karatu,hakanan daliban nasa sai jifa jifa kowa yana sabgar gabansa,don
haka kai tsaye suka wuce zuwa ainihin cikin gidan.

Da sallama a bakinta suka kutsa kai,gidan yana nan kamar kullum cike
da tsafta. Ba kowa a filin gidan sai hayaqi dake fitowa daga kitchen da alamu ana
gab da kammala tuwon dare. Yaransu bakwai da malam,maza hudu mata uku kuma dukkansu
sun aurar dasu,don haka inna ce kadai ke rayuwa cikin gidan,sai babbar jikarta da
aka kawo mata don ta tayata zama.

Sake sallamar tayi,kusan lokaci daya aka amsa mata daga kitchen din da
kuma rumfar dakin inna. Cikin qasa da second daya wadda ke kitchen din ta fito.
Matashiya ce da duka duka bata wuce sa'ar huda ba,murmushi sosai take saki,ta baro
cikin kitchen din tana goge hawayen fuskarta da hayaqi ya sanya mata tana takowa

"Adda sabreen.....kece yau a gari?" Miskilin murmushin nan nata ta saki

"Inji maqi baqo ko rumasa'u?" Sai ta saki 'yar dariya tana kamo haneefa

"Muje yau inna taga su auta,tanata zancanku tace kwana biyu shuru,gashi batasan
muhallinku ba bare ta binciki ko lafiya?,layinki Kuma kwata kwata baya shiga" Ta
qarasa maganar tana riqe da hannun haneefa wanda tuni sukayi gaba zuwa dakin innar.
Sai a sannan da rumasa'u tayi zancan layinta baya shiga ma ta tuna yana
daya daga cikin layukanta da suka tafi hutu,sai ta taka a hankali tana bin bayansu
zuwa ainihin falon innar.

Dare dare ta samu haneefa gefan cinyar inna. A duniya gidan yana daga
cikin gidan dasu haneefa din keson azo,don sai ya kasance musu kamar wani gida daya
qwaya tak na 'yan uwansu da suke iya ziyarta su kuma sake,sakewar da basa iyayinta
cikin ainihin gidan mahaifinsu.

Da murmushin tambayar da taji innar na yiwa haneefa ta qarasa shigowa
ciki

"Wa'alaikumussslam.... .ina nan ina tuhumar amaryata me takeci naga tana ta
tsaho?,kunyi nisan zango wannan karon AMEENATU(real name dinta kenan)". Murmushi ta
kuma saki,a duk sanda innan ko malam sukayi kiranta da sunan ba wanda ke fado mata
a rai sai mahaifinta. Shike yawaita kiranta da sunan,sunan da ya kasance na qanwa
ga mahaifinsu guda daya tak da aka haifa a tsakanin su maza su uku,tazo kuma ta
rigasu rasuwa a wajen haihuwa tabar nata yaran mata duka su uku.

"Kuna raina inna....abubuwa ne suka sha kaina" Ta fada tana zama itama.

Gaisawa sukayi sosai ta tambayeta malam

"Malam yau duka bai zauna ba,ya tafi kasuwar qauye,amma yana hanya nasan in sha
Allahu".

Kamar kusan kowanne lokaci idan sunzo gidan,komawa take 'yar
kallo,nadra haneefa harma da hudan suke sabgoginsu.

Lumshe idanunta tayi tana sauke boyayyar ajiyar zuciya. Ta tabbatar
yau ta faranta musu ta kuma rage musu kewa qunci da takurar zama waje daya. Tana so
ta dinga kaisu guraren da zasu dan sha iska,amma tana tsoron koda da kuskure suga
wani abu da zai iya affecting tunaninsu.

Suna matuqar son a zo gidan,amma kuma duk dadewar da za'ayi ba'azo din
ba ba zasu taba tada mata zancan ko suyi qorafi koda kuwa sau daya ba,har sai ranar
da sukazo din.

A nan sukayi sallar magariba,sukaci kuma tuwon dare. Suna haramar tafiya
malam din ya dawo.

Sosai shima yaji dadin ganinsu,ya bude kuma duk abinda yazo dashi din
kama daga rake,gyada,quli kabewa,dinya da sauransu ya diba musu. Walwalarsu ta dadu
sosai a sannan,duk sai da suka fice da zummar zasu tafi ya rage saura Sabreen
din,ta xuge jakarta ta fiddo kudi ta aje gaban malam

"Malam ayimin sadaka,sannan ayi mana addu'a". Kudin ya kalla sannan ya kalleta.

"Zan miki addu'a aminatu koda baki bada komai ba....."

"Malam bakai na bawa ba,yaran malam na bawa"

"Idan kin fita waje ki raba musu da kanki kamar yadda aka saba" Ya tareta

"Malam don Allah kayimin alfarma ko rumasa'u ta raba musu,tabbas don dare yayi ne
da bazan karya maka tsarinka ba,malam kai kemin fadan kaiwa dare a waje" Ta fada
murya a karye. Tanason masa ihsani,amma mutumin yana da wani irin kamewa da gudun
duniyar data tabbatar bazai karbi komai nata ba
"Shikenan,Allah ya karba.....kici gaba da kula da qannenki da kanki"

"In sha Allah malam" Ta fada tana yin qasa da kanta kunya da nauyinsa suna kamata.
Tana jin kamar inna ta gaya masa wani abu a kanta ko zata gaya masa,saidai ta sani
ko daya innar nada cikakkiyar kamalar da bazata taba fadin sirrin wani ba.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 49


Tunani ne kala daban daban cikin kanta sanda suke abun hawa har suka isa
gida.

Banda hadiyya data samu tana zance a farfajiyar gidan nasu bata hadu
da wani babba ba sai yara dake dan kai kawo a tsakar gidan nasu. Zuciyarta a karye
take bude musu qofar dakin. Wannan shine tabbacin basu da wani sauran gata.....ba
wani wanda ke tsaye yana jiran dawowarsu......babu wani da zai tambayi ina
sukaje?,me yasa suka dade wuni sur a waje?,ba wani me musu barka da dawowa,dasu
dawo da kada su dawo duk daya.....ire iren wadannan abubuwa ke qara mata wata
qaqqarfar zuciya tare da jin cewa.....ZATA SADAUKAR DA TATA RAYUWAR don samarwa
rayuwar qannenta gobe me kyau.....zata zame musu makwafin uwa da uba,dukkan wuya da
dadi.....zata hanasu dandanar duk wani kalar baqinciki na rashin gata dama rashin
abun kulawa da rayuwarsu.

Dukansu a qoshe suke kuma a gajiye,don haka basu jima ba kowacce ta nema
wajen kwanciya,don dama ita haneefa suna shigowa ta bingire a wajen.

Sau biyu tana yaye labulen tana duban tsakar gidan nasu. Wanka takeso
ta fita tayi saboda yadda gajiya kebin jikinta,uwa uba ma kuma ita din tun asali
mutum ce data saba da yin wanka da dare kafin ta kwanta,saidai kuma daga baya abun
ya zame mata qalubale babba,saboda kallon da ake mata da wasu idanu na daban.

Yadda ta fita dinnan ta wuni a waje ba zata iya kwanciya haka ba,don
haka taci gaba da dabuwa. Akwai daukewar qafafu sosai,wanann ya bata daman cire
kayan jikinta ta daura zani ta kuma lullube sassalkan gashinta da babban towel,ta
dauki kayan wankanta.

Tana shirin fita nepa suka kawo wuta,don haka ta tsaya ta kashe solar
din dakin ta maida musu nepa sannan ta fito.

Ta tsaya daga bakin famfonsu tana tarar ruwa. Tsakar gidan tarwai da
haske,kuma tsaf tsaf dashi,dabiar gidan qwaya daya tal dake burgeta,wanda idan ka
dauke wannan babu wani abu dake burgeta cikin gidan dama jama'ar gidan gaba daya.

Allah yasa har ta gama tarar ta wuce wankan ba wanda ya fito. Ta
kammala ta nade jikinta da zanin ta dauro towel din a sama ta fito.

Tana duqe baqin famfon tana daura alwala. Bude toilet din wankan da
akayi ya sanyata daga kai. Sukayi idanu hudu da ita,saita miqe sosai ta tsaya
maimakon dazun da take duqe tana daura alwala.

Kallon bibo din takeyi kamar yadda itama ita take kalla,tun daga
qafafunta har zuwa kanta da yake lullube da towel.

"Ha'illallahu.....mahammadurrasulillahi......ke duniya ina zaki damu?,aah?yanzu
wankan ma sai kinzo gida?" Bibo taja qaramin salati sannan ta kama haba tana sake
qarewa sabreen kallo.

Wani abune yazo ya yiwa sabreen tsaye a wuya,ta lumshe idanun takaici.
Ta gama fahimtar zahirin abinda bibo ke nufi......ta kuma gama fahimtar abinda inda
ta dosa,saidai kafin ma ta sake daga qafarta ta sake jin muryarta

"Kiji tsoron Allah 'yar nan......ki daina sanyawa mala'iku suna tsaida iyayenki cak
cikin kabarinsu......yanzu wannan wankan....." A fusace da kuma wani irin zafin
nama ta waiwaya tana duban bibo,abinda ya sanya towel din kanta zamewa sumarta ta
fito.

Bata qarasa ba itama sai tabi kan nata da kallo. A bushe yake ba kuma
alamun damshi ko lema,hasalima ta nannade doguwar sumar tata da tayi gado ta uwa da
uba a tsakiyar kanta ta cusata guri guda,wannan ya sanya bibo din hadiye abinda
taso fada din.

"Ke zaa cewa kiji tsoron Allah,kuma zan maimaita miki kiji tsoron Allahn" Ta fadi
da ita a nutse sannan ta fara takawa tana dosar dakinsu.

Idanma tace zata riqe zafin da qirjinta yakeyi da suya to tabbas ta
yiwa kanta qarya,don haka ta sulale saman kujerar falon ta saki wani marayan kuka.

Bibo na daya daga cikin qalubalen rayuwarta,bibo na daya daga cikin
mutane na gaba gaba da suke mata wata irin adawa mara fasali ba tare da tasan meye
ne ta tsare musu ba. Ta jima a wajen tana kuka har sai da fuskarta tayi wani pink
pink,sannan ta samu ta sauya kaya taja jikinta zuwa kan gadonta ta kwanta tana rufe
idanunta tare da sauraron bugawar jini daga kanta wanda keson komawa ciwon kai.

Sassanyan ringing dinnan shine ya sakata bude idanunta. Shaf ta mance
da batun wayar sai yanzu da tayi kuka. Tunawa tayi tayi alqawarin kai wayar a
yau,kada ma su tsammaci ko ta gudu da sune,wannan ya sanya ta miqa hannunta qasan
pillow din data ajeta dazu ta dauko da nufin dagawa ta basu uzurin gobe in sha
Allah aje a karba.

Bata wani tsaya bata lokacin duba me kiran ba,tunda tasan koma waye zai
kira a irin wannan lokacin tabbas makusanci ne,don haka ta shafa ta daga ta kuma
Kara a kunnenta.

"Assalamu alaikum anni?" Ya furta cikin husky voice dinsa dake cakude da wani irin
nannauyan sauti dake nuna izza da zatin mamallakin muryar. Yayi sallamar a sanda
yake tsakiyar system da kuma tarin tarkacen takardun dake dauke da plan na ginin
sabon kamfanin samar da kayan qyale qyale na mata mafi tsafa da daraja da za'a
dinga qawatashi d wani yanki na diamond d gold.

Wani yankewa gabanta yayi ya fadi,zuciyarta kuma ta buga sosai har tana
jin sautin bugun cikin kunnuwanta. Batasan dalili ba batasan kuma me yasa taji
hakan ba,sai ta buda bakinta a hankali da muryarta da tayi nauyi saboda nauyin dake
cike a qirjinta

"Ba ita bace". Shuru ne ya biyo bayan fitar sautin nata. Ita tana bawa kanta
tabbacin wancan mutumin ne daya kira duba da shurun da aka sakeyi mata kaman
dazu,shi kuma kwanyarsa tana son alaqanta sautin da muryar mara kunyar yarinyar nan
data dag masa waya.

Kusan a tare suka daga wayar daga kunnuwansu. Ta samu tabbacinne ta
hanyar karanta sunan dake yawo saman screen din.

Sauke wayar yayi daga idanunsa,yaja siririn tsaki yana kashe wayar.
Sautin tsakin yakai mata har kunnenta,wani mummunan baci taji ranta yayi. To ita
meye nata a ciki da har zai bita da tsaki?,waye wannan daya cika izza haka?,wanne
irin mutum ne me izgili da rashin sanin daraja da martabar dan adam?,don kawai a
bisa kuskure wayarsu ta fado cikin kayanta sai ta zama abar wulaqantawa?. Samun
kanta tayi da latse wayar kawai ta kasheta gaba daya ranta yana suya,cikin ranta
kuma tana yiwa kanta alqawarin a gobe wayar ba zatakai sha biyu na rana ba a
hannunta zata kira busari yakai musu duk inda suke.


"Wanne irin wulaqanci ne da rashin sanin abinda kukeyi da zaku ci gaba da barin
wayar anni a wani wajen?" Fuad din ya furta daidai sanda ya kira musaddiq.

"Kayi haquri hamma,ta fadi inda za'a karba anje ba'a samu ba,anyita kiran wayar
kuma ba'a dagawa".

"Koma meye banason na sake kira naji muryarta.....kuyi magana da ita idan wayar
takeso ta sauke layin daga kai,ka sanya ayima annin swapping a dauki wata wayar a
hada mata".

" Ka kwantar da hankalinka me babban suna,banjin yarinyar tana da niyya ko nufin
riqe wayar nan,akasi kawai dai aka samu da ajizanci irin na dam adam......tana da
kirki qwarai,ita ta kaini asibiti ta kuma zauna dani har sai da musaddiq ya iso".
Wata sassanyar iska ya saki daga bakinsa,sai yanzu ya tuna inda yasan muryar

"Itace mara kunyar yarinyar nan data tsaya tana yiwa mutane fada akai don ta kaisu
asibiti?" Ya jefawa anni tambayar da nutsatsiyar muryarsan nan.

Murmushi ne ya subucewa annin. Tasan halin fu'ad qwarai da gaske. Yana
da tsananin kamewa da rashin son shiga sabgar kowa

"Ba rashin kunya tayi ba muhammadu......fada ta yiwa musaddiq,kuma ai ta fadi
gaskiya ne,ta kuma yi daidai,sun tafi yawonsu sun barni,a jikina kuma babu inhaler
kwata kwata,a nata ganin indai hakan taci gaba da kasancewa komai ma yana iya
faruwa". Shuru ya ratsa tsakanin bayanin anni,yana ji kawai annin tana son bata
kariya ne saboda halinta na bawa kowa uzuri komai girman laifin da ya aikata mata

"Is okay....." Ya fada yana sauke siririyar ajiyar zuciya a qoqarinsa na fesar da
bacin da ranshi yayi

"Ya jikin naki anni?"

"Jiki alhamdulillah na warware"

"Suna kula dake kuwa?" Ya sake tambayarta da wannan seriousness din nashi. Murmushi
ta saki kadan

"Qannenka suna qoqari sosai,ina samun kulawa tamkar kana nan.....saidai kewarku,ina
fatan komai yana tafiya kaman yadda aka zata?,kowa kuma yana lafiya?" Murmushi ya
saki,wanda mutum uku keda wannan baiwar sakashi murmushin koda baiyi niyya ba,anni
abba da farouq kada ma farouq din yaji labari. Abune me wahala ka tsinci murmushi
akan fuskarsa,akwai mutane da yawa dake da tambayoyi da yawa a kansa

Anya kuwa ya taba dariya?
Wannan kuwa yana murmushi?.

Wasu tambayoyin na isa kunnensa ta harshen farouq,wasuma kam baisan ana
yinsu ba.

"Ba zamu wuce kwanaki hudu ba anni in sha Allah". Farinciki ya wadaci fuska da
zuciyarta

"To ma sha Allah.....amma baka shaidamin ba me babban suna?,banda na tambayeka da
ba zaka gayamin ba ko?".

"Aah anni......banason na sanyaki wannan hidimar me yawa" Murmushi ta sake saki

"Hidima ai bata qarewa Muhammadu muddin akwai rai a jikina.....fatan da zakuci gaba
da yi mana shine Allah ya qara mana lafiya....."

"......da nisan kwana me amfani" Ya qarashe fadi. Qaramar dariya ya sanyata a
wannan karon

"To da nisan kwana me amfanin mu daku gaba daya".

Koda suka gama wayar baiko motsa ba a wajen,yayi zaune da wayar kawai
a hannu yana juyata. Duk yadda zai fasalta anni a rayuwarsa da zuciyarsa bazai
kwatantu ba. Ita din uwa ce data amsa sunanta na uwa. Wadda tayi sadaukarwa da yawa
cikin rayuwarsu,sadaukarwar da tayi musu ba qarama bace,sadaukarwa ce da UWA kadai
ke iyayi wa danta.

Asthma dinta bata taba hanata taba ruwa saboda su,asthma dinta bata
taba hanata sammakon tashi koda da sassafe ne a lokacin da hazo da sanyi suka
lullube sararin samaniya......a yanayin da kuma yafi zama barazana ga masu
lalurar......asthma dinta bata hanata tsaftace musu muhallin kwanansu......bata
hanata dafa musu abinda zasuci

*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 50


koda ita din bataci ba,bata kuma hanata kulawa da lafiyarsu koda ita din
bata da cikakkiyar lafiya. Har tsakiyar zuciyarsa yana jin wata qauna me girma tana
tabashi game da anni,tayi musu abinda baki bazai iya fadi ba,zuciya da ruhi ba zasu
iya mancewa ba. Ta musu hidima da jikinta da kudinta da lokacinta harma da
lafiyarta,irin hidimar da ya debe tsammanin zasu sameta,irin hidimar da suka
buqaceta a yunwace daga wajen wadda tayi silar zuwansu duniya amma ta
gagaresu.....kulawar da baiyi tsammanin zasu sameta ba daga gurin kowacce mace a
duniya. Baiga abinda zai samu a duniya ba da zai manta da anni.....baya tunanin
akwai abinda anni zata nema daga gareshi ta rasa.

Yana shirin sauke wayar tasa don ya tattara tarkacensa ya wuce daki ya
samu bacci koda na awa biyu ne kafin zuwan lokacin sallar asuba sai kiranta ya
shigo.

Kamar ko yaushe ya zubawa kiran idanu,a duk sanda zata kirashin sai ta
tuna masa da abubuwa masu yawa. Aduk sanda kiranta zai shigo wayarsa saita tada
masa wani abu daga can qasan zuciyarsa.

Bashi da wani zabi da ya wuce ya daga din,sai ya sake zama sosai ya ya
dauki wayar yana karawa a Kunnensa,

Cikin jin isa da izzar cewa ta haihu.....cikin isa da jin izzar ita din
a yanxu wata abace cikin duniyar.....cikin jin izzar ta isa takai qololuwar gata a
cikin jerin iyaye mata ta amsa sallamarsa.
"Barka da dare.....an wuni lafiya?". Maimakon ta amsa masa saita sake daidaita
kanta,a dake take masa magana

"Yanzun ace bankai kima da martabar da a kullum zaka kirani kaji ya na kwana ya na
tashi ba?" Ta maida masa gaisuwar da qorafin abinda me masa suya a qirji.

"Afwan.....kiyi haquri" Ya zabi furtawan. Har cikin zuciyarsa,har kuma tsakaninsa
da Allah kirantan kaman yadda take buqata wani baqon abune cikin rayuwarsa dama
lokutansa. Yadda ta zamewa rayuwarsu baquwa haka dukkan wata mu'amala da zaiyi da
ita take zama baquwa a wajensa. Koda yayi niyyan yin hakan saboda sauke nauyi da
haqqin haihuwa dake wuyansa sai ya manta sam sam,tunda abune da aka fareshi bada
dadewa ba,sabo dashi kuwa zai dauki lokaci kafin ya shiga jiki da zuciya,bayan haka
ma......kwata kwata mu'amalar dake a tsakaninsu wata irin tattaurar mu'amala ce da
babu taushi a jikinta bare ta shiga zuciya da kyau ta tsayema tunani.

"Koda baka nemeni ba ni bazan zubewa duniya ku ba.....ku zama inuwar giginya na
nesa kasha dadi...." Ta fadi tana watsa hannuwa ba tare data tuna da kuskuren
rayuwarta na farko ba.

Numfashi ya aje,maganartata ta zama tamkar wani tuni ne daya dace ace
kanta da kanta ta

Please Login or Register in order to submit comment