You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kin sace ko kuma saimun dangana
da hukuma?" Hannayenta ta goye a qirjinta tana kallon qofa yadda mutane ki shige da
ficensu hankali kwance. Yana da ban mamaki......saidai ita din ta fishi abun
mamaki. Inda yasan meta taka a kansa......inda tasan cewa kafataninsa.....zahirinsa
da badininsa a tafin hannunta yake da baiyi gigin matsawa rayuwarta ba har ya matso
gareta har haka ba.

A nutse ta waiwayo ta zube masa farare tas din idanunta masu matuqar
jan hankali da fusgar tunanin me tunani

"Kana sha'awar yin gaba da gaba da hukumar ne?" Ta masa tambayar idanunta a tsaye
car tsakiyar nashi. Idan ya kira kansa gogaggen cikin duniya baiyi qarya
ba.....muddin kuwa ya kasance hakan yana ganin mugun ganganci ne zaiyi ya gaza
samun fikirar karantar mutum daga yanayin kallo zuwa lafuzan bakinsa ba.......

"Kina tunanin abune me wahala a gareni?" Ya amsa mata yana mamakin yadda wannan
mugun kwarjinin nata yake taka masa burki,kaifin idanunta ke hanashi daukan mataki
tare da aiwatar da abinda yayi niyya.......abinda zuciyarsa ke shawartarsa.

"Ko daya....daidai ne kuma" Ta amsa masa tana dauke duba da hankalinta daga kanshi
tana maidawa ga ma'aikacin wanda ya kammala lissafin yana gaya mata adadin abinda
zata biya.

"Okay" Ta furta hankali kwance tana maida dubanta ga daya daga cikin ma'aikatan
dake taimakawa da wadanda sukayi siyayya me yawa kamarta

"Ko zaka fitamin dasu gate na biyu?"

"Okay hajiya" Ya fada yana ajjiye qaramar calculator dake hannunsa yana qarasowa
gurin tare da jira a gama sanya dukka kayan cikin leda.

Sake Waiwayowa tayi gareshi karo na biyu. Kallon da tayi masa ta fahimci
yakai matakin qarshe a iya haqurinsa

"Malam naseer......ka shirya biyan duka bill na siyayyar sabreen ko kuwa tunda kai
ka kawo qafafunka duk da gargadinka da tayi?"

"Sabreen?" Ya maimaita sunan yana kallon idanunta. Kiran sunan sabreen da tayi a
maimakon basma shi ya batar masa da tunani cikin taqi qanqani.

"Zai biya duka bill din.....na gode sosai" Ta fadiwa ma'aikacin

"Naga uban wanda zai sakani biyan kudin nan......na fahimci na sakar miki fa da
yawa" Ya furta da zafi sannan a zafafe ya biyo bayanta. Ya tsammaci zata nemi
guduwa ko ta gudu dinma,amma ga tarin mamakinsa tun bai qarasa isowa gareta ba taja
cak ta tsaya tana sauraron isowarsa.

"Ka samu aminci game da haramtattun kayanka da aka aiko maka dasu ta cikin jirgin
ruwan dake tsakanin River Benue da riba niger?.......ko kuma ka shirya aci kasuwar
wannan sirrin da jami'an tsaron dake neman kayan tamkar yadda mutuwa ke neman
ruhi?".

Kamar wanda aka sanyawa sasari akan tsaida haka yaja wani wawan
burki. Kallonta yakeyi da madaukakin mamaki. Wanne irin hadari ne da ita har haka?.
Wanne nisan ji da gani ne da ita?,nisan binciken da ya bata damar gano birnannen
sirrinsa da ko matarsa da suke kwana daki daya su tashi daki daya bata sani ba?.

"Ka biyasu kudin siyayyarsu duk yadda suka buqata,na barka lafiya Alhaji Naseer" Ta
qarashe maganar tana takawa hankali kwance tana fita kwata kwata daga wajen.
"Malam qaraso ka bada kudin......ta atm ne ko cash zaka bada?" Muryar ma'aikacin ta
katseshi daga bin burbushin hanyar data wuce da kallo ya juyo zuwa wajen biyan
kudin yana sauke wani irin gauron numfashi me nauyi da zafi cikin tsananin mamaki
da tsoro.

*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA
TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_

_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

*Arewabooks@:Huguma*

PAGE 21

https://chat.whatsapp.com/DT97XBDyEfyEwniN0a09Cz
__________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*

*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA
KUNYA KUWA?_*

*_KAMAR SU_*

Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes

*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries

*_inganci da kwalliya shine muradinmu_*
____________________________


Sanda take sallamewa saita samu kanta da zama sosai a inda ta idar da
sallar tana irga tasbihi da yatsun hannunta,yayin da kunnuwanta kadan kadan ke jiye
mata tasbihin matar dake yinsa can qasa qasa,saidai lokaci lokaci yana qwacewa ya
fito,har zuwa sannan bata waiwaya ko sau daya ta kalli fuskarta ba,amma daddadan
turarenta bai fasa silalowa zuwa cikin hancinta ba.

Wayarta ta matsa haske ya bayyana ta duba lokaci. Tasan ko busari
bai iso ba to dab yake da isowar,ta maida wayar ta ajiye tana kallon sararin cikin
masallacin da babu kowa saisu uku. Daidai sanda zata dauke idanunta dai dai sannan
taji matar dake gefan nata taja wani irin qaqqarfan salati numfashinta yana
yayyankewa.

A tsorace ta waiwaya gefan damanta... Hannuwanta dukka biyun na
tallafe da qirjinta,tana kuma daga kanta sama tare da qoqarin maimaita

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Saidai tana kakkamota ne da qyar saboda yadda
numfashin yake son qwace mata.

Da hanzari ta miqe,hanzarin daya sanyata cilli da wayarta dake
saman cinyarta. Jikinta dukka yana rawa a gaggauce ta matsa jikin matar

"Lafiya?,me yake faruwa?" Ta furta cikin matuqar tsoro da kuma rudanin ganin yadda
take kaman shirin rasa numfashinta.

Bata iya amsa mata ba,wannan ya sanya sabreen zama sosai ta
tallafeta da kyau zuwa jikinta tana sake maimaita tambayarta a rude

"Ina ganin kaman asthma attack ne" Mace guda dayan data rage a cikin masallacin ta
furta bayan ta iso wajen itama tana dubanta

"Asthma?" Sabreen ta furta a gigice tana jin wani abu yana dukan zuciyarta. Shine
ciwo guda daya da kullum taji sunansa sai zuciyarta ya tsinke,ciwo qwaya dayan da
kullum takewa mummunan kallo,ciwo guda dayan da yayi silar wasu jigo na
rayuwarta,har ila yau ciwo qwaya daya da yake wujijjiga rayuwarsu.

Da sauri ta finciko jakarta bayan da tunaninta ya dawo,ta zugeta da
hannu daya daya hannun yana tallafe da ita,ta daga jakar ta zazzage duka tarkacen
dake ciki,cikin matuqar sa'a ta hangi inhaler dihta.

A gaggauce ta dauka ta kara mata,hannuwan matar dukka rawa suke sanda
ta dora nata hannun saman na sabreen kamar tana son tayata matsa inhaler din,kamar
tanason nuna mata tsananin buqatarta da takeyi.

Cikin mintuna qalilan ta fara samuwa,saidai har yanxun bata daidaita
yadda ya kamata ace ta daidaita din ba. Oily eyes dinta sun cika taf da qwalla

"Kamar asibiti tafi buqatar a kaita" Ta kasa haquri har sai da bakinta ya furta
hakan

"Zaifi kyau dai gaskiya don da alama tana buqatar iska sosai".

Dai dai sannan wayarta data watsar ta dauki ringing. Matar ce ta matsa
ta miqo mata,ta sanya hannu ta karba tana fadin

" Na gode" Tana duba me kiran.

Busari ne,ta latse wayar tana karawa a kunnenta

"Na qaraso,ina dab da bakin masallacin"

"Ka karba kayana wajen me gadi,gani nan fitowa asibiti zamu wuce" Bata tsaya
sauraren abinda zai fada ba ta katse kiran.

Idanunta ta mayar saman fuskar matar. Wani abu taji ya taba
zuciyarta,sai takejin kamar umminta ce ta dawo,sai takejin tamkar lokacin data rasa
umminta. A duk sanda take mutum me dauke da irin ciwon tsananin tausayinsa yake
kamata,duk da itama abar tausayin ce. Duk sanda taga babbar kaman haka yana
fafutuka da wannan ciwon sai ta dinga tuna umminta.

Su biyun suka tallafeta don taji qwarin jikinta,suna takowa a hankali
da ita har suka fito zuwa inda Kekenapep din yake

"Zan samu face mask a wajenka?" Ta tambayi busari.

"Eh hajiya" Ya amsa mata da sauri yana bude aljihun motar ya fidda shi sabo fil ya
bata.

A kusa da ita ta zauna tana riqe da face mask din,saita sauke idanunta
qasa tana jujjuyashi.

"Zan saka miki wannan saboda iskan mota,motan bana gida bane". Idanunta saman
fuskar yarinyar,har zuciyarta tana jin qauna da jinjina taimakonta a kanta,ta lura
tana d'anjin wani nauyi da kuma rashin sakewa. Qaramar yarinya haka me zuciyar
taimako?,sai abun ya qayatar da ita.

Mintuna ashirin daidai suka qarasa private hospital din,wanda a nan
file nata dana qannenta dukka yake. Tuntuntuni ta sallama asibitin gwamnati,yana
daya daga cikin muhallan da suka samarwa rayuwarta gibi,yana daya daga cikin
guraren da suka dasa qaton tarihi a rayuwarta,suka kuma ajiye mata wani tabo na har
abada,shi ya sanya daga sanda ta samu dama ta nisanta kanta da dukkaninsu daga
asibitin gwamnati.

Private hospital ne daya amsa sunanshi,babu nau'in wata kulawa da mara
lafiya baya samunta,saidai kuma kudi ne zasu fita sosai daga aljihun majinyaci ko
ahalinsa.

Private room suka bata,cikin mintuna goma sha biyar kacal suka bata
dukkan taimakon daya dace,bata samu nutsuwa ba sai da suka shafe awa guda taga
bacci sosai ya dauketa tana sauke numfashin a hankali ta cikin oxygen din da suka
maqala mata saboda yadda taso galabaita sosai.

Zama tayi kawai gabanta bayan taja kujera,ta maqale hannunta a qirji
bayan ta zube idanunta a kanta tana dawo da bayanan da likita yayi mata a kanta.

"Ta samu mummunan attack ne,tana samun kulawa sosai to amma kuma kaman yanayi ya
nuna ba'a kiyaye wasu dokoki na masu ciwon,sannan kuskure ne ta dinga fita hakanan
ba tare da inhaler ko wani a kusa da ita ba".

Idanunta ta qanqance sosai tana ci gaba da nazarin maganganunsa.
Hakanan sai taji ranta yayi matuqar baci,indai har mace me irin wannan shekarun
bata samu kulawa ba sai yaushe?,indai har ba za'a kula da dokokin da aka bata ba
meye amfanin makusantanta?. Dukkan alamu sun nuna,tun daga suturar jikinta da komai
nata ma cikin wadata da sukunin rayuwa take ainun,to meye zai hana su su bata
kulawa su ahalin nata?.

Idan zata iya tunawa mutum daya ne ta gansu a tare a tsaye cikin
store din,har tana bada umarnin a kira mata wani data kira a cici da kuma yawale.
Yawonsu kenan yafi musu kasancewa da ita?,yanzu haka fa mahaifiyarsu ce amma sun
gwammaci tafiya yawo akan su bata kulawa?.

Iska me zafi ta sake fesarwa ranta yana sake tunzura musamman bayan
data duba agogon hannunta. Aqalla awa daya harda rabi da barowarsu store din amma
har yanxun basu biyo address na asibitin data barwa wancan matar sun biyo bayan
baiwar Allahn ba?. Sake juya wayarta tayi su huda suna fado mata a rai. Ta tabbatar
zuwa yanzun sun dawo gida,suna can kuma zaune su daya a daki. Karon farko da taji
kaman ya kamata ta siya waya ko qwaya daya ce ta ajiye cikin dakin saboda lalura
irin haka,ko ba komai ba zata barsu cikin zulumi ba,zata kira taji lafiyarsu suma
suji lafiyarta,duk kuwa da cewa komai runtsi a gida takeyin magrib.

Daidai sanda tunaninta yakai nan taji an murda handle na qofar.
Kyakkyawan matashin ne ya fara bayyana. Dogo me matsakaicin haske. Kai tsaye idan
kace masa kyakkyawa bakayi kuskure ba,yana da cikakkiyar suma me santsi tun daga
kansa zuwa habarsa.

Yana sanye da dakakkiyar shaddar getzner Neautaral color daketa yauqi
da sheqi. Yanayin dinkin da aka yiwa shaddar yayi masifar dacewa da structure na
jikinsa. Dinkin zamani dake nuna zallar gogewa da wadatar arziqi na wanda suturar
ke kwance a jikinsa. Yadda shaddar ke walqiya hakanan hular kansa,wadda koda ba'a
gaya maka kudinta ba zakasan cewa bada qaramin zare aka saqata ba. Qafafun sanye
cikin takalmin Batozzi,hakanan cikin qasa da second biyar dakin ya gauraye da
sassanyan qamshin turarensa.

"Hamma mun sameta,gata tana bacci" Ya furta da kwantacciyar muryarsa da alama kuma
yana magana ne da wani a wayar dake manne a kunnensa,dukka hankalinsa da idanuwansa
suna kan matar dake kwance cikin mazari yana d'okin isa gareta.

"Okay hamma......in sha Allah" Ya sake fadi da sauri sannan ya jefa wayar a
aljihunsa yana isa inda take kwancen ba tare daya damu ya kashe wayar ba.

Rusunawa yayi sosai a gabanta yana riqe da hannunta da dukka hannayensa
biyun. Yayi wani irin laushi,don idan ka kalli hannunsa da kyau kana iya ganin
yadda suke danyin rawa.

Dauke dubanta tayi daga kansa haushinsa yana saukar mata,saita maida
kallonta akan wanda suka shigo din tare. Shine dai wanda ta gansu cikin store din
tare wanda ta bari ya biya kudin siyayyar da tayi.

"Kamar kece kika kawota ko?" Ya fadi saboda hada idanu da sukayi. Maganar tashi
taja hankalinsa,yadan sassauta riqon da ya yiwa mara lafiyan ya kuma waiwayo da
dukka nasa idanun yana dubansu,don shi sam sam bai ma lura da kowa ba a wajen.

Kamar yayi mata susa ne a inda yake mata qaiqayi,sai ta miqe a nutse
tana saqala Jakarta a kafadarta,haushinsu yana sake turniqeta

"Eh nice bayan kun yasar da ita kun kama gabanku ba?,waishin kunsan muhimmancinta
kuwa?,kunsan yadda ciwonta ke buqatar a dinga yawan kulawa da ita musamman ita da
shekarunta suka fara yawa?.

Ji yayi maganganunta sunyi girma ainun,tasan wace ita din a wajensu
har da zataga gazawa da kasawarsu?. Saidai bai datseta ba saboda yadda yaga hawaye
suna cika idanunta

"Mutane da yawa basusan muhimmancin iyaye ba sai sanda suka rasasu......amma ku
sani cewa......yadda suka baku kulawa a sanda bakusan muhimmancin rayuwa ba.....ba
komai bane don kun basu kulawa a sanda sukasan muhimmancin nasu rayuwar......ba
kowa a kusa da ita.....ba inhaler.....yanzu inda numfashinta ya katse fa?" Ta
qarashe fada adan tsawace hawayen na fara gangarowa ta idonta qwaya daya,sai tayi
hanzarin kauda kanta gefe ta dauke hawayen da yatsanta. Su kadai sukasan yanayin da
suke shiga idan ciwon ya tasar musu shi yasa babu me fahimtar abun sai wanda ke
cikin yanayin

"Kuji tsoron Allah ku kula da ita yadda ya dace,don yadda muke amana a hannun iyaye
haka suma amana ne a hannunmu,kuma Allah zai tambayemu game da yadda muka kula da
tsufansu" Tana kaiwa nan ta soma takawa tana ficewa daga dakin.
Gaba daya mamakinta ya cikashi,yadda take haqiqancewa ba tare da tasan komai
a kansu ba. Mahaifiyarsa itace rauninsa har abada.....wani abu guda daya me matuqar
tsada da muhimmancin da ba madadinta. Har ta fice ya kasa tsaidata kaman yadda yaso
har sai data bacewa ganinsu.

"Bita ka tsaidata......a qalla ko godiya ya kamata muyi mata,sannan kuma muji yadda
za'a maida mata kudaden data kashe tunda na samu an biya bill na komai"

"Okay" Ya furta a girmame yana juyawa ya fice a dakin.

Kamar wayar dake aljihunsa yaji yana motsi,ya dafe wayar sai kuma ya
sanya hannu ya fiddota da sauri. Mamaki ya kamashi,ya akayi bai kashe wayar ba.
Hamman ne har yanzu akan layi,duka mintunan da sukayin wayar na a kunne,sai ya
maida wayar kunnensa

"Waye yake mata fada saman kai?" Ya furta nutse

"Wanda ta kawota ne daga can store din"

"Don ta kawotan take ma mutane fada?" Ya furta adan harzuqe

"No hamma...." Ya fadi da sauri. Numfashi yaja yana ware idanunsa sosai

"Stop......banason a sake mata hayaniya a wajen nan....if not ran kowa zai baci"

"In sha Allah hamma"

"Idan ta farka ta dawo daidai give me a call"

"Done" Ya fada a taqaice kafin ya yanke masa waya,yana gama fadin kuwa yaji qit ya
gintse wayar,saiya cireta daga kunnensa yana girgiza kai.

"Hamma.....hamma" Ya maimaita sau biyu.

Koda cewa tayi fada cikin yanke hukunci akan abinda bata sani
ba.....bata da yaqini amma shi baiga laifinta ba,ya mata uzuri......hasalima ta
burgeshi qwarai,dukkan alamu yana nuna tasan darajar dan adam ne,sai ya maida
hankalinsa akanta yana duba shiga da fitar numfashinta.


*SU SAKE DAWO MUKU DA WASU SABBIN LABARAI*

*_BAYAN WASAN DA AKA BUGA GA WANI SABON WASAN_*

*_MIQAQQIYAR TAFIYAR NISHADI_*

*_KAFATAWA DA ZAFAFAN MUHAWARA_*

*_LABARAI MASU DAURE KAI DA SANYA NISHADI A CIKIN ZUKATAN MASU KARATU_*

*ZAFAFA BIYAR*

*_MASUBURBUDAR LABARAI MASU CIKE DA HIKIMA DA DEBE KEWA DA WASA TUNANI TARE DA
TSUMA ME KARATU DA TSUMAMMIYA KUMA TSAFTATACCIYAR SOYAYYA_*

*Hanzarta shiga ayarin ZAFAFA FAMILY(WATO IYALAN ZAFAFA DA BASA GAJIYA DA KASANCEWA
DA SU*

_TA HANYAR SHIGA RUKUNIN MASU SIYAN LITATTAFANSU KAMAR HAKA_
_QIRJIN ME HANKALI Miss xoxo_

_K'ALBIM Mamuhghee_

_AJIYA A DUHU Billynabdul_

_DUNIYATA Huguma_

_Dukka qunshin litattafan daga farko har qarshensu_

*hudu 2k*

*uku 1500*

*Biyu 1k*

*Daya 500*

_YADDA ZAKU BIYA IDAN KATI NE:_

*09032345899 KATIN MTN, IDAN AN TURA SHEDAR MA NUMBER ZAA TURAWA*

*IDAN BANKI NE A TURA SHEDA ZUWA GA*
*09033181070*

*BANK NAME/SUNAN BANKI: ACCESS BANK*

*ACCOUNT NUMBER/LAMBAR ASUSUN BANKI: 0022419171*

*ACOUNT NAME/SUNAN DA KE ASUSUN BANKI:MARYAM SANI GUMMI*

*AL'UMMAR MAQWAFCIYAR QASATA NIJER KUWA*🇳🇪🇳🇪

89825722
Nousaiba lawali maradi
1000cf

*_Madalla da masoyan ZAFAFA BIYAR_*

*_MADALLA DA KASANCEWARKU TARE DASU_*🥰🥰


*D U N I Y A T A*

*_H U G U M A_*

*Arewabooks@:Huguma*
https://www.arewabooks.com/book?id=675041625c3130f457519997

PAGE 22
__________________________
*_ALBISHIR A GAREKU!!_*

*_SHIN KUNSAN UMMUMAHNOOR LUXURIES TA TANADAR MUKU INGANTATTUN KAYAN ADO NA FITA
KUNYA KUWA?_*

*_KAMAR SU_*
Atamfofi
Laces
Shadda
Materials
Takalma
Jakunkuna
Mayafai
Trolley
Sarka da dan kunne
Oil perfumes

*_karki tsaya sanya har ayi babu ke,maza garzaya ta nan_*

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries

*_inganci da kwalliya shine muradinmu_*
____________________________



Batasan me yasa ba,batasan dalilin da ya sanyata takejin bacin rai
sosai akan abun ba. Ta dinga fidda numfashi me dumi a hankali daga baki zuwa
hancinta. Cikin nutsatsen takun nan nata take nufar inda tabar busari yana jiranta.
Takun da yayi matuqar tafiya da hankali da tunaninsa baya ga zubin mamallakin
takun.

"Wai har yanzu akwai irin mata masu wannan ajin?" Ya furta qasa qasa ba tare da
yasan a waje yayi maganar ba,tana ta'allaqa dubansa a kanta,yana jin tana tafiya da
gaba daya kuzari tunaninsa dama hankalinsa gaba daya.

Tamkar an zungureshi ko kuma anyi masa qaimi,sai ya saka hannu da wani
irin hanzari yana bude murfin motar. Sam gaba daya ya manta da dalilin daya kawosu
asibitin,ya kuma manta ma da waye yake tare,burinsa guda daya tal! A yanzu,ya samu
isa gareta,yakuma samu daman yin magana da ita.

Sallamar tashi ta ratsa kunnenta a sanda take dab da isa wajen da
Kekenapep din yake. Ta lumshe idanunta a nutse tana riqe masaqalin jakarta da kyau.
Dama tasan hakan zata iya faruwa duba,zaiyi wahala a kallon farko da tayi masa ya
iya tsallake halaye da kuma dabi'uj data hanga kai tsaye daga gareshi.

"Assalamu alaikum.....don Allah....." Ya katse maganar tashi da kan kanshi lokacin
da yasha gabanta idanunsu suka gauraya waje daya.

Wani kwarjini na musamman,wani yanayi ya tsarga masa irin wanda bai
taba jin irinsa ba. Nashi idanun ya janye a hankali yana qoqarin daidaita kansa
tare da zallar mamaki yana kuma tambayar kansa

"Meye haka?,ita din wace?". Baisan iya adadin kalar matan daya gani ba tun da ya
fara zama cikakken namiji zuwa yau. Baisan adadin matan da yayi mu'amala dasu ba
daga jinsin yare daban daban,amma yau daya wata mace da baya tunanin ta rufa
shekara ashirin da biyar a duniya na neman yi masa kwarjini?.
"Lafiya?" Ta jefa masa tambayar tana tsuke fuskarta tare da sake bada tazara
tsakaninsu. Qoqarin daidaita nutsuwarsa yayi,sai ya sake mata murmushi hadi da
gyara tsaiwarsa sosai a gabanta,yana jin ba wata mace da zata iya kaucewa tarkonsa
muddin ya d'ana shi.

"Ba lafiya ba......maganar gaskiya kenan.......akwai gagarumin tashin hankali" A
mamakance take duba fuskarsa tana yamutse tata tare da qoqarin sakeyi masa sabon
karatun da baisan tana yi ba

"Amma fa a zuciyata" Ya qarashe maganar yana dafe qirjinsa.

Numfashi taja sosai har cikin huhunta sannan ta fesar tana kauda
kanta gefe hadi da juya qwayoyin idanunta. Ba shine mutum na farko data taba gamuwa
dashi me irin wannan salon ba,don haka tafiyar dashi bazai bata wahala ba.

Dukkan wani d'a namiji da zai ratso rayuwarta tayi imanin QADDARARSA
ce a nan.......da kuma zallar tsautsayi. Mafi rinjaye daga cikinsu kuma SON RAI da
SON ZUKATA.

Ba kasafai ta fiya bada kai ta farat daya ba,koda ta tsara amsarka,don
tuni ta fahimci duk wani abu da akeson yayi daraja.....kar a bari samuwarsa ta zama
ta sauqi. Don haka ta soma tattaki da zummar kubcewa daga gabansa.

A gaggauce ya sake tare mata gaba yana dubanta cikin marairaicewa

"Ranki ya dade.......na tabbatar girmanki yafi gaban a tsaidaki a hanya....to amma
muddin na barki kika wuce din nayi imanin sa'ata ta rayuwa ce ta kubcemin gaba
dayanta......ki tallafeni ki sammin minti uku kacal" Ya furta yana nuna yatsunsa
guda ukun.

Juyowa ta sakeyi a karo na uku tana kallonsa. Ya fiya zaqin baki da
yawa,maza irinsa suna da wani hali da dabia da tuni ta gama karatunsa. Tabbas akwai
wani abu tattare dashi da wata qila take nema......tana hasashen yiwuwar samun wata
qaruwa me girman gaske. Taga irinsa ba daya ba.....ba biyu ba....ba uku ba,har ba
zata iya tantance adadi ba.

Duk da wannan hasashen amma bata yarda ta nuna masa komai ba. Sai ta
sake kau da kanta tana yamutsa fuska

"Matsawarka daga hanyata kamar zaifi zame maka alkhairi akan ci gaba da
tsaiwar......ina da tarin abubuwa a gabana....."

"Bansan ko me ke jiranki ba......amma na tabbatar koda baikai wannan tsaiwar tamu
alkhairi ba bazai wuceta ba" Ya fadi a zaqe da fatan samun nasara

"Na roqeki kada ki watsan qasa a idanu,ki wofantar da wannan kyakkyawar damar a
garemu gaba daya" Ya fadi yana marairaicewa tare da miqa mata wayar hannunsa yana
kasheta da idanu gami da karyar da wuya da raunanar da idanun nasa.

A nutse ta sauke kallonta akan wayar ta kalla. Tsaleliyar iPhone 16
wadda kana dubanta zakasan bata wani jima da baro dumin kwalin da aka qerata ba. A
yangance ta dauke kanta daga kai ta sake maidawa gefanta bayan.

Wani numfashi ya fusga da qyar bayan ya gama sauraren jerin lambar
wayarta data karanto masa. Sautin muryar nata yana masa wani irin amsa kuwwa a
kunnensa. Karon farko daya yadda cewa muryoyin wasu matan kadai suna iya haddasa
fitina a zukata da gangar jikkunan maza. Sai yakejin yana sake zurfi ason ya
kasance a tare da ita
"Sai nakega kaman girma da martabarki ya dara kihau napep.....da zai yiwu da kin
sadaukarmin da wannan tsadajjen lokacin na saukeki a gida....." Yana ajewa tana
daga masa hannunta,sannan ta fara takawa tana wucewa cikin abun hawan da busari ke
jiranta.

Har ya bawa napep din wuta suka fice daga harabar asibitin yana tsaye
a gurin. Sai daya tabbatar sun qwacewa ganinsa sannan ya buga qafarshi yana yarfar
da hannunsa,wani shu'umin murmushi yana kubce masa. Ba shakka ita din ME ZAFI ce,ta
kuma cancanci dukkan wannan dagawar da kuma jan ajin. Yana da makamai a hannunsa
masu tarin yawan da zai iya yaqar zuciyarta yakuma yi nasara

Please Login or Register in order to submit comment