You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zama,yayita
kallon duniyarsa da yanzun ta rarrabu da wasu hadakar qananun duniyoyin har guda
uku.

Murmushi ya saki yana gyada kai,shi za'a yiwa wariyar launin fata kenan
a ware masa abbansa?,kawai sai ya dauki waya ya kira musaddiq da nashi saqon.

Sanda musaddiq ke sanar da bada kyautar JADDA WINGS ga almustapha
kusan kowa sai da yaji shock,kafin daga bisani gurin ya kaure da tafi.

"Sannan nima ina gabatar da tawa qaramar kyautar motar" Ya fadi yana fiddo maqullin
motar daga aljihunsa ya dagashi sama ya kuma isa gaban abban nashi almustapha ya
ajiye. Motace me bala'in tsada new model,wadda har yanzun ko cikin masu kudi ba
kowa bane ya samu nasarar mallakarta ba. Tabbas abban abba ne,kusan yafi kowa a
cikinsu tashi da gwaggwabar kyauta.

Kafin abar gurin fu'ad ya sanya qaramar musabaqa ga yara masu haddan
qur'ani a wajen,daga shekara goma sha biyu zuwa qasa,koda izu uku ke gareka kuwa.
An gwabza musabaqa me kyau,abinda ya sake janye hankalin sabreen taji a duniya bata
da burin daya wuce yaran nata su zama mahaddatan alqur'ani.

Sai da aka kammala komai sannan anni itama ta gabatar da nata kyautan.
Motoci ne masu kyan gaske guda uku iri daya sak,dukkaninsu farare qal,amna kuwa
wani babban box ne da ba wanda yasan ainihin meye a ciki. Fannah ma ba'a barta a
baya ba,itama da nata gift din,haka dai kusan duk wanda yazo wajen da nasa
alkhairin da zai gabatar,

Muhammad fu'ad jadda ba qashin yarwa bane,komai arziqinka komai kuma
babunka ba zaka taba cewa baka amfana dashi da komai ba,wannan ya saya ma yaranshi
dama matarsa wata irin soyayya da qauna.

Taro ya tashi lafiya,yara kuma sun tabbatar da sunayensu na ALMUSTAPHA
MUHAMMAD JADDA(FAWAD). HAMZA MUHAMMAD JADDA(FAUZAN). da babban aboki amini kuma dan
uwa UMAR MUHAMMAD JADDA(FAWWAZ). Yaran sunzo da wani irin yanayi a dangi gaba
daya,yan uwa dama wadanda ba 'yan uwa ba kowa ya tafi da fawwaz fauzan da fawad a
bakinsa.

Kusan gaban idanunshi aka gama komai,koda ya dawo gidan wajen sha
biyun dare yayi mamakin haurowarta samanshi batayi bacci ba.

Daga qofa ta tsaya ta langabe kafada,ya saki murmushi yana cewa.

"Qaraso ciki........kinsa yau duka kishi ya kamani......na kasa sukuni sam". Ido ta
zaro,ya sakata sakin murmushin da bata shirya ba.

"Hamma.....kishin me?,duka mata ne fa a wajen,yaran dake wajen under age ne fa?".
Idonsa ya lumshe yana duban dukiyar fulaninta da suka tutturo kaman suna
tsokanarshi ne ma,lafiyayyar farar fatarta dake samun kulawa tana sake qawata
su,uwa uba kuma yanayin rigar da tayi amfani da ita V neck ne da aka shimfidawa
lace.

Wani abu ya hadiye a maqoshinsa kawai ya miqa mata hannu,tana mamakin
maganarsa ne,don haka sam bata lura da mayataccen kallon da yake watsa mata ba.

Tanata masa surutu na labarin taron suna,har sai da yayi mata wata
kyakkyawar runguma sannan hankalinta ya dawo jikinta,dif surutun ya dauke,shuru ya
wanzu a dakin,sai sautin bugawar zuciyoyinsu. Duk wani gaba ta jikinsa sai data
amsa,ya sake cusa hancinsa cikin jikinta yana jin qamshinta yana birkitashi.

"Sati uku adda na......sati uku da haihuwan su fauxan right?" Kai ta gyada masa,sai
shima ya jinjina kansa yana dan zame jikinsa kadan daga nata.

"Naga kaman kinyi sallah daxun da asuba ko?". Qirjinta ya buga tsoro ya saukar
mata.

"Hamma.....nayi sallah......amma fa three weeks....." Yadda ya zuba mata jajayen
idanunshi ya hanata qarasa magana,ta maida abinda takeson cewa.163


"Yayi wuri?,nasan haka zakice.....amma bakisan me nakeji bane sabrrrr".

" I know hamma......na sani,ba wani motsinka da zan kasa gane manufarsa.......I
will always be ready to accept you.....amma yanzu hamma,dr tace ina buqatar time
kafin wannan abun,yana da kyau nayi healing sosai". Zame jikinsa yayi yana lumshe
idanunsa ya koma wata kujerar daban ya zauna yana dafe goshinsa. Tausayinsa taji ya
kamata,ta tako a hankali zuwa gabansa ta tsugunna tana dora hannuwanta saman
cinyarsa.

"May I help you?.bette" Idanunsa da suka sauya launi ya bude a hankali yana
kallonta,saita sake gyara tsugunonta

"I will help you to feel better" Idanunsa ya ware a kanta yana dafe hannuwanta.

"No.....ba abinda hakan zai qara bazai magani ba.....komai zai iya faruwa don
qishirwa kawai zaki qaramin......dawo nan ki zauna muyi hira" Abinda yace kenan da
ita yana ture mata pillows din da suke gefanta.

Hirar kuwa tayi masa sosai,ta dinga bashi labaran abinda ya faru a
wajen. Tun yana tsume har ya ware,ya soma dariyan abubuwan da take bashi
labarin,qarshe dai a nan suka bingire yana rungume da ita,basu tashi farkawa ba
saida kiran wayar tashin triplet ya farkar dasu.

★Sannu a hankali kwanaki suka dinga tafiya,abubuwa da yawa sun lafa kuma
sunyi sanyi,kaman darajar haihuwan yaran yazo musu da abubuwa ne masu yawa.

Amna da fannah harma da huda dukkaninsu goyon ciki sukeyi,amma hakan
bai rage musu kwadayi ko sha'awar yaran ba. Babu wanda ke iya kwana biyu cikakke ba
tare daya kira yaji lafiyar yaran ba. Farouq kuwa da aka jarabceshi da son
takwararsa gidan ya zame masa kaman hanyar wucewa,sai aiki yayi mugun cude masa
yake kwana uku bai shigo gidan yaga yaran nashi ba,ya kuma kebe takwaransa sunyi
ganawa ta daban da sauran.

Ta bangaren maamah kuwa.....tun ranar daya kai mata yaran suka kasa
bacewa daga idanu da kunnenta. Cikin awanni ashirin da hudu na yininta kowanne awa
bata rufewa ba tare data tunasu ba. Sannu sannu sai takejin kamar tanason ta sake
ganin yaran,kaman tana kewarsu,idan tana dakin bata da aiki sai kallon muhallin da
ya kwantar dasu a waccan ranar. Wani abu takejin kamar yana shirin kamata me kama
da hauka hauka akan yaran,tana yawan jin irin kukan da sukayi a waccar ranar,tana
yawan jin muryoyinsu kaman suna wajen.

Daga qarshe dai ta fahimci son ganinsu takeyi,saita ta rasa kuma yadda
zata fahimtar dasu saratu tanason ta sake ganin yaran,don iyasu kadai kawai takeson
gani banda mahaifiyar tasu.

A hankali sabreen din cikin salo da hikima ta soma gyaran jikinta ta
hannun dattijuwar matar nan da tasan jiya tasan yau kuma har gobe ake tafiya da ita
wato Bgawos kitchen and aphrodisiac. Ingantattun kayan gyara natural na matan da
suka jima a duniya kusan shekaru hamsin.08127084190/08104553105(tasan sirrin gyara
sosai,gyara irin na dauri na tsaffin mata bana zamani ba,bana gama garin masu
magungunan matan yanzu ba,bama gyaran kadai ba,hadda duk wani nau'in abinciccika,na
biki ne suna taron sauka walima da sauransu,ko kuma kawai akwai ranar da zaki tashi
bakya sha'awar shiga kitchen?,kinaso kuma abincin gidan ki ya zama ready a tsaftace
kaman ke kika shiga kitchen din kikayi da kanki?,karki tsallake wannan).

A jikinta kawai taji canji me matuqar yawa,ta sake jinta tana sake
kintsuwa tako ina. Har ta soma gyaran jiki ta watsar,don ta tsorata sosai ranar da
fu'ad ya rutsata,da qyar tasha,amma daga qarshe ya gaya mata yana lissafe da
satittikan da suka rage.

Tunani ta shiga sosai na yadda zata kubce masa,tanaso ta sake warkewa
sosai,uwa uba kuma sunyi hira da fannah,har suka gangaro kan tsarin iyali.
"Muddin period dinki ya dawo to duk sanda kuka kasance tare xaki iya daukan wani
cikin" Idanu sabreen ta waro waje.

"Ciki fannah......" Ta danyi dariya.

"Satinsu fauzan nawa?" Dariya fannah tayi.

"Shi ba ruwansa da satin yaranki nawa......indai har period ya dawo daidai shikenan
magana ya qare"

"Fannan BB...." Sabreen ta fada tana cin serious.

"Adda sabreen" Ta amsa mata tana dariya qasa qasa.

"Kibar zancan nan tukunna......me zaki bani na gyara tsarabar bare bari" Gyara zama
fannah tayi.

"Kamar kuwa kinsan mu bare bari ba wasa bane" Sai suka saki dariya a tare.

"Bari na gutsira miki kadan.....ki samu 'ya'yan habbatussauda da dabino ki dinga ki
tsaga dabinon ki cire qwallon ki zuba yayan habba din ki dinga taunawa kullum safe
da dare". Da daya da daya ta dinga bata sirrikan da na barebari ne,ita kanta ta
qaru ta kuma sallama (sai damu wallahi😂).

A tsorace take har zuwa sanda suka cika sati shida,ganin sun tsallake
ranar baice mata komai ba,don washegari qaramar tafiya ta kamashi zuwa branch dinsa
na lagos,don haka kawai tayi amfanin da wannan damar ta tayar da yawon arba'in.

Dabara tayi,ta kira anni tace mata tana son zuwa din,amma bata samu
hamman ba,tunda tasan wani lokaci idan tafiya me muhimmanci wadda take ta gaggawa
irin haka ta taso masa yakan saka layinsa a flight mode ne

"Yana da kyau ai,ko don a sake ganin 'yan uwa,zan gaya masa da kaina" .

Hankali kwance tahau shirinta,so samu ma ta wuce mali wajen
mommanta,to amma mali din tasan tayi nisa ta tsallake zuwa can,don haka kawai saita
shirya zuwa abuja gidan yayan ummeenta da bai jima da dawowa Nigeria ba,ta shirya
su fauzan duka da masu aikinta,ta siya musu ticket suka wuce abinsu.

Sanda anni ta gaya masa harda 'yar mitarsa,yana tunanin cikin kano ne
zasuyi ziyaransu gidan kawu rufai da gidansu da sauran wajen 'yan uwa su dawo gida
su kwana.

"Anni kina ganin ba zata debowa yaran nan iska ba?,40 days fa kawai sukayi,nima
kwana uku kawai zanyi fa na dawo,meye na fitan?" Ya kasa boyewa sai daya furta.

"Banda abinka fu'ad ai sada zumunci ne,kuma a al'ada ai dama ana yin wannan
zagayen,kaman ba gajiya ne da kuma nunawa dangi lafiya kuke ne" Shuru ya
danyi,dondai anni ce,yana kuma kunyar jayayya da ita.

"Shikenan,Allah ya kiyaye hanya"

"Ameen ameen" Anni ta amsashi suka dan sake tattaunawa sannan suka shiga wani
maganan na daban.

_Yawon arba'in ko?....hmmmm😂😂......._

_get ready muna pages din qarshe ne fa in sha Allah_🥰🥰🥰
★Kwanansa uku a lagos,kwanan sabreen biyu a Abuja ya dawo kano. Har ya iso
gidan baiyi wani tunanin abuja ta tafi ba,sai bayan ya shigo ne yadda gidan yayi
masa shuru da yawa ya sakashi ya fara kokwanto. Tun a parlor na biyu ya soma da
duba kitchen. Ba alamun dazu ko jiya anyi amfani dashi,kai tsaye kawai ya wuce
bedroom dinta.

Yadda yaga komai a killace ya bashi amsar cewa ba mutum a gidan,mamaki
ya sanyashi zama gefan gadon nata,yana kallon inda aka shirya qananun gado saboda
su fauzan idan a dakin zasu kwana.

Sai lokacin yayi noticing wani abu,tunda ya tafi shi yake kiranta,idan
ya kunna wayar yana tunanin zai samu saqonta ko miscal dinta sai ya tarar
wayam,idan kuma ya tashi kiran nata sai ya kira sau nawa ana gaya masa isn't
reachable,sai daga baya ya sameta. Jiyama kwata kwata basuyi waya ba,don ya shiga
cikin qaguwar kammala aikin daya kaishi ya juyo gida.

Ya manta rabon da yayi nesa da ita har haka.....bare su yaran da dama
bai taba nesa dasu ba sai a wannan karon.

Koda ya ciro wayarsa sai ya rasa waye zai kira?. Anni dai ya tabbatar
bada cikakken saninta akan baisan nesa zasuyi ba akayi tafiyar ba........ita kuma
sabreen ya kirata yace mata me?.

Wani mummunan baci yaji ranshi ya soma yi,zuciyarsa ta soma tafasa
sosai,sai kawai ya fara maimaita

"A'uzubillahi minashshaidanir rajeem.....innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". A
hankali a hankali yaji zuciyarsa tana yin sanyi,gefe guda kuma yana tunawa kansa
maganganun malamai da yawa da kuma abbansa,hadisin manzan Allah S A W da yake
gayawa maza su waye mata?.....karkatacciyar halitta da aka halicceta da qashi mafi
karkacewa na haqarqari,da wannan ya danne zuciyarsa badon ranshi ya daina baci ba.

Samansa ya haura yayi wanka,ya dawo ya shirya cikin shigar wani
tattausan yadi ruwan sararin samaniya,kawai sai ya dauki key da wayarsa ya fice a
gidan,duk da cewa yunwa yakeji.

Da kansa yake driving,kanshi cunkushe da tunanin ina zata je?,ina
zataje da har bai sani ba?,ya miqa hannunsa ya dauki wayarsa da daya hannun dayan
kuma yana riqe da steering ya soma kiran anni.

Bugu uku annin ta dauka,yana iya jin maganarta da su nadra,yaran da
qiri qiri tace nata ne.....bama tun ya zu ba,tun a baya inda tasan dasu da tuni sun
jima da zama a hannunta,dole kowa dake da kwadayin daukarsu ya haqura yabar mata
su.

"Barka da dare anni" Ya furta muryarsa ba wani karsashi yana rage gudun motar.

"Barka kade me babban suna,abban abbobinsa" Ta fada da dan tsokana kadan a
muryarta. Duk yadda yakejin muryarsa a jagule saida sabon sunan data sanya masa ya
sakashi sakin murmushi.

"Mun yini lafiya?"

"Alhamdulillah.....ka dawo ne?". Sai daya hadiye wani abu sannan ya amsa mata.

" Na dawo dazun,bai wuce awa daya ba".
"To ma sha Allah,Allah ya bada abinda akaje nema da nasara me yawa"

"Ameen ya hayyu ya qayyumu" Sai kuma ya danyi shuru.

"Da wani abune?" Ta tambayeshi,kaman yadda ta saba da saurin gano damuwarsa tun
baikai ga furtata ba.

"Cewa nayi anni......wanne waje ne su fauxan suka je?" Banbarakwai anni taji
maganar

"Abuja mana.....ina cewa kun fara magana dama tun kafin ka tafi?". Kai ya girgiza a
hankali,ya fahimci inda maganar yanzun ta dosa. Idan ya cewa anni baisani ba hakan
bai dace ba,zai zamana kaman ya nunawa anni wani laifi nata da wala'alla zai saka
annin jin wani iri a kanta,don haka sai kawai yace.

"Ba komai anni......na dauka sun canza booking ne"

"Aah abujanne dai,gidan uncle mubarak ko".

"Ba matsala.......sai na shigo".

"To Allah ya kawoka lafiya" Har zai yanke kiran ta rigashi.

"Me kaci daka dawo?" Tayi tambayar ne don bata gamsu da yanayin muryarsa ba,kuma
wani tunani ne yazo kanta a sannan.

"Ba komai anni....amma zanci".

" Ka qaraso ga favourite dinka anyi".

"In sha Allah,godiya nake" Ya fadi yana yanke kiran.

Cilla wayar yayi seat me zaman banza yana jin wani bacin rai yana taso
masa. Duk wani dalili na kiranta yakejin babu shi yanzu a tattare dashi. Gudun na
meye?,kaman wadda yake sarar naman jikinta?,ko soyayyar daya bata ne ta mata yawa
takeson ta fara karya alqawarinsu,ta kuma fara wahal dashi kaman yadda sauran mata
sukeyi a sanda suka samu soyayyar d'a namiji yadda sukeso?. Shikam yana jin bazai
dauki irin wannan ba,ya tsare mata dukkan komai,itama ya kamata ta tsare masa.

_hausawa sukace zo mu zauna zo mu saba,ran maza ya baci_

_wanne hukunci kuke ganin ya kamata jadda ya yiwa sabreen?_😂😂164



Karya kan motar tasa yayi zuwa unguwar tasu,yana jin ya kamata ya duba
maamah,duk da ko bayan ya tafi kullum sai ya kira yaji ya suka kwana,ya kuma suka
tashi.

Tun daga gate masu aikin gidan suke gaidashi,har zuwa sanda ya isa qofar
parlor din. Takalmansa ya cire,sam bashi da wannan dabi'ar na shiga guri da
takalmi,duk da girman daraja da matsayin da Allah ya bashi,ya sanya kansa a parlor
din a nutse bakinsa dauke da sallama,duk kuwa da yadda zuciyarsa ke a matuqar
b'ace.

Muryarsa ta sanyata daga kanta da sauri daga karbar madarar da saratu
take bata. Idanunta ta kafe a kansa kafin ta maida dubansa zuwa ga bayansa kaman me
neman wani abu. Ita shima yake kallo,yana mamakin yadda taketa kallon bayansa
din,kwanyarsa nason lalubo masa dalilin kallon.
Bugun zuciyarta yadan qaru,sai taji zuciyarta tana dan washewa daga
sanda yayi sallama a parlor din. Can qasan ranta ta samu kanta da fatan Allah yasa
tare yake da yaran,Allah yasa tare suke,saidai duk walwalar da taji ta sauko mata
sai taji tana komawa sanda ya qarasa shigowa falon,ta kuma fahimci shi kadai ne.

"Kawo na qarasa bata" Fu'ad yace da saratu sanda ta gama gaidashi yaja kujera ya
zauna daura da maamah din. Amsa masa tayi cikin girmamawa,ta miqa masa hade da dan
qaramin towel sannan ta miqe tana basu guri.

Duk sanda ya miqa madarar bakinta sai yaga ta kafeshi da wani irin
kallo,ya kasa gane abinda yasa take binsa da kallon,saidai yasan cewa lallai akwai
wani abun a qasa.

Wani irin boundaries takeji tsakaninta dashi,zamansa kusa da ita yana
shayar da ita madarar sai taji kamar ana sauyata ana kuma sauya jiki da zuciyarta.
Fuskokin yaran guda uku take gani a tasa fuskar,tanaso tace masa ina suke?,tanaso
tace masa ina ya barsu?,tanaso tace masa yaje ya dauko mata su amma kuma ba halin
hakan,ba kuma bakin hakan a tare da ita.

"Akwai wani abu da kike buqata?" Ya tambayeta ganin yadda kallon yaqi qarewa yana
kallon hannuwanta. Kai ta girgiza masa a hankali,amma still bata daina kallonsa ba.

"Zaki iya rubutu?" Ya tambayeta bayan ya gama kallon hannunta guda daya wanda tun
wancan ranar yaci gaba da motsi. Kai ta daga masa a hankali tana jin zuciyarta tana
tsinkewa. Kowa da yake tare da ita ya gaza gano mata hanyar fadin abinda yake
bakinta amma gashi daga zuwansa har ya gano hakan.

Tana ji yana kiran saratu,sannan ya sakata taje ta dauko memo da
sticky notes a ajjiye mata koda yaushe a kusa da ita.

Sanda ta kawo din sai ya ciri sticky notes din guda daya da a biro
ya dora saman cinyarta

"Write it down" Ya fada a nutse yana kallonta. Gabanta ne ya fadi,jikinta kuma
dukka yayi sanyi tana jin wani yanayi daya haifar mata da fara rawa da jikinta
yayi. Sauke biron tayi tana jin ba zata iya rubuta komai ba. Tana jin kunyar
tambayarsa yaran duk kuwa da yadda take bala'in son ganinsu......ba abinda ya dawo
mata a lokacin sai gamuwarsu ta qarshe,daya ajjiye mata abun rubutu kaman haka,yace
kuma ta rubuta dukka adadin abinda takeso zai bata don ta rabu da rayuwarsu har
abada,kenan hakan yana nufin inda ta rubuta din sun rabu?,inda ta rubuta din da
yanzu ko dan tsako bata dashi wanda zai zauna haka a gabanta ya damu da damuwarta?.
Ga dukiyar ga komai tana gani......amma kuma bata wani jin d'andanonta sam a
tattare da ita.

Lumshe idanunta kawai tayi tana maida bayanta jikin kujera ta
jingina,yadan tsaya yana kallonta saiya kalli saratu.

"Idan bacci takeji a maidata daki a gyara mata gun kwanciya.....ni zan wuce,sai da
safe idan Allah ya kaimu"

"To ranka ya dade....Allah ya tashemu lafiya".

Kai tsaye gidan anni ya wuce,ya sameta da 'yan matanta guda biyun,nadra
da haneefa. Abinci sukeci,kai tsaye nadra ta shirya masa nasa abincin sannan sukayi
qoqarin tashi su basu waje shida anni.

"Kuyi zamanku" Fu'ad ya fadi yana ganin fuskar haneefa kamar sabreen ce a wajen
saboda kamannin da suke da ita.
Sosai yayi qoqarin share damuwarsa ta hanyar sakewa yayi hira da
anni,saidai suna tsaka da hirar kiran sabreen ya shigo wayar annin.

Bai sake cewa komai ba yaci gaba da cin abincinsa,saidai kuma yana iya
dauko sound dinta ta cikin wayar. Abinda ya sake quleshi yadda yaji tana hira
hankalinta kwance,suka gama maganganun da zasuyi da anni su haneefa suka karba suma
suka dora.

"Lafiya dai ko Muhammadu?" Anni tace dame babban suna wanda har ya kammala cin
abinda zai iya ci ya miqe. Murmushi ya qirqira.

"Ba komai anni......" Bata gamsu ba sam sam,saidai daga kiran da sabreen tayi kawai
taga fuskarsa ta sake canzawa,amma kuma bataso ta zama me yawan sanya kai akan
mu'amalolin gidajensu. Koda matsala ce tafison su koyi kasheta da kansu da
kansu,hakan zai koya musu jarumta da kuma dabarun xama da juna da kuma sake samun
shaquewa sosai da juna.

Ya yiwa anni sallama ya fito zuwa parking lot na gidan farouq ya
shigo shida fannah. Fanna ta gaidashi ta wuce ciki,shi kuma farouq din yayi tsaye
daga wajen motar fu'ad na daga ciki ya zuro qafafunsa waje.

"Inata tunanin kiranka ai" Fu'ad ya fadi yana dan shafa sumarsa,don duk yadda
yakeso yayi avoiding damuwar amma har yanzu yana jinta cikin kansa.

"Lafiya kake dude?" Farouq ya tambayi fu'ad din. Kaman zaice wani abu sai kawai ya
basar,yanason koma meye ya ganar da ita kurenta da kansa,basai wani ya ji ba.

"Share kawai......hannu nakeso ka sakamin a nan" Ya qarashe maganar yana miqaqa
farouq din. Karbar takardar yayi yana dubawa.

Takardar mallakar wani tafkeken fili ne me fadin qafa da tsaho me
yawan gaske. Daga kai tukunna farouq yayi ya kalleshi.

"Wanne company ne haka zai sake lashe girman filin nan?" Murmushi fu'ad ya saki a
gajiye.

"Ba wani company.........mafarkina nakeso na cika na gina mana gida guda daya amma
me gidaje sassa daban daban a ciki,wanda zai qunshi duk wani jinin jadda......ina
mana sha'awar mu rayu tare yadda yaranmu zasu tashi da zumunci fiye da namu in sha
Allah". Kai farouq ya jijjiga,sai ya maida file din ya rufe.

"Wannan burina ne.....ni na tanadar mana wannan filin,bazan kuma bari ka rigani
ba......kayi haquri ayi amfani da nawa" Kai fu'ad ya girgiza yana dage glass din
motarsa

"Is too late dude........saidai ka dauki wani abun daban........amma wannan kam na
riga na gama dashi,already ma yau nayi requesting ma wani company daga china zasu
zo su fidda komai yadda nakeso ya kasance......idan ka saka hannun ka ajjiye
documents din a hannunka,saida safe" Ya fada duka a dunqule yana jan murfin motar
ya rufe abinsa sannan ya tashi motar da gudu yana fita a gidan.

Da kallo farouq ya bishi har ga bace masa,sai kawai ya jinjina kai
yana maida dubansa ga file din,sannan ya fara takawa yana wucewa cikin gidan.

Ko sanda yaje lagos baiyi baccin wahalar da yayi ba a daren. Lagos
yasan baqon guri yake,gurin da ba iyalin nashi,amma anan gurin a yanzun yasan cikin
gidanshi yake,saidai ya kasance shi daya,don haka tunda asuba ya lalubi pilot nashi
yace ya nema musu izinin tashi zuwa abuja a yau din.
Sai wajen bakwai na safe ya kirashi,a lokacin yana cikin gym,ya sauko
daga saman machine din da yake kai ya dauki wayar yana duba kiran. Zama yayi yana
goge gumin jikinsa da qaramin towel.

"Sir......mun samu izini,amma qarfe biyu daidai na rana suka bayar"

"Good.....hakan yayi,zan kasance a airport din one din in sha Allah"

"Yes sir" Ya amsa masa suna ajiye wayar gaba dayansu.

Cikin wani baqin lafiyayyen yadi me tsada da aka yiwa dinkin kaftan
ya shirya. Hularsa zuwa takalminsa dukkaninsu gray color ne,sosai yayi wani wani
irin azababben kyau,kalar baqin kayan saman farar fatarsa ta zama wani abun kallo
na musamman. Haibarsa da kwarjininsa sun ninka na koda yaushe saboda rashin
walwalar dake shimfide saman fuskarsa.

Shi da saddiq kawai suka tafiyar,sai jordan daya zama kaman aljihunsa
saboda jajircewarsa da kuma qwarewarsa a aikinsa da kuma kula dame gidan nasa.

Kasancewar juma'a ce,sai daya tsaya central mosque sukayi sallan
juma'a. Yadan samu delay kafin subar masallacin,har la'asar saboda a ranar ana wani
taro a nan a buja daya shafi qasa,kuma manyan mutanen daya jima basu

Please Login or Register in order to submit comment