You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tayita qoqarin tuna abinda ya faru bayan zubewarta amma ta kasa tuna
komi......abinda kawai take iya tunawa sanda ya shigo dakin da fadawa jikinsa da
tayi tana neman tallafi cikin kubcewar numfashi.

Kiran farko dana biyu duka akan kunnenta akayi shi,bayan sauran
masallatai sun tada tasu sallar sai itama ta miqe ta bada nata faralin.

Ci gaba tayi da zama still a wajen......tana tsammanin wai ko zataji
bacci amma babu shi ba alamarsa. Wani firgici takeji har tsakiyar zuciyarta wanda
bada taimakon hailala da takeyi zuwa yazu batajin zata iya zaman dakin ma gaba
daya.

Sanda gari yayi haske ta kalli ma'u dake gefe a zaune,qaunar ma'un da
darajarta yana qaruwa cikin idanunta. Sam tana lura da ita batayi bacci ma itama

"Kije ki huta ma'u.....baki samu bacci ba kema" Sabreen ta fada muryarta a karye da
wani irin sanyi da bata taba yi ba. Dan murmushi ta saka tana gyara zamanta

"Ba wani damuwa.....bai kamata ai na barki ke kadai ba......saidai ko idan kina
buqatar cin wani abu?" Kai sabreen ta girgiza mata

"Bana buqatar komai.....kije kidan rage baccin ma'u ki kintsa......kya dawo daga
baya,bana buqatar komai". Kai ta jinjina sannan ta miqe tana mata sallama ta fice.

Qarasa shafa addu'o'inta tayi ta miqe tana son jin qara watsa wani
ruwan dumin ko jikinta zai qara yi mata dadi. Wannan karon saita taka zuwa bakin
qofa ta murza lock dake jikin qofar kamar me tsoron maimaituwar abinda ya faru
daren jiya ya sake faruwa,sannan ta juya a hankali tana wucewa toilet din.

Tare dasu Jordan da farouq ya kawo suka wuce sallar asuba,wadda duk da
qarancin baccinsa hakan bai hanashi samun sallar asuba ba. Tun daga fitarsu zuwa
dawowarsu su kansu sun fahimci sam yau ba'a mode dinsa yake ba. Idan kai baqo ne a
rayuwarsa ba lallai ka fahimci lokutan walwalarsa dana bacin ransa ba......kawai
zai zame maka kaman daya ne saboda rashin fara'a da bai da ita......amma gasu da
suke tare dashi tsahon shekaru,suna iya fahimtar walwalarsa da akasinta dukka
qarqashin dabi'arsa me kamanceceniya da juna.

"Mu qarasa ciki jordan" Yace da jordan din bayan sun shigo ainihin farfajiyar
gidan. Ba musu ya takewa uban gidan nasa baya suna takawa zuwa dakin da ya bada
umarni a ajjiye masa su.

Duk da kusan dabi'ar gidan shuru ce,amma a yau tana jin gidan ya sake
zama shuru gaba daya. Hakan yake don tun daga gate din farko na gidan zakaji gidan
yayi wani mugun shurun da ko tarin wani babu. Zaka rantse da Allah mutuwa akayi
cikin gidan saboda yadda kowa ya sake shiga nutsuwarsa. A mugun kasalance da wani
irin rashin kuzari ta shirya cikin atamfa dinkin plain zani da riga,wanda babu wani
ado da akayi mata ko guda daya face qwarewa da gwanancewar dinki daga telan nasu.

Dare daya amma gaba daya ta fada,tayi wani rama da ta bayyana har a
qasusuwan wuyanta,fuskarta tayi fayau,inda ya fashe a jiya sai yanxu ya fito sosai
ta ganshi. Tsaga ce 'yar siririya bame yawa ba,fuskarta tayi wani fayau kaman wadda
tayi zazzabin dare. Koda ta kalli fuskarta gaba daya sai taji zuciyarta ta karye,ta
koma da baya a hankali tana sake tuna yadda mashkur ya fado mata daki.

Duk wanda wani bala'i ya sameshi kalleshi kawai......ashe fiye da haka
matan da ibtila'in fyade ya fadawa suke ji?. Raurau idanunta sukayi,can qasan ranta
sai ta samu kanta da godewa Allah da ya bata ikon tsame mata da yawa da suka
fuskanci ibtila'i irin wannan zuwa sauyin rayuwa daya kawo musu sassauci da
rangwame.

Qasa tayi da kanta,daidai lokacin da taji ana mata knocking. A nata
zaton ma'u ce......wannan ya sanyata kanta tsaye ta nufi qofar ta kuma bude tana
bada hanya,saidai a maimakon ma'u anni ta gani,gefanta kuma amna ce tsaye tana riqe
da purse din annin.

Wani irin nauyi da bata taba jin irinsa ba ya saukar mata,tayi qasa da
kanta tana basu hanya.

"Ai jikinma yayi kyau.....basai mun shigo har uwar daki ba,mu koma falo mu gaisa a
can" Anni ta fada cikin dattakon nata tana juyawa da nuna alamu na surukuta

"Da kun qaraso din dai anni" Sabreen ta fada adan kunyace da nufin tsaida annin

"A'ah qaraso nan din sabreen.....ki fito a hankali karki gaggawa" Anni ta fadi tana
qara yin gaba,amna da abun yaketa burgeta takeson tayi tsokana nata binsu da
dariya.

Dukka hannayensa ya zube a aljihun wandonsa yana qare musu kallo cikin
quntataccen qaramin store din ajiyar kayan aikin sola dana engine din gidan idan ya
samu matsala. Daga daren jiya zuwa yau idan ka kalli fuskokinsu sai kace basu
bane,kada ma mashkur daya kwana a daure yaji labari.

A duk sanda ya kalli mashkur din shi kadai yasan abinda
yakeji......har yanzu maganganunsa sunqi daina amsa kuwwa a kuwwa a
kunnensa.......har yanzu ya gaza daina tuna sunyi gamayya a daki guda qarqashin
abun shaye shaye guda.
Taku biyu yayi y is gaban qofar yana duban mashkur din

"Waye ya aikoka?,ko kaine ka aiko kanka da kanka makasarka?" Kai ya mirgina alamun
eh.....koda meye zai faru bayajin zai iya buda baki ya fallasa wannan
sirrin.......sirrin da idan har ya bari ya fita to tabbas shima ya gama jin dadin
rayuwarsa har gaba da abada koda yayi escape. Abu ne bisa sharadi da yarjejeniyar
da aka qullata bisa masaniya da kuma abinda zai faru a qarshe.

Sosai fu'ad ya zuba masa idanu yana karantarsa,yanayinsa ya tabbatar masa
bai shirya fadin gaskiya ba duk da baqar wahalar da ta nuna kanta a tattare dashi.
Bayajin zai iya wahalar da kansa tsaiwa yana batawa kansa lokacin tambayarsu,yana
da wadanda zasu tafi masa dasu har su gane kuskuren da suka tafka na shiga gonar da
ba nasu ba. Hannu kawai ya daga ya yiwa Jordan alama,Jordan din ya jinjina kai
sannan ya juya yana fita hanyar waje da sassarfa irin ta majiyin qarfi,cikin qasa
da minti biyar sai gashi sun shigo da wani.

Kakkauran mutum ne,me qiba da madaidaicin tsaho,yana da baqar fata
data haska sosai cikin color din uniform din 'yan sandan dake jikinsa. Maqale da
jikin rigar rubutun sunansa ne S.nuhu,wanda iya rank dinsa zai nuna maka cewa shine
commissioner of police na jahar gaba daya.

Salute na juna sukayi shi da fu'ad din,sannan yace

"Yallabai yace idan da damuwa ayi gaba dasu" Kai fu'ad ya jinjina yana baro jikin
qofar yana takowa a hankali gami da dubansa

"A wuce dasu a ajjiyemin su,har sai zuwa sanda na buqacesu". Kai s nuhu ya gyada
cikin girmamawa,daga yanda fu'ad yayi maganar ya gama fahimtar komai. Suna
girmamashi kaman yadda yake girmamasu,tun daga can copral har zuwa matakin qarshe
na samansu,wannan ya sanya basuyi qasa a gwiwa ba suka bashi kyautar jami'an tsaro
cikin mutanensu,mutum ne me qoqarin kiyayewa da mutunta doka. Yana da qarfin mulki
dana dukiyar da zai iya komai da yaga dama musamman a yanayi irin na qasarnan da
zaka iya komai ba komai bane,amma baya yin hakan,komai din yana qoqarin ganin ya
azashi akan mizanin daya dace.

"Don girman Allah ka taimakeni.....kayimin sutura.....yallabai ni na fadi
gaskiya,na fadi gaskiyata......iyakar gaskiyata kenan". Hanzari ya fada yana hade
Hannayensa waje guda yana kallon fu'ad da tuni ya soma wucewa xuwa cikin gida.

Ko muryarsu bayason ji bare yakai ga kallon fuskokinsu,don haka baiko
waiwayo ba bare ya saurareshi. CP s.nuhu ya daka masa tsawa

"Miqe muje......ku daukeshi ku samin a mota,mutanen banza kawai......banda ma me
jadda din kuka samu waye kamanshi da zaku keta masa haddin gida ku shiga ku wayi
gari haka da sauran lafiyarku?,ba a nan zamu gane gaskiyar taka ba......muje don
ubanka" Cp ya fada shi kansa abun yana masa takaici.

Sam baisan da zuwan annin gidan da safen ba,don haka kanshi tsaye ya
shiga falon hankalinsa yana ga samanshi. So yake ya isa ya kulle kansa don baya
buqatar ganin kowa kaman yadda bai buqatar hayaniya ko dogon magana sam sam. Saidai
yana sanya qafarsa a falon yaji muryar annin sanda take fadin.

"Allah ya qara lafiya......yasa kaffara,saiki dinga kula da jikinki da kyau,Allah
ya inganta". Murna ta kama amna,duk yadda taso cinye maganar amma sai data fito

" Anni......wai.....wai hamma shima ya kusa zama daddy?".

"Ungo nan" Anni ta fada tana watsa mata yatsunta biyar,saita saka hannu ta qunshe
bakinta tana dariya.

Shikam daga shi har sabreen dake zaune daga gefe maganar tazo musu a
wani irin ba zata.

"Allah ya inganta?....zama daddy?,wata qaryar ta gilla musu kenan?" Ya fada qasan
ranshi yana yamutsa fuska gami da watsa mata wani irin kallo duk kuwa da cewa yana
nesa kadan dasu,sannan dukkansu ba wanda yasan ma ya shigo parlor din. Kai ya
jinjina wani abu yana tsaye masa a wuya

"To yaushe tayi cikin?" Yaji tambayar ta taso daga ransa,take yaji kansa ya qara
masa wani nauyi saboda wani tunani da yazo ransa.

Dukka juriyarsa da yakejin kamar tana sulalewa ya tattaro yana sake
maimaita sallamarsa,suka daga kai dukansu suna amsawa banda sabreen da tayi qasa da
nata idanun tana jin sam sam bata sha'awar dubanshi.

Gefan anni ya zauna kaman yadda ya saba a gida,duk sanda zai iso gabanta
gefan ta nan ne wurin zamanshi. Tuni amna ta kama kanta tana gaidashi cikin
tsoro,don tasan zai wahala baiji abinda ta fada ba.

"Ina kwana?" Sabreen ta samu kanta da fadi duk da bata dubeshi ba,haka kawai
takejin wani irin nauyin anni.

"Lafiya qalau.....ya jikin?" Ya furta a dake yana dan duban fuskarta kadan wajen
daya lura a jiya ya fashe,baiga komai ba don ta rufe wajen da dan kwali,sai ya
dauke dubansa daga kanta zuciyarsa tana masa zafi.

Ba abinda ya hanga saman fuskartata sai guntuwar wiwin daya gani jiya a
bakinta,zuciyarsa ta sake matsewa,baya jin zai samu wani nutsuwa a zuciyarsa muddin
bai samu cikakken bayani abinda yake faruwa ba ko kuma ya farun.

Hankalinsa ya maida kan annin ya soma gaidata cikin nutsuwa da
girmamawa. Yaji dadin yadda farouq bai daga mata hankali ba ya gaya mata abinda ya
faru a gidan ba jiya da daddare,yadai gaya mata kawai sabreen dinne bata da lafiya

"Allah ya qara lafiya.....sai ka kula da ita sosai.....inajin idan zai yiwu ma
nabar amna a gidan,don a yanayin mace irin haka zaman kadaici qara miki ciwo kawai
yakeyi". Dan satan kallon anni yayi,ya fuskanci tunda ta zauna a wajen kawai kallon
me ciki take yiwa sabreen din,inda anni tasan cakwakiyar da yake ciki zama zatayi
tayita masa kuka.

Kwata kwata a birkice yake kan lamarin,kusan komai nema yake ya dagule
masa,yana jin kamar kwanyarsa ta daina aiki yadda ya kamata. Ya lumshe idanunsa
yana jin ciwon yadda mahaifiyarsa ta xama silar qulluwar alaqa tsakaninsa da
yarinyar da kullum munanan boyayyun halayenta sake bayyana sukeyi.

"Ashsha......da kinyi zamanki ai,ina ke ina hidima damu ke da ba cikakkiyar lafiya
gareki ba?" Anni ta fadi sanda Sabreen din ta fito daga kitchen ta ajiye mata tray
dake dauke da spicy black tea soyayyen qwai da kuma farfesun kan rago wanda ta yi
tun shekaran jiya waccan amma ta kasa ci,kasancewar ita din cin abinci ba damunta
yayi ba. Zataci din amma gutsul gutsul kamar na dan qaramin yaro,shi yasa ko yaya
ita ko ma'u suka girka abu sai yayi musu yawa.

Sallamar da akayi daga bakin qofa ya maida hankalinsu can.

"Sannunku dai.....gafaranku" Zuwairan ke fadi tana rarraba idanu. Zuciyarta cike
fal da fargaban kada shigowarta ya zama silar barinta aiki.....amma kuma tana jin
relief na wani fannin idan ta tuna tana da assurance na bazaice komai ba muddin
annin tazo gaidawa.

Zubewa ta gaidashi,amsawa daya yayi mata,ganin hakan sai ta tattara
hankalinta ta maida kan annin tana zuba gaisuwa.

"Ya mukaji da wannan abu?" Zuwairan ta fada duk da a tsorace take.

"Ke!" Fuad ya fadi da kakkaurar muryarsan nan dake saurin isar da saqo gun wanda
aka kira saboda zurfin muryar da wani irin kaifi


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 62



62



"Eh......na'am" Ta fadi adan zabure

"Kin taba samun matsalan qwaqwalwa?" Ya tambayeta kai tsaye da wani kallo da yaso
rikita duk lissafinta. Kai ta fara girgizawa

"Ranka ya dade.....aah"

"Good" Ya jinjina kai

"Bacen a gun" Ya fada a taqaice wanda yana kaiwa qarshe tana miqewa da hanzari gami
da cewa

"Tuba nake.....tuba nake". Daga shi anni har amna binta sukayi da kallo,a mamakance
anni ta maido dubanta kansa bayan ta fice

"Allah me mutane.....ina ka samo wannan Muhammadu?"

"Maamah ce....." Ya fadi a taqaice yana jin wani abu game da matar tare da bin
hanyar da ta wuce da kallo kaman tana wajen har a lokacin. Tun bai qarasa ba ta
fahimci inda zancan ya dosa,kai kawai ta gyada tana fadin

"Allah ya rufa asiri......mu zamu wuce.....diyata" Anni ta fadi tana murmushi. Qasa
sabreen ta sakeyi da kanta tana dan qaramin murmushi. Karon farko idanunsa suka
soma kaiwa kanta,karon farko kuma yaga wani abu me.kama da murmushi akan
fuskarta......hakanan lokaci na farko da yaga wani alamu na wata aba wai ita KUNYA
a tare da ita. Tsaki yaja qasan ranshi,bayajin wannan abun da takeyi har qasan
ranta take yinsa,yadda ta wani sunkuyar da kanta,abinda bai taba gani ba a tare da
ita sai yau.

"Allah ya qara sauqi kinji.....ki kula da jikinki da kyau" Anni ta fadi tana jin
yaqinin kamar abinda dai take hasashen ne yake tare da sabreen. Har cikin zuciyarta
takejin yarinyar,tana kuma jin kamar ta taba ganinta a wani wajen kafin yanxu,amma
kuma ta gaza tunawa.

"Ameen anni.....na gode" Siririyar muryarta da yau kadai tayi wani irin laushi ta
fito tana furta hakan har yanzu kanta a qasa.

Dukkaninsu suka takawa anni xuwa inda lafiyayyar BMW dinta take
jiranta da masu tsaro lafiyarta mutum biyu

"Zamu tafi tare da amna din.....amma anjima da dare in sha Allah zata dawo,sai
kinfi jin dadin xaman......nasan halin Muhammadu....indai kin ganshi gida zaune to
saidai annual leave dinshi yazo ko kuma baida lafiya da gasken gaske". Haka kawai
ta samu kanta da kallonshi ta gefen idonta. Duk da ba dogon zama sukayi ba,gajeran
zama ne maras dadi da ma'ana,zaman da baida wani alqibla ko kadan,amma ta karanci
dabi'u masu yawa tattare dashi. Aiki kaman baisan ciwon kansa ba,kamar kuma yafi
kowa sanin muhimmancin lokaci,bata taba ganinsa ba system ko takardu ba.....sannan
zaman kadaici baya damunsa sam sam.

Suna a tsaye motar ta soma motsawa tana fita ta tafkeken gate din
gidan. Idanunta akan bayan motar,tana jin kaman ta hanasu tafiya ita da amna
din,dan wanzuwarsu na qananun mintuna kadai sai taji kaman an rage mata wani nauyi
da takeji a zuciyarta. Lallai maraici babbar masifa ce,ciwo ne wanda bashi da
magani har xuwa randa naka ajalin xai ruskeka,wanda ya rasa uwa shi daya yasan irin
asarar daya tafka da ba zata fadu ba.

Sai da motar ta gama ficewa tas sannan ta tuna a inda take a tsaye,da
kuma wajen waye take?. Ba tare data juya ta kalli inda yake a tsayen ba ta juya a
hankali tana komawa ciki.

Da kallo ya bita ranshi yana sake masa susa......idanunsa suka sauka
kan hips dinta da suka bayyana sosai saboda mayafin dake saman kanta bame girma
bane,take zuciyarsa ta wullo masa hoton hijabinta na jiya da yasha cukuikuiya,wani
zazzafan abu me tauri ya taso masa da ya sanya ya gaza riqe kansa,sai kawai yabi
bayanta yana jin ya zama dole lallai lallai yasan kome.

Tana dab da isa qofar da zata sadata da parlor dinsu na farko ya
cimmata. Bata zaceshi ba ta tsinceshi a gabanta. Kallon kallo suka yiwa
junansu,wani irin kallo na tsakiyar idanu,tsakanin shi da ita kowa zuciyarsa na
dauke da wani irin nauyi da baisan yadda zai rageshi ba.

Ta dauka zata iya jurewa ci gaba da kallon tsakiyar idanun nasa amma
sai taji ta sare nan da nan,ta janyesu bugun zuciyarta na daduwa wanda batasan meye
sila ba. Qasa tayi da kanta,so samu ta rabeshi ta wuce saboda fushi take gani cikin
idanunsa,ita kuma yanzu qirjinta bazai iya daukan fada masifa ko tashin hankali ba
hakanan. Kai kawo kawai adams apple dinsa keyi alamun akwai abinda yaketa qoqarin
hadiyewa,jiyan ce kawai ke dawo masa,yana tuna sanda ya dagata towel din jikinta
daya xame warwas a qasa,daga ita sai hijabi. Sai daya tabbatar yayi babban aikin
rage fushinsa da abinda yakeji sannan ya soma magana,cikin bacin rai amma kuma
yanata kokawar kalmasa harshensa,don bayani yake buqatar ji,duk da cewa ta kowacce
fuska.....duk kuma inda ya juya.....kowacce hujja idan ya daga,ya tattaro ta nan
data can ba abinda take sake nuna masa sai ainihin WACECE ITA.

"Wancan lokacin.......na taba ganinsa cikin hotel a abuja yana cigiyar karuwarshi
da suka kama daki,ta kwashe masa kudade masu yawa kwatankwacin yadda ya faru da
kamfanin JADDA DIAMOND CHORES RESOURCES,sanda naga fuskan wayar ba kowa bace a ciki
sai KE!......Wanene shi?,ya akayi ya shigomin cikin gidana?,cikin dakin da aka gina
da tsaftatacciyar dukiya ta halak?".
Wani irin duka tambayar tasa tayi mata,wadda tazo mata hade da labarin
da batasan ya faru ba......eh ta taba binsa abuja.....kuma aikin mashkur kusan
shine aiki na qarshe da tayi har yau kuma bata sake sha'awar maimaita wani abu
makamancinsa ba.......amma yaushe ya fiddo hotonta ya nunata a matsayin karuwa yana
cigiyarta?. KARUWA kalma mafi muni da tafi tsana taji ta gilma a
kunnuwanta......duk yadda takai tsakaninka da ita muddin xaka kira wannan sunan a
gaban fuskarta......to takan iya manta ya kuke da ita?.

"Am asking you......" Ya fada yana jin ya soma hasala ganin shurun da tayi kamar ba
da ita yake magana ba.

"Ban sani ba......." Ta bashi amsa muryarta tana so ta fara rawa. Me zata gaya masa
wanda zai sanya ya fahimceta?.

"Baki sani ba kaman yaya?,ya shigo har dakin ba tare an fasa kowanne gini na gidan
nan ba......ya shigo dakinki ba tare da kinyi yunqurin kiran koda security daya na
gidan nan ba......ya shigo dakinki daidai lokacin kwanciyar baccinki?,a sanda kike
daure da towel kadai da hijabi?" Ya qarasa maganar yana qarasawa dab da ita,yana
kuma kaiwa qarshe a tsawace har sai data lumshe idanunta ta kuma gaza budesu.

Tsawa......tsawa,bata son tsawa,bata qaunarta,tsawar ma daga wajen d'a
namiji.....wanda tuni ta karanci sun jima da raina ajawalin mata. Wani abu data
jima da shawa kanta alwashi,raini.....wulaqanci.....izgili da toxarci na da
namiji,ita ko 'yan uwanta ba wanda zata lamunta ya daukesu.

"Ban sani ba nima" Ta sake maimaita masa don da gasken batasan yadda akayi mashkur
ya shigo ba.

"Harda wayar daya baki kenan itama ita ta kawo kanta?!.....nace ita ta kawo
kanta?!!!" Ya fadi da qarfi kaman yana shirin fasa mata kunnuwa.

"Stop it!.....wanne kakeso na amsa maka?,wacce tuhuma kakeso na baka amsarta?!"
Itama ta maida masa muryarta na rawa,oily eyes dinta suna qara walainiya cikin
hasken ranar daya fara dagawa.

"Ni kikewa shouting?" Ya tambayeta da tsananin mamaki,saidai kuma qarar wayarsa ta
janye magana ta gaba da yaso fadi. Bai fiya daga waya a cikin irin wannan yanayin
da yake cikin tsananin fushi ba......amma yana expecting kira me muhimmanci daga
gurin wani dan kasuwa mazaunin qasar ivory Coast,dole ya ciro wayar.

Shi da ita dukansu akan sunan FAREEDA KHALEED MUSTAPHA ya sauka,ita ta
fara janye idanunta tana jin wata wani fushinta yana ninkuwa.

Ya sanyata a gaba da tarin tambayoyinsa amma shi a daidai lokacin
karuwarshi ko yarinyarsa.....batasan da wanne suna zata kirata ba ita ke kiransa?.

Ta nashi bangaren banda muhimmancin da wayar ke dashi a wajensa tabbas
ba abinda zai hanashi tarwatsata ita kanta wayar a wajen bama fareeda kawai ba.

"Sorry sir" Yaji an fada da sauri,abinda yakai hankalinsu kenan wajen. Me sunan
malam ne,da sassarfa yake barin wajen saboda kunyar yadda ya samesu a tsaye dab da
juna,baisan kuma zai samesu a hakan ba da bai biyo ta wajen ba.

"Zo nan" Ya kirashi a nutse yana duban hannunsa dake dauke da newspaper daya saba
ajiye masa duk safiya daga kamfanin jaridu daban daban.

Sunkuyawa tayi ta zame ta gefansa tana takawa don barin wajen,haka
kawai taji bama zata iya zama ta fuskanceshi ba sam. Kwata kwata bata yarda dashi
ba Shima.....wacece faridan?,meye alaqarsu da koda yaushe layinsa cikin karbar
kiranta yake?. Yana jin wucewarta amma bai waiwaya ba don hankalinsa yana kan me
sunan malam.

"Good morning sir" Ya sake gaidashi cikin girmamawa yana rusunawa ba tare daya miqa
masa newspaper din ba kaman yadda ya saba,duk da yawancin lokuta ma yana samunsu ne
a daura da dining suna jiran fitowarsa,idan ga kammala dubawa kuma zai kwashesu sai
kuma fitowar gobe.

"Morning.....how you doing?"

"Fine sir" Still ya kuma amsa masa amma ba alamun zai miqa masa su. Abun yadan bawa
fuad mamaki,yana shirin miqa masa hannunsa don ya bashi kira ya kuma shigo masa.

Kai tsaye aka gaya masa farouq ne don haka ya daga ba wani bata lokaci

"Good morning dude" Farouq ya furta kaman yadda ya saba masa,saidai kuma daga can
qasan muryarsa kaman yana iya tsinto wani abun

"Morning......mun tashi lafiya?"

"Fine.....ya jikin naka?,ka fita ne ko ka sauko daga stairs?" Duka farouq din ya
cure tambayoyin ya masa,abinda yaja hankalin fu'ad kenan.

"Ban fita ba......na sauko qasa na rako anni yanxun xan koma ciki".

"Good.....but do me a favor mana" Ya fada yana fatan idanunsa basuga abinda ya gani
ba.

"Ehnnnnn" Fu'ad ya fada yana jin zaquwa na jin abinda zai fito a bakinsa.

"Kayi skipping duba newspapers na yau mana......instead of that ka bani aron time
din muyi magana" Yadda farouq yayi maganan kawai ya sanyashi yasha jinin
jikinsa,sai kawai ya miqawa me sunan malam hannunsa yana masa nuni da newspapers
din da yake rqe dasu yana kafeshi da idanun nan nasa da kwarjini ke cike dasu
kullum ba tare da ya sauke wayar a kunnensa ba.

"Kowanne lokaci na yini na zan iya baka farouq,not the only news time" Ya bashi
amsa sanda me sunan malam ya miqo masa newspapers din da hannu biyu cikin mutuwar
jiki,ya kuma janye daga wajen da sassarfa don bazai iya tsaiwa yana dubansa a sanda
yake kallon labarin dake buge a jaridar ba.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_Zafafabiyar_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 63


63
"Wannan abun kawai nake buqata please" Farouq ya maimaita sanda ya shiga
motarsa dake farfajiyar gidan. So yake yaja maganan da tsaho sannan ya cimmasa
kafin ya duba abinda ke faruwan saidai sanda yake bashi amsa na qarshe yana bashi
amsar ne sanda idanunsa suka sauka akan tittle na labarin da yaci shafin farko gaba
dayansa na jaridun guda biyu.

*_TSINTAR DAMI A KALA_*

_BABBAR JARABAWA......SHIN KUSAN WACECE ASALIN MATAR MATASHIN MILLIONAIRE DINNAN
MAMALLAKIN KAMFANINNIKAN DAKE SARRAFA GWALA GWALAI?_

"Farouq.....you have my time,amma kafin sannan......" Maganar ta yanke masa sanda
makeken hotonta ya biyo bayan title din ita da mashkur.

Hoto ne da aka daukeshi gaban wani hotel da sunan kawai ya iya kalla
ba tare daya tantance wanne bane.......sanda ya bude mata murfin motar ita kuma
tana qoqarin fitowa a motar yana riqe da handbag dinta.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Ya fada yana jin dukka

Please Login or Register in order to submit comment