You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana kashe masa ido. Harara ya
gasa masa

"Gidan jarida na bude daga jiya zuwa yau baka sani ba?" Dariya sosai farouq ya
tuntsire da ita.

"Idanma hakanne Allah an maka uzuri.....da gaske ba wani abu sabo?,baka kawo
kusanci tsakaninku ba?"

"Kaga don Allah malam dakata" Ya fada da husky voice dinsa

"Na gama gane inda ka dosa gaba daya fa.....na gaya maka ne abinda yasa na kawo ta
cikin gidan nan kenan ko kuwa?,ko bunsuru ne ka aje?...." Dariya sosai ta qwacewa
farouq fiye da dazu,yayi qasa qasa da muryarsa yana dubansa

"Maganar gaskiya ban yarda dakai ba.....i know you kaima ka san da wannan......a
hadaka da halal dinka gidan da ba kowa saikai da ita.....kuma kacemin bakayi
filling distance din dake tsakaninku ba.....anya wannan kyan da naga kanayi
zakacemin duka a banza yake?". Rasa me zaiyi masa ya huce yayi,sai kawai hannunsa
ya fada kan remote din dake gefansa,ya shammaceshi ya wurga masa ya sauka a
kafadarsa. Duk duniya farouq kadai ke masa irin haka,yana sake hararasa yana zura
hannunsa a aljihu ya fiddo wayaraa

Idanunta kawai ta ware daga kashingiden da take sanda taji ana knocking
na qofar. Kashingidar da ta yita ne kawai tana tunanin abubuwa masu yawa tare da
qoqarin cudanya abubuwan dake mata kai kawo cikin kwanya. Tunani kala kala ta dinga
yi sanda taji ana knocking din.....shine ya biyota ya sake cin zarafinta ko
kuwa?.....wasu ne suka sake zuwa gidan ko ko yaya?. Daga qarshe da taga bata da
zabi dole ta motsa labbanta tana fadin

"Waye?"

"Nice adda....na shigo please?" Amna tayi tambayar cikin zaquwa. Kiran adda din da
akayi sai ya sosa mata wani miki,mikin kewar 'yan uwanta wadanda su kadai ke
kiranta da wannan sunan. Ambatar sunan ya sakata miqewa ta zauna sosai tana zuro da
qafafunta qasa.

"Shigo" Ta amsa kawai kai tsaye ba tare da tasan waye ba.

"Assalamu alaikummm" Amna ta furta duka tare da shigowarta cikin dakin cikin
murmushi tana riqe da handle din qofar idanunta akan fuskar sabreen yayin da
fuskarta ke qunshe da wadataccen murmushi

"Wa'alaikumussalam" Sabreen ta amsa mata tana mata duban rashin sani.

"Ma sha Allah" Amna ta furta a sarari tana kasa dauke idanunta daga kan
sabreen,murmushin saman fuskarta kuma ya kasa bacewa. Dama ta sani......ta sani
tabbas hammanta ya iya zabe......tasan hammanta lallai zai zabo matar da ba irin ta
kowa ba,amma bata taba tsammanin iya zabinsa yakai har kaman haka ba.

"I know.....kece adda sabreen dinmu ko?" Tayi tambayar da murmushi sosai tana
nunata da yatsa idanunta a kanta. Dan shuru sabreen tayi tana kallonta ba tare data
iya amsa mata ba,kwanyarta na mata lissafin wacece wannan din?. Tana da surutu
sosai da alama,amma kuma yanayinta kadai ya gaya mata me kirki ce.

"Sunana amna hamza kibiya.....nice autarsu hamma fu'ad". Tayi mata bayani a taqaice
saboda ganin yadda take mata kallon rashin sani. Ta fahimci sarai
bayaninta......qanwarsa takeson cewa,kamar ta basar sai kuma wata zuciyar ta
tambayeta
"Meye laifinta ita?" Don bataga wani hali na daban tattare da ita ba duk da a
yanzun ta fara ganinta,amma bahaushe yace alamar qarfi tana game qiba.

Har amnan ta sare,sai kuma taga ta saki qaramin murmushi da yayi
barazanar dauke hankalin amnan saboda yadda ya fidda kyawun innocent face dinta

"Qaraso mana" Ta furta tana miqewa tsaye tare da komawa saman sofa bed". Dukka
energy dinta ya dawo,ta tura qofar a nutse tana ci gaba da murmushi ta tako ciki
tana samun wajen zama saman wata sofa din ta daban


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 19


19


"Am sorry aunty.....hala nayi disturbing naki kina hutawa" Ta sake fadi tana
murmushi. Maida mata martanin murmushin tayi,wanda har sai da amnan ta furta

"Ya salam,wanne irin kyau ne haka?". Kai ta girgiza

"Ko kadan....."

"Barka da rana,kin yini lafiya?,ya baqunta?,anni na miki ban gajiya,munzo mu wuce
dake wajen walima......kowa yanaso ya ganki don jiya baku samu shigowa ba saboda
dare ko?" Ta jero dukka abinda ke tafe da ita da wanda ke ranta kamar ba itace anni
ta jawa kunne kada tazo ta cikata da surutu ba. A iya bayananta kawai ta gane
wacece ita.....diyar matar nan da cikin kalamanta kawai zaka fahimci nutsuwa gami
da tarin ilimi a ciki,wannan ya sanya sabreen sake sakar mata jiki kadan,saidai ta
wani bangaren tana tunanin ta inda zata zamewa zuwa walimar,don sam bata shirya
sake shiga kowanne taro ba. To na meye ma zata yita nuna fuskarta wa danginsu,bayan
bawai tazo bane don ta zauna?.

"Amma walimar......" Sai maganar tata ta katse saboda daga mata hannu da amna tayi
sakamakon shigowar kira,tayi blushing kadan sannan ta kalli sabreen

"Anni fa ba zama anyi suruka.....ungo nasan kirannan naki ne". Batason katsewa amna
doki da farincikin da take ciki,don haka ta miqa hannu dole ta karbi wayar

"Idan ba zaki samu daman zuwa ba diyata kada kiji kin takura.....kiyi zamanki,dama
taro ne na sanya albarka,sai a sallami mutanen". Ji tayi ba zata iya mata haka
ba,ba zata iya watsa mata qasa a ido ba,don haka tace a hankali
"Muna hanya in sha Allah"

"To Allah yayi muku albarka,Allah ya kawoku lafiya"

"Ameen ameen" Ta amsa tana miqawa amna wayar idanunta nabin amnan da kallo. Ta
fahimci wani farinciki takeji sosai,duk da batasan na meye ba,ganin amna din sai ya
tuna mata da huda dinta,duk da ta girmi huda,saidai ita kuma ta girmi amna qila sa
shekara uku ma ko hudu.

Dole ta miqe ta soma qoqarin rage yafen jikinta da dankwalin kanta don
shiga wanka,ta lullube jikinta da qaton towel ta wuce tabar amna tana bata labarin
sabreen din,abinda yaso badda bacin rai da takurar zuciyar da take ciki ta shige
bayi da boyayyen murmushi a qasan fuskarta.

Komai na toilet din na kayan wankan ba irin nata bane,amna tunda ta
karanta sunan products din da brand dinsu tasan harka ce kawai ta girma akayi. Daga
yanayin sulbi da qamshin shower gel din kadai ta sake sallamawa,wannan ya dauketa
minti kusan ashirin sannan ta gama. Towel biyu kawai ta shigo dashi,ta daura
dayan,dayan kuwa dole ta nade kanta dashi saboda sumarta data jiqa da ruwa,ba wanda
zata yafa don suturta jikinta,don haka ta sako shower slipper din zuwa bakin qofar
toilet din ta cireshi saman water proof doormats din dake sashe na biyu na toilet
din ta murda handle din ta bude qofar.

Daidai lokacin daya soma duba agogo ganin sun sakashi dabi'ar daba tasa
ba.....dabi'ar daya tsana ya kuma ja mata kunne a dazu da kada ta soma aikatata
kwata kwata. Tsaki yaja ya fara lalubar number wayar amna,saidai ya kirata kusan
sau uku bata daga ba,wannan ya sakashi miqewa a fusace yayi ciki yana cewa farouq

"Ina zuwa".

Takawa kawai yakeyi cikin hallway din ba tare da yasan wanne ne
dakinta a ciki ba?. Haka ya dinga gota bedrooms din a hankali,sai daya isa na
qarshe sannan yadan tsaya cak yana kasa kunne duk yasan bazaiji motsin komai ba
saboda yanayin door din,a jikinsa kawai yaji da mutum a nan,sai ya juya yana
fuskantar qofar ya murdata da dan zafin nama.

Opposite suke tsakanin qofar toilet din dana shigowa dakin,wannan ya
sanya kai tsaye kowanne idanunsa ya fada kan dan uwansa sanda qofofin suka bude
lokaci guda. Budewar da taja hankalin amna wadda take zaune tana jiran fitowar
sabreen.

Sarqewa idanunsu sukayi lokaci guda......fuskarta tayi fresh
sosai,glowing din nan da fatarta ta qara samu saboda gyaran data samu na musamman
ya sake bayyana. Ruwan da tayi wankan dashi ya sabbaba tarwatsewar qwayoyin ruwan
saman fuskarta,sai suma zame mata tamkar wani ado,musamman sumar gaban kanta data
kwanta sosai ta kuma fito ta qasan towel din daya kimawa kanta don ta samu ya
tsotse danshin da yake jiki. Ta sassannin dogon wuyanta duka wasu daga cikin sumar
sun kwanta,sai suka zamewa wuyan nata kamar wani ado musamman kafadunya dake a
tsaye da wani irin structure me daukan hankali da kuma tudu da zaunawar dukiyar
fulaninta sosai a qirjin.

Duka cikin qasa da second goma idanunshi suka kai wadannan. Wanda
baikai mintunan da hankali da zuciyarka zasuyi zaton duka wannan karatun za'a iya
yinsa a wadannan taqaitattun mintunan ba. Haduwar idanunsu na farko yayi mata ba
zata,don bata taba kawo bayyanarsa cikin dakin ba,don haka ta maida qofar da wani
irin sauri ta koma baya ta tsaya zuciyarta na wani irin bugawa.

Idanunsa da yaji sunyi wani irin laushi ya janye daga bakin qofar
yana tabe baki
"Kamar gaske" Ya furta qasan zuciyarsa,zuciyar tasa tana ayyana masa Allah ne kadai
yasan adadin mazan da suka ganta a hakan,tunanin daya sanya wani abu me ciwo ya
tsaye masa a wuya. Wai wanne ma tsautsayin ya kaishi ajiye kayan da suke tamkar na
kasuwa cikin gidansa?,zai iya killaceshi da gaske ya canza masa rayuwar da ta zame
masa jini da tsoka?.

"Ba damuta bane......damuwata na koya mata lesson ko saboda gaba......tasan ba
kowanne kalar mutum kake tabawa ka kwana lafiya ba".

Duban daya maida kan amna sai yaga itama shi take kalla.......daure
fuska yayi tamau saboda ya karanci abinda ke fuskarta harda wani qunshe dariya

"Karku kuskura ku wuce minti shida.....if not...." Sai ya nunata da yatsa kawai ba
tare da yace komai ba ya juya ya fice yana tura musu qofar.

"Adda......wallahi hamma ya tsani jira.....nasan kema kin sani,hurry up adda anni
ma jira take" Muryar amna data sanar da ita ya fita. Wani wawiyar ajiyar zuciya ta
saki,a hankali ta saki qofar data qanqame,sannan tabi hannuwanta da suke rawa da
kallo.

Da gaske ta tsorata,don tunda tazo duniya ba wani muharraminta daya taba
ganinta a haka,wannan shine karon farko. Qoqari tayi ta hade hannayenta waje daya
tana matsasu da kyau,sannan ta bude qofar sosai tana fitowa.

Miqewa taga amna tanayi

"Bari na baki guri adda ki shirya a nutse....."

"Yi zamanki.....zan shiga dressing room na shirya" Tace da amna din,don idan ta
fita ta barta fitowarta zatayi mata wahala.....infact ma zata iya canza shawarar
zuwan.

Tsaf ta shirya cikin wata doguwar riga ta atamfa bayan ta gama
bulayin neman kayanta na gida,saidai ko ire irensu bata gani ba,sun lume sun narke
cikin uban suturar dake danqare da closet dinta. Chantilly veil ta yafa daya dace
sosai da atamfar jikin nata.

Ta fito da wani irin kyau da kai tsaye bahaushe ke cewa qyallin goshin
amarci.....saidai itakam ba days,tsabar gyaran jikin da tasha ne da kuma yadda ado
ya zame mata jiki.

"Tubarkalla ma sha Allah......tabarakarrahman......kiyi haquri adda inata
tankaki.....i can't control my words ne wallahi". Murmushi kadan ta yiwa amna
din,zuwa yanzu sai takejin kamar ta saba da halinta ne ma,tana da saurin sabo da
shiga jikin wanda take so

"Na gode" Ta fadi tana sanyawa qafafunta wasu high hill wanda kaman an yisu ne dama
musamman saboda kayan jikinta. Kamar amna din ta mata magana amma sai ta bari kada
sabreen din taga kama ta fiya rawar kai,a haka suka jero suna fitowa zuwa parlor
din.

Yayi relaxing sosai cikin kujerar kamar wanda bacci ke shirin
dauka,saidai babu ko guda daya.....wata lafiyayyar kasala ce ta saukar masa tun
daga fitowarsa daga cikin dakin.

"Barka da fitowa sister" Maganar farouq kenan da taja hankalinsa,ya dauke idonsa
daga email din da yake dubawa wanda duka ya raba hankalinsa gida biyu ne,daya kan
ibtila'in faduwar darajar gold da diamond da suka wayi gari dashi......daya akan
saqonninsa wanda kusan duka maganar dai daya ce,shirye shiryen bude company da yake
tunanin jibi zai wuce abuja saboda baqinsa da yake kyautata zaton zasu fara sauka.

Farat daya ta gane muryarsa,kaman amna shima sai take kirkinsa ya
lullubeta,bawai murmushi tayi ba,amna ta sassauta fuskarta sosai suna gaisawa.

"Ya kwanan baqunta?"

"Alhamdulillah" Ta amsa masa itama tana rufe handbag dinta data jefa wayarta a ciki

"Ma sha Allah....Allah ya bada zaman lafiya,ya baki ikon riqeshi" Yayi maganar yana
maida dubansa ga fu'ad. Ko wajensu baya kalla tun duban farko da yayi musu bayan
fitowarsu.

Batace komai ba sai amna da tayi murmushi me sauti

"Dude.....muje ko?" Farouq ya buqaci hakan

"Kuje kai da amna.....gamu nan fitowa" Ya bashi amsa bai ko daga kansa ba.

"Alright" Ya amsa masa yana daukan gorar ruwan da fu'ad din ya fito musu da ita
yayi gaba amna na biye dashi.

Shuru ya shude a falon na kusan mintuna biyu,bata ce kanzil ba kaman
yadda shima baice ta tafasa a sauke ba,kowa yana ji da tashi izzar da girman kan.

Ji tayi ta dauki iya adadin tsaiwar da zata iya.....ba zata dauki
wannan halin nashi sam sam ba,don haka ta juya ta fara motsawa da zummar barin
wajen

"Hey!....Waye ya baki izinin tafiya" Ya fada da boldness cikin muryarsa. Abun taji
ya mata wani iri.......wani baqon abu guda daya cikin rayuwarta. Batasan namiji
yayi mata tsawa ba saidai ma ya lallasheta......batasan namiji yayi mata umarni
ba.....a kullum ita ke basu umarni.......ba'a keeping dinta ta jira mutum saidai
shi yayi jiranta koda awanni nawa tayi nufin qararwa a wajen.


*DUNIYAT LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK)*
08187255862

𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀
_ZAFAFABIYAR_

ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2

β±§Ι„β‚²Ι„β‚₯β‚³

π™‹π˜Όπ™‚π™€ 20


20


Tana tsara komai a sanda takeso a kuma yadda taga dama......kuma a bita
a hakan.

"Kina tunanin hatta dressing naki zakici gaba da yinsa yadda kika saba?......idan
nace komai naki zai canza ina nufin komai din......ciki harda shigar da bata dace
ba.....bata kuma yi ba,ki kalli amna.....kin ganta da irin wannan useless
mayafin?". Iska sosai ta shaqa har cikin ranta tana jin wani zafi.....abinda yakeyi
matan wasu abubuwa ne da babu d'a namijin da ya taba yi mata shi sai shi. Sai taji
haqurinta ya gaza jurewa......don haka cikin muryarta me nuna bacin rai tace

"Kana zaton baiwa ce daka shiga kasuwa ka siyo?......meye alaqarka da dressing
dina?". Maganar tata ta sakashi gyara zamansa sosai. Yadan jijjiga kai

"Kin shirya wasan kenan kema?.....musu?,taurin kai.....abubuwa biyu da nafi tsana a
rayuwata" Yayi maganar yana kada yatsunsa guda biyu idanunshi akanta duk da baya
iya ganin fuskarta

"Bauta.....meye marabar dambe da fada?.....kina tunanin kudin da kika sacemin kimar
kudin aurenki sunkai yawan haka?......banajin kinkai tsada haka.....well,ba wannan
ba,ki shiga ki sauke wannan banzan mayafin ki saka sutura sosai a
jikinki......karki bari na maimaita maganata......i hate it". Cak maganan ta tsaye
mata a rai,wani irin bacin rai ya taso mata. Wannan ya sanya da sauri sauri ta fara
yin gaba,don tanaji muddin taci gaba da tsaiwa a wajen zai iya gano lagon
fushinta,abinda kuma taci alwashin ba zata taba bashi dama a kai ba.

Ci gaba da birkita closet din tayi bangaren veils cikin bacin rai,gaba
daya veils din taji basu yi mata ba,sai kawai tahau tube kayan,ta kwabesu tas ta
fara neman wasu daban.

Turkey dress hannunta ya fada kai,cikin shigar da tafi so kenan,sai
ta fara shirya kanta cikin turkey abaya din wadda cikin qanqanin lokaci ta rufe
mata jikinta ruf,ta kuma fiddo da kyakkyawar baby face dintannan.

Haka kawai sai taji tafijin dadin shigar,duk da dama tun asali ita din
bata iya shigar bayyanar da tsiraici ba.....kawai dai Chantilly veil yana cikin
veils din da tafi so,kuma ko a yanzun ba zata bari ya rabata dashi ba.

Motsin tahowarta ya sakashi daga kansa a nutse. Duba daya yayi mata ya
kauda kanshi,sai ya miqe yana ficewa tun kafin ta qaraso.

"Ya Allah......wai BB don Allah a ina hamma ya samo adda?" Amna data kasa daurewa
sanda ta hangi sabreen na takowa zuwa inda motoci ke jiransu ta fada. Iya takunta
kawai saika dauka rausaya ko kuma yanga takeyi ta cikin hill shoes din data sakawa
qafafunta masu igiya.

"BB.....wai dama hamma shima yana kallon 'yammata don Allah?". Boye dariyarsa
farouq yayi,don sarai yaga isowar fu'ad wajen amma bai nunawa amna ba

"Me yasa kika ce haka?"

"To ai......hamma fa kaman horror yake......ina noticing nasa duka shekarun
nan,Allah saiki wuce ta gabansa amma baisan wacece ke ba......to amma ya akayi
idanunsa suka kai kan addana me mugun kyau haka?"

"Yaushe kika zama gulmammiya amna?" Farouq daya kece da dariya ya fada yana satar
kallon fu'ad dake tsaye kawai ya kasa cewa komai. Dariyan itama takeyi

"Allah BB......ban taba ganin mutumin daya iya zaben mace ba irin hammana......da
gaske hamma ya hadu tako ina,komai nasa ya banbanta dana kowa" Ta fadi hankalinta
kwance batasan yana a wajen ba.

Zabura ta danyi da jin gyaran muryarsa,tsaf ta dinke bakinta tana raba
idanu

"A nan za'ayi walimar ne?" Ya fada yana jifan farouq da wani irin kallo na zaka
sani ne. Dariyarsa ya yiwa control yana fadin

"No.....aike muke jira,ko ka manta kaika koromu waje zakayi ganawar sirri da madam"

"Enough" Ya fada yana tura masa murfin motar kaman zai bugeshi cikin nuna alamun ka
soma wuce gona da iri. Hakan shi yayi masa,don haka yaja murfin ya rufe yana gaya
masa shi da amna zasu tafi a nan.

Baibi ta kansa ba ya nufi ainihin motarsa qirar Mercedes Benz G400d
baqa wul daketa daukan idanu wanda haka ke nuna sabuntarta da kuma kalar kulawar
da take samu.

Da sauri daya daga cikinsu ya bude masa,kai tsaye ya wuce ya zauna
sosai idanunsa na sauka a kanta. Ya tsani jira sosai,baisan me yasa take tafiya
kaman ba zata qaraso wajen ba,bayan ya tabbatar taga inda ya shiga.

_wataqila da wannan take sake samun damar yaudarar maza_ tunanin daya d'arsa masa a
rai kenan,wanda ya sake sanya mishi qyamarta ainun,har yakejin kamar ma bazai iya
hada numfashi da ita cikin mota guda ba.

Ba zata bari ba ba kuma zata sake tayi wani abu na zubewar kimarta da
mutuncinta gaban guards dinsa ba,wanda dukkaninsu haushinsu takeji. Bataga meye
dalilin da zai zube qatti irin wadannan suna kewaye dashi ba kamar tsohon barawo ko
wanda yaci kayan wani ba(a iya nata sanin na iya tsaron daya zama dole me harka
irin nashi ace ya samu),me yasa bazaiyi rayuwa normal irin ta mutane ba?,da wannan
kalar tasa rayuwar kenan itama yakeso ya tursasata ta zama haka?,tayi rayuwa irin
nashi?,bazai yiwu ba kuwa.

Daidaita zamanta tayi sannan aka maida murfin motar aka rufe mata,sai
motar ta dauki shuru sai sassanyan qamshinsa daya danne nata,har ya zamana duk wani
numfashi da zata shaqa tare da qamshin nasa yake zuwar mata hunhunta. Tsaki ta saki
a boye yadda bazai ji ba,ta maida kanta daya window din da take zaune daura dashi.
Batasan sun fara tafiya ba sai da taga motar ta fara sulalawa tana nufar makeken
gate din gidan suna gilma shukokin da aka qawata wajen dasu.

Basuyi nisa ba kira ya shigo masa,wanda shi ya zame masa abokin
tafiya. Duka maganganun cikin harshen turanci yake yinsu da wani irin accent dake
nuna zallar qwarewa gami da gogewa a yaren. Kusan fin rabin maganganun nasa ba wani
fahimtarsu takeyi ba,don zuciyarta tayi nisa da wani tunani na daban. Ta wani
bangaren kuma yadda yake lanqwasa harshensa ba kowanne word take ganewa ba a
matsayin karatunta na wadda ya dakata daga aji biyar biyu na babbar secondary wato
senior secondary school.

Sanda motarsu ke qoqarin cusa kai ta cikin babbar gate din dake da
wani irin girma da kuma jan hankali,a sannan ne ya katse wayar ba kuma don ya gama
ba. Ya kashe wayar gaba daya tana kallonsa ta gefen idanu,ya zurata cikin wani dan
abu daya matsa ya fito ya saka wayar ya koma ciki. Adan qaramin zamansu na mintuna
ta karanci abubuwa daban daban tattare dashi,kusan kaman komai nasa na dabanne kuma
daban yake,saita tabe baki sanda suka isa babban parking lot na alfarma da gidan ya
mallaka.

Qasa tayi da kanta tana jan mayafin data lullube kanta dashi sanda
take hangar wasu mata suna bullowa daga wata qofa da tafi kusa da parking lot
din,kafin takai gayin komai amna ta bayyana ta kama murfin tana budewa,abinda ya
bata daman jin maganganunsu. Muryar amna ta fara ji

"Inna uwaisha......ga addan namu.......ku fito mana da ita a hankali" Ta qarasa
fada tana qaramar dariyar dake nuna zallar farincikinta
"Kinyi qoqari auta sannu.......kin gama naki" Wadda aka kira da uwaisha ta fadi
tana matsowa gaban motar

"Kamar gaske" Sautin muryarsa ta fita a hankali ya furta sanda kan sabreen ke qasa
tana jin wani fargaba haka kawai na haduwa da mutanen da batasan su kuma meye nasu
kalar halin ba,sunan auta da taji an ambata sai ya sanya duka tsigar jikinta ya
tashi,haneefa da tun da safe take kokawa da tunaninta ta fado mata.....ko yaya ta
wuni?.

"Zallar karamci da girmamawa da mutuntawa muke gabatar miki" Abinda inna uwaisha ta
fada kenan kamar tasan abinda sabreen ke wassafawa qasan zuciyarta. Miqa mata hannu
inna uwaishan tayi tana fadin

"Sauko a hankali nayi miki jagora zuwa ciki,ki shirya don kowa na dokin jiranki".
Bata musa ba ta sakawa inna uwaishan hannunta

"Fatabarakallahu ahsanul kaliqeeen......da iya lallen nan ma kawai an tashi kaina
yallabai". Inna uwaishan ta fada tana dariya dariya idanunta akan muhammad fu'ad
dake qoqarin ficewa a motar sannan ta maida dubanta ga amna data dage mata gira
alamun Yes.

Inna uwaisha na daya daga cikin makusantan anni da suka daukeshi
tamkar d'a,duk da cewa tana da jika qwaya daya amma idan kaga suna raha da amna
saika dauka yaya ce da qanwarta,hakanan suma ta daukesu duka mazan gidan. Bai iya
cewa komai ba,sai dan motsawa da labbansa sukayi alamun murmushin dole kawai ya
sanya qafafunsa ya fice daga motar.

Kunnuwanta kawai ke iya jin surutansu amma idanunta suna a rufe. Batasan
ina suke nufa ba saidai idanunta na iya kallon lullubabban luxury marbles din dake
shimfide a wasu sassan na gidan,a haka taji sun isa wani daki da a nan inna uwaisha
tace da ita

"Fell free sabreen.....ki shirya amna zata tsaya dake,idan kun kammala zan dawo mu
wuce wajen taron,kowa ke yake jira". Kai ta gyada a hankali,cikin ranta kuma tana
zancan zucin wanne shirin kuma zata sakeyi bayan na jikinta.

Sanda amna ta gabatar mata da komai na shirin shuru kawai tayi tana
bin kayan da kallo......shin da saninsu wanne irin aure ne akayi suke wahal da
kansu haka da kashe kudade da hidima?,ko kuwa kallo kawai sukewa abun irin duban
bangon littafi ga idanuwan da basusan meye a cikinsa ba. Wata lafiyayyar Moroccan
gown dake da wani irin ado na daukan hankali......saidai kuma duk da adonnan nata
sam bata da nauyi ko kadan. Hade take da wani irin hijab dan qarami da yafi mata
kama da na Indonesia ko Malaysia.....a ciki batasan wanne ne ba. Komai na kayan
fari ne qal da wani irin haske me daukan hankali. Ita kanta bayan ta gama shiryawa
batasan lokacin data dauka tana kallon kanta ba,sai take ganin kamar ba ita
ba.....duk da kusan komai ma yana zuwa mata ne da wani irin ba zata da bata taba
zato ko kawowa cikin rayuwarta ba.

Amna ce ta fara shigowa wadda fiye da dazun a yanzunma ta susuce
wajen yabawa sabreen din.

"Inna Allah kwanan nan hamma zai manta da wani gold da Diamond"

"Maza dai ya jiki" Inna uwaisha ta fada tana riqe hannun sabreen suna nufar qofar
fita.

Suna shiga wajen tasan sun iso,duk da kusan kowa na zaune a nutse ana
sauraren jawabi daga bakin malamai.
"Muna yiwa amarya barka da shigowa". Maganar data dauki amsa kuwa cikin hall din,ta
kuma bawa maamah damar fara gyarawa tsaf don bayyanar da kanta a wajen.



Please Login or Register in order to submit comment