You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qarqashin hidimata kuke....baqinmu ne ku daga South
Korea".

"Sannu sarkin noma.....godiya muke" Shima abban ya fada cikin barkwanci bayan ya
shiga motar.

Dashi da farouq din baya suka shiga bayan ya bawa shugaban security
dinsa umarnin su bisu a baya.

Kusan duka a hanya ma dai tattaunawar ta kasuwanci ce. Farouq din yana
bawa abban labarin yadda abubuwa suka kasance bayan tafiyarsu

"Amma tabbas sai ka sake sanya idanu akan mika'il.....ina suspecting wani abu
tattare dashi,duk da bana ce gashi ba,amma nasan kai din zaka fini fahimtar komai"
Farouq din ya furta.

Idonsa fu'ad ya dauke daga kan wayar hannunsa,wanda saqon mika'il dinne
ya shigo,mutum na farko daya fara masa saqon barka da dawowa kafin kowa. Bai cewa
farouq komai ba,amma kuma maganar tasa ta samu gurbi sosai a zuciyarsa ta zauna,sai
ya gyada kansa a hankali yana sake maida dubansa ga wayar.


**"Anni an gama komai" Ta furta sanda take saukowa daga saman tsararren dining area
din daya dauki kyakkyawan family dining table na wani mulmulallen tangaran kai kace
an samar dashi ne daga burbushin diamond ko gold da kamfanin jadda ke wankewa su
fiddashi. Fara ce tas,mai matsakaicin tsaho,saidai bata da qiba ko qanqani. Yanayin
sumar gaban kanta kawai zai fada maka akwai suma me yawa a saman kanta wadda bata
da duhu ta danyi brown kadan bame yawa ba. Yanayin yadda ta datsi daurin
dankwalinta daga tsakiyar kanta shi zai baka daman ganin hakan sosai. Straight gown
ce a jikinta ta atamfa me igiyoyi hagu da dama wadda ta daureta daga gefen qungunta
guda daya.

"Ma sha Allah.....sannunku da qoqari....sun wuce ne?" Anni data daga kanta daga tab
din hannunta da take duba wasu addu'o'i ta fada.

Fuska tadan yamutsa kadan tana zama kujerar gefan annin gami da ajiye
qaramin towel din hannunta a side table sannan ta dauki wayarta dake ajiye akai
tana qoqarin budeta

"Kowa ya wuce......yanxun abba da hamma kawai muke jira" Ta qarasa maganar
murmurshi yana subuce mata.

"Umhummm......wato shi saddiq shine marainin wayonki da baki ta tasa ko?" Anni ta
fada tana maida idanunta ga addu'o'inta . Fuska ta yamutsa,duk da bata kalli annin
ba amma ta amsa

"Bar wannan anni,wa yake ta tasa,ba abinda ya iya sai takurawa mutum ba
dalili......hamma takurawarsa me dalili ne idan bakayi abinda yace ba ko baka
kiyaye dokarsa ba......amma yaa saddiq.....hmmmm....ko wayar nan yanzun ya shigo
yana ina dannawa sai yayi challenging dina" Ta qarasa maganar tana zamewa ta
kashingida saman kujerar tana maida hannunta kan shafinta na X.

Ita da annin kowa ci gaba yayi da uzurin gabansa,wannan ya bawa falon
daman daukan shuru na wani lokaci kafin ta daga kanta. Haka kawai ta qarewa anni
kallo sai ta saki dariya

"Anni.....kinsan tsadar kayannan?" Ta fada tana kallon kwantaccen lace din jikin
annin dake wani yauqi da santsi duk kuwa da cotton ne. Peach color da ratsin
green,bashi da nauyi ko kadan

"Saikin fada 'yar kasuwa......" Ta amsa mata ba tare data dubeta ba

"Anni Allah hamma yana shagwabaki......ki zauna da kaya me tsada haka a gida duk
dogayen rigunanki?....amma dai....to,hala abba aka yiwa kwalliya?" Ta fada qasa
qasa tana qunshe bakinta da hannu. Kadan ta dubeta ta harareta

"Akwai kayan da sukayi tsadar da zan kasa yiwa abban kwalliya dasu?" Kai ta girgiza
tana qoqarin maida kanta ga wayarta tana qoqarin boye dariyarta

"Babu anni.....anni ta abbanmu".

"Amna.... Qoqarin maidani kakarki kike ko?"

"Aah anni wallahi" Ta fada da sauri tana duban anni still tana son shanye dariyarta

"Kici gaba.....inajin zan dauki shawarar farouqu ne,zaki komawa nanna ne kiyi
zamanki a can". Kyabe fuska tayi da kyau tana aje wayarta gefe kaman zata saki kuka

"Dama haka yaa farouq din yace?,duk haqurin zama cikin mazan da nakeyi ban da
sister?....."

"Oho koma.meye gwara ki koma can,tunda kinga can dinma akwai mata 'yan uwanki sai
kinfi jin dadi". Sosai ta sake kwabe fuska tana duban anni

"Da gaske anni zaki iya bayar dani?" Daga kai tayi ta dubeta
"Ba mace bace ke?,wataran ba aure zakiyi ba?" Ta tambayeta,ai kuwa saira soma matsa
hawaye tana juyawa annin baya

"Ai dama na sani......gidan nan babu wanda yake sona sai hamma da abba na......shi
dama yaa farouq kaman ya bayar dani kyauta yakeji.....ni bazanyi aure ba.....dake
zan yita zama". Yadda tayi maganar zata yita zaman da ita sai ya bawa anni dariya
amma ta dake

"Sai kiyi kuma" Tace tana ci gaba da scrolling sama tana duba adduo'inta.

"Kinga.....ki daina biyewa ta BB farouq.......indai ina nan ba wanda zai
matsa miki.......i swear" Muryar musaddiq ta biyo bayan sallamarshi. Tuni ta miqe
ta zauna sosai tana qoqarin goge hawayenta.

"Kaima kana biye musu yaa musaddiq wani lokacin.....amma dai ka fisu" Ta fada tana
daidaita zamanta saman kujerar.

Qaramar dariya ta qwacewa anni tana qoqarin ajiye tab dinta a gefe

"Uhumnnn..... Ai dama ba kasafai akewa amna abun arziqi ba.....wanda ke mata abun
arziqi kai tsaye a gidannan Muhammadu ne......har kun dawo?" Ta tambayeshi tana
duban musaddiq dake dariya qasa qasa.

"Eh anni.....su abban basu iso ba?"

"Sun sauka amma basu qaraso gidan nan ba.....amma na tabbata suna dab da isowa don
tun dazu suka tafi daukosu". Ta amsa masa tana miqa hannu ta karbi purse din nata
da yake miqa mata.

Tana yunqurin budewa su kuma suna magana tsakaninsu shi da amna. Ta
zuge jakar cikin rashin tabbas da yaqini,ta bude ne kawai don taga meye yayi saura
a cik,me ta samu?,amma ga mamakinta sai ta samu komai a muhallinsa ba tare da an
canzawa komai waje ba bare a cire wani abu,sai wayarta data nuna low battery da
alama ba'abi ta kanta bama bare a sakata a charge.

"Ikon Allah" Ta fada,abinda yaja hankalin amna da musaddiq kanta

"Ba abinda aka rasa a ciki musaddiq.....ba abinda ta taba kota dauka" Ta fada da
mamaki idanunta cikin jakar

"Nima dana bude nayi mamaki,amma nace bari na kawo miki ki duba komai bansan ko
akwai wani abun daban ba"

"Aiko yadda na zuba kudin a jere ba'a canza tsarinsu ba" Ta fada tana sake fiddosu

"Amma dai ka yiwa yarinyar godiya ka karbamin number wayarta ko?,ko mamarta na sake
yiwa godiya?"

"She's not natural fa anni" Ya fada a taqaice

"Kamar yaya?" Ta tambaya cikin rashin fahimta.

"To nidai anni ko qyallinta ban gani ba,a bakin wani waje wani ya tareni ya
bani,baicemin komai ba ya juya,nima haka na juya da kan motata na dawo gida"

"Ikon Allah......gashi bata bari ko sau daya na mata godiyar alkhairin data yimin
ba.....na kasa manta damuwa da kulawar data nunamin" Annin ta fadi tana juya abun a
ranta.
Bai samu ce mata komai ba saboda qarar bude gate da shigowar motocin
da suke da tabbacin baqinsu sun iso

"Alhamdulillah" Anni ta fada tana murmurshi gami da ajiye wayar da jakar a gefe.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

PAGE 53



Dukkansu da sallaman a bakunnasu suka shigo. Suka amsa musu suna miqewa
tsaye tare da dakon qarasowarsu cikin falon,saidai amna ta kasa jurewa. Da sauri ta
taka zuwa bakin qofa ta riqe abbannata da kyau tana dariya idanunta saman fuskar
fu'ad

"Abba sannu da zuwa....hamma....hamma sannu da zuwa" Ta furta matsanancin murmushi
yana subuce mata

"Sannu 'yar abba qanwar hamma.....hamman dai aka matso a tarba aka fake da abba".
Abban ya fada yana lakuce mata kumatu. Dariya suka saki fu'ad yana tayasu da
murmushinsa

"Amnee......barkammu" Ya amsa mata cikin kulawa. Sakin abba tayi ta matsa dab da
fu'ad din tana karbar briefcase dinsa

"Su amna an iya munahirci" Muryar sadiq ta shiga kunnenta,sadiq din dake tsaye ta
bayansu abban. Gotasu tayi kadan tana leqensa,sai ta bata fuska

"Duk abinka bazanyi welcoming naka ba.....abba me yasa baku samu wata bolar South
Korea kun yar dashi kun gudo ba?" Ta qarasa tambayar tana kallon abba a shagwabe.
Ba wanda maganar bata bawa dariya ba a cikinsu

"Idan muka yar dashi ke zaki fara qorafin muje mu dauko miki shi ai"

"Allah bazan nemi wannan ba....."

"......me qarya?" Saddiq ya datsi numfashinta yana fadi idanunsa a waje

"Dan aljanna" Ta fadi tana juya idanunta abinda zai sake tabbatar maka da sauran
quruciya a tare da ita,hakanan kuma tana fama da sakalcin auta da gasken gaske.

Kasa jiran isowar abban tayi,sai ta taka ta ruskeshi a tsakiyar falon.
Ta rusuna tana masa sannu da zuwa gami da gaidashi duka tare da qoqarin amsar
qananun tarkacen dake hannunsa. Cikin nashi tsananin kulawar da kallon kewa yake
amsa mata,fuskarsa ta wadatu sosai da fara'a yana tambayar lafiyarta dama ta
jama'ar gidan gaba daya.

Hankalinsa yana kansu,qauna da kulawar dake tsakanin anni da abba sune
abu guda daya tak da suka rage wadanda suke bashi hope din wataran qila zai iya
aure. Soyayyar da sukema juna wani irin dasashen abu ne da har yanzu yake tasiri a
tsakaninsu,babu alamun gushewa sam sam. Yanayin rayuwarsun yana burgeshi,wata irin
mu'amala annin kewa abba,irin mu'amalar da bai taba ganinta ba tsakanin MAAMAHnsa
da ABBEY dinsa ba. Mu'amalar da bai taba zaton akwaita tsakanin miji da mata ba sai
a wajen annin.
Gabanta ya qarasa shima kaman ko yaushe,cike da ban girman nan da yake
jinsa har cikin ruhinsa ya tsugunna yana gaidata. Bata iya tsaiwa saman kanshi ba
saboda girman shima da take bashi sakamakon sunan MUHAMMADU da yake dashi......da
wata ajiyayyar kima da martaba da take ganinsa dashi saboda dattakon halinsa data
sani tun bai cika shekara sha takwas bama a duniya.......uwa uba yadda yake
tattalin farincikinta kadai ya sanya kowanne lokaci takejin tamkar jikinta ya tsaga
ya fito.

"Lafiya alhamdulillah me babban suna.....jiki na warware tun tuni......dama ta jima
bata tashi ba,akasi kawai aka samu a ranar,nafi tunanin kuma matar da mukayi salla
tare ne turarenta yayimin qarfi da yawa".

Dan qwarya qwaryar zama sukayi cikin falon na duba lafiyar juna,qananun
zolaya tsakanin amna farouq da musaddiq abban yana shiga yana raba gardama kafin
daga bisani anni tayi umarni

"Abinci ya zama ready.....zaku shiga ku watsa ruwa tukunna ko?" Ta fada tana duban
abba me gayya me aiki

"Hakan yana da kyau ko me babban suna?" Ya maida tambayar ga fu'ad. Murmushi kadan
ya saki,suna girmama ra'ayinsa qwarai,sunan da yake dauke dashi ya bashi wannan
girman a iyalin da suka san girma da martabar sunan. Wani abu da sam sam bai gani
ba ga maamah,tana iya kiransa a lokacin quruciya da sunan ta kuma zabga masa zagi
fada da sauransu

"To abba" Ya amsawa Alhaji hamza yana miqewa. Farouq ne ya miqe ya dauki luggage
din fu'ad din yana nufar qofa

"Muje na taka maka badon halinka ba......don wallahi ka shiga uku duk sanda mukayi
aure muka barka kai kadai a gidan nan". Yayi maganar qasa qasa yadda su abba ba
zasuji ba.

Harara fu'ad ya zabga masa yana jan qaramin tsaki

"Sannu tattabara sarkin aure?,yanzun ma idan kaga dama ka koma mana ka
gani?......ni gwara fa ku qara gaba ku barni daga ni sai anni ko mayi kumari".
Dariya ya fashe da ita harda buga qafa kadan

"Kayi asara wallahi.....kai ta qara qiba ma kake,kaci gaba da gandamewa a gaban
annin?,idan bakayi wasa ba gaba gaba sadakarka za'a bayar Allah......"

"Munyi asara dai ni dakai mayen aure......idan kun tashi kuyi shelata a masallacin
juma'a".

"Basai munkai ga nan ba......owner na diamondchore resources company guda.......ko
a sirrance akayi shelarsa mugun ciniki zamuyi Allah,a zaba maka guda hudu
qwarara......matsalar kawai har yanzun ni kaina bansan color na macen da kakeso
ba.....". Shammatar farouq din yayi yakai masa wani wawan duka sai daya qame,don
maganar ta fara isarsa,yasan kuma farouq baisan bari ba,baisan ya isa ba.

"Kaci bashi......sai na dauki fansa.....ka qarasa cikin da kanka na fasa rakiyar"
Ya fada yana jingine masa luggage dinsa daidai qofofin sassansu

"Tafi nono fari" Fu'ad din ya fada yana zura key ma qofan sassansa yana
budewa,saidai fuskarsa kwance take da murmushi yana juya halin farouq din. Shi daya
farouq din yakewa haka.....kamar yadda shima farouq din kawai ke akwai 'yar hakan a
tsakaninsu.
"Alhamdulillah" Ya furta a sarari murya can qasan bayan ya isa ainihin bedroom
dinsa,yana jin ma'anar godiyar daga qasan zuciyarsa. Tarin godiya ce fal zuciyarsa
game da ubangijinsa,godiyar da har wani lokacin ya dinga jin baisan ta yadda
zaiyiti ba takai gurbin da akeso. Ubagijinsa ya gama masa komai.....ya kyautata
rayuwarsa fiye da yadda yake tsammani.

Komai na sashen nasa a killace a kuma tsaftace akan tsari fiye ma da
yadda yakeso. Wani irin qamshi ke tashi,abinda ya sanyashi sakin wata nannauyar
ajiyar zuciya data sanya yaji wani nauyi ya ragu sosai daga saman zuciyarsa. Yana
yiwa qamshi wani jarababben so,a duniya qamshin yana daya daga cikin jerin abubuwan
da yafi qauna. Qamshi yana sanyashi maqalewa waje,kaman yadda akasinsa ke sanyashi
rabuwa da waje.

Yana iya baiwa farouq dinsa komai amma indai ta fannin abinda ya shafi
turare ne to zaka iya jin musunsa dashi. Bai yarda ba a taba masa turaruka,gwara ka
zaba ko na nawa ne ya siya ya baka kyauta.

Kayan jikinsa ya dinga zarewa har sai daya rage saura fara qal din vest
din jikinsa da gajeran wandon da bai qarasa gwiwarsa ba. Muradadde kuma ginannen
jikinsan nan dake dauke da wasu lafiyayyun muscles dake alamta ainihin qarfi na
siffa ta zahiri da badini ya bayyana,lullube da wadatattun gargasa ta ko ina.
Wankan yakeson yayi amma shigowar kira ya hana masa hakan,tilas ya samu saman sofa
bed ya zauna yana amsa kiran.

Amsa kiraye kirayen ya daukeshi lokuta masu tsahon da har musaddiq ya
dinga zuwa dubashi zasuci abinci. Daga qarshe ya basu excuse akan suci din idan ya
kammala zai fito.

Fitowar da bai samu daman yi ba kenan,don sanda ya fito a wankan gaba
daya kasala da tsohuwar gajiya ce ta saukar masa,dole ya haye gadonsa bayan ya
maida da dakin dark ta sakin dukka manya manyan curtains dinsa,ya kuma kashe
kowacce fitila da zata iya bashi haske don baya son bacci a duhu sam sam. Koda
baccin yakeyi kana kunnata ka tasheshi. Sunsha fafatawa da farouq akan hakan,don
shi mutum ne da kwana cikin haske bai dameshi ba. Wannan dalilin yasa ko a yanzun
yafi sha'awar kowa ya zauna a sassansa,ba kasafai ya fiya son takurawa mutum da
salon tsarin rayuwarsa ba.

*****Su biyun dukansu suna zaune ne saman buzu na fatar dabbar da basusan wacce iri
bace. Kaman yadda dukkaninsu jikinsu ke sanye da sutura ta alfarmar da zaka fahimci
rayuwa ta basu sukuni yadda ya dace,saidai tasu salon miqa godiya wa mahaliccinsu
da suka munana hanyarta.

Daga atamfar jikin hajja har lace din da maahma ke sanye dashi wanda ya
darawa atamfar hajjan tsada isashen jari ne ga mutane masu yawan gaske. Kaman yadda
jakar maahma din da takalman data sanyawa qafafunta suke wani jarin me zaman kansa
ga wasu mutanen. Takalmin da fu'ad din yayi mata order dinsa da kanshi tun daga
qasar Italy.

Kusan yadda ta bawa mutumin dan duqurqushi me zubin wada hankalinta
hajja bata bashi nata haka ba.

Daya daga cikin qoqunan gabansa da suke kife ya daga,qoqon da babu
komai amma saiga haske ya cikashi. Tafukan hannayensa ya saka yana rufe qwayar da
hannunsa nasa. Idanunsa ya runtse,wasu irin maganganu ya dinga furtawa da ba'a gane
abinda yake fadi,tun yana fada a hankali a hankali har ya fara furtawa da sauri da
sauri da kuma qarfi har muryarsa tana amsa kuwwa. A hankali jikinsa ya fara wani
irin kakkarwa tamkar wanda aka jonawa shocking. Da wani irin sauri yan fusge
hannayensa daga saman qwaryar yana yarfar dasu kamar wanda wuta ta taba,sai kuma ya
sake maidasun yana canza salon yaron da yakeji ba irin na dazu ba.
Ya kusa minti biyu a haka,wata irin zufa da basusan daga ina take ba ta
gama jiqeshi sharkaf.....a hankali a hankali ya soma sassauta muryarsa sannan ya
fara daidaita yanayinsa kafin ya bude idanunsa da suka ninka ja akan asalin jan da
suke dashi.

"Matso!" Yace da maamah a tsawace. Tsoro ba kalma bace da ta santa ba kaf ray
uwarta......qafafunta sun taka gurare da dama amma a yanzun saita samu kanta cikin
shakka da d'ar d'ar har ta matso zuwa inda yake mata nuni

"Ba shine wannan ba?" Ya fada da qarfi yana nuna mata qoqon.

Fu'ad ne kwance saman gadonshi yana baccinsa hankali kwance kaman yadda
ya kwanta a ainihin dakinsa dake gidan Alhaji hamza kibiya. Mamaki ya qarasa
cikata,ba shakka fu'ad ne,kuma dakin ya mata kama da dakunan gidan Alhaji hamza,sun
dawo kenan kaman yadda yake shaida mata dazu da sassafe kan suna hanya?.

Daga ita har bokan ba wanda ya samu cewa wani abu dif hoton dake
cikin qwayar ya bace kaman an dakeshi harda tartsatsin wata wuta.

"Kin gani ko?,ba mutumin da muka sha wahalar kawoshi zuwa garemu saishi......baya
ga haka kinga yadda surarsa ta dauke da gaggawa......abinda ke bamu tabbacin
aikinsa yasha banban da dukka ragowar aiki da muka taba yi a baya......akwai tashin
hankali......akwai wahala.......akwai kuma qalubale!!!" Ya furta da kakkausar
muryarsa mara dadin amo da sauti bare sha'awar saurare.

Dukkan kayan aikin nasa ya tattara ya zuba cikin qwarya daya daga
cikin qorai biyu dake gabansa,take suka bace bat tamkar ba'a taba halittarsu ba a
wajen.

Jajayen idanunsa da babu rahama,musulunci ko imani a ciki ya daga ya
kalli maamah dake dubansa babu ko qiftawa.


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*


PAGE 54


Idanu yadan zuba mata na wasu mintuna da har sai data dan sha jinin
jikinta. Sai kuma ya saki wani busashen murmushi da yafi kama da kukan jaki yana
kallonta

"Ba shakka kin haifi jarumi......kin haifi yaron da taurarinsa suke da tsananin
hasken da ba kasafai ake samun galaba ayi kutse a cikinsu ba ko asha
kansu.......yaronki yana tattare da abubuwan al'ajabi da baiwarwarki masu yawan
gaske wadanda ko ke uwar da kika haifesa bakisan yana dasu ba......cikin mutane
dubu guda daya ake iya samu irinsa......". Kai kawai take jinjinawa tana
sauraronsa. Tun sanda ta haifi fu'ad din tasan daban yake da sauran yara,to amma a
yanzun kalamansa daga mata hankali sukeyi,kamar sunason shinshina mata rashin
nasararta ne......kamar suna shinshina mata rashin yiwuwar aikinta?.

Maganarsa ta gaba ta bata amsa ta kuma yanke mata dukkan zatonta

"Aiki a kansa ba qaramin abu bane me girma......akwai tsari a jikinsa......yana da
addu'a sosai tare da kare kowanne abu da musulunci yayi umarni akai.....baya shan
giya.....baya zina.......baya kallace kallacen abubuwan haramun......hasalima
azumin da addininku yace a dinga yi litinin da alhamis baya wuceshi.....abinda zai
bada mamaki banda wannan uwar goyon nasa da uban goyonsa ba wanda yasan yanayin
wannan azumin koda farouq makusancinsa......."

"Kana nufin yanzu mallakar da nakeso ayi masa.....da shiga tsakaninsa da iyayen
goyonsa bazai yiwu ba kenan?" Ta dawo dashi zuwa ga ainihin amsar da takeso taji.

"Zaki iya samun biyan buqata.....zaki kuma iya samun faduwa......biyan buqatarki ya
ta'allaqa da adadin sadaukarwar da zakiyi da kudaden da zaki ajiyewa shaqiqanmu don
suyi miki yadda ya dace......amma fa....." Ya fada yana daga yatsa

"Tabashi abune da zai iya zuwa da hadari......mafi qarancin sakamako shine a gaza
yin nasara a kansa......muddin rashin nasarar ta zarta haka kuwa.....dani da dukkan
wani shaqiqi da mukayi aiki dashi zamu iya samun nakasa,harda shudewa daga rayuwa
ma idan ta dauro,saboda haka......aikinki aikine me tsadar gaske " Yayi maganar
yanayin muryarsa daga qarshe yana canzawa alamu dake nuna saukar mutanen boyen da
yake aiki tare dasu a kansa.

Tsoro yadan shigeta kadan amma ta dake

"Kamar nawa zai kai?" Ta fada a dokance

"Kalli nan!" Taji an furta daga bakin mutumin amma da mabanbantan muryoyi marasa
dadi da batasan mutum nawa bane suka hadu suke maganar.

Waiwayawa tayi tana duban inda ya daka,saiga lambobi a jere wanda data
dubesu da kyau suka bayyana kansu a matsayin million goma.

Sosai adadin ya daketa,duk da tasan a qa'ida tana cikin arziqin data
bawa wannan adadin baya amma kuma batakai ga samunsu ba zuwa yanzu. Ta waiwaya ta
kalli hajja dake zaune tana kallon komai,don dokarsa shine me matsala dashi yake
magana. Da idani ta mata tuni da tsarinsa,baya yanka kudi a nemi ragi.....daya daga
cikin kusakuren da zaka iyayi wanda zai tunzurashi kenan.

Kamar wadda wuyanta ya qage ta maido dubanta gurin,saidai zuwa sannan
lambobin da hasken da suka nuna mata yawan abinda zata biya din ya shafe daga wajen
ba komai. Ta maida kallonta ga duqurqushin bokan da kamanninsa suka juye,saita
gyada kanta

"Na karba na aminta"

"Karki qara minti daya a wajen nan......kizo da sadakin aikinki kuma nan da kwanaki
uku kacal" Daga haka ya bace shi da dukkan sauran tarkacen dake wajen,sai gurin ya
rage daga ita sai hajja din. Zumbur suka miqe kaman yadda ya umarta,suna riqe da
hannun juna suka fara fitowa daga sarqaqiyar har suka cimma inda suka faka motarsu.

Sau biyu hajja tana juyawa tana kallon maamah wadda ta kafe kwaltar da
driver ke zabga gudu akai. Tunda suka fito daga wajen bata ce komai ba,magana bata
hadasu da kowa ba. Tun a dazun ta fahimci tayi nisa ne qwarai a tunani,kaman ta
qyaleta amma sai ta kirayeta don tanaso taji ta bakinta

"Banji kince komai ba tunda muka fito?" Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke sannan ta
dora idanunta akan na hajja din

"Daga yanayin ayyukansa,da kuma bayanansa kawai na gamsu cewa aikinsa me zafi
ne......abinda kawai ya tsayemin a rai yanzu shine ta yadda wadannan kudaden zasu
samu" Tayi maganar alamunta suna nuna lallai lallai a matse take da buqatar mafita
"Danki ne,dole ki bashi umarni yabi don babu wata uwa sama dake......idanma hakan
bai yiwu ba,cikin kadarorinki ki saida wani abu.......ko kice masa wasu zaa yiwa
wani abu da kudin da zarar yasa anyi abun ki saida abun kiyi zarafin gabanki".
Ajiyar zuciya ta sauke ranta yana mugun baci

"Yanzu har takai idan ina da buqatar abu a wajen dana saidai nayi qarya ko na biyo
ta wata hanyar?" Ta yiwa hajja tambayar.

"Biyan buqata ai yafi dogon buri,kome ya faru.....kuma kome kika saida,wuyarta aiki
yayi yadda akeso......sai kin maida ninkin baninkin da bakisan adadinsa ba......sai
kin karba kin gaji......saikin tara fiye da yadda kike buri......saikin zame musu
tamkar abun bautarsu wajen yi miki biyayya.....a yanzun da zan kira auwal dake wata
qasar,nace masa ya dawo nigeria yau yau inason ganinsa.......na rantse miki da
Allah a qasar nan zai kwana,koda babu jirgi bazai kwana a gida ba saidai a
airport.......saidai idan nice nace masa ya koma gida ya kwanta ya taso
gobe......koda ya koma bashi da cikakken nutsuwa har sai gari ya waye ya kawo kansa
gareni......bari yau zan nuna miki qarfin ikona ki gani da kanki" Ta fada tana
fiddo wayarta daga jakarta.

Kai ta jinjina kawai tana dubanta,tana jin inama ace itace
hajja?.....tana hasashen ranar da wannan damar zata samu a hannunta?.....tabbas
saita sanya aminatu kuka da idanunta........sai ta sanya zuciyar aminatu da hamza
sun buga da qasqancin da zasu gani daga yaran da su suka rainesu har suka zama
abinda suka zama a yanzu

(Tabbas gaskiya ne da akace ka guji sharrin wanda ka kyautatawa.......me makon jin
dadi kyakkyawan fata da kyakkyawan mu'amala ta shiga tsakaninsu da mutanen da suka
maida mata 'ya'ya mutum.....amma ga nata salon sakamakon,Allah kayi mana tsari daga
sharrin dukkan wani abu me sharri mutum ko aljan,me rai ko maras rai ameen ya hayyu
ya qayyumu).

Bugu daya tak aka daga kiran da hajjan tayi,muryarsa ta fito tarwai
yana gaidata. Cikin kulawa ta amsa masa sannan tace

"Kaga yahaya.......naje unguwa ne sai na sallami driver da xummar zan tuqo kaina na
dawo gida......."

"Me yasa hajja?,ta yaya zakiyi tuqi da kanki?" Ya fada

Please Login or Register in order to submit comment